Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 11
na yi miki haka, dole na kure ki, ki zage ni. Ai babu abinda ya fi kona rai a game da harka waya irin (Flashing), saboda ba ka san a wane yanayi mutum yake ba, watakila ma cikin jama'a yake, balle wannan da aka ce har cikin dare yin sa ake yi. A gaskiya ban goyi bayan masu wannan dabi'a ta Flashing) babu iyaka ba. Kar kuma kin mance, su masu hulda da jama'a ne, ke ki na (Flashing), wata can na yi, ko ma ince wasu, ai kin ga dole abin yayi masu yawa har su ji zafin abin." Ta kwada mata harara, ta ce,"Suyita jin zafin mana, mu muka sa su rubutun? Ta ce,"Ayya kawata. Ban so ki kasance cikin irin mutane masu ci, suna share baki ba. Ma'ana duk mutumin da zai miki abinda za ki amfana da shi. Ya fi gaban wannan furucin da ki ka yi. Ba karamin kuskure ki ka yi ba, da ki ka ce kin zage ta. Domin Manzon mu Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce,"Kada ku kasance cikin wadanda za su tashi ranar gobe kiyama suna matsiyata, alhalin sun yi ibadar su daidai. An tambayi. Mai girma da daukaka, wanene matsayin lahira?" Sai ya ce,"Shine wanda zai zo da aikinsa cif-cif! Amma ya ha'inci wannan, ya zalunci wancan, ya shiga hakkin wannan. Sai ya kasance an debe ladarsa, an biya su, har ta kai ga ba shi da sauran lada, daga nan za'a fara diban zunubansu ana dora masa. A karshe zai tashi a tutar babu. Wa-iyazubillahi! Saboda haka ki daina daukn irin wadannan abubuwan na shiga hakkin jama'a a kankanin zunubi. Ubangiji bai yafe hakkin wani har sai shi wanda aka zalunta ya yafe, ina fatan kin fahimce ni? Ta sauke tagumi ta ce,"Duk jiki na ya yi la'asar. Allah ka tsare mu da tashin matsiyatan lahira. Bari ma dai ki gani." Wayarta ta dauko,"Me za ki yi? Ta ce,"Neman afuwa." Dan murmushi tayi,"Ina son ki wajen daukar nasiha. Nemo ta mu gaisa. Daga nan mu nemi shawarwari." Cikin dan kankanin lokaci waya ta sada su da Momin Zariya. Jimawa kadan ta dauka tare da sallama. Kausar ta amsa,"Na san ba za ki gane ni ba Momi, amma an ta6a kira na fadi wata magana maras dadi akan maganar da aka yi sbd 'yan flashing. Gaskiya na yi tunani na ga abinda na yi bai da ce ba in kira ki, in ba ki hakuri. Momi ta ce,"Haka ne, kuma har ga Allah ya wuce. Rashin fahinta ke sa wa mutane ke ganin ba'a kyauta ba. Amma da an san irin kashin da 'yan flashing ke yi, da irin ku ba su zage mu ba. Bayan wannan wai har kiran waya ayi hankali tashe, ace don Allah ki bugo anyi mutuwa.Jiki na rawa zan kira, wai sai ki ji ana kyalkyar dariya. Menene wannan? Yanzun saboda Allah don ka kira mai irin wannan marasa hankali, wanda bai san inda ke masa ciwo ba. Ka yi laifi?" Ta nisa ta ce,"Tafdi! Lallai wannan rashi hankali ne, abinda kuwa ya raba mutun da dabba kenan hankali. Hakuri za ki yi Momi aikin jama'a ki ke yi, dole ki rinqa ganinsu iri-iri.. Tayi murmushi,"Wannan ya zama dole, ban kwana da kowa, ban tashi da kowa. Duk wanda ya gyara, ya sani, haka duk wanda ya 6ata, ya sani. Shi Dan-Adam ai tara yake, bai cika goma ba, babu wanda zai