You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kakeba yanzu kana gida" dan dagokai yayi ya kalli Arham din wata yar gajeren tsaki yaja yace "Omg wai why did u initiate this dinner stuff at the first place ma eh? Goddd! Mutum cannot rest again yayi abinda yakamata, am so so sick of this wedding, gosh!" girgixa kai Arham yayi ganin yanda yake masifa bil hakki ya karbe laptop din tareda shutting nashi down yarufe yarike ahannu sanan ya mikamai hannu yace "muje mushirya" ahankali yatashi Arham yabishi da kallo yana sanye da faran t-shirt sai wani 3quater short daya tsayamai wajajen gwuiwa shima fari, kafafunshi sanye cikin farin bathroom slippers, gashin kafarnan kwance lub lub irin na mugun dan hutun nan. Ahankali kaman wanda kwai yafashe wa aciki yake tafiya Arham yabude kofar hadadden bedroom dinshi suka shiga ciki, wajen wardrobe dinshi yayi yafito dawasu kaya da bama abude ba yazube su kan gadon sanan yabude ya shiga shiryawa cikin wata white suit na ermenegildo zenga, suit din yamugun fitting nashi daga kasan waje akamai order suit din aka tahomai dashi, sanan yadauki cover shoe dinshi na dinner sabo fil Black, designers shima na Testoni, tsayawa chak Arham yayi yana kallonshi yamugun yin kyau sai kallon kayan yake, juyowa Waleed yayi ya mikamai bow tie din dake hannunshi yace "tayani sawa blood" karban bowtie din Arham yayi yashiga samai kaman ba zaice komiba saikuma yace "amman wanan takalmin da suit din bashi mukaje muka sayo tareba a dunes ko?" girgiza mai kai yayi yace "Uncle yazomin dashi daga Ukraine jiya daya iso" gyadamai kai Arham yayi baisake cewa komiba yana gama samai yawuce yaje wardrobe yaciro wayanda suka sayo tare, yazaro tashi suit din black, dan abokan ango black suit zasu saka shikuma ango white, ya shirya tsaf sanan yataho key motar Waleed ya dauka yace "let's go" fitowa sukayi daga dakin, har zasu fita daga falon Ammi ta shigo dakin sun kusan cin karo, binsu tai da kallo yanda suka mata kyau sosai kafin ta sauke idanunta kan Waleed dayay mata wani irin kyau batasan lokacin data saki wani kayataccen murmushi ba, wucesu tayi tazauna kan sofa sanan takalli Waleed tace "zonan Son" tahowa yayi ahankali kaman wanda baison tafiya yazauna kusada ita inda take nunamai, hannunta takai tai cupping face dinshi tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi kafin ta shafa fuskar tace "you look so much like your father today, kayi kyau sosai, Allah ya maka albarka kaji" dan lusme ido yayi yana danne abinda yakeji a zuciyan shi yace "Ameen" purse din data shigo dakin dashi ta ijiye agefenta tadauka tabude taciro rapas nayan dollars guda biyu tamikamai tace "gashi kama y'ata manni dasu" karban kudin yayi ahankali dan baiso yaki karba taji haushi, rungume shi tayi ahankali taredamai kiss akumatu tace "stop being sad, I love you son, kaci abinci kuwa?" juyawa da sauri Arham yayi yafita daga dakin ya shiga mota Waleed din yay zamanshi a mazaunin direba, he just wish inama shine Waleed, kome zaiyi iyayen shi basa tabamai fada komin girman abun, unlike him da kullum abu kadan Umma fada takemai, abu dan kankani sai fada, Waleed ko abinci ma abaki ake bashi, bodyguard ma saida sukai fada da Ammi sosai dan anso kusan 10 sudinga binshi da kyar ya karbi daya wanda yadawo direban shi, bama abari yasha wahalan neman mataba aka samomai yar gidan masu kudi, graduate lawyer fa dudda dai bai taba ganinta ba aka bashi, just look at suit din da uncle dinshi ya kawo mai daga Ukraine, suit din ermenegildo yana costing about 22 to 28000 dollars, suit din jikinshi kadai worth a fortune dan yakai almost 8.8million naira a kudin Nigeria, takalmin kafanshi na Testoni kusan 3m ne shima, gata da dadi is beyond tunanin kowa ko shima inda bai gani da idanunshi ba dabazai taba yarda ana bama yaro gata irin gatan da ake bama Waleed ba, why was he born from the poor home? Maisa Umma ta auri Abban shi wani Malam Muhammad Bala, malamin