Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 11
alama bai ji wani matsugunni da zai aje Nusaiba ba. Sallama tayi masu, tana dan murmushi, suka amsa ta ce. "Kuyi hakuri, ku na ta tsayuwa ko? Sannun ku da zuwa." Sageeer ya ce, "No, kar ki damu. Ai ba mu wani dade ba. To ya ki ke? Ta ce,"Lafiya lau. Ku k'araso ciki mana." Ta fadi tana duban Naseer ido cikin ido. Kwarjinin Naseer ya zarce na yadda ta ji, a ganin sa na farko a hoto, shi yasa tayi saurin kauda idonta. Bismillah! Ta wuce suka biyo bayanta zuwa babban falon gidan, wanda ba kowa ke shigar sa ba. Naseer da Sageer, sun ga launanin abubuwan rayuwar duniya cikin falon nan, kai ka rantse ba za'a ta6a barin duniyar ba. Bayan sun zauna, ta gaishe su cikin kunya da ladabi. Abin ya burge Sageer, yanayin yadda ya ga Nusaiba. A na shi gannin, bai ga wani abin ki ba. Shi kuwa Naseer ba dole bane ya so wannan yarinya, duk da tana ingattatun abubuwan bukata. Shi abin daya sani Zara yake so, ita ya za6a, ita kuma yake son ya aura ya zauna da ita iya rayuwarsu." Bayan sun kammala gaisawa, ta mike tana fadin,"Minti 2,." Sageer ya ce,"Mun baki." Ta fice tana fara'a. Suka kalli juna jim. Sageer ya fara murmushi. Naseer ya kauda kai. Nan da nan ya hadiye murmushinsa, ya gyara zama a kujera. Ya fara lissafin zuci. Da sallama ta sake shigowa, dauke da dogon tire fari, shake da kayan lashe- lashe da shaye-shaye.ta aje masu.ta zuba (Drinks)' kala-kala, ta koma ta aje gaban sa, "Ku sha ruwa." Sageer ya ja robar Swan, ya dauki kofi,"Mun gode Malama Nusaiba." Ta koma gefe ta zauna. Sageer ke ta magana." To, ga fa aboki na Naseer. Ni kuma suna na Sageer. Ya ki ka gan shi? Ya dan sadda kai kunshe da murmushi ta ce, "Dai-dai." Yace kin tabbata, yadda ki ka yi mana dai-dai, haka shi ma yayi miki? Ta gyada kai, tare da fadin "Na'am." A karkace Naseer ke kallon ta, tana amsawa, ya numfasa, kamar wanda zai fadi wani abin kirki. Duk da yana son yayi mata magana, amma rashin sanin abinda zai fadin, yasa shi yayi shiru, kamar ba shi ba. Saboda haka ya bar Sageer , yana yi masa tad'in. Ya ce,"Gaskiya mun gode da fatan Allah ya sanya albarka a cikin abinda za'a kulla. Sannan wani hanzari ba gudu ba. Abba yayi miki bayanin akwai uwargida ko? Ta ce, "Eh." Ya ce,"Ina fatan za ku hade kan ku kamar Ya da Kanwa. Zarah babu ruwan ta, kuma tana da hakuri da hankali. Koda aka gaya mata zai aureki, addu'a kawai tayi, tare da fatan samun hadin kan ku." Hankali kwance ta ce,"Insha Allahu babu matsala, domin shi shirin Ubangiji kullum alkhairi ne ga bayin sa, idan ka ga akasin hakan to laifin daga mu ne 'Yan-Adam. Saboda haka ni ma ina mana fatan alkhairi tare da fahintar juna." Sageer ya jinjina kai, ya ce,"Amin. Naseer ka ji, ko kuma in bari in ba ku wuri ku gaisa." Ya dan muskuta ya ce,"Ina jin ma idan ma za kayi zaman ka, babu damuwa, ai ni da kai ba bambanci. Duk abinda ka fadi tamkar ni ne na fade shi." Ya riga ya gano shi, don haka ya ce,"Haka ne, amma waka a bakin mai ita, ta fi dadi, ko Malama Nusaiba? Ta ce,"To ni me zan ce? Ya mike ya ce,"Bari dai na jira ka a mota. Malama a fito lafiya." Ta ce,"Kuwa ba ka zauna shiru kai kaidai a mota. Ta mike, "Zo mu je." Ta fice ya bubbuga kafadar Naseerr, sannan ya bi bayan ta. Wata kofa ta bude, sai ga su a wani matsaikaicin falo. Ta ce ya zauna ta kunna masa T.V. "Wane ( Channel) Ka ke so? Ya ce,"Bar min labarai, na gode." Ta fita, jimawa kadan suka dawo tare da Mariya, dauke da kayan abinci da na sha, ta aje masa." Duk ni kadai? Tayi murmushi," Duk kuma na ke son ka cinye." To na gode." Ta sa kai ta fita. Sageer yayi kishingide a kujera, ya cigaba da kallon sa. Tana sallama babban falon. Naseer na daukan waya, "Yaya B, ya aka yi ne? Ka na wane gari ne yanzu? Ya ce,"Tafiyar nan bata yuwu ba B. Sai dai mun hadu, ka ji labari. Ina ma Kaduna a halin yanzu....... Takaici yasa Naseer B, ya kashe wayar sa. Jin shiru. Shi yasa shi ma ya cire ta a kunnan sa. Ya gama 'yan latsen-latsen sa tsawon lokaci, kafin ya dubi inda Nusaiba ke zaune. Kanta a sunkuye yake, don haka ya ci gaba da hararar ta. Jikinta ya bata ana kallon ta, saboda haka ta dan dago ba zato suka hada ido. Yayi sauri ya janye na sa................... ______________________________ Masu karatu, yaya za ta kaya ne? Wace badakala za ta faru a wannan labari? Ga Naseer Ga Nusaiba, cikinsu wa zai ci gari? Na yi gaba a dangaraman jirginmu na (MAIZAR AIRLINE). Mue je zuwa, wai mahaukaci ya hau Kura. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11