Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 11
wani garari, har yana tambayar kansa, "Da ya motar nn tawa cefa." Ya kada kai kadan yace, "Allah ya sanya alkhairi." yace, Amin. Ni zan tafi sai yaushe zaka bullo ne?"Da kyar ya amsa, "zan kira ka idan zanzo." Kukan wayarsa ya juyo daga daki, don haka ya juya da sauri ya koma dakin, yabar naseer tsaye ba tareda sunyi sallama ba. Yana shigewa yaga ya turo kofarsa. Sam-sam ran Naseer baiji dadin abinda takwarar sa yayi masa ba. Shiyasa har ya bar wajen, yana tunanin me ya faru tsakanin su? Don bai taba ganin irin wannan fuskar ba awajen takwaran na sa balle yayi masa irin abinda yayi masa yau. Da wannan tunannin fal, ransa ya gama raba tsarabar sa gidansu zahra da gidansu sageer. Kowa nata murna, yanasa albarka. Ya dawo gida karfe 12 dai dai na rana. Malam balarabe na zaman jiransa. Yana shiga ya hau fada, "ina ka shige saboda Allah? Bayan tun jiya na gayama sammako zamuyi zuwa kaduna nan! Karfe 12 yanzu, yaushe kakeso muje mu dawo?" Yace "yi hakuri Abba, ban san rana tayi haka ba. Ka gama shirin ne?" Yace "tun yaushe nake zaman jira? Tuwon girma, ai miyarsa nama. Wallahi sammako naso muyi wa Alhj, don nuna masa farin ciki na." Umma tace, "mallam ai gara ku tashi da wannan maida zancan da kukeyi." Gaban umman ya zube ledoji guda hudu,duk kayayya ki ne. Umma ta zazzage su. Wai! Haihuwa me rana, Kamar tayi kwalla saboda murna. Haka Abba yayi zugum, yna alajabi. Da ya tuna irin wuyar da naseer ya basu a can baya, sai ya nisa yace,"Allah abin godia ne mai shiryar da wanda yaso a duk lokacin daya so din. Allah ka kara shirya mana ." Murmushi naseer yayi, kwarai ya gane dalilin adduar Abba. Ya dubi umma itama shi din take kallo, fara'ar sa ta karu. Umma tace "me akayi?" Yace ba ayi komai ba umma. Baki gama abinci bane." Abba yace, "ba wani abincin da za'aci, tashi mu tafi, ko kuma inbi ta haya." Ya mike, ya kwaso takalma yayi waje ya cigaba da fadin. "Ai gidan Alhj Basheer ba bako na bane." Umma tace, "kaga, tashi ku tafi. Allah ya kiyaye hanya." Da sauri ya tashi, yabi shi suka damki hanya. Alhj na ofis lkcn da Naseer ya kira shi a waya. Ya shaida masa zuwansu, don haka kai tsaye can suka wuce. Malam Balarabe ya zuba godiya kwarai da gaske. Abin yayi wa Alhj basher dadi, shi yasa ya ce ba za su tafi ba, dole sai sun wuce gidan sa sun ci abincin rana ko dama cin abincin yake shirin tafiya. Lokacin da Naseer ya yo masa waya, ya ce suna tafe. Tare suka rankaya gidan na su. Suna falon baki, akai ta shigowa da abubuwan ci da sha iri-iri. Tare suka ci, suka sha suna hirar duniya. Sai misalin uku da rabi, suka baro kaduna. ************ Cikin wata guda, ginin da Naseer ke yi a cikin gidan su ya kammalu tsaf! Gwanin ban sha'awa, kowa ya ga tsarin da aka yi wa ginin nan, dole ya ba shi sha'awa. Bayan haka kuma sun yi shawara da Sageer akan bude shagon dinki, don haka Naseer yasa Sageer ya nemo shagon haya, ya biya kudin shekaru 2. Babu 6ata lokaci aka gyare shi, aka zuba kekunan dinki guda 2 da na aiki (Design) tare da na yin zig-zig. Sageer ya koma can ya samu mataimaka, kafin ya kammala karatun