islamiyya? Yataso ko gidan kansu basuda shi sai gidan haya, gidan dakuna ashirin da biyu da bayi guda biyu daya na kashi daya na fitsari, daga baya kuma yazo yarasu ya barsu cikin talauci, Waleed ne ya shigo rayuwan shi ya chanza mai komi..... Bude motan da akayi yadawo dashi daga daga dogon tunanin dayaje Ammi ne tabude ma Waleed din kofar motan tana kallon Arham tace "son ina gajiya" cikeda kunya dan yafi sakewa da Mom sabida ita tanada raha sosai while Ammi batada raha tanada fada, bata cika wasa da yaraba, aduniya in tana tareda Waleed ne kawai zaka dinga ganin dariyanta da murmushi ta abanza, da farkoma ya dauka bata sonshi ne sai daga baya ya lura haka Allah yayi ta ita kawai bamai yawan wasa da sakema yara fuska bane, cikeda girmamawa ya sauke fuskanshi yace "ina yini Ammi, ya taro" tana kokarin saka Waleed dake mata wani shegen shagwaba a mota tace "Alhamdulillah Arham, ai tuntuni muna tareda mahaifiyarka ma wlh, mamanka akwai kirki, kaga Arham gashinan drive him safe please, saikun dawo, bye Son, have fun okay, if u need anything ka kirani zan aikoma dashi" ta shafa kan Waleed din dake tura mata baki tana murmushi, kunna motar Arham yayi yaja Ammi na daga musu hannu tana murmushi, saida sukadan yi nisa ahanya sanan ya kalli Arham din dayaga yay shiru kuma ba halin shi bane yamika mai rapas din dollars din da Ammi tabashi duka biyun yace "use this" da sauri Arham ya kallai saikuma ya maida kanshi kan tukin yace "a'a, abinda Ammi tabaka zan karba" murmushi yayi kafin ahankali yace "take it inada wanda zanyi amfani dashi already" "shikenan" Arham yafadi ahankali kafin yace "thanks blood" murmushi Waleed yamai baice komiba, ahaka har suka karasa event centre babu wanda yakara magana cikinsu, daman yawanci in suna tare Arham ne mai kawo hira shi Waleed iya kanshi um a'a kokuma yan maganganu kadan, parking yayi yace "ka zauna aciki, I need to confirm in Amarya ta iso dan tare zaku shiga Hall din" bai jira amsanshi ba yamaida kofan yarufe yay wurin entrance din daidai zai shiga Abdul suna saukowa daga elevator tareda Salima suna hira shiru sukayi ganin Arham, Salima tace "you must be Arham ko? Best friend na ango" dan murmushi Arham yayi yana binta da kallo tana sanye cikin asshobi kawayen Amarya pitch yace "yeah nice to meet you Mss Salima" murmushi Salima tayi tana kallonshi ganinshi shima kyakkyawa sosai saidai dudda kyanshi baikai kyawun Dr ba, kuma Dr yafishi kaurin jiki da cikama mutum ido, ganin kallonshi take yasa ya katse shirun yace "ina Amarya? Cus they're going in together" "eh tana wani daki asama where is Dr?" juyawa yayi yace "lemme get him" har wajen motan yaje yabude motan ya kalli Waleed dake dandanna waya yace "let's go ango" ballamai harara Waleed yasakeyi hakan yasa Arham yace "sorry mana ai kuma gaskiya nafadi kai angon ne" ahankali Waleed yafito yana gyara suit din jikinshi su karan kansu su Abdul da Salima kallonshi suke yawani irin yin mugun kyau cikin white suit din dasukai mugun fitting dinshi maida kofar Arham yayi yana kallonshi yace "muje" ahankali suke tafiya har zuwa gaban entrance din Salima takasa daina kallonshi, dan kallonta yayi sanan ya kalli Abdul batare dayace musu komiba, anatse Abdul yace "sannu da zuwa Ya Waleed" bai kallesu ba yacema Arham dake kusadashi "let's go" wucewa sukayi dukansu suka shiga lift din yakaisu 4th floor, wani daki Salima tabude tana kallon Arham dan Waleed mugun cika mata ido yake tace "ku shigo tana nan" shiga ciki tayi suka hada ido da Ilham datasha uban gayu anmata makeup tasaka wani gown white daya mata fitinannen kyau ita kadai zaune kan wani Royal chair tai kyau sosai, cikin tafiyan nan nashi mai daukan ido daidai ya sawo kanshi cikin dakin Arham biyeda shi abaya, ahankali ta mike tsaye tana kallonshi hada ido sukayi hakan yasa ya tsaya chak shima, wani irin dadi ne ya lullubeta batasan lokacin data saki murmushi ba da sauri tazo wajenshi batai wata wataba tafada jikinshi