Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu abinci, cikin lokaci kad'an ta gama musu shinkafa da miya, koda ta gama wanka ta shiga tayi Bayan ta fito tasa wani wando da top, "k'aran wayarta yasa ta d'auka taga kabir ne

Tana d'auka yace gani a gate din skul d'inku ki fito kizo ki shigo dani

Tace dagaske?

Yace yes am serious

Tace OK gani nan

Hijab tasa akan kayan dake jikinta ta fita, da yake da nisa zuwa bakin gate machine tahau, Aiko tana zuwa taga motar kabir abun mamaki ya bata

Shida abokinshi Tahir, nufan motar tayi KABIR Ya sauke glass din motar tare da fad'in Shiga muje

Bud'e bayan motar tayi ta shiga suka fara tafiya har cikin makarantar Tana nuna musu hanya kusa suka faka motar a wajan parking space dake kusa da hostel d'insu

Tace I thought wasa kake min?

KABIR yayi murmushi tare da fad'in taya zanyi wasa da princess d'ina? Nayi missing d'inki naji ban iya hakuri yasa dole nazo in ganki

Dariya tayi tare da gaida Tahir dake gaba yana jinsu

Tahir yace AI Nayi shuru tunda kun manta Ina motar

Ibtisam tace Ayi hakuri bamu manta ba, kawai Ina mamakin zuwan bazata ne

Kabir ya cafe da fad'in sorry my ibti naso in fad'a miki sai kuma nace bari kawai inzo in miki surprise

Tace Aikam,, so ya hanya?

Yace lafiya kalau my amaryata nan da wata hudu da kwanaki

Murmushi tayi cikin jin kunya

Tahir yace hakane kam, Allah dai ya nuna mana wannan rana cikin koshin lafiya yasa Ayi damu

KABIR ya amsa da Ameen, "ita kam ibtisam cikin ranta ta amsa da Ameen

KABIR yace my ibti banji kince Ameen ba?

Murmushi tayi tare da fad'in nace

Tahir yace cikin zuciya?

bata ce komai ba sai dariya da tayi

Tahir yace ibtisam ya kamata musan wani event kike so kiyi, Dan mu Fara shiri

Ibtisam tace event kuma? Ni bana bukatar wani events

KABIR yace no my ibti dole muyi event auren soyayya nefa, bana kiyayya ba

Dariya ibtisam tayi yanda kabir yayi maganan

Tahir yace Aiko na kiyayyan ma ana event

KABIR yace Toh Kinji

Ibtisam tace toh yanzu ni ban San mai zance ba

KABIR yace inaga muyi dinner, ta gefena ta Wajanki kuma sai kuyi bridal shower, da kamu,"in kina da wani abu kuma saiki K'ara domin in San abunda my ibti ke shiryawa

Ibtisam tace Nop abunda ka fad'a is OK, bana son event yayi yawa Sosai

KABIR yace ok my ibti, yanzu dai zakiyi bridal shower, da kamu, so duka a hall za'ayi, sai kuma dinner

Tahir yace bridal shower ango na zuwa?

Ibtisam tace a'a baya zuwa only amarya da friends dinta ne

Tahir yace Toh naki a canza mana, ango yazo

Dariya sukayi shida kabir

KABIR yace a'ah baza'ayi haka ba, dinner kawai za'ayi duka da amarya da ango, amma duka biyun kamu da bridal shower babu wanda zani

Ibtisam tace amma ango na zuwa kamu AI, shida abokai suzo suyi spraying su tafi

KABIR yace my ibti ki bari ranan dinner kawai, ban so suyi ta kallonki

Tahir yace au hakane? Toh dad'in Abun Muma munada mata balle a mana gori

Ibtisam tace ba gori bane gaskiya ya fad'a

Tahir yace taran dangi zakuyi min?

