Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutuncin y'a mace

Ibtisam tace toh yanzu Mai kike nufi?

Granny tace babu komai, nidai Wlh bason wannan karatun nake ba kum....

Ibtisam tace ya isa haka, yanzu naji zance Wlh Granny ki daina min irin haka, bafa naso, kowa na karatu duk cikin jikokin ki amma nice kad'ai kika sama ido.

Granny tace Suwa suke karatun?

Ibtisam taja tsaki tare da fad'in Zarah bata karatu? Koshi NAJEEB baiyi karatu ba, ko Ahmad baya makaranta?

Granny tace kinma uwarki tsaki bani ba, shi miskili aiya gama tun tuni, baki ga illar da karatun Yaja mishi ba? Sai rashin Kunya babu abunda ya iya, sai raina mutane.

Sannan ita Zarah AI kin girmeta, yanzu AI abun kunya ne, mu Hausa Fulani ace kanwa ta Fara aure yaya batayi ba, ai sai Ayi dakai.

Sannan Ahamd Dan k'aramin yaron ne za'a mishi aure? Tunda a garin mahaukata muke ba.

Ibtisam tace oho dai, kwata kwata shekara d'aya naba Zarah, "sannan ni Wlh ba Abun kunya bane dan wacce na girma ta rigani aure ba, tab lallai ma Granny, Toh kunyar Mai zanji, Bayan nasan aure lokaci ne?

Granny ta cabe da fad'in ina ko zakiji tunda baki Santa ba, ni Wlh kina bani tsoro.

Ibtisam tace ke kika ga wannan, shifa aure lokaci ne, "amma ku Hausa Fulani saiku dinga ganin kaman mutum ne baya son yi, Yooo koda ina son inyi auren ai ban isa inyi ba sai lokaci yayi, "amma duk kubi ku damu mutum ya'ki aure ya'ki kaza "wlh ku cire al'ada ku Kama addini.

Granny tace uwarki muka Kama Inba addini ba?

Ibtisam tace al'ada mana, wacce kuka maidashi kaman addini

Granny tsaki taja tare da fad'in na fiki sanin aure lokaci ne, "amma da niya ba, tunda in baka da niyan aure taya lokacin zai zo?

Ibtisam tace nifa Kinga Granny ban son surutu, kawai ki tafi ki barni.

Granny tace oho dai, aure dai nan da wata biyar, zamu Kai mutum Dan ubansa ko baya so, dole ya zauna, "sai muga boko ai

Tsaki ibtisam taja tare da fita ta nufi falo tabar Granny a nan, tana fad'in "Aiko mutuwa za kiyi sai anyi wannan bikin yarinya kaman Mai iska

Koda ibtisam ta fito falo gaida Dad tayi cikin girmamawa.

Dad amsawa yayi tare da fad'in ina fatan kin shirya mu kama hanya koh?

Tace eh na shirya

Yace toh d'auko kayanki kikai Mota driver yasa miki a booth muzo mu wuce

Tashi tayi ta koma d'aki inda ta iske Granny itama na k'okarin fitowa sukaci karo

Granny tace au fadar dani zakiyi?

Ibtisam tace sorry ban ganki bane

Granny tace miye soro?

Ibtisam tace kiyi hakuri nake nufi

Granny tace yau naga tsiya, kefa tunda zaki tafi wannan makarantar kike nuna mana isa isa, kike ganin kin isa damu, wuyanki yayi kauri

Ibtisam ta Lura da Granny fushi takeyi dan zata skul ta barta, dan haka dariya kawai tayi ta wuce, ciki

Granny tayi gaba tana mita

Ibtisam d'auko kayanta tayi ta fita dashi taba driver yasa mata a booth

Granny na zaune a falo tana ta galla mata harara,"ibtisam kam dariya takeyi k'asa k'asa.

Abba ya kira sunanta da mamana

Tace na'am Abba

Yace toh Ina son ki sani, kin San yanzu dake da matar aure banbanci kad'an ne? "kin San mai yasa nace haka?

