Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
Cike da faraa tace, "tun yaushe? Ai muna shigowa kaduna, ana sallar magrib. Zaki zo goben?" "Me zai hana? Allah ya kaimu goben lafiya." "To shike nan ki gaida momi." "Zataji". Sukayi sallama. Tana cire wayar daga kunnanta, kiran wata bakuwar lamba ta shigo. Tayi zuru tana kallon wayar a yayin da tuni zuciyar ta ta aiyana mata mai kiran wayar. Nan da nan gaban ta yayi mugun faduwa. Hannun ta ya hau rawa,bata sami motsawa ba sai da kira ya katse, sannan ta sauke numfashi. Bata gama numfashibba wayar ta sake daukar ruri. Hannunta bai daina rawa ba illa ma karawa da yayi a hakata danna OK, cikin kasala ta kanga wa kunnanta, murya sanyaye tace, "hello! Ya numfasa ya amsa, "baki da alkawari. Haka mukayi da ke? Ta numfasa, yasa ta zama mara gaskia a zahiri,don haka ta amsa laifin ta, "Ayi hakuri, ban .... Ya katseta."baki damu dani bako Nusaiba? Ni kuwa ko alama na kasa sukuni, gaba daya lissafi na a dagule yake. Nasan ba zaki gasgata ni ba. Amma zaki sha mamaki idan nace miki gani a kofar get din ku." Ai kuwa bata gasgata abin da taji ba don sai data mike zumbur tsaye tace, "kace me? Dan murmushi yayi jim, yadda ta firgita, "tsoro kikaji? Tace, "dan Allah da gask kakeyi? Yace "ai ba karya a son da nake miki. Kawai na kira babana don nace masa na iso sai ya cemin shima yna nan Abujan yazo wani (conference) na kwana biyu, shine yace in jira shi mu wuce kano tare. Ina zaune a masauki tunannk ya addabeni ban san lokacin dana bugo mota na taho ba, ki fito ina nan waje." Shiru tayi ta rasa meke mata dadi? A lokaci guda tausayin shi ya dirar mata a zuciya ya bi ko ina a jikinta. "Me zance da bawan Allahn nan? Ta tambayi knta. "Hello! Kina kan layi kuwa? A firgice ta dawo daga duniyar tunannta ta dan nisa tace, "gaskia Ibrahim da dai kayi hakuri zuwa gobe kadawo, a san abinyi." Gaba daya guiwar sa ta kwabe ya, rasa kuzarinsa. Murya raunane yace, "Nusaiba ba kya sona, ita kenn karshen maganar. Abinda na lura da shi kenan tun farko. Ko kuwa saboda nace miki ina da mata shiyasa kika zuzzu ke mun? Ba yaudarar ki nakeson yi ba ina gaya miki gaskia ce tsakani da Allah. Mata ta batayi min komai ba shekarun mu uku da aure. Kawai Allah ne ya jarabce ni da sonki. Tsananin so mai tada hankali. Nusaiba da kinsan halinda zuciya ta tashiga tun daga lokacin da kika bar ni a (Airport), ya zuwa yanzu da baki ce in dawo gobe ba. Pls ki tausaya min ki fito, in sake ganin kyakkyawar fuskar ki ko nasamu barci yau." Ba karamin dafa mata jiki kalamansa sukayi ba, kwalla fal idanuwanta, sai dai babu abinda ta iya yi, domin bata ma san wa zata dunfara ta nemi izinin sa ba. Kana dan siririn hawaye ya gangaro bisa kuncinta, kafin tace, "duk abinda kake nufi ba haka bne Ibrahim. Kaga dazu Abba yayi mun fada yanzu kuwa babu yadda zaayi insake zuwa ince masa gaka nan, ka sake biyo ni. Shi yasa nace ka hakura zuwa goben zan san yadda zan bullowa alamarin. Kaji? Don girmn Allah kayi hakuri. Ka nemo layin Antina nasan zata kwantar maka da hankali ka......... Ji tayi dim!din! Din alamun an kashe wayar. Da