Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

no no am disappointed and heart broken Osijoban" Ammi tafada kaman zatai kuka, cikin wani irin calm voice vice president yace "listen to me Hajiya, wlh ina shirin kiranki kenan kiranki ya shigo wayana, as am talking to you now yanzun nan case dinan ya shigo office dina, Ministry of Women suke incharge of orphanage sunada wanan ikon su kulle duk wani gidan marayu dake harka mara kyau, danaga gidan marayun d'ana ne Waleed raina saida yabaci, namasa acema Minister inason ganinta yau yau dinan bama gobe ba, and I will promise you one thing, kibani lokaci kalilan sabida dole ayi bincike bazan iya kawai nace baza'ayi binciken ba, amman kibani nan da 30days namiki alkawarin zan budemai gidan marayun shi, da ace nasan kan case din kafin su yanke hukuncin nan dana hana amman sai yanzu nake sani, I will do everything in my power nabude mai gidan marayun nan for now ki kulada shi kinji Hajiya, take care okay, sai gobe" ahankali Ammi tacire wayan daga kunnenta ta katse sanan ta ijiye tanaso takira Maman Arham amman saitaga enough sunma kansu but wlh tayi alkawarin zatai maganin Arham, tana cikin tunanin Mom tabude kofa 5a shigo tana rikeda hadaddiyan jaka tayi kyau sosai tana ganin idanun Ammi tagane da wani abu da sauri ta ijiye jakanta kan centre table takaraso kan kujeran da Ammi ke zaune da sauri ta zauna takai hannunta kan wuyan Ammi tace "Adda bakida lafiya ne eh? Maisa idanunki sukai ja haka kaman kinyi kuka"? Ajiyan zuciya Ammi ta sauke tace "idan da zanga Arham yanzu zan iya shakeshi sainaga yana gab da shurawa zan sakeshi, an rufema Waleed gidan marayunshi! Da sauri Mom tace "what" gyadamata kai Ammi tayi tana cijan lips tace "not just that yahada ma d'ana shairi kala kala, ciki harda yay raping yan mata guda 8, can you believe yaran sun fito sunyi confessing wai Waleed yay raping dinsu da gaske agaban kowa harda kuka" ahankali Mom tace "innalillahi wa innailaihi raji'un" ahankali Ammi tana wani irin kallon Mom tace "ance Waleed na saida yara, yana trafficking yaran gidan marayun and maltreatment, Waleed told me an kwashe yaran an maida su gidan marayun Arham shima wai yabude gidan marayunshi" kasa magana Mom tayi wanan lokacin sai







