Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

is like kaman ya zama dole mace tayi, indai Tana son ganin ci gaba da taimakon Al'umma.

Zarah tace bank'i taki ba, shima auren yana da muhimmanci, sannan aure baya hana karatu, nidai Ina baki shawara a matsayina na y'ar uwarki, indai kabir dagaske yake kice Ya fito Wlh, Kinga kyaci gaba da karatun a d'akin ki, amma baki da wani hujja kice saboda karatu k'iki yin aure, Abba Nasan shi zai miki aure amma nikam Dad Nasan Wlh koda wasa saina gama wannan karatun zaimin aure, har shekara hud'u ta k'arasa maganan cikin tausayin kanta.

Muryan Granny sukaji Tana fad'in kuna inane haka?

Zarah tace Granny gamu a nan, Granny shigowa tayi ta saki baki Tana fad'in yanzu wannan kaman mota, motar nan taya akayi ta shigo wannan d'akin, naga dai kofar karama ce, ni ban taba ganin irin wannan motar ba Wlh, mota harda katifa, ya ake tukata?

Dariya suka saki su duka sannan zarah tace Granny gado nefa

Sakan baki tayi tana mamaki tare da fad'in yanzu bakya tsoran wannan abun, salan kina bacci ya fara tu'ka kanshi? Ina gadonki Nada?

Zarah tace Kai granny wannan fah ba mota bane, gado ne mai shape din mota, gadona Nada anbama Mai aiki takai gidanta da aka canza min wannan.

Sakan baki tayi tana mamaki tare da fad'in naji kince gado ne mai chape din mota, miye chape?

Dariya suka saki, itbisam tace haba Granny Tana nufin gado ne mai fasalin mota, yanzu kin gane?

Tace Hmmm wanna ai iskanci ne, in banda asaran dukiya, ace gado za'a saka a d'aki Mai fasalin mota da haka a siya motar mana a ajiye, yanzu wannan gadon nawa aka siya?

Zarah tace million biyu da rabi

Salati Granny ta saki tare da fad'in audullahi yana tunanin mutuwa kuwa? Yanzu gadon da zaki kwanta ki tashi shine har million biyu da rabi, oh ni Aminatu, wannan asaran dukiya haka Kai audullahi zai gamu dani, dama aure yayi miki keda wancan dan banzan, koda yake Bari in Gama da munafukin yayanki da wannan ta nuna ibtisam, sannan in dawo kanki, bari audullahi ya fito naji ance ya dawo yana hutawa

Zarah cikin jin dad'in maganan Granny tace Granny gobe ma zai zo gida NAJEEB din

Granny tace yauwa Alhmdlh Nima zani yola, dan Wlh wannan karan da Mata zai koma dan banza, sai na mishi iya shege, tunda bashi da niyan aure, inma aljana ce ta aureshi zata rabu dashi in na saka aka d'aura mai aure, zan zabo mata guda uku cikin dangi in tawo dasu ya zaba d'aya, inma duka yake so ya auresu dan banza kawai....... Muje zuwa muga had'uwan Granny da miskili, sannan muga ya zata kaya in aka zabo ma NAJEEB mata har uku kaman yanda Granny tace hhhhhh.