sa, wanda bai wuce wata 3 su fara jarabawar karshen ba, ta kammala Diploma. Shi kuma dan gogan fafitukan shirye-shiryen auren sa ya ci gaba da yi, don ita ma Zarah, wata 5 suka rage mata ta gama sakandire. Manyan akwatunan sa (Set) guda ya kusan shake su da kaya na gani na fada, na burgewa gaba dayan su, sai sharholiyar su suke yi, ba su da matsala, duk da cewar kusan kullun sai Zarah, ta amshi bakin 'yan mata a makaranta masu zuwa ganin ta, wanda akasarin su, su Lubabatu suke yi masu jagora. Abin ya daina tada mata hankali, ta daina wasi- wasi. Zuciyar ta ta sami sukuni. Domin ta hakikance Naseer na ta ne ita kadai, don bata ta6a gani ko jin yana neman wata ba, Masu karyar su 'yan matan sa ne, sun gaji sun daina, saboda rashin ganin fuska. Kirsa iri iri naseer na gani a wajen wasu yam matan marasa kamun kai da hakuri. Su kan mance mijinka, idan Allah ya kawo shi, kana kyakkyawan zaman ka zaizo ya sameka. "(Karshen zubar da aji kenan a waje na, kuma ina ganin ko a al'adar bahaushe. Saurayi shi ke zuwa tad'i, koda kuma had'in iyaye ne. "Ma'ana iyayenki suka ba shi ke, su kan ce ne ya zo ya ganki, ba wai ke za'a ce ki je ki gan shi ba. Mata kuna da kima da martaba mai yawa. Don Allah ku rika zama kamammu a kodayaushe, domin komai yawan da ake cewa kun yi, har ana muku kirarin kamar Janpa a jos. Wallahi babu wanda ya isa ya je gidan ku ya d'auko ki, dole sai ya bi ta yadda shari'a ta tsara." Ba wai da ganin saurayi, kina son sa ba, kita binsa kamar yadda wasu yam matan sukeyi a wannan zamani. Watanni uku bayan dawowar naseer daga Ghana, ranar litinin da safe yana office din Alhj Basheer kamar yadda ya bukaci ganinsa a wannan lokaci. Alhj ya dube shi irin wanda ya saba yi masa irin na kauna yace "Naseer ya maganar karatun ka ne? Diploma gareka ko degree?" Naseer ji yaji tambayar Alhj tadan sa shi al'ajabi, sai dai zuciyarsa bata raya masa komai ba, don haka yayi dan murmushi yace, "Alhj sakandire kawai na gama". Shima Alhj mamaki ne ya kama shi, fuska a yamutse yace, "why? Kuma shine tuntuni baka koma ka ci gaba ba?" Shiru Naseer yayi a dalilin bashida wata hujjar badawa. Shi yasa Alhj yaci gaba da cewa, "gaskia banji dadi ba, amma ba matsala, ka kawo min takardunka, ka zabi ko wacce makaranta kake son zuwa." Naseer ya shafa keya, shi kan sa nauyin ya fadin abinda yasa yake ji. "Ai ban....ban ma samu yin jarabawar ba. Take nan tausayi ne ya lullube Alhj Basheer, don babu abinda yazo zuciyar sa, illa matsalar rashin kudi, saboda haka bai nemi sanin dalili ba. Kai tsaye yace, "Anyway, tunda abin ya zama haka, sai kaje ka binciko lokacin da zaa fara biyan kudin jarabawar. Zan baka ka biya, ka rubuta. Idan (result) ya fito zaa san abinyi. Gaskia ban taba zaton haka ba, da tuni na tilasta maka ka koma school. Shi ilimi ai baa wasa dashi, domin wata fitila ce, wanda hasken ta bai taba dushewa har abada. A kowane lokaci zai yi maka amfani." Naseer ya kara sunkuyar da ido yace "Na gode Alhj. Ina ganin ma an kusan fara biyan external insha Allah zan biya." Yace "bance ka biya ba, ka kawo min yawan kudin nace, ni zan ba ka. Murmushi yayi kafin