Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jaridu na gidajen radio, Tv, da na yanar gizo suka Samu abun yad'awa, tuni labari ya watsu a cikin jahar Kaduna da wasu garuruwa da suke makwabtaka da ita na cewar Ashe Hajiya Saudat da Alhaji Mubasshir Mailafiya suna raye basu mutu ba. ************************* *BARAU DIKKO TEACHING HOSPITAL KADUNA* Kasancewar wannan Asibiti yana d'aya daga cikin manyan Asibitoci na gwamnati da ke cikin garin na Kaduna, can kotu ta bada umarnin a kai su Hajiya Hindu da sauran wadanda suka samu matsala na yanke ciki suka fad'i yayin zaman kotun, tuni likitoci suka rufu a kan su don basu taimakon gaggawa. ************************* UNGUWAR DOSA "Hajiya Laraba akwai babban matsala,domin da idona naga Usmanu, da Mubasshiru, ke har ma da Hasseenat da Maimunatu,! "Mun shiga uku! Yakubu har da fa su Maimunatu ka ce, tabbass lokacin tonuwar Asirin mu yayi domin dai kasan Maimunatu ta San duk wani kulle-kulle da mukayi game da kashe iyayen su ita da Haseenat." "Ni duk ba wannan ba ne ya fi damuna sai dawowar Usman da Mubasshir domin kin san kusan rabin dukiyar su yana hannuna saboda yadda na kwantar da kai na sa matar shi ta yadda da ni, sai da ya zama saura kiris in mallake duka dukiyar Sannan komai zai rushemun, wayyo Allah na kaico na, wannan shine karon farko da na so abu ban samu ba a rayuwata." "Wai kai Yakubu bakaji me nake cewa ba ne kai ta dukiya ma kake yi,? Maimunatu fa tasan komai." "Ba abun da zata tuna ni na sani." ************************* UNGUWAR RIMI. "Momy kin san wani abu na sha wuya kafin in shawo kan Hameeda fa." "Ni Abun da ke Ban mamaki wai a Ina kika san Alhaji Mubasshir yana raye.? Wash ai yau nayi kokari in har naga kun kara yawan comment tabbas zan kara yawan typing nima😂😂😂in kuma kunyi gantalellen comment kuga gantalellen typing ehe🙄🙄. Zeeey yar mutan zazzau ce🥰🥰🥰 [10/5, 10:29 AM] Zzz Yar Mama: 😭 KISAN RUDU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) Masoyana da masu bibiyar labarina, da masu kira na a waya duk Ina godiya, Alhamdulillah insha Allah na dawo kuma Zan cigaba daga in da muka tsaya, son so nake muku fans. Page 40&41 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM "Ka barni in shiga don Allah ranka ya dade ina son ganin Hajiya Saudat ne, akwai abun da zan fadamata." Tana k'arisa maganar idon ta cike da hawaye, dai dai lokacin da Kaka Mubasshir suka dawo daga Unguwar dosa zasu shiga gida kaka ta hango su suna takaddaman hana wata mata shiga, da sauri ta ce driver ya tsaya, bayan ya tsaya ne kaka ta sauko ta k'ariso gurin ta na zuwa gurin ta zaro ido jikin ta na rawa tana nuna Asabe ta ce, "Asabe ke ce!" Ita ko wacce aka kira da Asabe bin Kaka tayi da kallo saboda bata ganeta ba, "Asabe wai baki ganeni ba, Maimunatu ce fa ta gidan Alhaji Lawal k'anin Malam Yakubu na unguwar dosa," "Alhamdulillah Aunty Maimunatu Ina yaron da na baki, wlh shine sanadin dawowa na garin nan, nayi nadama nayi da na sanin abubuwan da na aikata a rayuwata shiyasa na zo don in bayyana gaskiyan lamarin, amma Ina yarinyar Hajiya Saudat din nan,? Ba