Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
nemi sanin mahaifin Naseer kuma ba 6ata lkc, ya kulla zumunci da shi mai karfi gaske. Sanin mahaifin Naseer Malam Balarabe, ba mai karfi bane, shi yasa Alhj ke yawan yi masa alkhairi akai-akai. Kwarai a halin da ake ciki yanzu Malam Balarabe yana alfhari da Naseer kuma yayi imani a polo abincin Naseer yake. Shi yasa Allah ya shimfida masa so da kaunar sukuwawan da shi a da yake ganin ba karamin saba masa yake yi ba. Sai dai duk da haka yana yi wa dan sa huduba da kar ya mance da ci gaban karatunsa, kamar yadda kullum Sageer da Zarah tare da iyayen ta ke masa matashiya akan gyara jarabawar sa, don ci gaba da karatunsa na gaba. Amma shi dan gogan ya riga ya raja'a akan abin da ya sa gaba, Kuma yake da buri a kan sa. Ko alama baya waiwaye, wanda hausawa ke wa kirari da adon tafiya. Inda ya sa gaban sa, kawai can yadosa bil hakki da gaskiya. A yan tsakanin ne kuma Sageer yayi nasara samun gurbin karatu a (poly) da ke Gaskiya, Tudun-Jakun Zariya, a fannun kasuwanci (Businees Admin). Baba 6ata lkc, ya kama karatun zango-zango, kuma abn mmk duk tare da gudumuwar aljihun Naseer karatun na Sageer ke tafiya. Bayan haka bai daina zuwa wajeb dinkinsa ba, a halin yanzu ma ya kware babu irin dinkin da ke gagaran sa, ta nan ma baya rasa taro sisi, duk da dai ogan sa, bai yaye shi ba. Yana nan tare da shi. Haka al'amuran suka rinka tafiya dai-dai da yadda Allah ya shirya wa kowa rayuwar sa. Soyayya tsakanin Alhj Basheer da Naseer kuwa kara shiga ran Alhj take yi tamkar yadda Naseer ke kara fito da (DABAI RIDERS) a duniyar Polo ciki da Wajen Najeriya, watau kasashe makwantan mu. Tuni Yakubu ya sakar wa Naseer kambunsa gaba 1, yana mai alfaharin shi ya kawo wa Alhj gwarzon Da, wanda yake ganin ma ya na taka rawar da shi bai taka rinta ba. Shi yasa kullum kirarinsa da babbar murya yake masa, "NaseerJah-Jah!" ***************** . BAYAN SHEKARu BIYU. A cikin shekarun biyun nan, ba sai mun tsaya dogon surutun irin tambarin da sunan Naseer Jah-Jah yayi a duniyar Polo ba.Musamman a cikin garin su da unguwar su, idan aka yi la'akarin da irin kwarjinin sa tun farko, balle yanzu daya kasance duk wanda ya dube shi, ya san yana hutawa,kuma yana kan lokacinsa,yayi fad'i, ya yi zabgege, ya k'ara fari da ka ganshi, ka ga d'an wasan motsa jiki. Maganar kyau da iya shiga irin ta sutura, abin ba dama, domin Naseer ya dad'e da gogewa wajen iya tsafta. Don haka ya zarce wa tsara. Ya zama abinda bature ke kira (TALK OF THE TOWN), wato abin hira a gari. Ta yadda ya tsara rayuwar sa. Abin ya na da ban sha'awa, saboda babu girman kai, babu wulakanci kuma abin hannu sa bai tsokane masa ido ba. A duk lokacin da yake gari, za ka ga samari na yawan sintiri gidansu. Can kuma 6angaren tauraruwar sa, komai tafiya yake dai-dai da ci gaban da aka samu, domin kusan a yanzu Naseer shine ragamar karatun ta. Bai kyashin kashe ko nawa ne a dangane da hidimar Zaran sa. Wani abin sha'awa da ya fi kowa, a cikin gidansu yake shirin fitar da wani gini mai bn mmk. Kasancewar gidan k'aton