KABIR yace a'a kasan nida ita komai namu d'aya ne, "d'auko wata Leda yayi na waya ya mi'ka ma ibtisam yace gashi

Tace bana fad'a maka Abba ya Aiko min da wacce ka siya min ba

KABIR yace kin fad'a min, ni kuma Na riga Na siya wannan sanda kika fad'a, toh kinga saiki had'a biyu, "wannan iPhone7 ne Kinga wancan Samsung ne saiki had'a, dama naga ku mata wayarku kenan iPhone

Dariya tayi tare da fad'in ni Wlh daka barshi

Kabir yace Kinga amsa dan bazan ri'ke ba

Amsa tayi tare da fad'in nagode Allah k'ara budi

Tahir dake gaban motar har cikin ranshi yaji dad'in addu'an da ibtisam tama kabir, wanda yanzu mata saika musu Abu babu godiya wata rainawa ma zatayi

Sun dad'e suna fira Kafin kabir yace zasu tafi, ibtisam fita tayi Bayan tayi ma Tahir sallama, shima KABIR fitowa yayi tare da matsawa inda take yana fad'in my ibti plz banda biyema friend plz Kinji?

Kaita d'aga mishi alaman toh

Yace sai yaushe kuma?

Tace sanda kazo

Yace OK ana ta aikin gidanki

Tace Allah ya taimaka

Ya amsa da Ameen

Dr jibril tun daka nesa ya hango su lokacin da kabir yama ibtisam sallama ya shige mota suka tafi dai dai lokacin  Dr kabir ya k'araso kallon ledan wayar dake hannun ibtisam yayi tare dayin gaba tana gaidashi bai ko bata amsa ba ya wuce ya shiga motarshi.....







Read and leave it, dnt share to anyone



*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*

*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*

3138831065 Firstbank Maryam Alhassan

*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*

*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*








Ibtisam kam hakan da yayi mata sai bataji dad'i ba, Koba komai tunda ta gaidashi ya kamata ya amsa bawai ya shareta ba"haka ta nufi d'akinsu jiki a sanyaye domin babu dad'i ka gaida mutun kuma kasan yaji yayi banza dakai

Koda ta isa d'akinsu babu wanda ya dawo, dan haka shiga tayi tasa wayar da kabir ya bata a caji tare da kwanciya, bata dad'e ba bacci yayi gaba da ita

Zarah sai wajan 6 suka fito daka lecture Kai tsaye d'akinsu ta nufa taita nocking shuru saida ta dad'e "ibtisam dake bacci ta farka taji k'aran ana nocking sannan ta tashi ta nufi kofar tare da tambaya Waye?

Zarah tace bud'e nice

Bud'e kofar ibtisam tayi Zarah ta shigo tana fad'in haba ashe bacci kikeyi sai yasa naji shuru inata nocking

Ibtisam tace Wlh bacci ya D'aukeni....

Katseta Zarah tayi tare da fad'in wannan wayar Waye a caji?

Ibtisam tace nawa

Zarah tace waya baki?

ibtisam tace KABIR yaban shine ya kawo min wayar

Zarah tace yazo ne KABIR din?

Ibtisam tace eh yazo bai dad'e da tafiya bama

Nan Zarah ta d'auki wayar tana fad'in a'ah Amarya wajan barrister Kabir gaskiya yana ji dake fa Sosai, "irin wannan wayoyi har guda biyu manya ga iPhone ga Samsung

Ibtisam dariya tayi tare da fad'in uhm bari kiga in fad'ama Ummi kar ta gani in shiga uku

Zarah dariya tayi tare da fad'in Aikam, kin tuna abunda ya faru kenan?

Ibtisam tace ai ban manta ba, saboda waya aka hanani zuwa skul gashi saboda Abun yasa zanyi aure ba tare dana kammala karatu ba, kaman yanda naso Nayi ba tun Farko.... D'aukar wayar da ummi tayi ne yasa ibtisam fad'in ummi Ina wuni?

Ummi tace lafiya kalau ya karatu?

