Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sharadi don ceton rayuwar sarki? Baka tsoron cewa idan dabararmu ta yi nasara sarki ya kubuta fishinsa zai iya tabbata akanka?". Koda jin wannan batu sai Shurkaib ya bushe da dariya, sannan ya ce, "Ku a tunaninku ni ina tsoron mutuwa ne? Ku tuna cewa shekaruna sun haura casa'in a duniya, na haifi ya'ya, ya'yanma sun haihu, nayi yakeyake da dama ba adadi. Babu irin masifar da ban gani ba a duniya, kuma babu wani buri da ban cika ba face guda daya, kuma yanzu ne na samu damar da zan cika wannan buri nawa bisa wannan uzuri da ke gabanmu. Inaa tabbatar muku da cewa duk dabarar da za ku kawo domin a kubutar da rayuwar sarki ba za a yi nasara ba. Tawa dabarar ce kadai za a bi a samu nasara. Yanzu na baku dama ku fara gabatar da taku dabarar idan ba a dace ba sai na fadi tawa, idan har sarki ya amince da sharadina". Sa'adda Karbuza da Barsuma suka ji wannan batu, sai suka fara cika da mamakin Shurkaib suka tabbatar da cewa da gaske yake. Karbuza ya ce, "Shi ke nan ai yanzu sai ka zo mu je wajen sarki domin mu gaggauta yin abin da ya kamata mu 24 TASKARNOVELS.COM.NG yi domin bata lokacinmuu cikin wannan daji tamkar baiwa abokan gaba dama ne su rigamu zuwa inda takobin Saiful Lujara take." Koda jin haka sai Basuma da Shurkaib suka ce a cikin hadin baki, "Zancenka dutse ne". Nan take su ukun suka dawo inda sarki Dujalu ke kwance a karkashin gawar wannan halitta. Duk su ukun suka durkusa a gabansa. A wannan lokaci Hursiya ta tallafo kan sarki Dujalu ta dura masa ruwa a baki. ya sha. Gama shan ruwan nasa ke da wuya ya yi arba da su Karbuza tsugunne a gabansa sai ya fusata ya ce, "Me kuke jirane har yanzu baku yi tunanin dabarar da za ku yi ba ta ceto rayuwata?" Kurbazu ya numfasa ya ce, "Ya shugabana ai abin da muka je muka tattauna ke nan, kuma kowannenmu yana da tasa dabarar dabam. Zamu fara jarraba tawa dabarar, in yaso a jarraba ta Barmusa, idan tawa ba tai nasara ba, idan shima tasa bata yi ba sai a jarraba dabarar Shurkaib. " Sarki Dujalu ya ce, "Na umarceku da ku aikata hakan cikin gaggawa domin idan muka kara kwana hudu anan cikin wannan daji rundunar Su sarki Maharaz za ta zo ta riskemu. Ni kuwa a 25 TASKARNOVELS.COM.NG shirina shi ne mu rigasu zuwa tekun bahar Sufiya ya zamana cewa kafin su isa tuni mun danko takobin Saiful Lujara." Karbuza ya dubi dukkanin dakarun aljanun da ke wajen ya ce, "Na umarceku da ku ruga izuwa cikin wannan daji ku tsunko murtuka murtukan jijiyoyin bishiyoyi dogaye ku zo da su yanzu. Kafin Karbuza ya gama rufe bakinsa tuni gabe dayan dakarun aljanun sun bace bat! Kafin cikar dakika sittin sai gasu sun dawo dauke da dogayen jijiyoyin murtuka-murtukan bishiyoyi masu yawan gaske tamkar za su yiwa dajin gaba daya rufi da su. Ba tare da bata lokaci ba Karbuza ya umarcesu da su kukkulla jijiyoyin wasu jikin wasu. Nan da nan aka samar da dogayen igiyoyi na jjiya barkatai. Karbuza ya saké bada umarnin a daura jijiyoyin a jikin gawar katuwar halittar. Kowacce doguwar jijiya daya aka sa kartin aljanu majiya karfi guda dubu suka riketa. A kalla an sami sama da aljanu miliyan daya. nan take aka basu