Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jibril tunda ya shigo bai k'ara zuwa ba sai yau, "dan haka ibtisam take ta karatu Dan ance mata in bai bata text ba, zai iya bada assignment, ko yayi tambaya wanda ya amsa ya bashi kyautar mark. Zarah dake faman zuba indomie a tukunya, tace Wai ya naga gaba d'aya kin dage ne haka? Ibtisam tace ba dole ba. K'aran wayar ibtisam yasa ta d'auka  domin ganin Sunan kabir Bayan ta d'auka yace hello my ibti Tace Barka da wannan lokacin Yace yauwa my ibti, ya skul din? Tace Alhmdlh, sai dai karatu akwai wuya Sosai Dariya yayi tare da fad'in dama hakane sai an dage Sosai Tace eh hakane, gashi inata fama da karatu,. Yace toh a dage sannan banda kula maza, ban son inga ana kula kowa Tayi dariya tare da fad'in  bana kula kowa, dama wa zan kula bayan Kai? Zarah dake kusa tace kidai fad'i gaskiya Kabir yace Zarah ce? Ibtisam tace eh, wai cewa take Indai fad'i gaskiya, Bayan shi nake fad'a Maka Kabir yayi murmushi tare da fad'in kice Ina gaidata. Ibtisam tace zan fad'a mata insha Allah Dan shuru yayi sannan yace next week Zan shigo in ganki, Nayi missing dinki Sosai, gashi bakya whatsapp da naga pic dinki Tace eh Wlh Yace zan tura miki kud'i Kisai waya, ko in tawo miki dashi Ibtisam tace waya kuma? "ka manta saboda shi aka hanani zuwa skul Kabir yayi dariya tare da fad'in ban manta ba, my ibti, Aiko da abunda yasa aka miki haka saboda ban turo bane, yanzu kuma an San dani, Kinga komai na baki babu damuwa, Abba bazai damu ba Tace uhm nidai gaskiya abar maganan wayar nan Yace OK zan tambayi Abba da kaina tunda bakya so Tace a'a ba haka bane, wlh tsoro nake ji Yace karki damu babu abunda zai faru Kinji my ibti send me ur account number Tace bani da account Murmushi yayi tare da fad'in y'ar jami'a guda, matar barrister Kabir, mrs KABIR ace bata da account? Tace uhm toh wa nake dashi da zai dinga bani kud'i, balle har in bud'e account? Kabir yace ni mana ur husband Uhm kawai tace cikin jin kunya, "yanzu taga gaba d'aya tunda kabir ya kawo kud'in sadaki ya canza, yana fira da ita irin firan da baya Mata da, "duk Da bai taba mata maganan banza ba, yanzu Abu kad'an daka ya kira magananshi shine ki ri'ke min amana, karki bari wani ya kwace minke tunda tazo jami'a ..... Katse mata tunani yayi da fad'in ya kamata ki bud'e account, in Zanzo zan Kawo miki wayar Tace toh Yace Bari in barki take care, but inaso ki kular min da kanki Sosai, and ki ri'ke min kanki banda bin bad friend Tace insha Allah tare da kashe wayar tana tunani... Toh mai KABIR yake nufi? Ko shima yasan irin abunda matan jami'a keyi ne? Toh amma Aiba duka aka zama d'aya ba, lallai dole rayuwar jami'a taba wasu tsoro, dan zaman da tayi dasu Aisha da hauwa, ta gano irin wayewar dake kansu, lallai sai yasa da yawa iyaye ke tsoran tura y'ay'ansu jami'a, sai suce gwara suyi a d'akinsu, wato gidan mijinsu Zarah ta Katse ibtisam da fad'in ga indomie d'in Amsa ibtisam tayi ta Fara ci Bud'e kofar akayi Hauwa ce ta shigo d'akin Tana fad'in Kai Wlh na gaji, "kallon su ibtisam tayi tace Aisha bata dawo ba? Zarah tace eh bata shigo ba Hauwa tace