ta rungume shi, ihu dakin ya dauka Arham ya shigo dakin da kyau yana kallonsu yana murmushi, da sauri Salima taciro wayarta tafara musu hotuna, ahankali yadaga hannayenshi ya rungume ta back, wani irin ajiyan zuciya ta sauke ta shige jikinshi sosai tana shakan kamshin dayakeyi, kaman ta jawo gobe takeji ayi a daura musu aure tayi ta dawo matar this ajebota handsome rich kid, "wai anan zamu kwana ne" Abdul yafada yana dariya, ahankali tasake shi cikeda jin kunya hakan yasa shima ya saketa, juyawa tayi suka hada ido da Arham da tundazu yake kallon bayanta Allah Allah yake yaga fuskarta, dan murmushi tayi sanan tajuya ta kalli Waleed din, dan lumshe ido yayi yabude kaman mai rada yace "my best friend, my brother, my blood, Arham" wani irin murmushi tayi ta juya ta kalli Arham tace "the great Arham nasha jin labarin ka tun abakin Ammi, my husband best friend childhood friend, so nice to meet you" dan murmushi Arham yayi yakasa daina kallonta yace "yes your husband is my blood we've been together since childhood, and he means the world to me, so ki kula min da abokina dakyau" dan dagakai tayi ta kalli Waleed kafin ahankali takama hannunshi tarike gam tana kallon face dinshi tace "I was born to do that, I love you so much Doctor na" ganin akwai mutane awajen yasa ahankali yace "thanks" wani iri Arham yaji he just feel inama shine yake da wanan soyayyan, Waleed is the definition of yaran da ake haifa da silver spoon abakin su, Waleed is just surrounded with love ne ta ko'ina, just look at yanda wanan hadaddiyar classic graduate lawyer yarinyar nan kesonshi tama mutu akanshi but yana yanga, infact baima sonta, baima son auren ko kadan, yarinya ga shegen kyau, itama yar masu kudi but yake yanga, he just wish zai sami yarinya haka dazata dinga mutunmai dinan, Salima ne ta katse silent din tace "I think we should go anfara event fa tundazu" fitowa sukayi duka atare, bayan an sanar da isowansu a hall aka kunna music suka shiga cikin kasa ita sai hotuna ake musu, sosai akai event kala kala duk in Ilham zata dagokai saita hada ido da Arham dake kallonta saidai ta sakanmai murmushi ta maida hankalinta kan Waleed, anso sai asuba za'a tashi 1 nayi Waleed kaman zaiyi kuka yakira Arham awaya bai dauka ba, ganin duk yay wani iri yasa Ilham tace "me kakeso baby?" batare daya kalleta ba murya chan kasa yace "nagaji i think atashi" ayanda yay maganan saida yasa har wani lumshe idanu tayi, Waleed is handsome gawasu mayun pink lips dayake dashi dake shinning kaman ka lashe, she can't wait to have a taste of them, kasa cemishi komi tayi sai binshi take da kallo, ganin kiss call dinshi yasa Arham yazo gayamai yayi atashi yagaji bacci yakeji, Arham baimai musu ba ya sanar da dj a kunne, yan abubuwa kadan akayi aka tashi, dudda yanda Waleed keso yaje gida Arham yace mai ba haka akeba shizai raka Amarya gida sanan saisu tafi, yanaji yana gani Arham yasa aka saka Amarya a bayan motansu yasa Waleed din kusada ita sanan yakoma gaba ya shiga ya tukasu, sun danyi nisa da tafiya Ilham ta matsa kusadashi ahankali tareda saka hannunta kan nashi ta kama gam, shiru yamata yana dan lumshe ido kafin daga baya bacci yay nasa ran kwasheshi ya daura kanshi kan kafadarta, wani irin dadine ya kasheta tai dan murmushi tace "haka abokinka keda saurin bacci?" ta glass din gaban motan ya kallesu yay dan murmushi yace "ai zakisha shagwaba, haka Allah ya yishi, mijinki shagwababbe ne" murmushi tayi ta shafa fuskarshi bata sake cewa komiba shima Arham haka har suka kai gaban gidansu, ahankali ta gyaramai kai tareda pecking nashi ta kalli Arham daya bude mata mota tace "good night our blood" murmushi yayi yace "good night our wife" gyadamai kai tayi tawuce yamaida kofan yarufe yana dan satan kallon bayanta, ta shiga gidan su, dakinta tawuce direct inda Salima da wata kawarta suke zaune harsun chanza kaya dansu tun dazu suka iso itakuma dayake ahankali Arham ke gudu saisa basu iso dawuri ba.