~MARYAM OBAM~


*NAJEEB*


*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*



*DEDICATED TO.....*

*MY BESTY OF LYF HABIBA BUZY🥰🥰 LOVE U WUJIGA WUJIGA💘💘*




*PAGE 6*




*wai Mai yasa wasu mutane basa tsoran Allah ne? Sai dai a baki kawai, nifa Maryam bacewa Nayi bana son kud'i ba, Yooo ni wacece da Zan'ki son kud'i ai kud'i Abun sone, but in mutum zai naima kud'i saiya nema ta guminsa, akan wani dalili zan zauna in bata lokaci na inyi typing in rubuta Basira na, bata wani ko wata ba, in siya data da kud'ina ba tare da nace wani ko wata ya siya min ba, sai na gama rubuta y'ar basiran da Allah yayi min sai wani ya d'auka ya dinga neman kud'i dashi, toh Wlh Wlh daka yanzu bazan k'ara d'auka ba, abun ya zama raini dacin fuska, da farko an d'auki novel d'ina har guda uku ansa a okada ba tare da neman izini naba, ansa BA'KIN ALJANI in zaka karanta saika biya 500, ansa FATIMA ZARAH, shi kuma in zaka karanta saika biya 200, ansa DUKIYAR MARAYA, wanda barawon ya canza mishi suna izuwa dukiyar marayu, in Zaka karanta saika biya 300, akan wani dalili, ni Ina rubuta littafi a kyauta sannan wani yaje ya kaimun okada yana amsan kud'i da Littafina Wanda Nina rubuta bashi ba, nima fah ina son kud'in bawai banso ba, amma nayi a kyauta, akan wani dalili Kai ko ke zaku dinga siyar da novel din mutane without our permission, sannan Bayan haka wasu suna bud'e group akan in zasu tura maka novel complete saika biya kud'i, kuma Abun haushin basu suka rubuta novel d'inba, novel dinmu da muka rubuta suke saidawa, wasu ma saisu cire sunanmu akan novel din su saka nasu, Toh Wlh duk wani wanda ya k'aramin haka Wlh bazan d'auka ba, ba cika baki ba ko fariya Wlh akan hakkina Zan iya Shari'a da mutum, Abu d'aya shine in samu number d'in mutum, shikenan an wuce wajan,na fad'a zan k'ara fad'a maryam novel d'ina kyauta ne kar ku yarda ku biya kud'i domin a tura muku novel d'ina, ga sunan littafai na Zan fad'a, *FATIMA ZARAH*
*DUKIYAR MARAYA*
*BA'KIN ALJANI*
*BANDA ZABI*
*AMINIYA TACE*
*KISSA KO MAKIRCI*
*SUHAILAT*
*TAMBARIN TALAKA*
*JAWAHEER*
*SAINA AURESHI*
*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*
*BARIKI NA FITO*
*SAI YANZU WANDA NAKE RUBUTAWA NAJEEB*
*Gaba d'aya kyauta ne karku yarda wani yace saikun biya kud'i ya tura muku, kuma inna k'ara Kama wani yana saida min da novel saina d'auki mataki*










Zarah tace Kai granny mata har uku? Sai kuma ta fashe da dariya tare da fad'in sunyi mishi yawa ai.

Granny tace rabu da dan banza, koya zabi d'aya koya auresu duka, dan wannan karan bazan mishi wasa ba, inda a kauye ne da yanzu an fara maganan zai aurar da y'a, amma wai sai yanzu zaiyi aure, wannan lalacewan har ina, wlh ni rayuwar Bariki batai min ba.

Ibtisam tace uhm toh saiki koma kauyen ai ki zauna, Muma sai mu huta

Granny taja tsaki tare da fad'in basai ki Mai dani ba, mutuniyar banza, fita tayi dan taji muryan d'an Nata yana waya, alaman ya fito

Alh Abdullahi yana ganin Granny ya kashe wayar yana gaidata cikin girmamawa tare dayi mata ya hanya.

Tace Alhmdlh Ai Kai zance ma ya hanya kaida ka dawo daka k'asa Mai tsarki.

Zama yayi suka fara fira da Uwar tashi, suna cikin firan mum tazo itama anayi da ita, Alh Abdullahi yace Ina mamana ibtisam?

Mum tace suna ciki ita da zarah, bari in kirasu, tashi tayi ta nufi d'akin sai gasu tare sun dawo, ibtisam gaida uncle din Nata tayi cikin girmamawa, ya amsa tare da sakin fuska yace kin Kawo takardun naki koh, y'an makaranta.

Granny tayi caraf tace dakata ni dan Allah, wai ku Mai yasa bakwa maganan aure saina karatu? Kallesu yara duk sun girma suna shirin tsufa a gida, kwata kwata bakwa maganan aure, saina karatun banza da hofi, toh Wlh na gaji, bazaku sa a dingayi dani ba, ina tafiya ana nunani ba, nazo ne muyi magana akan yaran nan dan Wlh wannan karan rai zai baci in akak'i bin abunda nazo dashi, nazo ne akan maganan auran wannan dan banzan najibu naga ku kaman Abun bai dameku ba....