ce ya wuce zagi a doron kasa. Saboda haka ni duk wanda ya zage ni, na yafe masa, ni ma ina rokon wanda yake ganin na 6ata masa, to ya yafe mi. Saboda halin rai." Kausar ta cika da al'ajabi, har ta rasa ta cewa. Jim kadan ta ce,"Ga kawata Nusaiba, za ku gaisa ta ma kusa aure, sai ki bata shawarwari. Nusaiba ta amsa, ko dama sifikar a bude take, tana jin komai. Bayan sun gaisawa. Momi ta kara da cewa,"Shawarwari suna nan jibge, cikin littafai. Idan mai karatu ya natsu, zai fahimta, ba wai dadin lbr kawai ba. A karshe sai ince bayan hakuri, a kara da juriya. Jurewa kwaramniyar aure, shi ke sa wa zama ya dore irin na iyaye da kakkanin mu. Allah yayi yagora, ya zaunar da mu lafiya da mazajenmu." Ta ce," Amin. Mun gode Momi. Don Allah zan tambaye ki, ina fatan ba za ki yi fushi ba?" Ta ce,"Allah yasa na sani. Don Allah shekarunki nawa? Kuma 'ya'yanki nawa? Ta ce," Bana ina da shekaru arba'in da daya 41. 'Ya'yana takwas 8,, sai daya da Allah yayi wa rasuwa. "Wai, lallai Momi kin mika, to Allah ya raya su, rayuwa mai amfani, ya jikan wanda ya rasu. Mun gode." Ta ce,"Amin, ni ma na gode." Kausar ta daga murya,"Sai anjima Momi, ni suna na Kausar! "To Kausar, ke kuma yaushe ne auran na ki?" Ta ce,"Da saura Momi, karatu na ke yi." Shi kenan Allah ya za6o na gari. Sai Anjima." Amen. Suka kashe waya. Nusaiba ta budi Kausar,"Kin ji ko?" Ta ce,"Borin kunya kawai na ke yi, ashe sa'ar Momina na zaga. Daga yau Insha Allah ban sake ba. Ta ma yi wani littafi TARKON AMANA, ban karanta shi ba. Amma gobe zan shiga kasuwa." Tana dariya, kawai suka tsinkayi kiran sallah cikin masallaci dake like da gidan." Wai azahar ce tayi,? Inji Kausar. Nusaiba ta ce,"To da zauna nan kina zagin mutane, sai dai ki ji wuf a kabari. Ta shige bayi ta bar ta da kwakwazo," Banza! An dai yafe min, ko dama da wa da na zaga??" ******************* Shi kuwa Abba bayan kammala shirin sa, misalin sha dayan rana ya bar gida bai zame ko'ina ba, sai Zariya. Malam Balarabe na zama jiran sa kamar yadda ya shaida masa ta waya cewar yana tafe, don gabatar da wata magana. Shi kan sa da ya iso gidan su Naseer, ya ga sauyi.Koda ya shiga ciki kuwa abin ya ba shi mmk. Kuma Naseer ya kara burge shi, ganin yadda ya gyara gidan su gwanin sha'awa, cikin falon da aka sauke shi. Nan ma komai ya ji dai-dai k'arfin samun Naseer, hakika kowane ya zo, za'a fita kunya. An kuwa fita kunyar Alhj domin tarba ta musamman aka shirya masa, duk da cewa Naseer kan san bai san da zuwan Alhjn ba, kuma Abba bai gaya masa ba. Saboda lkcn da Alh. Basheer ya yo waya. Naseer bai gida. Bayan natsuwar su, su biyu a cikin falon. Alh. Basheer yayi gyaran murya, ya fara gabatar da abinda ke tafe da shi, "Na san zakayi mmkn zuwa na, ba saboda zumuncin da ke tsakanin mu ba. Amma watakila dalilin zuwa na, ya ba ka mmk. Sai dai a hakikanin gaskiya, ba abin mmk bane ga shirin Ubangiji, domin shiya hada ni da Naseer kuma ya sanya min kaunarsa. Kaunar tayi yawa Malam Balarabe, har na ji ina son hada zuri'a da ku. Ma'ana 'ya ta Nusaiba na ba