amma Aisha ko yar iska shine tace min Tana nan tun dazu h.... Shigowan Aisha yasa hauwa yin shuru, tare da fad'in kika cemin kina nan tun d'azu Aisha tace ke saboda kiyi sauri ne yasa nace haka Hauwa tace miye Toh kike nema na? Aisha tace ke zan had'aki da wani ne Keda wata"kin San yau inada lecture din Dr jibril sai yasa ba zani ba Hauwa tace shine sai kin had'ani da wata, mata biyu yake ci lokaci d'aya? AISHA tace a'ah, lesbians za kuyi keda wacce Zan had'aku, idan kukayi a gabansa shi abunda yake so kenan, shikenan saiya  biya ku, kuma da dollar yake biya Ihu hauwa ta saki tare da fad'in amma wannan ko shege wato shi yaga mace da mace nacin juna shine bukatar shi? Kai ana bura uba a duniya Dariya Aisha ta saki tace Wlh kuwa, Kedai bari, gashi tsoho mutuwa yau ko gobe Hauwa tace Hmmm tsohon banza, mudai Indai za'a bamu kud'in komai za muyi, yaushe zamu tafi? Aisha tace yanzu mana, ita yarinyar nake jira yazo, saiku tafi Ibtisam gaba d'aya mamaki suke bata, lallai duniya ta lalace, dole aji tsoran matan jami'a., jiba yanda suke magana babu ko kunya, kuma zunubi zasu aikata wato Bayan bin maza harda lesbians sukeyi? "gaba d'aya ibtisam sai taji Sun Fara bata tsoro....... Read and leave it, dnt share to anyone *IDAN KIKA KARANTA BAKI BIYA BA INA BINKI BASHI, KUMA NAUYI NE A KANKI* *WACCE TAKE SON BIYA ZATA TURA 200 TA ACCOUNT NUMBËR DINNAN* 3138831065 Firstbank Maryam Alhassan *SAI A TURO SHAIDAN BIYA TANAN 08060860886 IDAN KUMA KATI NE MTN SHIMA TA NUMBER DIN ZAKI TURA 200 NAIRA ONLY* *KARKI MANTA KINYI ALKAWARI, BAZAKI FITAR MIN DA NOVEL BA, IDAN KIKA FITAR DASHI KEDA ALLAH, KUMA KINA D'AYA DAKA CIKIN MUNAFUKAI, DOMIN ALAMAN MUNAFUKI GUDA UKU NE, 1 IDAN ZAIYI MAGANA YAYI K'ARYA 2 IDAN AKA AMINCE MASA YAYI HA'INCI 3 IN YAYI ALKAWARI YA SABA, KIN DAI JI, KINCE KIN MIN ALKAWARI, IDAN KIKA SABA KIN ZAMA MUNAFUKA, KUMA WUTAR MUNAFUKI DABAN TAKE, IDAN KIKA FITAR KINMA KANKI* Hauwa ta kalli Aisha tace nifa kin San ba iya wannan lesbians din nayi ba, kar inje in kwafsa Aisha tace tsaya in baki ki kalla, "d'auko wayarta tayi ta kunna Mata video tare da bata, "baka jin k'aran komai saina nishi sama sama tare da shhhhh sai kuma dariya Jin k'aran yana ma ibtisam wani iri yasa ta tashi da sauri tabar d'akin, "ganin haka itama Zarah ta mi'ke ta bita waje. Ganin Sun fita hauwa tace karmu lalata y'ay'an mutane fah. Aisha tace ai irinsu haka suke, farkon zuwansu waje suyi ta Abu kaman na Allah, Bari kiga nan gaba, zaki sha mamakin su, Idan suka saki jiki, yanzu duk na munafunci ne, kowa da kike gani dan iskan kanshi ne, sai dai na wani yafi na wani, sannan mu namu ne ya fito, akan masuyi a boye fah, ai gwara mu Hauwa tace kai gwara masuyi a boye fah, "Allah zai iya shiryar dasu, muma muna fatan shiriya Dariya suka saki, "hauwa taci gaba da kallon video din Tana fad'in Kai Wlh wannan Abun ko wahala, gaba d'aya baya burgeni Aisha tace Kedai kawai kiyi dan kud'i malama Hauwa tace amma wannan mutumin da zaki had'amu ko d'an iska, ace shi so yake yaita kallo.... Kofar da aka bud'e ne yasa suka d'aga Kai, wata yarinya ce ta shigo cikin d'akin tasha