gaske ne, ko dama rashin kud'i ne yasa yake a wulak'ance. Tuni aka fitar wa iyayensa 6angarn su. Shi kuma na sa 6angaran aka shimfida filat mai d'akuna 3. Ba shi da buri daya wuce ya tsara wa Zarah abubuwan da zai fiddo ta daga cikin tsara, tunda ga shi Allah ya ce su huta." Kwatsam! Allah da ikonsa sai ga takarda daga k'asar Ghana zuwa (DABAI RIDERS), suna neman izinin d'aukar Naseer haya na wata 1, don gudanar da wasa a wata kungiyar wasan Polo da ke can Ghana. "Al'amarin yayi wa kowa dad'i. Musamman Alhj Basheer da Yakubu kuma babu 6ata lkc. Alhj ya amince masa da tafiyar, babu wani sharad'i ko wata tsatstsaurar doka. Ranar tafiyar sa, yayi sallama da kowa, sannan ya nufi gidan su Zarah. Tana zaman jiran sa, kamar yadda ta san yana tafe. Kallo daya yayi mata, ya gane hankalin ta a tashe yake, ya karkade kai ya ce, "Wai ke ba za ki daina wannan kuncin ba? "To ko in fasa ne?" Ta ce,"Kasan ban isa in hana ba." Da sauri ya tari numfashin ta." Kina ganin ba ki isa ki hana tafiyar nan ba? Lallai za ki sha mamaki, idan aka wayi gari gobe ki ganni a garin nan.Me zan samo a Ghana, wanda ya wuce farin cikin ki? Look Zarah! Ina ganin ke har yanzu ki na daukata a matsayin yayanki ne, ba ki san cewa akwai banbnci ba. Wallahi, kin ji na yi miki rantsuwa ko? Muddin ba ki saki jikin ki akan tafiyar nan ba, zan fasa ta, kuma babu wanda zai sani dole. To kila ko su Abba su cika min ido. Ta numfasa ta ce, "Wai! Ai kuwa na gode Allah, tunda akwai su Abba, don na san zai wuya inji sanyi a raina, bayan na san yaya na zai bar ni tsawon wata 1, "Alhali ban saba ba." "Dan murmushi yayi, kafin ya ce,"To ai ba zan bar ki haka kawai ba, kin ga wannan? Sabuwar wayar ki ce dalilin siyan kawai don murinka sanin halin da muke ciki ne, kodayaushe. Amshi nan."Ta saki baki tana kallon kwalin rantsatstsiyar wayar da aka ce tata ce a lkcn 1, kuma tana tambayar kanta yaushe yayana ya siyo min NOKIA ta hannu na?" "Kin amsa na ce, ki ka baje min ido, ki na kallo na." Tasa hannu ta k'arba,"Amma dai yayana ka na son kashe kudi, ita wannan Sabis d'in bai zuwa Ghana ne?" Dariya ta sake ba shi, ya ce,"Ina jin hakan a jiki na, zuciya ta na gaya min tana gargadina da cewa kai Naseer kar ka bar Nijeriya, ba tare da ka sakewa k'anwar ka sabuwar waya ba, don ka san ta hannunta ta shekara." Zai iya kasancewa ta fara bada matsala. To kin ji dalili, da a sami matsala, gara ayi wa tufka hanci. Ko me ki ka ce?" Ta d'an rausaya kai cike da mamakin yayanta, ta ce, "Godiya kwando-kwando yayana. Allah ya k'ara bud'i." Bai amsa ba. Wayar sa ta hau ruri, ya jawo ta cikin alhu ya duba lambar. Alhj Basheer ne, kamar yadda yake a rubuce cikin wayar (Alhaji). Ya dube ta ya ce"Mintu 2, "Sannan ya danna Ok." Suna magana da Alhj. Amma ita Zarah kallon sa take yi, kasancewar hankalin sa ba ya gunta. Sai ta sami damar kare masa kallon da ta jima da mancewa da ranar da ta yi masa irin wannan kallon. Nan take zuciyar ta, ka karan ta mata ba k'aramar sa'a ta yi ba, da samun Naseer. Kwarai ta tantance Naseer watanne, tamkar yadda take Zarah. Anya kuwa 'yan