yace , "to Alhj nagode. Bari in karasa wajen Yakubu." Ya amsa, "To, shike nan. Yauwa, gobe in Allah ya kaimu zan tafi Abuja, 'yar waje na zata dawo daga jordan, zan dauko ta a (Airport). Koda yake bka san ta ba. Nusaiba sunan ta, ta kare digiri din ta bana. (Arabic and islamic studies)." Naseer ya numfasa yace "tayi kokari, nayi mata murna. Allah ya kai mu lafiya." "Amin, amin. Kana iya tafiya, shike nan." Zaharaddeen shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-07 Posted by ANaM Dorayi on 08:04 AM, 09-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ .Ya mike ya sallame shi, ya fito Alhj ya raka shi da kallo. Yana rufe ofis din, ya dan kada kai. Haka kawai Allah ya sanya masa kaunar Naseer. Bai ki kodayaushe su kasance tare ba, sosai yake jin sa cikin zuciyar sa, tamkar dan daya haifa.Wani lokaci har ya kan tambayi kan sa ko don ba shi Da namiji ne? To ai kuma yana da yara masu yi masa hidima a ko'ina, tun kafin zuwan Naseer,amma bai ta6a jin wanin su a cikin ran sa, kamar yadda Naseer ya kama zuciyarsa ba. Komai zai iya wa Naseer dai-dai yadda zai yi wa Nusaiba 'yar cikin sa. Kawai ya kan danne wasu abubuwa ne, saboda kar sauran yaran sa su ce ana nuna masu bambanci ko su fa zargin wani abu. Washe gari k'arfe 2 na yamma Alhj Basheer ke tsaye wajen tarbar fasinjojin a filin jirgin sama na tarayya Abuja. Bayan wasu 'yan mintocin jirgin da ya taso daga Jordan ya sauka. Daya bayan daya fasinjojin da ke ciki suke fitowa. Jimawa kadan wata tsaleliyar budurwa ta fito saye da doguwar riga da dan karamin farin hijabi, wanda gaba daya tsayinsa bai zarce kafadunta ba. Wankan tarwada ce sosai, fatar ta ke ta walwali ga kyakykyawar fuska mai dan fadi. Hakan ya dai-daita zaman siririn hancinta da tsarraren baki. Tana da wadatar idanuwa fa gashin ido da gira. Dan matsakaicin tsayi gare ta, sai dai za ta dan d'ara Zarah kadan, tofa! Mekuma yakawo wannan zancen? Maji ma gani... jaye take da wata jaka ruwan toka mai matsaikacin girma ga kuma karama rataye a kafadarta.Tun da suka hango juna. Su kai musayar murmushi har ta karaso fara'ar ta ta kara karuwa take yi, tana isowa ta saki jaka ta rungume mahaifinta, "Abba na!"haka lallausar muryar ta ke fadi, tamkar Zarah ce ke magana. .*****Tinani**** kodai..........uhm banda shishshigi ANaM... saboda kwarai yanayin sautin muryar su, yayi iri daya.Alhj ya dago ta bakin sa har kunne ya dube ta,"Yar gidan Abba kenan, "To ya hanya?" Ya su Antinki?" Ta ce,"Lafiya lau Abba na. Ina Ummi?" "Bata zo ba?" Umminki na gida, ta so zuwa, amma kin san ta so lazy, you know?" Wai kuma ta fasa saboda tafiyar mota'¿ Ta kayata fuskarta da lafiyayyen murmushi, "Lallai Ummi, ko kewa ta ma bata yi ko?" Ai shi ke nan." Ya ce,"Ba ga Abbanki ba? Duk na kosa ki dawo my baby, kullum na dubi kofar ki a kulle, sai inji raina sam ba dadi." Ta kara kwantar da kanta bisa kafadar sa,"Ni ma haka, na yi Missing din ka Abbana."Cikin jin dadi ya rungumo kafadarta, ya ce, "To mu je mota, direba na jira." Dai-dai lkcn da aka kwarara sallama, duk suka duba suna amsawa." Wani kosashshen matashi ne, cikim adon bakaken (Suit). Yana