Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 11
dama ya zauna rumfar Baban sa, idan bai yi ra'ayi ba kuma ya buga yawon sa, musamman idan akwai wasa a filin sukuwa. Kwalejin jeka, ka dawo ta gwamnati da ke kufena, ita Naseer ya samu, yayin da Sageer ya sami kwalejin Alhuda-huda. Karatu ya kankama, hakan bai hana Naseer kula da 'yar kanwar sa ba. Kullum safiya a bakin kofar mkrntr su take samun sa yana zaman jiranta, sai ya danka mata kudin tara da dukkan abinda ya ci ya rage mata, sannan ya wuce." Bai hada wata 3 ba, gaba daya a mkrntr sunan sa yayi tambari, ko dama shi ne shugaban ajin su watau (Monitor) Tun daga Malamai har manyan da ke gaba da shi, sun san Naseer da kokari da rashin ji. Babu damar manyar sa su ta6a shi, ana fita wajen mkrnt, zai tara masa duwatsu. Suna ji suna gani Naseer ya gagare su, ba'a dade ba, ya zama abokin kowa, suna kiran sa HUKUMA. Ba wanda bai san Naseer Hukuma ba, har shugaban mkrnt (Principal). A yau da aka kawo masa Naseer gaban sa da laifin rufewa Malamin su kofa.Principal ya dube shi da kyau ya ce,"Mece ce hujjar kullewa Malaminka kofa?" Yana daga durkushe kyar! Ba alamar tsoro ya ce,"Duk ranar da babu asanbili, karfe 7 da rabi yake rufe mana kofa, duk wanda ya zo bayan wannan lkc, sai dai ya zauna a waje. Darasin English ya wuce shi kenan. Shi yasa na gaya kowa yayi kokari yau ya zo da wuri, sai kuma ga shi yau Malam bai zo ba, sai takwas saura kwata, dalilin da yasa kenan na rufe kofa, don shi ma ya makara. Principal ya tsura masa ido, yana mamaki,"A ina ka ta6a jin an rufe wa Malami kofa?" Ya sosa keya ya ce,"A kufena." Nan da nan Principal ya shaka,"Iskancin ka ya zo kaina ne? To na lura ba ka da tarbiyya, sbd haka bayan sajen ya hukunta ka, za ka koma gida ka huta sati 2, idan za ka dawo kuma da Babanka." Naseer yayi shiru, ko ajikin sa, shi nan take ma yake tunanin zai sami isasheshen lkcn zuwa filin Sukuwa. Yana tsaye garau! Sajen yayi masa bulala goma masu kyau. Aka mika masa takardar hutun cewa aji." Ga wata sanarwa!. Zan tafi Saudiyya, sati 2 zan yi idan Malama ya sake rufe ma ku, kofa ku aika min da sako daga can zan sa masa (Road block' . Duk suka dau ihu........ Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-02 Posted by ANaM Dorayi on 09:40 PM, 03-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_____________Ya daga hannanyensa sama, ya ce,"Sai na dawo!" Suka ce,"Hukuma!" Hukuma!!" Ya ce,"Ko ba'a rarrashe ta ba, hakuri take don U........in karasa?" Ihu kawai suka yi. Shi ya jawo hankalin Malamai. Nan take aka firfito da su waje, duk aka ce su zube sajen yayi masu biyar-biyar. Shi kuwa Naseer aka tasa keyar sa ana dukan su suna ihu." Abar mana Naseer! A bar mana Naseer!! Karfe tara da kwata ya dawo gida, lkcn Baban sa ya riga ya fita. Umman sa ta ji motsin bude dakin sa da ke zaure. Ta leko, don ganin wa ke taba kofar, Sai ta gan shi. Fuska yamutse ya ce,"Koro ni aka yi." Ta ce,"Ka biya kudin mkrnt Naseer, me zai sa a kore ka?" Yayi dan shiru, ka