bayata fadi bisa filo, me zatayi? Ba kuka ba. Gaba daya lokaci guda taji Ibrahim na ratsa ko ina cikin jikinta, sabd tsabar tausayinsa. Rike hannayenta kawai taji anyi, gaban ta ya sake faduwa da jin muryar umminta, "ke! Nusaiba menene? Ta tarairayo ta, ta tashi zaune.Da sauri ta rungume Ummin." Na ce menene? Tayi shiru, don bata da abin cewa.hasali ma ba'ason ranta Ummi ta riske ta a wannan yanayin ba." Bebin Abba na ce menene?"Tana kudundune ta amsa, "Ba komai ummi." Ta ce,"Karya ki ke yi. Haka kawai ba za ki hau kuka ba, akwai dalili."ta dago mata fuska,"Dube ni nan." Tayi zuru, kwalla na diga." za6in Abbanki ne, ba kya so?"Da sauri ta kada kai,"A'a Ummi. Allah ba haka bane. Ta ce,"Nusaiba, sanin kan ki ne Abbanki ba zai cutar da ke ba, haka kuma ba zai so ya ganki cikin irin wannan damuwar ba.idan kin san bakya son Yaron nan, to ki gaya min gaskiya, in rarrashi Abbanki ya hakura da wannan abu. Shi yana can daki, yana ta murna yana sa miki albarka, ke kina nan ki na ta koke? Bebi na, ke kadai gare mu, ba za mu so wani ciwo ya kama mana ke ba, har mu rasa ki. Menene gaskiyar magana?"ta goge hawaye, kalaman Umminta suka sanyaya zuciyarta. Ta dube ta ta ce,"Ummi wallahi duk abinda da na gaya wa Abba na, gaskiya ne." To menene dalilin kuka? Ta sunkuyar da kai kasa, ta warware mata labarin Ibrahim. Ummi tayi shiru, kafin ta nisa ta ce "Lallai Ibrahim abin tausayi ne, amma bai kamata ki kwanta ki na koke-koke ba, sai kiyi addu'a.Allah ya sanya masa hakuri."Ta ce,"Ni dai ko, Ummi ki gaya wa Abba na gobe, idan ya zo, ya kira shi, ya ba shi hakuri. Ya gaya masa ina da wani." Ko ba haka ba?"....... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-08 Posted by ANaM Dorayi on 08:10 AM, 09-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ .Ta shafa kanta ta ce,"Haka ne Bebina, to ki daina kuka. Naseer yaron kirki ne, don ya fito daga gidan mutunci. Sai ki ci gaba da addu'a.Allah ya tabbatar da alkhairi. Yadda ki ka faranta mana rai. Insha-Allahu ke ma za'a faranta miki. Allah yayi miki albarka."Amin Ummina." Ta ce, tana dubanta. Ummi tayi murmushi, ta dan kama ha6arta ta ce,"Ila gadan! Insha-Allahu. Inji Nusaiba fuska sake.Ma'ana ta ce,"Sai da safe." Ta amsa da "In Allah ya yarda." Ummi ta mike ta bar dakin, tana waigen 'yarta.Wata ajiyar zuciya tayi, ta koma da baya ta sake kwanciya. "Allah gani gare ka, ka za6a min wanda ya fi zama alkhairi." Idonta kuri, ta kasa barci.ko alamar sa ma bata ji.ji take kamar son Ibrahim yana neman ya rinjaye ta." Zakakan kalaman sa sun yi ta zuwa, suna dawo mata a rai, irin labaran daya rinka zuba mata a jirgi. Idan ta rufe ido, shi take gani. A karo na farko daya zauna kujerar da ke gefen ta, ya yi mata sallama." Assalamu- alaikum.............! Kawai ta kan tsinci bakin ta yana sake amsa sallamar, ba tare da sanin tana yi ba. Dare ya tsala, ta rasa me zuciya ta ke da Ibrahim? Don haka tayi wuf, ta mik'e ta nufi bayi, ta shiryo lafiyayyar alwala, ta fito ta nufi sallaya. Hijabinta da zani, ta daura ta dora hijabi, tayi niyyar nafila. Bayan ta kawo raka'a 2 masu kyau, sannan ta