Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kaunata kayi sani cewa ina binka bashin kubutar da rayuwarka da nayi daga hannun wadannan muggan aljanu na cikin kogon Mazubatul Dulshul masu tsaron takobin 73 TASKARNOVELS.COM.NG Saiful Lujara. Baka da wani abu wanda za ka iya biyana wannan bashi domin kai fakiri ne a kaina koda kuwa nan gaba ka mallaki duk kasashen duniya sun zamo karkashin mulkinka saboda a cikin wannan gida nawa akwai tsubin dukiya wacce tafi duk dukiyar duniya yawa. Ina son ka biyani bashin da abu daya Hantaru ya ce, "Mene ne abin da kike so na biya ki da shi?". Maimakon Hayatul Lumihas ta ce wani abu sai taje ta dauko wani hoto da aka sasssakashi cikin siffar gunki ta mikawa Hantaru. Da ya karbi gunkin ya dubeshi da kyau sai ya ga ashe kamannin gimbiya Hayatul Lumhas ne sak tamkar an tsaga kara. Hantaru ya sake dago kai ya ?ubi Hayatul Lumhas ya ce, "Me zan yi da wannan gunki mai siffar fuskarki?". Hayatul Lumhas ta ce, "Ina son komai wuya komai gumu, ka kai wannan gunki izuwa birnin Hindu ka sada shi ga mahaifiyata sarauniya Mashlima wacce a halin yanzu ita ce ta gaji karagar mahaifina. Ka bata Labarina da irin daular da nake ciki amma ka sanar da ita cewa burina bai cika ba wanda shi ne burin mijinta, don haka har abada ba zamu sadu ba kuma nima ajalina yana daf kamar yadda na 74 TASKARNOVELS.COM.NG mahaifina ya kasance. ldan kayi haka ka biyani bashin da nake binka, idan kuma baka aikata hakan ba kaci amanata". Koda gama fadin hakan sai Hayatul Lumhas ta juyawa Hantaru baya ta ce, "Ka mike ka ci gaba da tafiya izuwa bangaren gabas za ka riski wata kofa a gabanka da ka shiga cikinta za ka tsinci kanka a wajen gidan nan inda za ka iske doki da guzuri wanda na tanadar maka, amma ka sani cewa daga yanzu har izuvwa sa'adda za ka isa kofar birnin Darul Mahabul kana da damar sauya ra'ayi na dawowa gareni, kofar gidana a bude take gareka kuma ina mai marhaban da sake karbarka. ldan kuwa baka dawo ba shi ke nan har abada ba zamu sake saduwa ba domin ni da kai duk ajalinmu na kusa." Koda gama jin wannan batu sai Hantaru ya nufi gabas yai ta tafiya a cikin harabar gidan ko Waiwayowa bai yi ba, sai da ya ga ya yi nisa da Inda ya bar Hayatul Lumhas a sannan ne ya tuno da irin shakuwar da ya yi da ita a cikin kwanaki goma sha hudun da kuma irin dawainiyar da tayi da shi na jinyarsa har ya sami lafiya. Hantaru ya tuno da irin tsananin 75 TASKARNOVELS.COM.NG kyawun Hayatul Lumhas da kuma irin daular da take ciki da matsayinta na 'yar sarkin birnin Hindu, birnin da a wannan ZAmani duk duniya babu kamarsa a karfin mulki. Nan take Hantaru yaji nadama tazo masa, kuma ya kamu da tsananin tausayin gimbiya Hayatul Lumhas, bai san sa'adda hawaye ya zubo masa ba, kawai sai ya waigo baya bisa tunanin ko Zai hangoi Hayatul Lumhas. Yana waigowa sai ya ganta a tsaye daf da shi idanunta sun yi sharkaf da hawaye. Nan take Hantaru ya rungume Hayatul Lumhas ya fashe da matsanaicin kuka ita kuwa sai ta bushe da dariyar farin ciki bisa ganin cewa zuciyarsa ta karaya ya fasa tafiyar ya barta. Bisa mamaki sai Hayatul Lumhas taji Hantaru ya yi wuf ya tureta daga cikin jikinsa kawai