Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ko arba'in sai sarki yakwanta rashin lafiya har sai an nemo likitoci sun kawomasa daukiwani lokacinma sai bokaye sun bada taimako sannan yake samun lafiya.Duk irin zaluncin da sarki yasabayi na kwacewa talakkawa dukiyarsu ya daina kuma har tsawon shekara ukku bai kara yiwa wata budurwa fyadeba.Gaba daya mutanen birnin kufa sai da suka cika da matukar mamaki bisa ganin halayyar sarki ta sauya a lokaci guda.Kai bama mutanen birninba hatta sarakunan sauran kasashe dake makwabtaka dashi.Dama dukkan sarakunan suna tsananin tsoron sarki lafaru suna biyayyar dole agareshi domin duk shekara sai kowannensu yakawo haraji maiyawa gami da bayi. Lokacin da'aka sami shekara ukku da samun sauyin al'amura ga sarki lafaru sai wani sarki da ake kira Nurbas wanda ke mulkin kasar zaruf yakawo haraji da bayi. Dama can shi sarki nurbas gawurtaccen matsafine mai taurin kai kuma yanada zakwakuran mayaka ababan dogaro.A lokacin da sarki lafaru ya aika masa da sakon ya aiko da haraji sai yayi taurin kai ya bijirewa umurnin.Nan take sarki lafaru yayi shirin yaki 185 TASKARNOVELS.COM.NG shi kadai ya shiga birnin zaruf ya rinka ragargazar dakaru har sai da ya shiga cikin fadar sarki Nurbas aka rasa wanda zai iya kawar dashi.Koda sarki Nurbas yaga karfin tsafinsa yaki yayi tasiri akan sarki lafaru kuma ya tabbata kasheshi zaiyi ya mallake kasarsa sai ya fadi kasa yana kuka da tuba yayi ta neman gafara,kuma yayi alkawarin cewa duk shekara zai rinka bayar da harajinsa da bayi sama dana kowanne sarki.Koda ganin yadda sarki Nurbas ya wulakanta agaban fadawansa da jama'arsa kuma ya mika wuya sai sarki lafaru yafasa kasheshi ya bushe da dariya yafice daga cikin fadar yatafi abunsa.SARKI Lafaru na zaune a fadarsa,fadawa sun kewayeshi ana tafiyar da harkokin mulki sai ga manzo daga kasar zaruf dauke da wasika.Da zuwan manzon sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa cikin alamun tsoro duk jikinsa na karkarwa ya mikawa magatakarda wasikar shikuma ya warware wasikar yafara karantata a fili kamar haka; Takarda daga sarki mai cikakken iko wanda a halin yanzu ya sami yancinsa Sarki Nurbas na birnin zaruf. Zuwa ga makaskancin sarki wanda a halin yanzu yazama akuya ba kuraba..."Koda magatakarda yazo nan a karatun wasikar sai muryarsa ta sarke kuma 186 TASKARNOVELS.COM.NG hannunsa yakama karkarwa saboda tsoron kada sarki ya huce haushi akansa bisa abinda yakaranto na kaskanci.Lokacin da sarki lafaru yaji irin wannan cin mutunci da sarki Nurbas yayi masa a wasika sai ya kamu da tsananin takaici yaji kamar zuciyarsa zata faso kirjinsa ta fado kasa,yatuna irin tsananin tsoronsa da sarki Nurbas keji ada ,amma yanzu shine harda zaginsa cikin wasika.Cikin karfin hali da barazana sarki lafaru ya dakawa magatakarda tsawa yace maza kaci gaba da karanta wannan wasika muji karshenta nan take magatakarda yaci gaba da karatun wasika muryasa na rawa kamar haka;Yakai sarki lafaru mai birnin kufa kayi sani cewa a halin yanzu tsirara nake kallonka babu sutura a jikinka,dalili kuwa kayi sake har sharlis 'yar boka Narwas ta karya alkadarinka.Nasan cewa kamanta da kowanene boka Narwas to kayi saurare dakyau yanzu zan tunamaka shi domin kasan cewa tsohon abokin gabarkane wanda ya mutu da bakin cikin daka turamasa amma kuma sai gashi 'yarsa sharlis zata dauki fansa akanka. Nan take magatakarda yaci gaba da karatun wasika muryasa na rawa kamar 187 TASKARNOVELS.COM.NG