An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
KISAN RUƊU
[10/5, 10:00 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAR RUƊU😭
Wa yayi kisar?
TSARAWA DA RUBUTAWA✍️
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka bani ikon rubuta abun da al'umma zasu anfana da shi.🙏
SADAUKARWA
Littafin nan tun daga farkon shi har ƙarshen shi sadaukarwa ce wa kaina ni Zainab, kuma littafin free ne, sai dai duk wanda ya karanta ina buƙatar ya sani a addu'a Allah ya biyamun buƙatuna na alheri, ya yayemun damuwa ta.🙏
GARGADI
Wannan labarin ƙirƙirarren labarine, ban yarda wani ko wata su juyamun labarina ko su ɗoramun a wata manhaja ba tare da izinina ba ko su siyar mu da labarina ba saboda haƙƙinane basirata ce saboda haka don Allah a kiyaye.
FATAN ALHERI ZUWA GAREKA
Yaya na mai ƙaramun ƙwarin gwiwa koda yaushe HUSSAINI M YERO(GARKUWAN UBAN GARIN ZAZZAU).
Page 1
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Wed may 2022
12:00am
Agogo ya buga daidai lokacin da wata yarinya ƴar kimanin shekara Sha huɗu ta fito daga wani ɗaki ta nufi ɗakin da ke kallon na ta, kallo ɗaya zaka ma yarinyar ka fahimci irin sangartattun yaran nan ne da ba'a kwaɓa musu, kofar ɗakin ta tura tana faɗin, "Momy ina jin yun..." maganar ta ne ta maƙale sakamakon ganin Mahaifiyar ta kwance cikin jini, ga kuma Kakar ta riƙe da wuƙa a hannun ta ya na ɗigar jini, nan da nan jikin Hajiya kaka ya fara rawa ta yar da wuƙar tana faɗin, "wallahi bani na kashe ta ba Aneesa ki yarda da ni.!
Hajiaya Kaka ta ƙarishe maganar cikin tsananin tashin hankali, ta nufa in da Aneesa ta ke tsaye tamkar an dasa ta, ganin Kakar ta nufo ta ne ya sa tayi firgigit ta nufi gawar Mahaifiyar na ta tana sakin wani irin marayan kuka mare sauti, shikenan Kaka kin kashe min mahaifiya kin ji daɗi dama kin dade kina ikrarin sai kin kashe Momy,! to kin kashe ta kaka kin huta, na ce kin huta ta bar miki duniyar, ki tattara dukiyar kiyi yadda kike so, kuma wallahi ki sani yau ba sai gobe ba zan kai ƙarar ki saboda duniya ta san me kika aikata."
Aneeesa na gama faɗin haka ta kama hanya ta fice daga ɗakin, in da take jin zuciyar ta gaba ɗaya ta bushe, kawai ɗaukar fansa ce a ran ta.
Durƙushewa kaka tayi a gurin tana faɗin, "Kaico na ni Hajiya Hindu mai na aikata kenan, yanzu duk duniya ba wanda zai yarda cewa bani na kashe Saudat ba.!
Kuka sosai Hajiya Hindu takeyi tamkar ranta zai fita ga wani irin tsoro da ya dirar mata.
Tafiya take tamkar mahaukaciya kafafun ta ba ko takalmi kanta ba ko ɗankwali burin ta kawai ta isa police station ɗin da ke bayan layin su a zo a kama kaka kafin ita ma ta kashe ta tamkar yadda ta kashe mata mahaifiya, tana isowa kofar get ɗin police station ɗin ta fara bugawa tamkar mahaukaciya, iya ƙarfin ta tana bugawa tana kiran police, da gudu wani ɗan sanda ya futo riƙe da bindiga yana faɗin, "waye yake bugamana get kamar zai karya.?
"Nice nan Aneesa ƴar gidan Commisioner, ƙara na kawo.!
Ta ƙarisa maganar tana ƙara fashewa da kuka, binta da kallo ɗan sandar yayi tamkar yana nazarin wani abu game da ita, sai can ya ce ma ta, "mu shiga ciki ƴan mata, bin shi tayi har zuwa office ɗin ogan su, suna shiga ya sara ma oga ya ce mai, "sir wannan yarinyar ce ta zo mana a ruɗe kuma tana wani magana da ban fahimce ta ba shiyasa na kawota gurin ka domin alamu ya nuna cewa ba a hayyacin ta take ba, ko gama rufe baki bai yi ba Aneesa ta tari numfashin shi tana faɗin, "wallahi ranka ya daɗe ina cikin hayyacina, ƙaran kaka ta na kawo ta kashemun mahaifiya yanzu haka tana can kwance cikin jini, kuma da ido na na gan ta yallaɓai.!
