kyar a
lokacin da numfashinsa ke sarkewa ya kura
mani ido a lokacin da hawaye ke shatata daga
cikin idanunsa, sannan yayi mani murmushin
karfin hali ya ce yake yar babbar masoyiyata
kiyi sani cewa ina farin ciki a yau daya kasance
zan mutu a wannan kyawawan hannaye na ki,
ba wani bane yayi mani wannan mugun aiki ba
face mahaifin Barzuma Ibn Kalsuwar domin yq
dauki fansar kisan da nayi wa dansa, farin cikina
na biyu shine na sadu dake kafin raina ya fita
dan haka yanzu take zan mallaka maki dukkan
303
TASKARNOVELS.COM.NG
wani sirrin tsafina dana gada a wurin mahaifina,
ina mai gargadinki da kada ki kuskura kiyi
amfani da wannan sihiri face a ranar da wani
gawurtaccen boka yazo wanann birni naku da
nufin ya rabaki da mahaifinki, magnata ta
karshe a gareki ita ce duk yadda zaki yi kiyi
domin ki tabbar da cewa kin auri mijin da
gimbiya Ramlatus siyam yar sarki Nashmir zata
aura, ta haka ne kadai zaki iya samun babban
matsayi da daukaka a duniya, yanzu na
umarceki da ki bude bakin ki.
Koda jin haka sai na bude bakin nawa ba tare da
wata gardama ba, nan take naga wani irin jan
hayaki yana fitowa daga cikin bakin aljani
Sautul Baharu yana shiga cikin nawa bakin,
hasken na gama shiga sai jikinsa ya sandare
komai nasa ya daina aiki. Koda ganin haka sai na
rungumeshi na fashe da matsanancin kuka
saboda tsananin shakuwa da shakuwar da nayi
da shi, naji kmaar a sannan ne na rasa
mahaifiyata. Na dade a cikin alhinin rashin
Aljani Sautul Baharu bn samu nutsuwa b sai
bayan wata uku.
Sa'adda Gimbiya Rahila ta zo nan a zancenta sai
boka Muzafar da sarki Lafaru suka cika da
304
TASKARNOVELS.COM.NG
tsananin al'ajabi, boka Muzafar ya ja dogon
numfashi annan ya ce hakika Ruwa baya tsami
banza, ai tunda naji kin fadi sirrina nasan cewa
kina tare da sirrin tsafi mai karfin garske a
jikinki, yanzu na ji labarinki sai kuma ki fada
mana sharadin da kike son gindaya mana.
Tai murmushi tace ai nagama gindaya maku
sharadina a cikin labarin dana baku, sharadin
kuw shine bazan sa aljani Maraful Dauwas ya
biya maku bukatarku ba face kun dauki
alkawari cewa idn har bukatarku ta biya sarki
Lafaru zai aure ni a ranar da ya auri Gimbiya
Ramlatus siyam domin na samu matsayi da
daukaka irin nata, tunda yanzu ni da ita munyi
kunnen doki a fagen kyau.
Lokacin da boka Muzafar da sarki Lafaru suka ji
wannan batu daga bakin Gimbiya Rahila sai
suka dubi jjuna tare da yin shiru har izuwa
tsawon yan dakiku, suka ma rasa abinda zasu
ce, daga can sai boka Muzafar ya dago kai ya
dubi Gimbiya Rahila ya ce ki bamu zuwa gobe
muna da bukatar yin shawara.
Da jin haka sai Gimbiya Rahila ta yi murmushi
sannan ta juya da nufin ficewa daga cikin tantin,
305
TASKARNOVELS.COM.NG
har ta je bakin kofar fita sai ta juyo ta dubi sarki
lafaru ta ce kada ka kuskura ka bayar da
labarina ga sauran abokan tafiyarmu, domin
bana son su san koni wace ce, kuma suga
zahirin kyawuna da surata har sai mun isa
kogon darul ikisina, tana gama fadin hakan sai
ta fice daga cikin tantin ta bar boka Muzafar da
sarki Lafaru a cikin wani irin yanayi na tsananin
damuwa kamar ruwa ya cisu.
