kinji ki daure ki ci abinci ko ba yawa ki daina zama da yunwa."
Daddah ta ƙarasa maganar tana mai kai ma Saudat abinci bakin ta, tuni saudat taji cikin ta ya wani juya bata son ƙamshin abincin ga wani amai da ya taso mata ai da gudu ta fita xuwa bakin fanfon su ta fara kwara amai tamkar ran ta zai fita.✍️✍️✍️
SHARE FISABILILLAH🙏
.Zeey yar mutan zazzau ce🥰🥰
[10/5, 10:12 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wane yayi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
Allah ka ji ƙanmu ya gafarta mana zunuban mu ka zaunar da ƙasarmu lafiya, marasa lafiya na gida da na asibiti Allah ya basu lafiya, mu da muke da lafiya Allah ya ƙaremu da lafiya mai anfani ya ubangiji kai mana rowan ciwo, Allah ka zaunar da ƙasarmu lafiya ka kawomana ƙarshen wananan kashe-kashe da muke fama da shi Ameeen ya rabbil alameen.
Page 8
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
A ruɗe Dadda ta bi Saudat ta ruƙota sai da ta gama aman gaba ɗaya ta galabaita ta fita hayyacinta, ta taimaka mata ta wanke fuska da baki ta ruƙo ta suka dawo ɗaki, ƙureta da ido Daddah tayi gaban ta na cigaba da faɗi domin ganin wasu canje-canje a tattare da ƴar tata, da kyar ta tattaro natsuwarta ta kalli Saudat ta ce mata, "Saudatun Baffa."
A ruɗe Saudat ta ɗago ta kalli Daddah don tasan babban daliline zaisa Daddah ta ambaci Sunan ta haka, bata gama tunani ba taji Daddah ta jefo mata tanbayar da ya sa gabanta yankewa ya faɗi.
"Yaushe rabon da kiga baƙon ki.?
Cewar Daddah tana kashe ɗiyar tata da ido, gefe guda kuma tana addu'ar kar Allah yasa zargin da take ma ɗiyar tata ya zama gaskiya, dagowa Saudat tayi tana kallon mahaifiyar tata cike da firgici da tsoro ga wani rawa da jikin ta yakeyi take faɗin, "Daddah yau wata uku kenan tun ana gobe Hamma zai tafi da nayi wanka."
Wani irin zabura Daddah tayi haɗi da rafka uban salati tana cakumo wuyar Saudat ta fara bata wasu lafiyayyun tagwayen mari sannan ta rufe ta da duka tana faɗin, "yau ni nashiga uku ni Hafsatu,! Saudat ina tarbiyan da muka baki? uban wa kikaje kika miƙa ma kanki har ya san ki a matsayin ɗiya mace ya ɗirka miki ciki,! yau na bani na lalace kaico na ni wata irin uwace da na gaza gurin kula da ƴata, Saudat zaki faɗa mun wanda ya miki cikin nan ko sai na kashe da duka, da ki haifemun ɗan shege.!
Gaba ɗaya Saudat ta ruɗe ga azaban ciwon da mararta yake mata ga azabar ciwon dukan da Dadda take mata, ga matsananci tashin hankali da ruɗani da ta shiga, taya zata iya kallon idan mahaifiyarta ta faɗa mata cewa wanda sukafi yarda da shi fiye da kowa shi yayi mata ciki, taya zasu yarda mutumin da bai ƙasar ma, wayyo Allah ita kaicon ta tabbass rayuwar ta tana cikin garari wai yau ita ke ɗauke da cikin shege, bata gama tunani ba taji Daddah ta jawota ta haye ruwan cikin ta ta ɗaga muciyar da ke hannunta zata bugamata sai ga Baffa, ai da gudu ya ƙariso ya daka ma Daddah wani uban tsawa da sai da tagigice ta saki muciyar da ma a ruɗe take, yana zuwa ya finciketa daga kan Saudat, in da tuni numfashin Saudat ya tafi na wucin gadi, "baki da hankali ne Daddah yara kashemun ƴa zakiyi,! in rai ya ɓaci ai hankali ke nemoshi komai ta miki ai sai ki bita a hankali ko.!