haka;Yakai sarki lafaru mai birnin kufa kayi sani cewa a halin yanzu tsirara nake kallonka babu sutura a jikinka,dalili kuwa kayi sake har sharlis 'yar boka Narwas ta karya alkadarinka.Nasan cewa kamanta da kowanene boka Narwas to kayi saurare dakyau yanzu zan tunamaka shi domin kasan cewa tsohon abokin gabarkane wanda ya mutu da bakin cikin daka turamasa amma kuma sai gashi 'yarsa sharlis zata dauki fansa akanka.yakai wannan sarki kayi tunani izuwa kimanin shekaru ashirin baya,a shekarar daka hau mulki bayan mutuwar mahaifinka sarki Hurdas. bayan an nada Sarki lafaru a matsayin sabon sarki,akwai wata rana da ya tafi rangadi izuwa kauyukan kasarsa har tsawon kwana arba'in yana kewaye kauyukan kamar yadda kowane sabon sarki keyi idan ya hau karaga bisa al'ada.Kauyen daya ziyarta na karshe shine kauyen Bairul. Da isarsa kauyen sai ya umurci dukkan attajiran garin dasukawo masa gaba dayan dukiyarsu.gaba dayansu sai suka cika umurnin face mutum daya wani takadarin boka mai suna Narwas wanda kowa ke shakkarsa a garin.Boka Narwas bai amsa kiransa ba kawai sai yayi zamansa a gidansa kuma ya aiko gidan hakimin yace a gaya masa 188 TASKARNOVELS.COM.NG cewa bazai amsa kiransaba kuma bazai bada komai ba daga cikin dukiyarsa,koda yaji wannan batu sai ya harzuka yasa akayi masa jagora zuwa gidan boka Narwas Da zuwansa ya iske boka Narwas a kofar gidansa yarike kugu yana jiransa domin yasan cewa lallai yana tafe,saboda boka narwas ya yarda da kansa a fagen tsafishiyasa yake ganin bazaka iyayi masa komai ba kuma a tunaninsa zai iya hallaka sarki lafaru farat daya. Da zuwan sarki lafaru sai boka narwas yafara watsa masa wutar tsafi,bisa mamaki sai yaga gashi dai wutar ta zuba jikinshi amma sai takasa konashi.Cikin fusata yaci gaba da watsa masa abubuwan sihiri kamar kibiyoyi,macizai da kunamaiamma duk sai suka ki yin tasiri akansa.Nan take sarki lafaru ya shako wuyansa da hannu daya ya dagashi samasai gashi yana kakarin mutuwa idanunsa sukayi kulu-kulu kamar zasu fado kasa kafafunsa na wutsil-wutsil a sama,kawai sai ya fyadashi da kasa ya baje wanwar a sume.Kafin boka narwas ya farfado daga dogon suman dayayi sai yasa aka shiga gidansa aka kamo iyayen boka narwas da matarsa gami da wata kanwarsa kyakkyawar gaske mai suna lasirat dakuma 'ya'yansa guda ukku kananan yara biyu 189 TASKARNOVELS.COM.NG mace daya.A wannan lokaci matar narwas tana dauke da tsohon ciki haihuwa ya kogobe,amma saboda wulakanci a kasa dakarunsa suka rika janta suna fincikarta tana ihu tamkar suna jan mushe Bayan anzo da iyalan boka Narwas gaban sarki lafaru sai yasa aka daddauresu a jikin dirkar gini,shikuwa boka Narwas yasa aka dagashi sama aka daureshi sannan aka watsa masa ruwa ya farfado.Koda Narwas yabude idonsa yatsinci kansa daure ajikin dirka kuma yaga dukkan iyalansa da iyayensa a daure sai hankalinsa ya dugunzuma yakurma uban ihu yafara kokarin kwance daurin da akayi masa da karfin tsafi amma sai tsafin yaki yayi tasiri.Koda ganin haka sai sarki lafaru ya bushe da dariyar mugunta sannan ya murtuke fuskarsa kamar an aiko masa da sakon mutuwa yakama gashin kan narwas ya finciko baya da karfi,yayi ihu sakamakon zafin dayaji,kawai sai ya tofamasa yawu a fuska yabude baki cikin kakkausar murya yace.;Ya kai wannan makaskancin boka kayi sani cewa kayi babban kuskure har da kake zaton zaka iya bijire mini.Yanzu kayi laifi har guda biyu.Na farko ka karya dokar kasata kayi tsafi wanda hukuncinsa kisa ne akanka.Na