Ita matar aure an d'aura aure mutane sun shaida, dama shi aure shaidu yake bukata

Idan aka bada sadaki, sai shaidu kuma

Toh ke mun amsa sadakin ki, saura shaidu kawai su shaida, ina son ki sani mun amsa kud'in sadakin ki domin munba Kabir ke, kuma munyi bincike dan gidan mutunci ne, ina son kiji tsoran Allah koda Kinje makaranta karki kula kowa, sannan ki kame kanki, karki manta inmu bama ganinki Allah yana kallonki shida ya halicceki , "sannan ba tsoranmu muke so kiji ba, face kiji tsoran Allah daya halicceki

Sannan shi mutunci madara ne, idan kika kama kanki babu wani mutumin banza dazai zo miki, amma idan kika banzatar da kanki toh ko wani irin mutum zaizo gareki, "sai kiji ana fad'in tana da farin jini wanda ba haka Abun yake ba, yawan samari ga d'iya mace ba alkairi bane "bazan tsaya miki dogon magana ba koh bayani ba, Nasan kina da ilimin addini, abunda zan fad'a miki a matsayina na mahaifinki shine kiji tsoran Allah a duk inda kike, Allah yayi miki albarka

Ibtisam wani irin hawaye ne ya zubo mata, tare da amsawa da Ameen

Ummi tace toh Allah ya taimaka abbanki ya Gama cewa komai, sai dai in k'ara da komai kike bukata, bamu ce ki tambayi kowa ba, ki kiramu zamu baki, koda kuwa wanda zaki aura karki tambaye shi, domin har yanzu nauyinki na kanku, tunda kina gabanmu, "Allah ya bada Sa'a, yayi miki albarka

Ibtisam ta amsa da Ameen

Dad yace Toh Bari mu kama hanya,tare da tashi

Abba kudi yaba ibtisam dubu ishirin tare da fad'in gashi ki ri'ke wannan, ya kamata ki bud'e account

Tace Nagode Abba, tare da fad'in zan bud'e insha Allah "Zarah Nada account in za'a min sa'ko sai inyi amfani da nata

Abba yace hakam yayi

Granny tace Allah ya kiyaye hanya, Tana fad'in haka tayi ciki Tana y'ar share kwalla"yau ibtisam zata karatu ta barta ita d'aya bata da abokiyar hira, " Granny kaf jikokinta babu wanda take so kaman ibtisam sai kuma miskili duk tafi son su.

Su Abba da ummi har waje suka rasa Dad, inda Abba yake fad'in wannan makarantar dai mama bata sonshi

Dariya Dad yayi yace kasan ita mama bazata gane muhimmancin ilimi ba, gani take duk Wanda yayi ko zaije Tana mishi kallon d'an iska, kuma ba haka Abun yake ba, duk da akwai Mara sa ji, Aiba duka aka taru aka zama d'aya ba

Abba yace hakane, Amma yaran dai sai a hankali, kasan muke kasuwa, muna ganin yara y'an makaranta Wanda suke zuwa siyan kaya, in kaji irin firansu babu kamun kai, kai Abun dai sai Addu'a, Allah dai ya shirya mana zuri'a

Dad ya amsa da Ameen

Ibtisam da dad suka shiga mota, ibtisam ita da Dad duka baya suka zauna "Da gaba zata shiga Dad yace ta dawo inda yake, dole ta koma ta zauna dashi a baya, suka Kama hanyar zaria



*ABU ZARIA*

Bayan sun isa cikin makarantar, Dad kiran Zarah yayi a waya tare da fad'a mata ta fito waje yana kusa da hostel d'insu .

Tace OK Dad amma baka fad'a min zaka zoba? Gani nan zuwa. My Dad kayi min surprise visit, Tana fad'in haka ta kashe wayan

Dad bayan ta kashe wayan kallon ibtisam yayi tare da fad'in dama bata san zaki zoba yau?