sai ya dubeta ya ce, "Ki gafarceni yake tauraruwar zamani, hakika ke abar tunawace a zuciyata har abada, kuma lallai sai na biyaki bashin da kike bina ka fin cikar ajali, amma ki sani cewa har abada ba za ki mallakeni ba nima ba zan mallakeki ba domin ba a yimu domin juna ba Koda gama fadin hakan sai Hantaru ya juya ya ci gaba da tafiya abinsa. Kawai sai yaji Hayatul Lumhas ta 76 TASKARNOVELS.COM.NG fashe da matsanancin kuka wanda ya kara dugunzuma hankalinsa kuma ya kamu da tsananin tausayinta har yaji kamar ya hakura da tafiyar ya koma gareta amma sai ya kanne ya ci gaba da tafiyar, yana tafe yana zubar da hawaye har ya yi nisa sosai ya daina jiyo sautin kukan Hayatul Lumhas a sannan ne ya iso bakin kofar gidan. (Ta tabbata dai hayatul lumhas tawace, Ni mai typing Abu Saleh AlQuyraemey). Da isarsa daf da kofar sai ya ga kofar ta bude kanta, kawai sai ya ga wani ingarman farin doki a tsaye shi kadai yana harbin iska ga jakar guzuri daure a kansa. Cikin murna Hantaru ya ruga izuwa ga dokin yai tsalle ya haye kansa sannan ya sakar masa linzami ya sukwaneshi da gudu izuwa cikin daji. Daga wannan rana Hantaru ya ci gaba da tafiya a cikin daji ya kwana nan ya tashi can har tsawon kwanaki masu yawa amma mamaki ko sau daya bai gamu da wani mugun abu ba kuma bai sha wahalar komai ba. Wata rana da yammaci yana cikin tafiya kawai sai ya hango kofar birnin Darul Mahabul a gabansa nesa kadan. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki ke nan, domin da can tafiyar da yake yi kansa a 77 TASKARNOVELS.COM.NG juye yake bai ma san inda ya nufa ba kawai inda ya ga dokinsa ya yi nan yake bi baya sauya masa akala. Koda Hantaru ya hango kofar birnin Darul Mahabul sai ya cika da tsananin farin ciki don haka sai ya sakarwa dokinsa kaimi ya zabureshi da gudu. Da isarsa bakin kofar birnin sai ya ci gaba da gudu kuma ya rufe fuskarsa da rawani, sannan ya boye takobin Saiful Lujara a cikin jakar guzurinsa bai zame ko ina ba sai gidan Shurem. Da isar Hantaru kofar gidan sai ya iske Shaulat matar Shurem ita kadai tana baiwa dokin mijinta ruwa. Koda Shaulat ta ga mutum a gabanta bisa doki kuma fuskarsa a rufe sai ta razana ta yunkura za ta ruga izuwa cikin gida. Cikin sauri Hantaru ya kira sunanta yana mai cewa, "Ya ke kakata yau kuma jikanki kike gudu?" Koda Shaulat taji muryar Hantaru sai tayi jifa da bokitin hannunta ta ruga gareshi. Hantaru ya sauko daga kan dokinsa da sauri suka rungume juna tana dariyar farin ciki, daga can kuma sai yaji ta fashe da kuka. Al'amarin da ya matukar firgitashi ke nan ya janye jikinsa daga cikin nata da sauri suka fuskanci juna a lokacin da ya rike 78 TASKARNOVELS.COM.NG kafadunta ya ce, "Ya ke kakata ina dalilin wannan kuka naki?" Shaulat tayi ajiyar zuciya ta ce, "Ya kai Hantaru kayi sani cewe bayan taf?yarku izuwa kogon Mazubatul Dulshal kai da sadauki Rabbasu don dauko takobin Saiful Lujara mutane da yawa sun rasa rayukansu sakamakon mutuwar mahaifin Rabbasu da kuma mahaifin mijina, wato boka Sulbaini domin mutuwar tasu ta kawo rudani da tashin hankali a tsakanin kabilarmu da kabilar su Rabbasu har tasa muka dinga yakin sunkuru muna kashe juna sai