biyu nabaka umurnin ka kai min dukiyarka kaki 190 TASKARNOVELS.COM.NG kaiwa.Ka sani cewa kaine mutum na farko daya kawo raini a cikin mulkina kuma yakarya dokata saboda haka bazan kasheka ba sai dai na nuna misali akanka domin ka zamo darasi akan masu sha'awar jaraba taurin kai a garemu.Lallai zan dandana maka azaba irin wacce ba'a taba dandanawa wani ba kuma zan cusa maka bakin ciki a zUciyarka wanda har karshen rayuwarka bazaka sami natsuwa da kwanciyar hankali ba".Koda gama fadin haka sai sarki lafaru ya zaro wata sharrbebiyar wuka daga kugunsa sannan yayiwa mahaifin boka Narwas da mahaifiyarsa kisan wulakanci ta hanyar yanke makogoransu yanka daya a lokaci guda.Take jini yai tsartuwa daga wuyansu ya wanke fuskar boka Narwas.Narwas ya tsandara ihu kuma ya fashe da matsanaicin kuka.Yana cikin wannan bakin cikine sarki lafaru yakamo wadannan 'ya'ya nasa guda uku,wato kananan yara ya take wuyansu da kafafunsa daya bayan daya suna ihu yayi musu yankan rago.Gaba daya mutanen dake wurin sai da suka zubar da hawaye do tausayi.Shi kuwa sarki lafaru ko ajikinsa wai an mintsini kakkausa. Yayin da boka narwas yaga irin kisan wulakancin da yayiwa 'ya'yansa,sai nan take ya haukace 191 TASKARNOVELS.COM.NG yakama sambatu.Hakan baisa sarki lafaru ya hakura ba,sai ya kamo wannan kanwa tasa kyakkyawar budurwa,wato lasirat ya maketa ta fadi kasa sumammiya.A gaban jama'a ya murkusheta ya biya bukatarsa da ita,sannan itama yayi mata yankan rago.Tun sa'adda matar Narwas taga yanda sarki lafaru ya kashe 'ya'yanta ukku sai ta sulale kasa sumammiya bata farfado ba sai bayan yakashe lasirat.Ai kuwa tana bude ido tayi arba da gawar lasirat a gabanta sai ta kwala ihu.Nan take nakuda tazonata.kawai sai sarki lafaru ya kura mata ido yana ta kyalkyala dariyar mugunta kuma yahana kowa ya taimaka mata.Sai da ta shafe sa'a biyu tana nakuda sannan ta haifo tsaleliyar 'ya mace a gaban kowa.Da kanta ta yanke cibi ta goge jinin jikin Jaririyar.Jaririyar ta kama tsala kuka har ta yunkura zata baiwa jaririyar nono sai sarki lafaru ya kwace jaririyar daga hannunta ya cillata cikin wata katuwar kwata wacce ke cike da ruwa.Nan take jaririyar ta nutse izuwa can kasan kwatar kuma gashi ruwan kwatar mahada ne na kogin garin.Koda matar Narwas taga ya jefa 'yarta cikin wannan kwata sai ta sulale kasa sumammiya.Da ganin haka sai sarki lafaru yasa aka dinga yiwa boka 192 TASKARNOVELS.COM.NG Narwas azaba iri-iri har sai da ya suma sau bakwai sannan aka kyaleshi.Nan take sarki lafaru yasa aka yashe komai na gidansa ba'abar masa ko tsinke ba har dabbobisa sai da aka kwashesu daga cikin garke,gonakinsa kuwa yasa aka konesu sannan aka gine wajen aka rufe ba shiga ba fita.A sannanne sarki lafaru ya hau dokinsa yai tafiyarsa izuwa birninsa na kufa.Yakai wannan sarki,tun daga wannan lokaci baka sake tambayar labarin boka Narwas ba. Babban kuskuren da kayi shine barin Narwas a raye. Bayan wata ukku da haukacewar boka narwas wani dan uwansa yazo daga wata kasa dabam yayi masa magani ya warke daga cutar hauka.Wannan 'ya tasa jaririya da aka jefa cikin kwata bata mutuba.Ruwa yataso da ita sama. wani masunci ya tsinceta ya reneta har izuwa tsawon shekara bakwai a wannan lokaci tuni Narwas ya kara samun ilmin tsafi ninkin wanda yake dashi a da sau dubu kuma yayi bincike yagano 'ya tasa da aka jefa cikin kwata bata mutu ba tana hannun wannan masunci don 193 TASKARNOVELS.COM.NG haka sai yaje ya karbo 'yarsa yaci gaba da renonta