fin ya ce,"Laifi na yi Umma. Ta tsura masa ido, ta ce,"Haka dai, kullum kai ba ka girma Naseer, balle ka yi wa kanka fada. Laifin me ka yi kuma?Kai tsaye ya gaya mata abinda ya faru. Ta kame ha6a ta ce,"Tirk'ashi! Allah ya shirye ka. Zaman gida ka fi so ko? To ai shi ke-nan, sai ka yi ta zama ranka na maka dad'i." Ta juya ta shiga cikin gida abin ta. Ya tura kofa ya shige d'aki, ya watsar da littattafansa gefe, ya kwanta ringigine bisa 'yar katifarsa yayi shiru, can ya ja d'an tsaki ya ce,"Komai dai ni ne mai laifi, mutum ya raina mana wayau, sai a k'yale shi? Mts........." Ya ci gaba da kuncin rai, wai kullum shine mai laifi. Da yamma Baban sa ya dawo. Mairo ta mayar masa da abinda ya faru. Yayi shiru bai iya cewa komai ba. Suna zaune k'ofar gidan su Sageer, shi din ke masa fad'a. Naseer 6ata lokacin ka ka ke yi. Wallahi ina gaya ma wannan maganar ka na ganin ihun banza nake, ba za ka gane kuskuren ka ba, sai nan gaba. Shi karatu ko na k'wana d'aya ya wuce ka, ai an cuce ka, balle na sati 2. Amma fa sai ka yarda." Ya ce,"Me zai faru, idan ban yarda ba? Ya amsa,"Me kuwa?" Kawai ina gaya ma gaskiya ne." Ya nuna shi ya ce,"To ashe kai ne babban mai 6ata lokacin sa. Ni nan da ka ke gani, ba'a raina min wayau. Gidan su Zarah za ni, za ka?" Ya hahare shi ya ce,"Ban zuwa.." Kar ka je, sai me?"Yayi banza da shi. Ya mike ya wuce abin sa. Sageer ya bi shi da kallo, ya kad'a kai ya ce,"Ina tausaya ma Naseer. Allah ya shirye ka." Shi kuwa gidan Zarah ya je suka sha hira cikin gidansu da Innar ta gab da kira magariba, sannan ya koma gida. ************** Washe gari da safe 7:30, kamar yadda ya saba fitowa yana tsaye gefen titin Kongo, wanda ta mik'a har (W.T.C). Jar T.Shirt ce a jikin sa da wandon Jeans. Nan ya saba jiran Zarah, don bata kud'in tara.Zuwa can ta doso, kayan makaranar nan sun sha guga, sai d'aukan ido suke yi tamkar yadda ita kanta Zarah ke d'aukan hankalin jama'a, sbd tsabar kyau da kullum take kara yi. Kayataccen murmushi suke wa juna, sai da ta zo gab da shi, ta ce,"Yayana, ban gane ba, ina uniform?" Ya tura hannayen sa aljihu ya ce,"Ga su nan a jiki na." "Wai ba za ka makarantar bane ko yaya ne?"Ya zura mata ido yadda take motsa bakin ta, yake burge shi,"Huta na ke yau." Ta ce,"Wasa da karatu Yaya na?" Gaskiya ni ma zuwa na bai da amfani, mu je gida kawai ni ma in cire." Yayi d'an murmushi ya ce,"Ki na so in yi miki bulala kenan? Ita ma murmushi tayi,"Ka san Allah, sai na had'a ka da Inna. Ya sanya mata ido, ya kasa cewa komai." Ka na ta kallo na, magana na ke." Ya ce,"Yau fuskar ki tayi min kama da hasken zara, sai na tuna ashe zarar ce." Ta dan shagwa6e fuska,"Kai yayana, maganar makarantar na ke. Ka koma gida ka sayo uniform, ka wuce makaranta, idan ba ha ka ba Inna za ta ji " Ya ce,"Don Allah ki share." "To me ya hana ka zuwa?" Ya ce,"Hmm......laifi na yi." "Wane irin?" "Ke dai zo mu je in raka ki, na gaya miki a hanya. Suka wuce ya na labarta mata. Ta dube shi,"Kai yayana, saboda Allah me yasa haka?" Ban