Naseer." Gaban Malam Balarabe ya fadi ba kadan ba, sannan ya rasa a wane yanayi yake? Ana wata ga wata kenan, ya ma rasa wane, bayani zai yi? A matsayi da girman Alh. Basheer, ya d'auki 'ya ya ba su, ai kar6a ya zama dole, don ko mafarkin bai ta6a gigin tunanin wannan abu ba. Kwarya ta bi kwarya...........Inji hausawa. Allah mai iko. Bakin sa har kunne ya ce,"Kai! Kai!! Kai!!! Alhaji wannan sako da girma, yake, mun gode, Allah ya saka da alkhairi, ya taya mu rik'e amana."ya ce,"Amin, sauran magana kuma Naseer ya je su ga juna, domin jiya ta dawo daga Jordan, ta kammala karatunta." Ya ce,"Madalla, kawari Naseer ya gaya min shekaran jiya har yake ce min ka yi masa maganar makaranta, ka na son ya ci gaba.Na ce,ai shi ya tsaya shishirinta da yanzu ya gama. Sai dai akwai wani hanzari, ba gudu ba Alhj, wanda ya zama dole in fade shi. A hakikanin gaskiya akwai wata yarinya da aka ba Naseer tuntuni, jira ake ta gama sakandirinta ayi auran. Bana ma za ta gama. Ka ji abinda ya sanya ni a damuwa, ban kuma san yadda za'ayi ba?" Shi kansa Alh. Basheer zancen ya motsa zuciyarsa, jikin sa yayi sanyi jin shiru yana dogon tunani. Amma ko alama ran sa bai jirkita da wani bakon tunani ba, tsabar kaunar Naseer ke nuna masa babu wata matsala. Ya dubi Malam Balarabe ya ce,"Ai Naseer mijin mace 4 ne, so ina ganin ba wata matsala, na riga na ba shi Nusaiba, ya hada duka ya aura, na dauki nauyi komai. Allah ya taya shi riko bisa adalci." Fafdi! Wace irin kauna kuwa Alhj ke wa Naseer? ko alama Malam Balarabe bai san irin ta ba. Ashe akwai sauran irin su Alh. Basheer a duniya? Ya karkada kai ya ce,"Ba ni da bakin godiya Alhj. Bari dai in kira Maman shi, ta taya ni." Ya mike da rawar jiki, ya leko ya kwalawa Umma kira. Ta amsa, ta same su a falon saye da bakin hijabin ta, gefe ta zauna. Sannan Malam Balarabe ya mayar mata da bayani. Ita kan ta, ta ji dadi fuskar ta, ta nuna karara, sai dai tunani dan gogan take yi, jin cewar bai ma san da zancen ba. Da wace fuska zai dauki al'amarin? Bata da amsa tilas, Naseer ne zai fayyace komai.Wannan tunani shi ya sace mata guiwa. Bayan ta gama murna da godiya ga Alh. Can ta koma kuryar dakin ta tayi zaune gefen gado tana jujjuya al'amarin cikin ranta. Tare da tambayar kan ta."Wane irin bayani za mu yi wa iyayen Zarah? Ta nisa ta ce,"To ya Allah kai ka shiryo wannan al'amari, ina rokonka ka sanya mana fahimtar juna." Tana gama addu'ar ta, ta jiyo kiran Malam, ta amsa. Ya ce ta zo Alhj zai koma. Ta yo waje, nan tsakar gida ta iske shi, suka yi sallama tare da kara kwarara godiya. Hannu ya zura aljihu, ya debo kudin da shi kansa bai san ko nawa bane, ya mika mata. Ta kada kai ta ce,"Alhj ai mu ne za mu bada tukuici. Ya dubi M.Balarabe." Malam, Naseer d'anta ne ko d'a na?" Ya amsa yana murmushi,"Ita ma ta san dan ka ne Alh. Ya juya kan ta,"Amshi na ce, ba ruwan ki da zancan Naseer." Ta sa hannu ta kar6a tare da godita mai tarin yawa. Bata gama rufe baki ba. Naseer ya bugo sallama, ya shigo, suna amsa masa. Bakin sa har kunne, "Ah! Alhaji, na