ta k'arisa maganar ba Kaka ta ce, "mu shiga daga ciki Asabe wannan maganar ba ta waje ba ce." ************************* Bayan sati daya komai ya lafa an sallamo Hajiya Hindu sai dai ta kamu da ciwon barin jiki, wacce yanzu gaba daya Hajiya Saudat da Mubasshir suke kulawa da ita kullum cikin kuka ta ke tana rukon su yafiya, tun ba ma in ta kalli Mubasshir ba sak dabi'un shi irin na mahaifin shi ne, haka in ta juya ta kalli Haseenat da jikokin ta mussamman ma Ayrah da yanzu wani shakuwa ce mai tsanani tsakanin ta da Mubasshir wanda komai tare suke da shi, in da gefe guda kuwa Habibullah bai k'aunar ko ganin Hajiya Saudat, haka dai kowa ya cigaba da zama don jiran tsammanin ranar da za'a koma kotu, in da gefe guda iyayen Maza suke ta cuku-cuku yadda kotu zata sallami Shari'a tun da dai abun ya zama matsala ce ta family, amma kwamitin kotu da lauyoyin gwamnati sun ce ba su yarda ba, haka dai suka hakura akan za'a koma kotu nan da uku ga watan October. ************************* "Ina so ki sani Laraba banga wanda ya isa ya kama ni ba tare da wani kwakkwaran shaida ba, sannan Ina so ki sani kowa ya ci tuwo da Yakubu miya ya sha." "Malam Yakubu Ina ga ka samu tabin hankali ko, to bari ka ji jiya da naje gidan Mailafiya ba wanda babu shi a cikin zuri'an shi, sannan ina so ka sani jiya har Asabe na gani wannan mai aikin na gidan Yaya Lawal." Mik'ewa Malam na unguwar Dosa yayi a zabure ya ce, "wata Asaben kike nufi wacce nayi yunkurin kashewa? Innalillahi wa'innah ilaihir raji'un." Zufa ne ya fara karyo ma Malam na Unguwar dosa yayi zaman yan bori jikin shi ba in da bai rawa. ************************* "Marry kunyi kokari sosai gurin ganin an kammala aikin nan, saboda haka Ina bukatar ku tattara gaba daya bayanan saboda uku ga wata zamu koma kotu." "Ok sir." Cewar Marry bayan ta sara ma shugaban na su, ta juya ta fice daga office din na shi." ************************* "Aslamu Alaikum, Sunana Barrister Mansur ko zan iya zama.? Dagowa Barrister Zainab da Khashefat sukayi a tare suna kallon mai maganar, sosai Barrister Khashefat ta had'a rai, Barrister Zainab ce ta ce mai ya zauna, bayan ya zauna ne ya fara magana, "Ina so ku fad'I ko nawa kuke so za'a baku matukar ba ku gabatar da duk wani shaida a gaban kotu ba." "Barrister get out of my office.! Cewar Barrister Kasheefat da ta mik'e a fusace. "Ok ni kike wa tsawa, fine zaki san kin mun tsawa akan kudi ba abun da ba zanyi ba.! Ficewa ya yi daga office din ya na karada hannu. Kallon ta Barrister Zainab ta yi ta ce, "baki jin tsoron mai zai yi, kin san mutanen nan ba imani garesu ba." "Karki damu kawata da Allah muka dogara."