Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana tafiyar tatata kamar sabon dan kaciya a lokacin da karyayyen 47 TASKARNOVELS.COM.NG hannunsa ke gilu-gilu kamar zai fadi kasa ya nufi inda Hantaru ke kwance a sume. Nufinsa kawai yaje ya tallafo kan Hantaru ya yi masa rotse a ka, wato ya dagwargwaza fuskar Hantaru. Har Maridin ya isa kan Hantaru ya tsaya, Hantaru bai farfado ba. Nan take Maridin yasa hannunsa ya tallafo kan Hantaru da nufin ya naushi fuskar da dukkan karfinsa. A dai-dai wanann lokaci ne Hantaru ya farfado, idanunsa suka bude. Koda ya ga maridin ya daga hannunsa lafiyayyen zai nausheshi. sai ya yunkura cikin mugun zafin nama ya kamo kary?yyen hannun ya fincika. Saboda tsananin zafi da zogin da maridin yaji bai san sa'adda ya saki ftsari ba. Kafin ya yi wani yunkuri na cutar da Hantaru tuni Hantaru ya sake kamo daya Iafiyayyen hannun shima ya gabza mAsa naushi da guiwar hannunsa. Take hannun ya karye ya yi kara 48 TASKARNOVELS.COM.NG kamar na farko. Maridin ya fadi kasa da ruf da ciki. Duk da haka Hantaru bai kyaleshi ba sai da ya kama kafafunsa duka biyun da karfin tsiya suma ya kakkaryasu daya bayan daya. ihun da maridin ya yi a lokacin da Hantaru ke karya masa kafafunsa ya ninka wanda ya yi da furko sau goma, domin gaba daya halittun da ke dajin sai da suka firgice suka kama sauya sheka. Sauran wadunnan rijiyoyi kimanin guda dari da casa in da ya'ya sai da murafensu suka bude, gaba daya a lokaci guda. Abinda ya fara yin fitar burgu daga cikin rijiyoyin shi ne, takobin Saiful Lujara. Wata irin takobi ce ta musamman wacce aka kerata da lu'u lu'u sai sheki da walwali take tana kashe idanu. Nan take haskenta ya haskake kogon gaba daya. Da wani irin mugun karfin gudu takobin ta taso sama. Koda Hantaru ya yi arba da takobin sai ya yi wuf ya taka bayan maridin ya daka tsalle sama yabi takobin tamkar an harbashi daga cikin kwari. A can saman ya kamo murikin takobin. Koda ya sunkuyo da kansa kas 49 TASKARNOVELS.COM.NG a lokacin da yake durowa sai ya yi arba da mugayen abubuwan da ke fitowa daga cikin rijiyoyin, sai hankalinsa ya dugnzunma ainun, domin ya san cewa irinsa ari ma ba za su iya hallaka abubuwan ba. Zan ci gaba. Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part D Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey 50 TASKARNOVELS.COM.NG Mugayen dabbobin daji ne suka rinka fitar burgu daga cikin rijiyoyin, mASu yawan tsiya ba iyaka. Daga manyan zakuna, irin wanda ido bai taba gani ba, sai manyan Kuraye da Damisoshi, kuma fitowa suke tayi daga cikin rijiyar kamar ba za su kare ba. Rijiyar da takobin Saiful Lujaran ta fito ne kadai wani abin bai sake fitowa daga cikinta ba. Tun a saman Hantaru ya kara rike takobin Saifal Lujara da hannayensa biyu gam-gam. Ai kuwa yana dira a cikin kogon azababben yaki ya kacame tsakaninsa da miyagun dabbobin, suka yanyameshi suna kai masa cizo da yakushi, shi kuwa ya dinga ragargazarsu da takobin Saiful Lujara, sai dai ka ga a lokaci guda ya dara dabbobi uku ko hudu ya tsargesu gida biyu sun zube kasa matattu. In banda cewar Hantaru mutum ne mai matukar zafin nama yana kaiwa dabbobin sara ta ko ina, wato gabas da yamma, kuda da arewa, sama