Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 11
k'arasowa bakin titi, sai dai yau babu yayanta a wajen, kamar yadda kullum safiya shine mutum na 3 da ke faranta mata rai, daga iyayenta, sai shi. Don haka ta tsaya shiru cike da mamakin me ya hana yayanta zuwa yau? Ta kusan minti 5r a tsaye, sannan ta wuce jikinta duk ya mutu. Kuma ko alama zuciyarta bata cikin sukuni har na rashin ganin Salis jiya da daddare, kamar yadda yayi mata alk'awari. Ta fe take tana zancan zucci fad'i take,"Ina ka ke yayana?" Zarah." Ta ji an k'wala mata kira. Ta waiga gefen da aka kirata, firgici. Bak'in get din ofishin "Yan sanda ta hango Sageer tsaye da kayan makaranta. Da sauri ta tsallako. Hankali tashe, ta tambaya,"Ina yayana ne?" Ban gan shi ba yau." Cike da damuwa ya amsa,"Ai yayan nan naki, sai a hankali. Yana nan ciki." Ta k'ara ware ido ta-ce,"Ban gane yana nan ba?" (Police Station)Na ga ka nuna! Ya ce,"Eh mana.." Hankalinta ya k'ara tashi,"Wa ya kawomin shi?" Bata jira ya bata amsa ba, ta wuce, ya biyo ta, yana fad'in,"Wallahi tsautsayi kawai, jiya ya je wajen wani wai shi Salis, suka fara gardama akan ki, sai fad'a. Kin san halin yayan naki, k'ashi daya ke gare shi, yana dukan sa, ya fad'i a sume." Tun da yake magana, ta rage sauri. Yana sa aya, ta juyo ido cike da kwalla ta ce,"Shi da Salis suka yi dambe? To saboda me?" "Oho! Amma a kan ki ne Zarah. Naseer bai son Salis na zuwa gun ki, gargad'in da na ji yana masa kenan. Abin ya kai su ga dambe." Ta tsura masa idanuwanta da suka cika tam! Da hawaye, ta ce," Za'a bar ni in gan shi?" Ya amsa,"Ban sani ba. Ni ma yanzu na kawo masa abinci, mu je mu gani. Suka shige cike, da k'yar aka sake yarda su gan shi,don bai jima da komawa ba. Ana fito da shi, suka yi ido 4 da Zarah, sai ya juya, ya koma ciki da saurinsa. Kamar za ta burma ciki, ta bi shi, kira take,"Yayana! Yayana ka zo mana, in gan ka!" Dan sanda ya ce,"Yan mata, ihunki fa yayi yawa wajen nan. Hala saboda ke aka yi fad'an?" Bata iya cewa da shi komai ba. Sageer ke jawo ta waje. Zarah, ki yi hak'uri ki tafi makaranta, ni ma yanzu zan wuce."Insha Allahu na san zuwa anjima, za'a bada belinsa. Yi hak'uri." Tayi tsaye tana share k'walla." Zo mu je." Suka fito bakin titi. Sageer ya tare mai mashin, ya yana fad'in,"Ki wuce Zarah, kin ga lokaci yana kurewa." Ta ce,"Zan ta fi." Mai mashin ya ja, suka tafi. Yana waigen ta, yana nuna mata alama da hannu ta wuce, har suka yi nisa. Tsaye kawai take kikam! Ta rasa na yi. Tunanin ta, me ya kai Naseer fad'a da Salis?Nan take ta samo amsar. Wani ni'imamman farin ciki ya lallube ta. In banda abin yayana, ai sai ya gaya min kai tsaye, menene na fad'a da Salis? K'walla suka cika idanuwanta, tana kallon ofinshin "Yan sanda,"Ba zan iya zama cikin aji ba, kai kuma ka na tsare a nan yayana. Ta goge kwalla ta kwashe sauri sauri sai gida. Babu ko sallama, ta fito dakin. "Ke! Lafiya?" Innar ta, ta tambaya, kuka ta fasa,"Inna 'Yan sanda sun kama yayana! Ta dafe kirji a firgice ta ce,"Me yayi?" Bakinta na rawa, ta mayar da abinda