kyauta ba ko?" Ya tambaya. Ta ce,"Gaskiya ba ka kyauta ba, don wanna 6ata Record ne. Don Allah kar ka sake. Ya numfasa ya ce,"An gama.Kuma sai da ki ka fad'a na gane ban kyauta d'in ba. "Tayi 'yar dariya, yana kallonta,"Yayana, kai kullum ba ka sanin ka yi laifi, sai na fad'i? Amma in na ce ka gyara, sai ya gagara." Ya dan ja ya tsaya,"Me ki ka ce in gyara, ban gyara ba?" Ita ma ta tsaya,"Da kana gyarawa, yaushe za'a ba ka hutun dole? Yadda yayana ke so na, ya kamata ace komai na ce, ta zauna. Yanzu ni ka ga babu yadda za'ayi in tsallake maganar ka." Yayi murmushi, suka ci gaba da tafita, yana tad'in,"Komai ki ka ce, ba na tsallakewa, ke ce ba kya ganewa." Ta dube shi kamar yadda yake kallon ta, ta ce,"Na sakar ma yayana." Suka yi ta tafiya har kusa da mkrnt, sannan ya ja birki ya ce,"To bari in bar ki anan, amma Zarah hak'uri za tayi, yaya bai da kud'in (Break)." Ta shagwa6e a gaban sa,"Ni a'a. Allah ni na saba kashe kud'in yayana." Ya d'aga lallausan gashin girar sa, bak'i wulik! Yana kallon ta. 'Yar dariya yake yi mata. Ita kuwa shagwa6ar ta take,"Allah ni ma zan koma gida!" Ya laluba aljihu, ya ciro Naira 20 ya mik'a mata. Ta amshe tana fad'in,"Dama tsoka na ce? Shi kenan ni ma ba zan rage maka abinda na ci ba." Ya ce,"Har kin isa. Ki na son bulala kena." Ta yi murmushi ta ce,"To na gode, sai na dawo. "Ya ce," A dawo lafiya." Ta juya ta shiga cikin 'yan mkrnt, tana tafe tana waigen sa, shi kuwa yana tsaye, ya kama tafiyar ta k'ule masa.Ya sauke numfashi, ya juya ya dawo gida. Sati 2 suka cika. Naseer zai koma makaranta. Malam Balarabe ya ce bai san zancan bin sa makarantar ba. Ran Naseer ya 6aci, ga shi yana son komawa makarantar, don kar Zarah ta ce shine bai son zuwa. Sageer ya samu a karo na farko ya rok'e shi, su je ya rarrashi Baban sa yayi hak'uri, su tafi makarnta gobe tare. Abin ya ba Sageer mamaki k'warai, kuma yayi farin cikin jin hakan. Saboda haka babu 6ata lokaci, suka same shi da daddare. Sageer yayi ta rok'o a madadin Naseer. Malam Balarabe ya ce,"Sageer ni na haifi Naseer, amma ko alama Naseer bai san mutuncina ba, bai san mahimanci na a gare shi ba. Tun da abin nan ya faru, ban iya cewa da shi k'ala ba, sbd takaici da 6acin rai, amma Naseer bai san ya durk'usa gaba na ya ce Baba ka yi hak'uri akan abin da na aikata ba. Sai yanzu ne zai ce in zo muje makaranta? Me zan ma sa? Bayan ba ni da amfani a gun sa? Sageer ya kara duk'awa ya ce,"Baba ka yi hakuri, ka yafe masa." Ya ce,"Naseer yaro ne?" Shekarunsa goma sha takwas, yayi hankalin da zai san 6acin ran iyayensa. Babban kuskur ne a gare shi. Amma shi komai yayi, sai ya d'auka dai-dai ne. In banda tsageranci, menene na rufewa Malimin ka k'ofa, don shi yana rufe ma ku? Ashe za ka iya rufe min gida, duk ranar da na yi dare a waje. Ka kiyayi duniya Naseer, ranar da za ta koya ma hankali sai ka gwammace ba ka zo cikinta ba." Ya k'ara sunkuyar da kai ya ce,"Ka yi hak'uri Baba, in Allah ya yarda ba za'a sake ba."Sageer ya ce,"Baba, ka amince goben