✍️✍️ Sai fa kunyi hakuri da ni kunsan aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi kuma kwana biyu nayi busy ne😒🙏 Zeey tar mutan zazzau🥰🥰🥰 [10/5, 10:29 AM] Zzz Yar Mama: 😭 KISAN RUDU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) Masoyana da masu bibiyar labarina, da masu kira na a waya duk Ina godiya, Alhamdulillah insha Allah na dawo kuma Zan cigaba daga in da muka tsaya, son so nake muku fans. Page 42&43 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEMRAHEEEM ************************* *KOTU* Yau ta kama uku ga watan October, in da kaf familyn Mai lafiya sun hallara a kotu, in da gefe guda kuma an kamo Malam yakubu da Hajiya Laraba, bisa shaidan takardun tuhuma daga kotu, kowa ka kalla a kotun zakaga ba annuri a fuskan shi, bayan shigowar Alkali da lauyoyi da wasu daga cikin ma'aikatn kotu, kowa ya natsu. "A yau ne kotu zata cigaba da sauraran shari'a Aneesa da take karar kakan ta bisa kashe mata mahaifiya, in da kuma Shari'a tayi kokarin juyewa zuwa wata shari'an da ban, saboda haka yanzu kotu tana bukatar ganin lauyoyin wanda suke kara da wacce ake kara." "Ya mai girma mai shari'a sunana Barrister Khasheefat Ahmad lauyar wacce ake kara, tare da ni akwai Barrister Madina Abdulwahab da Zainab Abubakar." Ta k'arisa maganar tana sunkuyawa alaman girmamawa. "Sunana Barrister Mansur Tanko tare da ni akwai Barrister Ungozi ekechi da Barrister Lado Zubairu nagode." Shima ya fad'i haka yana duk'awa. Bayan alkali ya danyi rubuce rubucen shi sannan ya dago ya na fad'in kotu ta na buk'atar lauyoyi su fara gabatar da hujjojin su a gaban kotu." "Ya Mai girma mai shari'a Ina son kotu ta bani dama in fara gabatar da shaiduna ga wannan kotu mai albarka." "Barrister Khasheefat kotu ta baki dama." "Nagode ya mai girma mai Shari'a, a ranar ashirin ga watan maris ne aka kama Hajiya Hindu da zargin kisan Surikarta Hajiya Saudat, in da a yanzu nake so in wanke Hajiya Hindu daga zargin da ake mata saboda kwararan hujjojin da nake da shi, a ranar talata Ana saura kwana biyu Hajiya Saudat zata mutu, Aneesa ta ziyarci Malam Yakubu a unguwar dosa bayan dawowar ta makaranta ita da kawayenta Marry da Daniel, bayan sun isa ne suka fara maganar yadda za'a kashe Hajiya Saudat a dora ma Hajiya Hindu laifin kisan, bayan sun gama shirya komai sai ta kamo hanya zuwa gida." "Barrister Kasheefat shin kina da kwakkwaran sahidar da zai bayyanawa kotu cewar Aneesa da Malam Yakubu su suka shirya wannan kisan.? "Eh ya mai girma mai shari'a tabbass Ina da shi." Fito da wani madaidaicin recorder tayi ta kunna sai ga muryan Malam Yakubu yana fad'in, "ki saurareni da kyau ki ji ni Aneesa karki bari a samu kuskure domin zan tura killer daren jumma'a ki tabbatar kin kauda duk wani abu na zargi, sannan ki bata maganin barcin da zai sa har a shiga a aikata lahira ba wanda ya sani." "Ni fa Uncle Yakubu bana so a kashe momy gaskiya, amma ban k'aunar ganin Hajiya Hindu." "To ki sani dole Hajiya Saudat ta mutu in har kina son ganin bayan Hajiya Hindu, sannan kina son ki samu kaso mafi tsoka a cikin dukiyar mahaifinki dole ki kauda su duka domin kin san komai dadewa in har suna raye sai an san cewa ke ba yar su ba ce kinga kin ta shi a tutar babu, bakiga bayar makiyiyarki ba sannan kin rasa gata da kudi sai ki koma rayuwar talauci." Nisawa tayi ta ce, "tabbass ba zan iya rayuwar talauci ba dole kam duk su mutu." Dariya sukayi baki d'ayansu, nan dai suka tsaya akan cewa in an gama da su zasu raba dukiyar biyu kowa ya dauki kashi d'aya. Bayan tafiyar Aneesa Malam yakubu ya