ya faru. Inna ta d'auki salati, kan ta ya d'aure"To ki yi shiru, bari Baban ki ya fito wanka. Kai yara babu hankali, koma dai menene cikin zuciyarsa, ai sai yayi hakuri, menene abin fad'a?." Shigowar Malam Umar yasa tayi shiru,."Me ya faru? Inna ta amsa,"Naseer ke hannu 'Yan sanda. Wai jiya sun yi fad'a da yaron nan daya zo gun Zarah jiya, har sumar da shi." Ya ce,"To saboda me?" "Oho!" Yayi dan tsaki ya ce,"Yara ba sa jin magana, menene abin fada anan? Ko shi ma sonki yake yi?" Ta sunkuyar da kai ta ce,"Nima ban sani ba."ya ja tsaki. Inna ta ce,"Idan ma sonta yake, me zai kai shi, fada in banda abin Naseer. Shi ma ya san babu yadda za'ayi mu hana shi, mu ba Salis in har ya furta. Allah shi kyauta. Yanzu yaya za'ayi Malam?" Ya ce,"Bari in shirya, in je in ga Baban na sa, sai a san abin yi. Ke kuma ga shi kin makara. Ki bata sauran 20 din nan, maza ta je ta hau mashin ya kai ta. Ya fice daga dakin. Inna ta dauko 20 din ta bata,"Tana bayan mashin hankalin ta na ofishin 'Yan sanda. Haka suka wuce tana kallon wajen har suka k'ule. Malam Umar ke wa su Malam Balarabe sallama a k'ofar gida. Tare da Mallam Lawal mahaifin Sageer. Bayan sun yi Musabaha, sun gaisa sai ya ce,"Magana na ji babu dadi, shine bari in zo in ji yadda aka yi?" Malam Lawal ya ce,"Zaman nan da ka ganmu nan, rarrashi kawai na ke yi. Malam Balarabe ya ce babu ruwan sa a ciki. Sannan baban tashin hankali, na je ofishin, don in yi belin sa." Yan sandan, suke gaya min iyayen wancan yaron, sun ce kara za su kai kotu, wai da wuk'a ya zo, yana neman kashe shi." Da wuk'a? Ya ce,"Sharri ne kawai, don Sageer ya gaya min tare suka je, kuma babu komai a hannu Naseer. Dukan sa kawai yayi, ya suma. Shi kuwa Naseer tun yana yaro haka Allah yayi shi da karfin tsiya. Malam Umar ya kada kai cike da damuwa, "Wannan al'amarin bai yi dadi ba. Su kuma bai kamata su yi haka ba. Menene amfanin yin sharrin?" Malam Balarabe ya amshe,"Laifin su ku ka gani? Karan banin da ya kai shi,ya ta6a masu yaro. Shi zai fidda shi. Saboda haka kar ku wahalar da kan ku, ku kyale shi, su koya masa hankali." Malam Umar ya ce,"Ba kuwa za'a kyale shi ba." To wallahi babu hannuna acikin, kun ji kuma na rantse.." Ya ce,"Shi kenan Malam Balabare, amma ina tabbatar maka, bai kamata ka yi saurin rantsuwa ba. Tunda abin ya zama haka, mu sai mu je ko? Ya fad'i yana kallon Malam Lawal, duk dacewar ba su taba sanin juna ba, sai yau. Ya ce,"Taso kawai mu tafi." Rai 6ace suka bar wajen, tamkar yadda ran Malam Balarabe ke bace. Ya jima a zaune, yana tunani da tambayar kan san "Yaushe Naseer zai daina bata min rai?"Ya ce,"Taso kawai mu tafi." Rai bace suka bar wajen tamkar yadda ran Malam Balarabe ke bace. Ya jima a zaune, yana tunani da tambayar kan san."Yaushe Naseer zai daina bata min rai?" Ya kada kai ya ce,"Allah ka shirya min." Ya mike, ya shiga gida, ya mayar wa Umma zancan kai Naseer kotu inji iyayen Salis. Idanuwanta suka kada, cike da tashin hankali ta ce,"Wannan sharri ne, na san Naseer bai jin magana, amma bai ta6a daukan makami ya hari