zauna ta dukufa addu'an Istahara. Sai da ta kammala, sannan ta sami nutsuwa cikin ranta. Ta sake mikewa ta kawo wutiri, kafin wani lkc ta soma jin barci. Nan bisa sallayar ta, barci mai nauyi ya dauke ta.... Tana ta tsala kuka, kofar wani tsalelen gida mai kyan gaske, ba za ta iya sanin tsawon lkcn da tayi tana zuba kukanta ba, mai tsuma zuciya da ban tausayi. Kafadar ta, ta ji an dafa, wata sansanyar murya ta kira sunan ta "Nusaiba!, Ta dago idanuwa jajur! Ta dubi mai kiranta. Naseer ne dafe da kafadar, suka zuba wa juna ido. Jim! Sannan ya ce,"Taso mu shiga ciki." Ba musu, ta mike, yana jaye da ita har bakin kofa. Ja tayi ta tsaya cak! Tare da shirin fizge hannun ta. Cikin sauri ya sake kamo ta,"Kar ki k'i shiga gidan ki Nusaiba, ki sa ni ke uwar 'ya'yana ce. Ba a son raina............." "Nusaiba! Ke Nusaiba, ki tashi asuba tayi...Cikin mafarkin muryar Umminta ke kwala mata kira. Firgigi! Ta tashi, hawaye ne sharkaf a fuskar ta, nan da nan ta kawo salati tare da share hawayen, sannan ta amsa kira." Na tashi Ummi."*****Allah Sarki*** Ta dafe goshi, jikinta tamkar an mata shegen duka, da kyar ta mike ta nufi bayi, ta fito da alwala, don sallatar asubah. Tana ta lazimi bisa gadon ta. Amma tunanin mafarkinta take yi. Menene musabbabin kukunta? Babu abinda ta kawa wa ranta, illa watak'ila Ibrahim ne zai zame mata k'arfen k'afa. Idan son shi ya hanata yi wa iyayenta biyayya, ai ya cutar da ita. Naseet dai ta gani kiri-kiri, amma ta kafe ta k'i shiga gidan sa. Nan da nan ta daga hannu sama." "Ya Allah na roke ka, kar ka kawo min ranar da zan yi musu da iyaye na. Allah ka musanya wannan kuka nawa, ya zama farin ciki a gare ni. Allah ka daidaita zuciya ta akan tsananin son za6in su Abba. Ya Allah ka amsa, don albarkar da ka yi wa Manzonka. Muhammad (S.A.W)." Haka ta koma ta kwanta, ranta cunkushe har wani 6arawon ya sake dauke ta. Kamar a mafarki ta ji rurin wayarta, ta bude ido cike da mamakin ba irin barcin daya dauke ta mai nauyi gaske. Ta dauko waya ta duba. Abban ta ne. Da sauri ta dauka." "Abba na!" Ya ce, "Duk gajiyar ce? To ki zo mana in gan ki, kafin na fita." " 'Yar kunya ce ta sata murmushi,"Yi hakuri Abba, gani nan." Ta diro da sauri, tayi bayi ta wanke baki da fuska. A gurguje ta sauya kaya, ta fice. Lokacin kafe 9 dai-dai. Da gudunta ta haye 6angaren Alhjn, ta tura kofa tare da sallama. Ya amsa yayin da take takowa cikin sauri tana fadin, "Kaifa asbahta ya Abba! Shima fara'a yake yi, har ya iso inda yake zaune. Ita ma zama tayi, ta yada kai bisa kafadarsa." Abba ina kwana?" Lafiya lau." Na ce duk gajiyar ce har karfe 9 ban ga Bebina ba?" Ta ce,"Barci ya sace ni." Ya ce,"Ummanki ta gaya min sak'onki, kar ki damu, zan kira shi ya zo yau, don in yi masa bayani kin ji? Sannan ina ganin ma tare za mu fita, mu je ki za6i irin motar da ki ke so. Akwai sabbabin shigowa kala-kala, sai kin darje Bebina." Bakinta har kunne, ta k'ara langwa6e masa,"Na gode Abba na." Amma in tamabaye ka mana Abbana?" Ya ce,"Me zai hana? Ta ce, "Shi Naseer wacce yake hawa? Ya ji dadin tambayar ta, domin kawari yana son ya rink'a jin