riga da wando gaba d'aya dressing d'inta y'ar musulmai bazata iyayi ba, amma abun mamaki sai naji suna kiranta da Zainab Zee,. Hauwa tace shegiya zee, Dama tare zamu? Aisha tace eh tare zaku,. Zee kai hannunta tayi kan nonon Hauwa Tana fad'in Bari in fara tabawa tun daka nan. Hauwa tace Wlh ke y'ar iska ce, nifa ban wani iyaba sai yasa nake kallon video Zee tace toh Abu Mai sauk'i, Bari muyi a nan, Kafin muje can. Aisha tace a ina? Kunga ku tashi ku tafi tun Kafin ya kirani,kuje can kuyi a gabansa Tashi sukayi suka fita su Duka harda Aisha data rakasu Bayan ibtisam ta fita gaba d'aya gefen hostel d'in ta Bari, inda ta zauna akan wani bishiya, "lallai rayuwar jami'a Abun tsoro ne, dole kabir yaita mata kashedi sai yanzu take Lura da abunda yasa yake mata kashedi har take mamaki take ganin ya canza ba kaman daba, Ashe da gaskiyan shi. Gaba d'aya ibtisam taji bata son zama dasu hauwa da Aisha cikin d'aki d'aya, ajiyan zuciya ta sauke tare da fad'in lallai yanzu wannan abunda muke gani wai sunan muna cikin hostel ne, "in muka fita waje kuma fah? Tab gwara nan dinma zaifi gaskiya Tana nan zaune wayarta tayi k'ara d'auka tayi taga ummi ce, "sawa tayi a kunne tare da fad'in Ummi Ina wuni Ummi ta amsa da lafiya kalau ibtisam ya karatu? Tace Alhmdlh Ummi, "Ina Granny da Abba? Ummi tace Abbanki yana kasuwa, "Granny kuma gaba d'aya ta addabi mutane akan kin tafi karatu, "kullum mita daka an zauna taita fad'a an Turaki karatu. Ibtisam tayi dariya tare da fad'in kai Granny ko rigima, "Tana kusa ne ki bata wayar mu gaisa? Ummi tace bari inkai mata wayar "koda ummi ta shiga d'akin Granny bacci taga tanayi, dan haka ummi tace ma ibtisam tana bacci sai dai inta tashi sa gaisa din Ibtisam tace toh ummi, tare da fad'in Ummi dama ina son inyi miki magana Ummi tace name? Ina jinki Ibtisam tace ummi yanzu Ina matukar bukatar babban waya, saboda duba internet in an bamu assignments in duba a ciki, "ummi tace hakane zanyi ma Abbanki magana. Ibtisam tace ummi Kabir yace zai kawo min waya, shine nace mishi a'a amma ya dage Wai sai Yaban, harya nuna rashin jin dad'inshi akan nace a'a. Ummi tace karki damu bari abbanki ya dawo, zan Mai magana, "sannan shi KABIR in banda abunshi ina shi ina k'ara siyan miki wata waya, mutumin da yake hidiman aure ga gini, wanda ya baki ai Tana nan, zanyi magana da Abbanki in yaso saiya baki wannan, amma bai kamata yasai miki wata ba Ibtisam tace toh ummi, saina jiki Ummi tace toh, tare da fad'in ina zarah? Ibtisam tace Tana d'aki, ni na fito waje insha iska ne Ummi tace ok sai anjima tare da kashe wayan Zarah ce ta k'araso inda take tare da fad'in Ashe nan kika zo, kika makale, inata nemanki Ibtisam tace eh nan nazo. Zarah zama tayi kusa da ibtisam tare da fad'in kai Wlh yau garin babu dad'i wani iri nake ji Ibtisam tace ko baki da lafiya ne? Zarah tace lafiya na kalau, kawai dai ina jin kaina wani iri ne yau, "gashi inada lecture 4 Ibtisam tace Kinga Muma muna dashi 3 ga time ya kusa Ibtisam tace Zarah wlh ni yanzu tsoran su Aisha nakeji Dariya Zarah tayi tare da fad'in tsoran Me kuma? Ibtisam tace naga iskancinsu yayi