wani da shi ba. Gaskiya Malam bai kamata ka tsame hannunka daga maganar ba." A fusace ya ce,"To ai sai ki dauka ki maida min. Ya ja tsaki, ya bar gidan, ya wuce kasuwa. Ya bar Mairon, kamar ta aza hannu bisa kai tayi kuka. Duk iya kokarin da su Malam Umar suka yi, don ganin su kwantar wa iyayen Salis hankali, don su janye kudirin su, sam sun ki sauraron su, shi mahaifin sa ma ya ki yarda su gan shi ido da ido. Abokan Salis din ke gaya masu, an ma riga an shigar da kara. Takarda kawai suke jira a aiko ofishin 'Yan sanda........... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 11:44 AM, 04-Nov-15 Under: Ajininsa yake ___ NA ZULAIHAT SANI KAGARA___________ Al'amarin bai masu dadi ba ko alama. Karfe 11:30 duk suka koma gida. Inna na zaune, duk tunani ya addabe ta. Malam Umar ya shigo. Yadda ta lura ran sa a 6ace yake, yasa nan da nan ta gane ba ayi nasara ba. Hannu ta a kunci, ta ce,"Ya dai Malam?" Ya jinjina kai ya ce,"Ai komai ya kwa6e A'i. Iyayen Salis sun kai shi kotu." Kotu?" Me yayi zafi? Shi Salis din rauni yayi sosai?" Ya ce,"Ko alama, duk da dai ban gan shi ba, amma an ce ya bar asibitin. Abin ma dasharri ya zama, wai dawuka ya je kashe shi......." Da sauri ta katse shi,"Wannan karya ne. Naseer bai daukan makami, bar shi dai da saurin duka ga karfi." Ya ce,"Babban abin tashin hankali ma, shi Malam Balarabe ya ce, ba ruwan sa ciki. Saboda haka al'amarin sai addu'a . Mu jirar ranar da za'a shiga kotu. Ni takaici na yaron nan jarabawa suke yi. Mts!" Yayi tsaki, ya kardada kai.Ta ce,"To yaya zai yi? Ba dole yayi hkr ba. An san abin akwai 6acin rai. Allah shi kyauta." 2:15 Zarah ta shigo gida a dokan ce, duk a zaton za ta ji an ce yayanta ya baro ofishin 'Yan sanda, sai ma ta ji wani labari sabo. Ta ha de kai da guiwa, hawaye na ambaliya.Inna ta ce,"Hak'uri za ki yi Zarah, haka Allah yaso, fatan mu kawai Allah ya takaita abin. Tashi ki zubo abinci ki ci." Ta girgiza kai,"Ba zan iya ba Inna. Ya za'ayi wa yayana sharri, wanna ai zalunci ne." To ya za'ayi? Tun da ya riga ya bi shi, har gidan su ya ta6a shi, ai bai da mafita, sai dai Allah. Allah ya isa. Wallahi! Kuma Salis din zai zo ya same ni!" Ta tashi fu......... ta wuce. Daki ta nufa ta kifa bisa gado, tana murzar ido hawayenta bai yanke ba. *************** Bayan sallar La'asar. Inna ta gama shirinta tsaf! Ta tsaya kan Zarah da ke zaune bisa sallaya, tunda ta idar da sallar, "Tunda nayi-nayi da ki tashi ki tafi Islamiyya, kin ki motsi, ni zan tafi layin Labadiya in yi wa Umman Naseer jaje. Sai ki kula da gidan, ga miya can na dora, idan kuma kin ga dama abincin na ki yana nan a kicin din." Ta sa kai ta fice, ba tare da Zarah ta ce, wani abu ba. Minti 10 bayan tafiyar Inna sai yaro yayi sallama, ya shigo ya ce ana kiran Zarah inji Salis. Da ita yaron ke magana, don haka ta ce,"Ka ce tana zuwa." Ta mike da hijabin da tayi sallah ta fito. Salis na cikin zaure ya sha wankan la'asar, yayi adon shadda bulu. Fara'a kawai yake yi, ita kuwa jikin bango ta ra6e, fuska daure. Ya dan matso yana fadin "Yan matan da ta dace da sunanta, ya sanyin la'asar????Ta dirka masa harara. Ya ce,"Wai! Me ya faru?" Ta gyara tsayuwa cikin fada ta ce,"Salis kar ka sake zuwa guna! Ban da lokacinka, ban da lkcn mai lakacin ka! Saboda haka ka fita harka ta kawai, idan ka na son kanka da arziki!" Ta juya za ta wuce, da sauri ya ce,"Me ya faru Zarah? Ke da ake neman kashe ni, saboda son da na ke miki? Labarin da na zo in ba ki kenan, ya za ki min haka?" Ta juyo ta nuna shi, "Sharrin da ku ka k'ulla masa a kanka zai kare! Kuma da yardan Allah, sai ya fito, ba zai mutu a hannun Alk'ali ba!"ta shige gida, ta bar shi sototo cikin duhu,"Me yarinyar nan take nufi? Ta san fadan da muka yi kenan? O.K, shi ma take goya wa baya, ba ni ba. Shi ta fi so kenan?" Ya huta, ya ce a fili,"Zan yi maganin sa kuwa. Kuma ba zan daina son ki ba." Ya fita, ya bar gidan ran sa 6ace." Haka Zarah ke cikin kunci, har zuwa dare babu abinda ta iya kaiwa bakinta. Sallamar Sageer, ita suke amsawa yanzu. Ya shigo duk suna tsakar gida zaune, ya tsugunna, ya gaida su Inna. Sannan suka gaisa da Zarah." Sai na dawo na ji sabon labari. Wallahi-wallahi Baba karya suke yi. Naseer bai je da komai ba a jikinsa."Ya ce,"To yau muke tare da Naseer? Duk iya kiriniyar sa na sani. Kawai sun san yana jarabawa ne, shi yasa suka ja maganar, don ya rasa. Sun kuwa yi a kansu. Idan kuma har son Zarah yake yi, ni na ba shi ita duniya da lahira. Za ta jira shi har ya sami madafa. Ba shi kenan ba? Na ga wani dan kusun uwar da zai sake zuwa min k'ofar gida." Ba k'aramin farin ciki ya ratsa zuciyar Zarah ba. Suka kalli juna da Sageer, yayi mata murmushi, ta yi sauri ta rufe fuska. Yayin da Inna ke fad'in,"Ka gama magana Malam. Allah yasa rabon sa ce." Sageer ya ce,"Amin. Ni zan wuce (Police Station) din, in gan shi." Zarah ta mike,"Baba ni ma in je?" Me za ki yi a can Zarah? ki yi zaman ki kawai, wurin nan ba wajen zuwanki ba ne."Ta marairace,"Zan gaishe shi ne Baba, kuma......kuma........" Kuma me?" Inna ta tambaya. Ta kwanto jikinta, ta 6oye fuska. Babanta ya ce,"Ba fa za ki ba. Ki ba Sageer sak'on ko menene a kai ma sa." Haushi ya kama ta, ta tashi ta shige daki. Sageer yayi masu sallama, ya fita. Yana tsaye gaban kanta aka fito da Naseer. Da ka kalli fuskar sa, za ka san ya fad'a, saboda bai saba da wajen ba, ga k'yamar k'azantar da ke wajen, shi yasa bai iya cin abinci sosai. "Ya aka yi?" Ya ce wa Sageer. Ya amsa, "Lafiya lau. Daga gidan su Zarah na ke duk suna gaishe ka. Zarah ma ta so biyo ni. Babanta ya hana. Ni da abinda na ke son in gaya ma ka, ko an je kotun nan, kar ka amsa laifin da ba ka yi ba." Ko na amsa, menene? Sun dade ba su min sharri ba." Ya ce,"To wai kai son Zarah ka ke, ko menene dalilin yin haka?" Ya juya lafiyayyun idanuwan sa, ya amsa,"Me ka fahinta?" Ya dan kada kai,"Naseer manya. In kasan haka ne, sai ka gaya mata kawai, menene na 6oye-6oye?" Ya ce,"Ai Zarah yarinya ce, bai kamata in kasa mata hankali ba. Ina sa uniforma, tana sa uniform, sai ince ina son ta? Da sunan me? Don kowa ya san ban isa aure