za ka d'in?" Ya ce,"Ya zama dole, tunda ka sa baki Sageer, don ka fi shi hankali, da ace yana koyi da kai, ai da ba haka ba. Ni dai bn ma sa mugun baki ba, iyakata da shi add'ur Allah ya shirye shi. Amma daga yau in ya sake d'ebo rigimarsa, ko alama ba ni a ciki. Kar ma ku dunfaro ni. Ina fatan kun ji abinda na ce,"Sageer ya ce,"Insha Allah." Ya ce,"Allah ya kai mu goben. Allah yayi maku albarka." Suka amsa da "Amin- Amin." ************** Washe gari Malam Balarabe ya maida Naseer makaranta. A gaban (Principal) da sauran Malami Naseer ya d'auki alk'awarin ba zai sake sa6awa dokar makaranta ba. Shugaban makaranta ya ce idan ya sake korarsa za su yi, don fitinar sa ta ishe su. Malam Balarabe yayi ta ban hak'uri, sannan aka sallame su. Malam Balarabe yayi gida. Naseer yayi aji. Akwai Malami a cikin ajin, don haka a salihin sa ya shige. Sauran d'alibai na ta bayyanar da farin cikin su bisa fuskokin su. Bai kula kowa ba, ya wuce mazaunin sa, ya zauna a d'aure. Malam na bada baya, duk suka yanyame shi"HUKUMA! HUKUMA!!" Ya dube su ya ce,"Yawa ku ke, kowa ya zauna, in ba ku wani labari." Suka zauna sauraron sa. Ya mike ya zo gaban allo ya tsaya. "Gata nan, gata nan ku!" Suka ce,"Ta zo mu ji ta!" Ya ce,"Da Naseer ne da Englishi Master, wata rana sun fita farauta, sai Naseer ya kafa Malam, ya na da A B C D. Englishi Master zai k'wace, dambe ya kaure. Naseer ya kada Malam, ya na da A B C D a gwafa, ya auna masa koda ya mike, sai ya rubta wa Naseer SUSPENSION."Gaba d'aya suka d'au dariya da tafi har da masu fito, ya ce,"A saurara! Sati 2 Naseer ya dawo, amma da sabon alk'awari." Ya kame kamar soja, hannun sa ma dama saitin kunne sa, ya ci gaba,"Na d'auki alkawari ga makarantar kufena. Zan zama mai ladabi da biyayya. Zan maida hankali ga karatuna, zan tabbatar da ci gaban ta, idan ba haka ba, kora ce!" Ta yadda ya aje salon kalmar k'arshe KORA ce! Shi yasa duk suka d'auki tafi,"Yayi! Yayi!! Allah ya bar mana HUKUMA!" Ya ce,"Hukama na ofishin principal, sbd haka kowa ya d'auki wannan alkawarin, kar fushinta ya kama shi." Ya d'auki alli ya rubuta bisa allo.,"Ya ce,"Wannan shine Nationar Anthem d'inmu. Suna ta hayaniya. Malamin Geography na tsaye yana kallon su, sai dai suka gan shi tsulum! Ya karasa shigowa.Da turanci yake magana,"Meke?" Naseer ya ce,"Ba komai." Ya aje alli, ya wuce wajen zaman sa. Malam ya dubi allo ya karanta abinda Naseer ya rubuta, ya dube su da kyau ya ce,"Wa ya rubuta wannan?" Baba wani 6oye-6oye Naseer ya d'aga hannu. Ya ce,"Ya mik'e tsaye. Tsaf! Ya tashi fuska d'aure. "Menene wannan?" Ya k'ara kirnewa, ya ce,"Sabon alk'awari ne, New testament ba." Dariya ta kubce masa, yayi d'an murmushi, ya ce,"Naseer ba ka ji ko?" Ya dan duk'a ya ce,"Allah ya shi taimaki Malam!" Suka d'auki dariya. Malam ya ce,"K'wana 2 ba na ganin ka, ina ka je?" Ya amsa"Saudiyya." Ya tsira masa ido, yana kad'a kai,"Hajji ko umrah?"Ya ce,"Umrah." An dawo lafiya? Ina tsaraba?" Ya nuna allo ya ce,"Ga ta nan kuwa." Malam d'aurewa yayi ya