yawa, nifa a duniya Ina tsoran abunda zai taba mun budurcina na, burina in kaishi gidan miji, saboda in samu y'anci da kuma girmama wa a wajan miji,"amma su Kinga har fad'a suke suna bin maza ga bin mata Kai Abun nasu yayi yawa, sai yanzu nake gane abunda Granny ke fad'i ashe gaskiya ne "tace anama matan jami'a kallon y'an iska Zarah tace Hmmm Abun dai sai a hankali, sai dai muce Allah ya shirya, amma abunsu Hauwa sai addu'a ,"su gaba d'aya basa jin kunyan fad'a wajan kowa cewa suna iskanci, wlh duk alaman karshen duniya ne, an maida zina kaman ado Ibtisam tace hakane wlh, alaman karshen duniya ne, dama ance zaka ga mutum na zina akan titi, toh gashi nan muna gani, wanda sai yanzu na Lura da abunda ake nufi da akace za'a ga mutane suna zina akan titi Mai imani ne zaice su matsa gefe, kin San yanda na Lura? Zarah tace a'a Ibtisam tace bawai ganin mutum zakayi akan titi a kwance suna cin junansu ba, a'a, irin abubuwan da ake nufi shine, zaki ga mace tayi zina bata jin kunyan fad'a tayi, sannan kiga mata a jere a titi suna jiran abokanan shashancin su, dan suyi zina dasu, toh kinga wannan shine ake cewa zaki ga mutane na zina akan titi, wlh duniya ta gama lalacewa, "Allah dai kawai yasa mu dace, ya tsare mana imaninmu Zarah ta amsa da Allahumma Ameen, "tare da fad'in duniya kenan, kai Allah ya kyauta. Ibtisam tashi tayi tana fad'in bari kiga inje in shirya time ya kusa,na shiga lecture Zarah tace nima bari inje in shirya domin 4 za muyi saimu fita gaba d'aya Tashi sukayi suka nufi d'akin, babu kowa a ciki suka shiga suka shirya, ibtisam wata doguwar riga tasa sannan ta yafa wani Gyale medium a saman kanta, duk da babu makeup a fuskanta tayi kyau Sosai, "ita kam Zarah jallabiya tasa suka fita Bayan Zarah ta d'aukesu a hoto Rufe kofar d'akin sukayi da key tunda dukansu Suna da key Kai tsaye inda su ibtisam za suyi lecture suka nufa, inda suka iske salis a ciki Ibtisam tace salis kai kullum saika riga kowa zuwa? Yace Wlh gwara in riga kowa, kin San Dr jibril baya wasa fah, yanzu sai ya fadar da mutum Ibtisam dariya tayi tare da fad'in Allah ya kyauta Salis Ya amsa da Ameen "tare da kallon Zarah yace Kai ibtisam amma wannan sister d'inki ce koh? Ibtisam tace eh Yace haba kaman tayi yawa wlh Zarah tace amma na fita kyau koh? Salis yace kai Anya kuwa? Gaskiya bazan iya zaba ba, dan dukanku ba baya ba Duka dariya sukayi, suna cikin fira mutane nata shigowa domin baifi 10mnt su Fara lecture ba Time na cika dai dai saiga Dr jibril ya shigo ciki, yana shigowa saiga Aisha, tsayawa tayi tana kallonshi domin tasan bazai barta ba. Baiko kulata ba balle ya Mata magana, ganin haka yasa ta juya dan tasan ko zata mutu bazai Bari ta shiga ba, tsaki taja tare da fad'in gashi Nayi late dama ni naje aka dan Sosa min In samu kud'in Dr jibril Fara lecture yayi inda ya nuna Zarah tare da fad'in stand up Tashi tayi tana kallonshi, sannan ya kalli ibtisam itama yace ta tashi Itama mak'ewa tayi Idonshi nakan Zarah yace yau na taba ganinki a nan, sai yau kika fara zuwa or what? Zarah tace a'ah sir, ni Ina karantar low ne, kawai na zauna ne Kafin time din