zancen Naseer a bakinta." Ya ce,"Uhm........... A halin yanzu dai (Civic) yake hawa." Ta dube shi da sauri "Abba sirikin (Dabai Motors) ke hawan (Civic)? Dariya yake yi, kafin ya ce," Kina da gaskiya, da ni tunanina, sai zai fara angwaci, zan canza masa. Amma tunda haka ki ka ce, za'a bari ku je tare ku Za6i irin daya. Ya yi miki hakan?" Ta gyada kai, "Yayi Abba, mun gode." Tana shiru Hjy Zulaihat na shigowa da tiran kayan abinci Alhjn. Nusaiba ta mike da sauri ta amsa, ta kai bisa shimfidar da yake zama, don cin abinxin. Bayan ta gaida Ummi. Suka baje nan suka karya tare. Suna hira. Hjy Zulaihat bata bar dakin Abba ba, sai 10:30, ta koma dakin ta, don yin wanka." Tana shiga, wayar ta da ke ta faman ruri ta katse. Kai tsaye can ta nufa, ta dauka, ta duba (Missed call) 5, duk lamba 1, wacce Ibrahim ya kira jiya." Ya salam! Ta fadi ido rufe Da sauri ta kira." Allah ya ba ki hakuri, wayar ma ba za'a daga ba?" Murya sanyaye ta ce,"Wallahi ba ni a dakin, ina can wajen Abba na ne, ka hakuri, ka ji? Sanyi ya ji cikin ransa, ya ce,"Ya zan yi, so ya kama ni, ai sai yadda akai da ni. Za ki sami fitowa ko sai gobe?" Tace,"Maida wukar, gani nan fitowa." Tana jin saukan numfashin sa ya ce,"Don Allah kar ki dade, na k'osa." Ta aje waya, ta nemi wuri gefen gado, ta dan raba hankali tayi shiru, ba tare da ta fahimci dalilin shirun ta ba. Can ta nisa, ta mike a natse, ta gyara zaman mayafinta da kyau, ta baro daki ta koma wajen Abbanta." Suna nan tare da Ummi. Kai tsaye ta shaida masu Ibrahim ya dawo. Ya dube ta da sauri, ya ce,"Je ki ce ya shigo, ku same ni a falon baki." Ta juya ta fiti cikin hanzari. Zaune yake cikin mota (Camry), yayin da ta budo get ta fito. Suna hada ido, zuciyar sa ta hau bugawa, tamkar za ta tsaga kirjin sa. Cikin kuzarinsa ya fito, baki har kunne. Da sallama ta karaso gunsa. Ya amsa." Sannu da zuwa." "Ke ma sannu da fitowa. Ya mutan gida? Ya jin dadin ki? Tayi d'an murmushi,"Duk suna lafiya, amma jin dad'i, ai ku ke da shi." Kallon ta kawai yake yi, zuciyar sa kamar anyi masa albishir da aljanna. Wani kayatacen murmusji yayi, kafin ya ce,"Wane jin dadi zan yi, bayan har yanzu ban kama dahir ba? Jiya zuciyata kamar za ta k'one, sbd tsabar rashin ganin ki. Me yasa za ki min haka?, So na ne ba kya yi ko? Ta dan yi shiru jim. Sannan ta ce,"Ba haka ba ne, amma yanzu mu shiga ciki. Abba ya ce yana son ganin ka." Ya fadada fara'arsa cike da jin dadi ya ce, "Rana kawai za'a sa mana, mu je in ga Abban." Yana kulle mota, jikinsa har rawa yake yi, haka ta sa ma sa ido, tausayin sa zalla cikin ranta." Ta wuce, ya biyo bayan ta, tayi masa jagora zuwa falon baki. Falon ya shiryu, iya shiryuwa. Shi kan sa masaukin ya kayatar da shi. Ta nuna masa kujera, ya zauna, kafin ta ce, " Miniti 2." Ya ce,"1 na ba ki." Ta wuce tana dan murmushi. Jimawa kadan, ta dawo dauke da tire cike da ingantattun abincin karin safe, ta dire a gaban sa, ta ce,"Abba ya ce," Ka yi (Break-fast), ga shi nan zuwa ku gaisa."Ya ce,"To, na gode kin kuwa san rabo na da abinci?, Ta dan dube shi yayi da take harjada masa abubuwan cikin filet, ta dan