Ta ƙarasa maganar tana mai fashewa da kuka mai tsuma xuciyar mai sauraro.
"What! haba ƴan mata taya za'ayi ki ce kakar ce ta kashe miki mahaifiya, yanzu ina ita kakar ta ki da gawar Mahaifiyar ta ki.?
"Wallahi yallaɓai da gaske nakeyi da idona na ganta, yanzu haka tana gida na kulle gidan don kar ta gudu.
'Officers ku je da ita ku tabbatar kunyi bincike sosai sannan a kamo ita wacce ake tsargi ɗin."
"Haba yallaɓai wani irin zargi in ce ma a idona ta kashe mun mahaifiya ka ce tsargi.
"Karki damu ƴan mata binciken mu shi zai tabbatar da haka ai....✍️✍️
SHARE FISABILILLAHI
Zeey yar mutan zazzau ce🥰
[10/5, 10:06 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wane yayi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka bani ikon rubuta abun da al'umma zasu anfana da shi.
SADAUKARWA
Littafin nan tun daga farkon shi har ƙarshen shi sadaukarwa ce wa kaina ni Zainab, kuma littafin free ne, sai dai duk wanda ya karanta ina buƙatar ya sani a addu'a Allah ya biyamun buƙatuna na alheri, ya yayemun damuwa ta.
GARGADI
Wannan labarin ƙirƙirarren labarine, ban yarda wani ko wata su juyamun labarina ko su ɗoramun a wata manhaja ba tare da izinina ba ko su siyar mu da labarina ba saboda haƙƙinane basirata ce saboda haka don Allah a kiyaye.
FATAN ALHERI ZUWA GAREKA
Yaya na mai ƙaramun ƙwarin gwiwa koda yaushe HUSSAINI M YERO(GARKUWAN UBAN GARIN ZAZZAU).
Page 2
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
"Sir ya kamata a rubuta startement akan case ɗin ta don magana ce mai girma, kuma case ce ta cikin gida."
"Eh kofur ka kawo shawara, kuje da ita ku rubuta startement ɗin sai ku ɗibi yara ku tafi."
Ƙamewa yayi ya sara mai haɗi da faɗin cewa, "Ok sir."
Ficewa sukayi da Aneesa sukaje kan Kanta aka rubuta startement sannan baki ɗaya suka dunguma suka shige mota suka saki jiniya sai gidan Commisioner.
*************************
Hajiya Kaka gaba ɗaya ta haɗa zufa jikinta ba in da bai rawa, tayi da na sani yafi a ƙirga tasan tabbass yau asirinta ya tonu kuma tasan in duk duniya zasu taru ba zasu taɓa yardan cewa ba ita tayi kisar nan ba domin Aneesa ta kamata dumu-dumu.
"Wayyo ni Hajiya Hindu na bi shawaran zuciya na biye ma son rai na gashi ina da na sani.!
Bata gama rufe baki ba taji jiniyar ƴan sanda nan da nan taji cikin ta ya juye, domin Hajiya kaka duk bala'in ta akwaita da tsoron ƴan sanda, bata taɓa sanin ƙiyayyar da jikan nata take mata ya kai haka ba sai yau, ba ta gama dawowa duniyar tunanin da takeyi ba taji ana faɗin, "officer gata can ita ta kashemun mahaifiya."
A gigice Hajiya Kaka ta ɗago kai fuskarta shaɓe-shaɓr da hawaye da majinu, hannunta kuma duk jini ta fara faɗin, "wallahi ranka ya daɗe bani na kashe ta ba, zuwa nayi na ganta a cikin wannan halin ni kawai taimakon ta na zo yi in cire wuƙar, ku yarda da ni.!
"Ke tsohuwa ki mana shiru, in mun je can office zaki mana bayani Jenet. ya kira sunan wata police da take daga bakin ƙofa.
"Yes Sir.
"Arest her, in mun je can tayi mana bayani."
"Ok sir"
Jenet ta faɗa tana ƙarasowa gurin Hajiya kaka, fuskar ta a murtuke ta daka ma kaka tsawa tana faɗin, "ban hannunki tsohuwa a haka kamar mutuniyar kirki, ta ƙarasa maganar tana sama kaka ankwa a hannun ta tuni Kaka ta fara sakin fitsari, haka suka tasa kaka aka bar daga Aneesa sai wasu police guda biyu.