ga motar ka a waje. Ai ban san za ka zo ba, da ban fita ba." Ya ce, "Ai wajen Malam na zo, shi yasa ban ce ma zan zo ba." Ya dan duk'a yana gaishe shi. Bayan ya amsa, ya k'ara da cewa,"Ni zan koma kenan." Suka wuce. Naseer ya taka masa zuwa, zaure. ya sallame shi, ya dawo ya bar su tare da Malama Balarabe. Umma na ta k'irgan kudaden ta 'yan d'ari biyar-biyar sabbabi dubu tara da d'ari biyar. A bisa dukkan alamu dubu goma Alhj ya so bayarwa, sharrin sababin kudi ne, d'aya tayi munafunci ta like can jikin 'yar uwanta a aljihu. Naseer na shigowa. Ya amshe su yana fad'in,"Su Umma kenan, ina nawa kason? Ta ce,"Ba ga su nan a hannun ka ba, diba mana." Ya zauna gefenta,"Zarah fa zan siya wa Cakulet." Ta fige tana fad'in komai Zarah, bakin ka bai ko gajiya." Yayi 'yar dariya "Umma ke ma fa kullum sai kin tambaye ni ita, me yasa na ki bakin bai gajiya?" "Ban sani ba." Ni kuwa na sani, son ta ki ke yi." Ta mike ta wuce uwar daka, don adana kudinta, ta bar shi nan yana mata dariya. Kafin ya ce,"Yanzu ma cewa tayi in gaishe ki. Na baro Inna shirye-siryen, dambu na ce su aje min, zan koma in ci. Za ki ci,in zo miki da shi?"Ta fito kofa, ta ce,"nagode.......Sallamar Malam ta hana ta k'ara wani abu." Ya tafi? Ya amsa." Ya tafi. Kai ba mu wuri. Magana za mu yi." Ya cewa Naseer yana kallon sa. Ya kwashe makullai, ya wuce Sabon bangaransa, ya bude ya shige yayi kwanciyar sa, don hutawa kafin la'asar ya fita filin sukuwa. Yana bada baya. Malam ya zauna kamar yadda Umma ke zaune zugum. Yai dan jim, kafin ya numfasa ya ce,"Yanzu ya ki ke ganin za'a 6ullo wa a'amarin nan?" Gada daya na rasa na yi." Ta ce,"Kai, ko ni? Ta yadda za'a fahintar da iyayen Zarah, shine magana." Cikin damuwa ya ce,"Ashe dai kin fahince ni. Wallahi Alhj ya cika min ido, sannan ina ganin girman sa da mutuncinsa, babu yadda za'a yi in ce masa wannan abu bazai yuwa ba. Ta ce,"Malam, ai iyakar kauna ce wannan. Duk wanda ya dauki dan sa ya ba ka, shakka babu ya gama da kai. Balle irin wadda muke ganin matsayin mu bai kai ace mun je neman aure gidan Alhj ba,sai ga shi da kan sa ya kawo mana. Kar6a ya zama dole, idan akwai abinda ya wuce dole ma, du ya wajabta a kan mu. Ina gani ka fara zuwa ka sami Malam Lawal ka shaida masa ka nemi shawararsa,ya nisa ya ce,"Haka din za'ayi. To shi dan gogan fa? Ta ce,"Je dai ka gama da babbar magana. Ya mike yana fadin, "Yanzu kuwa." Ya fice ya barta da zabgegen tagumi. Damuwar ta daya, yadda za'a shawo kan iyayen Zarah, da ita kan ta. Bus din da M. Balarabe tare da M.Lawal ke ciki, ita ke tafiya bisa titin da zai kai su Sabon gari. Suna zazzaune gidan gaba. M.Lawal ke fad'in "Malam Balarabe na ka kwantar da hankalin ka. Wannan ba wata maganar zafi bace, abu ne na fahinta, na kuwa san M.Umar ba shi da matsala, zai fahimci komai." Ya ce,"To ita yarinyar fa? Ba ka ganin ba za ta yi zaton da man can Naseer na neman yarinyar bane? Ka san fa mata." Ya ce,"Ina baka, ka na roko, kai kuwa. Na daina Allah ya kaimu lafiya. "Shi kenan abin cewa.Cikin kankanin lkc