mata za su kyale mata Naseer d'in ta ita kad'ai, yadda ya shiga yana fita gari da kashashen duniya da irin wannan baiwa da Allah yayi masa???"Nan da nan kishi ya rufe ta, idanuwanta suka fara kad'awa, sannan kafe suke tana kallon sa, ba tare da ta san tana yi ba. Kusan minti 2 da kammala wayarsa. Shi ma yayi zurun yana maida martani. Ganin idanuwan ta sun fara ja, shi yasa ya murza yatsunsa biyu, suka yi k'ara bisa fuskar ta. Cikin kunya ta sunkuyar da kai. Sai kuwa tambaye yake, "Menene?" Ta ce, "Ba komai." Kin san Allah, ban yarda ba, kuma ba zan bar wajen nan ba, sai kin gaya min ko menene ki ke tunani." Ta riga tasan halin yayan na ta, don haka ta d'an dube shi, ta ce, "Mata na zuwa kallon polo a Ghana?" Tambayarta ta d'aure masa kai, kuma take ya gane me take nufi. Amma sai ya nemi sanin dalilin tambayar ta, "Me ya sa ki ka ce haka?" Sannan ba ki ta6a tambaya ta hakan ba, sai yau? Shiru tayi, ta rasa bayanin da za ta yi, don ita ma ba'a son ranta tayi masa tambayar ba. Jin tayi shiru tsawon 'yan dakikai, shi ya sa ya ce, "Zarah, dube ni nan." A karkace ta dube shi, jim ta sauko ido. "Zarah, son ki ba karya bane a ciki rai na. Kar ki mance, tun bn san me zuciya ta ke nufi a game da ke ba, har na gane so da kaunar ki na ke yi. Ma"anar tun yarinta, har zuwa sanin ciwon kai na, ban jin akwai abinda zai cire min soyayyar ki Zarah. Don kin jima cikin raina shekaru masu yawa.Saboda haka ki kwantar da hankalinki, ni yayanki nai miki alkawarin har abada ke kadai ce, ba kari balle maganar canji. Kin ga zancen mata na zuwa kallon Polo ko ba sa zuwa, duk ba matsala da ta shafe mu bace. Kin amince?" Kad'a kai tayi, ta d'an nisa kafin ta ce,"Na gode yayana, amma maganar k'ari, ka na nufin babu zancen kishiya?" Da sauri ya amsa, "Nufe na kenan Zarah. Kin isheni rayuwar dauniya, domin komai na ki yayi min yadda ra'ayina ke buk'ata." Wannan karon ta kalle shi ido ciki ido, sannan ta ce, "Ban ji dad'in wannan maganar ba yayana, don ka shigo hurumin da ba na ka ba. Wannan hukunci ne na Ubangiji, wanda bai kamata ko ma ince bai halasta ko wane D'an- adam yayi shishshigi a cikin sa ba. Ka ga dai........."ya katse fuska daure, "Me ki ke nufi? Na yi miki k'arya kenan?" Ta ce,"Ban ce ka min karya ba, amma magana ta gaskiya, duk macen da aka yi mata alkawarin ba za'a yi ma ta kishiya ba, ta yarda ta amince. A hakikanin gaskiya ta yaudare zuciyar ta. Don shi aure al'amari ne na Allah, tamkar haihuwa da mutuwa. Ubangije ne kadai ya san yadda ya shirowa bawan sa rayuwa. Shi yasa na ke ganin bai halasta masoya su rinka yi wa junansu ko wane irin alkawari a hurumin da ba na su ba. Ina fatan yayana ya fahimce ni....? Tun da take mgn, yake kallon ta, sai dai laffuzan ta kawai ke sosa masa rai. Bai kamata ta ki amincewa da shi ba, don shi hakikanin gaskiyar sa ya fad'i. Kenan duk son da yake nuna mata karya ne. Nan da nan ya hassala. Mikewa yayi ya sungumi jakar sa da ke gefe ya ce, "Allah ya sa mugana."Ita ma ta mike,"Yayana fushi ka yi?" Tuni ya kai kan sa tsakar gida. Inna na zaune kofar dakin Malam Umar