Kafin Safe tuni labarin mutuwar Hajiya Saudat matar tsohon Commisioner lafiya na jaha ya karaɗe jihar Kaduna, mutane da yawa sun girgiza da mutuwar Hajiya Saudat, mace mai tausayi da taimakon al'umma, tuni mutane suka fara tsinema kaka da Allah wadai da abun da ta aikata.
*************************
WASHE GARI
Gidan Alhaji Mubashir Mai lafiya ya cika da al'ummar Annabi, in da dangi da ƴan uwa da abokan arziki suka cika gida har da maƙota, in da jimami ya zama biyu ga jimamin mutuwa ga na tsargin Mahaifiyar maigidan da akeyi da kashe matar gidan, mutane da yawa wasu ba gaisuwar ta kawo su ba gulma suka zo yi.
daga dare zuwa safe gaba ɗaya Aneesa ta fita hayyacin ta, tayi kuka har ta ba uku lada, a gaban ta aka ma mahaifiyar ta wanka aka mata sutura, sai da aka jira ƴan uwan Momy suka zo daga Taraba kasancewar ta ƴar can, sunyi kuka haka wata ƙanwar momy ta rungume Aneesa suka cigaba da kuka gunin ban tausayi, haka aka ɗauki gawar Momy bai bar fitar da jini ba, dubban ɗaruruwan mutane ne suka sallaci gawar ta kowa na faɗin halinta nagari ya bita.
1:30pm
POLICE STATION
Cincirindon mutane ne suka taru a bakin police station ɗin suna faɗi, "ba zamu yarda a bamu tsohuwar nan mu kashe ta kawai.! Gefe guda wasu kuma na faɗin we need justice for Hajiya Saudat.
SHARE FISABILILLAH
Zeeey yar mutan zazzau ce 🥰🥰
[10/5, 10:00 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wane yayi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka bani ikon rubuta abun da al'umma zasu anfana da shi.
SADAUKARWA
Littafin nan tun daga farkon shi har ƙarshen shi sadaukarwa ce wa kaina ni Zainab, kuma littafin free ne, sai dai duk wanda ya karanta ina buƙatar ya sani a addu'a Allah ya biyamun buƙatuna na alheri, ya yayemun damuwa ta.
GARGADI
Wannan labarin ƙirƙirarren labarine, ban yarda wani ko wata su juyamun labarina ko su ɗoramun a wata manhaja ba tare da izinina ba ko su siyar mu da labarina ba saboda haƙƙinane basirata ce saboda haka don Allah a kiyaye.
FATAN ALHERI ZUWA GAREKA
Yaya na mai ƙaramun ƙwarin gwiwa koda yaushe HUSSAINI M YERO(GARKUWAN UBAN GARIN ZAZZAU).
Page 4
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
"Hello kuna ji na ku tabbatar kun azabtar da matar nan yadda ya kamata har sai ta faɗa muku gaskiyar abun da ta sani, domin daga bakin ta ne kawai zamu samu asalin information ɗin."
"Ok ranki ya daɗe angama, keeee! ba zaki faɗa mana gaskiya ba ko, liti, makashi ku cigaba da dukar ta har sai ta magantu."
"Angama oga."
Wata mata ce ƴar kimanin shekara Arba'in da biyar kyakkyawa da ita cikin shiga ta alfarma, amma kasancewar irin azaban da waɗan nan bayin Allah suke mata yasa duk ta fita a kamanin ta, yanzu ɗin ma dai cigaba sukayi da jibgan ta a duk gabobin jikin ta tun tana ihu har ta sume, haka suka deɓo ruwan sanyi bokiti guda suka watsa mata amma shiru bata farfaɗo ba.
"Oga anya matar nan ba mutuwa tayi ba kuwa."
"What mutuwa fa kuka ce garin ya haka ta faru,? kuna so ku ɓata mana aiki ne.!
Cewar wani bakinkirin ɗin mutumi, yana gama faɗin haka ya miƙe a ruɗe ya nufi ɗakin da suka ajiye Matar.
*************************
TARABA JALINGO
Aneesa ce zaune ta tasa abinci a gaba ta kasa kai ko loma ɗaya bakin ta, a haka har Momy Mariya ta shigo ta sameta bata san ta shugo ba.
"Haba daughter ya kamata a ce yanzu kin fawwala ma Allah kisa danganaa cikin ran ki, sannan ki gane cewa a yanzu iyayen ki addu'an ki suka fi buƙata ba kuka da kikeyi ba."