Ibtisam tace lafiya kalau ummi.,"dama na kira in fad'a miki dazu KABIR yazo ya Kawo min wata waya, nace ya Bari tunda ga wanda yaban yace a'a wai yariga ya siya

Ummi tace mutumin da yake hidiman aure shine yake wani K'ara siyan miki waya? Kai Allah ya kyauta, shikenan saiki ajiye d'aya kar ki ri'ke biyun a sace

Ibtisam dariya tayi tare da fad'in haba Ummi sai kace autanki Ahamd

Ummi tace au shikenan, "Ina Zarah

Mi'ka ma Zarah wayar ibtisam tayi

Gaida ummi Zarah tayi cikin girmamawa, Ummi tace ya karatun fatan dai komai lafiya?

Zarah tace lafiya kalau ummi karatu Alhmdlh

Ummi tace toh Masha Allah, sai a dage sannan a k'ara tsare mutunci banda kawayen banza

Zarah tace insha Allah

Sallama sukayi Bayan ummi ta kashe wayan Zarah ta kalli ibtisam tace Wai Mai kika dafa ne?

Ibtisam tace Shinkafa da miya

Nan Zarah ta tashi ta d'auko plate ta zuba abincin tare da d'auko Titus ta fasa ta zuba akan abincin ta Fara ci

Ibtisam ita danna wayarta take abunda

Zarah tace abincin yayi dad'i fah, gaskiya kin iya girki Sosai

Ibtisam tace uhm Kedai kawai kice Kinji yunwa

Washe gari ibtisam Nada lecture karfe 8 dai dai, dan haka da wuri ta shirya ita d'aya ta tafi domin har yanzu su Aisha basu dawo ba.

Ibtisam basu fito daka lecture ba sai karfe 10, "zama tayi akan wani dakali, dan tasan kota koma Zarah bata nan dan tace mata 10 suma suke da lecture

Ibtisam na zaune tana danna wayarta gaba d'aya hankalinta nakan wayarta "sai jin muryan mutum tayi kaman daka sama ana fad'in madam danna waya

Da sauri ta d'ago kanta taga salis ne."murmushi ta saki tare da fad'in banga zuwanka bafa, kawai na daiji magananka daka sama

Salis yace yaushe zaki ji, tunda kina Bussy wajan danna waya, kina chatting

Tace uhm wani chatting, game nakeyi a wayar

Yace yau banga Aisha ta shigo lecture ba?

Ibtisam tace eh bata nan

Yace ok su Aisha manya indai mutum ya ganta a lecture Toh na Dr jibril ne, dan tasan baya wasa

Ibtisam bata ce komai ba, tana dai sauraranshi

Salis ya kira sunanta da fad'in ibtisam

Tace na'am

Yace ina son fad'a miki wata magana in babu damuwa

Tace ka fad'a karka samu damuwa

Yace OK...

Lokaci d'aya ya fara magana kaman haka, ibtisam tun sanda na ganki na yaba da hankalinki da kuma nutsuwarki, "duk da d'akinku d'aya dasu Aisha amma sai naga ke dasu ba irin halinku d'aya bane, kuna da banbanci Sosai

Ibtisam jinshi take

Yace tun sanda na ganki naji Ina sonki, sai dai nasan bazan samu karbuwa ba, may be kice Nayi miki k'arami ko kice muna karatu tare, naso Nayi shuru na boye abunda ke raina sai naga is better in fad'a May be in dace

Ibtisam tayi shuru Kafin tace"nagode da kauna, sai dai ina Mai baka hakuri akan biki na saura wata hudu da sati d'aya

Salis yace kai aure?

Ibtisam tace eh

Salis yace wow na tayaki murna, gwara kiyi auren domin shine darajan mace,"amma fa wlh kin burgeni da zakiyi aure tun yanzu, ba irin matan da za suce sai sun gama karatu ba, daka karshe samun mijin ya musu wuya ba

Ibtisam tace uhm ba tare da tace komai ba

Salis yace ya kamata dai yanzu tunda zakiyi aure kina da miji sai mu zama friends amma wanda zai aureki yayi Sa'a, yamin shigan sauri

Ibtisam dariya tayi domin maganan salis ta bata dariya yanda yace wanda zai aureta yayi mishi shigan sauri

Suna nan zaune suna fira ita da salis harya tashi yace Bari yaje ya amso sa'ko

Tace OK nima dai Bari inje in huta

Duka suka jera tare shiya Mike ita tasha kwana domin zuwa hostel, "koda ta koma d'akin taga su Aisha da hauwa da kubra a d'akin suna ta raban kud'i

Shigowan ibtisam yasa kubra fad'in matar Dr jibril

Ibtisam tace wa? Rufamin asiri dan Allah "tare da kallon su Aisha tace Sannunku

Aisha tace yauwa har an fito daka lecture din?

