Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

you this question also, I think today is the right day, Arham" Waleed yakirashi anatse, zubamai idanu Arham yayi irin ina jinka dinan batare daya amsaba, ahankali Waleed yace "Arham banso kamin karya, tell me please mekake yi da kudi"? Dawani irin sauri har yana neman taran numfashin shi yace "kaman ya menake yi da kudi" dan jim Waleed yayi yana kallonshi saikuma yace "okay lemme do it like this kafahimce ni, blood duk wata dawainiya dazata sa ka kashe kudinka na dauke makashi yet kullum bakada kudi, me kakeyi da kudi"? Wani irin zabura Arham yayi yamike tsaye daga kan kujeran dayake kai yana kallon Waleed din yace "mekake nufi da duk wata dawainiyar dazata sa na kashe kudi ka daukemin ita yet kullum banida kudi, Waleed gori kakemin sabida kana siyama mahaifiyata yar buhun shinkafa duk wata kana kaimata"? Waleed was still seated akan kujeran shi ya girgiza kai yace "uhm'uhn that's not wat I meant Arham, calm down and sit let's talk please, banga abin zafin nanb......" wani irin buga table dinshi Arham yayi da hannu yay kara yace "don't fucking tell me to calm down, on what account zaka dinga tambayana menake da kudi sabida ka daukemin dawainiyar kaina kana saima mamana yar buhun shinkafa da wake, Waleed ni kakema gori sabida kaga Allah bai horemana kaman kuba eh? Ni kake ma gori Waleed, am talking to you kamin shiru are you stupid"? Arham yadakama Waleed tsawa dayasa Waleed yaji ranshi yabaci dan ba'amai tsawa koda yana yaro baima sababa, tashi kawai yayi dan baiso yabiye mai suyi fada yay wajen hanger dayake makala suit dinshi yaja yadauka zai saka, wani irin shan gabanshi Arham yayi da jajayen idanunshi ya kalli Waleed yanuna kanshi da hannu yace "ni kakema gori Waleed, sanan inamaka magana kamin banza ni kake ma gori"? Kasa saka jacket dinma Waleed yayi sabida ihun Arham dayake mai a kunne kaman zai fasamai dodon kunne yamaida jacket din yarike a hannu sanan ya kalli Arham yace "since you are too dumb to understand a simple question dana tambayeka then take it anyhow you wish to take it" yana gama maganan yadau wayanshi daga kan table zai juya yay kofan fita Arham yasha gabanshi yace "ni kakema gori"? cikeda mugun bacin rai da kulewa da maganar Waleed yace "nayi, kai duk abinda kaga dama" kaman amafarki Arham bai wata wata ba ya daurama Waleed wata lafiyayyen mari ata gefen ido dan marin har yadan taba idanunshi na side din dama jikake kau! Idan Waleed yace he was expecting a slap from Arham he is lying, jin saukan mari yayi kawai daga sama baisan lokacin daya saki wayanshi da jacket din dake hannunshi akasa ba suka fadi, wani irin fincikanshi Arham yayi ya bugada bango bayanshi yabada bam, Arham ya shakemai wuya, cikin kunfan baki da mugun tsana yace "sabida rashi da talauci yasa am working under you, yaro dakai u are just 28 inada 35yrs na girmeka da shekaru shidda zaka tsaya kana gayamin magana yanda kaso, daman hausawa sunce yaro da kudi babba yake dawowa, this can not work with me, yau saina koyama hankali, I will teach you a lesson, fight me back now, fight me back" har alokacin Waleed was shocked yama kasa yarda Arham dinshi ke fada dashi haka, ya shakeshi yana neman kashe