tuntsire da dariya yana fad'in, "yaro man kaza.! Bayan Alkali ya gama sauraran duk tattaunawar Aneesa da Malam yakubu sai Barrister Khasheefat ta cigaba da magana kamar haka, "bayan an samu labarin mutuwar Hajiya Saudat sannan an dora alhakin kisan ga Hajiya Hindu bisa kamata dumu-dumu da akayi a dakin da akayi kisar dauke da wuka a hannun ta, hakan ya assasa zargin da ake mata, bayan da na fara gabatar da bincike game da kisar sai na fara zargin Aneesa, bisa bibiyanta da nayi da ganinta da nayi zasuje makabarta cikin dare na bibiyesu naga sunje don su hako gawar Hajiya Saudat, sai akayi rashin sa'an basu tarar da gawar a gurin ba, haka dai suka juyo ni kuma tun daga nan sai na gane akwai lauje cikin nad'i hakan yasa na tura k'awata Barrister Zainab ta bibiyeta har ta samu shiga gurin Aneesa, a kwanan nan ne kuma muka gano cewa Hajiya Saudat na raye a boye a gidan Hameedat bayan k'awata tayi iya k'ok'arinta gurin shiga jikin Hameeda bayan da mukaji bayanin sirri daga gurin k'awar Aneesa Merry cewa Hajiya Saudat na boye a guest house din Hameeda saboda tayi haka ne itama don daukar fansa akan Hajiya Hindu, da kyar Barrister Zainab ta shawo kan Hameeda har ta amince ta bamu Hajiya Saudat domin zuwa kotu don tabbatar ma da duniya cewa Hajiya Hindu bata kashe Hajiya Saudat ba." Bayan duk wadan nan bayanan da shaidun da Barrister Kasheefat ta gabatar sai Alkali ya danyi rubuce-rubucen shi sannan ya dago ya ce, "in Hajiya Saudat na kusa kotu tana buk'atar ganinta." Tasowa Hajiya Saudat tayi, in da gaba d'aya kotu ta d'auki hayaniya, gefe guda kuma Malam yakubu da Anesa sun jike da zufa jikin su ba in da baya rawa, bayan Alkali ya tsawatar kowa ya natsu ya dubi Hajiya Saudat ya ce mata, "Hajiya ko zaki iya ma kotu bayanin abun da ya faru." "Eh ya mai girma mai shari'a." Nan dai Hajiya Saudat ta labarta ma kotu duk abun da ta sani. Bayan Alkali ya gama sauraranta ya sallameta ta koma mazaunin ta, sai Barrister Khasheefat ta nemi da a kara bata izini ta gabatar da wata shaidan ta na gaba kotu ta ce ta bata dama, gaba d'aya su Barrister Mansur sun zama tamkar yan kallo sun kasa tabuka komai, ko motsi kwakkwara basayi. "Ya mai shari'a in da kotu zata tabbatar da cewa tsintacciyar mage bata mage shine in har ta ji cewa Aneesa ita tasa likitan Alhaji ya ba Alhaji guba sannan in an kirashi ya tabbatar da Cewar zuciyar Alhaji ce ta buga yasa ya mutu, bayan ta fahimci cewa basu ne iyayenta ba, tare da alkawarin zata bashi makudan kudad'e, shi kuma likita yaga ba zai iya cin amanar Alhaji ba hakan ta sa suka had'a baki da Alhaji aka chanja Alhaji da wani gawa da ban shi kuma Alhaji aka fitar da shi k'asan zuwa k'asar India, yace yayi hakan ne don ya nesanta da bak'in cikin mahaifiyar shi, duk da yana tausaya ma matar shi irin halin da zata shiga." Haka dai aka kira likita ya zo ya bada na shi shaidar, sannan Alhaji Mubasshir in da in ban da kuka ba abun da Hajiya Hindu takeyi. Bayan duk gama sauraran shaidu da kotu ta yi Alkali na shirin yanke hukunci Asabe ta mik'e tana fad'in, "ya mai shari'a ai shari'a bata k'are ba."