Kallon Ammi take jikinta yay morethan sanyi, cikin wani irin yanayi Ammi tace "ban taba son abotan shi da yaron nan ba daidai da sau daya, kullum sani kike nadinga ma Arham dariya tunda d'ana nason shi amman ban iyawa, kaman Allah ya nunamin nan gaba zai yaudari d'ana ne, Arham ya yaudari Waleed bakadan ba, he uses my child weakness against him, he cheated my son, ya yaudari yarona" tai maganan tana girgiza kai, ahankali Mom tamika hannunta takama hannun Ammi tace "Ammi listen to me, nasan halinki sosai, I know yanzu haka zuciyanki na kitsa miki abubuwa da dama, I want you to calm down Ammi, ba'a rama mugunta da mugunta, ba'a rama cuta da cuta, nasan yanzu haka duk inda Arham yake yana tunanin bama hakaba yana expecting zuwanmu for revenge ko rashin mutunci, Ammi kinajina please wanan karan ki sauraran, tunda dai Allah ya nuna mana wayeshi, sanan Allah yabude mana ido harda da Waleed munsan waye Arham din mubarshi da Allah, kome yama Waleed yama kanshi, ni to me da Waleed ma yahakura da gidan marayun dudda passion dinshi ne yana ma mahaifinshi ne but kawai yakoma normal hospital yafara aikinshi still lada zaikai ga Abba, yabar Arham da halinshi, yana kanshi yaci amanar kanshi, ya manta dashi da abinda yamai and move on, ga yaron shi chan, jibi suna yakamata yaje yagansu kiyakuri Adda na" shiru Ammi tayi tana kallon Mom ko kadan batason ta hakura tanason ta gwadama Arham ba'a taba mata yaro a zauna lpy amman kuma tana tunanin maganganun Mom, wani irin ajiyan zuciya ta sauke ya jingina da kujera ta lumshe ido takasa daina tunanin abinda Arham yama Waleed, takasa daina tunanin yanzu Waleed baida gidan marayu yanzu Arham ne mai gidan marayu da yaran gidan marayunshi. Ajiyan zuciyan takara saukewa hakan yasa ahankali Mon ta rungumeta tace "ya isa Adda I know what you are going through is okay, kiyakuri Allah natare da masu hakuri duk wanda ya cuceka kanshi ya cuta Adda so kibarshi da halinshi" haka Mkm ta dinga bama Ammi baki harta saukko sosai, suna zaune nan akasa sukaji anbude kofar dakinta daga sama da sauri Ammi da Mom suka daga kansu, Waleed ne yafito idanunshi sun kumbura suntum da sauri Ammi tai hanyar stairs din tace "Son katashi" tai maganan tana mika hannunta tarikeshi ahankali tace "katashi Waleed" gyadamata kai Waleed yayi yana kallon Mom dayagani biyeda Ammi tana kallonshi murmushi ya sakin mata yace "Mom kinzo" gyadamata kai tayi ahankali tace "nazo Dan Yaro na" ahankali yake saukowa daga stairs din tareda Ammi, murya chan kasa yace "Mom yunwa nakeji" Ammi jitayi kuka yazo mata tuntuni fushi take dashi tasan baya wani cin abinci yan kwanakin nan tunda yafadi da bakinshi cewa yunwa yakeji dat means yaji yunwa sosai dan Waleed bayacin abinci sosai, muryan Ammi na rawa sosai tace "sh.....shiga kitchen ki dafamai abin.....abin....d....yakes....." kasa karasa maganan tayi saikuma tafashe dawani irin kuka Ammi tayi da sauri tasaki hannun Waleed zata koma sama dan batason yaga tana kuka rike mata hannu yayi gam ahankali yace "Ammi" fadawa jikinshi tayi tasaki kuka tace "Waleed I am sorry, nima I abandon you jibi yanda kakejin yunwa eh, you have been going through alot Waleed wlh ban kula dakai yanda yakamata ba inda nayi da non of this would have happen to you" girgizama Ammi kai yayi yadagota share mata fuska yayi yace "shiiii Ammi don't cry, idan kina kuka I will break down Ammi, you are my strength, please kidena kuka if anything happen to you bazan yafema kaina ba, stop crying kinji Ammi na" gyadamai kai tayi tana kara share fuskarta, ahankali tace "Arham hurt you Waleed" hannun Ammi yarike yace "Ammi kidena maganan Arham, abinda yamin hurt me deep but such is life nayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau, please ku manta da komi kima dena kiramin sunan shi, I want to forget everything and move on Ammi, kinji" gyadama Waleed kai tayi, Waleed yakama hannunta sukai dinning, Mom kuma ta share gajeren hawayen daya zubo mata tai kitchen, spaghetti kawai ta dafa musu hadadden gaske, sosai Waleed yaci yanuna ma Ammi babu abinda ke damunshi duddan karsu damu itada Mom, saida yaci ya koshi sanan yatashi yace "bari naje nai wanka" murmushi Ammi tayi tace "ka shirya gabaki daya kawai sai muje muga Ilham da Baby mukai musu kayan suna ko" gyadamata kai yayi kawai yawuce yafita, duk suka bishi da kallo.