kuma ya bata dukkanin sihirin tsafinsa ya horar da ita bisa tafarkin dazata dauki fansa akanka.Ba wata bace wannan 'ya tasa face SHARLIS Budurwar dakayiwa fyade bayan dakarunka sun kashe mahaifinta da mahaifiyarta sun kawota fadarka.Dama boka Narwas yagayawa sharlis cewa alkadarinka bazai taba karyewaba sai a ranar dakayi mata fyade daga wannan rana sadaukantakar ka zata gushe kuma tsafi zai dinga tasiri a jikinka sakamakon sihirin dake cikin jikinta yafi naka.Nasan zakayi mamaki bisa yadda akayi duk nasan wannan al'amari,amma idan kayi la'akari da cewa nima tsohon bokane mai nacin bincike da yawan neman karin ilmi bazakayi mamaki ba.Yakai wannan sarki kayi shiri domin gani nan tafe izuwa kasarka nan da cikar kwana arba'in.Lallai idan nazo sai na kwace duk dukiyar daka mallaka abakacin harajin danayi ta baka a baya bisa dole kuma sai na kaskantar dakai kazama bawa mai kula da turken dokina.Bazan kasheka ba sai dai ka jira ranar da sharlis zata dauki fansa a kanka bisa abinda kayiwa mahaifinta.Ina yi maka albishir da cewa a halin yanzu sharlis na tare da danka data haifa 194 TASKARNOVELS.COM.NG dan shekara ukku kuma tasa masa suna shaddad.Nasani cewa tunda kasa aka kai sharlis bangarenta a cikin gidan sarautarka baka taba ziyartarta ba kuma baku sake ganin juna ba.Lallai abinda kake gudun ya faru sai ya faru,wato sai ka haifi dan da zai gajeka kuma sai ya fika shuhura a duniya kuma shine zai zamo babban makiyinka wanda zai dauki fansar abinda kayiwa kakansa.Lokacinda magatakarda yazo nan a karatun wasikarsa sai kawai aka ga sarki lafaru ya bushe da mahaukaciyar dariya.Cikin shammace ya zare takobinsa ya sare kan wannan manzo da ya kawo wasikar Nan take sarki lafaru yasa aka rubuta wasikar raddi,a cikin wasikar ya karyata duk abinda sarki nurbas yayi bayani cewar har yanzu alkadarinsa bai karye ba,sadaukantakarsa na nan kuma yana jiran isowarsa su gwabza yaki domin a bambance tsakaninsu a gane wanda yake karya.Da aka gama rubuta wannan wasika sai aka hadata tare da gawar manzon daya kawo wasikar farko a cikin akwati aka tafi dasu izuwa birnin zaruf.Sa'adda fadawan sarki lafaru da sauran jama'ar gari suka ji hukuncin da sarki lafaru ya yanke akan bayanin da wasikar sarki Nurbas yayi saisuka shiga wasi-wasi.Wasu suka 195 TASKARNOVELS.COM.NG fara tunanin cewa har yanzu alkadarin sarki lafaru bai karyeba duk da cewa yanzu ana yin tsafi kasarsa kuma yana yin rashin lafiya sabanin da.Dalilinsu na yarda da hakan shine inda sarki lafaru yasan duk abinda sarki Nurbas yayi bayani gaskiyane.To da ba zai taba yarda ya mai da masa da wasikar raddiba. Abinda basu sani ba shine,sarki lafaru kundunbala kawai yayi,saboda taurin zuciya da ki fadi ne irin nasa yaki yarda ya nuna gazawarsa domin kada talakkawansasu sami damar da zasu ci mutuncinsa su wulakantashi bisa mulkin zalincin da ya yi musu.Amma a zahiri yaji a jikinsa cewa duk irin jarumtakar da yake da ita a da yanzu bashi da kaso biyu cikin kaso darinta.Lokacinda fada ta watse sai mutanen gari suka tafi suna fadin albarkacin bakinsu bisa abinda ya faru a fada dangane da wasikar sarki Nurbas ya aiko da ita da kuma wasikar raddi wacce sarki lafaru ya aika masa da ita. Wannan abu daya faru sai ya jefa shakku a zuciyar dakarun yaki na kasar ya zamana cewa basuda tabbacin cewa zasu sami nasara idan akayi wannan yaki da birnin zaruf,kuma basu da tabbacin bazasu samu nasararba.Dole ne su zuba ido kawai su jira ranar daza ayi wannan 