suka sauka a kasuwar mata. Da kafa suka gangara wajen cinikin sa, inda yake gyaran kekuna na hawa. Tun daya hango su yake fara'a har suka iso. Suka yi musabaha tare da yiwa juna sallama.Cikin shagon da yake tara kayan aikinsa nan ya baza ta6arma, suka zazzauna.Jikinsa na rawa, ya fice minti 3 sun yi yawa, ya dawo da sassanyan ruwan leda (pure water), ya aje a gaban su, ya dauko ya mikawa gudu-guda,"Ku sha ruwa don Allah. Kai sannan ku da zuwa. Kun dauko rana." Malam Lawal ya ce,"Gaskiya yau ana zuba rana." Bayan sun kammala da ruwan sanyi, sun gaisa, Malam Lawal yayi gyara murya, ya ce,"M.Umar wata magana ce gagaruma ke tafe da mu, shi yasa ka gan mu cikin ranar nan face-face. Ina kasuwa M.Balarabe ya zo min, hankalinsa tashe yake ya gaya min Alh. Basheer mai gidan Naseer ya zo dazu har gida, ya same shi yake ce masa yana son hada zumunci, saboda kaunar da yake wa Naseer, watau ma'ana ya ba shi 'yar sa ya aura. Yayi masa bayanin akwai wacce aka ba shi tuntuni, amma ya ce babu komai sai hada 2, shi zai dauki dawainiyar komai. Hakika na san gaskiya hankalin M.Balarabe a tashe yake, don bai san yadda zai fuskance ku da zancen ba. Hatta shi kansa Naseer din bai san halin da ake ciki ba. Saboda shi Alhj bai gaya masa ba, kai tsaye wajen Malam Balarabe ya zo. To shine na ce ba mu ga ta zama ba, dole mu zo mu baka hakuri, don Allah don son Annabi, kar wannan abu ya kawo wani sa6ani, a bar shi a shirin Ubangiji. Don Allah............. Da sauri Malam Umar ya dakatar da shi da hannun sa, kafin ya ce,"Haba Malam Lawal wanna ai abin farin ciki ne, domin kuwa na tabbtar da kauna ce da yarda ta sa Alh. Basheer ya kaddamar da wannan al'amari, shi kuwa Naseer ya cancani a taya shi. Murna, saboda ya sami gatan da ba kowa ke samu ba. A matsayin na na uba ga Naseer, ina mai tabbtar ma ku da cewa ni ne zan amshi waliccinsa ranar dauri auransa a kaduna. Allah ya nuna mana ranar lafiya. Malam Balarabe kar ka ji komai akan wannan abu. Ina mai murna tare da farin ciki, addu'ar mu kawai. Allah ya taya shi rikon su bisa adalci. Suka numfasa, kalaman Malam Umar sun matukar gamsar da su. Malam Balarabe ya ce,"Mun gode kwarai da gaske. Sauran Zarah a rarrasan mana ita. Idan ma zai yuwu, ka turo min ita ni in rarrashe ta da kai na." Yayi murmushi,"Babu damuwa, kar ka dora wani tunani akan Zarah, zan mata bayani, Zata fahimta Insha Allahu. Yaushe ne Alhjn ya ce ranar bikin?" Ya ce,"Ai ina ganin hadawa za'ayi rana , don mu kawai yake sauarar mu gama kimtsawa. To shi kenan. Allah ya kai mu lkcn." Suka amsa da amin." Sun dan jima, suna hirarraki akan al'amarin, sannan suka yi sallama, suka koma. Malam Umar bai kawo tunanin komai ba, ya dorawa ransa, illa addu'ar Allah ya za6a mafi alkhairi. Idan kuma auran ya tabbata, to Allah ya zaunar da su lafiya. ************ Misalin karfe 1:30 na rana Naseer ya farka barcinsa, yayi alwala yayi sallah. Bai ci abincin Ummansa ba, don ya sa Inna ta aje ma sa dambu. Yana kokarin ficewa. Abban sa yayi kiransa falo. Can ya iske Umma a zaune, yana