[27/09, 11:51] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫
✍️ M SHAKUR
5️⃣
Bathroom tawuce dan shegen fitsari takeji, fitsari tayi sanan ta tube gown din jikinta tayo wanka gabaki daya tasaka bathrobe tafito tana kulle igiyan, zama kusada Salima tayi tana murmushi tace "I am so happy wlh, ina cikin tsananin farin ciki, am getting married to the man dat I love, wai kunga yanda Dr dina yay kyau kuwa" tai dan murmushi tana kallon lallen kafarta kaman mai tunanin wani abu tace "Dr na is so cute and duk mutanen dayake mu'amala dasu haka suke da kyau suma, just look at his best friend, shima yanada kyau wlh, so handsome saida baby na yafishi kyau nesa ba kusa ba" tai murmushi tareda danyin fari da idanu, dariya Salima da dayar kawarsu mai suna Nana sukayi dan is so obvious sonta yafi nashi yawa dat is inma yanason nata kenan, Nana tace "Ilham kinason Dr ki sosai wlh, har yanzu baki bamu labarin shi ba, waye shi a ina kuka hadu?" dagakai tayi tana kallon Pop dakin saikuma ahankali ta kwanta kan gado ta daura kanta ka hannayenta ta sauke ajiyan zuciya tace "Mummy na da Ammi (Maman) Waleed are gud friends very good friends, so su suka hadamu, parents dinmu suka hada auren maman shi na sona sosai, ita batason her only son ya auri any kind of girl saidai girl din da she trust sabida kar a cutar mata da yaro, tana sona sosai and taga nagama karatu na, inada good career ga kyau ga brains, gani yar aminiyarta saisa tace am the best choice for her son, that's that for that" tai dan murmushi taredayin tafi, Salima tace "to bamu labarin Dr" dan juya idanu Ilham tayi tareda gyara kwanciya tace "uhnnn Waleed baida wani much story to tell cus shiba loud person bane, baida hananiya, baida surutu sanan baya keeping friends, Arham shi kadaine abokin shi aduniyan nan" tasake yin shiru sanan tace "bayan su Mummy sun gama kulle kulle su kan zasu hadamu aure, sai wata rana Ammi ta aiko Waleed musamman danya kawo wasu kaya wajen Mummy na, itama Mummy na cus komi plan ne nita tura waje bayan ya iso tace na shigo dashi falo na karbi sakon, ina fita waje, Oh Allah" tai dan shiru sanan tace "wlh I've seen many men, many guys, yara masu kudi nayan gayuma, yaran baze da nile tun ina University but bantaba ganin one like Waleed ba, I saw a very tall full guy fari in complexion, ko kadan baida rama jikinshi acike, yana sanye da cooperate dress da alamu office zashi a ranan, wani farin riga ne ajikinshi da bakin wando yasa wani blue and white necktie, yanada full saje da gemu baki sidik, gemunshi a mugun gyare baida yawa sosai yana kyalli tsabagen gyaran dayaji, lips dinshi pink yirrr kaman zaka taba jini yafito look perfect a face dinshi and moist kaman ya shafa lip balm, gashi da dogon hanci idanunshi manya sosai yanada perfect black eyeballs, giran shi acike bakin kirin, gashin kanshi nada dan yawa ba chan chan ba gashin kanshi na kyalli kaman irin na larabawan nan, he don't really look Nigerian, dana ganshi kasama motsi nayi sai shi daya luradani yacemin cikin sassanyar muryan nan nashi Mummy na nan, Ammi sent me, yanda yake magana ko dole yatafi da imanin kine, yanada broadfull chest, that is it fa, bayan na karbi sakon da sauri mai dakin Mummy na nace Mummy waye wanan yaron, tacemin his name is Dr Waleed Warbai 28yrs of age, only son din Mrs Warbai kawata, yamin ina sonshi cus mamanshi naso tahadani aure dashi ne, wlh ko I was just blushing, I couldn't believe abinda naji bansan lokacin dana fada jikin Mummy ba ina murna dudda tsakanina dashi is just 2yrs ne cus 26 nake shikuma 28 ban damuba dan he looks older dan his age irin yaran yan gayun nanne dasuka ci dadi suka fashe, a hakan ma dan yana gym ne saisa kibanshi baiyi yawaba it looks perfect on him, shikenan aka bani number shi sanan yakanzo once in a while, this boy is rich, his late dad is multi billionaire, babanshi nada companies, yanada company building boat na ruwa, and his father was the first person dayakawo electronic