shi idanunshi sunyi jajir jijiyoyin kanshi sun fito, fuakanshi tai jajir abunku da farin mutum, ahankali ya iya yataba hannun Arham dake wuyanshi muryanshi bata fita sosai yace "u.....are....hurt.....ing me blood.....am....am.....my....my.....breath" yay maganan about to die amman Arham baida alamun sakinshi saima kara shakeshi dayayi yace "I said fight me, fight me mana, I want you to fight me dan Allah inka isa, kai fada dani kaga yanda zan baka kashi, na farfashe maka wanan bakin dakake min gori dashi kan kasayama Mahaifiyata wanan shegen tsukukun gidan kaman gidan kiwon kyankyasai, da shegiyar akurkan motar nan, inda don Allah kakeyi da tikeken gida zaka saya mata irin naku mansion, mota mai numfashi bata manoma ba, yau saina nuna maka kudin ka bazai iya taimakonka a hannunna ba, I will deal with you yau Waleed, wlh saikai fada dani zan kyaleka na rantse maka" daidai lokacin akai knocking kofar office dinshi, sake shakeshi yayi to the extend this time idanunshi sun soma juyawa gashi yakimai komi dan he can't raise his hand on his friend or hurt him in anyway ba, da kyar hannunshi ya iya komawa baya dashi yatataba flower verse din dake kan table dinshi ya kabar dashi kasa yay kara akasa sabida wanda ke waje ke knocking kofarshi yaji ya shigo, jin karan flower verse yasa Mama Iyami tace "subhallahi karan menene wanan" ta murza handle din kofan kawai ta shigo ciki, ganin yanda Arham ya shake Waleed yasa da sauri tai kansu yace "Mr Arham innalillahi wa innailaihi raji'un, wats happening here? Meke faruwa haka? Kaida abokin ka, let him go, sakkashi kaga" ta shiga kokarin fincike hannun Arham daga wuyan Waleed, cikin fushi Arham yace "wlh bazan sakeshi ba saiyay fada dani, sainaga uban karfin dayike dashi dayake juyani yanda yakeso sabida yaga yanada kudi dan ubanshi" ganin yanda Arham ya harzuka Waleed na neman mutuwa a hannunshi yasa tafita daga office din da gudu ta kurma uban ihu. "jama'a kuzo kutaima keni, Dr Waleed Warbai and Mr Arham are fighting, please helppppp" ihunta gabaki daya yadauki gidan marayun, da gudu wasu staff din Waleed da yaran gidan marayun damasu shara, gardeners da waye da waye aka shigo office dinshi da gudu, Nura dawasu maza hudune suka fizge Arham, suka jashi baya Waleed kuma yay baya zai zube wasu ma'aikatan suka tareshi, da gudu Iyami tafashe da kuka tace "innalillahi is sir alive jama'a?" wani ma'aikaci ne mai suna Auwal yace "he's alive but sai ankaishi asibiti" da sauri suka fita dashi daga office din, Mama Iyami tajuya ta kalli Arham dake huci yana tsaye ya fizge kanshi daga rikon da akamai tace "Mr Arham meya hadaka fada da abokin ka eh, dan uwanka fa, blood naji kuna kiran junanku, Mr Arham meya hadaku dashi" cikin wani irin fushi Arham yace "kije ki tambaye shi mana, dayake shi ogan kine bazaki iyaba shine yabaki aiki, yana baki na abinci bazaki iya tambayanshi ba, amman dayake ni kin rainani dole kitasani agaba kina tambaya, matsiyatan mutane, masuyin boyi boyi dan abasu kudi, fatararru kawai" yay maganan fuuu yafita daga office din ma'aikatan kowa yabishi da kallo ana mamakin tome yahada su tsawon shekaru nawa ba'a tabajin kansu ba saiyau, motarshi ya shige yaja motar yawuce yabar orphanage din.