shiga ta ce,"Ka ga abincinka a kicin? Ya ce,"Ban shiga kicin din ba, kin ma san na gaya miki Inna za ta aje min dambu." Ta ce,"Yayi kyau." Abba ya ce,"Naseeer, ban hankalinka nan. Alhj Basheer ya ce, ya ba ka auran 'yar sa, saboda haka ka je ku ga juna, ka yi masa godiya. Insha-Allahu da na Zarah za'a had'a, na ma riga nagayawa Malam Umar, mun gama magana." Tun daya fara magana, idanuwan Naseer ke kafe, yana kallon Abbansa. Gaba daya tsigar jikinsa ta mike, wani abu ya taso ya toshe masa makoshi, da kyau yayi iya cewa,"Abba ai ba mu yi wannan maganar da shi ba, maganar makaranta kawai mu ka yi, na kuma gaya maka. Ina ni, ina neman 'yar Alhaji?Gaban Umma ya fad'i, ganin yadda Naseer ke magana hankalinsa tashe. Kan ka ce kwa6o, kyawawan idanuwan sa, sun kada. Abba ya ce,"Kwantar da hankalin ka Naseer. Na san akwai maganar Zarah a gaban ka kuma ka na sonta.Duk na shaidawa Alhj. Ya amince a hade. Ina rokon ka Naseer da ka dubi girman Allah, ka dubi so da kaunar da dan tahalikin nan yake nuna mana. Ka kar6i wannan kyauta da hannu bibiyu. Ka je ku gaisa da yarinyar nan, sannan ka yi wa Baban ta godiya.."Umma ta amsa,"Alhaji ya gama maka komai Naseer, ka yi hamdala ga Allah daya hada ka da mai son ka. Sannan ina son ka sani, idan ka amshi wannan kyauta, mu ka daraja, idan kuwa ka butulce. Wallahi-wallahi ka tozarta mu Naseer. Sanin kan ka ne, matsayin gidan Alhj ya fi karfin mu, sai ga shi Allah ya kai ka wajen. Babu abinda ya dace kai, illa ka kara kusanci da yi wa Allah godiya ta hanyar amsar wannan magana cikin farin ciki da zuciya daya. Ka ji? Ya dube ta jim, kafin ya ce,"Na ji.." Ya mike ya ci gaba da fadin,"Ina zuwa." Abba ya ce,"Ina zaka, ba'a gama magana ba." Bai ce komai ba, ya dawo ya zauna. Yaushe za ka Kadunan? Gobe." "A'a yau ya kamta ka tafi. Menene na jira sai gobe? Ko kuwa Umman shi? Ta ce,"Haka ya kamata. Shi ma zai ji dadi, zai kuma san ka dauki abin da mhinmanci. Ya ce,"To Abba." Ya ce,"To je ka ci dambun, daga can ka wuce kawai. To din dai ya sake fadi, ya mike yayi waje har wani jiri yake gani. Umma ta bi shi da kallo, ta juyo kan Abba ta ce,"Naseer da mata 2, wannan mahaukacin Yaron." Ya ce,"Sai anyi da gaske. Fuskar sa akwai alamar tambaya. Kar kuma ki mance halin dan ki, akwai kafiya." Ta ce,"Allah zai tsare. Shigowar Sageer kenan cikin shagon dinki, daga makaranta yake, kamar tare suke da Naseer, yayi fakin a sikwane ya shigo. Ido jajur, bakinsa na rawa, "Sageer zo! Ya juya, ya koma mota. Nan da nan shi ma Sageer ya sami kan sa cikin faduwar gaba. Motars ya same shi ya hade kai da sitiyari." Menene Naseer? Ya dube shi zufa sharkarf jikinsa, ya ce,"Alhj ya kashe ni. Da na san duk abinda yake min ba saboda Allah bane, da tuni na rabu da shi." Cike da tsananin mmk Sageer ya ce,"Me yasa ka ke wannan maganar?" Dazu da safe ya zo kai tsaye ya sami Abba ya ce wai ya ba ni 'yar sa in aura. Me yasa? Don me? Wai kuma Abba ya amsa masa, maimakon ya ce ba zai yuwu ba kawai. Yanzu saboda Allah me su ke son in gaya wa Zarah? Kai ni