can ya nufa. "Inna na fito." To dan Inna. Allah ya kiyaye, ya tsare mana kai duk inda ka ke." Sai ga M.Umar ya fito wanka, yayin da Naseer ke amsawa da "Amin Inna." "Har ka fito?" Inji M.Umar. Ya amsa, "Eh, "Baba." "Madalla-madallah, to Allah ya ba da sa'a. Sai a kiyaye da ibada, ita ce gaba da komai, ka ji?" Ya ce,"To Baba na gode. Na bar ku lafiya." Ya wuce suna ta sa masa albarka, kafin Inna ta ce, "Ke ba za ki k'ar6ar masa jakar bane, ki raka shi?" Ta wuce da sauri ta bi shi, tana fad'in,"Kawo jakar yayana." Kamar ma bai ji ta ba, ya shige zaure abinsa. Da gudu ta karaso zauren, haba yayana, bai kamata ka yi saurin fushi haka ba." Ya juyo a fusace, har ta ji tsoro a zaton ta duka zai ka mata, ganin yadda ya nuna ta yana fad'in "Ki koma! Allah kar ki biyo ni, na gaya miki! Kin ji ko?" Ya juya ya fice daga zauran. Tayi tsaye cikin zauren shiru, idanuwan ta suka kawo kwalla. Menene abin fushi a bayanin da ta yi? Don dai ba'a son gaskiya?" Ai kuwa wannan maganar haka ta ke yayana, ko ka ki, ko ka so ba zan yaudari kai na ba. Alhalin na sani kai mijin mace 4 ne." Ta fad'a a ranta. Wanda ya k'ara birkito mata da wani salon kishi, har ya tilasta mata tsiyayar hawaye.Kusan minti 2 tayi a tsaye, sannan ta goge fuskarta da kyau ta dawo cikin gida. Daki kawai ta shige, ranta in yayi dubu, a 6ace yake. Shi ya sa ma ko sake kallon sabuwar wayar daya kawo mata ma bata yi ba, illa iyaka, ta bar nan tsakar daki, har Inna ta shigo ta gani. ********************* Kwana 2 kenan da tafiyar Naseer Ghana, amma babu motsin sa. Ko alama Zarah bata cikin sukuni, kuma yayan na ta ya bata mamaki. Wannan irin fushi haka, daga gaskiya? Zaune kawai take cikin ajin su, duk sauran dalibai na ta harkokin su a dalilin tashi (Break) din da aka yi. Amma ban da ita. Tunani ya addabe ta, ko alama ta kasa tantance me shirun Naseer yake nufi? Shin yana son ya nuna mata cewa dole sai ta yarda da ra'ayin sa ne? Ko kuwa so yake ya tilasta ma ta sakin na ta hangen? Ta nisa tana mai tsananin kewar yayanta, saboda ta tabbatar da shi ma yana cikin yanayin da take a halin yanzu, kuma ta yarda ta amince ko bayan sun yi aure, ya ce zai k'ara wani, ba wai ya na nufin ya daina son ta bane. Son ko wacce mace, na tasiri ne a zuciyar mijinta dai-dai da yadda ta zauna da shi. Duk da dai akan sami akasi ta ko wane 6angare, a sami rashin jituwa tsakanin ma'auranta, idan ba'a kai zuciya nesa ba, sai ka ji ana cewa a rabu. Amma magana ta gaskiya, ita ce so yana tafiya dai-dai da rikon amanar zaman tare. Yarda da juna, kyautayawa ta kowace fuska, hakuri da juriya. Duk ma'auratan da suka mallaki wannan, shakka babu za su ci ribar zamantakewar auren su. Musamman mu mata da muke zama a karkashin mazajen. Sai ki ga ko mata nawa ya ajiye, ba zai ta6a daina ganin kimar ki ba, a idaunsa. Sai dai miji butulu maras tsoron Allah. Zarah ta yarda ta amince da wannan, saboda haka take ganin ba za ta iya sakar wa Naseer jayayyar da suke yi ba. Kan ta a kife yake bisa tebur yayin da take rattafo wannan dogon tunanin. Sallama kawai ta ji bisa kanta, ta dago da suri ta dubi masu sallmar.Wasu kyawawan 'yan mata su 3 ta gani a tsaye, suna mata murmushi. Ta zauna sosai, ta ce,"Sannun ku." Dukkansu suka amsa, kafin guda ta ce,"Don Allah tambaya muke? Ta ce Allah yasa na sani.." Ta ce, "Ke ce Zarah?" "Eh ni ce." Mai magana ta ci gaba,"To ni sunana Lubabatu, sai kawaye na. Wannan Hauwa'u, waccen Maryan, dukkan mu muna S.S.3. Muke,...... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-06 Posted by ANaM Dorayi on 02:00 PM, 07-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ .may be ko ki na ganin mu anan." Ta karkada kai.Bisa teburin Lubabatu ta haye, kafin ta ce,"Dama abinda ya kawo mu, kin gane? Kawai ance yarinyar da Naseer Jah-Jah zai aura tana cikin school din nan.Shi yasa muka ce ya zama dole mu ganki, sbd mu Fans d'in sa ne. Ina fatan kin gane.? Zarah ta dube su dai-dai ta ce,"Na gane kuma na gode."Maryam ta ce,"Kuma wallahi kun dace, dan ke ma kin mana." Hauwa'u ta amshe,"Gaskiya ne, amma duk da haka kin yi da ce, so handle him with care, kin san yaron yana kan lkcnsa."kan Zarah ya d'aure, ta rasa ta cewa ko dama ita ba mai yawan magana bace ko cikin ajin su, ba da kowa take magana ba. Shi yasa 'yan ajin suke ganin kamar tana da girman kai. Saboda kyan da take da shi. Alhali ba haka bane, haka Allah ya halicce ta. Jin tayi shiru, yasa Lubabatu ta diro daga tebur ta ce,"To mun gaishe ki, mu za mu ari na kare. Muna S.S.3, in case ko za'a gaisa."Maryam ta amshe,"Ai ko bata zo ba, mu ya zama dole mu rinka zuwa muna duba ta, a madadin sa, kin san an ce ya fasa "Ghana. " Haka." Inji Lubabatu, "To sai kin sake ganin mu." Ta ce, "Shi kenan, na gode," Suka wuce ta bi bayan su da kallo har suka bar ajin. Tagumi ta zabga, tunanin ta ya dawo sabo, don 'yan matan sun firgita ta kwarai. Ashe ma anan kusa da ita tana da abokan hamayya bata sani ba?Shine Naseer yake son ya cusa mata wani ra'ayin da ba shi yuwuwu ? Bayan bata ma san meke faruwa a wasu wurare ba. Tsoro ya kama zuciyar ta, ba na wasa ba. Shi yasa ta aje a ranta, zai yi wuya Naseer ya kasance na ita kad'ai har abada, kamar yadda shi yake hasashe. A susuce ta kasance zuwa tashi gida. Ko a gidan ma tunanin ta bai sauyawa ba. Saboda ya kamata ace ta san halin da yayanta yake ciki a k'asar Ghana.Kwanan sa 5, babu bayani.Abin ya gagari zuciyar ta, ga shi har su Inna sun fara tambayarta labarin yayan na ta. Cikin shagon d'inki ta iske Sageer da safiyar yau lahadi.abin ya ba Sageer mmk kwarai, jin cewa wai Naseer bai kira Zarah sa ba, tun tafiyar sa. Alhalin shi kusan kullum sai sun gaisa da shi. Don haka ya tsare ta da tambaya," Kin masa laifi ne kafin ya tafi?"ta ce, "Eh toh, k'ila a wajen sa zai iya zama laifin , domin ko a ranar ransa 6ace ya tafi." Nan take ta warware wa Sageer komai. Dariya Sageer yayi, sannan ya karkada kai, cike da mmkin abokinsa. Sanin hali, yafi sanin kama. Sageer ya dade da sanin halin abokin sa, wani fandararran mu2m ne, mai tafiya akan ra'ayin sa. Wannan AJININ SA YAKE. Saboda haka ya ce mata, "To ai ke Zarah yakamata ki yarda da aboki na, don kin san yana