kada kai,"Tun wanda na dan ci jiya a jirgi." Ido waje ta ce,"Kai haba, me yasa? Ya ce,"Tunaninki kawai, sannan abinda ki kai min jiya, ko alama bai min dadi ba. Shima ya taimaka wajen hana ni cin abincin dare. Ina son ki Nusaiba, so mai ban mamaki, domin ni ban ta6a zaton zan so wata 'ya mace, kamar yadda na so mata ta ba. Sai ga shi tashi guda, kin rikita ni Nusaiba, har ina neman zarewa. Allah yasa yadda ki ke zuba min abincin nan, ki zabu min shi a cikin gidana." Ba ta ce komai ba, domin kalaman Ibrahim nema suke su kidima ta. Kai Nusyy mene abin kidimawa a wannan kalaman! Nima idan nadage zan iyasu... Koya kukace? Aje masa tayi a gaban sa, ta mike a hankali ta ce,"Don Allah ka ci da yawa, bari inje in dawo. Don me?" Please! Ki zauna, kan dole ta zauna, saboda a gaskiya bata son yadda Ibrahim ke cusa mata ra'ayin sa, tana tsoron kar a wayi gari ta kama da tsananin son sa, wanda zai iya wahalar da ita, kafin ta manta da shi. Tsit! Tayi a zaune, ba eh, balle a'a. Shi yake ta ba cikin sa abinci, wani lkcn ya kan yi santi da gangan, don tayi dariya, amma ina! Sai dai tayi murmusji, ta kauda kai, Bayan ya kammala, ta tattara kayan, ta dauka, yana fadin "Ki cewa Mama na gode da (Break- fast) Ta dan juyo, ta dube shi ta ce, "Zan fadi." Ta sa kai ta fice. Shiru yayi, yana mamakin kansa, domin shi abinci, idan ba na matar sa ba, duk gaibu ne. Ba wani sakin jiki ya ci shi yadda yakamata.Yayi kasake yana tunanin tsiyar da Ummansa take masa." Da kafin kayi auran. Abincin wa ka ke ci?" Uban 'yan gulma! Kada kai yai, yana wani bazawarin murmushi. Hannun sa daya yana shafar cikin sa har da wata gajeruwar gyatsa.Sallamar daya tsinkayo ce, ta sa ya dai-daita sahun sa. Yana amsawa, yana ganin Alhj yayi sauri ya mike tsaye, yana masa sannu cike da girmamawa." "Zauna mana." Inji Alhjin. Sannan ya zauna, suka ci gaba da ganawa.".... Nusaiba tare da Umminta suke hira a babban falo. Bayan wucewar minti 20,. Alh. Basheer ya dawo, ya cewa Nusaiba,"Ki je ki sallame shi, mun gama magana." Ta mike ta nufi falon baki, ilahirin jikinta a mace yake, sbd tsabar tausayin Ibrahim. Koda ta iso bakin kofar, haka ta tsaya kusan minti 3, kafin ta tura kofar ta shiga. Bai iya amsawa ba, kan sa a saye cikin guiwa. Zuciyar ta, ta k'ara raunana. Suka zauna shiru tsawon lkc, kafin tayi karfin hali, ta katse shirun." "Ibrahmin don girman Allah, ka yi hakuri kaji, mu yi addu'ar Allah ya sa hakan shine ma fi alkhairi a gare mu." Ya dago ya dube ta, ido jajur! Ya ce," Na yi Nusaiba, ni zan koma." Nan da nan idanunwanta suka kawo kwalla, murya raunane ta ce,"Bana so in yaudare ka ne Ibrahim shi yasa, don Allah kar ka dauki wannan abu da wata fuska." Ya kada kai, ya ce,"Hakan ya na da kyau Nusaiba, babu 6oye-6oye ko rufa-rufa. Abba yayi min kalamai ma su dadi da kwantar da hankali, sai dai kin san abinda rai ke so, bai ta6a samun nutsuwa lkc guda, muddin zuciya bata sami abinda take bukata ba. Na san zan shiga wani hali Nusaiba. Domin son ki ya riga ya shige ko'ina a jiki na." Ka barwa Allah komai." Ya ce,"Na bari kuma ina taya duk wanda ya same ki