✍️✍️✍️ An dai kusa zuwa final in har naga comment gobe in Allah ya kaimu ku jini in kuma ban gani ba sai jibi😂😂🤭 Zeey yar mutan zazzau ce🥰🥰🥰 [10/5, 10:29 AM] Zzz Yar Mama: 😭 KISAN RUDU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) Masoyana da masu bibiyar labarina, da masu kira na a waya duk Ina godiya, Alhamdulillah insha Allah na dawo kuma Zan cigaba daga in da muka tsaya, son so nake muku fans. Page 44&45 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM ************************* "Ya mai girma mai shari'a tabbass Shari'a bata k'are ba nasan mutane da yawa a cikin kotun nan zasu ce meyasa na fad'i haka, tabbass Ina da dalilina na fad'in haka domin Alhaji Yakubu shi ya kashe K'anin Mahaifinsu wato Alhaji Lawal tare da sa hannun y'ar uwar shi Hajiya Laraba, dalilina kuwa na cewa haka shine akwai watarana Hajiya Hauwa uwar d'akina ta aikeni in karbo mata sako gidan Alhaji Yakubu bayan na shiga haraban gidan har na gota in da ake parking motoci sai naji ana magana sama-sama sai na labe kasancewata mace mai son jin gulma, sai naji muryan Alhaji Yakubu da Hajiya Laraba suna fad'ama wani mutumi cewa ka tabbatar ka cire burkin motan da zasuyi tafiyan da shi, bayan na gama sauraran su ne na lallaba na shige gidan zuciyata cike da tunanin suwa Alhaji Yakubu suke so su kashe a iya tunanina na kasa fahimta, bayan kwana uku da jin wannan zance sai Alhaji ya shirya shi da mai dakin shi zasuyi tafiya zuwa Maiduguri sai da ba zasu tafi da Hasseenat da Maimunatu ba saboda Dukan su suna da exam a makaranta, sai suka koma gidan Alhaji Yakubu da zama kafin iyayen su su dawo ashe tafiya ce ba ta dawowa ba, an ce sun tafi ko Abuja basu kai ba motor su tayi had'ari kasancewar kwacewar burkin motan sai gawan su aka dawo da su gida sosai mutuwar ya bigi yaran Alhaji Lawal Haseenat da Maimunatu haka dai rukon su ya dawo Hannun Alhaji Yakubu in da yake nuna musu matukar kulawa ya hana kowa ya rabi yaran, haka dukiyarsu gaba daya yana hannun shi, bayan wasu shekaru masu yawa Ina tare da su Haseenat sai kwatsam Alhaji yakubu ya ce zai Aura ma Alhaji Usman Hasseenat haka ya shiga ya fita akayi auren saboda wani manufa na shi na daban domin sai da yayi duba ya tabbatr da cewa Hajiya Hindu ba zata taba barin Hasseenat ba, bayan Auran da shekaru masu yawa aka nemi Hasseenat aka rasa kowa ya mance da babin ta haka muka dunga rayuwa ni da Maimunatu a wahale a gidan Alhaji Yakubu saukin mu daya mai aikin gidan kawata ce, kuma akwai alakar sirri tsakanin ta da Alhaji Yakubu, akwai watarana na fito daga sashin mu don zuwa cikin gidan karbo mana Abinci na bi ta kofar baya kawai naga Alhaji Yakubu da kawata Tasalla suna aikata Zina wanda hakan yayi matukar gigitani gashi sun ganni tun daga nan Alhaji Yakubu ya samun karan tsana yake fad'amun cewa tabbas na tona musu Asiri sai ya kawar da ni kamar yadda ya kauda Ubangidana hakan ya sa na tsorota Sosai da lamarin shi, bayan wasu watanni da faruwar hakan k'awata ta zo ta sameni da maganar cewa ta na da ciki kuma na Alhaji Yakubu ne ya ce sai ta zubar ko ya kasheta ita kuma ta ce ba