lecture d'ina yayi 4. Kai ya d'aga alaman ok, "kallon ibtisam yayi wacce itama shi take kallo, "yace and you Kema Mai kikeyi a nan? Tace ina lecture ne, "yace you mean kina department dinnan ne na medicine? Tace eh cikin sanyin murya. Ok yace tare da fad'in su zauna Bayan ya kammala lecture yace ma ibtisam ta sameshi a office d'inshi yana son ganinta, "yau kwata kwata 30mnt yayi ya fita domin an kusa kiran sallah la'asar Ibtisam bayan ya fita ta kalli zarah dake zaune tana danna wayarta, tace plz muje ki rakani inji mai zaice min. Zarah tace wa ?lallai kije ke d'aya, nifa yanzu sallah zanje inyi daka nan inje lecture, "Nasan shima yanzu ko Kinje saikin jirashi ya dawo daka masallaci Salis dake bayansu yace ibtisam, idan Kinje ki rokeshi ya baki text din da bakiyi ba, domin 20mrk ba wasa bane Ibtisam tace kana ganin zai yarda inna rok'eshi? Salis yace Am not sure zai yarda, but try May be ya yarda, tunda mutum ne kuma yasan Allah Zarah tashi tayi tana fad'in bari inje inyi sallah, in tafi lecture Koda ibtisam ta fita itama taga Aisha ita da wasu mata a zaune suna ta surutu, kuma duka firan akan in sunje club ne ga yanda zata kaya,"ibtisam tace suko kunya basaji, "club din da babu abunda ake sai iskanci da shaye shayen giya Aisha ce ta katse mata tunani da fad'in ibtisam har kun fito? Ibtisam ta saki murmushi tare da fad'in eh yanzu muka fito, "naga kinzo kin koma. Aisha tace Aiko na shigo korana zaiyi wlh, baida mutunci ko kad'an Sauran matan da Aisha take fira dasu suka zuba ma ibtisam ido, "wata Mai suna kubra tasha attachment brown da wando an matse tace wannan fah? Ban taba ganinta ba sai yau Aisha tace d'akinmu d'aya sannan course d'aya muke karanta Kubra tace OK, amma shine bakwa zuwa club tare Aisha ta kalli ibtisam tace Kinji abunda take cewa, wai bama zuwa club tare Ibtisam murmushi kawai tayi, "amma cikin ranta tace Allah ya rabani da zuwa club, kuma ina muku fatan shiriya, ku tuba ku daina... Kubra ce ta katse ma ibtisam tunani da fad'in ibtisam koh? Ibtisam tace eh Kubra tace Sunan yamin dad'i, Sunan larabawa Ibtisam murmushi tayi tare da fad'in ngd Kallon AISHA ibtisam tayi tace plz zaki rakani wajan Dr jibril. Aisha tace ni? Rufamin asiri Mai zakiyi a wajansa? Ibtisam tace yace yana son ganina Aisha tace toh fah, Allah yasa dai lafiya, kodai shima d'an hannu ne, ya gani ya kyasa? Kubra ta saki dariya tare da fad'in uhm kibar lecturers dinnan, suna da iskanci, "amma Dr jibril ban tunanin zaiyi haka fah. Aisha tace ke ba'a shaidan mutum wlh, "yanzu mutum zai nuna Shina Allah ne anjima kiga ba haka bane, rayuwa kawai Ayi sha'ani kawai Kubra tace nikam ibtisam muje in rakaki, inje inji gulma komai zaice miki Ibtisam kam kunyar jerawa da kubra take, domin irin shigar dake jikinta, Wanda mutumin kirki dan musulmi bazaiyi ba, "amma babu yanda ta iya dole ta bita suje tare tunda tana neman dan rakiya, musamman da taji ana fad'in kodai dan hannu ne shima, "sai taji ta tsorata dan dama tasan ana cewa lecturer suna iskanci da student d'insu in ta'ki yarda sai su fadar da ita a course d'insu Har office din Dr jibril suka isa, da