ba. Da fa hankalina sarai. Su Baba ne suke ganin banda shi." Yayi d'an murmushi, ya ce,"To ai duk ta kare, tunda sun gano ka. Har Babanta ya ce,"In har son ta ka ke. Wallahi ya baka ita." Yayi jim! Yana masa duban mamaki, Ni zaka zolaya?" Nace wallahi, ka ce zolaya? Maganar da aka yi ta yanzu a gaba na. Zarah ma na zaune. Yayi 'yar dariya, kafin,"Yaya Zarah ta yi?" Tsaf! Fuskar ta, ta nuna min kai take so. Ai kun shak'u da Zarah Naseer, dole mata so ka. Ba ka ga yadda take rawar jiki, ta zo nan ba, aka hana ta. Tun jiya hankalin ta yake tashe."Ya lumshe ido, shiru yana tunanin zucci, kafin ya bude. Dan sandan da ke tsaye ya ce,"Lokaci yayi." Ya bude ido sosai,"Ka ce mata, kar ta damu, lafiyar ta lau, komai zai wuce Insha-Allahu." Dan sandan ya ce,"Mu je ciki Yalla6ai."Naseer ya dube shi a dage, ya ce,"Kai ne yalla6ai, ranka ya dad'e yace Sageer. Sai da Safe." Can a mak'oshin ya amsa, don har cikin ran sa yana bakin cikin ganin Naseer a wannan wurin. Ya fito ya nufi ciki da tunani. Karatu kawai yake yi, amma zuciyarsa na cike da tausayi Naseer, ganin har za'ayi jarabawa 4. Shi Naseer bai sami ko daya ba, abin ya dame shi kwarai, don bai da abin yi ne kawai. ****************** Abin kamar wasa, sai da Naseer ya kwashe kwanaki 3 ofinshin "Yan sanda, sannan takardar sammacinsa ta zo. Ranar juma'a aka fara sauraron shari'ar. Malam Balarabe dai babu ruwan sa, don haka bai ma je kotun ba, su M. Umar ne da mahaifin Sageer su ka je. Sageer kuwa yana makaranta, amma gaba daya hankali sa bai jikinsa. Balle kuma Zarah, wacce ta fi kowa kunci na ta na tsare. Tayi iya kar k'ok'arin ta, don ganin ta jure zaman ta cikin makaranta kamar yadda Babanta ya tilasta mata tafiya. Amma sam ta kasa. Bata fahimtar komai, kwance take kawai bisa tebur, zuciyar ta na zugin tunanin wane hukunci za'a yanke wa yayanta? Saboda Salis ya sha alwashin sai ya sa an d'aure Naseer, dalilin juya masa baya da Zarah tayi tashi guda. Naseer tsaye gaban Alkali, babu fargaba ko shakkar wani abu, yana saurare aka gabatar da k'arar sa, tare da laifin da ake tuhumar sa. Alkali ya tambaye shi,"Ka ji laifin da ake tuhumar ka?" Ya ce,"Ran ka ya dade, na ji." Ya ce,"To ka amince da hakan, ko ka na da abin cewa?" Naseer ya amsa." Ban amince ba, ni ban ta6a fad'a da makami ba. Kawai dukan sa na yi, ya suma."Wani Lauya da ke zaune tuntuni, cikin rukunin lauyoyin da ke zaune, yayi fit! Ya mik'e tsaye ya ce, "My Lord, Sunana Barista Usman, ni ne Lauyan mai kare wanda yake k'ara, watau Salis. Ina da 'yan tambayoyin da na ke son yi wa Naseer." Alkali ya ba shi umurni. Nan take, yayin da su Malam Umar da M.Lawal suke cike da fargabar wannan shari'a, gain har lauya su Salis suka d'auka. Lauya ya matsa kusa da Naseer, suka k'arewa juna kallo, sannan ya ce, "Ranar lahadi daya ga watan nan da muke ciki, da daddare ka je k'ofar gidan su Salis, ko zan san abinda ya kai ka can?" Naseer ya amsa,"Gargad'i na je yi masa, akan k'anwata Zarah, don ba na son ya rinka zuwa gunta." Ya ce,"Wane irin gargadi ne da za ka bi mu2m