Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 11
makaranta, ya riga ya tafi. Duk kadaici ya dame shi, ga yawan tunani, don haka ya kulle d'akin sa yayi wa filin sukuwa tsinke. Mutane 2 kawai ke cikin filin, can nesa da shi suna wasan kwallon Golf. Wata kujera mai zaman din-din-din ita ya samu ya zauna. Maganganu barkatai suka yi ta zuwa, suna wucewa cikin zuciyar sa, musamman wacce ta hanashi barci jiya. Rana ta fara yin zafi, ya zamana filin babu kowa cikin sa, sai Naseer da ke jingine da kujera ya d'aga fuska sama idauwan sa gaba 1 na rufe, kawai damuwa ta sanya shi kasancewa cikin wannan yanayin tsawon lkc, kafin ya fara tsinkar karar kofatan doki. A natse ya bude idanuwan sa. Ya juya ya dubi gefen da yake jin tafiyar dokin. Wani matashi ya hanga, ya sakar wa doki linzami, in ba ka yi, ba ni wuri, sukuwa yake yi, babu kama hannun yaro. Naseer ya saki ido, kaf hankalinsa ya koma ga mai sukuwa. Nan take damuwar sa ta kau daga zuciyar sa. Mai dokin nan shi kad'ai yake atisayen sa. Sai Naseer da ke masa kallon kauna da sha'awa."Zagaye karo na 3 kenan zai yi wa filin, wanna karon k'ure dokinsa matuk'a, babu 6ata lkc, doki yayi ta haniniya ya d'aga shi sama, yayi watsi da shi tamkar yadda aka shek'e dussa a matankad'i. A guje Naseer ya mik'e ya nufi inda matashin ke kwance shame-shame a sume. Ashe ba Naseer kad'ai ya ga wannan tashin hankali ba, har da wasu masu ababen hawa da ke tafiya bisa titi. Kasancewar filin yana gefen hanya ne. Nan da nan suka kawo masa d'auki, inda tuni Naseer ya fara ceto ran sa, ta hanyar rage masa wasu kayayyakin da ke jikinsa, kamar su hular kwanon da ke kan sa da sauran su. Daga nan aka shiga neman ko za'a samu wata sheda a jikinsa, wacce za ta bayyana ko shi wanene da insa ya fito. Cikin aljihun sa Naseer ya zak'ulo wayar hannunsa, don haka ya fara neman wace lamba zai kira. A dalilin bai san kan wayar ba, dannawa na farko da yayi, sai ga sunan Yakubu Jah-Jah ya baiyana watau(Dillied numbers) ya shiga, ma'ana Yakubu Jah-Jah, shine na k'arshen wanda matashin ya kira a wayar sa. Kai tsaye Naseer ya kira lambar. Babu jimawa kuwa ya d'auka,"Hello bros, ka same ni a gida kawai!" Naseer ya ce,"Bai mai wayar bane, dama mu na son mu shaida maka ne, ya fad'o daga doki, kuma yana cikin wani hali sbd haka ka hanzarta zuwa nan filin sukuwa." Cikin tashin hankali Jah-Jah ya amsa,"Subhanallah! Ga-ni nan zuwa Insha-Allahu! "Naseer ya dubi sauran jama'a, ya ce,"Na sami wani ya-ce yana zuwa yanzu, ina jin d'an-uwan sa ne." Yana rufe baki,wanda ya ruga neman ruwa, ya dawo da ledar (purewater), aka bud'a ana ta fesa masa. Amma har ya k'are saurayin bai farfad'o ba. Suna nan jugun-jugun! Cike da tausayin saurayin." 'Yan-uwan sa suka iso cikin wata mota k'irar (Honda Civic), nan da nan suka sa shi a mota, d'aya daga cikin s ya hau dokin yayi gaba da shi, jama'a kowa ya kama gaban sa, amma shi Naseer yana tare da su Jah-Jah da shi suka iso (Zaria Clinic) kuma da shi aka yi ta kai kawo har majiyacin ya sami natsuwa bisa gadon asibiti. Likita na duba shi.Yayi matuk'ar auna arziki, don babu karaya a jikinsa, sai 'yan raunuka da rashin farfad'owar sa. Sun d'an natsu hankalinsu kowa ya bar wa Allah