Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kake shiga gabanta!? Mutumin da bajin turanci yake ba yayi gaba Najeeb kallon ibtisam yayi itama akaci Sa'a shi take kallo wani irin mugun kallo ya Mata tare da fad'in idiot, kallon Zarah yayi tare da fad'in kuzo muje mu saukeku sai mu wuce Zarah da ibtisam bayanshi suka bi Mum tace a'a ya kuka dawo? Najeeb yace Mum zamu mu saukesu Mum tace ai mun koma baya, sai kuma mun k'ara dawowa fah, suje su shiga mota kawai mana, muda ga hanyar mu nan Yace Mum plz, muje ban son long magana plz Mum shuru tayi ba tare da ta k'ara cewa komai ba Najeeb kallon driver yayi tare da fad'in what are you waiting for? Driver yace nothing, "tare da tada motar suka k'ara kama hanyar zaria Cikin 45mnt suka k'arasa inda suka saukesu sannan suka Kama hanyar komawa kaduna dansu wuce Abuja Zarah ta kalli ibtisam tace Anya Najeeb baya sonki kuwa? Ibtisam tace kina da hankali kuwa zarah? Zarah tace da hankali na mana, kalla saboda ke fah yasa yace a Kawo Mu har skul, duk saboda abunda wannan mutumin yayi miki ibtisam yace badan ni yayi ba, karki k'ara fad'in haka, wlh a yanda dan uwanki ya tsaneni na tabbata ko fyad'e yaga wasu za suyi min bazai hanaba, kawai yayi hakan ne saboda ke Zarah tace ni kuma? Naga bani mutumin yayi ma Abu ba, ke akama Abu Ibtisam tace plz ya isa, ki daina min wannan maganan karki manta ni matar wani ce bikina saura wata d'aya so plz banso tare tajan tsaki tace ko maza sun k'are sai yayanki gwara in zauna banyi aure ba Tana fad'in haka tayi gaba cikin fushi....... Read and leave it, dnt share to anyone *IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI* *WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN* 3138831065 Firstbank Maryam Alhassan *SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY* *KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI* Zarah tsayawa tayi tana kallonta cikin mamaki, "lokaci d'aya tace ikon Allah, kai Indai ana son ganin fushin ibtisam toh a had'ata da Najeeb, ace sun dace, dariya Zarah ta saki lokaci d'aya sannan tayi gaba itama Koda ta k'arasa ganin ibtisam tayi dasu Aisha a cikin d'akin, "inda Aisha take tambayan ibtisam ina wannan handsome cousin din naki? Ibtisam tace Idan Zarah tazo ki tambayeta yayanta ne.... Shigowan Zarah ne yasa Aisha fad'in yauwa Zarah naji dad'in ganinki, "wlh tun jiya na k'osa ku dawo sai naga baku dawo ba, yanzu ibtisam ke fad'amin kunje kaduna ne Zarah tace eh bata wlh Aisha tace Zarah naga brother d'inki Kai Wlh ya had'u Sosai, plz ki had'ani dashi mana Zarah murmushi tayi cikin ranta tace aikam Indai Najeeb ne yafi karfinki domin keda kika watsar da kanki kizo kice kina sonshi, Allah ya kyauta, "amma a fili sai tace uhm karki bada mata mana Aisha tace Wlh Indai akan dan uwanki ne wlh zan bada mata kam, "Dan Allah Zarah ki had'amu dashi, "wlh sonshi kawai naji Inayi Zarah tace toh fah Aisha tace ki taimaka min da number d'inshi Zarah tace aishi baida number d'aya, domin baya zama waje d'aya Aisha tace miye aikinsa? Zarah tace pilot ne Aisha tace wow, Toh plz ki bani number d'inshi na Nigeria