"Malam kasan abun da ƴar nan tayi kuwa,? ciki gareta fa.!
"Ciki kuma.?
Da sauri ya ƙarisa kusa da Saudat ya ɗagota yana jinginata da jikin shi yana faɗin, "bani ruwa a kofi tafa suma."
Da sauri Daddah ta ɗebo ruwa ta kawo ma Baffa ya shafama ta, tuni ta sauke ajiyar zuciya tana buɗe ido ta kalli Baffa da sauri ta rungume Baffa tana kuka tana faɗin, "Baffa wallahi ba laifina bane laifin Hamma ne."
Wani irin ajiyar zuciya Baffa yayi, saɓanin Daddah da ta zabura tana faɗin, "kina nufin Mubashir.!
Kai ta girgiza alaman eh hakane, kuka Daddah ta saka tana faɗin, "yanzu haka yaron nan zai mana, malam ya naji kayi shiru wallahi ba zan yarda ba ƴata ta haifi shege.!
"Dakata Hafsatu ƴata ba shege zata haifa ba, ɗan sunnah zata haifa domin an daɗe da ɗaura auren Mubasshir da Saudat, rashin haƙuri ne dai irin na yaran zamani yasa har ya kasa haƙura a kaimai ita, amma tun da abun ya zo da haka zanje in samu Alhaji mu san ya za'ayi in za'a turamai matar shi ne a bishi can to."
Gaba ɗaya daga Daddah har Saudat suman zaune sukayi shaye da mamakin jin abun da Baffa ya faɗa, cikin fushi haɗe da ɓacin rai Daddah ta fara magana, "haba malam wannan wani irin ɗanyen hukunci ne ka yanke, kana sanin mahaifiyar yaron nan ba ƙaunar mu takeyi ba, sannan ka ɗauki ƴata ka ba ma yaron ta kaga kenan in kasheta ma zatayi kai baka da asara."
Daddah ta ƙarasa maganar ta tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya, da sauri ta tashi ta fice daga ɗakin, tuni jikin Baffa yayi sanyi ya tashi ya bi bayan Daddah, ita kuma Saudat ta jingina tanajin wani irin a zuciyarta farin ciki zatayi ko baƙin ciki.
*************************
Fitowar Daddah yayi dai dai da juyawar Momy da duk ta gama jin abun da suke cewa, hankali tashe Momy ta koma sashin ta, ko ganin gabanta ba tayi.✍️✍️
SHARE FISABILILLAH🙏
Kuyi haƙuri yau ban samu yin typing da yawa ba saboda an mana haihuwa Aunty na ta haihu nayi ƙani💃💃
Duk mai buƙatar a tallata mai hajar shi ko wani abu nashi kofa a buɗe take a tuntuɓeni ta wannan number 08037420816.
Zeey yar mutan zazzau ce🥰🥰
[10/5, 10:13 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wane ya yi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka bani ikon rubuta abun da al'umma zasu anfana da shi.
SADAUKARWA
Littafin nan tun daga farkon shi har ƙarshen shi sadaukarwa ce wa kaina ni Zainab, kuma littafin free ne, sai dai duk wanda ya karanta ina buƙatar ya sani a addu'a Allah ya biyamun buƙatuna na alheri, ya yayemun damuwa ta.
GARGADI
Wannan labarin ƙirƙirarren labarine, ban yarda wani ko wata su juyamun labarina ko su ɗoramun a wata manhaja ba tare da izinina ba ko su siyar mu da labarina ba saboda haƙƙinane basirata ce saboda haka don Allah a kiyaye.