Dad yace mama Nima Ina bukatan NAJEEB yayi aure Sosai, amma har yanzu ya'ki magana, ko ince ya'ki fito da Mata .

Granny ta tsuke baki tare da fad'in sai ka tsaya jira saiya fito da Mata ai, naga alama Kai ke d'aure Mai gindi yake iskanci Wlh, amma zanyi maganin ka Wlh, gobe zani yola da safe zanje in tawo da yara cikin dangi ya zaba wacce yake so, dan Wlh wannan karan dole yayi aure sai kuma ta fashe da kuka tana fad'in koso suke saina mutu banga y'ay'ansu ba, Nina tsufa yanzu banda wani buri face inga yaransu Kafin in mutu, amma naga kuke d'aure musu gindi, kuka take wi wi wi tana share majina da riganta

Alh Abdullahi cikin Tashin hankali yake bata hakuri tare da fad'in mama duk yanda kika ce hakan za'ayi ki zabo mishi wacce tayi miki sai a d'aura mishi insun fahimci juna

Suko su zarah da ibtisam dariya suke k'asa k'asa, suna kallon wannan jaraban ta Granny, tsohuwa sai iya jaraba

Granny tace a'ah Zan Kawo su da yawa, inya zaba sai in maida su, daka nan sai a d'aura aure, inda so samu ne da tare dashi zamu ma,amma Nasan bazai jeba, kuma ina son kona tafi kar wanda ya mishi maganan auran saina dawo.

Dad yace duk yanda kika ce mama hakan za muyi.

Tashi tayi tana fad'in nidai na fad'a maka, gobe karfe 6 Zan tafi saika tashi da wuri dan asan abun yi, bari inje in kwanta

Bayan Granny ta wuce suma su zarah suka wuce suna dariya, tare da fad'in Wlh Granny zata ballo ma NAJEEB aiki harda kuka, ita kam ibtisam dad'i take ji, don ta tsani NAJEEB gwara a mishi aure da y'ar kauye din zata fi kowa murna

Mum kam itama tana son dan nata yayi aure, sai dai bada irin matan da Granny tace zata bashi ba, tafi son a barshi ya kawo da kanshi akan a zaba mishi, tunda taga shi zai zauna dasu, amma zata zauna ta saka ido ta gani

Alh Abdullahi Bayan Tashin granny Kai ya girgiza, domin yadan Indai yana son ganin farin cikinta da albarka a rayuwa dole yayi abunda tace, kuma yasan koda ta kawo matan Indai NAJEEB ne gata gashi, shima Dad d'in yana son dan nasa yayi aure.

Washe gari kaman yanda Granny tace karfe shida dai dai aka sakata a mota ciki harda su zarah da ibtisam da sukace zasu bita, granny tace babu inda zasu, in suka bita a Ina zata saka y'an matan, dole suka hakura mum ta bata su dambun nama, cin cin, cake da sauransu, nan driver yaja suka tafi, cikin mota Mai k'iran Prado, duk da Dad yaso su bar tafiyan zuwa gobe suje a jirgi, granny tace yau zata tafi basai gobe ba, dole Dad ya hakura.

Su zarah gida suka koma, har zata kwana ta tashi tana kallon ibtisam tace Bari in duba d'akin bros in gani, tun jiya yace insa a gyara, kullum sai angyara amma in yazo in ba'ayi wasa ba sai yayi complain yace an bata mishi wani abu, ai gwara Granny ta mishi auren yaje can ya k'arata, tabe baki ibtisam tayi tare da juya baya ta kwanta abunta.

Ibtisam ba ita ta Farka ba sai wajan 11, koda ta tashi Zarah bata d'akin, d'aukan wayarta tayi taga lokaci, tace Kai nasha bacci Sosai, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito tasa wata jallabiya ba'ka sannan ta d'aura gyalen jallabiyan, zama kiran kabir ne ya shigo wayanta, inda ta d'auka suna ta fira daka karshe yace zaizo ya ganta anjima da yamma.

