Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa baya ganin darajanta, kai ta girgiza tare da fad'in next time zanyi k'okari in tabbatar bai shaba, muyi sex haka inga miye matsalan, daukan kud'in daya watsa mata tayi masu uban yawa, tace nagit has alot of money, I love you nagit, tana maganan tana murmushi.

Najeeb direct airport aka kaishi, kai tsaye ciki ya shiga inda ya amsa wasu takardu ya cika, sannan ya nufi cikin jirgi, inda mutane suka fara shiga,Najeeb shida wani bature ne a wajan tukin jirgin, kaman dai ko wani jirgi matuka biyu, lokaci d'aya jirgin ya d'aga zuwa America


*America*

Koda jirgin ya sauka mutane suka fara fita, Najeeb kam, wayarshi ya kunna, sannan ya tashi ya fita daka cikin jirgin shima, wasu takardu ya cika sannan ya fita daka airport din inda ya tsaida taxi ya shiga tare da fad'ama Mai taxi din inda zai kaishi.

Kofar wani Gida aka kaishi wanda ya fito yaba ma Mai taxi din kud'i sannan yayi nocking, wata baturiya cikin uniform Wanda zai tabbatar maka cewa Mai aiki ce ta bud'e nashi kofar tare da gaidashi cikin girmama, wanda wannan ne yasa na gane gidan Najeeb dinne.

Shiga yayi tare da nufa bedroom dinshi wanda yake a gyare kamshi na tashi tako Ina, cire uniform d'in jikinshi yayi, ya rage daka shi sai boxer kwanciya yayi akan gadon d'akin sai juyi yakeyi, lokaci d'aya yayi tsaki tare da d'aukan wayarshi yayi rubutu alaman message ya tura, bayan ya gama ya ajiye wayar.

Baiyi ko 30mnt ba sai ga wata kyakyawan yarinya baturiya ce amma tana da kyau Sosai, tasa dogon wando tare da wata top mara hannu, gashin kanta Brown, ganin Najeeb a kwance yasa tayi murmushi tare da fad'in sannu da hutawa cikin harshen turanci, kayan jikinta ta Fara tubewa, saida ta cire komai dake jikinta sannan tahau gadon domin massage yace yazo tayi mishi, hannuna tasa a bayanshi ta Fara mishi tausa tun daka kan wuyanshi har k'asan 'kugunshi, Najeeb har ido yake lumshewa alaman yana jin dad'in tausan da take mishi, lokaci kad'an bacci ya D'aukeshi, ganin haka itama yasa ta manneshi a jikinta tare da kwanciya tana kallonshi, Najeeb yana dakyau duk wasu abubuwa da ake bukata a samesu a wajan namiji Najeeb yana dasu, sai dai abu d'aya yana da wulakanci Sosai, mai mu'amala dashi sai yayi hakuri, inma mutum baida hakuri Toh bazai iya hulda da Najeeb ba.

Koda Najeeb ya farka baiga Angelina ba, toilet ya fad'a yayi wanka domin yana jin jikinshi wani iri, Bayan ya fito yasa singlet da boxer yayi falo inda yaga Angelina Tana zaune tana kallo.

Ganin Najeeb yasa ta tashi da sauri tayi hugging dinshi tare da fad'in zo muci abinci nasa anyi maka abinci, baice komai ba sai dinning daya nufa ya fara cin abinci tare da alcohol d'inshi, sai dai bada yawa yasha ba, dan haka bai bugar dashi ba, bayan ya kammala ya dawo kujeran falon ya zauna, itama Angelina Bayan ta gama tashi tayi ta nufeshi tare da zama akan cinyarshi tasa hannunta ta rungumoshi tace yau zamu club?

Murmushi yayi tare da fad'in may be.

Tace plz muje mana, kasan a club muka fara had'uwa, tun daka lokacin ka hanani zuwa, kace sai dai muje tare plz muje yau nayi missing abubuwa

Tureta yayi daka jikinshi tare da fad'in tashi ki tafi, karki k'ara nunamin face d'inki

Cikin tashin hankali tace najit maiya faru?