da kasa, da tuni sun tumurmusheshi. Duk da zafin naman nasa SAi da suka rinka kartar jikinsa suna cizonsa amma saboda karfin sihiri kaifin faratansu dana hakoran nasu baya tasiri a 51 TASKARNOVELS.COM.NG jikinsa, amma kuma sun kumbura masa jiki sun taru masa jim. Babban abin da ya fi tayar Masa da hankali shi ne, rashin karewar dabbobin, domin yana kashe su ne wasu na kara fitowa daga cikin rijiyoyin tamkara sannan ake haihuwarsu. Kuma abin da ya lura da shi shi ne, babu kokarin da dabbobin ke yi face su kwace takobin Saifal Lujara daga hannunsa. Hantaru ya yi nazari ya fahimci cewa idan da aka Sami koda rabin sa'a ne a na wannan gumurza lallai zai gaji har wadannan dabbobi su kaishi kas su turmusheshi, idon kuwa suka turmusheshi Lallai za ta kai cewa sun rabashi da takobin Saiful Lujara, Sannan su hallakashi. Koda Hantaru ya fahimci haka sai ya fara tunanin mafita. Abin da ya fara fado masa a rai shi ne, masu iya magana sun ce "Gudu ba tsoro bane idan masifa 52 TASKARNOVELS.COM.NG ta kai masifa " Koda gama aiyna hakan, sai Hantaru ya shammaci dabbobin nan ya daka wawan tsalle Sama ya yi fitar burgu daga cikin kogon, tun da dai saman kogon ya yaye sakamakon rugujewar da yayi. Ai kuwa suma dabbobin sai suka daka tsalle sama gaba dayansu suka bishi a sama. Hantaru na dira a wajen kogon bisa turba sai ya fara falfala matsanaicin gudu. Nan fa aka kasa tsere tsakaninsa da dabbobin. Gudun da Hantaru ke yi ya wuce gaban misali, domin gudu ne na sihiri, Sai dai ka ga yana gifta bishiyoyin dajin giftawar tauraruwa mai wutsiya. Abun takaici da ya waigo sai ya ga wadannan dabbobi na daf da shi kamar marabarsu bai wuce kamu daya ba. Inda zai tsaya da taku daya zasu iya tsalle su cimmesa, Abin da Hantaru bai sani ba shine gudun da dabbobin suke yi shima na sihirine. Sirrin shine duk halittar da ke cikin kogon da takobin Saiful Lujara take an sihirceta, yadda ba zasu taba bari kowa ya mallaki takobin ba sai sun tsare takobin don kar tabar hannunsu. 53 TASKARNOVELS.COM.NG Inda ace Hantaru ya yar da takobin dabbobin ba zasu biyoshi ba. Haka dai Hantaru ya cigaba da matsanaicin gudu, dabbobin na biye da shi daf da daf suna gurnani da kartar kasa kamar sa ci babu. shi kansa Hantaru duk da cewar yana da dakakiyar zuciya a duk sa'adda ya waigo yayi arba da dabbobin sai yaji zuciyarsa ta karaya domin ya san cewa akwai iyakar lokacin da zai iye jure wannan gudu, don haka idan ya gaji dabbobin za su bankeshi sai abin da hali ya yi. Komai jarumtakar mutum da juriyarsa idan ya ga yadda wadannan dabbobi suka tuso Hantaru a gaba dole ne zuciyarsa ta karaya domin ya san cewa idan ma zai tsaya ya ci gaba da yakarsu ba zai iya karar da su ba a cikin kwana bakwai saboda yawansu. Sai da Hantaru ya shafe sa'a bakwai yana gudu a cikin daji, wadannan mugayen dabbobin na biye da shi babu daga kafa. Sa'a bakwai na cika ne suka iso cikin wani irin daji mai yawan surkukiya da duhuwoyi gami da kayoyi masu tsini. Bisa mamaki sai Hantaru yaji 54 TASKARNOVELS.COM.NG kayoyin na huda jikinsa har jini na tsartuwa. Alamarin da ya janyo ya fara layi da tangadi ke nan. Amma saboda naci da juriya bai fasa gudun ba su kuwa dabbobin da?a matsawa suke