Da sassafe su duka suka tashi suka kimtsa,
jaruman biyar suka gyara makamansu kowa
yayi damara sannan boka Muzafar ya dubesu
daya bayan daya ya ce acikin ku waye zai wuce
gaba yayi mana jagora a cikin wannan daji da
zamu shiga?
Ko da jin wannan tambaya sai kowa yayi shiru
aka rasa wanda zai wuce gaba, koda ganin haka
sai sarki Lafaru ya ce ya kai wannan babban
boka kayi sani cewa ai kaine kafi kowa cancanta
da yin jagora a wannan tafiya, tunda kaine uban
tafiya, kuma kafi kowa sanin hanya.
Boka Muzafar ya ce kwarai kuwa haka ne
abinda ka fada, amman ni kaina ina shakkar
abinda ke kan hanyar nan, dan haka ba zan iya
306
TASKARNOVELS.COM.NG
wucewa gaba ba, face na samu wanda zai tayani
jagoranci har na samu kwarin guiwa, caraf sai
gimbiya Rahila ta ce ni zan tayaka jagorancin
wannan tafiya.
Nan take Gimbiya ta wuce can gaba ta tsaya
kusa da boka Muzafar, al'amarin da ya baiwa su
sadauki Haiman mamaki kenan, Zarina ta dubi
boka Muzafar ta ce wai shin ita waccan
budurwar da tayi gangancin shigewa kn gaba
wace ce ita? Me yasa tunda aka fara wannan
tafiya take boye fuskarta da kuma jikinta? Wai
shin ma mene ne amfaninta a wannan tafiya?
Boka Muzafar ya dubi Zarina ya ce Ya Zarina ai
bai kamata ki tambayi kaza hanyar rafi ba,
agwagwa zaki tambaya ki sha labari, babu
wanda zai iya amsa maki wadannan tambayoyi
naki face ita kanta.
Kafin wani daga cikin abokan tafiyar ya kara
cewa wani abu, sai boka Muzafar ya ce in son
duk wnada yasan shi ba jarumi bane ya tsaya a
tsakiya, ku kuma jaruman ku rabu gida biyu,
kaso daya su tsaya a baya, dayan kason kuma su
tsaya a gaba.
307
TASKARNOVELS.COM.NG
Ba tare da wata gardama ba kuwa aka yi hakan,
ya zamana cewa Lumaira, Masnur, mahaifiyar
jarumi Imran sarkin Farisa da Sadauki Shaharan
suka tsaya a tsakiya, Sadauki Haiman da jaruma
Shadira suka tsaya a gabansu, Lumaira, Jarumi
Imran da Zarina uwa suka tsaya a can baya,
faruwar hakan keda wuya sai boka Muzafar da
gimbiya Rahila suka wuce kan gaba suka nufi
cikin dajin, bisa mamaki sai boka Muzafar yaga
sarki Lafaru shine ke biye da su, al'amarin daya
matukar bashi mamaki kenan ya juyo ya
dubeshi gami da cewa ya kai abokina hin ka
manta cewa yanzu kai ba Sadauki ba ne?
Da jin wannan tambaya sai Lafaru ya jinjina kai
ya ce kawai gani nayi duk inda na tsaya walau a
tsakiya, gaba ko baya ban isa na gujewa
kaddarata ba, fatana kawai shine mu samu
nasarar abinda muka fito nema... Kafin Lafaru ya
gama rufe bakinsa sai kawai yaga sun shigo
cikin wani mugun daji mai matukar kwarjini da
ban tsoro, wasu irin dogayen bishiyune a cikin
dajin masu kahonnin, a jikin kahonnin akwai
kwarangal din kawunan bil'adama wadanda
daka gansu kasan sun dade a sagale tsawon
shekaru, domin har yana ta lullube wasunsu, a
kasa kwarangalolin ne birjit babu adadi, ta
308
TASKARNOVELS.COM.NG
kansu suka rika bi suna wucewa, da zarar sun
takasu sai dai kaji suna kakkaryewa da rgujewa.