Tace Allah ya kaimu, yace ta bashi address Sunan Layin ta fad'a mishi da no din gidan, yace OK saiya kirata

Koda suka gama waya, shuru tayi tana d'an tunani, ta rasa mai yasa take d'an jin kabir cikin ranta kwata kwata ko sati d'aya basuyi da had'uwa ba, jiya da yace zai kirata, bai kira ba duk ta damu, toh mai hakan ke nufi? Lokaci d'aya tayi murmushi tare da fad'in dan shine namijin dana Fara kulawa, kuma yana da hankali gashi ya iya magana Mai dad'i dasa nutsuwa.

Jin muryan Zarah tayi tana fad'in Ashe kin dad'e da tashi tunda har kinyi wanka, ina can ina taya mum aiki, wai yau ita da kanta zatai abinci d'anta zai zo.

Ibtisam da bata son maganan NAJEEB tace uhm, Zarah tace muje muyi breakfast tun d'azu nake jira ki tashi muyi tare, yunwa nakeji, yanzu na shigo in tasheki Ashe kin tashi.

Tashi Itbtisam tayi suka fita a dinning suka zauna suka fara cin abinci, bayan sun gama ibtisam tayi kitchen ta gaida mum, tare da fara tayata aiki, suna aiki suna fira, rabin firan duk na NAJEEB ne, shi yasa Itbtisam tayi shuru, sai dai takan yi magana jefi jefi, a haka har suka gama, aka jera komai akan dinning, wayar mum ce tayi k'ara dauka tayi cikin harshen turanci tace son har kazo kenan? Driver yana nan tafe Nasan yama kusa zuwa?

Yace mum nama ganshi saina k'araso, tace ok my only son tare da kashe wayan.

Mum ta kalli su Zarah tace harya k'araso, tunda ibtisam taji haka ta tashi ta wuce d'aki, domin bata son ganinshi balle ya k'ara raina mata wayau, ita rabonta dashi ma zaiyi shekara ko fiye ma

Tana d'aki tana jiyo maganansu harda na NAJEEB daya dawo, ciki harda Dad Sun dad'e suna fira sannan ya tashi ya nufi part d'inshi danya samu ya wuta.

Ibtisam tana nan kwance Zarah ta shigo tace baki fito kun gaisa da Bros ba.

Tsaki ibtisam tayi tare da fad'in dan Allah ki kyaleni inhuta.

Ibtisam dariya tayi tare da fad'in, Allah ya kyauta, itama zama tayi akan gadon d'akin Tana buga game a wayarta.

Kaman yanda Kabir yace wajan 7:30 sai gashi ya kira ibti yace mata yana waje,.

Kallon Zarah tayi tace kabir yazo, yana waje taya zan fita?

Zarah tace muje in rakaki sai in jiraki a bukka inkun Gama saimu shigo tare, ko kuma kice ya shigo mana.

Ido ibtisam ta zare tare da fad'in Rufamin asiri, so kike uncle ya ganni yace ban son karatu, Kome? Salan kisa yace aure nake so, nidai muje saiki jirani a bukka din in fita in sameshi, hakan zaifi

Zarah tace toh muje.

Har waje Zarah ta rakata suka gaisa da Kabir, har suna yar wasa da dariya kaman Sun san juna, komawa tayi ibtisam ta shiga gaban motar kabir.

Kallonta yayi Wanda ta canza kaya Kafin ta fito, wata doguwar rigan atamfa ne, saita yane kanta da wani karamin Gyale, ba karamin kyau tayi ba, duk da fuskanta babu make up, dama ita ba ma'abociyar yin kwalliya bace, yace ibti Anya zan iya jira shekara hud'u kuwa? Karfa wani yamin kwace

Murmushi tayi tare da fad'in ai kaman yanzu ne, shekara hud'un tayi, sannan kamin kyakyawan zato

Yace hakane, kaman yanzu ne, so ya Abuja din? Ashe kina da y'an uwa a nan?