murna, saboda ba k'aramar sa'a yayi ba. Amma zan so ace ki dan yi (Saving) lamba ta, mu rink'a gaisawa, kafin auran ki ya tabbata. Zan sami wannan taimakon?" zan yi (Saving), amma da sharadin gaisawa kawai." Da k'yar ya mik'e tsaye, ya sanya mata ido,"To na gode............... Ya ci gaba da kallon ta, fuskar dauke da 6acin rai a bayyane. Shi yasa ita ma ta kasa kallon sa. Kamar zai sake cwa wani abu, sai kuma ya kasa. Ya juya da suri ya fice daga falon. Ya dan jima da fita. Nusaiba na zaune tana ta sharar kwalla, kafin ta samu hawayen suka tsaya. Ta mike cikin hanzari, ta bi shi. A zatonta ma ba za ta same shi ba, amma tana tura kofa, ta gan shi zaune da hankicin yana share fuska. Kirjin ta ya ci gaba da har6awa, ta tsaya jikin kofa ta ce,"Allah ya kiyaye hanya, idan ka yi waya da Madam, ka ce ina gaisheta." Can k'asan mak'oshin sa ya amsa,"Za ta ji." Tare da sawa mota makulli, ya bata wuta, bai saurari komai ba, ya bar wajen. Nusaiba na tsaye sai da ya 6ace ta dawo cikin hanzari. Babu kowa a falon k'asan, don haka ta nufi 6angarenta. Kai tsaye shirin wanka tayi, dan lkcn kankani, ta kammala wankanta, ta tsala kwalliya da a tamfarta mai kyawun gaske. Kwanciya tayi shiru, tana tunanin abubuwa masu yawa. Duk da dai bata son ranta ya na sako mata Ibrahim, sam ta kasa fidda tausayin a ranta. Ta lumshe ido ta dawo da hoton Naseer cikin zuciyar ta,"Me yasa na ke ta faman kuka, ban son shiga gidan ka? Ta kasa ba kanta amsa, saboda ba ta ma san me ranta ke nufi a game da Naseer ba.Ita bata kin sa, ita kuma bata wani zazzafan dokin sa take yi ba, duk da ta hakikance za6in Abbanta ingantace ne. Amma kwarai mafarkinta na rikita ta, shi yasa ta ke masa fassara kala-kala. Cikin duniyar tunanin ta ne, ta jiyo kwakwazon Kausar. "Ahalan-wa-sahalan! Larabawan Jordan! Tayi wuf ta diro daga gado, tayo waje, suna kicin tare da Ummi suna gaisawa, can ta nufa suka nufi juna suka rungume. Kausar na da surutu, ga zak'in murya tare da saurin magana. Suka dubi juna. Kausar ta juya kan Ummi,"Ummi wallahi yarinyar nan tana jin dadinta, wai mai karatu ce, ta dawo kamar fanke! Suna dariya, ta bata amsa,"A'a kin manta alkubus ne? Ta ce,"Ananandai, kin kalli madubi kuwa kin ga wadannan kumatun? Ta tamabyeta, tana ta6a mata kumatu. Ta doke hannunta tare da fadin, "Ban sani ba, masharranciya. Ni don Allah zo mu je, 'yar sa ido. Suka wuce rike da hannun juna. Ummi da dariya ta kada kai." Kausar kenan!" Daki suka fada, ta wurgar da jaka gefe, ta zube bisa gado. Ina can tunanin ki ya isheni cikin aji, wawan lakcaran nan, ya ki sallamar mu." Nusaiba ta zauna gefen ta, ta ce,"Ai ka ji halin Dan-Adam. Yanzu da bai zo ba, sai ace ya ki zuwa, don rashin kishin kai." To kuma sai ya shiga lokacin mu?" Ke manta, don Allah ina tsaraba ta tukuna? Dan murmushi tayi, "Ni in gaya miki tun jiya da na jefar da jakar ko ta kanta ban sake bi ba. Ita ce can?" Ta fadi tana nunuwa. Mikewa ta yi ta tanyo ta," Ina fatan kin kawo min turarukan nan?" Bude dai ki gani." Ta wurgo mata dan makulli. Tasa ta bude dan kankanin kwadon da ke makale jikin zif din. Ta wangame Jakar. Su 