Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TASKARNOVELS.COM.NG 1 TASKARNOVELS.COM.NG MAZAN JIYA 2 MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part B Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey KASHE GARI da sassafe rundunar su Sarki Dujalu suka mike suka ci gaba da tafiya, bayan kowa ya kimtsa cikinsa. Tun da aka fara tafiyar sai sarki Dujalu ya lura da cewa 'yar uwarsa Hursiya bata da sukuni. A duk sa'adda ya dubeta sai ya ga alamomin damuwa cike a fuskarta kawai sai ya yi murmushi, domin shi kadai ne ya san abin da ke damunta. 2 TASKARNOVELS.COM.NG Abin da ya bashi mamaki shi ne, mene ne ya hanata ta baiyana masa abin da ke damunta, ba wani abbu bane ya ke damun Hursiya ba face tsananin son jin ci gaban labarin sadauki Hantaru. Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya har tsawon kwana uku. Duk sa'adda aka yada zango sai Husiyya ta lallaba sarki Dujalu domin ya ci gaba da bata labarin. Da zarar ya fuskanci abin da take so, sai ya kama gyan-gyadin karya, bisa dole Hursiya ta hakura itama ta kwanta har barci ya saceta bata sani ba. Da yammacin kwana na uku ne wannan runduna ta su sarki Dujalu ta iso wani katon daji mai ban tsoro wanda ake yiwa lakabi da Sauratul Auzur. Duk da tsananin yawan wannan runduna aljanu da mutane da kuma gagarumin shirinsu sa da kowa yaji tsoro ya shigeshi, bisa tsintar kansu a cikin dajin Sauratul Auzur, sarki Dujalu ne kadai bai girgiza ba. Shi dai dajin Sauratul Auzur babu komai a cikinsa face manya-manyan bishiyoyi da 3 TASKARNOVELS.COM.NG manyan duwatsu masu ban mamaki. Babu inda mutum zai je a duniya ya ga irinsu, sannan siffofin bishiyoyin da duwatsun ma ababan tsoro ne. Sau tari sai mutum ya ga suna motsi da rangaji tamkar za sun haifar da girgizar kasa a dajin gaba daya. Daga dajin Sauratul Auzur zuwa tekun bahar Sufiya tafiya ce ta wata hudu kacal, kuma cikin dajin Sauratul Auzur mutun zai yi ta tafiya ta tsawon wata hudu. Da isowar su sarki Dujalu farkon dajin Sauratul Auzur, sai sarki Dujalu ya bada umarnin a tsaya. Nan take kuwa na kan dawakai suka ja dawakansu, aljanun da ke tafiya a sararin sama kuwa suka saki fuka-fukansu suka sauko kasa. Nan fa kowa yai ladaf aka yi tsit tamkar babu mai numfashi a wajen. Sarki Dujalu yai gyaran murya sannan ya ce, "Ya ku jama'ata kuyi sani cewa mun iso dajin Sauratul Auzur. Daga nan zuwa tekun bahar Sufiya inda takobin Saiful Lujara take tafiyar wata hudu ce kacal. Ku yi sani cewa masifa da bala'in da ke cikin wannan daji sun wuce tunani don haka sai kowa ya gyara damararsa, domin 4 TASKARNOVELS.COM.NG komai zai iya faruwa. Ko shakka bana yi da yawa daga cikinmu za su iya rasa rayuwarsu a cikin wannan daji. Wadanda duk suka kai izuwa karshen wannan daji a raye a cikin koshin lafiya sun cika jaruman kwarai ababan yabo da jinjina." Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya dubi Hursiya ya ce, "Komai wuya da tsanani ki tabbatar da cewa a ko yaushe kina tare da ni Hursiya ta gyada kai tana mai nuna cewa lallai za ta kiyaye. Nan take sarki Dujalu ya zunguri cikin aljanin da ke dauke da su shi da Hursiya, suka fara wucewa kan gaba, sannan kowa ya bi bayansu a cikin yanayin tsoro da dari-dari. Sai da aka shafe sa'a guda ana tafiya a cikin dajin ba a hadu da komai ba kuma ba a ga wani mugun abu ba. Al'amarin da ya jefa kowa cikin tsananin mamaki ke nan domin in banda kukan kananan tsuntsaye da kwari babu wani sauti da ke ratsa kunnuwa. Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai kawai aka hango wata jibgegiyar halitta a can gaba ta cika 5 TASKARNOVELS.COM.NG hanya tun daga sama har kasa tamkar za ta tokare da hadari. Babu ta inda za a bi a wuce face ta cikin halittar. Ita dai wannan halitta tana kama da bil'adama, aljan da kuma dodo, Kuma gaba dayan jikin na ta ne yake da siffofi ukun. Ma'ana fuskarta da gangar jkinta da hannayenta. Koda aka yi arba da wannan halitta sai gaba dayan dakarun sarki Dujalu suka firgice suka tsaya cak! A waje daya Aljanin da ke dauke da sarki Dujalu wanda ake kira Rauzuf sai ya fara kada fuka-fukansa a hankali alamar shima ya tsorata, amma bai fasa tunkarar halittar ba saboda gudun fishin sarki Dujalu, amma gaba dayan jikinsa karkarwa yake tamkar wanda ya kamu da zazzabi mai zai." Koda sarki Dujalu ya fahimci halin da aljani Rauzuf ke ciki sai ya daka mäsa tsawa ya ce, "Ya kai Rauzuf a kul ka kuskura ka. ja da baya ko kuma ka tsaya ga ci gaba da tafiya idan kuwa ka 6 TASKARNOVELS.COM.NG tsaya ni da kaina zan zare maka ruhin numfashi" Koda jin wannan batu sai aljani Rauzuf ya kara karfin tafiyarsa ya tunkari wannan katuwar halitta kai tsaye. Sai da suka iso daf da halittar ya zamana cewa tazarar da ke tsakaninsu ba ta wuce kamu uku ba, sai halitar ta wangame katon bakinta mai kama da kofar gari ya buso wata irin iska mai karfin gaske tamkar guguwa. Take aljani Rauzuf ya fado kasa tim! Sarki Dujalu da Hursiya suka tuntsuro kasa daga kansa suka baje a kas. Hatta sauran dakarun da ke bayansu sai da iskar ta tarwatsasu, na sama suka rikito kasa, na kasa kuwa suka baje. Daga can sai katuwar halittar ta bushe da mahaukaciyar dariya mai tsananin ban tsoro wacce ta sa kowa da kowa ya sume face sarki Dujalu. Gaba daya dajin ya hautsine ya kama rangaji,wuta ta kama bishiyoyi. Babu abin da ya rage a tsaye bisa duga-digansa face sarki Dujalu. 7 TASKARNOVELS.COM.NG A wannan lokacin ne shirgegiyar halittar ta bude idanuwanta fala-fwala masu kama da girman rami ta dubi Dujalu cikin tsananin mamaki. Fiye da shekaru dubu da doriya wannan halitta ke tsare wannan hanya, duk abin da ya zo gabanta in dai tayi wannan dariya sai abin ya fadi kasa sumamme amma yau ga wani takadarin bil'adama guda daya a tsaye cak a gabanta ko girgiza bai yi ba. Cikin wata irin gaggausar murya halittar ta dubi aljani Dujalu ta daka masa tsawa. Duk da cewa sarki Dujalu gwarzon namiji ne wanda bai san tsoro ba sai da hantar cikinsa ta kada shi kuwa aljani Rauzuf take ya kara sumewa a karo na biyu. Halittar ta dubi Dujalu cikin nutsuwa ta ce, "Ya kai wannan hatsabibin biladama wane ne kai kuma wane tsautsayi ne ya shigo da ku cikin Wannan daji na Sauratul Auzur alhalin kun sin cewa ba a taba ratsowa ta cikinsa be?" sarki Dujalu yaji wannan tambaya sai ya bushe da dariya sannan ya murtuke fuskarsa kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa ya ce, "Ni 8 TASKARNOVELS.COM.NG ne sarki Dujalu mai mulkar kasar Hawarul din. Ya kai wannan babbar halitta ka sani cewa na yarda