umarni da su ja igiyar sama a lokaci guda, domin su daga gawar sama daga kan sarki Dujalu domin sami damar zareshi. Aljanun gaba dayansu suka tattaro karfin daratsensu suna jan 26 TASKARNOVELS.COM.NG jijiyoyin a lokaci guda. Maimakon gawar halittar ta rabu da kasa, sai gaba dayan jijiyoyinPartFaka daura a jikinta suka tsittsinke, aljanun suka fado kasa gaba dayansu Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki ke nan a wajen, kuma hankalisu ya dugunzuma. Sarki Dujalu ya juyo da wuyansa da kyar ya dubi Barsuma cikin alamun karayar zuciya ya ce, "Ya kai Barsuma babban gwarzo, NAMIJIN DUNIYA, mai dakawa maza gumba a hannu, ka ga yadda dabarar Karbuza ta kare, kai kuma wacce dabara ke gareka?" Barsuma yai gyaran murya sannan ya ce, Ina son aje a nemo mini giwaye adadin ninkin wannan aljanu sau dari. Ma'ana kowanne aljani guda giwa dari ce za ta wakilceshi, sanann a nemo mini dogayen sarkoki murtuka-murtuka na karfe a daura a jikin gawar wannan halitta sannan a daura a jikin giwayen domin su ja sarkar su janye gawar". Koda jin hake sai dakarun miliyan dubu daga cikin aljanun sulka 6ace bat a lokaci guda. Kafin kiftawar ido sai gasu sun dawo tare da wadannan giwaye da sarkokin karfe. Kamar yadda Barmusa ya bada umarni haka aka yi, 27 TASKARNOVELS.COM.NG amma koda giwayen suka yunkura suka ja sarkokin karfen, sai sarkokin suka tsittsinike saboda tsananin nauyin katuwar halittar sai gani aka y giwayen na faduwa wasu na danne wasu. Nan fa hankali ya kara dugunzuma fiye da ko a yaushe, zuciyar sarki Dujalu ta kara karaya ya fitar da rai ga cikar burin rayuwarsa ya fara tunanin cewa tabbas ajalinsa ya gabato. Duk da sanin hakan sai ya yi ta maza ya dubi Shurkaib ya ce, "Ya kai tsoho mai dabara, ya kai tudu mai nisan da yaro ba zai hango ba. Ya kai masanin jiya, kuma masanin gobe, ka ga yadda dabarun yan uwanka suka kasan ce. Ka sani cewa karfin tsafina da karfin damtsena ba za su ceceni ba daga cikin wannan hali da na shiga ba, wacce dabara ce da kai wadda in dai aka yi ta zan tsira da rayuwata? Na yi maka alkawari idan har ka ceci rayuwata duk abin da kake bukata zan baka shi in dai akwai shi anan duniya domin rayuwata ta fishi daraja a idanuna". Sa'adda tsoho Shurkaib yaji wannan batu na sarki Dujalu sai ya cika da tsananin farin ciki bai san sa'adda ya saki murmushi ba sannan ya dubi Dujalu cikin 28 TASKARNOVELS.COM.NG nutsuwa ya ce, "Ya shugabana idan na fadi dabarata ba a cimma nasara ba na yarda kasa a kasheni a take a wannan wuri. To amma ka sani cewa ba zan fadi dabarata ba face ka dada jaddada alkawarin da ka furta yanzu kuma ka rubutashi a rubuce tare da sa a buga hatiminka". Koda jin haka sai sarki Dujalu ya girgiza kai yana mai nuna alamar cewa ya aminta da hakan. Nan take ya sa aka kawo masa tauwada da alkalami gami da fatan rubutu. Har ya dangwalo tawada zai yi rubutun bisa fatar sai Hursiya ta yi sauri ta rike hannunsa a lokacin da hawaye ke zuba daga idanunta ta ce, "Haba ya dan uwana ina amfanin rayuwa idan buri bai cika ba? Yanzu idan Shurkaib ya ce abin da muka fito nema ya ke so fa". Koda jin haka sai kowa da ke wajen yai tsuru-tsuru har shi kansa sariki