son ki sosai, kuma na san babu yadda za'ayi yayi miki alkawarin da ba zai iya cikawa ba."Ta ce,"Saboda Allah Sageeer da mutuwa, da haihuwa, da aure duk na wanene?" Ya ce, "NaAllah." Ta ce, "Don me mu2m zai yi katsalandan a ciki? Sai kuma an sami akasi, sannan a fara "Wallahi- tallahi, ita ta lik'e min?" Don haka ku ke yi ku maza, da zarar za ku k'ara aure, sai ace wa uwar gida "Wallahi ta nace sai ni ne. To ba za'ayi haka da ni ba Gaskiya.Sageer ya kama ha6a ya ce,"Zarah kenan, shi yasa mutumin naki ke cewa sbd lafuzan ki yake k'ara son ki. Yanzu tunda abin ya zama haka, ga lambar da yake kirana da ita, sai ki kira shi." Tuni take kallon sa, baki sake, yana yin, shiru ta ce,"Wai ka na nufin yana kiran ka?""Kwarai kuwa kodayaushe sai yayi min tsiya, idan na ce masa ban sami zuwa na duba masa ke ba. Kin san sha'anin School, ba time.amma ki yi hkr, ga lambar." Ta ce,"Kyale kawai Sageer, ai dai har ga Allah gaskiya na fad'i. Da kan sa zai neme ni." Ta juya ta fito daga shagon, Sageer ya biyo ta, yana magiya.Sannan ta tsaya ta amshi lambar, suka yi sallama ta koma gida da mmkn Naseerrrrrrrr......!!!watau shi a dole da gaske yake yi ko?" "Eh mana." Inji wani 6angare na zuciyar ta. Su Lubabatu suka fad'o mata, take nan wata kwakwalwar ta mai kaifin hankali, ta gaya mata,"Kin san Allah, kar ki amince, gara ki tsaya tsaka-tsaka, idan tayi ruwa rijiya, idan bata yi ba masai!"Da daddare ta kasance ita kad'ai ta rage, bata yi barci ba, wannan kad'ai ya tabbar mata da lallai son yayanta.Wasi-wasi kawai take yi, ta kira shi? Ko ta share kawai? Ina ta kasa daurewa. Laluba wayar ta tayi, ta loda lambobin a ciki ta hau kira. Amma har ta kaste, bai dauka ba.Nan fa abin ya kara damunta. Fushi masoyi, akwai dalili. Ko dai kishi, ko kuma anyi masa kwakkwaran laifi. Kafin safiya ta amsa laifin ta, na kin amincewa da furucin Naseer.Kwarai yana son ta, kuma watakila alkawarin da yayi mata, ya kasance tabbatacce.Ko karin safe bata yi ba, ta nufi shagon masu kayan waya.Sabon layin Etisalat ta siyo, hada da katin 200, ta dawo gida ta dannan sabon layin cikin wayar ta. Sannan ta loda katin da ta siyo suka shige.Sai ga ta da bonus na naira 100, take nan kudi suka zama 300,. Bata jira komai ba ta nemo lambobin da take son dauka tun jiya. Bugu daya, ta juyo muryar da take ta kewa kwanaki 6 kenan. Sai dai tayi matukar mamaki jin ya ce,"Kanwata kenan."Jikinta yayi mugun sanyi, a lkcn guda kunya ta mamaye idanuwanta, don haka ta kasa cewa komai, ta bar shi da kiran, "Hello! Ba za ki magana ba? Yi hakuri ki ce wani abu, inji." Hawaye suka cika fal! A idonta kafin ta ce,"Ai ka nuna min iyakata, me ka ke so ince?" Tana jin hucin murmushin sa kafin ya ce, "Ina zaton kin daina so na ne, shi yasa na hkr. Amma na amsa laifin, tunda Sageer ya min fad'a. Yanzu kashe in kira, kar kudin su k'are. Kafin ma ta kashe. Shi ya kashe. Jimawa kadan wayar ta, ta dauki ruri, ba 6ata lkc. Ta danna O.K, "Ban ta6a tunanin za kai min haka ba yayana, amma ba komai rayuwa ce." Ya ce,"Zancen dai ki ke so aci gaba da yin sa, ni kuwa tuni na