ce,"To ka share." Ya k'ara duk'awa ya ce,"Allah shi taimaki malamin binciken yanayi." Ya fito yana na tafawa, ya d'auki abin share allo ya share."Malam an share." Ya ce,"Ka ci gaba da tsayuwa anan." Ya dubi d'alibai ya d'aga gira ya ce,"Soja kenan a fakaice." Nan ya ci gaba da tsayuwa har darasi ya k'are , kuma hakan bai hana shi abinda yake so ba, duk da cewa ya san tsayuwar ma horo ce aka ba shi. Naseer kam sai addu'a. ************** Sannu a hankali. Malamai da iyayen Naseer suna hak'uri da shi. Har ga shi gobe ake sa ran za su fara rubuta jarabawar su ta karshe watau, (WAEC). D'in su. Da yammacin wannan lahadin ce. Naseer ya d'auki wankan sa yayi tsaf! Cikin gogaggen yad'in sa ruwan madara yayi kyau sosai, dan shi Naseer akwai son gayu, ga kuma tsafta. Zai yi wuya ka gan shi a yamutse. Kayan sa kuwa duk inda zai nemo guga, sai ya nemo, sbd babu yadda za'ayi ya sanya kaya ba guga. Ya dan goge sandal d'insa bak'i, kai tsaye ya wuce gangare gidan su Zarah. Bai nemi Sageer ba, saboda ya san zai yi wuya ya fita yawo, saboda karatun jarabawa. Yana cusa kai cikin zaure, idanuwan sa suka nuna masa wani abinda bai ta6a jin fad'uwar gaba ba, sai akansa. Zarah ke tad'i da wani saurayi, wanda ita ma a yau d'in nan suka had'u da shi. Sarai Naseer ya san saurayin a nan layin sarki yake, sai dai ko gaisuwa bata ta 6a had'a su ba.Nan take kishi ya lullube shi, mahaukacin kishi kuwa, don sai da ya ji zuciyar sa ta kulle, ta tattaro ta dawo iya wuya. Duk da cewar bai ta6a furtawa Zarah kalmat so ba, illa iya ka komai take so, shima shi yake so. Tana ganin sa,tayi sauri ta rufe fuska da hijabinta, har ya wuce cikin gida, bata bude ba, haka kuma babu wanda ya tanka ma wani. kujera ya ja tsakar gida, suka gaisa da Inna, tana tsakar alayyahu. Ya jawo faranti yana tayata."Amma gaba d'aya hankalin sa bai jikin sa." Lafiya Naseer?" Ya ce,"Lafiya lau Inna, me ki ka gani?" Ta ce,"Na ji ka yi shiru ne, ko anyi fad'an da su Umma ne?" Ya kada kai,"Babu komai wallahi." To duk tunanin jarabawar ce?" Ya ce,"Jarabawa ai mun gama da ita. Insha Allahu babu abinda zai gagara." Ta ce,"Allah shi yarda Naseer, ai ba na haufi akan dan nawa." Ya mika mata alaiyahun da ya tara a hannunsa, ta karfa tana yankawa. Zarah ta yi sallama ta shigo, suna hada ido, ta rufe fuska da hannayen ta, ta fad'a daki. Ya ce,"Ki fito kawai, yau bulala za ki sha." Inna ta ce,"Yakamata, haka kawai ana zaune k'alau, za ta fara jawo mana samari, wai shi nan auran ta zai yi, ba yaudara ya zo yi ba." Shi d'in ya fad'i haka?" Inna ta ce, "Eh, ai sai da Babanku ya fita, ya tsare shi a zauren. Zuciya ta k'ara shak'e shi, da kyar ya amsa,"Inna Zarah ai yarinya ce, kuma karatu za ta yi." Ta ce,"Ni ma shi na gani, amma Malam ya ce tunda da gaske yake, sai ta tsaida shi, tana gama karatun, ayu da shi, idan Allah ya nufa.'Kyar yake kallon Inna. Zarah ce ta d'auke masa hankali da ta fito, tana fad'in,"Yaya na ina wuni?" Ya maka mata harara. Tayi murmushi, ta zauna kusa da shi,"Me na yi