Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rami mai zurfin kafa dubu, ya kai wannan sarki idan har ka samo sa'ar auran gimbiya Ramlatus siyam to a ranar da ka kwanta da uta a wannan lokaci ne sihirin daya shiga jikinka zai karye, sannan karfin damtsenka zai dawo. Ka sani cewa koda karfinka ya dawo ba zaka iya yiwa sharlis da danta komai ba, kuma wannan da data haifa sai ya girma ya zama gawurtaccen sadauki da babu kamarsa a duniya karfin damtse dana sihiri, kuma babu wanda zai iya tunkararsa har ya hanashi halaka ka, face yar da zaka haifa da gimbiya Ramlatus siyam nan da shekara daya idan har ka samu nasarar auranta a cikin watanni biyu masu zuwa. Hanya daya zamu bi mu samu haduwa da gimbiya Ramlatus siyam kafin cikar watanni biyu masu zuwa, hanyar kuwa ita ce dole ne muyi shiri ni da kai mu tafi kogon darul iksina dake can karshen birnin sin 209 TASKARNOVELS.COM.NG domin mu sadu da aljani Maruful dawwas, domin shine kadai aljanin da zai iya sato mana gimbiya Ramlatus siyam aga can birnin Hindu, kuma ya ganota gaemu cikin kwanaki ashirin da biyar kacal! Amman ka sani cewa kafin mu isa can kogon darul ikisina daga nan sai munyi tafiyar kwanaki talatin da uku, kaga kenan idan ka hada da kwanaki ashirin da biyar da aljani Maruful dawwas zai yi ya kawo mana gimbiya Ramlatus siyam akan lokaci, kuma idan har aka gota kwanaki sittin koda yini daya ne to fa aurenka da ita bazai taba yiwuwa ba, ka sani cewa akwai tashin hankali gami da bal'ai iri-iri akan dazuzzukan da zamu ketare kafin mu isa kogon darul ikisina, inda aljani maraful dawwas, ina mai tabbatar maka da cewa mu biyu kacal face da taimakon asu manyan jarumai guda shida wadanda suma basu da wani buri face suje kogon darul ikisina omin debe tsumin wannan maganin da zai warkar da masoyansu daga cutuka daban daban. Dukkanin wadannan jarumai sun kasa zuwa wannan kogo na darul ikisina saboda dole sai da ni dinnna sannan zasu iya zuwa, kasancewar ni kadaine nasan hanyar da za a bi aje wannan kogo na darul ikisina anan cikin duniya, ni kuma nayi al?awarin cewa 210 TASKARNOVELS.COM.NG bazan jeba duk da cewa idan naje zan samu damar cika babban burina na duniya, sai a yanzu da matsalarka ta taso sannan na san cewa burina zai cika, idan har na taimakeka matsalarka ta kau kuma ka cika alkawarin daka daukar mani, wadannan jarumai abokan tafiyarmu duk suna zaune ne a kasashe daban daban, amman duk zan iya kaimu wurinsu cikin kwana daya bisa taimakon wani babban hadimina mai suna Shaibatul Barbus. A halin yanzu duk duniya babu wani aljani da ya ke da gudun Shaibatul Barbus da zafin namansa face aljani maraful dawwas, har ma shi ninka Shaibatul Barbus sau goma a komai, shine dalilin daya sa zai iya shiga fadar sarki Nashmir ya sato gimbiya Ramlatus siyam ba tare da ya halaka ba. Jarumi na farko abokin tafiyarmu shine Sadauki Haiman wanda ke zaune a birnin Misra, ahalin yanzu duk duniya abu jarumin da ya kai Haiman iya sarrafa takobi, domin idan yana rike da takobinsa yana iya sare kawunan mutane ko aljanu guda dubu a cikin dakika biyar, dan haka komai yawan dandazon dabaru in har ya shigesu sai ya trwatsa su, ka yi sani cewa a cikin daji na farko da zmau riska kafin mu isa kogon 211 TASKARNOVELS.COM.NG darul ikisina akwai wadansu mugayen maridai