har k'ofar gidan sa, ka rufe shi da duka. Sai da ya daina numfashi, sannan ka yi k'ok'arin da6a masa Wuk'ar da ke jikinka?" Hankalin Naseer ya k'ara tashi, idanuwan sa suka kad'a jajur! A fusace yake magana,"Ba haka bane! Tare da aboki na Sageer muka je, na yi masa gargadi da baki, na ce kar ya sake zuwa wajen Zarah. Shi ya fara kai min duka, duka 1 na yi masa, ya fad'i sumamme. Abokan sa 2 na wajen, kuma suna gani! Lauya yayi d'an murmushi ya ce,"Malam Naseer. Lokacin da ka yi wa Salis lilis! Har ya suma ka yi iya k'ok'arin ka, don ganin ka dank'arawa Salis wuk'a. Amma ba ka sami nasara ba, sbd abokan sa da suka fi k'arfin ka. An kira 'Yan sanda sun zo wajen, har suka tafi da kai ofishin su. Amma abin mmk, babu wuk'ar nan a tattare da kai. Ko za ka gayawa kotu inda ka 6oye ta?" Ya k'ura Lauya ido, kamar shi ma ya sumar da shi yake ji, ya jima kafin ya ce,"Had'iye ta na yi." 'Yan kallo na ta dariya. Alkali ya ce kowa ya natsu. Sannan ya ce,"Nan a kota ka ke Naseer, ka kula da harshenka." Barista Usman ya gyara zaman kot d'insa, ya ce,"Kowa ya san wuk'a bata had'iyuwa gare ka, amma kowa ya ji da bakin ka ka ce tare da abokin ka Sageer ku ka je k'ofar gidan su Salis. Bincike ya nuna Sageer ya gudu kafin 'Yan sanda su zo. Menene dalilin gudun sa?"Ya kad'a kai tare da fad'in,"Ni ma ban sani ba." Lauya ya dubi Alkali ya ce,"My Lord, dole Naseer ya ce, bai san dalilin gudan abokin Sageer ba, domin shi ya mikawa wukar ya gudu da ita kafin isowar 'Yan sanda. My Lord, kudirin Naseer ya kashe Salis da ya sami damar yin hakan, sbd haka na ke rokon wannan kotu mai adalci, da ta daga sauraron wannan k'ara zuwa 27 ga wannan wata da muke ciki, don ba ni damar tattara shaidu na, wadanda za su tabbatar wa kotu wannan tuhuma da ake wa Naseer gaskiya ne. Na gode." Ya koma kujerar sa ya zauna. Zuciya kamar ta kashe Naseer., Kiri-kiri an lauya magana, ta zama sharri har ana neman jawo Sageer ciki Ba shi kad'ai ba, hatta Malam Umar haka zukatan su ke tafasa, shiru kawai suka yi suna sauraron jawabin Alkali. "Kotu za ta ci gaba a wannan watan kamar yadda lauya ya buk'ata. Sannan kotu ta buk'aci a kawo mata Sageer a wannan ranar. Shi kuma Naseer za'a aje shi a ruman har zuwa wannan ranar." Al'amarin daya fari a kotu, ya daga hankalin kowa, hatta Malam Balarane da ke ikirarin babu ruwan sa cikin rigamar da Naseer ya jefa kan sa. Sai dai bai fito fili ya bayyana damuwar sa ba. K'ala bai ce wa su M.Umar ba, har suka k'are bayanan su. Shiru na tsawon sakwanni bai tanka ba. M.Umar ya ce,"M. Balarabe ko ba za ka ce komai ba, ai ko tofa 'yar addu'a, don samun al'amarin. Ya dube shi tsakar ido ya amsa,"Naseer ba ya buk'atar addu'a, sai hukunci. Damuwa ta 1 ce, yaron nan da aka jawo shi cikin fitinar da bai ci ba, bai sha ba. Shi kad'ai ke buk'atar addu'a. Ubangiji Allah ya ku6utar da shi." M.Lawal ya ce,"Insha-Allahu baki dayan su za su ku6uta, duk da dai mu ba mu da k'arfin d'aukan lauya, ai Allah na nan, za mu gaya masa ya duba mana. Ni zan k'arasa gida M. Balarabe, kuma ina ba