Dujalu kuwa. Shi kuwa tsoho Shurkaib sai ya yi murmushi ya ce "Ko kadan bani da muradin kayan yakin MAZAN JIYA" Da jin hake sai sarki Dujalu yai mumushi, nan take ya yi rubutun yarjejeniya cewa ya amince duk abin da Shurkaib ya furta yana so zi bashi bayan dabararsa ta cimma ga ci. Bayan ya gama rabutawar ne aka kawo 29 TASKARNOVELS.COM.NG hatimi ya buga, kuma ya mikawa Shurkaib bada shakkar komaiba. Shurkaib ya karbi fatar yarjejeniyar ya sanyata cikin aljihunsa sannan ya dubi gaba dayan aljanun da ke wajen ya ce,"A cikinku wane ne mafi sanin sirrin hakan kasa?", Koda jin haka sai wani tsamurmurin aljani ya daga hannu ya ce, "Yau shekarata dubu saba'in ina sh akin hakan kabari a garinmu" Shurkaib ya dubeshi yai murmushi ya ce, "Matso nan kusa da inda sarki yake. Ina son ka haka rami karami dai-dai fadin gangar jikin sarki a farkashinsa yadda zai fada cikin ramin ba tare da kasa ta zabtare ba gawar wannan katuwar halitta ta sake danne shi ba". Nan take kuwa wannan aljani ya bi wannan umarni ya kama aikinsa. Ko sa'a daya bata cika ba sai ya kammala aka ga sarki ya fado cikin ramin daga karkashin katuwar gawar halittar. Cikin matukar zafin nama akayi sauri ake zare sarki Dujalu daga cikin ramin. Ai kuwa ana gama zareshi ke nan sai kasar wajen ta rusa saboda nauyin gawar halittar, gawar ta lume a cikin ramin, dajin gaba daya ya kama girgiza saboda gawar halittar, ta ci gaba da nutsewa izuwa cikin karkashin kasa. Ba shiri kowa da 30 TASKARNOVELS.COM.NG kowa ya kama gudu. Sai da aka yi gudu na sa'a shida sannan aka isa inda kasa bata girgiza sannan aka tsaya ana haki. Daga inda aka tsaitsaya ana iya hango yadda komai na wancana dajin ya nutse izawa cikin farkashin asa ya zamans cewa ba sauran bishiyoyi da duwatsu wadanda ake iya hangowa. A wannan lokaci ne kowa hankalinsa ya dawo jikinsa. Bayan an nutsu sai sarki Dujalu ya tako da kafafunsa yazo gaban Shurkaib ya tsaya daf da shi yadda har suna iya jin numfashin junansu. Sarki Dujalu ya dubeshi cikin murmushi ya ce, "Yanzu sai ka fadi muradinka naji domin na cika alkawarina". Koda jin haka sai kowa ya yi tsit! Dajin gaba daya yai shiru tamkar mutuwa ta gifta, kamar suma sauran halittun da ke dajin sun yi shiru suna sauraron munafunci. Tsoho Shurkaib yai gyaran murya ya ce, "Ba wani abu nake so ka bani ba face auren yar uwarka gimbiya Hursiya, kuma ba nine mijinta ba, dana za ka aurawa". Koda sarki Dujalu yaji wamnan batu sai gaba dayan jiikinsa ya kama karikarwa saboda tsananin bakin ciki, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar za ta kone. Nan nan Dujalu yaji 31 TASKARNOVELS.COM.NG nadama tazo masa bisa alkawarin da ya dauka, saboda wasu babban siri da ya 6oye a cikin zuciyarsa wanda duk duniya babu wanda ya sanshi face shi kadai. Inda sarki Dujalu ya san cewa abinda Shurkaib zai bukata ke nan da ya zabi a barshi a cikin halin da yake ciki ya rasa rayuwarsa, burinsa ya rushe in yaso gimbiya Hursiya ta koma gida ta ci gaba da sarauta. Kawai sai aka ga idanun sarki Dujalu sun kada sun yi jawur tamkar an gasa danbuda a wuta. Cikin sanyin jiki ya sunkui da kansa kas ya ce,Lallai zan zamo mai cika alkawari a