Yace How dare you, to say that in front of me? You are a cheater only god knows what you are doing when am not around, you even have the courage to say you miss something? Kina fad'in kinyi missing abubuwa miye babu a nan? Alcohol? Food? Kome? Kawai kice kina son zuwa kiga wani yana fad'in haka yayi d'akinshi Jim kad'an sai gashi da kud'i ya kamo hannunta ya bata tare da fad'in fita tun Kafin in fitar dake, bana hulda da macen da take hulda da wasu mazan.

Jiki a sanyaye ta Fara fad'in najit plz listen to me.....

Daka mata tsawa yayi tare da fad'in I said leave from here

Tsugunnawa tayi a k'asa tana ro'kanshi akan yayi hakuri, ba haka take nufi ba, amma najeeb yaki sauraranta, daka karshe ma falon yabar mata, ganin haka yasa ta tashi ta fita cikin takaici, ta tabbata ya barta kenan har abada, dama ya gaya Mata tun farkon haduwansu ta guji abunda zaisa yayi zarginta, daka ranan daya Fara zarginta ya barta kenan, ya kuma ja mata warning akan karya ganta da wani namiji, kuma tun daka lokacin ta kiyaye amma gashi bata tsira ba

Najeeb kam ranshi ya baci Sosai, tare da takaici kenan yanzu bayan yayi sex da ita ta kuma bama wani shima yayi, tsaki yaja tare da tashi ya d'auko kwalban alcohol ya bud'e tare dasa baki ya fara Kwan kwad'a dan yasan shine kawai zaisa ya manta komai in yasha, Hmmm Allah ya kyauta





*Nigeria*

Koda ibtisam ta shiga gida ta tarar da ummi a falo tana shirin fita, tace ummi Ina zaki?

Tace zan shiga gidan Hjy fati ne d'anta ya kone ban shiga ba, hjy fati makwabciyar suce.

Ibtisam tace Allah sarki, wanne a ciki? kai kuna akwai azaba Wlh

Ummi tace Sosai dan karamin yaronta Jamil, ibtisam tace Kai Allah sarki Allah ya sawake, ummi tace bari in dawo Ina son ganinki, ibtisam tace toh, fita Ummi tayi ibtisam tayi d'aki tare da ledan hannunta

Koda ta shiga taji kamshin sabulu alaman Granny tana toilet Tana wanka, ajiye ledan tayi akan gadon d'akin, cire hijab din jikinta tayi tare da bud'e ledan, su chocolate ne Kala Kala dasu biscuits masu tsada duk kuma na waje.

Granny ce ta fito daka wanka d'aure da towel Hhhhh, ganin kayan ciye ciye yasa tace ah Kinga d'an arziki.

Ibtisam tashi tayi tace Granny Wlh abunda kike min ya isheni, miye haka sai kace an gaji dani, baki San kina zubar min da kima bane

Tsaki Granny tayi tare da fad'in, kimar banza da hofi, ai babban Kima shine kiyi aure, kuma Wlh Bari kiga Kabiru ya turo zaki sha mamaki, gwara tun yanzu ki Fara kallon kanki a matsayin amarya, maganan karatu kuma saiki daina ja'ira, wannan rashin kunyar da fitsaran da kikeyi duk saboda Kinga kin ri'ka ne a gaban mu, inda anyi miki aure tun tuni da yaushe, yarinya kaman Mai iska kin dage ke boko, muda bamuyi bokon ba mun fasa rayuwa ne, wannan yaran dai na masu jajayen Fata munaji kad'an kad'an toh mai za'a nuna mana?.. Tsaki ta saki tare da fad'in wannan kayan kabirun ne ya baki

Ibtisam tace ban sani ba sai ki kirashi ki tambaya

Granny tace uwarki aysha kike fad'ama haka bani ba, aure ne dai sai kinyi ko zaki mutu, mutuniyar banza

Ibtisam tace kaman yanda zaki mutu, kowa ya huta ba

Granny tace oho dai, ko yanzu na mutu na taba aure kefa? Ai gwara ni amma ke babu aure

Ibtisam tace ni Wlh Granny ki koma Abuja da zama ki barni in huta

Granny tace gidan d'ana nake, dan haka ke zance ma ki tafi gidan miji kowa ya huta, ke in kika kalli madubi baki ganin tsufanki ace har yanzu kina gida

Ibtisam tace Kedai kika Sani, aure ne dai Banyi sai lokaci yayi.