FATAN ALHERI ZUWA GAREKA
Yaya na mai ƙaramun ƙwarin gwiwa koda yaushe HUSSAINI M YERO(GARKUWAN UBAN GARIN ZAZZAU).
Page 9&10
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
----------------------Ɗaki Momy ta nufa ta shige can Bedroom ɗin ta, wani zufa ne ya wanke mata jiki duk da sanyin Ac da ke kunne a ɗakin nata, fara kaiwa da dawowa takeyi a cikin ɗakin na ta tamkar wacce ta samu lalurar taɓun hankali, da sauri ta zabura ta nufi gefen gadonta ta ɗauki wayar ta danna na number boka Zalumu bugu ɗaya ana biyu ya ɗauka ya fara faɗin cewa, "kar wani ranki ya ɓaci la'ananniyar Allah sa'a tana tare da mu tabbass an ɗaura auran yaron ki da ita wannan yarinyar, kuma auren su ba zai taɓa mutuwa ba sai dai in har ɗaya ya mutu ya bar ɗaya, sai dai abu ɗaya zan miki shine kawai duk wani ciki da zata samu zamu miƙa ma aljani kundalo jinin shi ya shanye sai dai yabi rariya, shegiya kin amince ko.?
"Eh boka na amince ayi kawai.!
"Hhhhhh angama annamimiya baƙar azzaluma fara mai baƙar zuciya."
Kit ya kashe wayar bin wayar tayi da kallo tayi ƙwafa tana faɗin, "da ni kuke zancen ba dai ni za'a munafunta ba, haka ta fice falon tana maganganu.
*************************
ƘASAR INDIA
Kwance yake a makeken gadon ɗakin shi sai juyi yakeyi, gabaɗaya kewar matar shi yakeyi yana tuna abun da ya faru tsakanin su, lumshe ido yayi ya buɗe saboda jin ƙarar wayar shi da ke gefen filon shi, hannu ya miƙa ya ɗauki wayar zunbur ya miƙe ganin wanda yake kira, "Baffa barka da warhaka."
"Mubasshiru kamin babban laifi kuma kwata-kwata banji daɗin haka ba, meyasa baka faɗamun kana buƙatar matar ka ba kafin ka tafi, to yanzu dai mun gama magana da Mahaifinka za'a san cuku-cukun da za'ayi a turo ma matarka nan ku ƙarata tun da ku yaran yanzu baku da haƙuri, kuma bata da lafiya muna zargin ma mun samu ƙaruwa ne."
Baffa na gama faɗin haka kit ya kashe wayar.
Wani tsalle Mubasshir ya yi ya dira a kan gadon yana faɗin wai Allah ni ɗin ashe jarumine daga buga kwallo ɗaya har ya shiga raga, sai yayi sauri ya rufe idon shi yana jin wani kunya tamkar yana gaban Baffan.
*************************
NIGERIA
"Haba Alhaji a ce ina mahaifiyar Mubasshir ayi mai auren sirri, kamarka ɗan ka ɗaya tilo a rasa wacce zai aura sai ƴar matsiyata to wallahi ba zai yuwu ba sai ya saketa ko kuma nima in aura mai wanda nake so.!
"Kin ga Hindu ki barni ban son hayaniya kai na ciwo yakeyi."
"Eyyema haka ka ce ko to shikenan mu zuba ni da kai.!
Ta ƙarasa maganar tana wani huci ta fice fuuu tamkar zata tashi sama.
BAYAN SATI BIYU
Har anyi ma Saudat Biza, yau zata tafi india ita da Daddy da Baffa, bayan jirgin su ya ɗaga zuwa india a hankali a hankali ta ji kan ta na juyawa, da sauri ta ƙanƙame Baffa saboda jiri da tsoron da suka dirar mata a lokaci guda don wannan shine karon ta na farko da ta hau jirgi.
BAYAN AWA HUƊU DA TASHIN JIRGIN SU.