gareka bayan mun samo abin da muka fito nema" Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya tafi izuwa gaban wata korama ya zauna ya kurawa ruwan koramar idanu yana zubda hawaye. Ya yin da Hursiya ta ga hakan sai itama ta nufi inda yake. Koda sarki Dujalu ya waigo ya ga ita ce ke tahowa gareshi sai yai sauri ya goge hawayensa. Hursiya tazo ta zauna daf da shi sannan ta dubeshi cikin murmushi ta ce, ya kai dan uwana ina dalilin da yasa na ka ga shiga cikin halin damuwa bisa jin bukatar tsoho Shurkaib? Shin baka son na auri dansa ne 32 TASKARNOVELS.COM.NG saboda bai kasance jininmu ba?". Lokacin da sarki Dujalu yaji wannan tambaya sai ya dubeta ya maida mata da martanin murmushin cikin yake sanann ya ce, Ya ke 'yar uwata kiyi sani cewa bukatar Shurkaib tazo mini da shammace, ban taba tsammanin cewa kece muradinsa ba ga dansa. Ki tuna cewa a tarihin zuri'armu babu wani jininmu da ya taba auren bare, yanzu gashi Shurkaib zai karya mana wannan tarihi. Bugu da Kari, ina bakin ciki ace ranar da babu ni, mulkinmu da dukiyarmu da duk wannan daukaka da nake nema mana a yanzu Za ta koma wajen zuri'ar tsoho Shurkaib, domin idan kika auri dansa tamkar hakan ta tabbatu ne." Lokacin da Dujalu yazo nan a zancensa sai tausayinsa ya kama Hursiya ta rungumeshi ta fashe da kuka. Shi kuwa sai ya cika da tsananin farin ciki a cikin zuciyarsa. Hakika rashin sani yagi dare duhu. Inda Hursiyya ta san sirrin da sarki Dujalu ya boye ma ta da taji ta tsaneshi fiye da yadda ta tsani mutuwarta Haka dai Hursiya da sarki Dujalu suka ci gaba da hira a nan bakin koramar har izuwa lokaci mai dan tsawo. Da fatan an tashi lafiya, sannan duk 33 TASKARNOVELS.COM.NG wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part C Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Daga can sai Hursiya ta dago kai ta dubeshi ta ce, "Ya ki ?an uwana kayi sani cewa zuciyata ta kasa samun sukuni saboda rashin jin ci gaban labarin sadauki Hantaru. Lallai ina son naji yadda karshen rayuwarsa ta kasance". Sa'adda sarki Dujalu yaji wannan batu sai ya yi mrumushi sannan ya ce, "Ya ke yar uwata dama na san cewa kina cikin kaguwa bisa son jin ci gaban wannan labari, saboda haka Zan yi iyakar kofarina na kammala miki wannan labari kafin wayewar gari, domin so nake gobe da sassafe mu ci gaba da tafiya domin mu isa tekun bahar Sufiya akan lokaci, kafn su sarki Maharaz su zo su riskemu". Ya yin da Hursiya tajii wannan batu, sai ta cika da farin ciki ta nutsu tana mai kurawa sarki Dujalu idanu, shi kuwa sai ya yi gyarsn murya ya cigaba da ba ta labari kamar haka. Lokacin da hantaru ya zama katon dutse wannan jibgegegiyar Micijiyar ta hadiyesthi, sai 34 TASKARNOVELS.COM.NG macijiyar ta shiga cikin wani irin mugun hali domin dutsen ya zame ma ta masifa a cikin cikinta, yai ma ta nauyi, ya ZAmana cewa da kyar ta ke iya motsawa. Koda taji dutsen na damunta sai ta fara kokarin ta sake yin amansa waje da karfin taiya. Idan ta turo dutsen izuwa makogwaronta sai dutsen ya koma da baya, wato ya ki yarda ya ito. Nan fa Macijiyar ta kama tumuwa da kasa, tana dukan kowacce kusurwa ta kogon da kawunanta, al'amarin da ya sa gaba