Ganin wannan kwarangalolin ne yasa su Masnur
suka firgita ainun jikinsu ya kama kyarma,
tabbas inda zasu ji wani kwakkwaran motsi da
nan take zasu saki fitsari ko sun runtuma da
gudu, wani abun mamaki shine Lumaira da ta
kasance makauniya bata firgita ba kamar yadda
sauran suka firgita, kawai sai ta ci gaba da
dogara sandarta tana mai laluben hanya, kuma
tana amfanin da sautin sawun wadanda ke
gabanta, sai da su boka Muzafar suka yi tafiyar
sa'a daya da rabi cif sannan suka iso tsakiyar
wannan daji mai ban tsoro, ba su hadu da komai
ba kuma basu ji motsin komai ba koda kuwa
kukan tsuntsu ne, kwatsam! Suna cikin tafiya sai
suka ga wani abu kamar hayaki bakikkirin ya
cika sararin samaniya kamar hadarine ya
gangamo. Cikin razani kowa ya tsaya cak,
jaruman suka daga makamansu suka tsaya suna
jiran abinda zai biyo baya, kawai sai suka ga
wannan bakin hayaki ya rikide ya koma siffofin
wasu aljanu ababen firgitarwa, nan fa suka
ringa durowa daga sararin samaniya. Aljanun
suna da kawuna irin na birrai, kuma munana ne
basu da kyan gani, gangar jikinsu kuwa siffar
309
TASKARNOVELS.COM.NG
batoyi gareta, suna da kafafu da hannaye guda
shida-shida, a jikin kowanne hannu da kafa
akwai yatsu guda arba'in kuma kowanne dan
yartsa yana dauke da farce mai tsananin kaifi da
tsini tamkar adda sabuwar washi, ko dutse suka
karta da faratan nasu sai dai kaga dutsen na
rabewa gida biyu.
Koda su Masnur suka yi arba da wadannan
dodanni sai suka yanke jiki suka fadi kasa a
sume, saboda tsananin gigicewa, Lumaira ce
kadai ta rage a tsaye itama sabida bata da
idanune amman inda taga wadannan dodanni
aljanun da babu abinda zai hanata sumewa.
Sadauki Haiman, jarumi Imran, Jaruma Shadira,
Gimbiya Zarina, da boka Muzafar kuwa sai suka
dubi junansu, cikin hadin baki suka kwarara
uban ihu sannna suka ruga cikin aljanun suka
hausu da sara gami da suka, amman sai suka ji
kamar duwatsu suke sara, domin jikin aljanun
ko kwarzanewa baya yi, duk sa'adda makaman
su Haiman suka hadu dana aljanun sai dai kaga
tartsatsin wuta yana tashi sama, al'amarin daya
dugunzuma hankalinsu kenan ainun
musamman ma d suka fara jaraba kkarfin
310
TASKARNOVELS.COM.NG
sihirinsu sukaga shima yaki yin tashiri akan
aljanun.
A daidai wannan lokacin ne aljanun suka fara
mayar da martani suka fara kaiwa jaruman sara
da faratan hannunsu domin su nakastasu, kuma
suna ki masu suka a fuska dan su lalata masu
idanu. Haka dai suka ci gaba da shawagi akan
mata suna son su suresu suyi sama da su. Koda
su boka Muzafar suka gane nufin aljanun sai
suka saka matan cikin a tsakiya aka ci gaba da
bakin artabun a haka, ya zamana cewa su boka
Muzafar sun kasa tarwatsa aljanun, haka suma
aljanun sun kasa illatasu balle har su samu
damar sure matan, ana cikin wannan gumurzun
ne wasu daga cikin aljanun masu naci suka
samu nasarar yakushin boka Muzafar da
gimbiya Zarina a hannu, nan take suka kwala
ihu kuma suka zube a kasa a lokacin da jiri ya
debesu.