da kyar sarki ya tsaida wannan yaki. Ka sani cewa mijina ya mutu a wannan yak?, yanzu bani da kowa face mahaifiyarka Salimat da kuma kai a wannan birni na Darul Mahabul. Koda jin wannan batu sai Hantaru yaji wani irin mugun bakin ciki ya rufeshi, bai san sa'adda ya fashe da matsanaicin kuka ba. A dai-dai wannan lokaci ne ya hango Salimat ta fito daga cikin gida ta nufo inda suke hawaye na zuba a idanunta. Cikin hanzari Hantaru ya ruga gareta suka rungume juna suka kara fashewa da kukan murna bisa sake saduwa. Nan dai suka dunguma su ukun suka shiga cikin gidan. 79 TASKARNOVELS.COM.NG Bayan Hantaru ya huta kuma ya ci abinci sai Salimat da Shaulat suka rakashi izuwa inda kabarin Shurem yake ya durkusa a gaban kabarin yana kuka, sannan ya yi masa addu'oi irin nasu na kafirai da suka saba yi. Ba wani abu bane yasa Hantaru yake wannan kuka ba face gashi ya dawo daga kogon Mazutbatul Dulshal cikin nasarar ? auko takobin Saiful Lujara amma Shurem bai gani ba. Ya sani cewa a rayuwar Shurem wannan ce rana mafi farin ciki a rayuwarsa, wato ranar da zuri'arsu ta ci gasar da ta kasa kar6o kambunta a wajen zuri'ar su Rabbasu tsawon shekaru. Sa'adda Hantaru ya gama 'yan addu'oinsa da koke-kokensa a kabarin Shurem sai Salimat ta tasheshi tsaye suka koma cikin daki suka zauna a sannan ne ya bude jakar guzurinsa ya ?anko takobin Saiful Lujara ya nuna musu sannan ya kwashe labarin tafiyarsa kaf ya zaiyane musu tun daga lokacin suka fara shan wahala shi da sadauki Rabbasu da kuma sauran wahalar da ya sha har kawo izuwa lokacin da Rabbasu ya karaya ya kashe kanSa ya isa cikin kogon Mazubatul Dulshur da irin gwagwarmayar da 80 TASKARNOVELS.COM.NG ya yi da masifun ciki har da yadda ya dauko takobin ya gudu don tsira da rayuwarsa har ya fadi kasa sumamme ya farfado a gidan gimbiya Hayatul Lumhas da duk abin da ya faru tsakaninsa da ita har suka rabu ya taho birnin Darul Mahabul. Koda gama wannan labari sai Salimat da Shaulat suka cika da tsananin al'ajabi kuma suka jinjinawa Hantaru domin sun san cewa ya yi gagrumar bajinta wacce abu ne mawuyaci nan gaba a sami wanda ma zai iya kwatanta irinta. Haka dai suka ci gaba da hira har dare ya raba sosai. Hantaru da Shaulat suka kwanta suka kama barci amma ita Salimat sai ta kasa kwanciya kuma idanunta suka bushe ya zamana cewa ko kadan bata jin barci. Ba komai ne ya haddasa ma ta hakan ba face tsananin fargaba bisa labarin da Hantaru ya baiyana ma ta dangane da abubuwan da gimbiya Hayatul Lumhas ta zaiyana masa akan ababuwan da za su same shi anan gaba. Tun sa'adda Hantaru ya tafi neman takobin Saiful Lujara ya zamana cewa kullum sai Salimat... 81 TASKARNOVELS.COM.NG Tun sa'adda Hantaru ya tafi neman takobin Saiful Lujara ya zamana cewa kullum sai Salimat tayi mugun mafarki akansa kuma abin da ake nuna ma ta a cikin mafarki shine, Hantaru ya rusa ma ta dukkan farin cikin rayuwarta. Koda ta tuna wadannan mafaekai da wannan labari da yazo ma ta da shi sai ta tabbatar da cewa Lallai mafarkin nata zai iya zama gaskiya. Bisa Wannan dalili ne Salimat ta kasa barci ta dinga sakar zuci bata san sa'adda ta fara kuka ba. Sautin kukan nata ne ya sa Haataru ya