dayan kogon ya ragurguje ke nan ya kama girgiza. A duk sa'adda micijiyar ta tumu da kasa sai dutsen cikin cikin nata yaji kamar zai tarwatse don haka bisa dole dutsen ya taho da kansa izuwa makogwaronta. Koda jin hakan sai Macijiyar ta wangame bakinta wanda dutsen ke ciki, sannan ta sake wangame wani bakin dabam ta sokashi a cikin wancan domin ta zaro dutsen. Koda dutsen ya ga haka sai ya rikide ya zama wuta. Ai kuwa Macijiyar na hadiye dutsen wutar sai tayi bindiga ta tarwatse, sassan jiikinta ya yi flla-flla a kasa tamkar an yankashi gutsun- gutsun, sai ga dutsen wutar ya gangara Can gefe daya. Nan 35 TASKARNOVELS.COM.NG take dutsen ya rikida ya zama sadauki Hantaru kwance kasa, duk jikinsa yai kaca-kaca da raunika, jini na zuba yana numfashi da kyar kamar ransa zai fita. A Sannan ne nadama tazo masa, ya tabbatar da cewa abune mawuyaci ya sami nasarar daukar takobin daraja a cikin wannan kogo, musamman da ya dubi ragowar rijiyoyin da bai bude ba guda ?ari tara da casa 'in da tara. Babban abin tsoroa gareshi shi ne, rashin sanin rijiyar da takobin Saiful Lujara ke ciki, ko shakka babu kowacce rijiya ba Za a rasa mugun abu ba a ciki. ldan ya bude wadda ya gamu da abin da zai hallakashi a ciki shi ke nan burinsa ya yanke, kuma dak wahalar da ya sha a baya ta zAma a banza. Hantaru ya tuno da batun mahaifiyarsa Salimat wadda ba ita ce ta haifeshi ba amma kuma yana kaunarta fiye da kowaa rayuwarsa sai kuma gimbiya Larziya wadda a halin yanzu ya kamu da tsananin begenta har ya amince ya sallama rayuwarsa domin ya mallaketa. Hantaru ya tuno da batun cin amanar da mahaifiyarsa ta jini ta yiwa sarki Kusaidu ita da boka Ardusa. Lallai yana son ya koma birnin Kisra domin ya 36 TASKARNOVELS.COM.NG yiwa Farzira da boka Ardusa hukunci bisa wannan cin amana, kuma ya sadu da sarki Kusaidu wanda ke matukar kaunarsa a matsayin dan cikinsa. To amma ai Salimat ta gargadeshi akan kada ya taba lafiyar Zarifa. Abu na biyu da ya fadowa Hantaru a rai shi ne, batun alkawarin da ya ? aukarwa gimbiya Lazirina cewar duk wuya duk rintsi ba za su rabu ba, kuma duk bukatar da tazo masa da ita zai biya ma ta ita. Koda Hantaru yazo nan a tunaninsa sai zuciyarsa ta karaya, ya fara tunanin hanyar da zai bi ya yi jinyar jikinshi sannan ya ci gaba da bude ragowar rijiyoyin guda dari tara da casa'in da tara har ya sami wadda takobin Saifal Lujara ke ciki. Hantaru ya tambayi kansa a cikin ziciyarsa ya ce, "Yanzu ta ya ya zan reyu a cikin wannan kogon dutse babu ruwa babu abinci?" Koda aiyana hakan, sai idanunsa suka kai kan sassan jikin Macijiyar da ya kashe da kuma jinin jikinta da ya malala ya cika kasan kogon wanda za a iya yin wanka a cikinsa. Hantaru ta daga kansa sama ya yi arba da wasu tsirarun ciyayi da kananan bishiyoyi da tsirai da suka tofo a cikin dutsen, 37 TASKARNOVELS.COM.NG sai farin cilki ya kama shi, don ya fahimci cewa zai iya rayuwa a cikin kogon izuwa tsawon kwanaki kadan. Hantaru ta daga kansa sama ya yi arba da wasu tsirarun ciyayi da kananan bishiyoyi da tsirai da suka tofo a cikin dutsen, sai farin cilki ya kamna shi, don ya fahimci cewa zai iya rayuwa a cikin kogon izuwa tsawon