ta cikin kayoyin tamkar suna hawa kan kalmami jikinsu ko kwarzAnewa baya yi. Sannu a hankali Hantaru ya fara gani dishi- dishi sakamakon jinin da ke zuba a jikinsa mai yawa ya zamana cewa yana gudu ne kawai amma baya ganin abin da ke gabansa. Kwatsam! Sai yai karo da ka da wata katuwar bishiya tamkar fyadashi aka yi a jikinta. Nan take jini yai fitar burgu daga cikin bakinsa de hancinsa ya fado da baya a sume ya baje a kas. Takobin Saiful Lujara ta subuce daga hannunsa ta fadi gefe daya. A dai-dai wannan lokaci ne wadannan miyagun dabbobin suka iso kansa suka yi masa kawanya suna shirin yuyyagashi. Daya daga cikin dabbobin wani murgujejen tsohon Zaki sai ya yi girgiza ya rikide ya zama wani tsohon aljani wanda shekarunsa sun haura dubu ashirin. Kawai sai ya nufi inda takobin Saiful Lujara take 55 TASKARNOVELS.COM.NG da nufin ya dauka. Kwatsam! Ba zato ba tsammani, sai ga wata irin guguwa mai karfin tsiya ta baiyana ta tarwatsa gaba dayan wadannan dabbobi tayi jifa da su can nesa har shi kansa wannan tsohon aljani mai shirin ?aukar takobin Saiful Lujara. Kafin dabbobin sU Sake rugowa da gudu inda Hantaru yake kwan ce a sume, tuni guguwar ta ?auke Hantaru da takobin Saiful Lujara tayi sama da su ta luluka a cikin gajimare ta 6ace bat tamkar basu taba wanzuwa ba a saman. Kawai sai wanann aljani da dabbobin suka tsaitsaya cak suka daga kawunansu sama suna kallon daidai wajen da guguwar ya kule da Hantaru. Daga can kuma sai suma suka 6ace 6at. Lokacin da Hantaru ya farfado daga dogon suman da ya yi, sai ya tsinci kansa a cikin wani kasaitaccen ?aki kwance akan wani luntsumemen gado mai taushin gaake. 56 TASKARNOVELS.COM.NG Komai na cikin dakin an yi shi ne da zinare, don haka gaba dayan dakin sheki da walwali yake. Abu na farko da Hantaru ya fara arba da shi shi ne, takobin Saiful Lajara jingine a jilkin bango bisa wani ma'ajiyi. Koda ganin takobin sai Hantaru ya saki murmushin murna ya mike zaune sanann ya zuro kafafunsa kasa daga kan gadon ya nufi inda take yana tafiya da kyar a lokacin da yaji gaba dayan jikinsa ya yi tsami. Saura kiris! Hannnunsa ya kai kan takobin sai ya dubi wani madubi da ke kusa da takobin. Nan take ya ga ashe gaba dayan fuskarsa a kumbure take ba kyan gani, kuma tayi kaca-kaca da rauni sakamakon muguwar buguwar da ya yi da bishiya, musamman idanunsa sun yi luhu-huhu da kyarma yake iya budesu. Koda Hantaru ya ga yadda fuskarsa ta baci, sai takaici ya kamashi, amma da ya tuno gimbiya Larziya sai farin ciki ya cika zuciyarsa bisa ganin cewa ya sami nasarar dauko takobin Saiful Lujars, da zarar ya koma birnin Darul Habur sai dai a... 57 TASKARNOVELS.COM.NG Koda Hantaru ya ga yadda fuskarsa ta baci, sai takaici ya kamashi, amma da ya tuno gimbiya Larziya sai farin ciki ya cika zuciyarsa bisa ganin cewa ya sami nasarar dauko takobin Saiful Lujars, da zarar ya koma birnin Darul Habur sai dai a daura aurensa da gimbiya Larziya. Cikin hanzari Hantaru ya dauki takobin Saiful Lujara ya nufi kofar fita daga dakin, kawai Sai ya ga wata tsaleleliyar budurwa ta baiyana a gabansa fuskarta cike da murmushi. Cikin tsananin mamaki da firgici Hantaru yaja da baya yana kallonta ya ce, "Mutum ko