Granny tace zanga karshen kafiya, naga dagaske kike, saina gama dake zan koma kan miskili shima, naga abun naku iskanci ne, musamman ma miskili da in ana magana ya dinga wani kallon mutane Wai shi bature baya jin Hausa, wannan karan ashar zan dura ma d'an banza Nasan zai gane, ta k'arasa maganan tare da tsuke baki alaman bada wasa za tayi mishi ba

Ibitsam kam babu abunda take sai dariya tare da fad'in tunda mutum baya jin turanci basai kayi hakuri ba, ko dole sai kinyi magana dashi

Granny tace ai zanyi maganin d'an banza Wlh, kauye zani in samo mishi Mata, insa a d'aura Mai, zanga karshen miskilanci da rashin jin Hausa ta k'arasa maganan cikin jin haushin jikanta baya jin fulatanci baya jin Hausa, Hhhhhhhhhh su Granny manya muje zuwa















~MARYAM OBAM~
*NAJEEB*


*BY*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam obam)*


*https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/*


*http://WWW.Maryamobamnovels.com*

*Wattpad@ Maryam-obam*

*Instagram@maryam_obam*



*DEDICATED TO.....*

*MY LOVELY MUM*




*PAGE 5*






Ibtisam kam dariya take, Koba komai zata so Granny tasa a d'aura ma wannan shegen Mai girman kan y'ar kauye kodan taga yanda zaiyi, ibtisam tace uhm Granny ai inaga Najeeb yana jiran ku zaba mishi mata ne, sai yasa har yanzu bai fito da Mata ba.

Granny tayi shuru can tace hakane kam, zanyi magana da audullahi, zanje yola a duba mishi Mata wacce zata dinga koya mishi fulatanci.

Ibtisam dariya take Sosai cikin ranta, tare da ro'kan Allah yasa ayi mishi hakan.

Granny tace toh ke ya Magananki da kabir? Ina fatan kin amince koh?

Ibtisam tasan ta gama magana da kabir, dan haka tace na amince Granny Indai zaki ma Najeeb aure, amma ina son a fara nashi Kafin nawa, tunda Kinga ya girmeni Sosai, ban so In rigashi aure

Granny cikin jin dad'i da murnan ibtisam ta yarda zatai aure tace karki damu, gobe ni dake zamu habuja din inga audullahi muyi magana.

Koda ummi ta dawo ta kira ibtisam, Bayan ibtisam tazo, ummi tace Waye yazo nemanki?

Ibtisam tace ummi shine wanda ya rage mana hanya shekaran jiya, nan taba ummi labarin yanda suka had'u.

Ummi tace naga kaman ya baki, Leda, ban San amshe amshen kayan samari, Indai kin San ba auranshi zakiyi ba gwara ki sallameshi, ban son fitina

A hankali tace toh ummi, tare da tashi ta fita

Washe gari da safe ibtisam ta shirya ita da granny Wanda Abba bai San da tafiyar Granny ba, sai ganinta yayi da safe ita da ibtisam, yace mama zaki rakata garage ne?

Tace miye kuma wani garan?

Yace ina nufin tasha.

Tace wani rakiya? Tare da ita zamu, muje ka sauke mu tasha sai mu shiga mota

Yace mama tare kuma zaku?

Tace eh ko saina tambayi izini ne, Kafin a barni inje inda nake so?

Yace a'ah kiyi hakuri mama ba haka nake nufi ba, naga tun jiya baki ce zaki jeba sai yanzu.

D'aure fuska tayi tare da fad'in Ummaru zaka kaimu tasha ko mu tafi da kammu?