Tuni Saudat ta fara jin wani azababban ciwon mara tun tana daurewa har ta zo ta kasa daurewa, wani ƙara ta kwalla wanda ya dawo da hankalin ƴan jirgin baki ɗaya, tuni masu bada taimakon gaggawa na cikin jirgin sukayo kan ta, kafin ka ce wani abu tuni jinin ya fara zuba mata,iya taimakon da ya kamata su bata domin ceto rayuwar cikin abun ya ci tura, har suka iso India nan da nan motar Asibiti ta zo aka kinkime Saudat da tuni ta fita hayyacin ta dai dai da lokacin ƙarisowar Mubasshir tuni su Daddy suka shiga motar shi suka bi bayan motar Asibitin.
Washe gari bayan an samu daman ceto ran Saudat bayan matuƙar wahalar da ta sha, sai dai an rasa abun da ke cikinta in da ita da Mubasshir suka zauna suna ta kuka, su Daddy suna lallashin su, a washegarin rana ta biyu Aunty Saudat ta dira ƙasar don kulawa da su, kasancewar ita a lokacin bata da miji mijin ta ya rasu shiyasa baffa ya ce ta zo ta zauna da su.
BAYAN SATI ƊAYA
Su Daddy sun shirya tsaf don komawa amma haka Saudat ta rungume Baffa tana ta kuka tamkar ran ta zai fita gunin ban tausayi da kyar Addah Hafsatu ta riƙeta su Daddy suka shige jirgi jikin su sanyaye Baffa yana jin kamar yayi ma ƴar ta shi kallon ƙarshe ne.
BAYAN SA'O'I HUƊU DA TAFIYAR SU BAFFA.
Su Mubasshir ne suna zaune a ƙayattaccen falon su, yayin da Saudat ta kwanta a cinyar mubasshir suna hira cikin so da ƙauna, remote ya ɗauko ya kunna TV dai dai ana wani sanarwa game da jirgin da ya tashi ƙarfe bakwai da rabi na safe a ƙasar India ya samu hatsari wanda har yanzu an kasa tantance ko akwai wanda basu mutu ba a ciki, gaba ɗayan su miƙewa sukayi a ruɗe yayin da farantin fruit ɗin da ke hannun Addah Hafsatu ya faɗi ya fashe a guje ta ƙariso falon ganin Saudat ta tafi luuuu zata faɗi.✍️✍️
AYIMUN AFUWA WALLAHI MUNA FAMA DA RASHIN WUTA SANNAN KUMA NA ƊANYI BUSY KWANA BIYU SHIYASA KUKA JINI SHIRU AMMA INSHA ALLAH ZAN DUNGA ƘOƘARI INA YI MUKU KO BA YAWA INA GODIYA DA KULAWAR KU MY FANS🥰🥰
SHARE FISABILILLAH🙏
Zeeey yar mutan zazzau ce🥰🥰
[10/5, 10:14 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wa ya yi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
FATAN ALHERI ZUWA GAREKA
Yaya na mai ƙaramun ƙwarin gwiwa koda yaushe HUSSAINI M YERO(GARKUWAN UBAN GARIN ZAZZAU).
Page 11
BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Kafin dare Mubasshir ya gama cuku-cukun yadda za'ayi su tafi gida Nigeria, don dama jirgin yafi kusa da Nigeria shiyasa aka ƙarasa da gawarwakin wa'in da aka samu, wasu ko sam ba'a ga gawarsu ba ma, bayan Mubasshir ya dawo da ƙyar suka samu jirgin da zai tafi gobe da ƙarfe biyu.
*************************
"Don Allah Hindatu kiyi haƙuri komai muƙaddarine daga ubangiji, kuma dole kowa zai mutu."
Cewar wata tsohuwa da take riƙe da momy.