196 TASKARNOVELS.COM.NG yaki sugani idan har yanzu jarumtakar sarkinsu na nan tunda shine abin dogaronsu. Al'amarin sarki lafaru kuwa,bayan fada ta watse sai ya shiga cikin turakarsa ya zauna yayi tagumi cikin tsananin bakin ciki,yana tunani da mamaki bisa yanda al'amura suka sauya masa. MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part M Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Al'amarin sarki Laffaru kuwa,bayan fada ta watse sai yashiga cikin turakarsa yazauna yayi tagumi cikin tsananin bakin ciki,tunani da mamaki bisa yadda al 'amurra suka sauya masa a cikin shekaru ukku kacal.Nan take ya tuno da irin tsananin jarumtakarsa ta yanda shi kadai yana iya yakar gari guda ya cisu da yaki,ya tuno da irin yadda gaba dayan sarakunan dake 197 TASKARNOVELS.COM.NG kasashen da suke makwabtaka suke tsananin tsoronsa tare da yin biyayya a gareshi amma gashi yau an wayi gari an sami daya daga cikinsu yana aiko masa da zagi dakuma gadarar ayi yaki.Nan take hawayen takaici ya zubo masa.Sarki Lafaru yaci gaba da tunani bisa makasudin faruwar wadannan al 'amurra wato haduwarsa da sharlis.Nan take bayanin wasikar sarki Nurbas yasake fado masa a rai cewar a halin yanzu Sharlis ta haifae danta kuma 'dan shekara uku a duniya sannan zai zamo abokin gabarsa ya dauki fansar abinda yayiwa kakansa.Sarki Lafaru bai san sanda zancensa na zuci ba ya fito fili ba ya ce, "Ya za a yi 'dan cikina yazamo abokin gabata?Lallai idan nabari wannan yaro yagirma nagama tozarta a duniya.Yanzu ya za a yi na salwantar da rayuwar sharlis da wannan yaro data haifa kuma ya za ayi nayi mugun tanadi bisa wannan yaki dazamuyi da sarki Nurbas nan da kwana arba 'in na sami nasara akansa don natsare mutuncina da darajata a idanun jama'ata da sauran sarakunan kasashen makwaftaka? " Lokacin da sarki Lafaru yazo nan a tunaninsa sai hankalinsa ya dugunzuma fiye da komai ya tabbatar da cewa yana cikin TSAKA MAI WUYA 198 TASKARNOVELS.COM.NG domin GABANSA TSINI NE,BAYA SIYAKI.Yanzu dai gashi yana zaune da abokiyar gabarsa cikin gidansa kuma babu yadda zai yi da ita.Abu na biyu kuma yana cikin barazanar sarki Nurbas wacce idan har bai sami mafita ba nan da kwana arba 'in zai rasa dukiyarsa,mulkinsa da darajarsa a duniya gaba daya.A iya rayuwar sarki Lafaru bai taba jin yayi nadama ba bisa irin rashin imanin dayake ma mutane ba da mulkin zaluncinsa sai a wannan karon saboda da inda bai ci zarafin boka Narwas ba da duk wannan sauyin al 'amurran na rayuwarsa bazasu faruba.Haka dai sarki Lafaru yaci gaba da kukan takaici gami da tunani yakasa zaune ko tsaye cikin tsananin fargaba da tashin hankali har dare ya raba sosai yakasa barci.Yana cikin wannan hali ne wata dabara ta fado masa ya ce da kansa, "Ai masu iya magana sunce ta inda aka hau tanan ake sauka.Me zai hana naje wajen Sharlis na yaudareta ta hanyar neman gafararta bisa abinda nayiwa mahaifinta kuma na bata dukkanin abinda take bukata na daga dukiya domin ta taimaka mini na samu nasarar yaki akan sarki Nurbas inyaso nima daga baya sai nashiga neman ilmin tsafi a sirrance kafin dana ya girma nasami sihirin dazan iya ganin 199 TASKARNOVELS.COM.NG bayansa shi da mahaifiyarsa ".Koda gama aiyana hakan sai sarki Lafaru ya fice daga cikin turakarsa ya nufi bangaren da Sharlis take a cikin gidan sarautar a wannan tsohon dare.Da isar sarki Lafaru gidan da Sharlis take sai ya iske kofar gidan a bude wanwar kuma gaba dayan dakarun dake gadin gidan a kwance suke