car a Nigeria, baban shi mahaifin shi, that is his grandfather balarabe ne matanshi yar Nigeria saisa Waleed inji Ammi da babanshi yake kama, kanin babanshi daya a duniya yana Ukraine shima kudine dashi sosai but baida yara shima saisa Waleed keda gatan duniya, his uncle nasonshi kaman me, all kudaden da mahaifinshi yabarmai he use them yabude gidan marayu, akwai hospital agidan marayin da nakasassun, akwai school tundaga nursery har secondary kuma duk wanda wish to further yana kaisu University, insuka gama yabasu aiki in sunason suyi aiki gidan marayun yayi in a outside nema yabasu sanan yamusu aure, matan inhar sunada tsayaye yana aurar dasu tun kafin ma su shiga University, as small as Waleed but taimakon dayake ko mahaifina baya irinshi, na auri someone like Waleed na haifama family su magaji nida talauci har lahira saisa dazaran na shiga gwaranni zan dingayi ko Mummy ma haka tafadamin haka zan dinga yi, to shikenan labarin and I can't wait for tommorow muyi aure, can't wait to make luv to my Waleed, shagwabben mijina" dariya duk sukayi haka suka dinga hira har bacci yay awon gaba dasu.
***
Ance rana bata karya saida uwar diya taji kunya, yau asabar dubbannin jama'a ciki harda gwamnoni da representative na shugaban kasa, dan ansan marigayi mahaifin Waleed, sanan har gobe suna business da companonin shi aka shaida daurin aure tsakanin Waleed Warbai da Khadija Ilham Maifanko akan sadaki 3million naira.
Sosai idanunshi sukai jaa sosai, kasa amsa gaisuwan yan uwa da abokan arziki yayi, ga employees dinshi sun cika wurin sunamai Allah ya sanya alheri gyada musu kai kawai yake dan baijin zai iya bude baki yayi magana ba ayanda yakejin kanshi sai Arham dake tayashi karban gaisuwan cikeda fara'a kaman shine ango, ganin kanshi yasoma juyawa yasa kaman an tsikareshi ya mike tsaye hannunshi cikin aljihun Arham hakan yasa da sauri Arham dake magana dawani yajuyo ya kallai, Waleed bai damu da kallon da Arham kemai ba yazaro key mota yay gaba da saurinshi yana tafiya kaman zai tashi sama yakarasa wajen motan su yabude ya shiga mazahnin6direna da sauri rabon dayay tuki da kanshi harya manta, harya tada motan Arham yazo ta wajen glass din yana kallonshi yace "are you crazy x-man? Where do you think u are driving yourself too? Bazaka tsaya ka gama amsan gaisuwan mutane ba zaka gudu kana ango? Banda hakama kaine zaka tuka kanka katuna the last time you drive?" tsayawa yayi kallon Arham for few seconds inyace zai bude baki yamai magana he might cry hakan yasa ya dauke kanshi ya sauke ajiyan zuciya sanan yawani irin fizgan motan yay reverse da sauri Arham ya matsa baya, ganin yanda aka juyo ana kallonsu yasa yadan saki murmushin yake yace "ahhhhm mantuwa ango yayi gift din dazai bama amaryan shi na daurin aure" murmushi duk akayi banda uncle dinshi dayane nan fari fat kaman bature yana sanye da manyan kaya da farin glass a idanu, yataho inda Arham din yake, cike da girmamawa Arham yace "sannu Uncle" cikin fada yace "ya akayi kabarshi yay driving kanshi so kake ka kashemana d'a?" wani irin dukan zuciyan shi maganan Uncle Arham yayi hakan yasa yadago Kanshi ya kalli uncle din ahankali, cikin fushi uncle yace "if u can't take care of our son wats the point of being his friend eh? Wlh bansan shirme mtdww" yaja tsaki sanan yajuya ya kwalama direban bodyguard din Waleed dake chan suna cin abincin su da gudu yataho yace "Allah taimaki yallabai gani" cikin fushi Uncle yajuyo ya kalli Arham din yace "ina yaje?" ahankali kaman wanda yake rashin lpy yace "I think gida yaje" "you think! What an insolence" Uncle yafada cikin bacin rai sanan takalli direba yace "drive home in Waleed nagida call me ka sanar dani, be fast he just left" da sauri direban ya shiga mota yaja shikuma uncle yajuya yakoma wajen friends dinshi akabar Arham shikadai awajen a tsaye idanunshi sunyi jazur, ganin yanda yan wajen ajikinsu ke kallonshi yasa ya kakalo murmushi yamusu yataho inda suke yacigaba da hirada su.