Zarah fad'a mata tayi, domin tasan indai Najeeb ne gata gashi Ibtisam kam sai taji tausayin Aisha ya kamata, ita ta rasa wanda take so sai wannan mara imanin, mara tausayi Wanda bai san darajan dan Adam ba, lalle Tana da aiki, inda tasan Waye shi dako kallo bai isheta ba, miye ma Abun so a tare dashi? Tsaki ta saki mara sauti Karfe hudu dai dai ibtisam ta tafi lecture wanda Dr jibril ne ya shigo musu, bayan ya gama lecture ya bu'kaci ibtisam ta sameshi a office Koda ibtisam taje office d'inshi tayi nocking, "bada izinin shigowa yayi Kai tsaye ibtisam ta bud'e kofar sannan ta shiga, "gaida Dr jibril tayi Idonshi na kanta ya amsa tare da nuna mata kujera ta zauna.. Ibtisam zama tayi Dr jibril baice mata komai ba sai rubutu da yayi tayi, a kalla yayi minti Goma yana rubutu sannan ya d'ago ya kalleta tare da kiran sunanta da Amina.. Amsawa tayi da na'am sir Yace Amina Mai yasa kike son bata rayuwarki? Koma ince kin bata, keda y'ar uwarki Kallon mamaki take mishi alaman bata gane abunda yake nufi ba Yaci gaba da fad'in, "koda kika ga ina biye miki, ina son hulda dake badan komai bane sai yanda naga irin nutsuwarki, da kunyarki, Ashe ba haka kike ba a cikin zuciyarki .... Amina a yanda na fahimta, koma ince gidanku kaman dakyar aka barki kika zo skul, na tabbata gidanku gidan tarbiya ne, koda ka irin firan da naji kinayi kwanaki keda granny d'inki, "is lyk ba'a son kizo skul but an barki kinzo shine kike son cin amanar iyayenki kika Fara bin kawayen banza Kece har tafiya kaduna Da sauri ibtisam tace sir bani d'aya naje ba, wlh nida Mum ne da Zarah Kallonta yayi cikin mamaki yace a wajan garage din Kawo na ganku kuna fitowa zaku shiga mota Ibtisam Labarin abunda Ya faru ta bashi, lokaci d'aya hawaye ya siraro mata, wanda bana komai bane sai na zarginta da yayi da Farko, Koba komai a zargi mutum abunda ciwo Sosai Dr jibril ido ya kura mata, yana kallonta yanda take hawaye, "lokaci d'aya ya sauke ajiyan zuciya tare da fad'in miye na kuka ibtisam??  Yau ce rana ta farko daya kirata da ibtisam Kasa magana tayi balle ta bashi amsa Dr jibril yace ibtisam abunda yasa na kiraki har nake fad'a miki haka, because ina miki kallon sister na, so am so sorry Kinga inda bakiyi min bayani ba zanyi ta miki wani irin kallo Ibtisam ta share hawayenta tare da fad'in hakane, ngd daka fad'amin Nan Dr jibril yaita bata shawara akan ta k'ara kame kanta akan kawayen banza, "daka karshe ya bata umarnin ta tafi, "koda ta tashi da ido ya bita har saida ta bace ma ganinsa Ibtisam da Dr jibril yanzu sun saba Sosai, har takanje office d'inshi tayi mishi tambaya wani zubin, "inda su Aisha suke fad'in soyayya suke ita da Dr jibril din Duk yanda ibtisam tayi musu bayani akan ba soyayya suke ita da Dr jibril d'inba sunki yarda Dan haka kawai ta barsu a haka dinne,. Su ibtisam Sun Fara exam gaba d'aya koda yaushe bata samun kanta saina karatu kullum suna cikin karatu ba dare ba rana Kabir ya kawo mata Katin biki danta rabama friends d'inta, "amma ibtisam ta'ki bama kowa, inda Zarah tace abama su Aisha Katin Ibtisam tace a'ah bata so ta gayyaci su Aisha, domin wlh