kwanaki kadan. Hantaru ya fara da tunanin abinda ya kamata ya fara yi a yanzu tun da gashi har jiri ya fara dibarsa sakamakon jinin da ke zuba daga raunikan jikinsa Lallai ya zama dole ya yi tunanin abin da zai ya tsaida jinin. Cikin matukar karfin hali ya mike tsaye yana tangadi ya kama hawa kan duwatsun dake cikin kogon yana dogarawa ya isa inda ya hango wata bishiya mai faffadan ganye. Sai da ya rage saura baifi taku uku be ya isa inda bishiyar take sai ya zame ya fado kasa Haka dai ya daure ya sake tashi ya hau kan ?utse. A karo na biyu ma bai nasara ba sai ya fado. A karo na uku ne ya samu dama da kyar ya tsinko ganyen ya fado kasa a matukar galabaice. Da jen ciki yaje inda wata busasshiyar karamar bishiya take ya karyo kirare a jikinta, ya sake dawowa 38 TASKARNOVELS.COM.NG da baya ya dauki duwatsun wuta biyu ya dinga gogasu akan wadannan kirare har wuta ta kama A haka ne ya dinga narka ganyan wannan bishiya da ya karyo yana mannashi a jikin raunikan jikinsa. Duk sa'adda ya manna ganyen sai yaji kamar ya kurrma ihu saboda tsananin zafi da zogin da ke shigarsa. Har wani irin gumi da haweyen azaba ne ke zubo masa. Bayan ya gama sa maganin a jikin dukkanin raunikan jikinsa ne ya kwanta ya huta tsawon rabin saa a sannan ne jini ya daina zuba daga jikinsa ya dawo cikin haiyacinsa sosai. Nan take Hantaru ya mike zaune ya tsinto sassan jikin Macijiyar nan ya soka a jikin itace ya gasa, wato yai tsire. Haka ya ci gaba da gasa naman Macijiyar har ya gasa mai yawa ya zamana Cewa naman ya gasu sosai yadda zai kwana biyu bai lalace ba. Daga wannan rana Hantaru ya ci gaba da rayuwaa cikin wannan kogo yana mai ci gaba da jinyar jikinsa domin ba zai iya ci gaba da bude Sauran rijiyoyin ba, ya zamana cewa bashi da abinci sai wannan gasasshen naman Macijiyar, kuma bashi da ruwan sha sai jininta da ya malala a kasa. Har sai da jinin Macijiyar ya daskare ya 39 TASKARNOVELS.COM.NG ZAmana cewa sai ya sareshi da takobi yake sha. Wannan gasashen naman kuwa sai ya lalace ya rube har ma ya fara tsutsa, amma a hakan yake cinsa domin ya rayu kada yunwa ta kashe shi. Hantaru dai bai samu cikakkiyar lafiya ba sai bayan kwana goma sha uku. ranar kwana na goma sha ukun ne Hantaru ya je gaban rijiya ta biyu ya tsaya yana shawara da zuciyarsa akan ya budeta ko kada ya bude. Da zarar ya kai hannu da nufin zai sare mukullin rijiyar sai hannunsa ya kama karkarwa ya kasa saboda tsoron kada ya budo abin da yafi na rijiyar farko balai wanda ka iya zama sanadin ajalinsa gaba daya. Sai da Hantaru ya jarraba hakan sai ya kasa sare mukulin, Nan take Hantaru ya tuno da irin gwagwarmayar da ya sha a baya da lamarin da ke gabansa na auren gimbiya Larziya da batun komawa birnin Sin, sei kawai yi kanin tsoro ya kau dagA zaciyaraa Nan take ya daga takobinsa sama yana kurma ihu ya sare makullin. Nen take murfin rijiyar ya fadi cen gefe daya. Bisa mamaki sei baiga komai ba Hantaru ya sake rike takobinasa da kyau ya gyara tsayuwa ya jiran yaga abinda da zai fito daga cikin rijiyar. 