yake kubra tasan office din, nocking sukayi yace yes coming Bud'e kofar kubra tayi ta Fara shiga, ibtisam na bayanta kallo d'aya zaka mata ka gane jikinta yana d'ari d'ari Karatun al'qur'ani yake saurara Ganin Sun shigo yasa ya kashe karatun tare da kallon kubra yace lafiya? Tace sir cikin d'ari d'ari na rakota ne. Yace OK you can leave Fita kubra tayi da sauri Ibtisam kanta na k'asa idon Dr jibril na kanta ganin yanda ta tsorata ba tare da ance wani abuba, inda zaiyi ihu da karfi zata iya zabura A hankali yace you can sit Zama tayi akan kujeran daya nuna mata Yace ya sunanki? Tace Amina, but ana cemin ibtisam Yace OK Tare da fad'in mai yasa kika fita a lecture Rannan da zan bada text, ko mark dinne bakya so? Da sauri tace a'ah Yace so tell me why kika fita? Tace saboda ban San abunda zan rubuta ba, sai yasa na fita, ranan shine farkon shigana lecture Yace amma ai an dad'e ana lecture why baki Fara attending ba sai ranan? Tace akwai problem din da yasa ban fara attending da wuri ba, sai daka baya aka yarda inzo Yace which problem? Shuru tayi tana d'an nazari, can tace "sir is family issue Murmushi yayi tare da fad'in oh ok sorry for asking you So yanzu kinyi missing 20mrk kenan right? Ibtisam tace plz kayi hakuri ka bani inyi, tunda ranan na fara attending kuma kona rubuta I will fail, that is the reason da yasa naga gwara kar in rubuta din Idon Dr jibril na kanta yana kallon yanda take magana, ba kaman daba da take kaman a tsorace, "yanzu ta dan sake Yace OK zan baki text, but not now kizo gobe by 5pm sai in baki. Da sauri ta d'ago ta saki murmushin da yake k'ara Mata kyau, tare da fad'in "nagode sir Yace karki damu you can go Tashi tayi cikin murna ta fita.. Dr jibril da ido ya bita yana murmushi. Koda ibtisam ta fita taga kubra tsaye tana jiranta. Bayan ta fito kubra ta kura mata ido tun daka sama har k'asa Ibtisam tace lafiya irin wannan kallon? Kubra tace ina son insan koya miki wani abune, "Sai yasa nake kallonki inga Ina ya taba . Ibtisam tace auzubillah "wlh kinyi mishi sharri domin ba haka yake ba, kuma ko maganan banza baiyi min ba, "infact ma magana yayi min akan Mai yasa da yace zai bada text na fita? "shine na fad'a mishi dalili, har yace zai ban text din inyi, "ni Bama yanda nake tunanin ana fad'a akanshi Nayi ba, mutum ne mai sauk'in Kai a yanda na Lura raini ne kawai baya so, "sannan yana kama kanshi ne da shaidanun student masu kaima lecturer tallan kansu. Kubra tace uhm ibtisam kenan, daka had'uwa dashi yau yau har kin Fara bada shaida a kansa haka? Ibtisam tace ba haka bane, kubra Ina son ki gane wani abu, koda yanzu kika had'u da mutum indai kuka zauna kukai maganan minti biyar Zaki dan iya fahimtar Waye mutum da kuma irin abunda mutane ke fad'a akanshi Kubra tace toh ba girin girin badai, "Allah yasa Dai kar nan gaba inji kina tsine Mai, kina fad'in Ashe haka yake Ibtisam tace insha Allah bazaiyi abunda za'ace tir ba, domin koda Yana aikata wani mummunan Abu, yanayi a boye Toh Allah zai iya shiryashi tunda a boye yakeyi "amma wanda yakeyi a fili shikam sai dai ace Allah ya kyauta, mutum ya dinga Abu baya