Tace eh bamuyi waya ba

Dad yace sai yasa take mamakin zuwa na

Zarah ce ta fito, cikin jallabiya tare da yafa gyalen jallabiyan akanta, bud'e kofar motar yayi ganin ibtisam yasa ta saki ihu tare da janyota ta fito daka motar "rungumeta tayi tana fad'in wayyo yau ina cikin farin ciki.

Dad shima fitowa yayi, yana fad'in shine tun Farko baki fad'amin an hanata zuwa skul ba?

Zarah tace Dad wlh kwata kwata na manta, kuma nasan inda na fad'a maka daka sa Abba ya barta,"and abunda yasa ma ban damu in fad'a maka ba, ta fad'amin yanda sukayi da kabir sai yasa.

Dad yace Toh shikenan, gata na Kawo ta, sai a d'age da karatu banda wasa, musamman ke ibtisam da aka wuceki wajan sati biyu da wani abu yanzu, saiki dage da karatu Sosai

Ibtisam tace insha Allah zan dage sosai

Dad yace Toh Allah yayi muku albarka

Su duka suka amsa da Ameen

Dad ya kalli Zarah yace Mai kike bukata Zanzo in wuce,

Tace Dad inada kayan abinci,kasan da yawa na siya mana, tunda mu biyu ne, sai kuma Abba ya hana ibtisam zuwa, so yanzu tunda ya yarda wlh nafi kowa murna "ni yanzu Dad kud'i kawai zaka bamu

Dad yayi murmushi tare da bud'e Mota ya bud'e wani k'aramin akwati ya d'auko kud'i ya mi'ka ma zarah da ibtisam yace ko wacce ga 100k sai ku dage da karatu banda wasa, sannan banda bin kawayen banza

Ibtisam tace mun gode

Zarah tace insha Allah Dad zamu dage

Yace toh Bari mu kama hanya

Driver ya ciro ma ibtisam kayanta daka cikin akwati, "Zarah ta tayata d'auka sukai cikin d'akinsu inda hauwa ke kwance ke bacci

Ibtisam kallon d'akin tayi gado ne guda hud'u, sama da k'asa, d'akin ba wani girma gareshi ba, sai kayan sawansu dake akwati, dana abincinsu sai su gas Mai had'e da cylinder.

Gadon ibtisam dana Zarah sama da k'asa, ibtisam tace ita saman take so, tare da fad'in kar indau k'asa Zarah ki fadomin akai

Zarah ta kwashe da dariya tare da fad'in sai kace wata giwa

Dariyan Zarah ne ya tashi hauwa dake faman baccin gajiya

Hauwa tace Zarah kinyi Bakuwa ne?

Zarah tace itace cousin d'ina da nake fad'a muku, gashi yau tazo skul

Hauwa tace eyya sannu da zuwa, ibtisam koh?

Ibtisam tace eh haka Sunan yake

Hauwa tayi dariya tare da kallon ibtisam sama da k'asa, lallai wannan Tana dakyau zatai kasuwa, but sai dai na ganta da hijab, Allah yasa dai ba y'ar saka hijab bace

Ibtisam cire hijab d'inta tayi tana fad'in Wlh na gaji Sosai

Idon hauwa na kanta, ba komai take tunani ba, sai inta had'a ibtisam dana miji zata samu kud'i

Hauwa tayi caraf tace ai Wlh ana zafi ma, gwara ki cire kisha iska ga gajiya duka
.ibtisam tayi murmushi tare da fad'in Wlh kuwa yau naga garin kaman za'ayi rana, "koda yake naga is lyk kaman ke baki fita ba, tunda naga yanzu kika tashi daka bacci.

Hauwa tace Aifa kam, yanzu na farka

Bud'e kofar akayi aka shigo dan basu rufe ba.

Aisha ce ta shigo hannunta ri'ke da y'ar jakarta, fad'awa tayi kusa da hauwa tana fad'in Washhhhh Na gaji Wlh "tare da kallon hauwa tace ke kin had'ani da jarabban mutumi gashi ya daure min hannu da kaca, babu daman in tureshi, gashi shegen hariji, Kinga irin cin da yayi min kuwa? "amma wlh ke y'ar iska ce hauwa da baki fad'amin ba, cikin dare yayi wajan sau hud'u ko biyar zance ma? ni nama manta wlh saboda tsabaragen Wahala, gashi cin hauka yake ma mutum yana wani buga maka banana cikin hq kaman ana buga guduma akan k'arfe

Hauwa dariya ta saki tare da fad'in sai yasa naki zuwa ai,.