gaba 1 ma ban ji ina wannan ra'ayin ba, don haka ba zan aure ta ba. Su da suka kar6a, sa san yadda za su yi." Yana maganar sa. Sageer na kallon sa, shi kan sa zuciyar sa ta girgiza, saboda Zarah da ke tsakani, amma da yayi tunani nan da nan yayi amfani da kwakwalwarsa,"Yanzu ka na nufin babu zaancan Zarah! Wai in hada su 2 ayi biki gaba 1, sbd an gaya masa yawon kida za ni!Dan murmushi yayi ya ce,"In don haka ne Naseer, ai babu laifi, za ta fahimce mu. Amma magana ta gaskiya. Alhj kauna ya nuna maka......... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-10 Posted by ANaM Dorayi on 04:42 PM, 09-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ .Cikin zafi ya katse shi,"Sageer fita a motan nan!" Ba zan fita ba Naseer....."Ka fita na ce ko? "Ba zan fita ba Naseer, me yasa kai kullun ba ka son gaskiya? Ko kuwa ka na nufin dole sai na goya ma baya, mu kwance wa iyayen mu zani kasuwa? Ba haka rayuwa take ba Naseer, ina kuma mai tabbatar maka cewa ba karamin kaunar ka Alhj yake yi ba, tunda har ya ce ka hada su 2, ka aura. Ya kamata ka duba wannan, idan ma ba ka dauke shi a hakan ba, sai ka duba darajar su Abba, su duka amshi maganar." Wani mahaukacin kallo yake masa. Wanda ya nuna Zahiri lallai kura tayi lafiya, da tuni ya kashe masa baki, ya gama sarewarsa kaf, sannan ya ce,"To na ji Baba na, sai anjima ko?" Sageer ya karkada kai cikin murya mai taushi, ya ce "Naseer, Zarah na da tunani, tana da hankali, domin ta ta6a yin wasu maganganu wajen nan, wanda yasa ka ga na hakikance za ta fahimce mu. Ka ban izini in je ni kadai in yi mata bayani, zan dawo ma da amsa." Ya nuna shi,"Ban aike ka ba! Babu kuma ruwanka a cikin wannan maganar. Fita-fita kawai! Yayi jim, suna kallon juna, sannan ya ce,"Naseer saurin fushi ba naka bane, ka bi maganar nan a hankali tare da dogon tunani kafin ka yanke hukunci. Auran mata 2, a lokaci daya, ai na dan gata ne, yaushe rabon da ka ji anyi irin sa? Kamar Naseer ya kwarma ihu yake ji, saboda bakin cikin Sageer ya ki fitar masa daga mota. Zuciyar sa na ta kara tafarfasa.Sageer na hada ka da Allah da Manzonsa ka fita a motan nan, ka ki ko? Ya ce,"Ai ita kanta wannan motar Alhj ne ya ba ka ita, menene damuwar ka akan zama na a cikinta? Zuciya ta shake shi tamau! Idanuwansa suka kara firfitowa jajur! Ya ce,"Haka ne, ka kuma kyauta da ka tunasar da ni. Saboda haka ga ta nan ka maida masa abar sa." Cikin za fi ya hankade murfin motar, yayi waje. Ganin haka yasa Sageer ya fito ya tarbe shi,"Zancan bai kai haka ba Naseer. Tunda na gaya ma gaskiya ba ka yarda ba, shikenan. Ta Malam bata wuce amin. Ka yu hakuri ka koma motar ka." Ya ce,"Ka san Allah sai ka maida ta, ka ga daga nan ya ba ka tukuicin 'yar, ba shi kenan ba. An raba gardama? Ransa bace ya ce,"Allah ya tsare ni. Ka san ba haka na ke ba, ba kuma zan zama ba." Uban tsaki ya ja. Sageer na kallo, ya tsare dan aca6a ya dare, ya bar shi nan yana kwala kira. Jingina yayi da motar rungume da hannayen sa, yana kada kai. "Rigima sabuwa, me yasa su Abba suka kar6i