aljan?". Ba komai ne yasa Hantaru ya yi ma ta WannAn tambaya ba face ganin tsananin kyawunta wanda ya ninka na gimbiya Lariya sau uku. 58 TASKARNOVELS.COM.NG Budurwar tayi murmushi wanda ya kara baiyana kyawunta karara har Hantaru ya kara dimancewa sannan kuma sai ta murtuke fuska ta dubeshi ta ce, "Haba gwarzon shekara wane irin sauri kake yi haka? Shin baka ga yadda fuskarka take bane har kake tunanin komawa birnin Darul Habur cikin wannan sifa? Yaya masoyiyarka gimbiya Larziya za ta kasance idan ta ganka a cikin wannan siffa? Bai zamo dole ba ma ta shaidaka ba, kamanninka gaba daya sun sauya. Ka sani cewa jikinka a cike yake da raunika da kuma taruwar jini, idan ka ce za ka cigaba da tafiya a haka wa?annan mugayen dabbobin na kogon da takobin Saifal Lujara take za su sake binka su rabaka da takobin, kuma su hallaka ka, kaga kenan kayi biyu babu, babu ranka, kuma babu takobin, duk wahalar da ka sha a baya ta zama ta banza.' Burin dangin mahaifiyarka na cin gasa bai cika ba, kaima burinka na auren gimbiya Larziya ya rushe, bare kuma har ka koma birnin Kisra ka sadu da mahaifnka sarki Kusaidu 59 TASKARNOVELS.COM.NG wanda kullum dare da rana a cikin begenka yake." Sa'adda kyakkyawar budurwar tazo dai-dai nan a jawabinta sai Hantaru ya cika da tsananin mamaki ya kura mata idanu kawai yana mai kara kankame takobin Saiful Lujara a kirjinsa. Sannan ya ce,ya ce, *Ya ke wannan kyakkyawa, wace ce ke, kuma me yasa kika ceto rayuwata daga hannun wadannan dabbobi na kogon da wannan takobi take ciki kika kawoni nan?". Koda jin wadannan tambayoyi sai buduwar tayi ajiyar zuciya sannan ta ce, "A gaskiya ba zan iya gaya maka amsar wadannan tambayoyi ba a yanzu, sai bayan ka sami lafiyar jikinka gaba daya, wato ranar da zamu yi bankwana ka tafi 60 TASKARNOVELS.COM.NG izuwa birmin Darul Mahabul. Wata kila daga Wannan rana ba zamu sake saduwa ba, wata kila kuma daga wannan rana ba zamu sake rabuwa ba". Hantaru yai shiru a karo na biyu yana nazarin abin da ta fadi. Amma bai fahimci komai ba, kawai sai ya dago kansa ya sake dubanta ya ce, "Tsawon kwana nawa ne zan yi na gamna jinyar jikin nawa na tafi?", Budurwar ta ce, "A kalla kwana goma sha hudu. A sannan ne fuskarka za ta yi fes ka koma ga masoyiyarka cikin kyakkyawar siffa, Koda jin haka sai Hantaru ya yi murmushi. Amma da ya dubi budurwar sai ya ce a ransa. "Ina ma ace gimbiyu Larziya ce da kyau irin na Wannan budurwa, da na gama morewa a duniya, domin na tabbatar da cewa a duniya kaf ba za a sami kamarta ba. Ashe har akwai wadda tafi Larziya kyau a cikin wannan duniya?". Hantaru ya tambayi kar sa a cikin zuciyarsa. Kamar budurwa ta San irin Zancen Zucin da yake yi sai ya ga tayi masa murmushi sannan ta tako kafafunta a hankali cikin tafiyar kasaita tamkar dawisu tazo daf da shi ta kamna hannayensa ta jashi izuwa kan gadonta ta zaunar da shi ta ce, "Ya kamata yanzu ka ci 61 TASKARNOVELS.COM.NG kasha sannan ka sha magani ka kwanta ka huta". Kafin Hantaru ya ce wani abu sai ya ga wadansu kyawawan kuyangi guda biyu Sun baiyana tsulum a gabansa. Daya na dauke da katon faranti cike da abinci iri-iri dayar kuwa kayan shaye-shaye ne kala-kala har da na magani. Har a Wannan lokaci