Aisha tace Aida kin fad'amin irin cin da yake ma mace Aida banje ba wlh, duk da ina neman kud'i gashi wai shegen dubu hamsin Yaban duk wannan cin da yayi min

Hauwa tace toh Ina laifi kin samu 50k Kinga saiki saka ruwan dumi ki gasa wajan

Dariya Aisha tayi tace uhm ai naga rayuwa wlh, na ciyu iya ciyuwa wlh, Amma yanzu tunda na samu kud'in babu laifi Kinga anjima in Naje club na samu na drinks

Dariya suka saki, hauwa tace nima kya siya min, "yauwa Ina kaso na? Dubu ishirin din?

Tsaki Aisha taja tare da fad'in kin manta duba d'ari ne, "bude jakarta tayi ta kirgo dubu biyu ta mi'ka ma hauwa tana fad'in gashi

Hauwa ta amsa Tana fad'in raba mugu da makami ibada ne

Aisha tace au nice muguwar?

Hauwa tace a'ah Indo

Aisha kallon ibtisam take da take ta faman kallonsu tana mamaki, tace wannan black beauty dinfa?

Hauwa tace itace cousin din Zarah yau tazo..

Aisha tace eyya ibtisam koh?

Hauwa tace eh ita

Aisha ta kalli ibtisam tace sannu ibtisam kice yau kika shigo skul din?

Ibtisam tace yauwa, "eh wlh yau na shigo

Aisha tace naji ai course d'aya muke karanta, medicine department dinmu d'aya, karfe 4 muna da lecture saiki shirya, domin shegen lecturer dinnan baya wasa, inya rigaki shiga kin bani, domin wlh ko zaki mutu baki shiga, gashi shegen shi babu ruwanshi da mata, balle mukai kanmu ko nono ya taba.

Hauwa dariya tayi tace Tab, sai yasa naga bakya wasa da course d'inshi, duk inda kika je indai zai shigo sai inga kin dawo..

Aisha tace ba dole ba, in dawo ba, "nifa duk iskanci na, ina son in fita da First Class,in ban samu ba sai ince second class.

Ibtisam da Zarah kam jinsu suke, ita Zarah firan nasu baya bata mamaki danta saba, jin Wanda yafi wannan ma

Ita kam ibtisam mamaki take, yanda suke ta sakan zanje, lallai dole maza suce macen da take jami'a idonta ya bud'e, Allah dai ya kyauta, danna wayarta tayi karama taga 3:30 tashi tayi ta d'auko akwatinta ta bud'e ta d'auko wata jallabiya milk colour, da gyalenshi domin ta shirya dan tana fashin sallah

Zarah tace Mai zaki ci?

Ibtisam tace na koshi saida muka biya muka ci abinci Kafin muka karaso

Zarah tace au na manta Ashe da Dad kika zo, nake wani tambayar Mai zaki ci, dama Nasan Dad dole ya siya muku abinci

Hauwa tace OH dama Dad d'inki ya Kawo ta? Shine baki kirani IN gaidashi ba?

Zarah tace naga kina bacci ai shi yasa

Karfe hudu saura Aisha da ibtisam suka nufi lecture inda suka tarar lecturer din bai shigo ba, hakan yasa ibtisam sauke ajiyan zuciya,.

Karfe hudu dai dai sai gashi ya shigo din, saurayi nema, ba wani babba ba, ita ibtisam tasha ko zata ga babban mutun irin wanda ya manyanta sai taga matashi, wanda bai wuce sa'an Kabir d'inta ba

Lecture ya farayi musu, ibtisam gaba d'aya hankalinta nakan abunda yake musu, wannan ne shigarta na farko class, gashi kuma an wuceta, shi yasa gaba d'aya ta maida hankalinta wajan Dr jibril, domin sauraran abunda yake musu

Lokaci d'aya yace zai basu text yanzu kuma 20mrk

Ibtisam ido ta zaro tare da furta na shiga uku cikin ranta, yanzu mai Zan rubuta?