watsar dashi, tunda ba ki yarda ba.Ni Naseerr na sharo ta ko? Ko kuma yaudarar samarin zamani ta zo gare ki kenan." Muryar sanyaye ta amsa, "Ban fad'i haka ba, ranka ya dade." Ai inda kasa nan ake gardamar kokowa. Ga fili, ga mai doki." Ya ce," "Ni Jah-Jah zan gwada sukuwa ta, wacce ta sha ban-ban da ta kowa. Insha-Allah sai na ba ki kunya."Ta ce,"Ni kuma? Sai dai 'yan matanka a sake masu kiran kan su, wai fans din ka." Kan sa tsaye bata amsa, "Ke ki ka san wannan, amma ina gargadin ki da ki kiyayi zargi da surutan 'yan karan kad'a miya. Masu ara su yafa. Alhalin ni bn ji ba, balle in gani. Muddin kika cigaba da sawa ranki cewa fans dina 'yan mata na ne, ina me tabbatar miki zuciyar ki za ta buga akan aikin banza." Aikin banza yayana?" "Eh mana....... "Wai kai a'a, ashe fa kishi ne ko? Ki na son yayanki kena. To na gode, sai dai don Allah ki rinka daurewa. Naseer na ki ne. Jah-Jah kuwa na fans ne a filin sukuwa. Kin amince da ni?" Ta ce,"Uhm...." Ya ce,"Ban amsa sosai inji, ba uhm...... Ba." Ta yi dan murmushi ta ce,"Na amince." To ya su Inna da Baba?" "Suna gaishe ka. Ni ba zan tambayi Ghana ba, don tai min ba dai-dai ba." Dariya ta ba shi, shi yasa ya ci gaba da tsokanar ta, suna hawa suna sauka." ******************* Wata guda da kwana 2,"Naseer ya dawo gida Najeriya, bayan ya kammala aikin da aka dauke shi haya a k'asar Ghana.Kamar kar su bar shi ya dawo, sbd iya aikin sa da kwarewar sa wanda yasa ba k'aramin masoya yayi ba a can maza da mata.Kaduna ya sauka daga Abuja, inda Alhaji da kan sa tare da Yakubu suka dauko shi a filin jirgi. Bargar dawakin Alhj suka wuce. Naseer ya warware gajiya, sannan aka maida bayanai akan kudaden sa da suka shigo ta banki Naira dubu dari shida, sun jima da shiga akaunt din sa.Alhj Basheer bai bukatar ko sisi daga hannun Naseer, maimakon haka ma take nan ya mika masa kyautar makullin mota, don nuna farin cikin sa ga manya-manyan lambobin yabon da Naseer din ya dawo da su, wadanda za'a aje tarihi a ofishin Alhj.Naseer kuka ne kawai bai yi ba, sbd murna da farin ciki. Bayan sallar azahar suka koma (Dabai Motors), inda Alhj ya nuna wa Naseer motar sa. (Honda civic) ce mai kofa 1, kowa sai taya Naseer murna yake yi.Shi kuma Naseer Yakubu ne kawai cikin ran sa, don komai Allah yayi Yakubu ne sila. Tankinsa cike da mai, yana gaba Yakubun na bin sa a baya akan hanyar su ta dawo wa Zariya.Allah ya kawo su lafiya, kowa ya nufi unguwar su. Arziki kashi, abin har daure wasu Umma kai yayi, wai yau Naseer din su ke jan motar kan sa. Ba abin mamaki a al'amarin Ubangiji, Don shi yake fitar da mai arziki daga talaka. Idan kuma ya ga dama ya fitar da talaka a jikin mai kudi. Shine kuma mai bada baiwa da hikima, mai daukaka mu2m duniya ta sanshi har yayi sunan da wani mai mulkin bai yi ba.Shine mai rufawa bawa asiri ta yadda ba wanda ya isa ya tona masa, har jama'a su rinka ganin shi wani abu ne.Ubangiji gare ka muke neman rufin asiri. Ya Allah ka amsa!...Amin ya Allah (ANaM) Allah ya kam ya rufa wa Naseer asiri, yayi masa baiwa, ya kuma daukaka shi ta yadda jama'a suke