da tsayi sosai, don ya kare Alhj Basheer." Ga fadi da alamar hutu, shi ba fari ba, fara'a sosai bisa fuskar sa, yayin da ya dan duka yana fadin "Ina yini Baba?" Tuni Nusaiba ke kame da baki, tana masa kallon mamaki, ido waje. Alhj Basheer ya amsa." Lafiya. Da ga ina? Ban shaida ka ba._? Ya ce, "Dama.............." "A jirgi mu ka hadu Abba. Wai sunan Sa Ibrahim." Nusaina tayi saurin taran numfashin sa. Alhj Basheer ya dan tsuke fuska yana dubn ta, "I see, ina mota ki same ni can." Ya juya kan Ibrahim ya ci gaba,"Ka gaida gida." Ya kara rankwafa ya amsa, "To Abba na gode." Ya wuce ran sa bai masa dadi ba." Yana bada baya. Ibrahim ya dan runtse ido ya fada a hankali "Yes!" Ta ce, "Don me za kai min haka?" Ya ce,"Shi yasa ki ka fito da sauri kenan." Bai kamata ka zo kai tsaye wajen Abba na ba, haka kawai daga gani na a jirgi. Ya ce, "Oh, duk bayanin da muka yi, fita suka rika yi suna bin iskar jirgi?" Haka bai dace da ke ba, yakamata ki amince da cewar da gaske nake yi." Cikin damuwa ta ce,"Ina cewa na gaya ma sunana, na ba ka (Address) da lambar waya, sai me? Karshen amince kenan a zato na." Tsararren bakin ta kawai yake kallo, sansanyar muryar ta na sa shi dogon tunani. Ya shafa kai, ya numfasa ya ce, Fakat! Kin kare magana. Mu je in raka ki, kar Abba ya ga kin dade." Ta ce," Na gode." Ba sai ka raka ni ba, ina jin kunyar Abba." Amma yakamata in ce da shi Allah kiyaye hanya. Ko kuwa?????""Ta juya, ta ja jakar ta, ba tare da ta amsa ba. Biyo ta yayi da sauri, yana fad'in "Please, da zarar kin sanya layin ki, ki yo min (Flashing) don in san kin maida layin, ina fatan za ki taimaka? Ta tsaya cak! Ta ce, "Ni ma ka taimake ni ka koma, zan kira din." Ya kare mata kallo, kafin ya ce, "Promise?" "Na yi." "TO Allah ya kiyaye hanya, ki ce wa Abba a sauka lafiya, kin kankane min shi." "Dan murmushi ta yi ta wuce abin ta. Shi kuwa nan yayi tasye yana kallon yadda take takawa har ta fice daga wajen." Yayi zazzafan ajiyar zuciya, ya so ace ta dan sake waigowa ya kara ganin kyakkyawan fuskar ta, amma ina, hakan bai samu ba. Shi yasa ya jima ya na wasi-wasi, yana ganin kamar bai sami kar6uwa ba. Alhj Basheer ke zaune a cikin lafiyayyar motar sa (KIA). Ko alama fuskar sa babu walwala. Isowar Nusaiba ma yasa ya kara tsuke fuskar. Tana karasowa jikin but, ya dago mata shi ta bude, ta jefa jakar ta ciki, ta rufe. Sannan ta iske shi a ciki. "Mu je ko Abba." Bai amsa ba, yayi wa mota key, ya fito harabar aje motoci. Ya dauki hanya. Shiru suka yi na 'yan dakikan, ran Alh. Basheer na sosawa akan al'amarin daya gani wanda yake ganin yakamta yayi wa tufkar hanci da gaggawa, don cimma burinsa. Buri kuma!!!! Baridai inyi tanbaya a nan, friends kunsan burinsa? Inna jiran amsarku wadda ita zatazama matakin dorawa daga wannan page, idankuka Marubuciyar tabamu baki daya ta hutashshemu kenan!! ANaM Dorayi ***Smile*** Haka zalika ran Nusaiba yake kuntace....domin ba'a son ranta Abban ta ya ga Ibrahim ba, saboda bata gama tantance shi cikin ranta ba. Musamman jin cewar yanada mata daya da yaro daya. Shirunsu yayi yawa kuma, abinda Nusaiba ta lura kamar ran Abbanta a bace