farka daga barci. Koda bude idanunsa ya ga Salimat a zaune tana kuka sai ya mike zumbur cikin razana yazo gareta ya rungumeta yana cewa ya ke, "Ummina kiyi sani cewa har abada wannan mafarki naki ba zai tabe Zama gaskiya ba, domin babu wani aba da ya fiki matsayi da muhimmanci a wajena, na rantse da darajar 82 TASKARNOVELS.COM.NG kaunar da ke takanina da ke da mijinki har abada ba zan taba juya mikk baya ba. Na yi imani cewa babu abin da zai gagari tsafi saboda haka koda mafarkinki zai zama kaddara a garemu to ni zan sauya wannan kaddar da karfin tsafi, bayan mun karbo kambun gasa wajan sarki an daura aurena da gimbiya Larziya saboda haka inason gobe da sassafe ke da Shaulat ku rakani fada domin na gabatar da takobin Saiful Lujara ga sarki a gaban jama'ar gari domin burin zuri'armu ya cika nima nawa burin ya tabbata. Sa'adda Hantaru ya zo nAn a jawabinsa sai Salimat taji hankalinta ya dan kwanta, don haka sai ta share hawayen idanunta ta dora kanta bisa kirjin Hantaru shi kuwa ya ci gaba da rera waka, A cikin sanyin murya yana karanto baitoci masu kwantar da zuciya da sanyayata. A haka barci ya sace Salimat bata sani ba, Har gari ya waye Salimat na barci akan kirjin Hantaru bai yarda ya motsa jikinsa ba don kada 83 TASKARNOVELS.COM.NG ta farka daga barcin kuma bai daina rera wannan wake ba saboda tsananin biyayya da son ganin kwanciyar hankalinta. Hudowar hasken rana ne yasa Salimat ta farka daga barci, koda ta ga kanta bisa kirjin Hantaru kuma ta ga idanunsa wasai babu alamar ya yi barci sai ta cika da tsananin damuwa ta ce, "Ya kai ?ana ya ya aka yi nayi barci akan kirjinka amma baka tasheni ba, domin kaima ka kwanta kayi barcin kuma mene ne ya hanaka kaima kayi barcin?". TYPING BY : SHURAIH 99% Sa'adda Hantaru yaji wadannan tambayoyi sai ya yi mumushi ya ce, "Ai kwanciyar hankalinki shi ne nawa, inda baki samu Wannan barci ba da sai na kwana ina kuka da bakin ciki." Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga jama'ar zuri'arsu na ta shigowa cikin gidan da murna suna yiwa Hantaru barka da sauka tamkar an yanke musu dukkan bakin cikin rayuwa. Al'amarin da ya ?aurewa Hantaru da Salimat kai ke nan suka cika da mamaki bisa yadda jama'a suka san cewa ya dawo harma suke zuwa yi masa barka da sauka. 84 TASKARNOVELS.COM.NG Abin da basu sani ba shi ne, tun a yammacin Jiyan wata kuyangar gidan ta watsa labari. Nan da nan gidan Shurem ya cika ya batse da jama'arsu tamkar ana wani gagarumin shagalin biki a garin. Bayan jama'a sun gama taruwa sai aka cabawa Hantaru ado sannan aka rakashi izuwa fada ana tafe ana kade-kade da raye-raye gami da bushe bushe. Nan da nan birnin gaba ?aya ya dauka cewar ga Hantaru can ya dawo gida. Nan fa jama'a suka yi tururuwa izuwa fada domin su ganewa idanunsu shin Hantaru ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara ne ko kuwa bai samu ba, sannan suna son su ji labarin Sadauki Rabbasu yana raye ne ko kuwa ya hallaka a cikin wannan tafiya. Lokacin da su Hantaru da sauran jama'ar gari suka isa fada sai suka iske fadar a cike makil 85 TASKARNOVELS.COM.NG babu masakar tsinke. Sarki na zaune bisa karagar mulki ya ci ado na kasaita sai