zata zubar ba, muna cikin wannan magana ya zo ya samemu ya ce mata wato ba zata zubar ba ko to tabbass da ni da ita duka sai ya kashe mu kamar yadda yaga bayan Alhaji Lawal da Alhaji Usman karaf a kunnin Maimunatu kuma yaga shigowarta hakan ta sa ya kulle mu a d'akin satin mu d'aya ga nakuda ta kama Tasalla da taimakon Allah muka samu hanyar fita daga gidan cikin dare muka kawota Asibiti dai dai an kawo Hajiya Saudat Mai lafiya gashi lokacin bamu da ko sisi da kyar wata nurse ta karbemu da sharadin zamuyi mata abun da take so, bayan tsawon lokaci Tasallah ta haihu tare da Matar Alhaji Mubasshir sai dai Allah ya ma Tasallah Rasuwa ko ganin abun da ta Haifa batayi ba, a gaban Idon mu aka canza shegiya da mai Uba ma'ana aka dauke yar Tasallah aka ba Hajiya Saudat bisa umarnin uwar Mijin ta mu kuma aka bamu d'anta da sunan muje mu birneshi da ran shi, gaba daya jikin mu yayi sanyi domin kuka sosai mukeyi kasancewar Maimunatu ta girmeni sosai a lokacin don da tayi auren wuri irin namu na kauye zata haifi kamata hakan yasa ta ce zata rike yaron nan iya karfinta zata shiga duniya zatayi nesa daga gida domin tsira da rayuwarsu, amma komai dadewa zata dawo d'aukar fansan jinin iyayen ta, haka muka rabu Ina kuka tana kuka a cikin daren kowa ya Kama gabansa ba mu kara haduwa ba sai shekaranjiya." Jikin Alhaji Yakubu ne ya fara rawa kar ga wani gumi da yake keto mai ya fara nuna Asabe da hannun shi yana fad'in, "kina Nufin kice Aneesa y'ata ce keban....! Luuuuu yayi ya fad'i ya Sume a gurin. Ruwa aka kwara mai ya farfad'o Alkali ya fara magana kamar haka, "in Maimunatu tana kusa kotu na bukatar ganin ta da kuma ji daga Gare ta." Tasowa Kaka tayi ta iso gaban kotu ta gabatar da Kanta. "Maimunatu muna bukatar jin karin Bayani game da Maganar da Asabe tayi shin da gaske ne.? "Eh ya Mai girma Mai Shari'a da gaske ne, bayan rabuwar mu da Asabe a Asibiti...✍️✍️✍️🤪🤪 Banga wani comment ba fa da yawa ah to kuna so a gama littafin nan kuwa.? Zeeey yar mutan zazzau ce🥰🥰🥰 [10/6, 5:28 PM] Anty Hauwa: 😭 KISAN RUDU😭 Wa ya yi kisan? TSARAWA DA RUBUTAWA ZAINAB SALIHU YARIMA (sarauniyar kanawa) Masoyana da masu bibiyar labarina, da masu kira na a waya duk Ina godiya, Alhamdulillah insha Allah na dawo kuma Zan cigaba daga in da muka tsaya, son so nake muku fans. Final Page🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEEM ************************* KOTU "Eh ya mai girma mai shari'a tabbas maganar da Asabe ta fad'a gaskiya ce, bayan mun rabu da Asabe a cikin daren na nufi tashar mota, na hau mota zuwa Lagos, kasancewar akwai dan wasu kud'ad'e da ke hannuna bayan tashin motar mu haka na zura ma jaririn da ko wanka ba ai mai ba gashi Allah ya saka mai hakuri ya na ta barci abun shi ba mu muka isa lagos ba sai gurin karfe shidan yamma, tun bayan saukan mu na rasa Ina zan dosa, can dai na yanke ma kaina shawaran in nemi in da zan siya abinci in ci da ruwa in yi ma yaron wanka nima in yi sannan in rama salolin da ake bina,washe gari haka na nutsa cikin gari neman aikin da zanyi na sha wahala a ranar gashi kud'in hannuna sun kare ga