Idonshi ya sauka a kanta kaman zaiyi magana kuma saiya basar

Ibtisam kam gaba d'aya tsoro ya hanata komai, gashi ance baya wasa, dan haka kawai ta tashi ta fita tabar class din domin tasan kota zauna ta rubuta babu abunda zata ci, toh maima zata rubuta ita da yau ta Fara attending lecture

Ido Dr jibril ya bita dashi.........









Read and leave it, dnt share to anyone


*IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI*

*WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN*

3138831065 Firstbank Maryam Alhassan

*SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY*

*KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI*



Koda ibtisam ta fita zama tayi wajan wata bishiya, ta kifa kanta akan giwowinta, ba komai take ba sai takaici yanzu zatai asaran har 20mark, "wani irin tsaki taja Mai sauti, tare da fad'in na shiga uku

Shiko Dr jibril, ganin yanda ta fita da sauri Abun ya bashi mamaki, "lokaci d'aya kuma ya d'aga kafad'a alaman I don't care, ya basu text din tare da cewa 5mnt kawai ya basu 

Nan suka fara sauri, Kafin time ya cika, domin yana da wani hali, idan time din daya baku ya cika, indai yace kuyi submitting yaga wani yana rubutu to bazai amshi nashi ba, "irin lecturer dinnan ne masu shegen tsanani da ka'ida, sannan basa wasa.

Lokaci na cika yace time off

Duka suka tsaya

Koda Dr jibril ya fito a inda ibtisam take zaune a nan ya ganta kai a kife, ".wucewa yayi ba tare daya kulata ba

Aisha ce ta fito tana fad'in ibtisam ya zaki fita? 20mrk fah.

Ibtisam tace in ban fita ba, mai zan rubuta?  " karki manta fah yau na fara attending lecture maina Sani dazan rubuta?

Aisha tace ai bazaki rasa abunda zaki rubuta ba, wlh Nasan ko 5 zakici, amma ki tashi ki fita, "baki ga yanda yake miki kallon mamaki ba da yaga Kin fita ba.

Ibtisam tace uhm, ni yanzu Ina son ki taimaka ki koyamin abunda akayi baya

Aisha tace bari in had'aki da wani, yaron kuru ne akwai brain, saiya taimaka miki, domin ni bako wani lecture nake shiga ba

Ibtisam tace OK, tare da tashi

Tafiya sukayi inda suka koma class din da sukai lecture da yawa sun fita, wajan wani guy Aisha ta tsaya tare da kiran sunanshi da salis

Ya d'ago yana fad'in Aisha manya, ya akayi?

Tace lafiya Wlh, ga kawata yau ta Fara zuwa lecture, kasan tayi missing abubuwa, shine take son ka taimaka mata

Salis yayi dariya tare da fad'in Aiku manya ne, Aisha, ko baku shiga lecture ba zaku wuce

Aisha tace uhm wani ko bamu shiga lecture ba, kana ganin Indai wannan Dr jibril din zaizo dolen mutum yayi attending ko yaci ubansa

Dariya salis yayi,tare Da kallon ibtisam yace ya Sunan dalibar tawa?

Murmushi ibtisam tayi tare da fad'in Ibtisam

Yace wow Sunan larabawa, nice name,"Toh amma naga sanda akace za'ayi text kin fita, kuma banga kin dawo kinyi ba

Ibtisam tace uhm toh mai zan rubuta inna zauna?

Salis yace AI bakya rasa abun rubutawa ba, da baki fita ba, "amma tunda ya faru yanzu dai zamu fara saiki dage Sosai

Tace insha Allah

Aisha tace ni zan koma, na gaji ga yunwa, inkun Gama saimu had'e

Ibtisam tace Wlh bazan gane hanya bafa. "koda yake ga salis zai rakoni

Aisha tace waya fad'a miki maza na shiga hostel din mata?