murmushi yake ya kasa rufe baki dalili kuwa shi ne tuni bokaye sun bashi labarin cewa Hantaru ya dauko takobin Saiful Lujara. A hannun daman sarki gimbiya Larziya ce a Zaune ta caba ado na ban al'ajabi sai sheki da walwali take tamkar wata dan daren goma sha biyu, kuma itama tana ta yin murmushi irin wanda ka iya zauta duk wani baligi da ya kuskura ya kura ma ta idanu. Da shigowar Hantaru cikin fadar tare da jama'arsu sai Dakaru suka tsaida kowa daga baya, Hantaru kadai aka bari ya nufi inda karagar sarki take. Tun daga nesa ya hada idanu da masoyiyarsa gimbiya Larziya ya ga tana yi masa murmushi tamkar ta mike ta rugo gareshi amma sai ta kanne. Shima Hantaru haka ya rinka ji a cikin ransa amma sai ya jure ya rinka maida mata da martanin murmushin. Sa'adda Hantaru ya iso kusa da karagar sarki sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa, fadawa suka karbi gaisuwarsu sannan sarki ya dubeshi ya ce, 86 TASKARNOVELS.COM.NG "Ya kai NAMIJIN DUNIYA, ina labarin abokin tafiyarka Rabbasu, kuma me ka zo mana da shi?" Sa'adda Hantaru yaji wannan tambaya sai jikinsa yai sanyi, nan take idanunsa suka ciko da kwalla. Ba tare da 6oye komai ba Hantaru ya kwashe labarin tafiyarsu tun daga farko har karshe ya zaiyane musu. Yana gama bada labarin sai ya ga ashe gaba dayan jama'ar da ke fadar kuka suke yi saboda tausayi a lokacin da shima kansa yana ta zubda hawaye. Nan take Hantaru ta fiddo takobin Saiful Lujara daga cikin rigarsa ya zareta daga cikin kufenta. Koda zare takobin sai haskenta ya cika fadar gaba ?aya, ta rinka kashewa kowa idanu. Gaba dayan bokayen garin da ke tsaye kusa da sarki sai sukayi sujjada ga takobin suka hada baki suka ce, "Daukaka da jinjina sun tabbata ga jarumin jarumai, gwarzon shekara, sadauki Hantaru mijin gimbiya Larziya". Koda jin wannan batu sai fadar gaba daya ta rude da shewa, kida da wake-wake. Sai da sarki ya daga 87 TASKARNOVELS.COM.NG sandar mulkinsa sannan aka yi tsit! Nan take sarki ya mife tsaye da kansa ya kirawo Halifan baban Rabbasu ya karfi kambun gasa daga hannunsa sannan ya taka yaje gaban Hantaru ya nuna nasa kanbun ya ce, "Gobe wannan kambu zai dawo jannunku ku zuri'ar Shurem," Koda jin haka sai fadar ta sake ru?ewa da shewa. Sarki ya sake daga kwagirinsa a karo na biyu aka yi tsit, tamkar mutuwa ta gifta, sannan y ce,"Hakika sadauki Hantaru ya bar abin tarihi kuma abin tunkaho a wannan birni namu, wanda zamu ci gaba da tutiya gami da alfhari da shi a dukkan sauran kasashen duniya saboda shi ne jarumin da zai auri 'yata gobe da yamma anan fadata. Tabbas Hantaru ye kawo karshen gardama da gaba a tsakanin zuri'ar makera da ta mafarauta da a wannan an gari nawA mai albarka saboda haka A yau na rushe wannan tsohuwar al'ada ta gasar tseren gudun barewa". 