yayana? Wannan harara ta bata min fuskar ka, dan yi murmushi mana, haba Big Bros." Ya dubi Inna fuska daure, "Kin ji yadda yarinyar nan ta raina ni ko?" Ta ce,"Kai ka kyale ta." Ta d'auke alayyahunta ta shige kicin. Shi kuwa hararar Zara ya ci gaba da yi. Ta sanyaya murya, ta ce,"Ba ka ga yadda ka yi ba, me yasa?" Ya ce,"Karatu za ki yi, ko tara samari?" Ta ce,"Salis ne kawai yayana, don Allah ka yi hak'uri." Ya ce, "Zarah! Zarah!! Zarah!!! Ta amsa." "Na'am." Sau nawa na kira ki?" Ta ce,"Ina jin sau 3 ne." Ya k'ara dubanta," Ki na ma ji ne?" To shi ke nan." Ki saurare ni." Ya mik'e yana fad'in."Inna na wuce!" Ta lek'o ta ce,"To Naseer, agaida su Ummah." Yayi waje. Zarah na bin sa."Yayana, me zan saurara na ce?" Ya juyo cikin zaure, ya ce,"Ai ba ki tabbatar da ko sau nawa na kira ki ba, it means hankalinki ba a waje na yake ba. Saboda haka ni zan yi wa tufka hanci, don hankalinki ya tsaya waje 1." Ya sa kai ya fice ya bar ta cikin duhu. Yana ji tana kiran sa, amma kishin daya mak'ure masa wuya, ya hana shi amsawa. Bayan sallar isha'i, gidan su Sageer ya nufa. Ya yaye labulen dakin ya shiga. Kwanon abinci Sageer d'in, ya bude zai fara ci." Me ka ke yi?" Ya ce,"Abinci zan ci, zo mu ci mana." Ya ce,"Don Allah ka rufe abincin nan, ka taso ka raka ni nan layin sarki." To ka za mu ci abinci mana!" Kar in rasa wanda zan je nema ne. Don Allah ta so mu je." Sageer ya rufe abinci, ya sanyo takalaman sa, ya rufe dakin sa, suka wuce layin sarki, ba tare da ya san me za su je yi ba.Kawai Naseer ya ce,"Wani zan je gani." Suna zauna da abokan sa 2, labarin yarinya Zarah yake ba su, lokacin da Naseer suka iso tare da sallamar har da Musabaha, kamar abin arziki. Naseer ya dube shi ya ce,"Ah! Kai ne Salees ko?" Ya ce,"Eh ni ne, lafiya?" Ya ce,"Ita ta kawo hakan. Na san ba sanni ba, amma watak'ila da, da rana na zo, da ka gane ni. Well kar mu je da nisa, kawai gargadin ka na zo yi akan yarinyar nan Zarah. Ban som in k'ara ganin 'yar k'afan ka a gidan su. In kunne ya ji........" Ya juya zai wuce. Salis ya dafo k'afarsa ya ce,"Dakata mana. Kalle ni, idan ka na takama kai dan Tudun wada ne, ni ma kazalika haifaffen Tudun Wada ne, saboda haka karan daji bai isa ya budewa karan gida ido ba." Naseer yayi dan murmushi ya ce,"Allah ko?" To lulaba da kyau ka ji, wannan ba kare ba ne, kura ce, don uban kare karyar sa." Sageer ya rik'o shi yana fad'in." Naseer! Dama rakiyar da ka ce in zo yi kenan, Meye haka?" Abokan Salis ma suka taso." Me ye haka ku ke yi? Don Allah ku bari, yawa ne. Zaarah sai wanda ta za6a, sbd ha..........." Wani wawan mari Naseer ya tsinkawa, mai maganar. Shi yasa yayi gum da bak'in sa. Salis na ganin haka, shi ma ya ware. Sageer ya kamo Naseer ya ce,"Naseer, kada ka kuskara ka dauko wannan fitinar! Ka ga k'ofar gidansu ka zo, duk inda aka je, kai ne mai laifi! Ya ce,"Da shi na ke magana, daya sanya min baki?" Yana rufe da baki, ya ji saukan naushi. Cikin zafin nama Naseer yayi kukan kura, ji ka ke yi dim! Ya sakarwa Salis