Cikin ikon ubangiji ya iso gida lpy, ta Gate din bayan layi yay parking tareda kashe motan, ahankali ya sauko yana ganin jiri yabude Gate din ya shigo ya shiga flat dinshi bedroom dinshi yawuce direct yawuce bathroom ya shiga kwara uban amai gwanin ban tausayi, saida aman ya tsaya sanan yay flushing aman yabude tap ya kuskure bakinshi tareda wanke fuskan shi yajawo dan gajeren towel dinshi ya shiga goge fuska yana sauke ajiyan zuciya yafito, rage kayan jikinshi yayi jikinshi yadau mugun zafi ahankali yakarasa ya kwanta kan gado sai bacci.
Ahankali yaji ana kiran sunanshi sama sama ta cikin bacci, bude idanunshi yayi kadan ganin fuskar Arham yasa yabude idanun completely ya kallai, kafin ahankali yatashi ya zauna ya jingina bayanshi da bangon gado, zama Arham yayi agefenshi sanan ya fuzar da huci mai zafi kafin yadago kanshi ya kalle Waleed din yace "Waleed" Arham hardly call him da sunanshi saidai ya kirashi da Xman, yanda yakira sunanshi yasa ya kalleshi, anatse Arham yace "today is the last day dazan maka tambayan nan, wlh in bakaban amsaba bazan karabi ta kanka ba am telling you, bansan meke damunka ba, for god sake Waleed u weren't like this before, remember am your blood right, I know all ur worries, nasan anything that has to do with you, tun zancen auren nan naka ka chanza gabaki daya, I know magana dama namaka wahala but banda ni, amman this days harni din da kyar kake kulani, Waleed what is wrong? What's the matter with you? What is bothering you like this talk to me Waleed, talk! " Arham yadaka mai tsawa sosai, hannu yasa da sauri ya yatoshe kunnenshi saiga hawaye sun zubo, da sauri yasa hannu ya share, ganin hawaye akan idanun Waleed yasa jikin Arham yay sanyi ahankali ya matsa kusada shi yatsun shi biyu yakai kan fuskan shi ya dangwalo hawayen dayake kan fuskan shi ya kalli yatsunshi ganin hawaye ne da gaske yasa cikin wata irin muryan mamaki yace "t......tears X-man? Ar.....are you crying?" yay maganan da mugun mamaki dan zai iya cewa rabon dayaga kukan Waleed tun suna yara, cikin wata irin damuwa yace "Waleed wats making you cry like this? Baka rasa ci ba, sha ba, sutura ba, Waleed duk wata jin dadin zaman duniyan nan damuke ciki kanada shi, tari kadai zakayi sai sama da kasa ta kusan hadewa dan kawai asan dalilin dayasa kai tarin, look at your room" yabi ko ina da kallo adakin yace "dakinka ko dakunan 10star hotel albarka, everthing imported, designers kasa kaya mai tsada, kanada mesarati, ferrari, g wagon, brabus, benz, range rover wanan danake magana fa duk na 2020, kaci mai tsada, kahau mai tsada, ka taka mai tsada ka kwanta amai tsada, Waleed babu abinda kanema karasa aduniyan nan, kudi kaman zasu fasa account dinka, inda ace suna magana da naka harda fito zasu dingayi, banga abinda karasa awanan duniyan nan tamaliki yaumin deen ba u are loved banga wanda baya sonka ba, just look at how Ilham take sonka kaman zata mutu sometimes I use to wish inama nine kai dan banga wani abu dazai dinga damuna ba, koma abu nadamu na I can use my money na kauda duk wata matsala ta, money is problem
Book Chapters
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36