yake, ba yadda ta fara ganin shi ba, don haka ta nemo abin cewa. "Abba na". Ta kira shi. "Uhmm!" Tace, "Ummi taki zuwa dauko ni, abin yana ta ban haushi." Da wutsiyar ido ya kalleta, "Ni ba wannan matsalar ta dameni ba." "Meya dameka Abba?" Yayi dan jim, kafin yace, "me kike tunani gameda Ibrahim?" Kunya cike da idon ta, ta dan sunku yar da kai, tace "Abba, Ibrahim a jirgi kawai muka hadu." Yace, "wannan ba itace amsa ba, zaka iya ganin mutum yanzu take nan ya shiga ranka, shi yasa na tambaye ki menene raayinki akansa." Tayi shiru, jin tayi shiru, yasa ya c igaba. Kar kiji kunya, ki gaya min komai Nusaiba, kin san ni mahaifinki ne, kuma ke kadai ke gareni, kuma ina alfahari da ke. Saboda haka ki warware min komai, menene raayinki akan Ibrahim?" Tadan cire kai ta dube shi, tace "banda wani raayi akan sa tukuna, saboda kasan komai sai da shawara da tunani." Yace "hakane, amma zanso ace kin gaya mun wani abu." Tace, "bansan komai a gameda Ibrahim ba, illa ya gaya min shi dan gidan Alhj Abdul Mutallib Kazaure ne.Shahararren dan kasuwan nan na kano. Garkuwan kazaure. Shi maaiksaci ne a (Nigerian Embassy Jordan), yanada mata daya da da daya." Alhj ya kada kai yace, "Nusaiba." Ta amsa "Naam Abba." Yace, "idan nace ki aje Ibrahim a filin jirgi, tunda a jirgi kawai kuka hadu, zaki iya?" Kai tsaye ta amsa, "me zai hana Abba? Kaban umurni, in ketare, mecece hujjata a matsayinka? Biyayya a gareka dolene Abba, muddin ban sabi sharia ba, saboda haka na aje Ibrahim, ban san abinda ka hango min ba." Ya kare mata kallo, sannan ya aje numfashi. Shi yasa yake son Nusaiba kamar ya hadiye ta. Yace "yar albarka mai kaifin hankali da sanin matsayin na gaba." Musamman iyayenta da take jin su sosai cikin ranta. Abbanta ma yafi shiga ranta, ba kadan ba, saboda yadda ya nuna mata kauna da soyayya, tun tana yar mitsitsiyar ta. A lokacin data mallaki hankali kuwa, sun kasan ce abokan shawarar juna, babu abinda ya dami Alhj Basher, zama yake da abar sa, ya war ware mata duk abinda ke cikinsa. Walau farin ciki ko akasin hakan. Balle ita da take a matsayin mai karancin shekaru, bata zar tar da komai sai abban ta yasani. Hakan ba kankanin tattalin kaunan dake zukatan su yayi ba. Mika hannu yayi, ya dauko nata, yadan matse shi, kafin yace "Nusaiba na gode Allah daya bani ke daya tal! Amma ki ka zama tamkar dubu. Kinsan dalilin cewa ki aje Ibrahim?" Ta kada kai tana dubansa. Yace, "miji na zaba miki.". ****Uhm*** anxo gurin, amma banan gixo ke sakarba!!!!! Haka kawai taji gabanta ya fadi, sai dai kuma ta rasa dalilin bayyanar murmushi a fuskar ta har da wata bazawarar kunya data sauka cikin idanuwanta, masu kyau da haske. Aje kai tayi kasa taci gaba da murmushin. Abinda ya kara faranta ran Abbanta kenan. Ya Kara runtse yatsunta, yaci gaba da cewa, "Naseer yaro ne dan mutunci. Dan babban gida. Ba wai ina nufin babban gida irin na wannan zamanin ba, kamar yadda mutane suka maida rayuwa akan tarin dukiya shine mutunci da babban gida. A'a ina nufin kyan asali, addini,da dabiu na gari, wanda yakan samo asali ne daga tarbiyar iyayen babban gida. Aunty Zulyma ta