2 suke fiddo kaya kala- kala na sawa, turaruka , mai iri-iri, a goguna da dukkan kayan kyale-kyalen mata. Kausar ta darji na darza, ta maida jakar ta. Bayan sun kammala da tsaraba. Nusaiba ta kira Mariya 'yar yarinyar da ke masu aiki, ta kawo wa Kausar abubuwan kusa da ba ka za6in ta. Da kofi jus a hannun ta, ta dubi Nusaiba ta ce, "Bebin Abba kenan, to yanzu kuma sai me? Ta dan ta6e baki, ta ce,"Sai me kuwa? Zama tare da Abba na, gani ga shi." Tayi 'yar dariya, ta aje kofi k'asa,"Magulmaciya, ai karyar korar samari, ta kare. Dole yarinya ta tsaida na aure, ko mu samu wani Sugar Daddy mu mik'a masa." Ta zungura kafadar ta,"Aniyar ki ta bi ki. Kin san ma me ke faruwa?" Sai kin feshe ni." Ta dan karkace kai, ta bata labarin Ibrahiim yadda suka hadu a jirgi. Ta kwa6e fuska ta ce, "Amma guy din yayi, sai dai ya dan kwafsa, tunda yana da mata. Ajinsa ya sauko." Ya sauko?" "Eh, mana, kin san fa ni duk harkar kishiya ba ni a ciki." Dariya ta bata,"Ke bakin kishinki zai hallaka ki, ina ruwanki da ita?" Ai ni duk inda ta fadi, sha ne, ni dai rokona Allah ya hada ni da na gari. Aje wannan maganar, da alama so ya kamaki." Eh, ya kamani, sai dai abin ba zai yiwu ba." Ta dan ware ido." Don me, bayan ki na sonsa? Matar ce jaraba?" Ta dan nisa ta ce,"Abba na ya za6a min miji." Mai-maita don Allah?" Na ki maimaitawa, kada Allah yasa ki ji." Na ji abin ne kamar a oldings days. Me yasa Abba yayi maki haka?" Ya ga shi ne ya fi dacewa da ni, kin kuma san Abba ba zai kai ni gidan wahala ba." Ta kada kai tare da yamutsa fuska,"Ni kuwa kin ga inda za'ayi daga dani kenan. Abar ni in darje, in za6i wanda ya kwanta min."ta zuba mata ido, kafin ta ce,"Kausar kenan. Kawata kaza kanki da motsi." Ta ce,"Allah ya isa, banza! Ta 6alla mata harara, ta juya tare da sakin wawan tsaki. Don na mutu a tausayinki, shine zaki wulakanta ni. Allah yasa mai duka ne, Abba bai sani ba, kullum yayi ta jibgarki, kamar 'yarsa."Ta sa dariya, ta sa hannu ta jayo ta, "Kawalli kenan. To huce, ki ji wani dan bayani...........Ta katse ta,"Ba wani bayani, kawai ki gaya wa Ummi ke ga wanda ki ke so. Kar fa ki manta, wanda ba ka so, ko kallon sa ba ka so yi balle aje ga biyayyar aure. Amma ke na ga alama za ki yi wasa da rayuwar ki." Ta ce,"Ba haka bane kuma zan so ki dan natsu ki fahimci abin da zan ce." Ina jin ki." Ta ce,"Na dade ina wani nazari akan auratayya a wannan zamanin. Ta yadda aka maida aure abin wasa ko kuma ince don wani jin dadin bukata, sa6anin ibada kamar yadda ya zo daga Manzon mu. A zamanin da can kamar yadda a kakanin mu suke ba mu labari, sai ranar da aka kai ki dakin miji, sannan za ki san wanda ki ka aura, haka shi ma mijin, a lkcn zai san ki. Amma abin mamaki sai ki ga sun zauna lafiya. Mutu ka raba. Da tafiya tayi tafiya, anyi karatun boko, wai an waye, sai aka ce wannan tsarin auran dole ne. Aka soke wannan tsari, aka ce abar kowa ya aure za6in sa. Sai ga shi a lkcn auran za6in abubuwan sun rikice. Aure ya zama wasa, an maida saki ba a bakin komai ba. Wallahi wani auran ko Shekara ba'ayi za'a fara sa, in sa. Wani lokacin ma ki tsince su