Ibtisam tace toh fah, wlh ban sani ba, ashe ba'a shiga

Aisha tace eh, amma mata na shiga hostel d'in maza

Ibtisam tace Kai tare da zaro ido, alaman mamaki, lallai duk macen data shiga na maza ta bani....

Aisha ta Katse ma ibtisam tunani da fad'in bani number d'inki, in kun gama saiki kirani.

Ibtisam tace OK, tare da fad'a ma Aysha number d'inta

Bayan Aisha tasa number din, ta kira ibtisam tare da fad'in sai kiyi saving

Ibtisam tace OK

Tafiya Aisha tayi inda salis ya fara koya Mata abubuwa, kuma babu laifi tana ganewa, ba yanda tayi tunani bane, irin zai bata wahala ba

Sun d'auki wajan Awa d'aya da rabi Kafin salis yace sai gobe kuma

Ibtisam tana ta mishi godiya, tare da amsan number d'inshi tayi saving, sannan yace muje in rakaki, in kin kusa zuwa saiki kira Aisha

Tare suka fito har kusa da hostel d'insu sannan ta kira Aisha ta fito suka shiga ciki


*AMERICA*

Najeeb ne cikin shiri yasa farin kayanshi na Pilot daka gani fita zaiyi, zuwa airport

Wannan balarabiyar ce ta fito itama cikin shiri, tare da rungumo Najeeb, Tana fad'in "Najeeb you always look handsome

Murmushi Najeeb yayi tare da rungumota jikinsa, shima ya manna mata wani hot kiss "sannan yace Najwa, "mazan dake k'asar ku babu wanda yayi miki?

Tana manne a jikinsa tace Babu, "ni Kai d'aya nake gani Najeeb, "inda zaka aureni da nafi ko wace mace Sa'a a rayuwa

Kallonta yayi cikin idonta," Sannan ya sakar mata murmushi, lallai inda na shirya aure ko ince inda inada ra'ayin aure dana auri Najwa, domin tana d'aya daka cikin matan da nake so, musamman yanda take bashi kulawa Sosai, tare da gamsar dashi, duk sanda suka had'u, duk da wannan shine haduwarsu ta biyu

Hura mishi iska tayi a kunne tare da fad'in, why are you stare at me like that?

Murmushi yayi tare da kissing d'inta a baki, "Sun d'auki lokaci suna haka, tun suna tsaye har Najwa tayi k'asa, domin bazata iya ri'ke kafafunta ba.

Ganin tana son tayi nisa, alaman ta Fara tafiya yasa Najeeb sakinta tare da fad'in "let me go baby

Dukan wasa takai Mai alaman ya zakai min haka.

Kamoshi tayi sannan ta tashi tsaye tana k'ara gyara rigan jikinta, "idon Najeeb na kanta, lokaci d'aya yasa hannunshi akan nononta tare da janyota ya matseta ta baya, hannunshi nakan nononta, yana shafa mata su.

Ita kam sai faman lumshe ido take, Tana wani sauke numfashi kaman wanda aka sa mata banana.

Najeeb ya d'auki lokaci a haka shida ita, Kafin ya saketa tare da fad'in let go, "yayi gaba abunsa

Binshi tayi a baya, har cikin motarshi da yake zaune mazaunin driver, "itama bud'e gaban tayi kusa dashi ta shiga, inda ya tada motar suka nufi airport.

Kai tsaye Najeeb ciki ya shiga, "sai dai ita Najwa baza'a barta ba, coz ba pilot bace, zama tayi tana jiran ace passenger su Fara shiga

Baifi 30mnt da zuwansu ba, aka fara shiga, "shi dama Najeeb ya dad'e da shiga, yana wajan tuk'i, shida wani pilot din wanda Najeeb yake kira da Moh, sunanshi muhammad, "suna shiri Sosai da Najeeb.