Ibtisam tace eh tare da fad'in harya bamu text baki shigo ba

Aisha tace bar shegen zanje in sameshi nasan Dan bai ganni bane ya bada text din, dan inje ya cini ne dan bura uba

Hauwa tace Waye?

Aisha tace Daniel mana

Hauwa tace tir harda Arne yake cinki? Aiko anyi Asara

Aisha tace Wlh banga Asara ba, wlh ki gwada bashi ya iya cin mace

Hauwa tace Allah ya kiyaye ai duk iskanci na, Banyi da wanda ba musulmi ba wlh

Kubra tace nima kaina ban hulda da Arne duk da ina yare, balle ku hausawa

Aisha tace kwaji dashi

ita kam ibtisam mamaki suke bata, yanda suke sakin zance anyhow babu boye boye ko tsoran Allah

Suko kunyar junansu basayi, kai Allah ya kyauta yasa mu dace

Nan suka zauna sunata fira

Kubra tace kun San Jamila fashion ta kusa da d'akin mu?

Hauwa tace eh na santa naji ance wai ta shiga cult dagaske ne?

Kubra tace gulman da zanyi muku kenan"ashe Kun sani?

Aisha tace nidai ban sani ba, sai yanzu, "haba sai yasa take shiga cikin manya manyan motoci Ashe ta shiga cult?

Aikam muna dan gaisawa zanyi taka tsan tsan da ita Wlh, kar taje ta bada jinina
.dariya suka saki su duka

Ibtisam kam Abun mamaki yake bata, dama an fad'a mata indai jami'a ne zata ga mutane iri iri, wasu y'an lesbians wasu bin maza, wasu y'an cult Ashe dagaske ne tunda gashi taji suna fad'i, "Aiko dole in dage da addu'a.

Washe gari su ibtisam karfe 8 suke da lecture kaman jiya, yau dr jibril ne zai shigo musu

Ibtisam da wuri ta isa tana shiga ita da Aisha shima ya shigo

Bai wani bata lokaci ba Ya basu text, Bayan sun gama ya k'ara basu assignment tare da fad'in 5mrk ne assignment din, text shima 5 duka 10mrk

Koda ya gama lecture fita yayi yabar ajin ba tare daya jira wani bayani daka bakin kowa ba

Aisha kallon ibtisam tayi tare da fad'in naga sai kallonki yake tayi daka na d'aga ido sai inga yana satar kallonki

Ibtisam tace Taya kika san ni yake kallo? Kenan Indai hakane Kema shi kike kallo

Aisha ta kwashe da dariya tare da fad'in Toh fah, kodai kishi kikeyi ne? "kawai inna d'ago ne sai inga yana kallonki

Ibtisam tace uhm Allah ya kyauta tare da tashi zata fita."salis yace ina zaki yanzu wani kecturer zaizo 10 dai dai gwara ki zauna

Zama tayi tare da fad'in au ai ban sani ba, nasha ko Mun gama babu Mai shigowa

Salis yace Tab yau fah muna da lecture 4 ma Akwai lecturer din da zaizo mana

Ibtisam tace Kai yau akwai zama..

Aisha tace ba kadan ba..