Koda ganin haka sai wasu aljanun suka yunkuro
zasu yanyamesu domin su dada sassarasu, koda
Gimbiya Rahila ta fahimci abinda aljanun ke
nufin yi sai ta daka tsalle sama ta tarwatsa su da
karfin sarar takobinta, nan fa ta rinka
ragargazarsu cikin tsananin bajinta gami da
311
TASKARNOVELS.COM.NG
al'ajabi, domin tun a saman ta dinga katantanwa
da shawagi tamkar tsuntsuwa hakan yasa ta
addabi aljanun gaba dayansu, kuma ta hana
dayansu ya cutar da su boka Muzafar da ke
kwance a kasa.
Koda ganin wannan gagarumar bajinta da
gimbiya Rahila ke yi sai su sadauki Haiman suka
cika da tsananin mamaki, kuma suka samu
kwarin gwiywar kara zage damtse, nan fa aka ci
gaba da bakin gumurzu mai ban tsoro, ana cikin
haka ne Sadauki Shaharan ya dawo cikin
hayyacinsa ya lura cewa idan aka ci gaba da
wannan yaki a waje daya tabbas su Gimbiya
Rahila zasu gaji, in kuwa suka gaji to sai aljanun
sun samu nasara akansu, koda gama ayyana
haka a cikin ransa sai ya yunkura cikin tsananin
zafin nama ya suri yaro Masnur ya goyashi a
bayansa ya daure shi tamau, sannan ya falfala
da azababben gudunnan nasa, ai kuwa sai wasu
daga cikin aljanun suka rufa masa baya aka kasa
tsere. Nan fa aljanun suka ga abin al'ajabi iri
wanda basu taba gani ba, domin sunga
bil'adama wanda yafi aljani gudu, irin gudun da
Shaharan yake yi yafi gudun tauraruwa mai
wutsiya
312
TASKARNOVELS.COM.NG
.
.
.
Sai kawai suka tarwatse suka fada dajin suna
masu neman maboya, kafin kace kabo babu
kowa a gaban Gimbiya Rahila face aljanun dake
zube kasa nakasassu. Koda ganin haka sai
Gimbiya Rahila ta sunkuya ta sabi Shaharan ta
dirashi a bisa kafadarta ta wuce da shi izuwa
karshen dajin, inda ta kai su jaruma Shadira ta
ajiye.
Su boka Muzafar sun kwakkwance suna jinyar
raunikan jikinsu sai kawai suka hango gimbiya
Rahila ta tunkaro su dauke da sadauki Shaharan
akan kafadarta tana mai tafiyar kasaita tamkar
ta dauko buhun yayi. Da kyar cikin juriya suka
mike tsaye suka kura mata idanu cikin tsananin
mamaki har ta iso garesu, tana ajiye Shaharan a
kasa sai jaruma Shadira ta yi sauri ta zo kansa ta
fara sa mashi magani akan raunin nasa, nan take
jinin dake zuba a bayan nasa ya daina zuba.
Daman tun kafin Rahila ta zo da Shaharan duk
313
TASKARNOVELS.COM.NG
masu raunika an yi masu magani sun dawo cikin
hayyacinsu.
Bayan kamar dakika dari da sittin sai Shaharan
ya farfado, koda ya bude idanunsa sai ya budi
baki ya ce Ina dokina ya ke?"
Cikin fushi Gimbiya Rahila ta dubeshi ta ce da
shi yanzu kai baka damu da rayuwarka ba,
dokinka ne ma a ranka.
Shaharan ya ce ai dana rasa dokina gwara na
rasa rayuwata, tunda saboda shi na siyar da
rayuwata na taho wannan daji. Rufe bakin
Shaharan keda wuya sai ga aljani Marhabul
Zaurus a sama dauke da dokin Shaharan. Cikin
tsananin farin ciki Shaharan ya mike tsaye yana
kallon dokin nasa, aljani Marhabul Zaurus na
sauka kasa sai Shaharan ya ruga gareshi ya
rungume dokin nasa yana shafa wuyansa cikin
murna.
A sannan ne boka Muzafar ya dubi aljani
Marhabul Zaurus ya daka masa tsawa ya ce ina
ka tafi ne tunda muka fara gumurzu da
wadannan mugayen aljanu ban ganka ba?