Staff, ma'aikata, yaran gidan marayun aka fiffito aka taru awaje, daman ance bad news yafi yanda wuri nanda nan aka cika ko'ina, aka cika gaban clinic da saida Dr Kemi da Dr Ayo suka kira security gate biyu sukazo, akasa kowa yakoma various places dinsu, Baba Mani ne kawai da Mama Iyami aka bari suka shiga asibitin har zuwa dakin da aka kwantar dashi likitoci akanshi ba'a bari sun shiga ciki ba, fuskarshi tai mugun jan da saita baka tsoro, gefen idanunshi na dama ya kumbura dan hardan tsagewa yayi jini yadan fito, kasa daurewa Mama Iyami tayi ta fashe da kuka a rayuwa tanason Waleed, bata taba haihuwa ba, mijinta yarasu, an koreta gidan haya yazo batada inda take kwana, abakin titi takoma tana bara tana tara kudin datake samu danta kama haya, wata rana tana cikin baranta taga anyi parking, Waleed yafito kai tsaye yace mata mesa kike bara Mama, tace banda kowa, mijina yarasu, banda y'aya Allah baitaba bani haihuwa ba, ankoreni agidan haya, bara nake natara kudi nasami matsugunni, budan bakinshi bazaki kara baraba, sanan yajuya yay wajen motarshi yace zomuje, gabanta nafaduwa amman hakanan taji zuciyarta nacemata tabishi, motar ta shiga, yana zaune agefenta ga basket da alamun abinci ne aka dafamai agida, dauka yayi duka basket din yabata yace kici, budewa tayi ta shigaci kaman bata tabacin abinci, yakaita gidan marayun shi, yakaita asibitin shi yasa tai wanka, aka kawo mata kayan asibiti tasaka yadubata tsaf bata dawani ciwo sai maleria yay treating nata, sanan dakanshi yakaita girls hostel yabata daki na musamman dake dauke da komi sanan yace "aikinta kawai ta dinga kulamai da activities din yaran nan, she's in charge anan section din, zai dinga biyanta duk wata, sanan yasa akayo mata dinkunan kaya masu kyau aka kawo mata, tundaga ranan kulada ita yake to the extend har Ammi tasani tanada number ta, Ammi data ambata aranta yasa taciro wayarta ta shiga neman number Ammi tana kuka sosai, kaman wayan zata katse sanan Ammi ta dauki wayan, cikin kuka Mama Iyami tace "Allah yataimaki Hajiya amin afuwa hala ban kira alokacin daya kamata ba, amman dolece tasa nakira" takara wani irin rushewa da kuka dayasa gaban Ammi ya shiga dukan uku uku tama kasa magana tsabagen faduwan gaba dan tanada hawan jini, Mama Iyami cikin kuka tace "Hajiya kome kikeyi kibarshi kizo ba'asan ko karshen ne yazo ba, wayyo Allah na Hajiya" takara kecewa da kuka dayasa Ammi bakinta yafara motsi tana kokarin furta magana takasa dakyar tana wani irin nishi tace "k.....kar.....shen wane.... Iya.....mi"? Cikin wani irin mahaukacin kuka kaman wacce akama mutuwa Mama Iyami tace "karshen Dr Waleed Hajiya, Mr Arham yama Dr Waleed shegen duka, yanzu haka Dr Waleed baisan inda kanshi yakeba, likitocin mu gabaki daya na kanshi baisan inda kanshi yakeba ana kokarin ceto rayuwanshi, saisa nace kizo idan ma cikanwan ce yacika agaban ki, ai Mr Arham bai kyauta ba da kyar muka kwaci Dr Waleed a hannunshi Hajiya, dan Allah kizo yanzu koda karshen ce yayi ta a hannunki, wayyo Allah na Dr Waleed" tarushe dawani rikitaccen kuka tana katse wayan, majina shabe shabe.