ka shawara fushin farko ba na ka bane. Ka sani bakin mahaifi dafi ne ga 'ya'yansu, yayin da suke cikin fushi da su. Saboda haka ka sanya wa ranka ruwan sanyi, mu rungumi k'addara. Ya mik'e, ya na k'ara fad'in,"Malam Umar ni zan wuce, sai yadda hali yayi kenan?"Ya ce,"To Allah ya jishe mu alkhairi, ya kuma sauka mana wahala." Ya amsa da amin, duk suka yi Musabaha. Ya wuce ba tare da M.Balarabe ya k'ara tofa wani abu ba. Bayan tafiyar M.Umar, ya dube shi, ya ce,"Malam Balarabe ka yi wa girman Allah, ka sanya wa ranka cewar wannan abu mukaddari ne daga Allah, babu makawa sai ya faru." Ya ce,"Shi fa Allah baya d'ora wa bawa abinda ya fi k'arfin sa, sai abinda shi bawan ya d'ora wa kan sa. Idan yayi taka tsan-tsan da rayuwar sa, yana kiyayewa, sai Allah ya taya shi kiwo. Shi yasa Ubangiji ya ce,"Idan kun ga sharri, to daga gare ku ne, sai ku binciki kan ku. Amma shi ya ce yana 1 daga cikin imani yarda da k'addara mai kyau ko maras kyau.Na yarda cewa Naseer shi ya jawo wa kan sa, sai dai kai ina son ka yarda da cewa kaddara ce Allah ya dora maka, babu makawa sai ka ga wannan 6acin ran, amincewar kuwa shine ka daina fushi da Naseer, ka taya mu addu'a Allah ya ku6utar da su." Yayi shiru kamar ba zai tanka ba, tsawon lkc. Sannan ya sauke numfashi ya ce,"Na ji Malam Umar, na kuma gode. Allah ya bar zumunci, amma kar ka manta, na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba." Malam Umar ya mik'e rai 6ace, ya fice daga rumfar Malam Balarabe. Babu Sallama. Malam Balarabe ya bi shi da kallo, kawai na tausayin su ya lullube shi, ya kad'a kai, ya ce a ran sa,"Naseer na da gatan sa, amma shi bai san hakan ba. Allah ka shirya." Haka hankali Sageer yake tashe, jin cewar shi ma ana buk'atar sa a kotu da laifin shi ya gudu da wuk'ar da ake zargin Naseer ya je kashe Salis da ita. Bai san lokacin da ya kawo kan sa gidan su Zarah ba.tana kwance ruf da cikin, gefen tabarma da suke tare da Innar ta,har ya gama gaisawa da Inna Zarah bata iya dagowa ta dube shi ba, sbd jin muryar sa ma k'ara dagula mata lissafi yayi, wasu sabbabin hawaye suka cika idanuwan ta tam! Kayan makaranta ke jikinta, don bata iya cire su ba, tunda ta dawo ta sami yadda shari'ar ta kaya a kotu, ido jajur! Sageer ya dubi Inna,"Yanzu mecece mafita Inna?" Gaba 1 tausayi yaran ya gama kashe mata jiki. Ya nisa ta ce,"Mafita 1 ce Sageer, ita ce addu'a wajen Allah. Ka kwantar da hankalin ka. Insha Allahu za ku ku6uta. Kar ka damu ka ji?"Ya ce,"Shi kenan Inna. Allah ya taimake mu." Ta ce,"Amin." Ya sauke idanuwan sa, inda Zarah ke kwance, yayi kiran ta,"Zarah! Bata amsa ba, ya ci gaba,"Kiyi hak'uri Zarah." Dasauri ta mike cikin sassarfa, hawaye na zuba ta nufi daki. Dai-dai k'ofa ta tsaya tana fad'in,"Sai Allah ya tsinewa Salis!wannan sharri yayi yawa. Insha-Allahu sai ya ga k'arshen sa!" Ta juya cikin d'aki da gudu. Sageer ya ce,"Yaya za mu yi Zarah? Sai hak'uri kawai." Ya juya kan Inna,"Bari in koma Inna, ki gaida Baban. Gobe asabar. Insha Allahi zan je in ga Naseer d'in." Ta ce,"To Allah shi kare." Ya