314
TASKARNOVELS.COM.NG
Marhabul Zaurus ya risina cikin biyayya ya ce
Ya shugabana ka sani cewa idan na fusknaci
wadannan mugayen aljanu dukan falan daya
zasu yi mani na halaka, bisa Wannan dalili ne na
shiga kogon wata bishiya na saje da ita, ina
kallon duk abinda ke faruwa tsakaninku da
aljanun har saida naga jarumar jarumai, kuma
boyayyar basadaukiya ta ragargazasu ta kuma
dauki Shaharan ta tafi, sannan na fito daga cikin
kogon bishiyar kum na dauko dokin Shaharan
na taho nan.
Da jin wannan batu sai boka Muzafar ayi ajiyar
zuciya nan take yaji yayi nadama bisa
jagorantar wannan tafiya, domin a yanzu
zuciyarsa ta karaya, ya fahimci cewar abu ne
mayuyaci gabadayansu su iya tsallake
hatsarurrukan dake wannan daji, tunda gashi
tun kafin su shiga wadannan mugayen
dazuzzukan guda biyar sun raina jarumtakarsu,
kuma wacce ba a taba zaton zata yi wani abu ba
sai gashi ita ce ta fi kowa jarumtaka, kuma inba
dan taimakonta dana sadauki Shaharan ba da
sai kowa ya halaka.
Boka Muzafar ya kira gimbiya Rahila suna
tattauna, inda ya dubeta ya ce yake jarumar
315
TASKARNOVELS.COM.NG
jarumai kuma kuma sarauniyar kyawawa yq
akayi kika samu irin wannan gagarumar
jarumtaka haka ta karfin damtse alhalin a zahiri
babu wani alamun sadaukantaka a tare da ke.
Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya Rahila
tayi murmushi tace inda zamu kwana uku ina
baka labarin yadda aka yi na samu
sadaukantaka ta lokaci ba zai ishemu ba har na
gama baka labarin, amman gaba idan muna raye
kuma da dama zan baka labarin, yanzu sai ku
tashi mu cigaba da tafiya domin mu riski rukuni
na biyu dana uku na wannan mugayen aljanu
mu gama da su sannan mu shiga manyan
dazuzzukan guda biyar wadanda daga su sai
kogon darul ikisina.
Sa'adda Rahila ta zo nan a zancenta sai boka
Muzafar ya dubeta ya ce haba yake jarumar
jarumai shin bakya ganin gabadayanmu babu
mai kwarin jiki a jikinmu face wadanda
tsautsayin bai rutsa da su ba, ke kadaice mai
cikakken lafiya a cikin wadannan jaruman
wannan tafiya, ai dole ne mu zauna anan muyi
jinyar jikinmu koda tsawon kwana biyu ne
kuwa.
316
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokacin da boka Muzafar ya zo nan a jawabinsa,
sai sarki Lafaru dake daf da shi ya ji hankalinsa
ya tashi, ya ji kamar ya fashe da kuka. Cikin
tsananin ya dubi Muzafar ya ce ya kai babban
boka shin mantane cewa ka ce dole ne na auri
Gimbiya Ramlatus siyam a cikin kwanaki da
baza su haura sittin ba, dan kuwa har muna bata
lokaci a cikin wannan tafiya haka to gabadaya
shirinmu zai wargaje.
Koda jin haka sai boka Muzafar ya daka wa
Lafaru tsawa ya ce ya kai wannan sarki kayi sani
cewa halin da muke ciki yanzu ba na tunanin
yadda burinmu zai cika bane, muna kan tunanin
yadda zamu tsira da rayuwarmu ne.
Sarki Lafaru ya dubi boka Muzafar a fusace ya ce
wace irin magaana kake haka, ai rai ba a bakin
komai yake ba muddin akwai biyan bukata.
Boka Muzafar ya sake fusata ya daka wa Lafaru
tsawa a karo na biyu ya ce idan kai baka damu
da rayuwarka ba, mu mun damu da tamu.
Saboda haka idan zaka iya sai ka kama hanya
kayi tafiyarka kai kadai, na fuskanci ka manta da
cewa idan buri y cika babu rai sam bashi da
wani amfani.