wadanda adadinsu ya kai miliyan dubu, wadannan maridai saboda tsananin tsawonsu idan mutum ya daga kai ya kallesu sai yaga kamar sun hade d sararin samaniya. Komai yawan runduna ta aljanu idan tazo giftawa ta saman wadannan maridai sai sun cafcakosu sun ciccinyesu, babu wanda zai iya tarwatsa wadannan maridai har mu samu ratsawa ta cikinsu mu wuce ta cikinsu face Sadauki Haiman, amman fa wannan ba yana nufin cewa ya zama wajibi dukkaninmu mu tsallake sharrin maridan, komai zai iya faruwa ga dayanmu, domin tsafi da karfin jarumtaka ba zasu cecemu ba face sa'a da tsananin rabo. Zan ci gaba. Da fatan mun wuni cikin koshin lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsap 212 TASKARNOVELS.COM.NG Fiye da shekaru dubu baya mutane da aljanu suka daina ratsa wannan daji, Sadauki Haiman na da wata kyakkyawar mata guda daya wacce aljanu suka shafeta ta makance, babu irin neman magani da bai yi ba domin idanunta su bude amman abu ya gagara, sai daga baya ya gano dole sai na rakashi izuwa kogon darul ikisina ya debo wannan tsumin maganin ya baiwa matarsa ta wanke fiskarta sannan zata warke. Wani abun mamaki shine Lumaira matar Sadauki Haiman tun tana jaririya wannan lalura ta makanta ta sameta, dan haka bata taba ganin kalar iyyaenta, danginta da mijinta ba, kuma ba baiwa Haiman auren Lumaira ba sai bisa alkawarin komai dadewa sai ya nema mata magani. Sau bakwai sadauki Haiman yana zuwa wajena akan batun tafiya kogon darul ikisina sannan yana mani alkawarin zai biya dinare dubu, amman sai nake fada mashi lokacin tafiyarmu bai yi ba, lallai idan lokacin tafiyarmu yayi zan nemeahi da kaina. 213 TASKARNOVELS.COM.NG Abikin tafiyarmu na biyu ba kowa bane face Jaruma Shadira ta birnin Baitul Halwal, a halin yanzu duk duniya bau wanda ya fi jaruma Shadira iya harbi d kibiya, domin tana iya harba kibiyoyi guda dari a cikin dakika Ashirin, tana da wani irin kwari na musamman mai harba kibiyoyi Ashirin a lokaci guda. Tsananin zafin naman jaruma Shadira yafi gaban tunani, acikin daji na biyi da zamu wuce kafin mu isa kogon darul ikisina, akawai wasu mugayen burirrika kimanin guda dubu dari hudu, wadanda suke yawo a sama tamkar tsuntsaye domin suna dauke da fuka-fukai, kuma suna da zara-zaran farata masu tsananin kaifi da tsini, wanda da zarar sun cafi wuyan mutum sai dai kaga sun cisge masa kai, tabbas jaruma shadira ce kadai zata iya tarwatsa mana wadannan mugayen burirrikan har mu samu damar ratsawa da wannan daji mu wuce, wannan baya nufin dukkaninmu zamu iya tsallake sharrin burirrikan dukkaninmu face sa'a da kuma nasara. Jaruma Shadira tana da wani dn uwa nata wani karamin yaro mai kimanin shekaru tana ana kiransa da suna Masnur, tunda aka haifi Masnur bai taba magana ba, kuma shima aljanu ne suka shafeshi aka tabbatar da cewa 214 TASKARNOVELS.COM.NG bazai tab warkewa ba face an debo wannan tsumin maganin na cikin kogon darul ikisina an bashi ya sha. Jaruma Shadira tana matukar kaunar Masnur fiye da komai a duniya, domin su goma sha daya ne a wajen mahaifinsu, amman mutum tara duk sun mutu saura su biyu kacal, sakamakon wani azababben yaki da aka yi a kasarsu, wanda aka kashe kaso takwas cikin kaso goma na jama'ar kasar gaba daya. A wannan ya?i ne su jaruma Shadira suka rasa iyayensu da dukkanin