masa kallon mai kudi a halin yanzu. Shi yasa abin ya k'ara rikita Zarah, lkcn da ta fito ta ga yayanta a mota, kwarjininsa ya zarce misali.komai kyau yake wa Naseer, shi yasa ta kwana addu'ar Allah ya sa zancen Naseer ya tabbata gaskiya. Don bata jin za ta yarda da duk wani kalubale Naseer na ta ne, ita kadai. Washe gari banki ya fara shiga, bai gushe ba. Sai da ya turawa Yakubu Naira dubu hamsin cikin (Account) din sa, sannan ya fitar da wasu Naira dubu hamsin din. Ya nufi shagon siyar da atamfofi, ya zo6o tsala- tsala guda 6 'yan dubu bibbiyu. Ya za6o Engilsh guda 2 ya had'o da shaddoji kala 6, masu kyau. Sannan ya koma 6angaren kayan sanyawa na maza. T.Shirt da wanduna Jeans da Shirt masu dogon hannu, nan ma ya kwasa iya yadda yake so. Yana barin nan gidam su Yakubu, ya wuce sashin mahaifiyar sa, nan ya shiga da atamfofi kala 2 cikin leda. Bayan sun gaisa, tayi masa lale da dawowa daga Ghana. Ledar kaya ya mika mata ya ce ga tsarabar ta nan.Kai tayi farin ciki ta kuma sa albarka kwarai da gaske.Yana kokarin tashi, sai ga sallamar Yakubu, ya shigo. "Naseer!" Yayi kiran sa ya ce," Na'am yayana. Ina kwana?" Ya amsa, lafiya lau. Ai yanzu na fita zan fito da mota a wanke, sai naga taka motar a waje, kuma dama wajen ka za ni. Sako na gani an aiko min a waya, wai an min tiransifar dubu hamsin daga, (Account) dinka." "Dubu hamsin?" Hajiya ta sake maimaitawa. Ya ce, "Wallahi hajiya." Naseer ya ce,"Haba yayanmu, kamar wasu kudin kirki?" Ka cancani haka ne shi yasa, kuma ni ba ni da abinda zan saka maka da shi, don komai na samu, kai ne sila." Ya zauna hannu kujerar da yake kafin ya ce, "Naseer kenan, to Allah ya bar kauna. Hajiya sai a tayani godiya. Ta ce,"Dole, ka ga ni ma ga tawa tsarabar. Allah yasa a kare da iyaye lafiya. Ya ce, "Amin , Hajiya." Ina takwara na ne? Halan bai tashi barci ba?" Yakubu ya ce,"Kamar kuwa ka sani, yana can yana barci."mik'ewa yayi, suka yi sallama da hajiya suka fito tare da Yakubu, shi ya wuce sashinsu, don yin wanka. Naseer kuwa waje ya fito, ya bude mota ya dauko wasu kayan a wata babbar leda, ya nufi dakin da ke kofar gidan, yana kwankwasa. Zuwa can aka bude cikin fara'a Naseer ke fadin"Ka na huta wallahi." Ya dan duba shi, ba tare da ya ce komai ba, ya juya ciki. Naseer ya biyo shi, "Watau ba ka ma tashi barci ba? Ya murtsuke fuska da hannayensa, sannan yayi mika, kafin ya ce," Na gaji ne." Ba aikin fari, balle na baki ka ke fadin ka gaji. Jiya ma ina ta sa idon ganin ka, sai na ji shiru, wayar ka kuma na kashe." Ba wata walwala a fuskar sa, "Ban da caji ne, jiyan nima na so zuwa, lkc ne bn samu ba." Ya ce," O.k, to ga tsarabar ka. Ya mika masa ya kar6a, sai kawai ya wurga bisa katifa, yana fadin , ,"Na gode." Abin ya daure masa kai, har ya kasa cewa wani abu. Haka suka danyi jim shuru kafin Naseer ya mike, "bari in karasa gida." "to sai anjima". yace yana kwanciya a katifa.” bakaje kaga mota ta ba, ko bakada labari ne?" ya dago fuska daure yace "Oh, naji, mancewa nayi." ya mike suka fito. Ya kare wa motar kallo, zuciyarsa ta kara shiga

Chapter 6 of 11