Flat dinshi ya shiga ya maida kofan yarufe bedroom dinshi ya shiga ya zauna akan gado yanzu ne komi yake kara dawomai fresh, kaman zai fashe da kuka yakeji, wani irin ciwo yakeji da bazai iya misiltawa ba, baison yana tunanin Arham ne yay mishi all this abubuwan saiya kawar da tunanin kawai dai yasan yarabu dashi, tashi yayi da kyar ya shiga bayi wanka yayi yafito ya shirya cikin wata Ash color shadda gizna datamai bala'in kyau kaman bashine ke cikin matsala ba, turare ya feshe kanshi dashi sanan yadau dark shade yasaka dan idanunshi sunyi ja, yadau wallet dinshi yafito, bude kofa yayi yafito ahankali yake tafiya haryay wajen da motarshi take a pake ya kwalama Ammi kira da Mom. "Ammi, Mom kufito am outside" yay maganan yana juyawa ya kalli gate jin anyi horn gateman yafito da gudu yana bude gate din, wata brand new ferrari ne yaga ta shigo compound din da baima iya hango na cikin motar glass din motar is tinted, dawani irin gudu mahaukacin motar ta taho harsaida gateman yace "kai" saura kiris motar ta buge Waleed a inda yake tsaye amman ko matsawa baiyiba sabida hakanan ranshi ya fadimai Arham ne, daga kofar akayi Waleed na kallon kofar daga inda yake, kashe motar akayi aka sawo kafa akasa, kafanshi na sanye da wani tomford mai bala'in tsada sanan yafito daga cikin motar, Arham ne yana sanye dawasu hadaddun suit ajikinshi baki idanunshi sanye da bakin glasses yana kallon Waleed yana wani irin murmushi sanan yafara taku daidai yana tahowa gaban Waleed din daya tsareshi da ido yazo har gabanshi ya tsaya yace "call me Mr Arham Abdallah CEO of Arham jikan Malamai orphanage home and home of the disables, Mr Waleed I heard what happen to your orphanage saisa nazo nan, I come to offer you a job agidan marayuna".




[23/10, 07:45] M Shakur: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_💫






✍️ M SHAKUR








3️⃣8️⃣




Dan murmushi yasake yi yakai hannunshi ya zare bakin glass din kan idanunshi ya kalli Waleed din yace "am willing to offer you a Nani job a boys section dina, idan irin kananun yaran nan dabasu iya magana ba sunyi kashi ko fitsari ajiki saika wanke musu, am ready to pay you 100k monthly for just that Waleed" daidai lokacin Mom da Ammi dasukaci gayu sosai sun fito yar aikin Mom biyedasu takwaso wasu hadaddun kaya dazasu kaima Ilham, hango Arham yasa da sauri Ammi tace "Arham!" juyowa Arham yayi yazuba mata idanu da sauri Ammi tayi wurin Mom biyeda ita tana zuwa ta tsaya kusada Waleed sanan ta kalli Arham din cikin fushi tace "how dare you step into my house with those your filty legs, ubanme kazoyimin agidana" wani irin kallon Ammi yayi sanan ya kalli Mom kafin yatabe baki ya nuna mata Waleed da hannu yace "nazo nabama danki aikin Nani ne idan yanaso agidan marayu na" wani irin sake handbag Ammi tayi akasa ta chakumo rigan Arham tace "how dare you Arham? Kasa an rufemai gidan marayu har kanada gut din shigowa gidan nan eh? How dare you waye kai? Kai dinan waye? Uban waye ubanka waye ya tsaya maka, kasan waye Waleed kuwa? Dan kasa anrufe gidan marayun shi sai me? Bari kaji yanzu haka Waleed nada kudin dazai iya gina gidan marayu dari inyaso, d'ana baida lokacin ka, baka gabanshi yanzu, yabarka har, so I expect you to do dsame stay out of my sons way inba hakaba Arham zan koyamaka hankali wlh" tai maganan tana sakinshi ta tureshi dan murmushi Arham yayi yasa hannu ya kakkabe kwalan shi yace "my expensive suit, anyway is fine" ya kalli Waleed yace "katuna abinda nataba fada maka kwanakin baya Waleed?" wani irin murmushi yayi batare daya kalli Ammi ba yace "nasan ka manta, lemme remind you, Waleed nafadi maka cewa duk abinda kaci sainaci, duk abinda kasaka saina saka" yanuna mai suit din jikinshi dan irin wanda Waleed yake sakawane masu tsada, yace "duk abinda kahau sainahau Waleed" yanuna mai motar sanan yace "duk matakin daka tsaya wlh saina tsaya, meet Arham the newest CEO of orphanage home how does that sound a kunnuwan ku" gate Mom tanuna mihsi tace "munji Arham kayi gidan marayu and muna maka fatan alkhairi the gate is over there kawuce kabar mana gida" girgixa mata kai yayi yace "a'a Hajiya bangama da danku ba tukunna" ya kalli Waleed yace "not all those orphanage student are in my orphanage, kasan kuma wanake cewa nabaka awa uku kasa wanan specific one din dakasan akanta nake magana kasa amaidata gidan marayu na dan ina bukatan ta if not things will get dirty yaro".