317
TASKARNOVELS.COM.NG
Koda gama fadin haka sai boka Muzafar ya
koma gefe daya ya kishingida yana mai duban
raunin dake jikinsa, shi kuwa sarki Lafaru sai ya
matsa daf da gimbiya Rahila ya dubeta y ce Ya
ke jarumar jarumai me zai hana ki zo mu cigaba
da wannan tafiyar biyu rak, dan na fuskanci
cewar ke kadai ma zaki iya maganin dukkan
wasu masifun dake kan hanya.
Da jin wannan batu sai Gimbiya Rahila ta dubi
Lafaru cikin tsananin fushi ta ce indai haka kake
tunani to ka yaudari kanka, ina tabbatar maka
da cewa idan har muka kuskura muka shiga
wadannan dazuzzuka guda biyar babu jaruman
can to sai mun halaka, domin ko wanne daji
akwai jarumin da zai iya ceton rayuwarmu,
dukkansu can da kake gani kowa da irin tasa
baiwar da kuma sadaukantarsa, gama fadin
hakan keda wuya sai Rahila ta je ta zauna nesa
kadan da kowa, sannan ta kwanta domin ta
huce gajiyar da ke jikinta.
Wannan shine abinda ya faru ga su sarki Lafaru
bayan sun tattaro abokan tafiyarsu sun nufi
kogon darul ikisina.
318
TASKARNOVELS.COM.NG
Acan birnin Kufa kuwa a ranar da kwanaki
arba'in suka cika, tunda duku-dukun safiya aka
hango dakarun sarki Nurwas sun durfafo,
saboda yawan rundunar idan mutum ya
hangosu daga nesa sai yayi zaton cewa sun
tokare da sararin samaniya, saboda ba a iya
hango karshensu, karar kofaton dawakansu da
rakumansu kuwa ya cika kunnunwan mutane
har ta kai cewa sun haddasa karamar girgizar
kasa, ya zamana cewa gabadaya gidajen birnin
Kufa sun kama girgiza kamar zasu ruguje. A
lokacin da wannan al'amari ke faruwa sharlis na
cikin bangarenta da danta Shaddadu a zaune
tana koya masa yadda ake fada da takobi. Koda
taji sukuwar dawakan abokan gaba sun durfafo
birnin sai ta yi sauri ta shiga daki ta cire tufafin
jikinta ta saka fararen sulke sannan ta saka
wasu siraran takubba a kugunta na hagu da
dama, kuma ta saka hular karfe sannan ta saka
wasu dogayen takalma na fata iya gwiywa,
hakika shigar da Sharlis ta yi ba karamin kyau ta
yi ba, kuma ta yi kwarjini ainun. Da fitowarta
daga cikin dakin sai kawai ta dauki danta
Shaddadu ta goyashi ta daure tamau a bayanta,
kawai sai ta ji Shaddad ya ce da ita Ya ke
319
TASKARNOVELS.COM.NG
Ummata ya zaki tafi da ni yaki ban dauki
takobina ba.
Koda jin haka sai sharlis ta yi murmushi ta ce
kada ka damu ya kai dana lokacin fara naka
yakin bai yi ba, yanzu dai in so kaga yadda nake
nawa yakin ne dan ka koya. Tana gama fadin
hakan sai ta fice da sauri ta nufi bangaren Sarki
Lafaru, ga dakaru tsaitsaye a bangaren sarki
Lafaru amman babu wanda yaga Sharlis da
danta har ta isa can cikin turakar tasa. Da isarta
sai kawai ta yi arba da Sarki Lafaru a tsaye yana
shirin fita yaki har ya daura damara ya soka
takobinsa, al'amarin da yayi matukar baiwa
Sharlis mamaki kenan.
Koda Sarki Lafaru yaga sharlis tsulum a gabansa
sai ya ja da baya a tsorace ya cw da ita Mene ne
kuma ya kawoki wajena tare da danki?