Yace a'ah muje in saukeku, ummi ta basu kayan miya sukai ma mum tare dasu gurasa da sauransu, sannan ta musu Allah kiyaye hanya suka fita.

Saida Abba ya biya ATM ya cira kud'i sannan sukai hanyar garage, inda ya d'aukan musu shatan mota su biyu, nan ya biya kud'in motan, sannan ya bama Granny kud'i itama ibtisam ya bata, saida suka wuce sannan ya shiga tashi motar ya wuce kasuwa.

Sai wajan 3 da wani abu suka isa Abuja, dai dai kofar gidan alh Abdullahi aka saukesu, inda suka nufi gate din gidan suka fara nocking, wani soja ne ya le'ko yana fad'in 'who is that? Ibtisam tace mune cikin harshen turanci take bashi amsa.

Granny tace Mai yace? Ibtisam tace tambaya yake su Waye? Granny tace oh yanzu har sai an tambaya, kai dan ubanka zoka bud'e Uwar Mai gidan ce,

Dai dai lokacin sojan ya bud'e karamin kofar gate din, inda mutum zai shiga Inba da mota bane.

Kallonsu yayi sannan yace wa kuke nema?

Ibtisam ta bashi amsa da fad'in Munzo wajan matar gidan ne?

Yace tasan da zuwanku?

Ibtisam na k'okarin bashi amsa, Granny tace wai Mai yake cewa ne?

Nan ibtisam ta fad'a mata, Granny ta kalleshi cikin jin haushin tambayar da yake musu, tace Kai Dallah bamu waje mu shige tare da k'okarin tusa kanta cikin gidan.

Sojan yayi sauri ya tareta tare da magana cikin gurbattaciyar hausan shi yace mama inane zaka? Ka kira ajiya sai in Barka ka ciga, lokaci d'aya kuma ya kalli ibtisam yace ki kira madam a waya in tace in barku saiku shiga.

Granny kam in banda faman surfa bala'i tare da fad'in audullahi yasa Anci min zarafi yanzu in banda iskanci In za'a zo gidansa sai an kirasu a waya, har dani uwarsa.

Ibtisam dake k'okarin kiran mum tace Granny dan Allah kiyi shuru, shifa wannan bai San ke maman uncle bace, inda ya sani Aida ya Bari kin shiga, kuma daka gani sabon zuwa ne, dan duk zuwan da nake ban taba ganinshi ba.

Granny ta galla mata harara tare da fad'in Dallah ni kirata Ina jin fitsari kaman marata zata fashe

Kiran mum tayi, bayan mum ta d'auka tace ibtisam Kun zone, Ashe da Granny kuka tawo, yanzu na gama waya da abbanki.

Ibtisam tace Munzo muna Gate, ance mu kiraki.

Mi'ka ma Sojan wayarta tayi Mai tocilan, ya amsa tare da sakawa a kunne, naji yana fad'in ok ma, ok ma, lokaci d'aya kuma ya fara sorry ma, tare da kashe wayan ya mi'ka ma ibtisam, ya fara basu hakuri, cikin harshen turanci tare da cewa ibtisam taba granny hakuri bai San Maman oga bace.

Nan ibtisam ta fad'a ma Granny abunda yace, Granny ta kalleshi tare da fad'in Dallah bani waje, munafuki, da sauri ya matsa suka shiga, tun Kafin su k'arasa wata yarinya Doguwa chocolate colour kyakyawa ta rugo da gudu ta rungume ibtisam tare da fad'in oyoyo, lokaci d'aya kuma ta saki ibtisam ta rungume granny

Granny tace Dallah sakeni karki Karya ni, saida kika gama rungume y'ar uwarki sannan zaki zo kaina.

Ibtisam tace zarah Kinga kyaleta zomu shige

Granny tace zanyi maganinku Wlh, yara duk sun girma Sun Fara tsufa amma babu aure, ji yanda zarah ta k'ara fashewa, nidai Amina wani laifi na muku babu maganan aure a tsarinku, kwafa tayi sannan ta shige ciki ta barsu nan tsaye suna murnan ganin juna, sun dad'e a nan Kafin suka shiga ciki inda suka tarar da mum a falo ita d'aya.