shi yaron na ta kuka na rasa yadda zanyi haka na samu guri na zauna nima Ina kuka wata mota ce ta parker a kusa da mu aka zuge glass din baya wata hamshakiyar mata na gani, ta yafitoni na ta shi cikin hanzari na isa kusa da motan ta ce mun meya sa nake kuka, na ce mata yarona ne yake jin yunwa ga shi bani da kud'in siyan madara, haka matar nan ta taimake mu ta kaimu gidan ta ba abun da bata mana ba ni da Yarona bayan sati daya sai ta ce mun ta na so zatayi tafiya Dubai amma tare zamuje in dunga mata wasu aikace aikace na ce mata ba komai na Amince, bayan zuwan mu Dubai ne na gane cewa ashe wannan Hajiyar mace ce mai zaman kanta kuma safarar y'an mata takeyi dalilin jinta da nayi tana waya tana fad'in Alhaji gaskiya ka karamun farashi domin wannan fa yarinyar mai zafi ce kuma danyar goyo gareta, tuni na fahimci ciniki na akeyi saboda da turanci take maganar kuma ni na nuna mata banjin turanci a daren ranar na gudu daga gidan na ci bak'ar wahala a k'asar da ba tawa ba, har kamani akayi nayi zaman gidan yari ba irin wahalar da ban sha ba, har ta kawo na fara aikatau a gidajen masu da shi a haka na saka Mubasshir a makaranta islamiya da boko." Ta k'arisa maganar tana mai fashewa da kuka, sosai jikin kowa a kotun yayi sanyi wasu masu saurin kuka kuwa kuka sukeyi sosai saboda tausayin halin da Maimunatu ta shiga saboda Dan da bata haifa, bayan alkali ya gama tattara bayanai gaba d'aya sannan ya fara magana kamar haka, "a yau ne wannan kotu mai adalci zata yankewa duk wanda suke da Hannu a cikin wannan badakala, kotu ta yanke ma Alhaji Yakubu hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kwararan shaidu da aka gabatar a gaban kotu, in da kuma aka yanke ma Aneesa Mubasshir zaman gidan yari na shekaru goma sha biyar da horo mai tsanani bisa yunkurin kisan kai da tayi har sau biyu, sannan an yanke ma Hajiya Hindu zaman gidan na wata takwas bisa cutar da jikan ta da kishiyar ta, sannan Hajiya Laraba itama an yanke mata hukuncin zaman gidan Kaso na shekara daya bisa hada baki da ita gurin yin kisan kai, sannan kotu tayi umarni ga Alhaji Yakubu ya tattaro duk abun da yasan na su Maimunatu ne ya basu hakkin su, wannan shine hukuncin da kotu ta yanke, sanan Alkali yana jinjina ga Barrister Khasheefat tare da Barrister Zainab gurin namijin Kokari da sukayi gurin ganin sun fito da masu laifi." "Ya mai girma mai shari'a muna rokon wannan motu Mai adalci da a bamu belin Hajiya Hindu duba da halin rashin lafiya da take ciki, sannan ni a matsayina na jikan ta na yafe mata duniya da lahira, kamar yadda Mommah Haseenat ita ma ta yafe mata, nagode ya Mai Shari'a." "Bisa duba da wa'inda akai ma laifin sun ce sun yafe, kotu ta sassauta ma Hajiya Hindu a madadin zaman gidan yari zata ba da taran kud'I naira Miliyan biyar." Bayan Alkali ya kammala jawabin shi ne ya buga guduma kowa ya mike, aka tasa keyar masu laifi, nan aka turo keken marasa lafiya dauke da Hajiya Hindu wanda kunyar Duniya ta kare mata. *BAYAN WATA UKU* Gaba d'aya ahalin ne suke zaune a kayataccen falo in da kowa ka kalla yana cikin farin

Chapter 10 of 11