naushi a mukamuki. Nan take kamar almara. Salis ya fad'i a sume. Abokan Salis suka rude. Sageer ma ya firgice, ya rinka jan Naseer, yana fad'in,"Ka gani ko?" Ka ga irin ta ko?" Su kuwa abokan Salis cikin gida suka shige, neman taimakon jama'a."Ka zo mu tafi Naseer!" Yana jan sa, yana tirjewa,,"Babu inda za ni!" Ka kyale ni. Duk abinda suka ga dama su yi!" Ya ce,"Haba Naseer! Me yasa kai zuciyarka bata kulla maka alkhairi ne? Dubi fa abinda ka aikta? Ka na zaton iyayensa za su kyale ka ne? Wallahi da na san abinda za ka zo ka yi aikata kenan. Sam da ban biyo ka ba, ba za ka ja min masifa ba wallahi! Ya dube shi da kyau, ya ce,"Sageer! Bi tannan, in bi ta can, idan ka kuskura muka had'u, sai na fasa maka baki! Yana sa aya ya wuce, ya bi ta inda ya nuna, suna jin abokan Salis na fad'in Ga shi can zai gudu! Sageer ya shafa a guje, ya tsere. Shi kuwa Naseer ja ya yi, ya tsaya har gayyar jama'ar suka zo gunsa.Me yayi maka, za ka kashe shi?" Ya ce,"Ku zuba masa ruwa, ya farfad'o, sai yaga maku." Samari suka yi caa! Za su rufe shi da duka, mahaifin Salis ya hana, don tuni ya tura daya daga cikin abokan Salis din ofishin 'Yan sanda. Ana ta kwaranniya, ga Salis a kwance shame- shame. "Yan sanda 2 suka iso, nan take suka wuce da Naseer da laifin yunk'urin kisan Kai, kamar yadda aka shaida ma su. Salis dai sai da ya hau gadon asibiti a daren nan, sannan ya farfado. Wuyan sa a kage, bai iya juyawa ta gefen da Naseer ya naushe shi. Kai tsaye gidan su Naseer, Sageer ya nufa. Yana ta hak'i, kamar ran sa zai fita. Malam Balarabe da Mairo, suka firgice. "Menene Sageer?" Ya ce,"Ba lafiya Baba, ina zaune Naseer ya ce in zo in raka shi layin sarki. Ashe fad'a za shi yi. Wallahi Baba ban sani ba, a takaice dai ya naushe masu yaro ya fad'i, suma yayi mutuwa yayi? Allah kad'ai ya sani, ya zo ma mu gudu, ya ki. Can na baro shi, ban san halin da ake ciki ba!" Mairo salati da d'auka, shi kuwa Malam Balarabe cewa yayi,"To ba shi kenan ba, ka koma gida abinka, ka yi kwanciyar ka. Tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa zai yi wa banzan duka. Idan sun so ma, kar su bar shi da rai, babu abinda zai dame ni." "Baba...." Ya katse shi,"Babu ruwanka na ce! Ka wuce gida abin ka, idan kuma kai ma can d'in za ka sake komawa, to Bismillah! Amma ni Balarabe ba ni a cikin wannan maganar." Tuni Umma ke tsiyayar hawaye,"Sageer mu je, ina ne, suke fad'an?" Ya ce," A layin sarki ne." Malam ya ce,"K'ofar zaure ban ba ki izinin takawa ba. Yauwa." Ya sa kai, ya koma d'aki. Umma ta koma bisa tabarma, ta tallabe kai ta ce,"Wannan yaro, wannan yaro. Allah ka shirye shi.Sageer ya tsuganna ya ce,"Umma ki yi hak'uri, ki daina zubda masa hawaye." Ta dube shi cike da damuwa ta ce,"Bari fad'i Sageer, ya zama dole in yi hawaye, don bansan masifar da Naseer ya jaji6o mana ba wannan karon. Me ya had'a su da yaro?" Ya ce,"Ni ban san takamaiman zancen ba, amma na ji wai yana masa gargad'i akan Zarah." Ta ce,"Zarah? To shi me ya dame shi da saurayin Zarah? Auranta