Tace lafiya kalau Alhmdlh, eh uncle d'ina ne

Yace toh nidai na fad'ama ibti koni wanene amma ita ta'ki fad'amin

Murmushi tayi tare da fad'in mai kake son sani a tare dani?

Yace komai, inason sanin komai akan matata dazan aura insha Allah

Murmushi tayi cikin jin kunya, sannan ta Fara fad'a mishi ko ita wacece, tace toh kaji komai yanzu

Yace eh naji komai, ina Ahmad din bros dinmu?

Tace sai Friday yake dawowa gida, boarding school yake, duk da skul din akwai day, yace yafi son boarding din, so duk Friday yake dawowa, saiya koma Sunday, in anyi hutu kuma sai yazo Kano

Kabir yace Allah ya taimaka, ta amsa da Ameen.

Kiran sallah isha'i da akeyi yasa Kabir fad'in Bari in shiga masallaci, da yake akwai masallaci a jikin gidan wanda Dad yasa ayi, itama tace ok bari in shiga gida nima inyi sallah.

Fita tayi tana k'okarin yin nocking aka bud'e gate din, ido biyu sukayi dashi, gabanta taji ya fad'i, shiko kawar da kanshi yayi tare da wucewa masallaci, bayan yaja kofar ta datse kuma yasan ciki zata shiga, tsaki taja tare da fad'in dan rainin wayau, nocking tayi aka bud'e Mata kofar sannan ta shiga, a bukka ta samu zarah Tana sallah, itama alwala tayi a famfo din dake gefe ta cikin ciyayi, bayan zarah ta idar ta amshi hijab din Zarah tayi sallah, Bayan ta idar Zarah tace ya tafi ne?

Ibtisam tace a'ah yana masallaci, yan..... K'aran wayanta yasa bata k'arasa maganan da take son yi ba ta d'auka ganin kabir ne, sawa a kunne tayi ban San mai yace mata ba, naji tace ganinan

Tace ma zarah bari inje in ganshi yace In fito yanzu zai wuce ma

Koda ta fita a tsaye ta ganshi a jikin motarshi, hannunshi ri'ke da Leda, murmushi ya sakar mata tare da fad'in ibti Mai yasa koda yaushe inna kalleki sai inga kin k'ara kyau ne, miye sirrin

Murmushi tayi tare da fad'in babu wani sirri, kawai idonka ne yake ganin maka haka

Yace Kai Anya kuwa? Ni Inda idonane da nafi kowa murna, dan ban son kowa yaga min kyanki saini d'aya, mi'ka mata ledan hannunshi yayi tare da fad'in zan gudu ana son ganina, sai munyi waya.

Tace gskya wannan kyautar da kayi hakuri ka barshi, inaga kaman yayi yawa.

Yace karki manta shaidan shike maida hannun kyauta baya, kuma in banyi ma matar da zan aura abuba wa zamma? Very soon Indai na turo komai ni zan dinga miki dan bazan bari Abba yaci gaba ba.

Uhm kawai tace tare da fad'in ngd, yace ko kefa, sai munyi magana, koda yake muje in rakaki, har kofar gidan suka jera dai dai lokacin NAJEEB yazo shiga gida, ganin yanda suke ma juna dariya abun ya bashi haushi yaja tsaki tare da shigewa gida tunda an bud'e kofar, itama shiga tayi tana fad'in sai anjima.