hutashsheku!! Ammafa...... Uhm! Muje zuwa wai Mahaukaci ya hau kura.... Baki nan aka kawo min Naseer, yana min wasan polo, a maganar nan yanzu da nake miki, ya zama wani jigo a harkar wasan polo abin alfahari. Allah ya sanya min so da kaunar Naser fiye da tunaninki, wanda har ya kai ni ga son hada zuria da shi. Sai dai bani da kowa sai ke Nusaiba, shi yasa nake rokon ki da nuna min isa da ke kuma biyayya ta karshe da zaki min, ki amince da zabin da nayi miki" Wasu kwallane ke cike fal! Cikin idanuwan ta, wadanda ita kanta bata san dalilin taruwar su ba. Daga bisani ne ta fahimci cewar kalaman Abbanta na karshe, su suka tara mata hawayen da suke neman sauka bisa kuncin ta. Jin yayi shiru, yasa ta dube shi, duba na aminci da girmamawa, tace Abbana kaban mamaki daka ce kana rokona, kenan kana kokwanto akan ba zan maka biyayya ba. Ai...." Hawaye shar shar! Bisa kuncinta. Shiya hana ta karasa zancen ta. Tasa hannu tana sharewa wasu na kara fitowa kamar ma kukan naso yaci karfin ta. Hankalin Alhj Basheer ya tashi matuka. Fuskar sa ta nuna karara, "ba haka nake nufi ba bebina, kin ga dubeni. Ki dubeni nace" Ta dago idanuwanta jajur! Ta kalle shi, yayi sauri ya goge hawayen ta sannan ya dawo da hankalin sa ga tukinsa, bakinsa na fadin, "wannan maganar ta wuce. Yanzu gaya mun yaya kikaji daga ambatar sunan Naseer?" Tace "Abbana ai tun ina yar yarinya raayinmu daya dakai, balle a yanz dana mallaki hankalina, nasan cewar ba zaka taba kai ni inda zan cutu ba. Dadin dadawa kuma a shariance, matsayin dana ke yanz na wacce bata taba yin aure ba. Hakkin Kane ka zabar min miji na gari wanda kake min hangen farin ciki da kwanciyar hankali. Don haka Abba ka daina roko na, kace mun Nusaiba na baki umurni kawai, ni kuwa inbi."Bai san lkcn daya fashe da dariya ba,yana fadin, "Bebina gime a hug!" Ta matsa kusa da shi sosai, tayi kwance bisa kafadar sa kunshe da murmushi bisa fuskarta." Allah yayi miki albarka."Insha Allahu yadda ki ka faranta min rai, haka ke ma zaki kasance cikin farin ciki." ****Uhm! To Allah ya amsa?**** Ta k'ara makale masa ta ce,"Amin Abba na........." Ta ja sunan Abban yayi tsawo, don jin dadin sa. Haka suka kasance har isowar su Kaduna." Labarin Naseer yake bata. Jaruntakar sa da kwarewar sa akan wasan polo.Haka kuma bai 6oye mata karancin karatun sa ba. Take nan suka zakulo yadda za'a warware wannan 'yar matsalar. Ko alama Nusaiba bata yi kama da Hajiya Zulaihat ba, watau duk kyanta a wajen Abban ta ta samo shi. Ita fara ce sol! Tana da manyan kyau, ma'ana da ka dube ta, za ka gane kyakkyawa ce. Sa6anin Nusaiba, ita kananan kyau gare ta, kana kallon ta, tana qara kyau, ba za ka ta6a ganin sauyi ba. An riga anyi sallar magariba, lkcn da suka iso gida. Tana rafka sallama. Ummin ta ta fito, "Oyoyo, bebin Ummi! Nusaiba ta cunno baki," Ba wani." Ai wallahi Ummi......." Rungume ta tayi, shi yasa ta kasa k'arasawa. Ummin ke cewa, "Yi hakuri, jiki na ne na ji yayi min nauyi, shi yasa ban biyo Abban ki ba. To ya hanya?" Ta ce,"Lafiya lau. Su Anti na gaishe ki."Ta ce,"Kyale Antin nan ta ki, wai a waya take min shegantakar da ta saba." Tayi 'yar dariya