"Guggo baki san in da nake ji bane, kwata-kwata fa ba'a ga gawar Alhaji ba, bamu da tabbacin ya mutu ko yana raye, kuma a wani hali yake ciki, ta ƙarisa maganar cikin rushewa da wani sabon kuka.
Gefe guda Daddah ne ta tasa gawar Baffa wanda ko kwarzane baiyi ba, ban da addu'oi da salati ba abun da takeyi in da tuni ƴaƴan ta da suke Taraba sun iso gabaɗayan su, kowa yana zaune sanye da hijabi da tasbaha a hannun su.
Haka aka gama zaman makoki da komai ba wani labarin Alhaji.
Tun daga lokacin Hajiya ta buɗe wani tashen rashin mutumci in da ta ce ma Daddah su tashi, haka daddah tana ji tana gani ƴaƴan ta suka ɗauketa suka maidata Taraba suka siyamata gida mai kyau madaidaici, sai dai ta tafi tana matuƙar kewan ƴar ta da irin halin da zata shiga a hannun azzaluman uwar mijin ta.
*************************
BAYAN SHEKARA GOMA
Wata hamshaƙiyar mata ce fara tas da ita zaune a wani ƙayataccen falo hannun ta riƙe da littafin hisnul muslim tana karanta addu'oi sai da na mata kallon tsaf na gane Saudat ne wacce yanzu ta zama Hajiya Saudat, bankaɗo kofar falon akayi ba ko Sallama Hajiya Hindatu ne ta shigo ta ƙara gogewa irin na manyan mata masu ji da Naira don tun bayar rasuwar alhaji bata kara aure ba ita ta cigaba da juya dukiyar shi har lokacin da ta mallaka ma Mubasshir wani kaso ya fara gina Asibitoci kasancewar karatun likitanci yayi, har ya zo ya zama Comissional lafiya, in da ya ƙara tara dukiya ninki abun da mahaifiyar shi ta bashi, har yau kuma Hajiya Hindatu ba ta kyale Saudat ta haihu ba, don in dai zata samu ciki matuƙar ta san da shi to sai ta ɓarar, haka ta dunga aura ma Mubasshir mata kala kala suna fita suna barin gidan kuma basu taɓa haihuwar ba kullum Hajiya sai ta zo gidan kasancewar yanzu ba gida ɗaya suke zaune ba, hakan ta kasance yau ma ta shigo ta tsaya ta gama ƙarema falon kallo tana yamutsa fuska, yayin da gefe guda Saudat ta sauka daga kan kujera ta duƙa tana faɗin, "Momy sannu da zuwa ki zauna mana."
Ta ƙarisa maganar tana sunkuyar da kai.
"To annamimiya mai ladabin munafurci, juya wacce ta ƙasa haihuwa sai dai ta ci tai kashi, inna auro mai masu haihuwa kiyi kicin-kicin ki koresu to ki sani wlh nine ajalinki shegiya ƴar matsiyata irin maita.!
Kuka sosai Saudat takeyi in da sabo yaci a ce ta saba da masifar uwar mijin nata amma har yau ta kasa, ta zugunne har Alhaji ya shigo ya ganta a wannan halin tuni ya gane mai ya faru, ajiye jakar hannun shi yayi ya dago matar shi ya rungume ya fara rarrashin ta suka shige ɗaki tuni labari ya sanja a ranar aka samu cikin Aneesa amma ba wanda yasan da haka.
*************************
BAYAN WATA TARA
Nakuɗa sosai ya taso ma Saudat kasancewar Hajiya Hindu bata ƙasar ta tafi wani harkan kasuwanci a Dubai tsawon wata shida, kuma cikin bai bayyana ba sai da ta kusa haihuwa aikuwa sosai Alhaji Mubasshir yayi farin ciki ranar da Saudat zata haihu ranar hajiya ta dira a Nigeria, hankalinta yayi matuƙar tashi jin cewa Saudat zata haihu nan da nan taje ta haɗa baki da Nurses ɗin da kuɗi masu dumbin yawa akan tana so a kashe duk abun da zata haifa, lokacin ita kuma saudat tana can tana fama da nakuɗa in da har ta fita hayyacinta, kasancewar ita da wata mata ce suke naƙudar a tare sai da yadda ta lura matar nan kamar wata ƴar duniya gashi tun da aka kawosu ba wanda taga ta zo kusa da Matar.