"get out butulu kawai, leave my house kafin ka kirga uku matsiyaci dan gidan talakawa," kallon Ammi yayi saikuma ya kyalkyace da dariya yadaga hannu sama cikeda isgilanci yace "I come in peace, you seems angry menene wai? Bari nabar miki gidanki kinsan they can't arrest newest CEO" wajen motarshi yayi ya shiga sanan yasake leko da kanshi ta window mota ya kalli Waleed yace "don't forget my offer and maganan dana maka Waleed I need that girl in my orphanage nabaka 3hrs" yatada motarshi yay reverse yawuce yabar gidan, juyowa Ammi tayi zata rufe Waleed da fada dataga baicema Arham uppan ba Mom ta girgixa mata kai alamun kartayi sanan tace "mutafi Waleed" juyawa kawai yayi yabude gaban motar ya shiga sukuma suka shiga baya suka zauna Waleed yatada motar, Ammi ta shiga masifa tace "wanan irin yaron ne Waleed zai kama danshi ya radamai sunanshi tirrr wlh, tier, I hate Arham with passion my heart is burning with rage, I want to deal with this boy dabazai kara tunanin crossing anylane with my son ba amman kin hanani kina cemin nabarshi da halinshi sabida yaga d'ana karami baida shekaru kamanshi sanan baida fada he is calm shine zai dinga gayamai maganan just look at the gut har gidana zai tako yama d'ana rashin mutunci wlh Arham yaci ganye, yaci ganye sosai, and zai gamu dani" tai kwafa Mom ta shiga bata hakuri, Waleed duk yana jinsu yay kaman baya jinsu at this point ya shafe zancen Arham a ranshi gabaki dayan hankalinshi ya karkata zuwa kan Saheeba, yasan tanachan gidan nan tana musu kuka dan batasan dukansu ba, and maganan da Arham yamai yasan kan itane yamai maganan, and koda zai bada komi daya mallaka ne bazai taba bari Arham ya karbi yarinyar nan ba, sabida yarinyar nan nabukatan kulawa da medication shikuma baidashi dazai bata koma bawanan ba bazai taba bama Arham itaba.