ta ce,"Zan cen Anti bai wuce na amarya. Na dai ce mata ta bari sai an rangado mata, sannan ta sami bakin magana." Yauwa, na gode da ki bata amsa, sannan sallamar Alhaji." Kin ma tsaya ki na hira da ita ne, bayan ta ki zuwa dauko ki." Dukan su dariya suka yi." Abba na ai rike ni tayi." To kwace ki gudu kawai, kar tayi miki wani dadin baki." Ta ce, "Yanzu kuma Abba." Ta suri jakar ta nufi dakin ta. Ummi na fadin, "Au, zuga ki yayi?" Ta juyo dauke da murmushi, ta kada kai ta wuce abin ta. Hajiya Zulaihat tayi wa Alhj sannu da zuwa. Ya amsa, tare suka haye sama." Nusaiba na shiga dakinta, ta yar da jaka, ba6ata lkc ba, bayi ta shige, jimawa kadan ta fito da alwala, tayi sallolin ta. Ta jima bisa sallaya tana lazimi har zuwa kiran isha'i, ta mike ta ci gaba da sallah. Bayan ta idar, sannan ta cire kayan jikin ta, tayiwanka ta nufi. Madubi da ke shirye tsaf! Da kayan kwalliya iri-iri, ta ja kujera ta zauna." Daddaga kayan da ke wajen tayi, duk sababbi ne aka zuba mata. Dan murmushi tayi, ta fada a ranta,"Ummi na kenan." Ta shafe jikin ta da (Lotion), sannan ta mike ta nufi Wadirof, ta janye murfin gilas din, haka tayi tsaye wangame da baki. An cire wadirof din ta tsadaddun kayayyaki kala- kala. Wani farin ciki ya sake kama ta, a lkcn guda zuciyar ta ta kara kamuwa da tsananin son iyayenta. Ta shiga dubawa, gaba daya ta rude ta ma rasa wace riga za ta sanya." Domin duk wacce ta d'aga, sai taga ta fi ta farko kyau. Da kyar ta iya dai-daita zuciyar ta, ta dauki wata 'yar kanti ruwan hoda, doguwa mai karamin hannu ta sanya. Gaban rigar akwai ado na furanni farare kanana, su suka kara wa rigar kyau. Da ta koma jikin madubi kuwa, ka rantse da Allah sbd jikin ta kadai aka yi rigar, ita kanta ta tantance hakan. Gashin kanta da ke sake, shi ta kama tana daurewa da wani dan karamin (Ribbon) da ke makale jikin rigar. Bata kammalaba Umminta ta budo kofa ta shigo, "Ke! Wai ba za ki fito cin abinci bane, iyayen gayu?" Da sauri ta tarbi Umminta ta rungume, "Allah sarki Ummina, na gode da kaya." Ta dago ta, "Gaskiya kuma kin yi kyau bebin Abba. To mu je ki ci abinci. Abbanki ya ce idan kin gama, ki same shi daki." Bakin ta har kunne ta amsa,"Minti 2, Ummi gani nan." Ta wuce dauko mayafin rigar. Ummi kuwa ta fice daga dakin." Akan tebur, daga ita sai Umminta, domin shi Alhj Basheer bai damu da ya ci abinci bisa tebur ba, ya fi son akai masa cikin dakin sa ya ci. Abinci kala-kala, kowa ya za6i abinda yake so ya ci. Nusaiba ta yayyafita, saboda kosawa tayi ta ji kiran Abban ta. Tana mikewa. Ummi ta ce,"Ke ba dai kin koshi ba? Ta nuna hanyar sama ta ce, "Abba na kira can za ni." "Cewa yayi ki ci ki, koshi kafin ki je." Cikin doki, ta ce,"Na koshi ummi, idan ma zan kara, na kara a wajen Abba na."Ta sumbaci kuncinta ta haye sama da gudu. Ummin ta, ta raka ta da ido har ta kule." Ta aje numfashi, tana karkada kai. Tabbass tayi kewar 'yar diyar ta, tilo tamkar dubu." Sallamar Nusaiba Alhj Basheer ya amsa. (Laptop) ce a gaban sa, yana ta 'yan dube- duben ajiyar sa. Koda shigar ta, kwarai ta ga dakin ya sauya mata. Ga wasu bakin makamakan hotuna guda 4 da suka kara