40 TASKARNOVELS.COM.NG koda ya ji shiru sai ya matsa gaba da nufin ya wuce kan rijiya ta uku itama ya budeta. Yana gifta wennan rijiya ta kwatsam sai ya jiyo wani irin gurnani irin wanda bai ta6a ji ba da huci na busowa. Cikin razAni Hantaru ya ja aa beya ya sake gyara tsayuwa Wani irin dogon hannun bil'adama ne lafcece ya fara lekowa daga cikin rijiyar, sannan hannu na biyu ya leko. Daga can kuma sai ga mutum ya taso sama a hankali gama mikewa gaba daya. A sannAn ne Hantaru ya gA she maridi ne. Tun da Hantaru yazo duniya bai taba ganin bil'adama mai tsananin tsawo da kauri ba tamkar wannan maridi, domin ita dai rijiyar zurfinta ya kai kamu dubu, amma gashi ta yiwa maridin kadan, tsugunnawa ma yai a cikinta. Fadinta ya kai kamu arba'in, amma da kyar maridin ya fito daga cikinta, sai da ya muskuta kirjinsa sannan ya sami damar fitowa. Hantaru ya karewa wannan maridi kallo daga sama har kasa sai zuciyarsa ta karaya ya tabbatar da Cewa rayuwarsa na tsakanin RAI DA MUTUWA. Kawai sai yaja da baya ya takure a jikin bangon kogon, amman bai yar da takobinsa ba. Maridin 41 TASKARNOVELS.COM.NG ya wangame katon bakinsa ya kurma wani ihu, wanda ya haddasa girgizar kogon gaba ?aya har duwatsu kanana suka rinka zubowa kasa. Karar ihun tasa Hantaru ya yarda takobinsa ya rufe kunnuwansa har ya tsugunna kasSa yana neman maboya, domin ji ya yi kamar dodon kunnensa zai fado kasa. Nan take maridin ya shako wuyan Hantaru ta baya da 'yan yatsun hannunsa biyu ya ?aga sama tamkar ya dauki fara, sai ga kafafun Hantaru na wutsi-wutsil, gaba daya jikinsa na reto. Maridin ya tsaya yana tunanin irin kisan da ya kamata ya yiwa Hantaru. Da farko sai ya dunkule hannu ya kai masa wawan naushi a fuska. Duk da cewa yana ruke da wuyan Hantaru gam- sai da Hantaru yi waf ya zunguri idon maridin da f kafa, domin ya tabbatar da cewa idan maridin ya gabza masa Wannan naushi, sai ya tatitse fatarsa tamkar an taka ayaba akan dutse. Tsokanewar idon da Hantaru ya yiwa maridin ne yasa ya dimauce ya saki wuyan Hantaru ya fado kasa, amma huk da haka sai da hannun Maridin ya nutse a cikin bangon kogon dutsen tamkar ansa diga da guduma an buga a cikin bengo sai gashi ya 42 TASKARNOVELS.COM.NG haddasa wawakeken rami ajikin bangon, amma bai ji zafin komai ba a hannunsa tamkar ma takarda ya huda. A fusece maridin ya juyo ya ?aga kafarsa pa y kawowa Hantaru mugun taku. Cikin matukar zafin nama Hantaru ya goce ya bar inda yake. Sai ga kafar Maridin ta lume a cikin kasa iya kaurin gwiwarsa. De ya zare kafarsa kuwa sai ga rami zururu wanda za a iya saka mutum uku a ciki a binnesu. Nan fa aka fara guje guje tsankanin Hantaru da Maridin a cikin kogon, yana kai masa wawan naushi da bugu da hannu da kafa shi kuma yana gOcewa da zallewa. Dak inda maridin ya gabza sai ya haddasa mugun rami, walau bango ko kan kasa. Al'amarin da ya janyo gaba dayan kogon ya kama rugujewa. Sai ga kafar Maridin ta lume a cikin kasa iya kaurin gwiwarsa. De ya zare kafarsa kuwa sai ga rami zururu wanda za a iya saka mutum uku a ciki a binnesu. Nan fa aka fara guje guje tsankanin Hantaru da Maridin a cikin kogon, yana kai masa wawan naushi da bugu da hannu da kafa shi kuma yana gOcewa da zallewa. Dak inda maridin ya gabza sai ya haddasa mugun rami, walau bango ko kan kasa. 43 