Ibtisam gaida mum tayi, mum ta amsa cikin sakin fuska tare da fad'in ya hanya?

Ibtisam tace Alhmdlh, sai dai rigiman Granny, duk ta isheni dariya suka saka, mum kana kallonta Kaga balarabiya sak ita NAJEEB ya d'auko sai dai wasu sukan ce farinta ya d'auko yafi kama da dad d'inshi wasu suce da ita yake Kama, mum in kaji hausarta saika d'auka ba Hausa takeyi ba dan in tanayi kaman tana larabci

Granny ce ta fito cikin tan'kamemen falon Tana gyara zani tare da fad'in ku komai naku daban dana mutane, Kun tashi kun ajiye mara mutunci a bakin gate.

Zarah tace Kai granny maiya miki kuma?

Tace ban sani ba, in banda wulakanci in za'a shigo gidan sai ace sai an kira a waya, in mutum baida Kati fah, ko in bashi da wayan gaba d'aya fah?

Zarah tace saiya koma, Granny ko a addinance anaso in mutum zaizo wajanka ya Sanar dakai, bawai yazo kai tsaye ba K....

Granny tsaki taja tare da fad'in tunda bakwa son mutane ba, ai dole ki Kawo maganan addini..

Dariya suka saka, mum tace mama muje kuci abinci ku huta

Granny tashi tayi aka nufi k'aton dinning table, harta zauna, lokaci d'aya kuma ta tashi tare da fad'in nifa wannan abubuwan ban cika sonshi ba, in mutum zaici abinci saiya wani zauna a kujera kaman Maye, ni kusa min in zauna a k'asa Inci

Zarah da ibtisam babu abunda suke sai dariya

Granny tace uwarku kuke ma dariya, akan Mai yasa za'a ce cin abinci sai an hau saman kujera maima kuke kiran kujeran Denis ne ko Mai ohon muku

Zarah saboda dariya har dayin k'asa tace miye kuma Denis dan Allah granny kar kisa cikina ya fashe saboda dariya. Tsaki Granny taja tare da zama ta mi'ke k'afa a k'asa tana fad'in nidai ban hawa Denis din nan wlh

Mum da itama take ta dariya k'asa k'asa ta Fara zuba ma Granny abinci, Bayan ta gama ta ajiye mata a k'asa inda ta zauna, Granny Fara cin abinci akayi ana mamula baki.

Bayan sun kammala, Granny tace audullahi bai dawo bane har yanzu?

Mum tace tun dazu yace Sun sauka, Nasan yana gab da gida yanzu

Tashi Granny tayi, tace ni bari in shiga in huta kafafuwana duk sunyi tsami, d'aki ta nufa

Ibtisam taba mum tsaraban da Ummi ta bata, mum taji dad'i Sosai tana ta godiya, inda zarah taja ibtisam sukai d'akinta, wanda d'akin yayi mugun had'uwa, komai dake d'akin pink ne, sai rasi rasin blue kad'an, zama sukai akan gadon d'akin Mai shape din mota, zarah tace kin Fara shirin zuwan mu skul kuwa?

Ibtisam tace na Fara mana, sai dai Granny ta sani gaba da maganan aure, kai wannan tsohuwar akwai jaraba

Zarah tace Niko Tana sani dariya wlh, dama ta mana wata biyu a nan

Ibtisam tace Aiko ko sati tayi a nan sai kince ta isheki, ko sanda take zuwa kina skul in kin dawo kin gaji, yanzu da kike zaman Gida ai wlh saita isheki, dariya zarah tasa inda suka fara tsara yanda za suyi a skul, wayan zarah dake wajan wardrobe d'inta ne ya fara K'ara, tashi tayi da sauri ta d'auka, ganin Mai kiran yasa tayi saurin d'auka tare da fad'in bros

Yace yakike? Cikin harshen turanci

Tace am fine my bros, sai dai nayi missing dinka

Murmushi yayi tare da fad'in gobe Zanzo Nigeria, make sure kisa a gyaramin part d'ina

Tace an gama bros, Granny tazo ma

Tsaki yaja tare da fad'in har yanzu bata mutu ba?