Idan Abba ya gansu zaice da y'an duniya nake kawance Zarah taci dariya tare da fad'in Allah ya kyauta, "in mun dawo skul zasu San kinyi aure ai, zaki sha ciwon baki, suce baki fad'a musu ba Ibtisam tace karki damu Nasan yanda zanyi musu kawai Kedai kiyi shuru dan Allah karki fad'a musu Zarah tace shikenan, Nina k'osa ma muyi hutu wlh muje mu fara shiri dashi yanzu saura sati uku Ibtisam tace uhm nikam ko kad'an ban k'osa ba wlh Zarah tace uhm wai irin gulman nan na amare Ibtisam tace Wlh dagaske nake Zarah tace "kabir fah zaki aura masoyinki, Wanda kike so, kuma kike k'auna, wanda kuke burin mallakan junanku "ko yanzu dai an rage sonshi ne? Ibtisam tayi murmushi tare da fad'in ko kad'an, wlh Zarah ina matukar son kabir, tsantsar so nake mishi, bazan iya kwatanta miki irin sonda nake ma kabir ba, but zan iya cewa sonshi yana tafiya tare da jinin jikina ne, domin daka ranan da sonshi ya fita ina tunanin nabar duniya kenan, domin jinin dake gudana a jikina ya tsaya cak.... Zarah tace ikon Allah, haka kike son kabir din? Ah lallai Kabir yayi Sa'a Sosai Ibtisam murmushi tayi tare da fad'in, ko kuma kice Nayi Sa'a ba, domin na samu namiji kamili, bai tabamin maganan banza ba, wanda da yawa mazan yanzu in suka had'u da yarinya maganan banza ke kawo su Zarah tace hakane kam, sai dai muyi fatan Allah ya had'amu da maza na gari Ibtisam tace Allahumma Ameen. Kullum Aisha bata da hira yanzu saina Najeeb tare da k'ara fad'a musu yanda take sonshi, da kuma irin haduwarshi, gashi kullum ta kira baya d'auka Shi kam Najeeb a duniya ya tsani yaga aita kiranshi da yawa, sai yaji kawai baya bukatar d'aukan wayar, domin kuwa a cewarshi Indai aka kira mutum sau d'aya sau biyu bai d'auka ba, saika barshi yana uzuri, inya gani zai kira, "amma bawai kaita kira ba, yana ganin kira da wata number wanda bai sani ba, baya d'auka ne kawai saboda baya son yawan kira, sannan yasan koma Waye mistake din number yayi domin Najeeb waya Sani a Nigeria balle ya kirashi, duk Wanda ya sani yana da number d'insu, saina ibtisam dana Granny da baida shi. Najeeb wannan karan shi d'aya yazo, ba tare da y'an matanshi ba, dan haka sai yaji kwata kwata baiji dad'in k'asar ba, dan haka ya yanke zai koma jibi kawai. Ranan dasu ibtisam sukai hutu harna wata d'aya da sati d'aya, haka suka dinga sallama da kowa, yayinda wasu ke murna zasu gida, sukam irinsu Aisha haushi sukeji, domin Sun san idan suka koma Gida babu runs, dole a kame Kai sai an dawo skul Ibtisam office din Dr jibril taje amma bata sameshi ba, dan haka ta tura mishi message da fad'in "sir I come to your office but you are not around, "nazo Nayi sallama, but mun wuce sai an dawo skul, Tana fad'in haka ta tura mai sa'kon sannan ta wuce tare da saka wayan cikin jaka Ibtisam da Zarah motar Haya suka shiga, inda suka tafi Kano, domin dai Zarah tace Tana tare da ibtisam tunda biki ya matso. Koda su ibtisam suka isa Gida, basu suka kaiba saida yamma, gaba d'aya a gajiye suka k'arasa gida, domin motar da suka shiga batai wani gudu Sosai ba Granny ganin su ibtisam da zarah yasa ta saki gud'a tare da fad'in kunga