Wani irin baya Ammi tayi zata zube akasa daidai lokacin mai aikinta tafito daga kitchen dauke da katuwan kulan abinci, wani irin sakin kulan tayi akasa tai kan Ammi da gudu kafin Ammi ta zube ta tareta tareda ihu tace "Hajiyaaa!" duk masifar Ammi tana bala'in sonta dan tayi aiki a gidaje da dama bata tabayin aiki agidan dataji dadi irin na Ammi ba, ganin Ammi ta sume yasa ta kuma ihu. "Mai gadi, direba, duk wanda yake awaje ya shigo ku taimake ni, Hajiya ta suma" da gudu ma'aikatan gidan suka shigo, su mai gadi naganin Hajiya assume sukai kitchen suka fitoda ruwa agora yayyafa mata ruwa sukayi tawani irin sauke ajiyan zuciya tare da bude idanunta, ahankali take kallonsu one by one, kafin ahankali tace "ku kaini wurin Waleed gida a orphanage, dan Allah ku kaini wurin Waleed dina a orphanage".
[14/10, 18:22] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫





✍️ M SHAKUR





2️⃣8️⃣






Direba ne yace "Waleed kikeson gani Hajiya"? Gyadamai kai tayi hakan yasa yarike ma Ammi hannu yar aikin ma tarike ta suka dagata da kyar ta iya tsayuwa a feet dinta, mai gadi yacema yar aikin. "kawo mata mayafinta da jaka da takalmi" da gudu yar aikin tai sama dakinta ta shiga tadauko mata hadadden mayafinta da takalmin ta da jaka ta sauko kasa yafama Ammi mayafin tayi akan tsadadden lace din dake jikinta sanan tasa takalmin, ta karbi jakan dan tasoma dawowa daidai sukai waje da ita motar ta direba yabude ta shiga baya ta zauna suka rufe ta sanan ya shiga gaba yatada motar gateman yabude gate suka fice, suna ficewa motar Mom na sawo kai tabi motar Ammi da kallo daya wuceta da gudu yar aikin tafita waje taje wajen motar Mom cikeda girmamawa tace "sannu da zuwa Mom, Mom please jibi Hajiya, ankirata awaya bansan me aka fadi mataba amman saida ta sume kuma yayyafa mata ruwa ta farfado tace a kaita wajen Waleed agidan marayu yanzu sun tafi, please kibata I don't want wani abu ya saman mini Hajiya" cikeda tashi hankali Mom tace "karki damu bari na bita" kwana tayi da sauri tabi bayan Ammi itama.



Motar Ammi na zuwa gate kasancewan security sun santa suka fara ihu. "Hajiya Don come Hajiya Don come, open the gate" sukahau jin dadi dan bata cika zuwa gidan marayun ba but duk randa zatazo ruwan kudi take musu, dan yake ta musu ta saka hannunta cikin jakan da yar aikinta tabata rapas din yan dubu sababbi ta dauko guda biyu ta mikama babban su, ihu sukahau yi suna mata godiya direba yaja motar ciki, kafin su rufe gate saiga second Mom, dadi kaman yau ana baki itama kyautan tamusu mai tsoka sanan ta shiga ciki, har gaban office din Waleed inda yake parking motarshi direba yay parking, tsabagen yanda jikin Ammi ke rawa kasa bude kofan tayi saida direba yafito yabude mata tasa kafafunta tafito tana fitowa motar Mom na sawo kai wajen, parking tayo tafito da sauri tai wajen yayanta data tsaya chak tana kallonta tace "Adda meya faru?" kasa magana Ammi tayi tajuya kawai Mom biyeda ita, itama Mom ganin yanda mutane suka taru a tsakar wajen yasa taji gabanta yafara faduwa, ana ganinsu aka fara gaishe dasu. "Barka da zuwa Hajiya, barka da zuwa Hajiya" kasa amsa kowa sukayi Ammi tai gaban asibitin daidai Mama Iyami dake kuka sosai tafito tawani irin zube agaban Ammi tace "Hajiya ku shiga yana ciki, wayyo Allah na mun shiga uku, gatanmu na kwance a asibiti raga raga, rai na hannun Allah" tsallaketa Ammi tayi tasa hannu tabude kofan ta shiga ciki Mom biyeda ita, Nurses din data gani charko charko tsaye agaban reception din tawani irin dakama tsawa. "kuna kallo na bazaku gayamin inda d'ana yakeba" arude duka nurses din suka mata pointing dakin da aka rubuta emergency asama, yanda Ammi ke ihu yasa Mom takama mata kafadar Ammi alamun tai calming down, kabar da hannunta Ammi tayi tai hanyar dakin, tana zuwa batai watawataba tabude kofan tasa kanta ciki, Dr Kemi da Dr Ayo ne akan Waleed din dahar lokacin bai farfado ba, ancire mai riga da singlet, dagashi sai dogon wandon jikinshi da belt anmai dauri akafada ta wajen hammata an hade da hannunshi kaman wanda ya karye, fuskarshi tai jajajir, gefen idon damanshi dama idanun duk sun kumbura, gefen bakinshi ya tsage yanadan jini tsabagen marin dayasha na Arham, wuyan shi tsabagen matsan da riga da necktie din wuyanshi sukamai har ciwo suka jinmai jini nafita wuyan yay jajir kaman an zaneshi da bulalan inji.