Horn yayi agaban gidansu Ilham mai gadinsu yafito yabude musu suka shiga ciki, yarane atsakar gidan sunata wasa saiga Mummy tafito tana murmushi tana musu sannu tazuwa tace "oyoyo oyoyo" parking Waleed yayi su Ammi suka sauko daga motar sukai wajen ta, sanan Waleed ma yafito yabi bayansu, cikeda girmamawa dakuma kunya yace "ina yini Mummy" "ina yini Waleed, sannunku da zuwa ku shigo dan Allah kunga yara duk sun cika gidan wlh yaran yan biyu ne, sunyi tafiya suna dubai fa bama suga baby ba har yanzu, amman yau mukesa ran zasu dawo in sha Allahu" Mom ce tace "Allah yadawo dasu lpy" hadadden falon su suka shiga Waleed yasami kujera ya zauna su Ammi zasu zauna Mummy tace "kawa bazamu bar yara su zanta ba, muje sama, Waleed bari aturo ta" tai maganan tana kwalama Ilham kira. "Ilham, Ilham kifito ga mijinki" wani daki Mummy tabude musu suka shiga, basu dade da zama ba saiga Ilham ta shigo tana sanye cikin wata atampa riga da zani, tai wani irin kiba nonon ta sun ciko sunyi suntum sabida shayarwa, tai duhu sosai kaman ba itaba sabida zafin ruwan zafin jego, har kasa ta tsugunna agaban Ammi da Mom tace "sannunku da zuwa Ammi ina yini" kanta Ammi ta shafa tace "daughter na sannu kinji ya jego? Nonon ki naciwo ne" gyadama Ammi kai tayi tace "eh yanamin barin ma inzaisha nono" cikeda tausayawa Ammi tace "kije yana falo ki fadamai inyaso yasamo miki abinda zakisha sannu kinji" gyadama Ammi kai tayi ta kalli Mom tace "ina yini Mom sannu da zuwa" "sannu Ilham ya jego kinji yanda mukeji ko yanzu damuka haifoku" dariya Mummy tayi tace "ai ingaya muku yaron nan inyafara kuka itama farawa takeyi kullum bamu baccin dare, kai jikan Kawata badai kuka ba" tai maganan cikeda zolaya, Ammi tace "inkin gajine bani kayana na tattara natafi dasu mufa ba'a mana wulakanci" dariya duk sukayi adakin, Ammi tasake kallonta ganin tana inda take tace "jeki gaida mijinki" tashi tayi Mummy tace "ko dauko yaron nan daga bacci kikaimai" gyadamata kai tayi tafita, dakinta ta shiga ta dauko Arham karami tarikeshi a hannu sanan ta sauka kasa tundaga sama Waleed kebinta da kallo harta karaso gabanshi tana murmushi ta zauna kusadashi ahankali tace "Baby oyoyo, sai yau zakazo kaganni nai fushi" dan murmushi yamata yasa hannunshi ya karbi danshi yarike ahannu yace "sorry I've been busy" sanan yazuba ma yaron ido yana kallonshi yaron dako sunanshi ba'a yiba amman yay kato yay kyau sosai sai kallon yanda yaron yag kamada Arham yake, yanda taga yana kallon yaron saida gabanta yafadi akullum gani take kaman dazaran ya kalli yaron zai gane dan Arham ne, ganin kallon dayake mishi yasa tace "Baby kakosan Arham ko zuwa duba takwaran shi baiyiba, ko kiranmu ma awaya baiyiba wlh baby abin yaban mamaki" murmushi yayi yakai Arham kafadarshi dayake son yafara ihu danhar yatashi yace "zaizo he's busy" ahankali yace "yimin list din abubuwan dakuke bukata na suna" murmushi tayi cikedajin dadi tace "Baby ni nafison kaban kudin zan aika ayomin siyayyan" gyadamata kai yayi yace "nawa kike so"? Wani irin dadi taji danso take tahada kudaden data samu da wanda zai bata tabama Arham tamai transfer halan zaisa yafara daukan wayanta dan gabaki daya bai daukan wayanta bai mata reply na message gashi batada halin fita tana jego saisa har Allah Allah take tai arba'in, ahankali kaman wata marainiya tace "5m ma zai isa" gyada mata kai yayi yace "ok zan miki transfer to your account anjima" rungume shi tayi tace "thank you Baby na Allah barmu tare" haka suka zauna afalon sukai shiru sai kallonshi take dan yamata kyau yan kwana biyun nan dabata ganshi ba gani take kaman tai shekara bata ganshi ba