amsa da "Amin." Ya mik'e ya bi Zarah d'aki. Can yayo ta rarrashinta har suka shirya tafiya gidan yari gobe, ganin Naseer, ba tare da sanin su Inna ba, don kar su hanata. Karfe 10 na safiyar asabar a k'ofar gidan yari tayi masu. Sun jima suna neman yadda za su yi, a bar su ga Naseer d'in, kafin suka sami amincewar hukumar gidan mazan. Suna zaune cikin wani d'an d'aki wanda za'a iya cewa ofishin gandirebobin ne, aka fito da shi. Bak'in k'ofar yayi tsaye ya sanya wa Zahar ido. Kwanaki 5r kenan, amma ji take tamkar shekaru 5r ne. Rabon da ta sanya shi a ido. Tausayinsa yasa take ganin ya rame, ya dishe kamar ya shekara yana ciwo. Hawaye kamar fanfo, suka tsunke mata. Naseer ya juya da sauri cikin 6acin rai ya ce wa gandiroban,"Maida ni ciki!" Ko kafin Sageer ya ce wani abu, har Naseer ya kai bak'in k'aton gate d'in da ke k'argame a bakin babbar k'ofar da za ta kai ka ciki. Gandiroba na biye da shi,"Ba ka son ganin su ne?" "Eh!" Ya amsa ba tare da ya waigo ba. Gandiroba ya bud'e get, yayin da Sageer ke k'arawa wajen," Naseer! Naseer magana na ke so mu yi! Ya shige ciki, aka rufe, sannan ya juyo ya ce,"Idan za ka zo, ka zo kai kad'ai, ban da Zarah! Ya wuce cikin sassarfa ya bar wajen. Sageer yayi tsaye, yana kallon sa, har ya daina ganin sa. Ya tako a hankali inda Zarah ke durk'ushe, kanta cikin guiwa. Ya ce,"Zarah! Taso mu tafi." Da kyar ta mik'e, gaba 1 Gandiroba da ke wajen, babu wanda bai kalle ta ba, wasu ma dariya ta ba su, ganin yadda Sageer ke jan hijabinta, tana jefa k'afa kamar makauniya.Daya daga cikin su da ke zaune gaban wani katon tebur da alama yana daya daga cikin manyan wajen. Tsam! Ya mik'e ya nufo su, abinka da yare kuma babu musulunci, yana zuwa ya rungumo kafad'un Zarah ya shiga rarrashin ta,"Kin kuwa san yadda ki ke da kyau, ki ka zauna ki na kuka? Don wannan tsohon mai laifin, ya ce bai son ganin ku?" Da sauri ta kwace kafad'un ta, ta balla masa harara." Tsohon mai laifi? Yayana ba tsohon mai laifi bane,sharri aka yi masa, kuma Allah zai fitar da shi! Tuni ta bar Gandiroba nan a tsaye. Sageer ya biyo ta. Dariya suka ci gaba da yi, abinda ya k'ara hassala zuciyar Sageer. Gudun mai zai faru, idan ya tanka, shi yasa ya rufawa Zarah baya, suka bar harabar wajen. Tafe suke. Zarah na koken,"Kiri-kiri yayana ya ce baya son gani na, me yasa?" Ya ce,"Ai ba zai so ganin ki a yanayin da yake ciki ba. Ba zai so ki rink'a kuka ba Zarah.." Ta ce,"Ba wani Sageer, akwai abinda yayana ke nufi." Bai nufin komai, yakamata ki gane, ba kowane zai jure ganinsa a haka ba. Kawai ki manta Zarah, addu'a kad'ai za ki taya mu." Ta sauke numfashi ta ce,"Yadda yayana ke so na, haka na ke son shi Sageer, ya kuwa zama dole in yi kuka, tunda yana cikin wani hali. Na san yayana jarumi ne, komai zai iya jurewa, amma zama cikin wannan shegen gidan rayuwar kunci zalla cikin sa. Salis ya bi son zuciya zai kuma ga 6acin ta yarda Allah." Dai-dai suna tsayuwa bakin titi. Sageer ke fad'in,"Zarah yayenta kenan, soyayyar ta d'aure min kai. Shi kuma Salis ai har

Chapter 3 of 11