daa kaina domin ni ne DODON MAZA ne a wannan zamani, magajin MAZAN JIYA. Duk bala'in da ke cikin wanann daji na san da shi kuma sai na ketare ta cikinsa domin na isa tekun bahar Sufiya don na dauko takobin Saiful Lujara." Koda sarki Dujalu yazo nan a zancensa sai katuwar halittar ta sake bushewa da dariya a karo na biyu sannan ta ce, "Sama da mutum dubu dari ire-irenku wato masu irin wannan buri naka sun hallaka bisa wannan tafarki wadanda duk abin da kake takama da shi sun fika. Babu wanda ya taba haye bala'in bare har ya shafe sauran tafiyar da ke cikin wannan daji na Sauratul Auzur ya ketare sauran masifun da ke cikinsa ya isa bakin tekun Bahar Sufiya. Ina mai shawartarka da ka juya da baya kai da jama'arka domin kada ka janyo asarar miliyoyin rayuka a banza." Sarki Dujalu ya yi murmushi mai nuna yarda da kai, sannan ya ce, "Ko mutum daya daga cikin Jama'ata ba zai rasa rayuwarsa ba. Ni kadai zan samar mana da hanya mu wuce gaba saboda 9 TASKARNOVELS.COM.NG haka ina mai shawartarka da ka kauce daga kan hanyarmu idan har kana son ka tsira da rayuwarka don ban ga abin da ya isa ya hanani ratsawa ta cikin wannan daji ba." Kafin sarki Dujalu ya gama rufe bakinsa tuni katuwar halittar ta mike tsaye. Al'amarin da ya sa gaba daya dajin ya yi lumshi tamkar rana ta fadi, ashe da can a zaune take ba a tsaye ba. A sannan ne sarki Dujalu ya daga kansa sama ya dubi halittar sai ya ga cewa a wannan karon baya hango kanta. Nan take halittar ta sake buso iska ga sarki Dujalu, wannan karon sai iskar ta dagashi sama ta fara gwarashi a jikan manyan bishiyoyin dake dajin. A dai-dai wannan lokacin ne Hursiya da sauran Dakarun gaba daya suka farfado daga dogon suman da suka yi suka ga abin da ke faruwa. Koda suka ga sarki Dujalu a sama ana gwarashi a jikin bishiyoyi har ya fara galabaita sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka karaya. Ita kuwa Hursiya sai ta fashe da kuka domin ta tabbatar da cewa shi ke nan ta rasa dan uwanta. 10 TASKARNOVELS.COM.NG Gaba dayan dakarun dai sai suka cika da mamaki saboda a yadda suka san sadaukantakar sarkinsu da karfin sihirinsa amma sai gashi duk sun zamo a banza ya kasa ceton kansa ma bare suma ya cecesu. Nan fa wasu daga cikinsu suka fara tunanin su ja da baya don kada wannan halitta ta gama da sarki Dujalu sannan ta dawo kansu. Kafin su yanke hukunci ne wani abin mamaki ya faru, kawai sai gani suka yi shima sarki Dujalu ya yi nuni da hannunsa izuwa ga wannan iska mai karfi da take wujijigashi take wata irin iska ta fito daga cikin hannun nasa ta kama daya iskar mai wahalar da shi suka kama gumurzu. Nan fa kallo ya koma kan iskokin biyu suka rinka tsiri a sama suna fitar da wata irin tsawa da kugi mai razanarwa. Wani lokacin idan iskokin suka yi sama sai ka ji sun fado kasa fat! Tamkar giwa ta fadi. Katuwar halittar da sarki Dujalu sai suka zuba idanu kawai suna kallon gumurzun da iskokin ke yi. Nan fa dajin ya kara ruguntsumewa domin a duk sa'adda iskokin suka hada jiki sai ka ga wuta feshi da tartsatsi. Al'amarin da ya sa gaba 11 TASKARNOVELS.COM.NG dayan dakarun suka dimauce ke nan suka kama guje-guje a cikin dajin suna neman maboya. Kafin a jima filin wajen ya dade babu kowa face sarki Dujalu sai aljaninsa Rauzuf