Momy Mariya ta ƙarasa maganar tana jawota jikinta sannan ta ɗauki plate ɗin abincin ta fara rarrashin ta tana bata a baki, da kyar ta samu ta ci loma biyu, haka ta dunga lallaɓata amma taki ci, haka ta haƙura ta kyaleta, wayar Momy Mariya ce tayi ƙara miƙewa tayi ta isa saman kujera in da ta ajiye wayar ta ɗauka haɗi da zama saman kujerun falon tana faɗin, "salamu alaikum, iyeeeh! Uktee ɗin ce ba'a ganta ba kamar ya.? ta ƙarisa maganar tana miƙewa fuskar ta ɗauke da tashin hankali, da sauri Aneesa ta ta so ta zo gurin da Momyn nata take tsaye ba in da jikin ta bai rawa ta ruƙota tana faɗin, "momy mai ya faru kuma wani abun ne ya faru."
Ta jero mata tanbayar a ruɗe, "Aneesa ɗauko mayafin ki zamuje Jalingo yanzu can gidan Ukhtee."
Tana gama faɗa mata haka ta juya cikin sauri, da wani kallo mai ɗauke da ma'anoni kala kala Aneesa ta bi Momy da shi.
*************************
KADUNA
12:00pm
Barister Khasheefa ne zaune a gurin da aka tanadar don ganawa da masu laifi tana jiran fitowar Hajiya Kaka, bayan kamar minti biyar sai ga ta an fito da ita wata yar sanda na biye da ita a baya, bayan sun iso ta zauna ne Barister Khasheefa ta fara gaidata, kallo ɗaya zaka ma Kaka ta baka tausayi domin duk ta fita hayyacin ta ga wani rama da tayi, gashi har yanzu ba'a ma sa ranar kai su kotu ba balle ta sa ran samun sassauci, Barister ce ta kalleta cike da tausay tana faɗin, "Hajiya ina so ki bani labarin tun farkon rayuwarki da ƴaron ki har zuwa zaman ki da marigayiya har kawo yanzu da nake zaune a gabanki."
Niasawa Hajiya Kaka tayi sannan ta share kwallan idon ta ta fara bata labari kamar haka....
*ASALIN LABARI*......
SHARE FISABILILLAH
zeey yar mutan zazzau ce🥰🥰🥰
[10/5, 10:09 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wane ya yi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka bani ikon rubuta abun da al'umma zasu anfana da shi.
SADAUKARWA
Littafin nan tun daga farkon shi har ƙarshen shi sadaukarwa ce wa kaina ni Zainab, kuma littafin free ne, sai dai duk wanda ya karanta ina buƙatar ya sani a addu'a Allah ya biyamun buƙatuna na alheri, ya yayemun damuwa ta.
GARGADI
Wannan labarin ƙirƙirarren labarine, ban yarda wani ko wata su juyamun labarina ko su ɗoramun a wata manhaja ba tare da izinina ba ko su siyar mu da labarina ba saboda haƙƙinane basirata ce saboda haka don Allah a kiyaye.
FATAN ALHERI ZUWA GAREKA
Yaya na mai ƙaramun ƙwarin gwiwa koda yaushe HUSSAINI M YERO(GARKUWAN UBAN GARIN ZAZZAU).
Page 5
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Hajiya Hindatu Mai lafiya ita ɗin mata ce a gurin Alhaji Usman Mailafiya wanda aka fi sani da Alhaji Mailafiya sanannen mutum ne a garin Kaduna in da ya kasance mutum ne mai taimakon talakawa da gajiyayyu da marashi, kuma shi mutum ne mai matuƙar haƙuri da kawaici da kauda kai, sabanin matar shi da ta kasance mace ce mai matuƙar jin kai da ɗagawa gata bata da haƙuri ko na minti guda, gata kwata-kwata bata so ta ga wani ya raɓi mijina hatta ƴan uwan shi ta rabashi da su, duk da kasancewar Auren haɗi akai musu domin da mahaifin shi da mahaifinta wa da ƙani ne, amma hakan bai hata tana wulaƙanta ƴan uwa ba, in har kai ka kasance baka da arziki a cikin dangin to ko ka zo in da take kallon banza ke rabata da kai sosai tayi bakin jini a cikin dangi baki ɗaya ba wanda zakiji ya faɗi alkairita sai sharrinta, ita ko Hajiya Hindu ko a jikinta, saboda duk yawancin zaman su sunfi yi a Abuja kasancewar mijin ta babban mai muƙamine kuma ɗan siyasa ne da ake gogawa da shi a wannan lokacin, hakan ya sa Hajiya Hindu haɗuwa da matan manyan masu