budurwar na rike da hannayen Hantaru, wani irin laushi da yaji a hannayenta ne yaji ko kadan baya son ta saki hannayensa, domin bai san sa'adda ma ya fara lumshe idanu ba amma da zarar ya dubi fuskarta sai ya ga tana rikida tana zama gimbiya Larziya. Kaico! Hakika soyayya dafice wadda idan ta ratsa sassan jikin mutum, fitarta sai yaki. Duk tsananin kyawu irin na wannan budurwa wanda ya ninka na gimbiya Larziya sau uku bai sa Hantaru ya fi sonta ba akan Larziya saboda tuni zuciyarsa ta gama cika da begen Larziya babu sauran gurbi wanda wata za ta samu! Ba tare da bata wani lokaci ba kuyangin suka ajiye farantan biyu bisa kan wani tebur da ke gabansu Hantaru sannan suka bace 6at! Bacewarsu ke da wuya sai budurwar ta fara ciyar da Hantaru da hannunta kuma tana ciyar 62 TASKARNOVELS.COM.NG da kanta. A haka sai da suka koshi sannan ta baiwa Hantaru ruwan magani kala shida ya sha. Yana gama shan maganin sai ya dubeta ya budi baki domin ya tambayeta sunanta amma sai yaji bakin nasa ya yi masa nauyi ya kasa magana, idanunsa kuwa sai suka kama lumshewa kawai sai ya tuntsure akan gadon ya kama barci. Koda ganin haka sai budurwar ta kura masa idanu tana murmushi, daga Can kuna sai idanunta suka ciko da kwalla ta fara zubar a hawaye. Jim kadan kuma sai ta fashe da matsanaicin kuka sai da ta shafe sa'a guda tana ta kukan tamkar wacce ta rasa ivayenta a lokaci guda sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin tana waigen Hantaru kamar har abada ba Za ta sake ganinsa ba. Daga Wannan rana kullum Wannan kyakkyawar budurwa na tare da Hantaru dare da rana tana jinyarsa kuma tare suke cin abinci safya, rana da dare, sannan su yi ta hira basa rabuwa face ta ga Hantaru ya soma jin barci sannan tayi masa sallama ya tafi turakarta. Tsawon kwanaki goma sha hudu, Hantaru bai taba fita ba daga cikin dakin da ake jinyarsa face ya 63 TASKARNOVELS.COM.NG shiga Wani kewaye idan bukata ta kamashi. Hatta wanka Hantaru ba ya yi da kansa budurwar ce take yi masa don haka ne suka shaku ainun suka saba da juna amma babu wani abu da ya taba shiga tsakaninsa. Wani abin mamaki shi ne a tsawon kwanaki goma sha hudu basu taba yin hirar soyayya ba kuma Hantaru bai taba jin sunan budurwar ba a duk sa'adda yaso ya tambayeta sunanta sai ta bagarar da zancen ta sauya hirar da suke. A iya rayuwar Hantaru in ka ? auke Salimat wadda ta raineshi a matsayin mahaifiyarsa bai taba samun kusanci ga ya mace ba gami da sabo face wannan budurwa. A ranar da kwanaki goma sha hudu suka cikane, Hantaru ya tashi da sassafe daga barci koda ya dubi kansa a cikin madubi sai ya ga fuskarsa da jikinsa sun yi kyau matuka kuma sannan ya yi haske da kiba har wani irin sheki fatar jikinsa ke yi. Nan take yaji wani irin farin ciki ya baibayeshi musamman da ya tuna cewa yau ne zai bar Wannan gida domin ya tafi izuwa birnin Darul Mahsbul. Hantaru na tsaye a gaban madubi yana kallon kansa sai kawai ya ga wannan budurwa tsulum 64 TASKARNOVELS.COM.NG a gabansa, idanunta sun kada sun yi jawur kai da gani ka san cewa ta dade tana kuka, Al'amarin da ya matukar ?ugunzuma hankalin Hantaru ke nan yaji kamar ya fasa tariya a yau, kawai sai ya budi baki da nufin ya tambayeta