maganar nan, ba tare da sun shawarci Naseer ba? Kodayake suna ganin sun isa da shi ne. Yakamata Naseer ya gane hakan." Ya numfasa ya ce,"Allah ka dai-daita, idan da alkhairi." Ya bude mota ya shiga, ya ja ya maida ta gidan su yayimusu bayanin yadda suka yi da Naseer din. Nan ya tafi, ya bar su da hannu a kunci cike da zullumi me zai je, ya dawo? Filin sukuwa mai mashin ya aje Naseer, ya fiddo kudi ya mika masa, yayi gaba abinsa, shi kuwa waje ya samu ya zauna, ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Abin kamar a mafarki yake ganin sa. Zuciyarsa na yi tayi masa saka iri-iri, yana shigewa. Wucewar minti 15 da zaman sa, wayarsa ta buga.Da kyar ya ciro ta. Ya duba lambar. Abba ne ke kiran sa. Kawai yasan Sageer ya je gidan kenan, don haka ya maida wayar aljihu, ya ki dauka. Mikewa yayi ya sake neman dan aca6a ya dare suka yi wa Tudun Jukun tsinke. Yakubun da ya je nema, bai dawo ba, amma Naseer B yana nan, don haka bayan sun gama gaisawa da mutan gidan, dakin Naseer B suka zube a katifa. Naseer B ya kare masa kallo, kafin ya ce,"Ban ga motar ka ba? Ya ce,"Gida na bar ta." Ya ta6e baki,"Aca6a ka ke son hawa? Jin dadi." Yayi shiru bai tanka ba. Wai baka da lafiya ne? Na ga kana yi kamar mai ciwo?" Ya kada kai, ya ce,"Masifa ce ta same ni." "To fa, wacce irin masifa? Bai 6ata lkc ba, ya warware ,masa halin da ake ciki. Take, yanke Naseer B ya turnuke da bakin ciki. Hassada ta kama shi, yayi kasake tamkar mai tunanin abin kirki." "Taf! Lallai Naseer wawa ne, abin farin ciki ya sa me shi, amma ya ce masifa." Auran jari? Mutum ya sami wannan, ai ya haye. Mts........ Ya ja dogon tsaki,"Da ni na sami haka, ko ma wace yarinya na ke nema, ai don uban ta dole ta daga min kafa, ta nemi wani mijin, yaushe zan tsaya bata lokaci na auran su su 2? Wani wawan tsakin ya kuma mamaitawa, sannan ya ce,"Yanzu kai ina mafitar ka? Ya ce,"Wallahi ban sani ba, ni dai yarinyar nan ban ta6a ganin ta ba, kai koda ma na ganta, ba za ta yi min ba, tunda ina da wacce na ke so. Ni abinda ya fi bata min rai, wai kai tsaye Abba ya samu. Ai da sai ya kira ni ya ce Naseer 'ya ta ta rasa miji don Allah ka aureta. Zan maka komai. Ka ga ni na san bayanin da zan masa.Naseer B ya zazzago idanuwan munafunci ya ce,"Gaskiya ne. Ai dama idan ka ga irin haka, kwantai yarinya tayi, ake neman kai da ita. To yanzu kai zama za ka yi haka kawai, ba za ka ta6uka komai ba? Kamar yayi kuka yake kallon sa, domin hawaye ne tamke a idonsa,"Me zan iya yi B? Bayan na gaya maka. Abba yayi ruwa, yayi tsaki kamar su za su zauna da ita. Mts! Ya kama baki yana kada, kada,"Amma ka ban mmk. Shi kenan an maka auran dole. Sabon yayi kenan, namiji da auran dole. Na ga ko matan ma ba yarda suke yi ba. Wata ta sha fiya-fiya, wata ta banki kalanzir, koda yake Malamai sun ce yin hakan mutuwar kafirci ne. Sannan kai ma na ka na lokacinka ai ba za ka mutu saboda 'yar Alhaji ba. Amma ina ganin ai za ka iya daukan jaka, ka bar masu garin, sa gane kuran su." Ya dube shi da kyau ya ce,"Ka na nufin

Chapter 9 of 11