Amarya wajan kabiru Ibtisam da gudu ta nufi Granny din tayi hugging dinta tana fad'in wayyo Granny I miss you so much wlh Granny tace karki karyani miye kuma nis ziyu Dariya ibtisam da Zarah suka saki, sannan ibtisam tace Granny ina nufin Nayi kewarki da yawa Granny tace au yanzu na gane Nan sukai ciki inda suka zauna a falo sunata fira harda ummi. Koda ibtisam suka shiga d'aki ta ciro wayarta cikin jakarta Wanda tunda ta saka wayoyinta cikin jaka bata K'arabi ta kansu ba, sai yanzu, ganin misscall  d'in Dr jibril tayi har guda biyu, sannan message d'in da shima yayi mata kaman haka... Plz just give me 5minnute muna meeting, I need to see you before you leave. Koda ta gama karantawa ido ta lumshe alaman kash mai yasa nasa wayar cikin jaka? Gashi banji kiranshi ba and banda message d'inshi ba, kiranshi tayi amma taji baya shiga har sau biyu tana kira amma not reachable dole ta hakura ta barshi Tun daka ranan da ibtisam ta dawo aka fara Mata gyaran jiki, su dilka Gefen maganin Mata kuma Granny tace baza'a bata wani abu Sosai ba, tunda budurwa ce, kar a wahalar Mata da jika, gwara inta tare da sati biyu sai ta Fara shan maganin Mata, granny Tana gyara ibtisam Sosai, kaman yau ibtisam da Zarah na zaune saiga Granny da wani magani tazo tana fad'in firan Mai akeyi ne haka? Zarah tace firan duniya mukeyi da kuma yanda biki zai kasance Granny tace ai ranan saina taka rawa, "lokaci d'aya kuma ta saki gud'a Ibtisam dariya ma Granny ta bata, tare da fad'in ai dole ki taka rawa tunda burinki ya cika za'ayi min aure, kinyi nasara Granny tace Wlh kuwa, kaman kin sani, yarinya ai bazaki gane ba, sai an d'aura kin shiga daka ciki, zaki gane banbancin aure da kuma rashin aure, "wlh ibtisam babu abunda yakai dad'i yau a duniya kaman ace mutum na d'akin mijinshi, cikar mutum saida iyali, "yau ki duba koda namiji ne In baida iyali duk dukiyarshi sai kiga ana mishi wani kallo, in ba'ayi wasa ba sai kiga ana zargin mutum, wanda ba komai yaja mishi ba sai rashin iyali da bai dashi Zarah tace Wlh hakane Granny ai cikar mutunci shine gidan miji, sannan in mutum Nada aure ana mutunta shi Sosai, fiye da wanda bai dashi Granny tace yauwa y'ar albarka, "Kema Bari a Gama na takwarata sannan in dawo kanki keda wancan dan banzan miskilin, ni naji ance yazo yana nan koya koma? Zarah tace kaman yana nan fah, dan munyi waya dashi d'azu amma yace cikin week dinnan zai koma Granny tace saboda tsiya bazai tsaya Ayi auran ibtisam ba, Kafin ya koma? Zarah tace Granny ai saiki kirashi kice karya koma ya jira Granny d'auko yar karamar wayarta tayi tana fad'in kiramun mamanki tare da mi'ka ma Zarah wayar Zarah saka number d'in Mum tayi tare da dialing number din sannan ta mi'ka ma Granny Ringing uku Mum ta d'auki wayar tare da sallama, tana gaida Granny Granny amsawa tayi, tare da fad'in "Ina miskili? Mum tace yana d'akinsa...  