dalilin da ya sa ya ga idanunta sun yi jawur, kawai sai budurwar ta juya masa baya ta dauko takobin Saifal Lujara ta mika masa ya karba sannan ta kama hannunsa ta jashi suka fita daga cikin dakin. Nan fa suka kama yawo a cikin harabar gidan, su shiga nan su fita can. Nan fa Hantaru ya cika da matukar al'ajabi ya zama cikakken dan kauye, saboda ganin irin daular da aka shirya gidan ko a tarihi bai taba jin labarin gidan sarautar da ya kawatu ba kamar wannan. Duk wani abu na jin dadin duniya an tanadeshi a cikin gidan har da ma wanda ido bai ta6a hasashen gabaninsa ba. Sai da guka shafe sa'a ukU suna shiga sako sako, lungu-lungu na gidan amma Hantaru bai ga alamar Sun kusan kure gidan ba. A?amarin da ysa yaji ya kagu ke nan, domin hankalinsa na kan tafiya birnin Darul Habul. Koda budurwar ta fahimci halin da Hantaru ke ciki sai ta ruko hannunsa suka tsaya 65 TASKARNOVELS.COM.NG cak kuma suka fuskanci juna, kawai sai ya ga hawaye ya zabo daga cikin idanunta. Alamarin da ya matukar baahi mamaki ke nan ya dubeta cikin kaduwa ya ce, "Ya ke Wannan ma'abociyar karamci da kyawu ina dalilin zubar wannan hawaye nak?i?" Koda jin wannan tambaya sai ta yi murmushi mai taushi a gareshi ta ce, "Ya kai jarumin jarUmai, gwarzon zamani, kuma traron wannan shekara, kayi sani cewa sunana Hayatul Lumhas. Na kasance 'ya guda daya jal ga sarki Thibur na birnin Hindu. A halin yanzu masAna bincike sun tabbatar da cewa duk duniya babu wata mace mai kyau kamata, amma tun ina jaririya mahaifina ya boyeni a cikin dakin tsafinsa ban taba fita ko Ina ba har na girma na cika shekara goma sha takwas, shi yasa a duniya ba a sanni ba. Kaine Damijin fark? da na taba gani a rayuwata ban da mahaifina, hatta mahaifiyata ban taba ganinta ba, ban San ta ba umn ban sha nononta ba har aka kawoni wannan gida kimanin shekaru hudu da suka gabata sa'adda nake da shekaru goma sha hudua duniya. Lokacin da mahaifina ya kawoni wannan gida ya ajiye ni a sannan ne na 66 TASKARNOVELS.COM.NG ga ya dubeni ya fashe da kuka. Al'amarin da ya dugunzuma hankalina kenan na ruke kafadarsa cikin matukar damuwa na ce, "Ya kai Abbana ina dalilin kukanka, kuma me yasa ka kawoni cikin wannan gida wanda ke tsal kiyar dokar daji?. Sa'adda mahaifina yaji wannan tambaya sai ya share hawayensa sannan ya ce, "Ya ke yata ki yi sani cewa ba komai ne ya sani wannan kuka ba face sanin cewa yau ne ranar da zan rabu da ke rabuwa ta har abada, domin yau saura kwana bakwai kacal na bar duniya. Abin da ya sa na kawoki nan na ajiyeki kuwa shi ne, anan ne kadai ZA ki iya zama lafiya har izuwa karshen rayuwari, idan na barki a can kasarmu kika gaji karagata ta mulki duniya ba za ta zauna lafiya ba domin gaba dayan sarakunan duniya za su tayar da hankalinsu a kan sai sun mallakeki saboda tsananin kyawunki, al'amarin da zai janyo yakin duniya ke nan ayi asarar rayuka da dukiya wacce bata da adadi. Bisa wannan daili ne yasa na rabaki da mahaifiyarki tun daga ranar da aka haifeki kuma na Boyeki da karfin sihiri yadda babu wani mahaluki walau mutum ko aljan da zai iya 67 TASKARNOVELS.COM.NG ganinki bare bar ya kai labarinki wani wajen. Baki san kowa ba, kuma ba ki shaku da kowa ba face