da kuma Hursiya wadda jikinsu ke makyarkyata saboda tsananin tsoro, shi aljani Rauzuf ma bai san sa'adda ya fara sakin fitsari ba, amma bisa mamaki sai ya ga na wannan feshin wuta da tartsatsin basa zuwa inda suke shi da Hursiya sai dai su zuba a gefensa. A duk sa'adda iskokin biyu suka fado kasa kauwa, sai gaba dayan dajin ya kama tambaltambal tamkar jirgin ruwa akan kogi sa'adda igiyar ruwa ta kada. Haka dai aka ci gaba da wannan dauki ba dadi har tsawon sa'a guda. Daga karshe ne iskokin biyu suka kankame juna suka kama da wuta suka kone kurmus suka zama toka. Koda faruwar hakan sai aka fara kallon-kallo tsakanin sarki Dujalu da katuwar halittar a ya yin da ta sauko da dogon kanta kasa tamkar zalbe ya leko da wuyansa waje daga cikin tagar daki. 12 TASKARNOVELS.COM.NG Koda sarki Dujalu ya yi arba da mummunar fuskar halittar sai yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske. Wannan shi ne karo na farko de sarki Dujalu yaji tsoro ya shigeshi arayuwarsa. Bisa dole Dujalu ya ja da baya taku uku, amma saboda yana da dakakkiyar zuciya sai ya ki gudu ya tsaya ya zare takobi, kuma ya gyara tsayuwa akan aljani Rauzuf. Ya yin da babbar halittar ta ga abin da Dujalu ya yi sai ta bude hannayenta biyu ta dagasu sama kai kace tagwayen tsaunikane ke yawo a samaniya sannan sai ta wangame katon bakinta ta kwarara uban ihu wanda ya zamo sanadin sake ruguntsumewar dajin fiye da ko yaushe. Shi kansa Dujalu bai san sa'adda ya kara ja da baya ba. Ita kuwa Hursiya sai ta kankame Dujalu ta baya ta fashe da kuka. Cikin kwarin zuciya Dujalu ya 6an6areta dag jikinsa ya zaunar da ita kasa bisa kan aljani Rauzuf sannan sai ya tashi sama kamar tsuntsu ya juyo ya dubi aljani Rauzuf ya ce, "Ku dan ja da baya kadan ku zuba ido ku ga abin da zai faru. Idan na sami nasarar hallaka wannan halitta sai mu ci gaba da tafiya idan kuma ta hallakani ku 13 TASKARNOVELS.COM.NG koma da baya ku nemi sauran abokan tafiya domin ku koma can birnin Hawarul din, gimbiya Hursiya ta gaji karagata". Koda gama fadin haka sai sarki Dujalu ya yunkura da dukkan karfinsa ya tasamma katuwar halittar ya kai ma ta wawan sara a hannunta na hagu." Koda takobin Dujalu ta sari hannun sai tartsatsin wuta ya tashi gami da wata irin kara tamkar karfe da karfe. Halittar ta yi girgiza tamkar susa aka yi ma ta. Dujalu yaja da baya kadan, koda ya dubi kaifin talkobinsa sai ya ga ta dakushe. Al'amarin da yai matukar girgiza hankalinsa kenan ya gamsu cewa lallai yau ya gamu da gamonsa. Dujalu ya kurawa halittar idanu yana tunanin irin dabarar ya kamata ya yi don ganin ya kawar da ita. Abu na farko dai shi ne, ya tabbatar da cewa in dai batun farfin damtse ne ba zai iya da ita ba, don ko ba a gwadaba linzami yafi karfn bakin kaza. Haka kuma idan batun karfin sihiri ne nan ma ya san babu nasara tun da an gwada an yi RAGAS. 