Yauwa gashi ya fito ma in bashi wayar ne? Granny tace a'a koya amsa wayar Mai zaice? Koni Mai zance Mai tunda ba yaran juna muke jiba Mum dariya tayi tare da fad'in hakane Mama, Yadai kamata ki koya wannan yaran na Najeeb Granny tace wa? Allah ya kyauta barni da nawa Yaran, kina jina? Mum tace eh inaji Mama Granny tace ki fad'ama miskili ya tsaya Ayi bikin ibtisam Kafin ya tafi, "naji Zarah tace Zai koma.... Kallon Zarah tayi tace yaushe ma kika ce zai koma? Fassara min d'azu naji turanci kikayi Zarah dariya ta saki sannan tace cikin satin nan, "Granny tace yauwa kina jina Mum da itama Dariyar takeyi tace eh inaji Granny tace cikin satin nan zai koma, kice ya tsaya Ayi bikin dashi, dan naga shi baya son zumunci sai rashin mutunci ya iya Mum tace zan fad'a mishi yanzu sannan sukai sallama da Granny Mum kallon Najeeb tayi dake zaune yana danna waya, tace Najeeb yanzu mukai waya da Mama Kallon Mum alaman wace Mama kuma? Mum kaman tasan abunda yake nufi tace da Granny mukai waya, tace in fad'a maka ka jira Ayi bikin ibtisam dakai Tsaki Najeeb ya saki tare da fad'in that old woman sai kuma ya kuma sakin wani tsakin tare da fad'in bazan tsaya ba akan Mai zaisa in tsaya? Mum ki fad'a mata nace bazan tsaya ba, ina ruwana da wani biki? Miye nawa a ciki da zan tsaya? Plz Mum ni inada abunyi Mum tace Najeeb bikin y'ar uwarka nefa za'ayi, kake fad'in haka Yace Mum banda business da bikin, saboda biki sai inki tafiya wajan aiki? Mum tace zaka iya d'aukan excuse ai Najeeb, inaga hakan zaiyi NAJEEB yace no Mum gobe zan koma, bazan zauna ba, sannan aure kuma Allah ya bada zaman lafiya, I have nothing to do with d weeding infact yarinyar da bata da kunya why will I have to attend her wedding Mum tace toh fah, kai kowa kace baida kunya?lallai kam amma k'aryar mutum yace ibtisam bata da kunya yarinya mai ladabi Najeeb tabe baki yayi Mum taci gaba da fad'in aure ne dai kace bazaka tsaya ba, amma kar ka k'ara fad'in cewa ibtisam bata da kunya domin kuwa tana dashi Sosai ga girmama na gaba Najeeb yanda Mum take Yaban ibtisam sai Abun ya bashi mamaki da dariya kuma, cikin ranshi yace Mum bata san wacece wannan yarinyar bace, green snake kenan Hhhhh kunji NAJEEB wai ibtisam ce green sneak Granny Bayan ta gama wayar ta mi'ka ma ibtisam maganin dake hannunta, tace gashi Kinga nama manta na tsaya fira gashi ki dinga tsarki dashi ibtisam tace Granny miye wannan kuma? Granny tace maganin sanyi ne, kin San yanzu idan Mace Nada sanyi saiya rage mata ni'ima, kiga miji yana Abu da mata baya jin dad'i Ibtisam kam kunyar maganan Granny taji Granny ta lura da hakan tace yama kuke kiran abunda da turanci? Zarah tace infection Granny tace yauwa shi, ai mugun ciwo ne, kusan yawanci mata na d'auke dashi, wasu sun sani wasu basu sani ba, sai dai muce Allah ya kiyaye, "Dan haka ke ibtisam saiki Fara maganinshi NOTE: yana dakyau in yarinya zatai aure tayi treating infection, kije hspt a dubaki aga ko kina dashi, ko baki dashi, inko kina dashi ki nemi magani Kafin aure, domin infection yana rage ma mace ni'ima Sosai, bawai aita dura ma yarinya maganin Mata ba, a'ah ku nema Mata maganin sanyi, domin duk maganin da zaku bata babu abunda zai Mata Indai tana da infection, domin yakan saka ni'imar mace ta daskare, gashi kunyi ta dura mata maganin Mata, wanda zai tursasa ni'imar fita, gashi tana da infection