danginsu, saboda haka Shadira ta dauki alkawarin cewa ko da zata rasa rayuwarta sai ta nema wa dan uwanta magani, domin babban burinta shine taji ya budi baki ya ambaci sunanta kafin ajali ya risketa, bisa wannan daliline ma yasa jaruma Shadira taki yarda ta yi aure duk da cewa ta kasance kyakkyawar budurwa abar kwatance. Abokin tafiyarmu na uku shine jarumi Ishran Bn Suhairu wanda ke zaune a birnin Istim, a halin yanzu duk duniya babu wanda ya fi jarumi Ishran iya sarrafa sanda, domin idan yana yaki da sanda a hannunsa komai yawan abokan gaba dayansu bazai iya taba jikinsa ba, sabida zafin 215 TASKARNOVELS.COM.NG namansa da kuma karfin dukansa, kuma yana iya shafe kwana biyu yana yaki ba tare da ya nuna alamar gajiyawa ba. A cikin daji na uku da zamu wuce kafin mu isa kogon darul ikisina akwai wadansu mugayen tsuntsaye wadanda adadinsu ya kai kimanin dubu dari biyar da arba'in. Kaifi da tsini baya tasiri a jikin wadannan tsuntsaye, haka ma karfin sihiri, sai dai a makesu da sanda ko icce, idan wadannan tsuntsaye suka karci jikin mutum da faratansu ko kuma da tsinin bakinsu take wajen zai zama gyambo har da tsutsa, babu wanda zai iya trwatsa mana wa?annan tsuntsaye mu iya ratsawa ta cikin dajin face Jarumi Isran Bn Suhairu. Isran yana da mahaifiya wacce ta tufa tukuf ainun, ammnan tunda aka haufeta bata taba taka kafafunta ba, domin a lankwashe suke kamar lauje, kuma itama aljanu ne suka shafeta, babu irin neman maganin da ba a yi ba, amman abu ya gagara, sai daga baya bikaye suka tabbatar da cewa sai an shafa mata ruwan wannan maganin na kogon darul ikisina annan zata warke ta iya mikewa. Isran yayi alkawari koda zai rasa rayuwarsa sai yaje kogon darul ikisina ya debo wannan magani, sau tara Isran yana zuwa wajena akan 216 TASKARNOVELS.COM.NG na rakashi kogon darul ikisina, amma sai na fada masa yayi hakuri sai idan lokacin tafiyar tamu yayi zan nemeshi da kaina. Abokin tafiyar mu na hudu ba kowa bane face Gimbiya Zarina ta birnin Farisa, a halin yanzu duk duniya babu wanda ya lakanci sanin sirrin daji sama da Gimbiya Zarina, domin tafi kowa kwarewa a iya farauta da sanin sawun ko wace irin dabba gami da hadarinta. A cikin daji na hudu da zamu ratsa kafin mu isa kogon darul ikisina akwai mugayen dabbobin daji wadanda suke lambo da buya, sai dai kawai mutum yaji sun dira a jikinsa sun turmusheshi, kafin ya ankara sun halakashi, akwai hanyoyi da wurare a dajin wanda dabbobin basu isa su bi ba, wadannan hanyoyine kawai mutum zai bi ya iya tsira daga sharrin wadannan dabbobin, domin dabbobin dake wannan daji basa jin sara sa suka kuma tsafima baya tasiri a jikinsu. Gimbiya Zarina ce kadai zata iya fitar damu daga cikin wannan daji. Sarkin Farisa ya kasance dan uwa ne a wajen Zarina, kuma tagwaye aka haifesu tamkar an tsaga kara haka suke a kamanni, sannan sun kasance kyawawa ne na gaban kwatance, tunda 217 TASKARNOVELS.COM.NG sarkin Farisa ya girma ya zama saurayi bai taba sha'awar ya mace ba, domin aljanu sun shafi al'aurarsa. Babu irin neman maganin da ba'ayi ba amman abu ya gagara. Daga baya ne bokaye suka tabbatar da cewa sai an debo masa tsumin ruwan maganin kogon darul ikisina yayi tsarki da shi sannan zai samu lafiya har ya iyayin aure. Zarina da sarkin Farisa sun shaku ainun, kuma ko kadan batason