Suna nan zaune lecturer din ya shigo yayi musu lecture shima ya basu assignment ya fita

Ibtisam tashi tayi ta fita domin kabir ya kirata, tafiya take tana waya ita da Masoyin Nata cikin shauki da kaunar juna, "tun tube taci zata fad'i ji tayi an ri'keta Wanda idonta a lumshe yake gaba d'aya ta sadakar ta fad'i k'asa, "jin an ri'keta yasa ta bud'e ido a hankali ganin wanda ya ri'keta yasa ta tashi daka jikinshi da sauri

Dr jibril yace ki dinga kallon gabanki

A hankali cikin jin kunya tace ngd

Jin maganan Kabir yana hello hello

Yasa ta maida wayar kunnanta tare dayin gaba, Tana waya

Shiko Dr jibril gaba yayi abunsa



*BAYAN 3MONTH*

ibtisam da Zarah sun fuskanci abubuwa iri iri daka kawayen zamansu, inda suka dinga tura musu ra'ayi akan rayuwar banza, amma basu biye musu ba.

Shiko salis da ibtisam sunyi mugun sabo domin yana taimaka mata Sosai ta fannin karatu, "ganin haka ibtisam yasa ta sake dashi suke shiri Sosai dashi

Sannan ta gefen Dr jibril yana bama ibtisam shawara Sosai, tare da fad'a mata ta kame kanta daka kawayen banza, sau da yawa inya ganta dasu Aisha saiya kirata akan ta rage hulda dasu, "duk da ta fad'a mishi dakinsu d'aya dasu

Duk wanda ka gani a skul din zaka gansa yana karatu domin Sun kusa Fara exam, karatu suke Sosai Babu wasa.

Zarah da ibtisam dasu salis suna zaune a wajan wani bishiya wayar Zarah tayi k'ara d'auka tayi taga Najeeb mamaki ya rufeta ganin number d'inshi na Nigeria, "tace yaushe yazo k'asar?

D'auka tayi tare da fad'in bros yaushe kazo k'asar?

Najeeb cikin hausarshi wacce ya dan Fara koya saboda granny yace kwana 3,"sai kuma ya sauya zuwa English yace come out Ina skul d'inku

K'ara ta saki tare da fad'in kana ta wajan ina?

Fad'a mata inda yake yayi, "tashi tayi ta Fara tafiya da sauri kai tsaye inda Najeeb ya fad'a mata ta nufa

Hango wata mota tayi Prado tasan kuma ta gidansu ce, kai tsaye motar ta nufa tare da bud'e motar "k'ara ta saki ganin Mum da Najeeb

Tace mum dama har dake?

Fitowa Mum tayi suka rungume juna ita da Zarah sannan suka koma cikin motar zarah tace driver yaja su k'ara gaba

Zarah gaida Najeeb tayi tare da fad'in bros Nayi missing din'ka. Ya America?

Najeeb fine kawai yace tare daci gaba da danna wayarshi

Gab da inda su ibtisam suke zaune ita da salis suka faka motar, "Wanda dai dai lokacin Najeeb ya d'ago kansa Wanda idonshi ya sauka a kansu,"lokaci d'aya ya saki murmushi tare da fad'in wai ita ta shiga university har an fara wayewa tare da fira dako wani namiji

Bud'e kofar motar din Mum tayi suka fita ita da Zarah.

Ibtisam hango Mum yasa ta tashi tare da nufan Mum da sauri tayi hugging d'inta tana fad'in sannu da zuwa Mum

Mum cikin dariya tace yauwa ibtisam, y'an jami'a. " Ya karatun naku?

Ibtisam tace lafiya kalau Mum Alhmdlh

Muje ciki Mum

Mum tace toh har sunyi gaba ibtisam tace ah Zarah kuje ina zuwa, wayoyina yana wajan salis bari in amso

Zarah tace ok sukai gaba ita da Mum

Kai tsaye ibtisam wajan salis ta nufa inda ta ganshi yana k'okarin tashi, "tace Ina zaka ga wayoyina a kusa dakai

Kallon wayoyin yayi tare da fad'in kai Wlh ban Lura ba, kice dana tafi da wani ya samu

Dariya ta saki Tana fad'in dana shiga uku

Salis shima dariya yayi tare da fad'in keda sai miki akeyi a free, ai baki da matsala