ya'ki fitowa sai yaita sama yarinya ciwon ciki da sauransu, "so plz maganin Mata bashi bane, Nop kuyi maganin infection shine babban matsalan, da yawa Mata na complain akan matsalan wata tace tayi na asibiti baiyi ba wata tace tayi na gida shima baiyi ba, y'ar uwa saifa kin dage, domin infection ba lokaci d'aya yake tafiya ba, shigarshi baida wuya amma fitanshi akwai wuya, musamman masu abokiyar zama, inke kina magani keda miji, ita abokiyar zamanki batayi Kinga infection bazai barki ba, sai dai ya ragu, so mata ku daina wani rubibin siyan kayan mata, just ki tsaya ki nemi lafiya daka wannan cutar ta infection Najeeb kam kaman yanda Ya fad'a Washe gari yabar k'asar domin shidai bazai iya zama ba, gashi babu giya babu y'an mata, dole yasa ya koma inda yafi wayau An fara hidiman bikin ibtisam da Kabir, ibtisam tayi wani mugun cikowa, tare da wani haske Tana shinning, lallai anyi mata gyara ko Ince ana kanyi, ibtisam gaba d'aya ta saki jikinta Sosai ana hidiman da ita, dan tasan Kabir bata da matsala dashi akan karatun ta. Yau za'a kawo kayan akwati  dan haka ibtisam da Zarah suka bar gidan gaba d'aya, suka shiga kasuwa, Dan suyi siyayya Zarah da ibtisam suna wani shagon siyan Gyale domin Zarah zata siya, saiga kiran Dr jibril ya shigo wayan ibtisam mamaki tayi domin tunda ta kirashi baije ba tun sanda sukai hutu bata K'ara kira ba, dan haka ta d'auka tare da sawa a kunnenta Tace ina wuni sir? Dr jibril ya amsa da lafiya Amina, ya gida hope ana karatu a gida? Ibtisam tayi dariya tare da fad'in eh munayi sometimes Yace sometimes kuma? Tace eh sir kasan ba kaman a skul ba,  nan mutum yana gida, koka Fara wani abun zai taso dole ka bari kaje kayi, ga kuma Aiki, Kaga duk a skul babu wannan Yace you are right, I just call to say hi Ibtisam tace nagode sir, tare dayi mishi sallama Zarah ta kalli ibtisam Bayan ta kashe wayan, tace Dr jibril neko? Ibtisam tace eh Zarah tace yasan ko zaki aure kuwa Ibtisam tace a'a nifa babu wanda ya Sani a skul Zarah tace inaga yana dakyau ki fad'ama Dr jibril zaki aure Ibtisam tace akan wani dalili zan fad'a masa? Zarah tace saboda wlh mutumin nan koda bai fad'a ba, sonki yakeyi Tsaki ibtisam taja tare da fad'in kema kin Fara biyema su Aisha koh?.. Zarah tace ba haka bane, na dad'e Ina nazari akai, amma ina Mai baki shawara ki fad'a Mai zaki aure domin.... Toh wai miye na boye boyen zaki aure ne ma Ibtisam tace Kinga malama biyashi kud'inshi mu tafi inada abunyi Zarah tace uhm Allah ya kyauta tare da biyan kud'in gyalen suka fita Shop rite, suka je daka kasuwa, inda suka fara siyayyan kayan za'ki, duk dan su bata lokaci kar suje gida da wuri, tunda 4 akace za'a kawo akwatin. Y'an Kawo lefe Sun kawo akwati goma sha biyu, aka kawo set biyu kenan, gaskiya kabir yayi k'okari domin ya zuba kaya na Kece raini, anba ma y'an Kawo akwati abunda aka tanada na ciye ciye tare da kud'i wanda ake badawa na tukwici Au ibtisam sai wajan 6 suka dawo gida a gajiye, suna shiga toilet ibtisam ta fad'a domin tayi wanka, dan KABIR yace zaizo anjima ita kam zarah kayan akwati ta tsaya gani tana fad'in ibtisam anyi