14 TASKARNOVELS.COM.NG To wai shin mene ne zai kwaceshi a hannun wannan halitta? Ai babu mafita face sa'a. Kafin sarki Dujalu ya gama aiyana wannan furuci a bakinsa sai halittar ta yi masa wawan mangari da hannunta guda a fuska saboda karfin dukan sai da sarki Dujalu ya ga taurarin wahala a idanunsa, numfashinsa ya sarke a lokacin da yai sama tamkar an janyeshi da kugiya Dujalu ya gwaru da bishiya har keyarsa ta tsage ta fado kasa a cikin wani irin mugun hali mai kama da rabin suma. Koda jibgegiyar halittar ta ga ta sami wannan nasara sai ta bushe da mahaukaciyar dariya. Koda gama fadin haka sai Hursiya ta kwarara uban ihu ta fashe da kuka, domin zuciyarta ta gama karaya ya sallama cewa dan uwanta ya gama halaka, Shi kuwa aljani Rauzuf sai ya yunkura da nufin ya bude fuka-fukansa ya gudu. Ai kuwa shima sai ji ya yi an fyadeshi ya baje a kas, sai ga jini na zuba ta cikin hancinsa da bakinsa, ko motsi bai yi ba tamkar gawa. A dai-dai wannan lokaci ne katuwar halittar ta fara tako kafafunta ta nufo inda sarki Dujalu ke kwance da nufin ta mitsttsikeshi da kafarta, sannan ta hallaka Hursiya. 15 TASKARNOVELS.COM.NG Cikin karfin hali Hursiya ta ruga kan Dujalu ta fara kokarin janyeshi daga inda yake kwance, don kada halittar ta cimma nufinta. Hursiya na cikin jan sarki Dujalu sai kawai taji ya cije. Nan take ya bude idanunsa ya dubeta ya ce, "Ma za ki mike ruga izuwa baya, yanzu za mu fara gagarumin yaki ni da wannan halitta wanda zai iya janyo hallakar duk wani abu mai rai da ke cikin dajin nan saboda haka kiyi ta gudu iyakar iyawarki har sai inda kuzarinki ya kare, kar ki damu dani, nai miki alkawari lallai zan riskeki a duk inda kike kuma a raye." Koda jin wannan batu sai Hursiya ta mike zumbur ta falfala da gudun tsiya. A dai-dai wannan lokaci ne halitar tayi taku daya jal, ta isa daf da Dujalu ta daga kafarta guda sama za ta mitsttsikeshi. Yadda Dujalu ya ga fadin kafar halittar tamkar katon tsauni ne zai danneshi cikin tsananin zafin nama sarki Dujalu ya daka tsalle ya haye kan saman kafar halittar ya kama azababben gudu akanta, yabi ta kan kansakalin kafar ya bi ta cinya tamkar kadangare na hawa bango. 16 TASKARNOVELS.COM.NG Koda halittar taji Dujalu na tafiya a jikinta sai ta rinka kawo masa duk da tafin hannunta. Da zarar ta kawo dukan ya goce sai ka ji wata irin kara fau tamkar an buga tambura, wani irin gagarumar iska na tashi. A haka ne Dujalu ya samu ya isa kan kafadar halittar, sai da ya yi irin gudun rabin sa'a uku akan kafadar sannan ya iso inda fuskar take ya sake daka tsalle sama ya sari habar halittar da takobinsa. Sautin karar haduwar karfe da karfe ne ya tashi kawai. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Dujalu ke nan domin shi zatonsa halittar za ta ji sara a fuska. Nan fa aka fara sabon gumurzu a tsakaninsu ya zamana cewa Dujalu na ta tsalletsalie akan halittar tamkar mai yawo a cikin katon daji. Ita kuwa halittar ta rinfka kai masa duka da cafka, aka rasa wanda zai sami nasara a cikinsu. Sai da aka shafe sa'a tara ana wannan gumurzu. A sannan ne sarkı Dujalu ya gaji ainun, ita kuwa halittar ko kadan babu alamar gajiya a tare da ita tamkar ma a sannan aka fara artabu. Koda sarki Dujalu ya fahimci cewa idan fa aka ci gaba da wannan gumurzu a haka izuwa tsawon 17 TASKARNOVELS.COM.NG sa'a daya jal zai sare ya kasa komai, halittar ta sami nasarar hallakashi sai hankalinsa ya dugunzuma ya fara tunanin abin da zai fissheshi. Tsawon rabin sa'a Dujalu bai yi tunanin mafita ba. A dai-dai wannan lokaci ne halittar ta shammaci Dujalu ta mangareshi ta baya ya rlkito kasa daga kan kafadarta. Koda ganin haka sai halittar tayi