Bayan an gama shiga, jirgi ya fara tafiya, inda yayi tafiya Sosai cikin airport din, Kafin ya juyo da d'aga sama

Bai tsaya ko inaba sai k'asar Dubai

Kai tsaye mutane suka fara Fita, "Najeeb shida Moh suna ciki, basu fita ba, "Najeeb ya kalli Moh yace wai yaushe ka dawo ne daka Paris?

Moh yace tun last week Ina nan AI.

Najeeb yace ok I thought kana can

Moh yace a'a na jima da dawowa America ,"Moh tashi yayi yana fad'in Bari Kaga tunda nazo Dubai yau, dole inje in shiga inyi yawo

Najeeb murmushi yayi tare da tashi shima suka fita tare, "inda ya tadda Najwa na jiransa.

Tana ganinsa ta nufeshi tare dayin hugging d'inshi, lokaci d'aya kuma ta sakeshi tare da bashi peck kiss a goshi, "tana fad'in shall we go?

Yace yeah of course let go

Tana k'okarin ta manne Mai a jiki, yaja baya tare da cewa Nop bana son irin haka.

Dole ta hakura ta bishi suka fita haka "shikam Moh dariya yayi tare da fad'in Najeeb kana abunda kake so




*KANO NIGERIA*

Granny ce zaune tana ta faman fiffita domin an d'auke wuta, gashi ana zafi garin, bini bini tayi tsaki

Ummi ta shigo d'akin Tana fad'in lafiya mama? Tun ina kitchen nake jiyo tsakin ki.

Granny tace Wlh zafi nakeji, yanzu inda takwarata Tana nan da batai min fiffita ba, kun tashi kun turata har wani gari karatu, saboda ku baku damai fad'a muku "yanzu yanda duniya ta lalace yaro na gabanka yaka iya dashi balle baya gabanka

Ummi tace mama insha Allah babu abunda zai faru, ki dinga musu kyakyawan zato

Granny ta tsuke  baki tare da fad'in aikin kenan, Hmmm Allah dai ya kyauta, in banda iskanci da fitsarewa babu abunda yara ke koya a jami'a, ki duba miskili kiga yanda ya canza, muna fad'a yana fad'a "wani lokacin ma kaman zai bugemu yake ji,"gaba d'aya kun canza ma yara tunani da wannan shegen bokon, wanda nidai banga wani amfaninsa ba wlh, sai dai illarshi da nake gani

Shima kabirun da shegen iyayi, ya turo iyayenshi yana cewa a barta taje boko, Allah yasa ta samu wani ya kwace mishi ita, "ni gaba d'aya ya fara fitar min a rai, tunda yace ibtisam taje jami'a ya yarda

Ummi tace Mama kiyi hakuri, karki manta wacece takwarar ki, inaga kaman kin fini ma samin halinta, Kinga bai kamata ki dinga damuwa ba.

Granny tace dole In damu mana, mun bama yara tarbiya dai dai gwargwado, "amma kun turasu inda za'a bata su, "waiku abunda miskili yakeyi duk bai isheku ishara bako?

Hmmm shikenan ai, tunda hakan kuke ganin yafi muku, sai kuje kuyi tayi.

Ummi dai shuru tayi, danta Lura da Granny tunda ibtisam tabar gidan, ta tafi skul kullum tana neman hanyar rigima

Fita Ummi tayi tabar mata d'akin

Ganin ta fita yasa Granny sakin tsaki tana fad'in, aikin banza aikin hofi, ko uban Mai bokon zai musu oho, gashi shima munafuki kabirun yasa ankai biki har wani wata biyar dan iskanci,"in ginin ne bai Gama ba sai a d'aura auren inya gama ta tare



*A B U ZARIA FEMALE HOSTEL*

ibtisam ne ita da Zarah a d'aki, ibtisam tana ta faman karatu domin so take duk abunda tai missing taga ta iya, idan salis Ya koya Mata inta dawo taita bita, "kuma babu laifi tana saurin gane Abu, "yau da karfe 3 suna da lecture din Dr

Please Login or Register in order to submit comment