suna ta shara barci,al 'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan.Nan take zuciyarsa ta buga da karfi yaji tsoro ya darsu a ransa amman sai yai ta maza ya kunna kai izuwa cikin gidan ya wuce kai tsaye izuwa wani babban falo,da shigarsa cikin falon sai ya iske gaba daya tagogin falon guda goma sha biyu a bude suke kuma babu kowa a cikin falon har kuyangin dake yiwa Sharlis hidima kuwa.Sarki Lafaru yaci gaba da lekawa cikin sauran dakunan gidan guda bakwai amma duk inda ya leka sai yaga wayam babu mutum a ciki sai kayan sai kayan alatu kawai da aka tanada a ciki.Cikin matukar damuwa da sakar zuci ya dawo cikin gidan in yaso ya bayar da cigiyar Sharlis a tafi nemanta a cikin gidan sarautar.Wata zuciyar tace dashi anya kuwa Sharlis ba ta yi hijira ba daga gidan gaba daya?Ai tunda yanzu tana da karfin sihirin tsafi babu abinda bazata iya yi ba. Gama aiyana 200 TASKARNOVELS.COM.NG hakan keda wuya sai yaji wata irin iska mai karfi ta taso irin wacce ke tsorata mutane sannan iskar takulle tagogin falon gaba daya sannan fitilun dake kunne a cikin falon suka mutu,wani irin duhu yamamaye idanun sarki Lafaru tayanda ko tafin hannunsa baya iya gani kuma har a sannan iskar naci gaba da kadawa,daga can kuma sai yaji an bushe da wata mahaukaciyar dariya.Duk da cewa sarki Lafaru yagane muryar dake dariyar hakan bai hana yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske a karon farko a rayuwarsa yaji tsoro ya shigeshi.Daga can sai dariyar ta dauke iskar dake kadawa ta tsaya cak sannan haske ya mamaye falon.Sarki Lafaru yayi arba da Sharlis cikin shigar fararen kaya zaune akan wata karagar mulki,sarki Lafaru ya daka mata tsawa ya ce menene na son ki tsoratar dani?Sharlis ta bushe da dariya sannan tace ina so na nuna maka nafi karfinka ta ko ina baka da wata dabara dazaka iya tsallake sharrina.Kada ka yaudari kanka yakai wannan sarki domin tuni alkadarinka ya karye kuma har abada jarumtakarka bazata taba dawowa ba.Na sani cewa sarki Nurbas ya tunamaka da kisan wulakancin dakayiwa kakannina kuma kaso ka 201 TASKARNOVELS.COM.NG hallakani tun ina jaririya amma dayake ina da nisan kwana a duniya sai da na rayu.Yanzu gashi lokaci yayi dazan dauki fansa a kanka to ka sani cewa ramuwar gayya tafi ta gayya ciwo.Sharlis taci gaba da cewa da sannu zan dauki wannan fansa a kanka yadda zaka dandana azababbiyar wahala irin wacce waninka bai taba sha ba,sannan ka dandana dacin bakin ciki marar tukewa.A karshe ni da dana muyi maka kisan mummuke irin wanda zamu zare maka ruhin numfash a sannu da sannu.Ina tabbatar maka cewa baka da tudun tsira,baka da mafaka ko maboya duk irin mugun tanadin da muka shirya akanka ni da mahaifina sai ya tabbata a kanka kuma bazaka fara dandana azabarmu ba sai bayan 'dana ya girma.Yanzu menene ya kawoka wajena?"Sarki Lafaru yai ajiyar zuciya sannan yace,"Nazo ne naga dana da kika haifa?"Koda jin haka sai Sharlis ta bushe da dariya sannan ta murtuke fuska sannan ta ce,"Zanyi maka alfarma guda daya zaka ganshi yanzu sau daya amma bazaka sake ganinsa ba sai ranar da zai kasheka." Koda gama fadin haka sai tayi nuni da hannunta izuwa kofar wani daki sai kofar dakin ta bude wani kyakkyawan yaro dan shekara uku yafito 202 TASKARNOVELS.COM.NG daga ciki yana sanye da fararen tufafi na alhariri,riga da wando kuma yayi damarar yaki,da wata karamar takobi ta wasan yara daure a qugunsa.Koda yaron yaga sarki Lafaru a gabansa sai ya zare wannan takobi tasa ya