Bayan wasu awowi ta haifi sankacecen ɗan ta namiji nan da nan Nurse ta kira hajiya ta shaida mata cewa ta haihu amma namiji amma yanzu haka ta sume, haka ta ce su ɗauki yaron suje su yar da shi can in da ba zai taɓa dawowa garesu ba, in da hali ma a bar ƙasar da shi, tun da tace matar da take kusa da ita itama ta haihu ƴar ta rasu itama ta rasu to a mayarma da Saudat matacciyar ita kuma wancen a nemo gawan wani jaririn a ce nata ne, haka ko akayi Saudat na farkowa ta tarar da wannan jaririya a ƙasa amma tamkar bata da rai wata nurse ce ta shigo ita bata san meke faruwa ba tana zuwa ta ɗaga ƴarinyar taga alamun numfashi a tare da ita nan ta fara bata taimakon gaggawa nan da nan yarinya ta canyara ihu ashe wahala ce yasa tayi tamkar ta mutu, nan da nan aka gyarata aka fito da uwar da ƴar zuwa ɗakin hutu, farinciki gurin Alhaji Mubasshir bai faɗuwa, tun daga asibiti ya fara rabon kuɗi har aka sallamosu, sai dai wani abun mamaki yarinyar kwata-kwata batayi kama da iyayen ba amma su basu ga haka ba ko ƙaɗan sun ɗauki son duniya sun ɗora mata.
Anyi suna na kece raini tamkar ba'a san zafin naira ba in da gefe guda kuma Hajiya Hindu tamkar zata mutu don baƙin ciki, gashi da hannun ta ta ja ɗan ta zai raini ƴar da ba'a san aslinta ba gashi ba daman ta tona tamkar ta tona ma kanta asiri ne.
*************************
BAYAN SHEKAR BIYAR
Aneesa ta ta so akwai izza da isa, gata ba ta jin magana ko kaɗan duk da hajia Saudat tana iya ƙoƙarin ta na gurin bata tarbiyan da ya dace amma duk da haka abun nata gaba gaba yakeyi, gashi ta tsani taga an zo gurin mahaifiyar ta neman taimako ta dunga hararar mutane kenan, gata sangartacciya ce ta ƙarshe ga rashin ƙoƙari a makaranta kullum in taje makaranta sai ta ɗauko magana, tun tana shekara huɗu ta iya ta ɗauki ƙuɗi a ɗakin mahaifiyar ta, kwata-kwata basa shiri da Kaka kasancewar kullum tana ganin kaka tana ma Momyn ta Masifa, ita kuma duk wannan halaya nata bata taɓa yarada a ci zarfin mahaifiyar ta ta kyale hakan yasa in Hajiya tana faɗin ita ce ajalin Saudat, itama sai ta ce in har ta girma sai tayi ajalin hajiya kaka, momyn ta ta sha buge mata baki akan haka tai mata faɗa sosai ta ce kar ta ƙara faɗa, amma bashi zai sa in ta ji Hajiya Hindu ta zo tana masifar ba ita ma ta zo ta yi mata har ta kai Aneeesa tana ƴar shekara biyar Hajiya Hindu ta na shakkar ta.
*************************
BAYAN SHEKARA GOMA SHA UKU
Aneesa ce ta dawo makaranta sanye da Unifom kasancewar ta yarinya mai saurin girma zaka ɗauka ƴar shekara sha takwas ne ita domin komai na alaman budurci ya bayyana a tare da ita, jakar hannun ta ta jefar a kujera hijab ɗin ta ta cire ta wurgar haka takalmin ƙafar ta da safa kujera ta haye ta zauna ta fara kwalama mai aikin su kira, "Harira! Harira!.