tsoran kowa, baki'i uban kowa ya gani ba, Kinga wannan yayi nisa baya fatan shiriya,"kuma shaidan duniya itace ta k'iyama daka ranan da mutum ya mutu za'a turo mala'iku suzo suji abunda mutane ke fad'a akan ka Idan mutane na fad'in oh an rage mugun iri, ka bani Inko aka samu ana yabanka ana fad'in mutumin kirki, koda kana aikata sabo a boye babu wanda ya Sani, sai Allah to Allah zai yafe ma mutum tunda wannan tsakanin Allah da bawa ne, kuma sirrin da Allah ya rufe babu Mai tona shi Kubra tace Allahu Akbar, "Ashe ibtisam din malama ce? Ibtisam tayi murmushi tare da fad'in daliba dai, muna koya ne Tafiya sukayi daka wajan inda suka nufi d'akin su ibtisam din, suka iske Aisha na zaune tana waya Ita dai ibtisam zama tayi tana jiran gobe tayi taje Dr jibril ya bata text din, d'auko littafi tayi ta Fara karatu Bayan Aisha ta gama wayar ta kalli kubra tace ya kuka kaya dashi? Kubra tace korana yayi da muka shiga Aisha tace ita d'aya kika bari? Maiya mata? Ibtisam dake karatu tace babu komai, tare da bata labarin abunda ya faru Aisha tace kodai yana miki wayau ne nan gaba ya fito da mayyatarshi, dan naga nashi Abun kaman da salo yakeyi Ibtisam tace Wai Mai yasa kuke mishi mummunan zato ne? Dan Allah ku daina Wlh babu kyau, tunda baice komai ba Kubar mishi mummunan zato, ku dinga kyautata zatonku akanshi plz Aisha tace lallai ibtisam ke yarinya ce baki San mai duniya ke ciki ba, kin ganni nan, "babu irin iskancin da ban sani ba, "sannan babu wani salo dana miji zai kawo in kasa gane inda ya dosa, "kuma Wlh zaki ce ni Aisha na fad'a miki, wata rana saiya fito miki da manufarshi Mutumin da baya wasa, baya sakar ma kowa, in bakayi text d'inshi ba, kokai Waye kayi missing kenan, 'amma ke har yace kije office d'inshi sannan ya yarda zai miki, uhm akwai wata a k'asa Dai Ibtisam cikin ranta tace Wai Mai yasa mutanan da suke aikata sabo suke ganin kaman kowa ma haka yake. Lallai maganan da malamin su ya taba fad'a musu gashi yau ta tabbatar, in mutum yana Abu sai yaga kaman kowa ma irinsa ne, sai yaga kaman kowa ma yana irin abunda yakeyi," mutumin kirki shine wanda yake ganin kowa kaman na kirki ne, na banza yana ganin kowa na banza ne. "Amma a fili sai tace nidai bayyi min Kama da mutumin banza ba Kubra tace bazaki gane ba, gaba muke miki tunani kuma zakice mun fad'a Tashi kubra tayi tana fad'in bari inje in dawo tare da kallon Aisha tana fad'in "anjima 8 akwai birthday din fatin d'akinmu ta fad'a miki kuwa? Aisha tace eh ta fad'amin Zanzo Kubra tace OK tare da kallon ibtisam tace Kema Ina inviting d'inki Tana fad'in haka ta fita Aisha ta kalli ibtisam tace ina fatan zaki je koh? Ibtisam tace Kai Anya kuwa Aisha tace a cikin skul ne ba wani waje ba Ibtisam tace OK tunda cikin skul ne Zanzo nida Zarah Aisha tace OK saimu je tare gaba d'aya Koda zarah ta dawo ibtisam tace su shirya zasu birthday din wata cikin skul din za'ayi Zarah tace ok, amma fah ni bana son shiga iri irin wannan Abun. Ibtisam tace nifa da Farko nace ba zani ba, saida akace a skul za'ayi Zarah tace ok. Ibtisam da zarah sun shirya duka cikin dogayen riga,

Chapter 14 of 46