kayata kafcecen dakin, daya kai girman wani falo. Uku daga cikin hotunan Alhj Basheer ne tare da Naseer rike da wasu kofuna tare da wasu kyaututtuka. Dayan kuwa Naseer din ne shi kadai, ya da wani katon kofi sama, dariyar da yayi ta kara kwarjinin fuskar sa. Kai tsaye gaban hotunan ta tsaya ta zuba ido. Domin ko alama bata tantama wannan shine Naseeerrrrrr!!!!......." Ba wai son sa bane take ya kamata, a'a kwarjinin sa ne ya debi hankalin ta har ta ji faduwar gaba, kuma ko alama bata ji tana kin sa ba. Tana kokarin kaucewa hotunan, ta ji hannun Abbanta ya rungumo kafadar ta, ya lika ta kuibinsa. Ta dan sauke numfashi kadan, ta ce,"Hotunan ko sun yi kyau." Yayi dan murmushi ya ce,"Allah ko? To ki canka waye a tare da ni? Cikin zolaya t amsa, " Bebin ka of course." Ya ja hancin ta ya ce, "Stop joking." Ba ni ce a tare da kai ba Abba?" A hoto na ce, kin sani sarai, come on, gaya min." Tayi 'yar dariya, "Uhmm...........jarumun dan wasan polon nan da aka kawo ma ka shi, lkcn da ba nan. Ya ma sunan sa?" Ta tambaya, tana duban sa. Haka shi ma yake kallon ta kafin ya ce, "Sunan sa ya 6ace miki kenan? Maganar Abba bata da muhimmanci ko?" Ta kada kai, Wasa na ke, ai da shigowa ta na gane Naseer ne." "To yaya ki na son sa?????""""" Da sauri ta bar wajen, ta koma bisa wasu kujerun farin karfe na alfarma ta zauna. Kunya ce mai karfi ta kamata. Shi ma ya tako a natse ya zauna gefen ta." Wannan shine zabin da na yi miki, ina son ki gaya min yayi, ko bai yi ba?" Kan ta a kasa, ta amsa, "Yayi Abba." Ki na son sa?" Tayi shiru jim. Sannan ta kalle shi,"Ummi ta ce kana kira na." Wannan shine kiran, ki ga mijin da na za6a miki, sannan in tabbarar da ki na son sa. Ki gaya min." Abba na ce yayi." Ba yayi ba, ki na son sa?" Alhj fa ya tasa ta gaba, ita kuma duk kunya ta rufe ta, da kyar ta cije ta daure ta amsa, "Eh!" Ta mike a guje, ta bar dakin. Alhj Basheer ya bi ta da kallo yana dariya, sannan ya numfasa yayi hamdala ga Allah. Kai tsaye Nusaiba dakin ta shige, ta fad'a bisa gado, ta nutse cikin katifa.Ta jima a kife, kafin ta birkito ta tsirawa fitlun da ke cunkushe suna lilo a saman tsakiyar dakin ido. A zahiri su take kallo, amma ko alama ba kyan tsarin bane cikin ran ta.Zuciyar ta yamutse take da tambayoyi masa yawan gaske a game da za6in da Abban ta yayi mata." Shin waye Naseer? Wane irin sani Abban ta yayi masa? Duka zahiri da badini? Ya za kai kar6e ta, idan ya ganta? Watakila shi ma hoton na ta ya gani, kamar yadda ita ma ta gan shi................... Ta sauke numfashi, ta fada a ranta,"Allah ka sa aure na da Naseer alkhairi ne." Ta yunkura ta tashi zaune, "Yar jakar hannun ta da ta yasar bisa gadon tun shigowan ta, ita ta jawo gaban ta, ta bude zif din ta dauko wayar ta. Ta mike ta koma jikin wata dirowa, wacce jerin akwatuna ke bisa kanta." Ta jawo ta tsakiya, ta binciko (Sim card) na ta, na gida Najeriya ta dawo bakin gado ta zauna. Sannan tayi aikin maida shi cikin waya. Jimawa kadan ta nemo wata lamba mai dauke da sunan KAUTHAR. Ta kira babu wani bata lokaci aka sada ta da kauthar. Can ta tsinkayi ihunta, "ba dai kin iso ba!

Chapter 7 of 11