Zarah tace what? Sai kuma ta fashe da dariya tare da fad'in Bari Dad ya jika, kana ma mum d'inshi fatan mutuwa.

Kashe wayan yayi ba tare daya kuma ce mata komai ba.

Kallon ibtisam tayi tare da fad'in bros gobe zai zo,, rabonshi da gida wajan wata hud'u kenan

Tabe baki ibtisam tayi tare da fad'in wannan ba damuwa ta bace.

Zarah dariya tayi tare da fad'in oh na manta Ashe enemy d'inki ne, sai kuma ta saki dariya tare da fad'in nima a waya yake sake min, inya dawo sai yayi ta d'aurewa kaman dodo, na rasa irin halinshi Wlh, zanso inga matarshi inya ya zai dinga mata.

Itbtisam tace lallai Aiko duk wacce ta auri wannan ta shiga uku, sunanta sorry, lokaci d'aya kuma ta tuna da abunda ya kawo Granny, cikin ranta tace Allah ya tabbatar inga yanda zaiyi.

Zarah tace dama Ayi auran zumunci ke dashi, tunda naga halinku d'aya K....

Da sauri tace aniyarki ta biki, da in auri wannan yayan naki gwara in mutu Banyi aure ba, wannan wani banzan tunani nema kikayi haka, tsaki ta saki cikin bacin rai.

Zarah tace Allah ya huci zuciyarki, wasa nake miki, ai nasan in aka had'aku wata rana k'ona gidan zakuyi

Itbtisam dake huci tace wannan Aiba wasa bane, in mala'iku suka amsa fah? Haba dan Allah, wlh gwara in mutu yau da ace na auri NAJEEB, dan Allah karki k'aramin wannan Wasan plz, wlh kinsa raina yayi mugun baci Sosai

Zarah tace ikon Allah, haka tsanan NAJEEB yayi girma cikin zuciyarki? Adai dinga hakuri d'an uwanki ne dai

Tsaki Itbtisam taja tare da tashi tana fad'in naga baki da wata firan arziki saina wannan yayan naki Kinga Bari inje wajan Granny n....

Da sauri zarah ta janyota Tana fad'in na daina miki firanshi, amma kudaina wannan abun babu kyau Wlh, duk da Nasan laifin bros NAJEEB ne, yana da shegen miskilanci da raini wlh, kodan ya girma mutane ne oho, wlh koni hakuri nake dashi, ga Dad komai yace saiya biye mishi tsaki taja

Itbtisam tace Kema kenan, balle ni ki.... Karan wayarta ne yasa bata k'arasa abunda tayi niya ba, d'auka tayi taga kabir ne wanda a jiya tayi saving number d'inshi, sawa tayi a kunne tare da fad'in hello

Ta gefenshi yace ibti Barka da yamma, sorry ban kiraki ba, aiki yamin yawa, yanzu nace gaskiya sai naji muryanki, ya kano?

Tace uhm lafiya kalau, nima bana Kano Ina Abuja

Da sauri yace yaushe kika zo Abuja?

Tace d'azu nazo nida Granny gidan uncle d'ina

Kabir yace shine baki fad'amin jiya ba, muzo tare

Tace naga hakan bai kamata ba, bai dace in bika ba har zuwa wani gari, hakan ba dai dai bane

Murmushi yayi tare da fad'in hakane, my ibti, tare da fad'in na gode ma Allah daya had'ani dake, ina Mai farin ciki, Allah ya tabbatar yasa ki zama mallaki na

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.

Yace anjima zan kiraki, ina fatan zaki bani dama inzo in ganki a nan?

Tace babu damuwa tare da fad'in sai anjima, ta kashe wayan.