NAJEEB kam haushi Kabir ya bashi, ya rasa wanda zaiso sai wannan karamar yarinyar mara kunya da bata gaida mutane, hhhhh kunji najeeb fah, wai bata gaida mutane, ya tsaya yana mata dariya, y'ar 15yr ko 12 zance ma, tsaki ya kuma ja, tare da fad'in wasu mazan basu da tunani mutum ya tsaya yana soyayya yana bata ma kanshi lokaci dama Kananan yara ba babban mace ba, yaushe har tayi girman data iya magana da maza, lokaci d'aya ya d'aga kafada tare da fad'in miye nawa a ciki ma

Ibtisam bukka ta nufa inda taga zarah na zaune tana game a wayarta, Zarah ganin leda a hannun ibtisam yasa ta amsa tare da fad'in Bari muga maiya Kawo, tare da bud'e ledan, chocolate ne sai kwalin waya Samsung, Zarah tace inye kin fito gari za'a fara chatting

Ibtisam tace uhm, ai baki Sani ba Abba ne baya son in ri'ke babban waya, yanzu wannan ma ban San yanda zanyi dashi ba Wlh, ko in maida Mai kawai

Zarah tace Kai yanzu saiki maida Mai? Lallai dako kin cika mara wayau, ki boye kawai, balle yanzu nasan dole Abba zai yarda ki ri'ke babban waya, saboda makaranta su browsing da sauransu.

Tashi sukayi suka shiga ciki, inda suka tarar da NAJEEB a falo da Mum yana kallon ball, mum tace daka ina kuma haka?

Zarah tace Mum mun fita siyo abune, ibtisam tace sannu da hutawa Mum, tare da shigewa ciki, NAJEEB kam ko kallo basu isheshi ba, idonshi nakan tv, itama zarah ciki ta shige inda tace ma ibtisam tasa wayar a caji, suje suci abinci, ibtisam tace plz ki kawo mana nan, ki zuba mana, ban son fita na gaji, Zarah tace ok bari in Kawo mana.

Yau kwanan Granny uku da tafiya yola, kuma a yau tace zata dawo, tunda ta tafi sukan yi waya jefi jefi, domin inda Granny take babu network Sosai.

Ibtisam tunda ta had'u da NAJEEB sau d'aya basu k'ara had'uwa ba, ta fito sanye da hijab ya tsaya mata dai dai Giwa, ana ganin dogon wandon da tasa, NAJEEB na kwance akan kujeran falon yana danna waya daka duka alamu yana chatting ne, jin motsin mutum yasa yace a bashi ruwa ba tare daya d'ago ba, banza dashi tayi tare dayin gaba abunta, jin ba'a kulashi ba yasa ya d'ago ya ganta dai dai lokacin tana fita, ranshi yaji ya baci tare da fad'in I will teach her a lesson

Ibtisam samun Kabir tayi a waje, inda ta shiga cikin motarshi, sun dad'e suna fira yayin da NAJEEB yake ta kallonsu ta CCTV, ganin ta fito a motar yasa ya dawo falon ya zauna, koda ibtisam ta bud'e kofar falon a tsaye ta ganshi a gabanta, d'aga hannu yayi ya tsinka Mata Mari tare da fad'in karki k'ara a rayuwa, ke wacece da ina magana zaki wuce ba tare da kinyi abunda nace ba?

Hannunta dake kan fuskanta ta saitin wajan daya mareta, alaman taji zafin Marin, ta cire tana k'okarin marinshi shima.. Da sauri ya ri'ke hannun tare da murde mata shi ya juyo da ita ta baya, duka suka kalli gaba, yace baki da hankali koh? Ni zaki mara?

Wani irin nishi takeyi na wuya, tare da kokarin ta samu ta kwaci kanta dan murde mata hannun da yayi tana jin zafi Sosai, amma ta kasa Kwacen kanta domin karfin ba d'aya ba.

Yace how dare you, ni sa'anki ne? Ni zaki mara? Jin nishin da takeyi na wahala harda kwalla daya Fara zuban Mata duk da ta baya take yasan tana hawaye dan yaji alama yanda take nishi tare da shessheka ,yace inaso ki bani hakuri tare da alkawarin bazaki k'ara raina wani ba in ur lyf Kafin in sakeki

Ibtisam duk da tana jin zafin murde hannun da yayi mata, bata tunanin zata bashi hakuri domin bata ga abunda tayi mishi ba, dahar zai mareta, sannan yace ta bashi hakuri kuma, jin tayi shuru yasa ya k'ara murde hannun da karfi lokaci d'aya hannun yayi y'ar k'ara 'Kas ta saki wani irin k'ara Mai sauti.......