taga abinda zai bata masa rai, a duk lokacin da sarkin Farisa a tuno da wannan lalura tasa sai yayi ta kuka da bakin ciki, kuma sai ya kwana uku bai ci abinci ba, ganin wannan hali da yake shiga ne yasa Gimbiya Zarina ta dauki alkawari cewa koda zata rasa rayuwarta sai ta je kogon darul ikisina ta debo wa dan uwanta tsumin wannan maganin. Zarina ta yi alkawarin zata bani dukiya iya adadin abinda ta gada a wajen iyayensu akan na rakata zuwa kogon darul ikisina, amma sai na fada mata tayi hakuri sai lokacin tafiyar yayi, itama zan nemeta da kaina. Abokin tafiyarmu na biyar shine Sadauki Shaharan Bn Lawwar na birnin Hairussalas, a duniya kaf babu wani mutum mai karfin gudu 218 TASKARNOVELS.COM.NG bisa turba tamkar Sadauki Shaharan, domin yana iya shafe gudun zira'i saba'in a cikin dakika sittin, a cikin daji na biyar da zamu ratsa mu wuce izuwa kogon darul ikisina akwai wata katuwar kunama guda daya jal, wacce ta kasance mai tsananin karfin gudu, domin udan ta kasa tsere da dawakai tana basu raya ta zira'i arba'in, kuma komai jurewar gudun mutum sai ta kureshi ta harbeshi, da zarar dafinta ya shiga jikin mutum take yake dahuwa ya narke kamar an kada ruwan kwai. Akwai wani ruwan kogi a karshen wannan daji, idan har mutum ya kasa tsere da wannan kunama kuma ya rigata fadawa cikin wannan kogi tana fadawa cikin kogin nan take zata mutu. Babu wanda zai iya kasa tsere da wannan kunama kuma ya rigata fadawa cikin wannan kogi face Shaharan, idan ya samu nasarar hakan ne zamu iya ratsawa ta wannan dajin ba tare da wannan kunama ta halakamu ba. Sadauki Shaharan yana da wani ingarman doki mai tsananin gudu, tamkar shi kansa, shi dai wannan doki Shaharan yana shiga gasar tsere ta duniya da shi, sau shida ana yin wannan gasa a birnin Hairussalas yana lashewa ya zama zakara. Kuma duk bayan shekaru hudu ake yin 219 TASKARNOVELS.COM.NG wanna gasa, yanzu abokan gasar tasa sunyi wa dokin nasa asiri ya gurgunce gashi saura shekara daya ayi wannan gasa. Babu irin neman maganin da Sadauki Shaharan bai yi ba amman sai abu ya gagara, daga karshe ne shima bokaye suka tabbatar masa d cewa shima sai ya samo tsumin ruwan magani a kogon darul ikisina an shafa a kafafun dokin sannan zai iya mikewa har yayi wannan gasa. Ssadauki Shaharan ya bugi kirji kan cewa koda zai rasa rayuwarsa ne to tabbas sai yaje kogon darul ikisina ya debo ruwan wannan magani, saboda gasar da za'ayi a shekara mai zuwa ita ce ta karshe, kuma zakaran daya lashe gasar za a bashi auren yar sarkin birnin Hairussalas gami da dukiya mai tsanin yawa da har mutum ya mutu bai isa ya karar da ita ba. Dama can Sadauki Shaharan ana yana mutuwar son gimbiya Sharilat yar sarkin birnin Hairussalas domin dare da rana a cikin begenta yake, yana raira mata wakoki yana zubar da hawaye, a rayuwar Sadauki Shaharan sau daya ya taba ganin Gimbiya Sharilat, tun daga wannan rana kuwa bai sake yin bacci da 220 TASKARNOVELS.COM.NG daddare ba saboda tsananin begenta, kuma ba zai baccin ba face ya mallaketa ta zama matarsa. Abokin tafiyarmu na shida ba wani bane face ni kaina, ni kadaine nasan hanyar da za bi a riski wadannan dazuzzuka guda biyar, kuma masifaffu sannan har abi ta cikinsu a isa kogon darul ikisina. Lokacin da boka muzafar ibn Mauzar yazo nan a jawabinsa sau yayi