a kotu. Shi yasa a nawa ra'ayin, ban ta'allaka soyayya zalla ba a cikin zama aure. Dole sai da addini, "Kyan asali, "Tarbiya. "Hakuri, "Juriya, da sanin me zai je, ya dawo? Wannan shine abubuwan da kakaninmu suka rinka dubawa wajen auratayya.Ina son ki sani,abinda babba ya hango. Yaro ko yahau rimi, bai zai gano shi ba. Ita kuwa zuciya a kodayaushe kyale-kyale tafi so, duk wanda ya biye mata kuma, karshen al'amarin ba zai yi kyau ba. Saboda haka Abba yayi dai-dai da yayi min zabi. Ubangiji Allah ya taya shi zabi. Abu na gaba da na ke so ki yi koyi da shi kawata, shine kar ki hakikance wa ran ki dukan abinda zuciyar ki ta bukata. A kodayaushe ki fi rinjaye bisa za6in Allah." Kausar ta numfasa ta ce,"In yi miki ta Indiya, Vah! Lak lak shukran, mere dost! Tana murmushi ta amsa, " Ki na nan da Indiyancin ki, na dai ji shukran godiya ce, wannan larabci aka sata. Na ce da kyau, godiya dubu-dubu kawata. Ai kin yi nasiha, na kuma gamsu Pyar ho gaya." oh ba za ki daina Indiyanci ba kenan, me ki ke nufi?" A sannu a sannu za'a so juna. Wai ma waye gayen da yayi sa'a haka? Ta ce," Ban san shi ba, hotonsa kawai na gani a dakin Abba, shi yake gaya min dan wasan Polon sa. Yaro ne mai hankalu kuma ya fita gidan mutunci... Comment dinku yana karamin Karin gwiwa, so keep it up Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-09 Posted by ANaM Dorayi on 04:39 PM, 09-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . Sunansa Naseer." Tayi fit, ta ce,"Naseer Jah-Jah!" Ke ba fa Yakubu Jah-Jah ba. Naseer aka ce ta ce, tun yaushe tutar Yakubu ya sauko, ai yanzu Naseer shi ke jah. Ki na nufin shi Abba ya za6a miki?" Ta zura mata ido,"Kin san shi ne?" Ta miko hannu,"Ke dai ban hannu tukuna."Ta bata suka tafa, jikin Nusaiba ya k'ara sanyi,"Don Allah san shi?" "Ba dole ba, ni da na ke bin Daddy kallo. Sai yanzu na k'ara yarda da maganar ki, komai babba ya hango. Yaro bai iya ganinsa ko ya hau abinda ya fi rimi tsawo. Naseer na shan yabo wajen kowa, sannan kowa na son sa. Lallai Abba ya san abinda ya dace da ke." Dan lumshe ido tayi, ta ce a hankali,"Masha- Allah." Sannan ta bude suna duban juna,"Kin ga abinda na ke ke gaya miki ko?" Yanzu me ya rage?" Kawai mu jira lokaci, biki mu guwangwaje, ranar ni kai na sai na hau doki. Shi kan sa Jah-Jan dole ya daga min kafa.Ta bata hannu suka tafa. Nusaiba ta ce,"Kin ga yanzu dole a nemo kayan aiki, ina littafan hausa? Ta ce,"Suna nan, amma fa na aje na Momin Zariya ban karan ta su yanzu." Don me?" Wasu maganganu tayi akan 'yan (Flashing) ya bata min rai, kai tsaye na buga waya na zagi banza." Inna-lillahi wa-inna-ilaihir-raji'un! Ki zage ta? Ta figo jakar ta tana fadin,"Bari ki gani, kullum yawo na ke da littafin, koda musu zai tashi in nuna shaida." Ta jawo shi, ta ta bude mata wajen, ta karanta. Tana gamawa ta dube ta. "Amma kuwa Kausar kin ba ni mmk. Yanzu ke saboda Allah ina hankali a cikin irin wannan (Flashing) Haka kawai ba sa ki aka yi ba, ki dauki waya ki hau (Flashing) sama da goma sha, har dan cajin mutum ya kare. Menene amfanin sa? Ke ko ni da ne ke kawar ki,

Chapter 8 of 11