ni, yau gashi lokacin rabuwarmu ya yi, don me ba zan zubar da hawaye ba? Na yi bincike a cikin taskar tsafii na gAno Cewa nan da shekaru hudu za'a sami wani gawurtaccen jarumi wanda zi shiga kogan mazzabatal Dulshul wanda ya gagareni shiga ya dauko wata takobi da ake kira Saiful Lajara WaR'nnan jarumi zai sha bakar wahala a cikin kogon tamkar zai rasa rayuwarsa da kyar zai iya guduwa daga cikin kogon. Aljanun da ke gadin takobin Saifal Lujara za su biyoshi domin su halaka shi, a sannan ne nake son ki je ki ceci rayuwarsa ki kawoshi nan gidan tare da takobinsa ta Saiful Lajara. Na sani cewa wannan jarumi idan ya ganki dole ne yaji yana sonki, fatana shi ne ki zamo abokiyar rayuwarsa domin shi kadai ne zai iya aurenki ya iya zama da ke lafiya". (Sai kuma ni mai typing Shuraih 99%)? Sa'adda mahaifina yazo nan a zancensa sai na dubeshi cikin mamaki na ce, "Haba Abbana ta ya ya zan iya zuwa na ceto rayuwar wanan jarumin alhalin ban kasance jaruma ba kuma 68 TASKARNOVELS.COM.NG bani da wani sihirin tsafi?". Koda jin haka sai mahaifina ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Ya ke 'yata kiyi sani cewa yanzu tate zan baki dukkan sihirin tsafina sannan mu yi bankwana na koma kasata na jira mutuwata". Koda naji haka sai na fashe da kuka na rungume mahaifina sannan na ce, "Ya kai Abbana me yasa baka nuna mini mahaifiyata ba koda sau daya ne mun ga juna kafin ka kawoni nan tunda gashi yanzu kaima za ka rabu da ni rabuwar da ba zamu sake saduwa ba". Koda jin wannan tambaya sai mahaifina ya kamu da tsananin tausayina har ya kasa cewa komai ya fashe da matsanaicin kuka har izuwa lokaci mai dan tsawo. Daga can sai ya janye jikinsa daga cikin nawa muka fuskanci juna ya ce, "Ya ke yata kiyi sani cewa ka'idar sihirin tsafina ce ta hanani na hadaki da mahaifiyarki idan kuwa na karya wannan kaida shikenan sihirin tsafina Zai rushe, duk dukiyar da na mallaka za ta salwanta. Da wannan furuci nake yi miki sallamar karshe." Koda gama fadin haka sai mahaifina ya dada kankameni a kirjinsa ya sake fashewa da matsanaicin kuka. Al'amarin da ya karya zuciyata ke nan nima na kama kuka, Ina 69 TASKARNOVELS.COM.NG cikin wannan hal? ne naji wani irin gagarumin karfi yana shiga jikina. Kafin na gama shiga sai mahafina ya bace 6atl Na nemashi sama da kasa na rasa. Nan fa na rushe da kuma na kama gujeguje da iface- iface a cikin Wnnan gida. Kawai sai Da... MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part E Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Nan fa na rushe da kuka na kama guje-guje da iface- iface a cikin wannan gida. Kawai sai naga kuyangin gidan sun baiyana a gabana sun kewayeni suna rarrashina, sannan suka yi sujjada a gareni suna cewa, "Ya shugabarmu ki ?auki hakuri da kaddara, ki sani cewa mu masu debe miki kewane da biyan duk bukatunki daga nan har izuwa karshen rayuwarki". Koda naji haka sai na dubesu cikin mamaki na ce, "ldan kuma mutuwa ta daukeki waye zai ci gaba da kula da ni?". Cikn hadin baki suka ce "Ai mu ba mutane bane kamar ke, mun kasance aljanu, muna dadewa a duniya fiye da ku bil'adama. Daga Wannan rana ne na shiga sabuwar rayuwa a cikin wannan gida kuma ya 70 TASKARNOVELS.COM.NG zamana