ajiyar numfashi domin makogwaronsa da harshensa su huta bisa doguwar maganar da yayi, shi kansa sarki lafaru sai da jaya dogon numfashi ya ajiye sabida tsananin mamaki, bisa jin wannan dogon bayanin da kuma sanin gagarumin aikin dake gabansu kan wanna tafiya mai tsananin hadari da wuya. Boka muzafar yayi gayaran murya sannan ya ci gaba da bayanu kamar haka al'amarin aljani Maruful Dauwas kuwa, wanda zamu rik a cikin kogon darul ikisina kuwa mu nemi taimakonsa akan yaje ya sato mata gimbiya Ramlatus siyam, abune mai tsananin hadari a garemu, ya kai wannan sarki kayi sani cewa shi dai aljani maruful Dauwas ya kai shekaru ubu biyu da dari biyu a cikin kogon darul ikisina, kuma tunda ya shiga kogon sai yayi zamansa bai sake fitowa ba 221 TASKARNOVELS.COM.NG balle yaga mutum ko aljan dan uwansa, haka kuma bai sake shakar iska irin ta duniya ba, sannan kuma bai kara ci ko shan wani abu ba, dalili kuwa shine duk halittar data shiga cikin kogon darul ikisina ba zata sake jin yunwa ko kishin ruwa ba, kuma duk irin cutar dake jikinka sai ta warke, ko yaushe kogon a ni'ima yake babu zafi hakazalika babu snyi, bugu da kari idan har halitta ta shiga cikin wannan kogo to fa sai ta ninka adadin shekarunta sau dari a duniya sannan zata mutu walau mutum, aljan, dabba ko kuma kwaro, duk da cewa kawai wadannan ni'imomi a cikin kogon darul ikisina kulum aljani maruful Dauwas kulum cikin kuka da bakin ciki yake, kuma sai yayi kwana arba'in yana raira wakar bege ga masoyiyarsa Gimbiya Rashmin yar sarkin aljanu na birnin Hindu, har takai cewa hawayen nasa sun taru sun zama kamar kogi a cikin kogon darul ikisina, wanann kogi shine ruwan maganin da jaruman biyar suke bukata. Yau kimanin shera dubu biyu da dari biyar kenan da mutuwar Gimbiya Rashmin wacce ta kashe kanta sakamakon mahaifinta sarkin aljanu na birnin hindu ya ki yarda ya aurar da ita ga bawanta aljani maraful Dauwas. Tun 222 TASKARNOVELS.COM.NG Aljani Maraful Dauwas yana da shekaru bakwai da haihuwa yake bauta a gidan sarkin aljanu, kuma Gimbiya Rashmin sa'arsa ce, wato kai daya suka taso, kuma tun a sannan shine bawanta mai kula da turakarta, abincinta gami da lafiyarta kasancewarsa dan babban likitan sarki. Sarkin aljanu ya aminta kwarai da aljani Maraful Dauwas, kamar yadda ya aminta da mahaifinsa marigayi, kuma yana kaunarsa matuka, ba wani abu ne yasa Sarki aljanu yake matukar kaunar shi ba face abubuwa uku; Na farko shidai aljani Maraful dauwas sadaukine, kuma tun yana yaro yake daka wa maza gumba a hannu a duk sa'ar da aka fita yaki. Abu na biyu yana da matukar karfin gudu a sararin samaniya fiye da tunanin mai tunani, dan haka duk wata bukatar sarki ta gaggawa shine ake aikawa. Abu na uku shine, shidai aljani Maraful Dauwas yana da amana matuka, domin komai yawan dukiya idan aka bashi ajiyarta bazai taba koda adadin kwayar zarra daga ciki ba, atakaice dai 223 TASKARNOVELS.COM.NG yadda sarki ya aminta da aljani Maraful Dauwas bai aminta da dukkanin iyalansa da matansa gami da sauran fadawansa ba. Kai wani lokacin ma bashi da abokin shawara face aljani Maraful Dauwas, duk da kasancewarsa karamin yaro amman akwai tunani gami da hangen nesa. A kwana a tashi sai gimbiya Rashmin ta girma ta zama kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance, ya