faɗa aji a gwamnati nan da na idon ta ya ƙara bushewa, in dai kaga Hajiya Hindu na harka da mutum to kin kasance ke wata ce, duk wani ragama na Alhaji Mailafiya Hajiya Hindu take juyashi, gashi har lokacin Allah bai basu Haihuwa ba kusan shekaran su biyar da Aure hakan yasa Alhaji ya fara tunanin ƙara aure, saboda dangi na ta ƙorafi akan haka ana cewa ya ƙara aure, lokacin da Hajiya Hindu ta ji batun ƙarin Aure hankalinta ya tashi matuƙar gaske haka ta shiga ta fita har sai da aka fasa wannan aure, haka Alhaji ya dunga neman aure amma sai abu ya kankama sai abun ya lalace, kwatsam sai Hajiya Hindu ta tafi wani taro da Matar shugaban ƙasa ta gayyacesu zuwa UK kuma zasu ɗauki tsawon wata uku, bayan tafiyar ta da sati ɗaya Alhaji Mailafiya yayi aure kuma budurwa ya ɗauketa suka tafi Dubai honey moon sosai suka gurci amarcin su ranar da suka dawo ranar Hajiya Hindu ta sauka ƙasar cike da shauƙi da kewar mijin ta kasancewar tana tsananin son mijin nata haka yasa ta kirashi ta faɗa mai cewar gasu sun iso Nigeria tana Abuja amma yanzu zata taso zuwa kaduna, kasancewar tun kafin ta zo tayi booking ɗin jirgi zuwa kaduna, sosai hankali Alhaji ya tashi domin yasan tabbas ba zaman lafiya in har ta san mai ya aikata na yi mata kishiya da yayi ya munafurce ta.
Jirgin su na sauka ta fito tana wara ido ta ina zata ga mijin nata kuma abun ƙaunar ta, can ta hangoshi jingine da mota, gabanta ne ya faɗi ganin irin kyau da wani haske da ya ƙara, da sauri ta ƙariso gurin shi ta rungumeshi tana faɗin, "i miss u hayaty."
"Miss u too wify, ya hanya, gaskiya Uk ɗin nan ya karɓeki kinga in da kika ƙara kyau kuwa."
"Kai Hayaty har na kaika, don bakaga yadda kake kyalli bane tamkar wanda yayi sabon aure."
Gaban shi ne yaji ya faɗi jin abun da ta faɗa, gaba ɗaya sai yaji ya ruɗe, da kyar ya tattaro natsuwar shi tare da zareta daga jikin shi ya buɗe mata mota bayan ta shiga ya rufe, ya zaga ya shiga ya tada motar nan da nan sauran motocin securityn shi suka rufamusu baya, tun da suka iso gida taji gabanta na faɗi, cikin damuwa ta dubi mijin nata ta ce mai, "Minie naji duk jikina yayi sanyi tamkar wata ta raɓeka, ko wani abu ya faru bayan bana nan, duk da zumuɗin da nake in kariso gareka in faɗa maka wani albishir amma sai naji murna na ta koma ciki."
"Haba Wify karki ɓata mana farin ciki mana kin san yadda nake son farin cikin ki kuwa."
Haka dai Alhaji mailafiya ya cika Hajiya Hindu da daɗin baki har suka shiga falon ta, tun daga falo ta fara nuna mai tsantsan kewar shi da tayi, tuni suka fara faranta ma juna rai da soyayya mai tsayawa a ran ma'aurata a haka har suka shige cikin bedroom sosai suka faranta ran juna su na tsawon watannin da basu tare basu suka samu kansu ba sai yamma domin a ɗaki suka ci abinci sukayi sallah sosai ya bata lokacin shi a wannan rana a haka suka kwana suna faranta ran juna in da take faɗa mai tana ɗauke da ciki na tsawon wata uku tun bayan tafiyar ta da kwana biyu ta fahimci haka da taje Asibiti likita ya ƙara tabbatar mata da hakan, sosai Alhaji mailafiya yayi farin ciki take ya shiga mata kyaututtuka na musamman, haka ya ɗauketa suka fita tuni ya mance da zancen wata Amarya ita ko Amarya tana can tana zuba ido ta ga Alhaji ya dawo amma shiru, wasa-wasa sai da akayi sati biyu bata sa Alhaji a ido ba sai a sati na biyu ya shigo sashin ta, "haba darling yau kimanin sati biyu kenan rabon da in saka a idona na kira wayar ka kwata-kwata bai tafiya."
Amarya ta ƙarasa maganar cikin shgwaɓa da bata rai.
"Haba amaryata afuwan wallahi wani tafiya ya taso mun cikin gaggawa na tafi ban faɗa miki