zai yi?" Ya amsa,"Bai ta6a yi min magana a kanta ba, sai dai bn san abinda ke cikin ran sa ba a game da ita." Ta sauke numfashi ta ce,"Dubi wannan abin kunya, akan budurwa, ya je yana haukan banza, idan ya kashe d'an mutane, ya yake son mu yi da ran mu? Yanzu kai Sageer ka yi hak'uri, ka koma ka bincika mana halin da ake ciki ka ji?" Ya ce,"Ya zama dole Umma, bari in tafi. Allah shi kyauta." Ta ce,"Aamin." Ya mike ya fice. Nan ta ci gaba da zama a kunci, tana mai tsananin al'ajabin halayen Naseer, kamar ba su suka haife shi ba, don ko 1 bauko halayyar su ba. Ta nisa face,"Kuda, ya haifi zuma. Allah ka shirya mana! Tsaye Sageer yake a cikin jama'ar da suka taru, suna ta maida labarin fad'an da aka yi karya da gaskiya. A nan yake jin Naseer na hannun "Yan sanda a anan caji ofis da ke kusa da su. Jikinsa na rawa, ya bazama ofishin. Cike yake daga waje, daga ciki kuwa abokan Salis suke ta bada bayanan yadda abin da ya faru (Statement). Shi kuwa Naseer yana tu6e, a bayan kanta. Yana isowa, mai magana lkcn ya ce,"Yauwa ga shi nan, tare suka zo, amma shi raba su yake yi, yana ta jan sa, ya k'i tafiya.Sai da ya sumar da shi." Dan sanda ya ce, wa Sageer shi ma ya fad'in abinda ya sani. Tiryan-tiryan ya maida wancan, dan sanda ya ce, ya dubi mahaifin Salis ya ce,"Duk mun ji bayanin kowa, kuma hakan ya tabbatar mana Naseer na da laifi dumu-dumu, saboda haka za mu tsare shi a a nan a bisa laifin tada husuma, har zuwa lkcn da Salis zai sami sauki. Sajent!"ya amsa,"Sir!" A wuce da Naseer cikin Cell."Sageer ya d'ora hannu a ka yana fad'in,"Inna-lillahi-"Wa-Inna-ilaihir raji'un!" Insfesta ka yi hkr, ka ba ni shi beli. Gobe za mu fara (Exams), ka ga za ta wuce shi." Dan sanda ya gyara fuska, ya ce,"Ya san da jarabawar, ya je neman fad'a? Bata dame shi bane, da ta dame shi, karatu yakamata ya zauna yayi, ba fad'a akan budurwa ba. Saboda haka babu, har sai Salis ya bar asibiti. Kuma gaba d'aya abinda aka kashe a asibitin, za'a kawo (Bill) nan, shine zai biya. Na gama da ku." Sageer ya na ji, yana gani, aka wuce da Naseer ko gezau bai nuna a fuskar sa ba. Har goma da rabi na dare. Sageer na aikin rok'on a ba shi Naseer akan beli, amma dan sandan nan ya k'i, anan iyayen Salis suka bar shi, kuma da gani akwai wata 'yar muna-muna tsakanin insfesta da iyayen Salis.Sha d'ayan dare, ya bar wajen ya koma gidan su Naseer, har sun kulle k'ofar gida, ya buga. Malam Balarabe ya bud'e, ya shigo ya kwashe kaf! Halin da ake ciki ya fad'i. Malam ya balbale shi da fad'a,"Me yasa ka ke wahalar da kanka akan wanda bai san ciwon kan sa ba? Shin ba cewa nayi ka tafi gida abinka ba? Yanzu k'arfe nawa ne?" 11 ta wuce, kai ma so ka ke ka 6ata wa naka iyayen rai ko? Ya karkad'a kai."To maza ka wuce gida, da safe kuma ka shirya ka tafi jarabawar ka, kar ka saurare shi! Maza sai da safe." Ya juya ya tafi, ran sa in yayi dubu toh ya 6aci. Abu 1 yake wa Naseer bak'in ciki, gobe ba zai samu zana jarabawa ba. Washe gari karfe 7:30 Zarah ke

Chapter 2 of 11