zamana cewa a wannan zamani babu kamarta a dukkanin matan aljanu na duniya, dan haka sai ?a?an Attajirai, bokaye, sarakai masu is da kansu suka rinka zuwa neman aurenta, ita kuwa sai ta ki yarda ta fidda gwani daga cikinsu. A wannan lokaci dare da rana gimbiya Rashmin na tare da bawanta Aljani Maraful Dauwas, hatta mahaifiyarta bata shaku da ita ba kamar yadda ta shaku da bawan nata, kuma babu abinda ke rabasu face kwanciyar bacci, wani lokacin ma Gimbiya Rashmin ata barin Aljani Maraful Dauwas ya fita daga turakarta koda tana jin bacci, idan yaga haka sai ya shiga raira mata waka mai dadi, a cikin waken kalamai ne na koda kyawunta dan haka bata sanin sa'ar da bacci ke saceta sabida jin dadin waken. 224 TASKARNOVELS.COM.NG A sannan ne yake samun damar fita daga cikin turakarta ya tafi nasa dakin. Ga bako idan yazo gidan sarautar sai ya dauka cewa Aljani Maraful Dauwas da Gimbiya Rashmin yan uwa ne na jini ba bawa da uwargijiyarsa ba. Alama daya ce zata tona asirin hakan ganin yadda Aljani Maraful Dauwas ke yin aikin bauta a gidan sarautar da kuma yanayin suturar da yake sawa wacce bta kai darajar ta ?a?an sarakai ba. Lokacin da sarkin aljanu yaga jama'a sun dameshi akan zuwan neman auren yarsa, sai ya kira Gimbiya Rashmin ya ce da ita "Ya ke yata na baki kwana arba'in kacal da ki fiddar da gwani daga cikin masoyanki, in ba haka ba kuwa zan baki wanda nake ganin ya dace da ke" Ko da jin wannan batu sai hankalin Gimbiya Rashmin ya dugunzuma ainun, ta ce ya kai abbana ka yi sani cewa ni ban ta?a yin soyayya da wani da namiji ba, koma ban san ma mece ce soyayya ba, ya za a yi kazo ka yi mani titsiye a rana ?aya kace na fitar da gwani a cikin masoyana, alhalin duk samarin dake zuwa 225 TASKARNOVELS.COM.NG wajenka suke zuwa ba wajena ba, kuma babu wanda na tana yin hirar dakika daya da shi. Koda jin wannan batu sai sarki ya turbune fuska tare da cewa Ya ke yata kiyi sani cewa idan baki yi aure a yanzu ba kimata da mutuncina ne zasu zube a idon duniya, domin dukkan masu sonki da aure sun kasance manyane a cikin al'ummar aljanu na duniya, shawara daya da zan baki itace kije ki samu wanda kike ganin kin yarda da shi, walau a cikin kawayenki ko yan uwanki, ko kuma mahaifiyarki kice da su suyi maki cikakken bayani akan irin namijin da ya kamata ki aura, kuma su fayyace maki mene ne so, domin ki san mahimmanci soyayya dan jada ki auri namijin da bakya kauna a cikin zuciyarki. Koda sarki ya gama fadin haka sai ya mike tsaye ya fice daga cikin falon da suke zaune, fitarsa keda wuya sai gimbiya Rashmin ta shiga zancen zuci tare da cewa To ni yanzu wa ya kamata naje nayi wa wadannan nan tambayoyi, nikam a duniya babu wanda na yadda da shi sama da bawana aljani Maraful Dauwas, sabida haka lallai da shi zanyi wannan shawara. 226 TASKARNOVELS.COM.NG Koda gama ayyana haka sai gimbiya Rashmin ta tafi izuwa turakarta, da shigarta cikin turakar sai ta iske Maraful Dauwas ya gama kimtsa komai na dakin yana gyara mata shinfida. Rashmin ta zauna a gefen gadon nata a lokacin da Maraful Dauwas ya kammala aikinsa tare da juyawa zai fice daga dakin, kawai sai yaji ta kira sunansa, kuma ta yafito shi da hannu tana mai yi masa nuni da ya zo ya zauna a gefen gadon kusa da ita. Koda ganin haka sai zuciyar Maraful Dauwas ta