Hawaye ne suka cika idanun Ammi takasa rikesu suka shiga zubowa har zafin dukan takeji ajikinta tsabagen tashin hankali, tunda ta haifi danta incident makamancin hakama baitaba samun dantaba, daidai Dr Ayo yagama gyara jinin wuyan yajuyo ganin Maman Waleed yanda jikinta ke rawa tana kuka yasa yace "calm down ma, bawani abu babba bane kashin kafadarshi tadan goce ta sanadiyan buga bayanshi da akayi da bango, saikuma bruises din wuyan nan dakuma na ido, dan jini yataru acikin idanunshi but with time zai washe, calm down Hajiya, nan da dan anjima kadan danki zai farfado" da sauri Dr Kemi data karaso wurinsu itama ta gyada kai tace "yes ma calm down please Ma" sukabi ta gefensu suka fita daga dakin, wani irin juyowa Ammi tayi cikeda wutan bala'i, da kunan rai da tsantsan bakin ciki ta kalli Mom sanan tanuna mata Waleed dake kwance kan gado da hannu tace "kinga abinda Arham yama d'ana ko? Kinga abinda Arham yama d'ana ko, kina gani daiko, yaron da dama kece tun day one kikai approving friendship dinshi da yaron, left to me yarona ya rayu ahaka baida aboki I his mother can be his best friend and his everthing aman kika nace saina barsu sunyi abota, dan haka karma naji kinhanani dauka hukunci dan wlh wlh bazan yarda ba" tai maganan tana dauko wayanta daga cikin jaka da sauri Mom tace "Adda kinga calm down yanda kike tafarfasan nan bai kamata kidau hukunci ba, dan Allah kiyakuri Adda" da wayan hannunta tanuna Mom tace "Zainab ki shiga taitayin ki, na rantse miki da Allah yanda Arham ya jima d'ana rauni ko kwana baza'ai ba shima sai anjimai, wlh saiyasan ya buganmini d'a, shidan ubanshi ubanwa yataba dukanshi haka? Waleed dakoni bantaba daga hannu na daka bane wani kato zai dokanmin wlh wlh saina ramamai, wlh kuwa kinji na rantse miki" Ammi tai maganan tana bude kofa tafita daga dakin tana dailing number Maman Arham.






Ringing daya Mama tai picking call din ganin kira daga Ammin Waleed, kafin ma Ammi tai magana cikeda fara'a tace "Assalamu Alaykum, barka da yamma Hajiya" ko amsa sallamarta Ammi batayi ba cikeda bacin rai tace " please kome kikeyi kibarshi kisamemu a orphanage na Waleed yanzun nan kizo, ina jiranki yanzun nan" tana kaiwa nan ta katse wayan jikinta na vibrating, Mom ma takasa cewa komi tazama yar kallo matsalan yayarta kenan intai fushi batada hankali, kuma bataji bata gani barin ma when it comes to Waleed matter.


Gaban Mama ne ya yanke lokaci guda ya fadi, tunda tasan Ammi tsawon shekaru kenan bata taba tamata irin wanan kiran ba saiyau, tomeya faru? Allah yasa alkhairi ne, ahankali tafara karanto innalillahi wa innailaihi raji'un kota samu natsuwa cikin zuciyarta, dan batada natsuwa ko kadan sabida zuciyarta wani irin mummunan faduwa kawai yake.