saitaga ya kara kyau, ga Arham ko kadan yaki kuka ajikinshi da normal ne yaron nan natashi zaisha nono ya koshi fa saiya fara uban kuka harsai yayi bacci amman yanzu yana jikin Waleed dakemai wasa yay shiru, cikin zuciyanta tace "danda bama nakaba jibi yanda yay bonding dakai I wonder yanda yaranka zasuyi bonding dakai" hannunshi takama ahankali tadaura kan boobs dinta tana kallon fuskarshi tace "ciwo yakemin Dr" sauke hannunshi yayi da sauri yana kallon boobs din yace "zan aiko miki da magani, sorry" yay maganan ahankali, gyadamai kai tayi yajuya yacigaba da wasa da Arham itakuma na kusadashi tana kallonshi, suna zaune ahaka har su Ammi suka fito, tashi duk sukayi aka shiga sallama sanan suka rakosu har mota, Waleed yabude booth yakira mai gadi suka shiga shigar da kayan dasuka kawo musu ciki sanan suka shiga mota suka musu sallama suka tafi, suna fita motar daya dauko su Anty Hassu suka shigo gidan, da sauri Ilham tafara murna tace "oyoyo yan dubai Anty hope kunyomin tsaraba" fitowa sukayi daga motar rungume su Ilham tayi sanan aka dunguma akai cikin gida, duk bajewa sukayi afalo da yaransu Mummy takawo musu Arham karami, Anty Hassu ce tafara karban yaron hadiye murmushin datake yi tayi ganin yaron gabaki daya sai tunanin ta yakoma kan fuskar Arham dasuka tabagani agidan har sau biyu, kaman Arham da yaron harya baci, dan murmushi ta kakalo tayi tamika ma Anty Hussai yaron, karbanshi tayi ta shiga murna dan ita mutum ce da batada lura haka, itakuma Hassu a kawai lura gata da kaf kaf da abu banbancin su kenan, sakewa Anty Hassu tayi gudun kar Ilham ta zargi wani abu suka cigaba da hira har magrib sanan aka tashi dan aje ai salla Mummy tabama Ilham yaron, tace "kije ki kwantar dashi ki zauna tareda shi mangariba tayi Ilham zama kake kusada yaran ka ka natsar dasu" karbanshi Ilham tayi tana murmushi dan dadi sosai takeji tana expecting kudi tai sama, bude dakinta tayi ta shiga tana shiga kafin ma ta kwantar da Arham aka bude kofa aka shigo dakin da sauri tajuyo Anty Hassu ce, maida kofar tayi ta rufe sanan tasaka sakata, tashi tsaye Ilham tayi rikeda Arham dake bacci akafadar ta tace "Anty Hassu" karasowa Anty Hassu tayi tamika hannu tace "bani shi na kwantar miki dashi" karbanshi Anty Hassu tayi sanan ta kwantar dashi ahankali cikin gadonshi ta gyaramai net sanan tajuyo ta zauna abakin gadon takamo hannun Ilham ta zauanr da ita tace "zauna nazo muyi magana ne saisa ma na kulle kofa dan banso aji maganan mu" zama ahankali Ilham tayi tana kallonta, hannayenta Anty Hassu takama tarike tace "Ilham, agidan nan bayan yayyin mu maza guda biyu, saini da Husai, sai wata data rasu kafin ke, saisu Farida, Ilham kinga kome zai faru we are family and we will always be, sanan babu wanda zai rufa maka asiri aduniyan nan kaman dan uwanka najini, kingani nan niba yarinya bace ke kanki kinada shekaru 26 sanan akwai wata data girmeki data basu kafin mu kinsan ko mun kwana biyu, kalleni da kyau Ilham niba yarinya bace, sanan duk gidan nan a duka yaran da Baba yahaifa shi kanshi Baba yafadi bai taba ganin d'a mai fikra da lura da abu cikin dukanmu kamani ni ba, ko rashin lafiya ake agidan nan kafin a fada ina ganin mara lafiyan nasan baida lafiya, so Ilham bansan kwana kwana, sabida inason na taimaka mikine tun kafin lokaci yakure miki" Anty Hassu tai maganan babu wasa tattare da ita sanan ta tsare Ilham din da idanun rass batako kyaftasu sanan ta nuna mata Arham dake cikin gadonshi da yatsa tace "dan chan yaron waye? Na mijinki ne kona abokin mijinki"? Wani irin faduwa gaban Ilham yayi da ita kanta Anty Hassu saida taga faduwar gabanta.