buga da karfi, yaji kamar an doki ransa da guduma, tsoro ya kamashi. Amman sai yayi ta maza ya je ya zauna nesa kadan da ita yana daridari domin a iya shekarun daya kwashe yana yi mata bauta yauce ranar farko data tab umartarshi daya zauna kusa da ita. Koda taga yadda yake dari+dari sai ta bushe da dariya ta cw haba ya kai abokina mene ne kuma haka naga kana rawar jiki, bafa wani abu zanyi maka ba, shawara kawai nake so ka bani, domin babu wani mahaluki dana aminta da shi sama da kai. 227 TASKARNOVELS.COM.NG Sa'adda da aljani Maraful Dauwas yaji wannan batu sai hankalinsa ya kwanta har ya saki murmushi tare da cewa To ina sauraronki fadi bayaninki naji kuma zanyi iya kokarina wajen baki shawarar da zata fissheki. Gimbiya Rashmin tayi gyaran murya sannan ta fara da cewa Ya kai abokina kuma amintaccena, kayi sani cewa ayau din nan sarki ya kirani kuma yace na fidda gwani daga cikin masoyana, ni kuwa sai nace da shi ya za a yi na fidda gwani alhalin bantaba yin soyayya ko da dayansu ba, kuma bnsan ma meye soyayyar ba. Koda jin haka sai yace dani naje na nemi wnada na aminta da shi ya bani shawara akan irin mijin daya kamata na aura, kuma yayi mani bayanin mece ce soyayya domin na fahimta sosai. Lokacin da Gimbiya Rashmin ta zo nan a zancenta sai Aljani Maraful Dauwas yayi murmushi sannan ya ce aiko kinyi tambaya gareni mai sauki kuma mai saukin bayani, da farko dai ina so kisan cewa ita soyayya wata abace wacce ake fara yinta bisa gamon jini, amince da kuma yarda da juna, daga nan sai sabo gami da shakuwa su sa tayi karfi ainun a cikin zuciyar masoya, har takai cewa suna son 228 TASKARNOVELS.COM.NG kasancewa a tare ko yaushe. Idan soyayyar tasu ta kara karfi sai suji cewa duk wuya d tsanani bq zasu iya rabuwa da juna ba, kuma basu da burin daya wuce su zama abokan rayuwa ga junansu, wannan shine abinda ake kira soyayya. Shawarar da zan baki dangane da irin mijin da ya kamata ki aura shine kada ki duba matsayinsa, mulkinaa ko kuma daukakarsa, kiyi duba izuwa halaye na gari, shi din mai gaskiya ne, shin idan aka bashi b zai ci ba, shin zai iya kare mutuncinki gami da lafiyarki, kuma zai iya sallama rayuwarsa domin kare ta ki, shin idan yayi alkawari yana cikawa, tsawon wane lokaci kuke tare sannan ya girman shakuwarku ta ke, yau udan babu mahaifinki zai ci gaba da darajtaki gami da ririta ki, waye zai iya jibantar alamarinki duk sa'ar da wata masifa ta fado maki ba tre da yayi shakkar komai ba. Wadannan sune abubuwan da ya kamata kiyi amfani da su wajen zaba wa kanki mijin da zai dace da ke. Sa'adda da Maraful Dauwas ya zo nan a zancensa sai kawai yaga hawaye ya zubo daga idanun Gimbiya Rashmin, al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalinsa kenan ya razana kuma ya sakko kasa daga kan gadon, ya 229 TASKARNOVELS.COM.NG tsugunna bisa gwiywoyinsa yana mai cewa ki gafarceni ya shuga ta idan har bayanin da nayi maki ya bata maki rai. Koda jin haka sai Rashmin ta share hawayebta sannan itama ta mike tsaye ta kama hannayen aljani Maraful Dauwas a karo na farko a rayuwarsu ta tadashi tsaye ta ce Ya kai amintaccena ka yi sani cewa ba komai bane yasa kaga wannan hawaye nawa ba face sai a yaune na san cewa akwai magani a gonar yaro, amman rashin sani ya hanashi amfani da maganin. Lokacin da kake