cewa ina yin abubuwan al'ajabi cikin karfin sihirin tsafi wadanda ni kaina nake mamaki. Haka na ci gaba da rayuwa cikin, koshin lafiya da kwanciyar hankali amma duk sa'adda na tuna da mahaifina sai na fashe da kuka, haka kuma idan na tuna cewa ban taba ganin mahaifiyata ba sai naji wani irin bakin ciki yai katutu a cikin zuciyata. Haka dai na kasance a cikin wannan matsayi har tsawon shekara hudu. A ranar da na ga hoton duk abubuwan da suka faru gareka a cikin kogon Mazubatul Dulshal ne naji na kamu da tsananin kaunarka don haka sa'adda wadannan aljanu suka biyoka za su hallaka ka sai na bi umarnin mahaifina na zamo guguwa naje na daukeka kafin su illataka na kawoka nan, nayi jinyarka kawo izuwa yanzu tsawon kwana goma sha hudu har ka sami lafiya. Wannan shi ne takaitaccen tarihin rayuwata ya kai jarumin jarumai, kayi sani cewa na gani a cikin bincikena na tsafi cewar idan har ka koma wajen gimbiya Larziya za ta umarceka da ka aikata wani mummunan aiki wanda zai zamo sanadiyyar batawarka da Salimat matar da ta rene ka har ka girma a 71 TASKARNOVELS.COM.NG matsayin danta na cikinta sakamakon hakan Salimat za ta kashe kanta. ldan hakan ta faru za ka tsani kanka kuma za ka tsani komai a duniya ya zamana cewa soyayyarka da gimbiya Larziya ta rushe, wato dai ba za ku yi ure ba. Ina mai shawartarka da ka mance da batun Larziya ka zauna anan tare dani mu yi aure mu more rayuwarmu cakin dadi da kwanciyar hankali. Ka sani cewa na fi Larziya kyawu, asali da matsayi a duniya, kuma duk abin da kake nema a rayuwarka walau dukiya ko daukaka in dai kana tare da ni tamkar ka samesSu ne. Sa'adda Hayatul Lumhas tazo nan a zancenta sai Hantaru ya yi murmushi gami da ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ya ke ma'abociyar kyawu, matsayi da daukaka, kiyi sani cewa babu ruwan S0 da kyawu ko matsayi, don haka martabar gimbiya Larziya a cikin zuciyata ta ninka taki sau dubu. Larziya ce mace ta farko da ta fara samun gurbia cikin zuciyata kuma ita ce za ta zamo ta karshe domin ba zan taba son wata ba face itan. Duk bayanin da ki ka yi na gamsu da shi, amma ban yi imani da shi ba domin na yarda da cewa zan iya sauya kowacce irin kaddara da ta sameni 72 TASKARNOVELS.COM.NG anan gaba muddin tsafi bai daina tasiri a doron kasa ba. Ki sani cewa idan suna nake nema a duniya na gama samunsa tun da gashi na dauko takobin Saiful Lujara a cikin kogon Mazabatul Dulshal aikin da ya gagari dubunnan sadaukai a tsawon dubunnan shekaru da suka gabata. Idan dukiya nake so ko mulki duk zan iya samunsu da karfin Wannan takobi da na dauko saboda haka ni yanzu baki da wani abu wanda zai janyo hankalina har yasa har na manta da masoyiyata abar begena dare da rana wato gimbiya Larziya. Abin da nake bukata daga gareki kawai shi ne ki fitar dani daga cikin wannan gida naki ki ?orani akan hanyar da ZAn nufi birnin Darul Mahabul domin naje na ida sauran burin rayuwata. "Ya yin da Hantaru yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa gimbiya Hayatul Lumhas tayi shiru bata ce komai ba tana mai sunkui da kanta kas saboda tsananin bakin ciki da takaici. Daga can sai ta dago kai ta dubi Hantaru ta ce, "Ya kai abin

Chapter 3 of 14