~MARYAM OBAM~

*NAJEEB*


*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*



*DEDICATED TO.....*

*SA'ADATU ALKALI TSAFE🥰🥰💘 MY LOVELY DAUGHTER WANNAN PAGE D'IN NAKI NE SABODA KE NAYI SHI, KIYI YANDA KIKA GA DAMA DASHI🥰*




*PAGE 7*







Ganin haka yasa ya turata ta buge da jikin bango, tare da fita yabar falon.

Mum ta fito da sauri tana fad'in ibtisam fad'i kikayi Subhanallah, tare da nufanta tana k'okarin d'agota, hannun daya murde mata mum ta kamo da sauri ibtisam ta saki k'ara domin wani irin azaba taji da Mum ta ri'ke mata hannun ganin haka yasa mum tace badai kin buge a hannun ba?..

Ibtisam hawaye ke zuba a idonta Sosai, ga hannunta dake mata zafi, ga bacin rai lokaci d'aya taji kanta na Mata ciwo, tare da tsanan zaman gidan, ji tayi gaba d'aya Tana son komawa Kano gidan Abbanta, mum jikinta ta kama da d'agota, tare da fad'in sannu maiya samu hannun?

A hankali tace babu komai, na fad'i ne, Tana fad'in haka ta wuce ciki inda ta samu Zarah na kwance tana bacci, itama kwanciyan tayi hannunta yana zugi, gaba d'aya ji tayi kaman k'ashin hannunta ya fita dan taji ba yanda ta saba jin hannun ba, wani irin tsanan NAJEEB taji ta kar'ayi ninkin banin kin wanda take Mai, lallai a duniya bata da makiyi yanzu kaman shi, inda za'a tambayeta wata tsana a duniya? Toh lallai NAJEEB zata ce, kwanciya tayi tana hawaye da haka bacci barawo ya saceta

Sai wajan 6 ibtisam ta farka gaba d'aya ta kasa d'aga hannun da Najeeb ya murde mata, ga wani irin rad'adi da zafi da yake mata sosai, Lokaci d'aya tasa kuka saboda azaba.

Zarah ce ta shigo ta sameta tana kuka, cikin tashin hankali tace lafiya kuwa ibtisam kike kuka?

Ibtisam tace zarah hannu na ciwo yake min Sosai, na kasa d'agashi, zafi yake min

Da sauri Zarah ta nufeta tana fad'in tashi muje hspt maiya samu hannun? Kinji ciwo ne?

Kaita girgiza mata alaman a'ah, tare da tashi tace muje Aban magani zafi yake min Sosai tana shesshekar kuka, fita sukayi inda suka ga Mum a falo.

Ganin ibtisam na kuka Mum ta Fara tambaya lafiya kuwa?

Zarah tace Mum ta buge a Hannu ne.

Mum cikin tashin hankali tace badai faduwan da tayi d'azu bane? Maza kuzo muje asibiti, sannu ibtisam, fita sukayi inda suka shiga mota driver yaja ibtisam na hawaye, har asibiti suka nufa, inda suka nufi reception, receptionist suka fito da file dinsu tunda family card ne, nan suka shiga wajan Dr, inda ya fara fad'in mrs Abdullahi, Sannunku.

Dr kallon ibtisam dake hawaye yayi, yace lafiya kike hawaye? Maiya faru?

Mum tace hannun ke Mata ciwo, ta fad'i ne, nan Dr ya tashi ya ri'ke hannun wani irin k'ara ta saki, ya dad'e yana dan juya hannun sannan yace gocewan 'kashi ne, Bari in kira Dr din kashi yanzu zai zo.

Ba'ayi ko 30mnt ba Dr din yazo bayan anyi gwaje gwaje inda aka fara gyara mata hannun, zo kuga kuka wajan ibtisam zarah kam gaba d'aya tausayin Itbtisam ya kamata harda kwalla, ita kam mum jikinta duk yayi

Please Login or Register in order to submit comment