ta yi mani wannan jawabin sai na fahimci cewar babu wani mahaluki da yake da wadannan abubuwa daka lissafo wanda na sanshi a rayuwata face kai, kqine kadai mahalukin da nayi sabo da shi, kuma na shaku da shi ainun, tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana, kaine kadai wanda nasan cewa zai iya sallama rayuwarsa domin tawa sabida ka tseratar da rayuwata sau ba adadi, kainne kadai nasan cewa na bashi amanata amman bai ci ba, kaine wanda baka taba karya mani alkawari ba, kuma kaine kadai nasan cewa ko babu ran mahaifina zaka ci gaba da darajta ni, ashe kuma lallai kaine namijin d ya dace na aura dan haka sunanka zan ambata a wajen mahaifina. 230 TASKARNOVELS.COM.NG Koda gimbiya Rashmin ta zo nan a zancenta sai Maraful Dauwas ya kamu da tsanankn tsoro kuma ya fisge hannunsa daga cikin nasa da sauri, a sannan ne shima hawaye ya zubo daga cikin idonsa kuma ya dan ja baya daga gareta ya ce "Ya shugabata ina kika taba ganin bawa ya auri yar sarkinsa, har abada ruwa ba sa'an kwando bane, ina mai rokonki da ki taimakeni kuna ki janye wannan batu daga zuciyarki gami da bakinki, ki tuna cewa mahaifinki yana da zafi, idan har kika furta masa wannan al'amari zna iya fuskantar fushinsa, kuma allura zata tono garma, wata kila ma sanadin rabuwarmu kenan. Koda jin haka sai gimbiya Rashmin ta rugo izuwa kan Aljan Maraful Dauwas ta rungumeshi, sannan ta fashevda kuka tana mai cewa aiko idan aka rabani da kai duk wanda zai aureni sai dai ya kwanta da gawata amman ba ni ba. Kafin Maraful Dauwas yace wani abu sai kawai suka ga an turo kofar dakin da suke ciki an shigo, ba wani bane ya shiga ba face sarki da mahaifiyar Gimbiya Rashmin sunata hira gami da dariya, koda suka yi arba da Gimbiya Rashmin tana rungume da aljani Maraful Dauwas sannan duk su biyu suna hawaye, sai 231 TASKARNOVELS.COM.NG sarki ya kwarara uban ihu cikin tsananin fushi, nan take dakarinsa suka rugu da gudubizuwa inda suka ji ihun sarki, da zuwansu sai sarki ya ce dda su su kama Maraful Dauwas uyita dukansa har sai ya suma sannan su kulleshi. Ai kuwa nan take wadannan dakarubsuka cika aikin sarki, a lokcin da Gimbiya Rashmin ta rinka ihuwa gami da kururuwa tana kokarin ta kifa kansa dan su daina dukansa, amman sai sarki ya riketa gam da hannunsa biyu, a gaban idonta aka sumar da masoyinta aljani Maraful Dauwas aka kuma tafi da shi. Nan take itama Gimbiya Rashmin ta sulale kasa sumammmiya. Cikin firgicewa da dimaucewa sarki da matarsa suka shiga yi mata fifita, da kyar da shidin goshi suka samu ta farfado. Daga wannan rana Gimbiya Rashmin ta kwanta cuta ya zamana cewa kullum tana kwance kuma bakinta baya ambaton komai face bawanta kuma masoyinta aljani Maraful Dauwas. Hakan bata sa sarki yayi umarni akan a saki Aljani Maraful Dauwas daga kurku ba, kawai ma sai ya mayarvda hankalinsa akan nema wa yarsa Rashmin magani, har sai da 232 TASKARNOVELS.COM.NG takai cewa an hada da karfin sihirin tsafi wajen juyar da kwakwalwar gimbiya Rashmin akan ta manta da bawa Maraful Dauwas sannan aka samo kanta ta samu lafiya. Shiko bawa Maraful Dauwas a kullum sai an gana masa azaba kala dubu a cikin wannan kurkukun, ya zamana cewa ya lallace kuma ya rame sanna ya fita daga cikin hayyacinsa, komai rashin imani da tausayinka idan ka

Chapter 10 of 14