88 TASKARNOVELS.COM.NG Koda gama wannan jawabi sai Sarki yaje ya kama hannun 'yarsa gimbiya Larziya ya ja ta suka shige izuwa cikin gidan sarauta t?na waigen Hantaru tamkar ta kufce ta rugo gareshi, shima Hantaru sai yaji kamar ya ruga ya rukota amma da ya tuna da cewa gobe ne za a daura aurenta da shi sai hankalinsa ya kwanta ya bita da kallo cikin murmushi kawai. (Hallau dai kuna tare da Shuraih 99%) Bayan sarki da Larziya sun shige cikin gida sai fadar ta watse kowa ya kama gabansa. Saboda tsananin ?oki da murna Hantaru bai yi barci ba a wannan dare, a yadda ya ga rana haka ya ga dare, wato dai ya jera kwana biyu ke nan bai yi barci ba. Da gari ya waye, tun da sassafe zuri'ar Shurem suka cika gari da kade-kade da bushe- bushe gami da raye-raye suka yi ta walima a gidagida, unguwa-unguwa, ya zamana cewa Ana a bushasha da abinci da abin sha iri-iri a ko ina cikin birnin Darul Dulshul bisa samun nasarar ?auko takobin Saiful Lujara. 89 TASKARNOVELS.COM.NG Haka dai aka ci gaba da wannan shagalin biki har izuwa yammaci. Bangaren zuri'arsu Rabbasu kuwa banda kuka da bakin ciki babu abin da suke yi, domin sun yi asarar abubuwa uku. Abu na farko da suka rasa shi ne, shugabansu wato mahaifin Rabbasu sannan sun rabu da kambun gasa wanda ke hannunsu tsawon shekara da shekaru. Abu na na uku shi ne, magajin shugabansu wato sadauki Rabbasu jarumin da babu kamarsa a gaba daya nahiyar. La'asar nayi sai fada ta sake cika ta batse jda ama'a fiye da taron da aka yi na safe, wannan karon ma gaba daya birnin ne ya cika da baki daga sauran makotan birane saboda jin cewa za a daura auren gimbiya Larziya da jarumin da yaje har kogon Mazubatul Dulshul ya dauko takobin Saiful Lujara. Tun ana baiwa baki masauki har sai da takai cewa an daina basu domin babu. A wannan rana 90 TASKARNOVELS.COM.NG mutanen birnin Darul Habul sun yi matukar al'ajabi domin basu taba ganin cikowar jama'a ba a garinsu irin haka. Abin da basu sani ba shi ne, fiye da kaso saba in na cinkoson jama'ar ba mutane bane aljanu ne daga sassa na duniya suka zo a cikin siffar mutane domin kawai su ga jarumi Hantaru sadaukin da ya yi gagarumar bajintar da ta gagari dukkanin sadaukan duniya tsawon shekaru dubu uku da suka gabata. Zan ci gaba. Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part F Na Abdulaziz Sani m gini 91 TASKARNOVELS.COM.NG Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Ba tare da 6ata lokaci ba aka daura auren sadauki Hantaru da gimbiya Larziya a gaban miliyoyin jama'a kuma aka ?ankawa Hantaru kambun gasa ya ?aurashi a hannunsa, ai kuwa fadar gaba daya ta rude da shewa gami da tafi har kowa yaji kamar kunnensa zai dode. Nan dai aka cigaba da shagalin biki aka yi ta watsa dukiya gA maroka da mabukata. Abinci kuwa sai da ya zamo ga shinan kamar shara aka rinka yin bolarsu tsibi-tsibi saboda an rasa yadda za a yi dashi. Kowa a garin sai da ya cika da mamakin irin wadatar da aka samu a wannan rana domin abin yafi karfin iyakar bajintar Sarki, kai da gani ka san cewa akwai sa hannun aljanu. Haka dai aka ci gaba da shagalin biki amma har dare ya soma ango bai ga amaryarsa ba domin tunda aka ?aura aurensa da ita sai aka shigar da ita 92 TASKARNOVELS.COM.NG cikin gidan sarauta aka killaceta a cikin turakarta aka yi ta tsala ma ta ado iri-irk, idan a ka yi wannan sai a ga bai yi ba a sake yin wani har sai da aka yi kala saba'in. A na saba'in ne matan da ke yin adon suka gamsu gaba ?ayansu cewar ya yi. A wannan lokaci dare ya fara tsalawa don haka sai aka dauki amarya cikin hanzari aka kai ta