rugo da gudu izuwa kan sarki Lafaru ya kawo masa duka.In ba dan sarki Lafaru ya goce ba da sai ya kwada masa takobin a fuska. Cikin sauri Sharlis ta ruke yaron sannan tace "Wannan shine danka SHADDAD Kuma na kulla gaba a tsakaninku irin wacce har abada baza ta gushe ba. Kullum sai na nuna masa fuskarka a madubin tsafi kuma sai fuskar taka ta rika barazanar cutar dashi, shi yara a duk sa'adda yaga fuskarka shima sai yayi kokarin cutar da ita.Da wannan furuci nake yimaka sallamar karshe,sai nan da wasu shekaru zamu sake ganawa". Koda gama fadin haka sai Sharlis da Shaddad suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa ba a cikin falon.A wannan lokaci ne sarki Lafaru ya fashe da kukan bakin ciki bisa ganin yanda aka hadashi gaba da dansa na cikinsa. Cikin matukar sanyin jiki da tsananin bakin ciki ya fita daga cikin wannan gida yakoma can turakarsa inda yaci gaba da tunani da zarya ya rasa abinda zai fissheshi a rayuwa.A wannan dare bai runtsa ba 203 TASKARNOVELS.COM.NG har asuba tayi a sannan ne wata dabara ta fado masa take kuwa barci ya sace shi bai sani ba sai da gari ya waye rana ta take sannan ya farka. Cikin hanzari sarki Lafaru ya tashi yaje yayi wanka sannan yaci ado tamkar babu wani abu dake damunsa yawuce fada ya zauna akan karagar mulki aka ci gaba da harkokin mulki kamar yanda aka saba yana ta nishadi da walwala abinsa.Lokacin da ya rage baifi rabin sa'a ba a tashi daga fadar sai sarki Lafaru ya bingire daga kan karagar mulkin ya fado kasa yana shure-shure da numfashi sama-sama kamar zai mutu. Cikin gaggawa Dakaru suka daukeshi suka kaishi cikin turakarsa aka kwantar dashi akan gado sannan aka kirawo likitocinsa suka shiga ayyukansu amma har tsawon sa'o'i ba a samu nasarar shawo kan lalurar sarki Lafaru ba.Koda ganin haka sai aka tura aka kirawo gaba daya sabbin bokayen da sukayi shuhura a garin domin su bada tasu gudunmawar.Nan fa bokayen suka rinka shiga cikin turakar sarki daya bayan daya kowanne nayin iyakar kokarinsa amma babu nasara. " Sa'adda boka na tara ya shiga sai ya dubi sarki Lafaru dakyau sai yayi murmushi sannan ya dubi gaba dayan hadiman sarki dake cikin 204 TASKARNOVELS.COM.NG turakar ya ce, "Kowa ya fita ya bashi wuri." Ba tare da gardamar komai ba kuwa suka fice. Fitarsu ke da wuya sai bokan ya karanta wasu dalasimai na tsafi ya tofa a kowacce kusurwa ta dakin sannan ya dubi sarki ya ce, "Tashi zaune ya shugabana. Na sani cewa babu wata rashin lafiya a tare dakai, wanda kake nema yazo, nine mai share hawayenka. Koda jin wannan bati sai sai sarki ya mike daram ya dubi vokan cikin alamun tsoro da fargaba ya ce Mene ne tabbacinka na cewar babau wanda zai ji abinda za mu tattauna a yanzu. Da jin wannan tambaya sai bokan ya ce saki ranka kamar tsumma a randa ya shugabana, ka sani cewa na tsaface wannan daki da muke ciki yadda ko makiyarka sharlis bata isa taji abinda zamu tattauna ba. Yanzu kuma duk matsalolin da kake ciki zan iya warware maka su idan har kabi umarnin da zan fada maka. Amman fa bisa sharadi guda daya, sharadin kuwa shine bayan bukatarka ta biya zaka raba kasarka da kuma dukiyarka kaso biyu ka bani kaso daya, idan ka kuskura ka saba alkawari zan lalata dul kariyar 205 TASKARNOVELS.COM.NG dana baka, abokiyar gabarka da danta su samu nasara a kanka. Sa'adda boka ya zo nan a zancensa sai hankalin sarki lafaru ya tashi domin yanzu dai ga mafita da waraka sun zo masa, to amman mene ne amfanin warakar tunda zai raba kasarsa