Duk wannan abunda suke idon Najeeb na kansu, "tsaki ya danja ya tsana yaga mace tana sakewa dako wani namiji, "jiba yanda take mishi dariya kaman wani d'an uwanta

Ibtisam tace Bari inje sai munyi magana Ltr

Yace OK tare dayin gaba

K'aran da wayarta keyi ne yasa ta d'auka ganin Mum ce

Bayan ta d'auka mum tace ibtisam kice Najeeb yazo mana yana Mota

Ibtisam kallon motar tayi wanda ita bata san dashi aka zoba, "amsa mum tayi da Toh, jiyo muryan Zarah tayi tana fad'in Mum maza basa shiga hostel d'in mata muje dai waje wani restaurant

Mum tace ok ibtisam barshi Bari mu fito ma
.ibtisam dad'i taji, domin bata tunanin zata iya mishi magana, "ita Tama manta da wani Najeeb tunda hannunta ya warke, "amma jin an kira sunansu sai taji wani sabon tsanarshi cikin ranta, domin tunawa da abunda yayi mata

Cikin ranta tace mugu azzalumi sai Allah ya saka min.

Zama tayi a wajan tana jiran su Mum su k'araso

Bayan su mum sun k'araso ibtisam ta tashi, Mum tace suje suci abinci

Zarah tace suje wani restaurant a cikin skul din

Zarah ta nufi mota tace Najeeb ya fito suje

Kaman bazai fito ba, komai ya tuna kuma saiya fito

Ibtisam ganin ya fito ta tamke fuska tare da kawar da kanta gefe

Tafiya suka farayi kai tsaye har cikin restaurant din, matan dake wajan sai kallon Najeeb suke

NAJEEB daya lura da hakan sai yaji abun ya bashi haushi, tare da fad'in matsalan matan Nigeria kenan, basu da aji

Ibtisam tace ita bata cin komai, a koshe take.

Mum ta kalli Najeeb tace kaifa Mai zaka ci?

Yace nothing

Mum tace cikinku

Mum fried rice tace a bata, Zarah kuma tuwo tace ita Tana so

Mum tace a k'aro wani rice takeaway akai ma driver shima

Ibtisam tace a kawo takai Mai Bayan an kawo abincin domin bata son zama inda Najeeb yake ko kad'an.

Amsan abincin tayi ta fita waje Kai tsaye driver taba abincin da ruwa, inda ya amsa yana mata godiya

Aisha ce tazo inda ibtisam take tana fad'in ina kika samo wannan Mai k'aton motar haka? Ko Sanata kika samo?

Ibtisam tace Rufamin asiri dan Allah

Aisha tace toh na daiga kaman daka motar kika fito

Ibtisam tace ba daga ita na fito ba sa'ko na bada

Aisha ta kalli motar sabuwa fil tana she'ki tace ibtisam Waye mai motar plz?

Dariya Aisha tana ibtisam domin yanda duk ta wani rud'e take tambaya Waye mai motar

Aisha tace tsarki ya tabbata ga Allah kalla wani guy hadadd'e,  wannan daka ganinshi Balarabe ne

Waigawa ibtisam tayi taga Najeeb ne wanda suka had'a ido, ta saki tsaki tare da Waigowa

Ta gabansu yazo ya wuce "Aisha tace kai Kinji kamshi wayyo ya barmu da kamshin turare amma wannan guy din ya had'u....  Shuru tayi tare da sakan baki ganin Najeeb ya shiga motar da ibtisam tace ta bada sa'ko

Aisha tace dama shine mai motar?

Ibtisam tace yayan Zarah ne fah

Aisha tace kina nufin Dan uwan Zarah ne?

Ibtisam tace eh

Aisha tace kai Wlh sai naje na nemi number d'inshi Dan yayi min wlh

Ibtisam tace gwara ki kama kanki wlh, domin gudun raini

Aisha murmushi kawai tayi tare dayin gaba tana fad'in Indai dan uwan Zarah ne sai tasan yanda akayi ta had'asu

Ibtisam wajan su Mum ta koma, bayan sun kammala cin abinci suka fito Kai tsaye wajan mota suka nufa inda Mum ta shiga tana fad'in zamu kama hanya

Zarah tace Mum Abuja zaku tafi yanzu?