Zarah dake zaune kusa da ita, tace ke dawa haka? Daka ji saurayinki ne yanda kike wani kashe murya

Ibtisam takai Mata duka tare da fad'in ta ina na kashe murya?kina da sharri Wlh

Zarah tace fad'amim Waye inji tare da d'aga mata gira

Nan ibtisam ta bata Labarin inda suka had'u

Zarah saida tayi dariya Sosai tare da fad'in Wlh Granny tana da matsala, Tab gaskiya ki daina fita da ita.

Uhm kawai ibtisam tace

zarah tace Amma inda nice ke Wlh zan yarda in aureshi, tunda muda zamu karatu kaduna, shi kuma yana Abuja, Kinga zaki samu daman karatu, yanzu fah maza tsada suke sai kiga mata da yawa babu mijin aure, wlh ibtisam inka samu dama Kar kayi wasa dashi, kyace ya jiraki shekara hud'u ai yayi yawa wlh, kina da tabbacin zai iya jiranki har shekara hud'u, haba ibtisam Wlh nima da badan Dad ba da yake son inyi karatu ba Aida aure zanyi Wlh, nifa aure nake so, Amma Dad ya'ki fahimta inaga saina fito na fad'a musu

Dukanta da wasa ibtisam tayi tare da fad'in amma dai da kin cika mara kunya number d'aya, Tabdi Niko Wlh karatu ne a gaba na, Kinga mazan yanzu basu da tabbas, wlh gwara koda zanyi auran saina gama karatu in samu aiki sannan inyi, dan ban son ina bin namiji Ina bani yana min wulakanci, gwara in tsaya da kafafuna, Suma yanzu mazan basu cika auran zauna gari banza ba, dan basa son wahala

Zarah tace uhm, ni Wlh aure nake so, ke nifa wannan karatun kaman dole ne, amma Wlh Ina bala'in son inyi aure, Kinga in Nayi sai inyi karatun a d'aki na, hankali kwance, amma hakan bazai yihu ba, Allah yaban iyaye duka y'an boko, ko wanne zai ka'ida, ba mum ba, ba Dad ba, yanzu koda wasa ban isa ince Ina son aure ba, wai dana shiga uku, ko bros NAJEEB baiyi ba shida yake aiki sai ni, Hmmm ta sauke ajiyan zuciya

Ibtisam tace zarah kin San muhimmancin ilimin mace kuwa? Inda za'a tambayeni tsakanin mace dana miji waya kamata a fi bama ilimi? Zance mace ya kamata, kin San mai yasa? Mace itace tushen gida Mace itace take zama a gida ita da yara ta basu tarbiya tare da duk wata kulawa, in mace bata da ilimi taya za tayi hakan? Da yawa yaran da zaki gani suna rashin ji Toh uwarsu bata da ilimi, sannan yana dakyau mata a dinga basu ilimi domin ko ina a dinga damawa damu, ki kalla aikin soja akwai mata Kinga wannan abun alfahari ne, ki duba fannin Siyasa akwai mata wanda da ana ma mace y'ar Siyasa kallon y'ar iska, amma yanzu an fara fahimta, inda babu Mata a Siyasa da baza'a dinga bamu hakkin mu ba, bazan musan miye Siyasa ba, sannan mune dai mukaci jefa ruwan kuri'a, sannan yana dakyau mata su dinga karatu kodan su zama likitoci, yanzu Idan mace tazo haiyuwa namiji zai amshi haiyuwar tayu ba musulmi bane, Kinga inda mata suna karatu Sosai da an huta, komai mu ana tauye mu, daka munyi aure shikenan, in namiji yace ba zamuyi ba shikenan ta zauna, bayan ilimi shine ginshikin rayuwa, wlh zarah in Kinga yanda in naga mace take burgeni in naga tana karatu ko aiki sai Kinji mamaki, zan iya bama mace tallafin komai nake dashi dan tayi karatu domin Nasan al'umma zasu amfana da ita, yana dakyau komai a dinga saka mata, ana bamu y'ancin mu, Idan kika duba yanzu zamani ya canza duniya ta canza, ilimi both na addini dana zamani

Please Login or Register in order to submit comment