Da jin wannan tambaya sai sharlis ta yi
murmushi sannan ta ce Na fito ne domin taya ku
yaki, ka sani cewa idan aka rushe daularka an
cuceni dan haka bazan samu damar daukar
fansa akan ka ba, sabida haka dole ne na bada
tawa gudummawar a wannan yaki domin kare
wannan birni. Sharlis ta sake duban sarki Lafaru
320
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin mamaki ta ce Yanzu kai saboda me kake
shirin fita yaki, alhalin kasan cewa na cire maka
dukkanin karfin damtsenka tun daga ranar da
ka sadu da ni?
Sarki Lafaru yayi murmushi ya ce Ai abin kunyq
ne a gareni ina sarki amman ace yau gashi an zo
yaki kasata na buya ban fito ba, gwara na fito
koda kuwa za a yi mani kwab daya ne na mutu.
Sa'adda Sharlis ta ji wannan batu sai ta bushe da
dariya sannan ta ce ai indai abin kunya ne ka
gamu da shi, sai nan gaba ma idan dana shaddar
ya girma ya zama gawurtaccen sadauki da babu
kamarsa, sannan ne zaka wulakanta
mutuncinka ya zube, kimarka ta watse, duk
dukiyarka ta salwanta, sannan a karshe ka rasa
mulkinka da rayuwarka bayan dana yayi maka
kisan gilla irin wanda kayi wa kakanni na da
iyayena, lokacin da Sharlis ta zo nan a zancenta
sai kawai taga sarki Lafaru ya takarkare ya
bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya ce Ni
kuwa zanga yadda dana na cikina zai zamo
abokin gabana har ya kasheni.
Da jin haka sai Shaddad da ke goye a bayan
sharlis ya leko sannan ya dubi sarki Lafaru ya ce
321
TASKARNOVELS.COM.NG
Ya kai abbana tabbatas zakaga yadda zan
wualakanta ka a duniya, na tarwatsa kwanciyar
hankalinka da dukiytarka, sannan da sannu na
zama sanadin ajalinka.
Da jin haka sai Lafaru ya sake bushewa da
dariya a karo na biyu, haka yayita wannan
mahaukaciyar dariyar kamar ba zai daina ba,
al'amari da yayi matukar baiwa Sharlis mamaki
kenan ta fara zancen zuci ta ce "Anya kuwa
wannan sarki Lafaru ne wanda na sani, a sanina
tun daga ranar dana cire wa sarki Lafaru
Sadaukantakarsa yake tsorona kuma ya tsorata
da lamarina, shin mene ne yasa yanzu ya daina
shakkata har ma yake magana cikin gadara, ya
zama dole a gareni bayan na gama wannan yaki
nayi bincike a cikin hallarar tsafina na gano ko
shine Lafaru na gaskiya.
Marubucin yace wane bangare ne zai samu
nasara a wannan azababben yaki da za'a fafata
tsakanin mutanen sarki Nurwas da mutanen
Sarki Lafaru?
322
TASKARNOVELS.COM.NG
Shin idan sharlis ta yi bincike a cikin hallarar
tsafinta zata gano cewa Lafaru dake tare da ita
ba na gaskiya ba ne, idan ta gano hakan wane
irin mataki zata dauka?
Wace irin bakar wahala su boka Muzafar zasu
sha a cikin wannan doguwar tafiyar dake
gabansu ta zuwa kogon darul ikisina?
Su waye zasu rasa rayukansu a tafiyar?
Shin aljani Maraful Dauwas zai amince da
bukatar su sarki Lafaru?
Shin sarki Lafaru zai samu mallakar Gimbiya
Ramlatus siyam har ya aureta?
Shin Gimbiya Rahila zata cika burinta na samun
daukaka da matsayin da take nema?
323
TASKARNOVELS.COM.NG
Marubucin ya ce mu hadu a Littafin Mazan jiya
na Uku dan jin karshen hikayar Jarumi
Shaddadu da kuma hikayar Sadauki Hulkas na
birnin Romaniya.
Daga mai debe maku kewa a kullum da koda
yaushe
Abdulaziz Sani Madakin Gini.
324
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 14