Kasa magana tayi saiji datayi bakinta ya bushe sosai ta shiga lashe lips dinta, Anty Hassu tace "bayan wanan bazan sake miki tambayan nan ba, yaron nan dan wayeshi na mijinki ne kona abokin mijinki"? Kasa magana still Ilham tayi tabude bakin ma komi takasa fitowa, gyadakai Anty Hassu tayi tace "yayi miki kyau Ilham, magana daya tal zan gayamiki, kwana chassain da tara na barawo ne kwana dayane tal na maishi, kibi duniya asannu sanan kidinga sara kina kallon bakin gatari dan karyazo daga baya yadauki wuyanki, bari naje nai salla" Anty Hassu tamike kaman ba ita tai maganan ba tai kofa tasa hannu tabude sakatar tabude kofan tafita daga dakin, dawani irin sauri Ilham ta tashi tai gadon Arham karami, yaye net din tayida sauri sanan ta kalli fuskarshi muryanta na rawa cikeda tashin hankali tace "wai daman ana gane kaiba dan Waleed bane? Tokodai Waleed yagane shiru kawai yamin yana kallona? Innalillahi wa innailaihi raji'un, ya Allah karufamin asiri"
[23/10, 21:19] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_💫






✍️ M SHAKUR








3️⃣9️⃣





Hawayen daya zubomatane ta share tana sharce majina sanan tadau wayarta dagakan gadon daidai alert na shigowa tabude da sauri instead of 5m data tambayay saitaga alert na 7m wani irin dadi taji ya lullubeta da sauri tai dailing number Arham amman harya gama ringing bai da gaba, takirashi yafi sau goma still bai dagaba cillar da wayan tayi cikin fushi tafashe da kuka, ace ta haihu yau yaro kwanan shi biyar amman har yanzu baizo ya duba dandan shiba, tamai text, tamai text, takirashi, takirashi harta gaji amman bai daukaba, baimayi acknowledging anyone of them ba, to wai yanzu baya sonta ne kome? Ina sonta dayace yake mata yake eh? Yanzu when she need Arham the most suhadu su kula da dansu yanzu ne zai juyamata baya baima damu da itaba, wlh tai nadaman budema Arham kafa harya shigeta yamata ciki ta haifan mishi d'a.




*
Koda sukakai gida yaso yafita dan ranshi sai kawomai Saheeba yake he could not stop thinking about her amman Ammi tahanashi fita tace yazauna agida, hakanan ya zauna agida sai nan nan dashi take dan batason yay tunani kowani abu. Wanan kenan



******
Tunda suka kai gidan nan kuka Saheeba take, kuka take kaman an yankata, gidane mai kyan gaske flat biyu ne aciki da compound mai dan girma, Baba Mani da Nura da maza biyun staff din Waleed ne sukadau flat daya sai Mama Iyami da Saheeba da Shamsiyaa sukadau dayan flat din, tun da suka shigo Saheeba bata barsu sun huta ba, gidan nan babu wanda bai lallashi teba amman kaman ba ita ake lallashi ba har kudi Baba Mani ya aika asayo mata abinci amman takici, da kyar suka samu anayin isha'i bacci

Please Login or Register in order to submit comment