gidan su Ango. Bayan masu kak amarya sun watse sai ango ya shigo ?akin amaryarsa yana sanye da tufafi masu tsadar gaske na alhariri. Da shigar Hantaru cikin dakin sai ya iske amaryarsa zaune a gefen gado ta sha lullu6i fuskarta a rufe. Cikin matukar farin ciki ya karasa gareta fuskarsa cike da murmushi ya kasa rufe baki. Hantaru ya zAuna daf da Amaryarsa sannan yasa hannayensa biyu ya yaye labulen da tayi. 93 TASKARNOVELS.COM.NG Koda ya yi arba da fuskarta sai hankalinsa ya dugunzuma ainun, ya dubeta cikin tsananin mamaki ya ce, "Ya ke masoyiyata abar begena dare da rana ina dalilin zubar Wannan hawaye na idanunki? Ki sani cewa yau rana ce ta farin ciki ba ta bakin ciki ba. Ina son ki gaya mini abin da ke damunki ko mene ne shi in dai ina da ikon kau da shi, sai na kawar da shi." Sa'adda gimbiya Larziya taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya tayi shiru kamar ba za ta ce komai ba, daga can sai ta daga kai ta dubi Hantaru ta ce, "Ya kai mijina hakika baka san komai na ba domin baka san labarina ba kawai ka zo garin nan ne a matsayin bako kana ganina ka kamu da kaunata. Ina son na sanar da kai cewa ina cikin wani bakin ciki tsawon shekaru wanda duk duniyar nan babu wanda zai iya kawar mini da shi face kai. Ka saurari labarin da zan baka yanzu da kunnen basira domin ka fahimci matsalar da kuma babban burin da ke gabana." Sa'adda Larziya ta 94 TASKARNOVELS.COM.NG zo nan a zancenta sai tayi shiru gami da ajiyar zuciya sanann ta ci gaba da labari Kamar haka "Mahaifina bai taba yin soyayya ba da wata ya mace har ya hau karagar mulkin wannan birni na Darul Mahabul kuma sai da ya shekara hudu akan karaga bai yi aure ba. Al'amarin da ya dami fadawansa kenan da sauran al'umman gari ke nan suka dameshi akan batun lallai ya kamata ya yi aure domin ya tsare mutuncinsa da masarautar gaba ?aya. Lokacin da mahaifina ya ga jama'a sun matsa ainun akan wannan batu sai ya tara dukkan jama'ar gari ya ce, "Idan har ana son ya yi aure dole ne ayi abu biyu. Abu na farko dole ne a samo masa kyakkyawar budurwa wacce babu kamarta a gaba daya nahiyar kuma dole ne a shirya gagarumar gasa irin wacce ko a tarihi ba a taba yin kamarta ba". Sa'adda sarki ya gama jawabi sai hankalin kowa ya dugunzuma aka rasa wanda zai ce kala. 95 TASKARNOVELS.COM.NG Daga can sai Wazirin sarki ya mike tsaye ya dubi sarki ya ce, "Ya shugabana hakika ka zo mana da baban al'amari wanda ba zamu iya saurin yanke hukunci ba face ka bamu lokaci mu yi tunanin mafita. Dole ne mu nemi manyan bokayen kasar nan domin su yi mana bincike bisa wannan al'amari". Koda jin haka sai sarki ya yi murmushi sannan ya ce, "Ya kai waziri na baka wuka da nama akan kaje ka zartar da komai amma ka sani cewa kwana goma sha hudu kacal na baka". Koda gama fadin haka sai sarki ya mike tsaye ya shiga cikin gida, a sannan ne fadar ta watse kowa ya kama gabansa. Al'amarin Waziri kuwa, bayan ya bar fada sai ya kira wadansu manyan hadimansa amintattu guda hudu ya basu wasika suka 96 TASKARNOVELS.COM.NG yi hawa izuwa manyan garuruWan birnin guda hudu akan su je su gaiyato manyan bokayen da ake takama da su. Su kuwa bokayen da ake takama da