shiri tana jira kawai Dujalu ya fado kan turba ta murkusheshi da guiwarta yadda za ta talitseshi. Saboda nisan da ke tsakanin kafar halittar zuwa kasa sai da Dujalu ya shafe dakika dari shida da sitin yana saukowa kasa. Sa'adda Dujalu yaji kafafunsa sun dira bisa turba sai ya yunkura ya kara daka tsalle sama tamkar akan sifirin ya dira, a lokacin ne kuma halittar ta tsugunno kasa da nufin ta talitseshi da guiwarta amma sai taji guiwarta ta bugu da kasa ta nutse cikin kasar ta haifar da katon rami mai zurfin kamu dubu. Kafin halittar ta zare guiwarta daga cikin karkashin kasa tuni Dujalu ya sake isa kan kafadarta. Kafafunsa na dira akan kafadar sai ya sake daka tsalle yai sama ya isa dai-dai fuskarta sai kawai ya soka takobinsa izuwa cikin hancinta guda. Ai kuwa sai halittar 18 TASKARNOVELS.COM.NG ta kwarara uban ihu bisa tsananin zafin da zogin da taji tayi taga-taga da baya. Tuni takobin Dujalu ta makale cikin hancin halittar, shi kuwa sai ya rike takobin da hannayensa biyu yana reto a sama kuma ya cigaba da kokarin zare takobin amma sai ya kasa. A duk sa'adda ya girgiza takobin sai halittar ta kara kwarara ihu ta kawo masa cafka da mangari amma sai ya wurkila kafafunsa ya goce. Shi kansa Dujalu ya yi mamakin yadda ya kasa zare takobin duk da cewa gaba dayan nauyinsa a kanta yake. Daga can sai Dujalu ya yi amfani da dukkan karfinsa ya finciko takobin ya zarota daga cikin hancin halittar. Takobin na zarewa sai ga jini na shatata tamkar teku ta balle. Dujalu ya rikito izuwa kasa, itama halittar sai ta taho kasa a sandare. Dujalu da halittar suka taba turba a lokaci guda. Kafin Dujalu ya goce wuyan halittar ya fadi a tsakiyar cikinsa, amma sai ya yi gwafa bai taba jikinsa ba, amma ya rufeshi yadda ba zai iya fitar da kansa ba. Halittar dai ko motsi bata sake yi ba, domin 19 TASKARNOVELS.COM.NG ta zama gawa. Har a sannan kuma jini na malala daga cikinta yana kwarara a dajin, tamkar ruwan samansa ake yi. Dujalu dai bai san sa'adda ya bushe da dariyar farin ciki ba, bisa ganin wannan gagarumar nasara da ya samu ta hallaka halittar, amma da ya dago kai ya dubi wuyan halittar wanda yai gwafa a kansa ya tokareshi sai hankalinsa ya yi mummunan tashi domin bai san yadda zai iya ture gawar haittar ba ya fito, saboda jikin halittar ba zai saruba da takobi bare ya sareshi. Dujalu na cikin wannan tunani ne ya hango yar uwarsa Hursiya ta rugo gareshi da gudu ita kadai tana murmushin farin ciki. A sannan ne kuma aljani Rauzuf ya farka daga dogon suman da ya yi, ba zato kuma sai ga sauran dakaru suna fitowa da dai-dai daga wuraren da suka buya sunaa rugowa wajen Dujalu suna ihu bayan hari. Duk wanda yazo ya ga wannan katuwar halitta kwance a kas a mace sai ya cika da tsananin mamaki. Nan fa dakaru suka kama fashewa da murna suna yiwa Dujalu jinjina. Duk wannan abu da ke faruwa zuciyar Dujalu tafarfasa take kamar za ta fone saboda tashin hankalin da yake ciki na ganin kansa a karkashin gawar halittar bisa sanin cewa ba zai iya fitowa ba. Daga can sai Hursiya 20 TASKARNOVELS.COM.NG ta lura da fuskar Dujahu ta fahimci cewa lallai a cikin tsananin damuwa yake. Cikin firgici Hursiya ta dubeshi ta ce, "Ya kai dan uwana ina dalilin wannan matsanaiciyar damuwa a gareka?". Koda