da dukiyarsa biyu ya bada rabi, ai idan hakan ta faru daukakarsa ta ragu a idon sauran sarakai. Amman daya tuna cewa idan fa bai yi hakan ba karshenta ne fa ya rasa komai. Lokacin da sarki lafaru ya gama wannan nazarin a cikin zuciyarsa, sai ya dubi bokan cikin nutsuwa ya ce Wai shin da farko ma wane ne kai? Shin yanzu kana nufin ka ce zaka iya dawo mani da sadaukantaka ta wacce sharlis ta rabani da ita? Kuma zaka iya bani nasara bisa yakin da zanyi da sarki Narwas nan da cikar kwanaki arba'in, kuma ka kareni daga sharrin sharlis da danta na yanzu da kuma shekarun gaba masu zuwa. Koda bokan ya ji wandan nan tambayoyi sai ya bushe da dariya ya ce Ko shakka babu duk zan iya yin irin wadannan abubuwa kuma ni kadaine a nahiyar nan zan iya, musamman idan ka yi la'akari da yadda duk nasan matsalolinka, 206 TASKARNOVELS.COM.NG da kuma yadda nasan sirrin abokiyar gabarka sharlis wacce ke shirin daukar mummunar fansa a kanka. Da farko dai ni suna na boka Muzaffar Bn Munzur, kuma ni haifaffen birnin Kisra ne, amman bisa wata bukata tawa na bar mahaifata na bazama duniya, yau shekara arba'in kenan da barina gida, ban sake komawa ba kuma har yanzu bukatata bata biya ba, sai idan na biya maka taka bukatar sannan kai kuma ka cika mani nawa alkawarin da ka daukar mani, kada kayi tsammanin cewa mulki da dukiyar da zaka bani sune bukatar tawa, ko kadan ba su bane, bukatar tawa wani babban sirri ne wanda duk wanda ya same shi sai ya fi kowa da komai matsayi a duniya, a iya bincikena na gano cewa lallai sai na mulki rabin kasarka, sannan na mallaki rabin dukiyarka, to a lokacin ne zan kai izuwa wannan matsayi. Yanzu sai ka saurareni da kyau dan kaji umarnin da zan baka idan har kana son karfin damtsenka ya dawo kafi karfin wulakancin da sharlis da kuma danta zasu yi maka a nan gaba, nan da cikar shekaru goma sha biyar. Ya kai wannan sarki da farko dai ina son ka sani cewa idan har kana son ka karya asirin da sharlis ta yi maka, har karfin damtsenka ya 207 TASKARNOVELS.COM.NG dawo kuma ya zamana cewar tsafi b zai sake tasiri a jikinka ba, sai ka auri budurwar data fi sharlis kyau a cikin watanni biyu masu zuwa nan gaba, ita kuwa wannan budurwa duk duniya a halin yanzu babu wata ya mace data kaita kyau ana kiranta da suna Ramlatus siyam. Ramlatus siyam ta kasance yar sarki Hindu na yanzu wato sarki Nasmir Bn Hayat wabda babu wani matsafi da ya fishi karfin sihiri a duniya, kuma babu wani sarki da ya fishi yawan zakwakuran mayaka wadanda suka siyar da rayuwarsu dan bauta masa, kai bama mayakansa ba hatta mutanen kasrasa suna bauta masa ne, saboda tsananin tsoronsa da suke ji. A duniya babu abinda sarki Nasmir yake so sama da yarsa gimbiya Ramlatus siyam, sabida haka ne ma ya bata tsaro na musamman a gidan sarautarsa da karfin sihiri, sannan kuma ya zuba dakaru kimanin miliyan dubu daya na aljanu suna shawagi a saman gidan nata dare da rana dan tabbar da tsaro. A kasan gidan kuwa ya zuba dakaru miliyan dubu daya na biladama suna gadi, tunda aka haifeta aka sata a cikin wannan gida, wanda girmansa ya kai na wannan 208 TASKARNOVELS.COM.NG birni na Kufa. Gabadaya ita da mahaifiyarta da barori masu yi masu hidima babu wanda ya kara shiga gidan ko ya fita face shi kanshi sarki Nazmir. Babu yadda sarki Nashmir ya amince ya baka yarshi gimbiya Ramlatus siyam domin ka aura, sai dai mu sato ta bai sani ba. Sato gimbiya Ramlatus siyam kuwa daidai yake da mutum yayi kundubala a cikin

Chapter 9 of 14