Mum tace a'a kaduna zamu shiga gobe zamu koma yanzu yamma tayi ban son tafiyan dare

Zarah tace Mum plz mu biku gobe sai mu dawo da kammu

Mum tace OK Toh kuzo muje, "amma baku da lecture ?

Zarah tace nidai banda shi, ban dai sani ba ko ibtisam Nada shi

Ibtisam tace banda lecture gobe sai 4

Mum tace toh kuzo muje

Zarah tace bari muje mu d'auko kaya, Jan hannun ibtisam tayi sukai ciki basu dad'e ba suka fito

Najeeb ganin Sun shiga motar da yake shi yana gaba yasa shi fadin Mum Ina zasu kuma?

Mum tace tare zamu gobe zasu dawo

Tsaki yaja

Driver dai tada motar yayi sukai gaba

Gudu driver din yake shararawa a titi, suna tafiya suna fira "Mum tace yanzu saura wata d'aya biki koh?
.zarah tayi caraf tace eh mum, kuma za'ayi bikin muna hutu wlh ba k'aramin dad'i naji ba

Mum tace Yadai kamata, naga ma ibtisam duk kin rame, ko karatu ne?

Ibtisam murmushi kawai tayi

Da yake da Hausa suke maganan najeeb na sauraransu sai dai wani ya gane wani kuma baya ganewa, Yadai San suna maganan ibtisam zatai aure, "cikin ranshi yace amma kam duk Wanda ya aureta zaiyi fama, yarinyar da kwata kwata nawa take? Shekararta nawa da za'ayi mata aure tun yanzu, "Wanda dai ya aureta zai auri rashin kunya sannan babu abunda zai samu dan banga alaman tana da abunda mata ke dasu ba

Kai tsaye basu tsaya koh inaba sai hotel 17, inda suka Kama d'aki, guda hud'u, Mum ita d'aya Zarah da ibtisam d'aya sai NAJEEB d'aya driver d'aya.

Kowa shiga d'akinshi yayi danya huta.

NAJEEB Bayan ya shiga abinci yayi order yace a Kawo Mai, "domin yunwa yake ji, and bazai iya cin abincin dasu mum sukaci ba a skul din su Zarah

Washe gari k'arfe 10 duka suka gama shiri domin Kama hanya bayan sunyi breakfast a restaurant din hotel din "shi kam NAJEEB baici komai ba dan bai fito ba, koda ya fito yace kawai su kama hanya basai yaci abinci ba

Zarah gaida Najeeb tayi ya amsa da fine kawai. " ganin mum a wajan yasa ibtisam itama gaidashi Mai yakon ya amsa saiya saki tsaki tare dayin gaba "ibtisam  wani irin haushin kanta taji gashi Mum hankalinta baya wajansu dama ta sani bata ko kalleshi ba

Mum tace ma driver ya kaisu garage susa su zarah a mota Kafin su tafi

Haka koh akayi Kawo garage suka kaisu, inda akayi ciniki driver ya dawo ya fad'a ma Mum, ciro kud'i tayi taba masu Zarah sannan suka fita Bayan sunyi ma mum Allah kiyaye hanya..

Wani dan tasha ne ya shiga gaban ibtisam yana fad'in hjy Ina zaki, daka ta matsa saiya shiga gabanta "tace Malam ba tafiya bane

Yace y'an mata kina dakyau fah ko zan samu number

Tsaki taja tana k'okarin matsawa ya k'ara shiga gabanta

Zarah tace Malam lafiya kuwa?

Shima driver da yake gaba ya waigo yana kallonsu tare da dawowa

Wanda a dai dai lokacin NAJEEB ya k'araso wajan wanda yana Mota yana kallon abunda ke faruwa bayan ya k'araso kallon mutumin yayi tare da tambaya lafiya

Please Login or Register in order to submit comment