goshi gaskiya kayan sunyi kyau, domin kaya ne masu tsadan gaske KABIR yasa ma ibti d'inshi Koda ibtisam ta fito daka wanka, bata koje inda kayan lefen suke ba, domin kunya takeji, Toh akan wani dalili ma zata tunda Nata ne, kuma tare dasu za'a kaita Wajan karfe 8 da wani abu saiga kabir yazo wajan ibtisam, kiranta yayi a waya tare da fad'in ina waje Fita tayi Kai tsaye hijab ne a jikinta domin wando tasa da top saita d'aura hijab, "Kai tsaye cikin motarshi ta shiga inda ta ganshi shi d'aya tace yazo su shiga falon ba'kin dake gidansu. Kabir yace a'ah nazo ne kawai na ganki, in wuce Nayi missing d'inki Sosai Murmushi ibtisam tayi tare da fad'in yaushe ma ka shigo Kano baka fad'amin ba sai d'azu naji ka kira zaka zo. Kabir yace Wlh Ina zaune kawai naji Ina son ganinki Ibtisam murmushi tayi tare da satan kallonshi taga shima ita yake kallo Da sauri ta juya tare dayin k'asa da kanta Kabir kam dariya yayi danya ganta sanda take kallonshi domin idonshi na kanta, "a hankali yace ibtisam bazaki iya kallon mijinki ba na wani lokaci? Uhm kawai tace tare dasa hannunta a fuska ta rufe tana murmushi Jin hannun Kabir tayi akan hannunta ya ri'ke yana k'okarin cire mata hannunta akan fuskanta Gabanta taji ya fara dukan uku uku, domin tunda take dashi Bai taba Taba mata jiki ba sai yau, harya cire mata hannun nata daka fuskanta kanta a k'asa ta kasa koda d'aga kanne domin ta rasa mai takeji a halin da take yanzu Hannunshi yasa ya d'ago Mata da fuskanta tare da juyo da fuskan Nata tana kallon nashi, ido suka had'a, da sauri ta lumshe idonta domin bazata iya kallon idonshi ba dan ko yanzu data kalla saida taji wani irin mugun faduwan gaba Shiko kabir idonshi na kanta, wani irin sonta ne ke fusganshi ji yake kaman yayi hugging d'inta, "lokaci d'aya ya saki murmushi tare da kiran sunanta da ibti plz open your eyes I need to see it Ibtisam bata bud'e idon ba,haka bata motsa ba, domin gaba d'aya jikinta a mace yake tunda kabir ya tabata, mamaki take cikin ranta tare da fargaba, ko ince sabon al'amari daka Kabir din data gani yasa ta kasa wani kwakwaran motsi. Kabir kam har yanzu idonshi nakan fuskan ibtisam yana kallonta, wanda idonta yake a lumshe, lokaci d'aya yasa bakinshi cikin nata ya fara kissing d'inta Ibtisam da sauri ta bud'e idonta tare da k'okarin tureshi amma ta kasa, a kalla yayi wajan 2mnt yana tsotsan bakinta, tun tana tureshi harta Fara hawaye..... Lokaci d'aya ya saketa. Ibtisam ganin ya saketa yasa ta Fara k'okarin bud'e kofar amma ya danna luck, wanda kofar ta kasa buduwa Kuka ta saki Sosai tare da fad'in ka bud'emin kofa in fita Kabir janyota yayi jikinshi K'okarin tureshi ta farayi amma ya ri'keta dakyau wanda yasa ta kasa kwatan kanta, dole yasa ta tsaya tare da k'ara kwantar da kanta akan jikinsa tana kuka A hankali yace am so sorry my ibti, na kasa controlling kaina, plz forgive me, sonki yasa nayi hakan amma ba halina bane ibtisam Bata ce mishi komai ba, sai dai kukan da takeyi yad'an lafa, ba kaman daba Nan yaci gaba da rarrashinta, cikin ranshi kuwa k'ara godema Allah yayi domin ya tabbata ibtisam

Chapter 17 of 46