Hijabi kawai ta dauka ta zira akan kayan dake jikinta, ta kwalama diyar kanwanta kira tace "nafita yar albarka saina dawo, ki daura abincin dare" daga ciki yarinyar ta amsa da "saikin dawo Mama" fita tayi daga dakin ta kwalama driban ta kira yafito, mota ta shiga tace yakaita orphanage dinsu Waleed ya amsa mata da to, yatada motar yafita daga gidan.


Ko cikakken 15min direban bai daukaba yakaita orphanage din, tana fadin mahaifiyar Arham ce ita aka barta ta shiga dan ta taba zuwa sau daya suka shiga ciki, kirjinta bai kara faduwaba sai dataga ma'aikatan orphanage din carko carko a tsaitsaye ana tattaunawa agaban clinic, parking direba yayi tabude kofa tafito daga motar kirjinta na bugawa, wayarta dake hannunta taciro tanemo layin Arham ta hau kiranshi danta tambayeshi maiya faru, wani abu yafaru ne amman har wayan ya katse bai dauka ba, hakan yasa tai dialing number Ammi, ringing daya Ammi ta dauka, ahankali Mama tace "Hajiya na iso" cikin muryan Ammi dabata fita sosai tace "kishigo asibitin muna emergency" shine kawai abunda Ammi tafadi mata ta katse wayan, sosai Mama taji kirjinta na bugawa yanda Ammi kemata magana, hakan yasa ta daga kafarta tana kallon mutane ta shiga tafiya harta karasa gaban asibitin tasa hannu ta bude kofar ta shiga ciki, kasan cewan emergency din asibiti bata boyuwa yasa tana ganin dakin tagane batare datama tambayi nurses din dake wurin ba tai wajen kofan, ahankali ta murza hannun kofan dakin tashiga ciki, Ammi da Mom tagani zazzaune, Mom kan kujera Ammi kuma kan gado gefen kafar Waleed, Waleed kuma kwance kan gadon asibiti, ansa mishi drip, fuskarshi tai jajir ta kumbura wuyanshi ma haka, hannunshi adaure daurewan irin na karaya dinan, wani irin mummunan faduwa gabanta yayi karfin hali tayi tadaga kafarta ta karaso cikin dakin ta tsaya gefen Waleed, bakinta har rawa yake tace "Ha....Hajiya meya sami Waleed? Meya faru? Meyasame shi"? muryanta na breaking sosai tayi maganar hankalinta a mugun tashe, dagokai Ammi tayi tazuba mata jajayen idanunta sanan ta tashi daga kan gadon tace "biyoni" da sauri Mom ta tashi tana girgiza ma yayarta kai amman Ammi ta dauke kai kaman bata ganta ba tabude kofa tafita Mama biyeda ita, itama Mom tabisu wajen, tsayawa sukayi a reception premises din cikin fushi Ammi tamata pointing dakin da Waleed yake ciki tace "wlh mutuncin ki danake ganine yasa nakiraki dan kizo kiga abinda yafaru da idanun ki, kinga Waleed dina, kinga yanda yake akwance agadon asibiti, kinga yanda yadawo, dan iskan danki ne ya mishi haka, Arham ne yama Waleed dina haka, jibi yanda yama d'ana dukan dakoni dana tsugunna na haifeshi bantaba mai irinshi ba, kitayani tambayan Arham da ina labo yazo yatayani nakudar d'ana ne dazai kamamin shi ya daddaka haka"? mamaki ne ya mugun cika Mama kaman wacce ke koyan magana tadafa kirjinta tace "Arham! " tana kwalalo idanunta waje tsabagen mamaki, cikeda masifa Ammi tace "duk abunda Waleed yama Arham da abunda zai saka mishi kenan, Waleed ko agogo nasaimai bayi karba saina sayo biyu nashi dana Arham, komi shida Arham, amman yau Arham ne zai kamashi yama wanan shegen dukan toh wallahi bazan yarda ba, wlh, bazanji kunyarki na cuci kaina ba, wlh wlh bazan yarda ba yanda yama yaron nan shegen dukan nan sai shima anmai irin ta, mai rabani da Arham sai Allah don saina yagashi, saina sa anmishi x10 abunda yama Waleed wallahi wallahi bazan yarda ba" Mom dai batace komai ba kuma batayi yunkurin hana Ammi fadan ba saboda zata iya komawa kanta, ita kanta abin ya daure mata kai har lokacin yanda Arham yakama Waleed ya daka haka. Numfasawa Mama tayi ta goge hawayen daya zubo mata tace "Hajiya kima Arham kome kikaga dama, karki barshi kisa shima amishi fin haka, fin dukan dayama Waleed ma dan abinda yayi bai daceba nabaki goyon bayan nan dan inbama kisa amai hukunci ba ni wlh sainasa" wayan dake hannun Ammi tabude takira inspector general of police na tafada mishi komai sannan tace mishi atabbatar ankarya ma Arham hannu da kafa kafin dare da toture na police, tana katse wayan ta shiga turama inspector address din gidansu Arham.
[14/10, 20:18] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫





✍️ M SHAKUR





2️⃣9️⃣





Hayaniya da zata iya cewa tunda take a asibitin bata tabajin irinshi ba, hayaniyan ya mugun cika mata kunne yasa tabude idanunta ahankali tana kallon dakin, idanunta sunmata shegen nauyi sabida bacci bai isheta ba, sosai kirjinta taji yana wani irin faduwa, ward din datake gabaki daya ta kalla babu kowa cikin ward din sai ita kadai dake kwance akan gadon an lullubeta da bargo sanan anmata parking gashinta gabaki daya anyi mata parking na ponytail, ihu dawani irin masifa dataji yana sauka akan kunnenta yasa ta yaye bargon jikinta ta tashi zaune dagakan gadon tana kalle kallen dakin, ihu da hayaniya da masifan da akeyi jitake kaman a brain dinta akeyi, sakkowa tayi dagakan gadon tazira pink slippers dinta dake wajen sanan tadau Teddy dinta ta kankameshi akirjinta ta shiga tafiya ahankali kaman ana kiranta, hannu tasa tabude kofar dakin datake tafito tana tafiya dogon jelar gashinta na lilo tana kankame da Teddy ta kaganta kaman kasace ta kagudu, tai bala'in kyau doguwan yarinya da ita, batada wani kiba tana sanye da gown din asibiti daya wuce guiwanta da kadan, batada wani cikan kirji sosai, kirjinta moderate yan daidai irin na yaran larabawan nan, kanta an mata parking an daure da ribbon gashin na lilo, tundaga nesa take hango su Ammi, Mama da Mom na hayaniya dayasa ta tsorata tasake kankame Teddy gam gam idanunta na kawo kwalla dan tsoro taji sun bata hakan yasa ta shiga waige waige tana neman Waleed, fitowa tayi daga corridor ta shiga tafiyanta kaman bana mutum ba a reception din su Mom ko kadan basu lurada itaba, tunawa da ranan Waleed yayi kofa da ita yafita da ita yasa tai wajen kofan da sauri tana cikin tafiya kaman ance ta kalli glass din kofar emergency ta hango Waleed kwance kan gado fuskarshi a kumbure yasa tai dakin da sauri, hannu tasa tabude kofan ta shiga duksu Ammi basu lurada itaba, maida kofar tayi tarufe, ganin ciwo ajikinshi yasa tawani irin saki Teddy ta akasa tai kanshi da sauri, hannayenta tadaura kan cikinshi tabude bakinta tana kokarin ma magana takasa sai kawai tasaki kuka sosai tahau jijjigashi, amman bai motsa ba, kai hannunta tayi ta daura kan gefen idanunshi daya kumbura suntum ta taba tana kuka sosai tanaso tai magana tama kasa, bama tasan sunanshi

Please Login or Register in order to submit comment