jin wannan tambaya sai sarki Dujalu yai ajiyar zuciya cikin karaya ya ce, "Ya ke 'yar uwata kiyi sani cewa wannan murna da kuke yi bisa samun nasarata dai-dai take da farin ciki da zuwan mutuwata. Ki dubi yadda na kasance a karkashin gawar wannan halitta, yenzu ta ya ya za ku iya zaroni daga karkashinta, shin a cikinku Wane ya yi tunanin wannan hali da na ke ciki?" Sa'adda Hursiya taji wannan tambaya sai ta dubi gawar halittar da kyau ta ga yadda ta rufe Dujalu ruf babu wata karamar kofa da za a iya zareshi. Nan take hankalinta ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya, don haka sai ta mike tsaye ta dubi gaba dayan dakarun da ke wajen mutane da aljanu ta daka musu tsawa. Gaba dayan dajin yai tsit! Kowa ya zuba ma ta idanu. A sannan ne hawaye ya zubo daga idanun Hursiya ta budi baki ta ce, "Ashe gaba dayanku nan taron banza ne taron wofi? Ku dubi halin da sarkinku ke ciki, ashe dayanku ba zai yi 21 TASKARNOVELS.COM.NG tunanin hanyar da za a bi a zaroshi ba daga karkashin gawar wannan halitta ba?". Koda jin wannan batu sai kowa yai tsuru- tsuru ya shiga taitayinsa aka marmatso ana nazarin yadda za a yi a janye gawar katuwar halittar daga kan sarki Dujalu. Nan fa aka shiga yin shawarwari. Wasu zaratan jaruman yaki guda uku, wadanda babu kamarsu a cikin dakarun suka ware gefe. Zan ci gaba. MAZAN JIYA Littafi na biyu 2 Part B Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Daya daga cikin wadannan zaratan jarumai aljani sunansa Karbazu, a gaba dayan dakarun aljanun da ke wajen babu sadauki kamarsa, kuma ma'abocin hikima ne da sanin dabarun yaki daya kuwa mutum ne, sunansa Barsuma. Barsuma shi ne sarkin yakin birnin Hawaru din. Shima ya kasance gagarumin sadauki kuma gwarzon mayaki a cikin jinsin bil'adama wadanda babu kamarsu a gaba dayan nahiyar. Shima ya kware matuka a sanin makama da dabarun samun nasara a yaki. Mutum na uku wani tsohon sadauki ne wanda shekarunsa sun haura casa'in amma har gobe yana dakawa 22 TASKARNOVELS.COM.NG matasa gumba a hannu wanda ake kira da suna Shurkaib bin Dallas. Lokacin da Kurbazu, Barsuma da Shukaib suka ware gefe daya domin su yi shawara bisa dabarar daza a yi a sami nasarar zaro sarki Dujalu daga karkashin gawar halittar sai Karbuza ya dubi Barsuma da Shurkaib ya ce,"Yanzu ku mene ne shawararku, ta ya ya kuke ganin za mu iya zaro sarki ba tare da lafiyarsa ta tabu ba? Abu na farko dai, janye gawar wannan halitta daga kansa ba karamin aiki bane, saboda girmanta da nauyinta. Idan gaba dayanmu zamu taru ba zamu iya ture ta ba da karfin tsiya. Idan muka ce zamu zauna anan muna kula da sarki har izuwa lokacin da halittar za ta rube mu sassareta to tabbas warinta ma zai iya zama ajalinmu gaba daya. Yanzu sai ku fadi shawarwarinku kafin na fadi tawa ku ji mu zabi wadda za ta fi inganci" Koda jin wannan batu sai tsoho Shurkaib ya yi murmushi ya ce, "Ni ba zan fadi tawa dabarar ba sai naji taku, kuma zan fadi tawa dabarar ne bayan an jarraba taku ba a sami nasara ba, kuma bisa sharadi guda". Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Karzuba da Barsuma. Barsuma ya ce, "Ya kai Shurkaib ka shiga taitayinka fa ka san abin da kake fadi. Yanzu har 23 TASKARNOVELS.COM.NG ka isa ka sanya wani

Chapter 1 of 14