su a cikin birnin Darul Mahabul guda biyu ne kawai wato boka Sulbaini da mahaifin Rabbasu suma sai WAZiri ya kirasu ya sanar da su cewa, "Ya tura a kirawo sauran bokaye kasar guda hudu domin a ZAuna gaba daya a tattauna akan matsalar sarki. Koda jin haka sai Sulbaini da baban Rabbasu suka yi murmushi, Sulbaini ya ce, "Ya kai waziri ai ka wahalar da kanka ne kawai domin mu kadai mun isa mu fadi hanyar da ZA a bi a warware matsalar sarki, to amma masu iya magana sun ce ba a kwacewa yaro garma kuma dan hakin da ka raina shi ke tsone maka ido. Babu mamaki wani daga cikin wadannan bokaye yazo da wani abin wanda yafi namu don haka zamu jira isowar sauran bokayen hudu" Sa'adda waziri yaji wannan batu sai yai murmushi sannan yayi godiya ga su boka Sulbaini ya sallamesu. Bayan kwana tara daidai sai ga wadannan bokaye sun amsa kiran Sarki. Da zuwan su sai waziri ya tara su a cikin gidansa tare da su boka Sulbaini sannan ya yi bayanin abin da yasa aka tara su kuma aka bukaci kowannensu ya fadi tasa shawarar. Daya 97 TASKARNOVELS.COM.NG bayan daya sai bokayen suka rinka nuna hoton budurwar da sarki ya kamata ya aura da inda take da kuma irin gasar da ya kamata ayi ta neman aurenta, a cikin madubin tsafi. Ya yin da bokan farko ya nuna tasa sai waziri ya kidime domin gani yake kamar a duniya ma kaf ba za a sami kamar ta ba, amma da boka na biyu ya nuna tasa sai ya ta fi ta waccan nesa ba kusa ba. Haka abin ya kasance bi da bi ta biyu ta fi ta farko, ta uku ta fi ta biyu, kuma ta hudu ta fi ta uku. Lokacin da aka zo kan baban Rabbasu sai ya nuna wata kyakkyawar budurwa wacce ?uk ta fi sauran kyau ya ce, "Wannan sunanta Zarifa kuma yar wani babban attajiri ce a birnin Kisra, tabbas a gaba dayan wannan nahiya babu mai kyau kamarta a can birnin Kisran ma tana da masoya da yawa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan manyan sarakai da ya'yan manyan attajirai da kuma 'ya 'yan manyan bokaye. A halin yanzu an rasa wanda za a baiwa ita daga cikin masoyan nata, amma komai na hannun sarkin Kisra, shi ake jira kawai ya yanke hukuncin akan ta. ldan har sarki ya sami nasarar auro Zarifa za a shirya gasar Jarumtama ta musamman a tsakanin manyan mayaka domin Su debewa jamaa kewa a lokacin da ake shagalin bikinsa. 98 TASKARNOVELS.COM.NG Lokacin da waziri ya ga Zarifa a cikin madubin tsafin Baban Rabbasu kuma ya gama sauraron jawabin Baban Rabbasu sai ya ude, kuma ya cika da tsananin al'ajabi ya ce, "Na rantsed darajar iyayena babu wata nahiya da za aje a SAmi kyakkawar mace kamar wannan Zarifan, don haka lallai zan kaiwa sarki labarinta domin ya shirya da kansa yaje ya nemi aurenta a can birnin na Kisra. Koda jin haka sai boka Sulbaini ya bushe da dariya, al'amarin da ya matukar baiwa kowa mamaki ke nan a wajen, aka yi tsit ana kallonsa kawai. Daga can sai boka Sulbaini ya tsuke bakinsa ya murtuke fuska sannan ya nutsu ya dubi kowa daya bayan daya ya ce, "Akwai wata budurwar wacce idan ba ta fi Zarifa kyau ba sai dai su yi kunnen doki sunanta Mafira, kuma 'yar uwar Zarifa ce uwa daya uba daya suke, wato Hassana da Hussaina ne amma ita Mafiran tun da aka haife ta bata taba

Chapter 4 of 14