TASKARNOVELS.COM.NG Al'amarin da ya janyo gaba dayan kogon ya kama rugujewa ke nan, ya zamana cewa shi kansa maridin hankalinsa ya tashi, don haka sai ya koma gefe daya ya tsaya cak Yana hanki suka kara kallon- kallo tsakaninsa da Hantaru. Babban abin da ya fi tayarwa da Hantaru hankali shi ne, kofar kogon ta rufe ruf, babu ta inda ma zai iya fita bare ya nemi hanyar gudu sakamakon rugujewar da kogon ya yi, manyan duwatsu suka rikito kasa. Nan fa Hantaru ya aiyana a ransa cewa bashi da wata mafita face ya tunkari wannan maridi ya San dabarar da zai bullo masa ya kashe shi. Dole ne ayi daya cikin biyu, ko shi maridin ya sami nasara ko shi Hantaru ya samu. 44 TASKARNOVELS.COM.NG Kamar hadin baki sai maridin da Hantara suka wangame baki a lokaci guda kowannensu y kama kwarara ihu. Abin da ya ?aurewa maridin kai kenan, domin a wannan karon ihun maridin bai ruda Hantaru ba, bare ya dimauce har ya toshe kunnuwansa. Tun da wannan maridi ya wanzu a cikin wannan kogo tsawon daruruwan shekaru bai ta6a ihu ba ga duk abin da ya shigo abin ya iya jurewa ba. Kai bama mutum ba hatta aljan idan yana Wannan ihu nasa firgicewa suke, wasu su kama gudawa, Wasu ma sanadiyyar kurmancewarsu ke nAn. Idan kuwa mutane ne ma take suke haukacewa, amma yanzu sai gashi Hantaru ya jure masifar ihun nasa harma yanA mai da martani da Dasa ihun. 45 TASKARNOVELS.COM.NG A zahirin gaskiya Hantaru bu karamar juriya ya yi ba a wannan karon, domin gaba dayan jikinsa ya kama tsuma da karkarwa domin ji yake kamar an dura masa kwari masu yawa ba adadi a cikin kunnuwansa, suna tsinttsinka jijiyoyin kunnen, kuma yana jin kamar ana tsotse jinin jikinsa. Bayan kowannensu ya yi ihu da kururuwa har gabadaya kogon ya gama rugujewa, duwatsun suma suka rikito kasa, al'amarin da ya janyo Hantaru ya sami sababbin raunika ke nan a sassan jikinsa, in banda ma yana gocewa da tuni manyan duwatsu sun danneshi. Shi kansa Hantaru ya san cewa tsananin sa'a ne kawai ya ceceshi a cikin wannan kogo, sa'adda yake rugujewar amma ba zafin namansa ba. Koda gama rugujewar kogon sai Maridin ya falfalo da gudu yana take duwatsu suna rumurmushewa, ya yiwo kan Hantaru gadangadan. Koda Hantaru ya ga mutuwa ta durfafoshi sai shima ya yi ta maza ya ruga izuwa kan maridin Shima yana mai ci gaba da kwarara 46 TASKARNOVELS.COM.NG ihu shima, maridin yana nasa ihun, kowannensu tafe yake cikin mugun nufi, kai da gani ka san cewa idan akayi wannan gamo dole ne mutuwa ta sami rabonta Sai da ya rage bafisaura taku daya ba A tsakaninsu ba sai Hantaru ya yi sufa a kasa tamkar akan kankara mai santsi yake ya shiga karkashin Maridin ya takarkare iya karfinsa ya gabza masa naushi da hannaye biyu a marainansa. Take maridin ya yi suman tsaye ya kame kamar ya zamo gunki. Cikin zafin nama Hantaru ya mike zumbur ta bayan maridin yasa guiwar hannunsa ya doki tsakiyar hannun maridin na hagu. Take hannun ya karye ya yi kara kas! Maridin ya kurma ihu ya juyo a fusace ya kawowa Hantaru mangari da daya hannun nasa. Cikin sa'a kuwa ya sami Hantaru a kirji. Karfin mangarin ne yasa Hantaru yai sama ya fado kasa kan dutse ya baje a sume. Maridin ya yunkura da kyar

Chapter 2 of 14