Da gudu wacce aka kira Harira ta fito tana amsawa ta zo ta duƙa tana faɗin, "sannu da zuwa Hajiya, bata ida rufe baki ta ɗauke ta da mari tana nuna ta da yatsa, "bance in na dawo in dunga samunki a falo kina jirana ba, da me mutum zaiji da kwalamiki kira ko da yunwar da ya kwaso dallah ki ciremun kaya sannan ki ɗauko min wasu sannan a kawomun abincina, jiki na rawa harira ta fara cire mata kayan makaranta daga ita sai bes da wando gajere iya cinya haka harira ta tattara kayan ta shige ciki ta dawo da wasu kaya a hannun ta ta nufota da shi zata samata, "ke malama dakata maida waɗan nan kayan ba zan sa su ba.
Sai da ta kwaso kaya fin kala takwas tana cewa ta maida sannan ta samu wanda zata sa.
*************************
Kwatsam wani dare suka tashi suka tarar Alhaji ya rasu ba ciwo ba komai Momy da ƴar ta Aneesa sun sha kuka tamkar zasu bishi haka Hajiya Kaka in da gaba ɗaya tayi sanyi ta rasa miji ta rasa ɗan ta mafi soyuwa a ran ta mai tsananin biyayya a gareta.
*************************
BAYAN SHEKARA SHA HUƊU
Idon Aneesa ya ƙara buɗewa in da yanzu take Sss one ta kai bata jin maganar kowa kaka kuwa ta maida ta tamkar kishiyar ta kullum cikin faɗa suke kasancewar yanzu gida ɗaya suke zaune, in da Hajiya Saudat sosai ta zama uwar marayu ita ce gina Masallatai da islamiyu da asibitoci tana cewa ladan ya kai kabarin mijin ta mafi soyuwa a gareta.
Shine kwatsam watarana da daddare ina kwance a ɗaki na ji kamar motsi hakan yasab na fito da sauri, ina zuwa na nufi ɗakin Saudat kasancewar naga kofar ta a buɗe, ina shiga na ganta cikin jini da wuƙa a cikin ta, gaba ɗaya na ruɗe na ƙarisa da sauri ina ƙoƙarin cire mata wuƙar ta cika.
Hajiya Hindu ta ƙarisa maganar cikin matsanancin fashewa da kuka tana faɗin Tabbass alhakin Hassenat ne da ɗana da na hanashi jin daɗin rayuwa har ya koma ga Allah sanadin bugawar da zuciyar shi tayi lokaci guda, ga alhakin Saudat da na rabata da ɗan da ta haifa na sata riƙe shegiya wacce bata da asali."
Sosai Hajiya Hindu ke kuka.
"Barister lokacin ku yayi fa har an ɗan kara muku lokaci."
Nisawa Barister Khaseefa tayi ta miƙe ta ɗauki jakar ta tana mai kallon Hajiya.
"To Hajiya nagode da haɗin kan da kika bani, insha Allah zanyi iya bincike na don gano gaskiyar lamarin, in kuma ina da buƙatar sanin wani abu zaki ganni na dawo."✍️✍️✍️✍️
Duk mai buƙatar a tallata mai hajar shi yana iya tuntuɓata ta wannan number 08037420816
SHARE FISABILILLAH🙏🙏
Zeeeey yar mutan zazzau ce🥰🥰
[10/5, 10:14 AM] Zzz Yar Mama: 😭
KISAN RUƊU😭
Wane yayi kisan?
TSARAWA DA RUBUTAWA
ZAINAB SALIHU YARIMA
(sarauniyar kanawa)
GODIYA
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kafa alƙalamina domin rubuta wannan labari, ya ubangiji ka haneni rubuta ba dai-dai ba, ka