al'amarin sa. Naseer ya matso kusa da Jah-Jah ya mik'o masa waya da wasu kudad'e kusan dubu hudu da d'ari biyar, ya ce,"Ga kayayyakin sa, ni na aje sbd sha'anin mutane, wani da zuciya 2 ya kan zo taimako." Yakubu yasa hannu, ya amsa tare da duban Naseer,"Gaskiya ne, kuma mun gode Allah ya saka da alkhairi. Ya sunan Malamin ne?" Ya ce,"Naseer suna na." Fuska cike da fara'a ya ce, "Ah! Ashe takwarar maras lafiya ne. Shi ma sunan sa kenan, kuma k'ani na ne, uwa d'aya uba d'aya." Ikon Allah, to Allah ya ba shi lafiya, ni zan k'arasa gida." Ya amsa da amin. Ya mik'a masa hannu, suka yi sallama. Sannan yayi sallama da kowa har da iyayen su Yakubun da ke wajen, ya tafi. Cike yake da al'ajabi tare da tausayin takwaran na sa. A lokaci 1 yana jin dad'in had'uwarsa da mutumin da yake burge shi a duniya, sbd wasan tseren polo, watau Yakubu Jah-Jah. Tuni ya mance da damuwar da ke ran sa, ya tsunduma tunanin yadda zai yi ya k'ulla zumunci da su Yakubu. Don shi ma ya sa mu ya kutsa cikin wasan polo, wanda ya jima cikin mafarkinsa. Yana tafe, yana addu'a Allah ya cika masa burin sa, idan akwai alkhairi, babu wanda bai ji lbrn abubuwan da suka wakana ba, iyayen sa, Sageer tare da Huril- aininsa Zarah. Haka yake kiranta(Huril-aini), watau sanyi idaniya. ************** Da yamma bayan sallar la'asar can ya nufa, ya tarar da takwaran nasa ya farfad'o, kuma Alhamdulillah, ya d'an murmure, yana amsa gaisuwa sosai. Yana isa. Yakubu ya gabatar da shi ga k'aninsa, domin tuni yake da lbrn irin gudumuwar da Naseer ya bayar. A nan ya kai magarib, suna ta hira da Yakubu Jah-Jah. Washe garei k'arfe 10, ya isa asibitin, bai iske kowa ba, sai takwaran sa Naseer. Bayan sun gaisa, ya tambaye shi jikin sa. Ya ce,"Ah jikin an gode Allah." Zauna mana." Ya ja kujera ya zauna, yana fad'in"Kai kad'ai ne? Ina yayan na mu?" Ya ce,"Ka san shi ya kwana, so ya koma gida, ya d'an huta, sai Mama, ta d'an zaga ne." Ya ce, "Ok.Sun d'an yi shiru, na 'yan dak'ik'a kafin Naseer da ke jingine da filo ya ce,"Ai na ji sauki, ni yau ma na so a sallame ni, amma yaya ya hana, wai in dai bari zuwa gobe a tabbatar da komai Normal." D'an murmushi yayi,"Gaskiya ne, gara dai ka d'an kwana biyun." Ya ce,"Wallahi sam na rasa dalilin da yasa hawan doki bai amshe ni ba, fad'owa ta ta 3 kenan fa." "Ah! Haba dai? To saboda me?" "Oho! Ni abin ma har ya fita min a rai ko dama yaya ke matsa min, wai yana son na gaje shi. Ni ina zan kai wannan wahalar?" Naseer ya kad'a kai cike da fara'a, "Ni kuma ka san wani abu! Bala'in son hawan dokin nan na ke yi. Tun ban da wayau na ke zuwa kallon sukuwa, ai na sha yin hannu da yayan na mu, ba dai zai gane bane." Ya ce,"Ka ce za ka zama mutumin yaya sosai, domin shi ido rufe yake neman masu sha'awar wasan polo." Zuciyar Naseer tayi fes! D'oki ya mamaye zuciyar sa. Ina yanzu Yakubu zai zo ya ce su tafi fili, ya koya masa sukuwa? Bai gama tunanin sa ba. Maman ta fito bayi. Naseer ya tsugunna ya gaida ta, ta amsa tana mai jin dad'i a ran ta. Kuma kwarai take yaba Naseer cikin zuciyar ta, tun jiya da ta fara ganin sa. Wannan A JININ SA YAKE! Farin jini ga kowa, duk inda ya kutsa. Allah yayi wa Naseer wannan kwarjinin. Da ita suka ci gaba da hira, babu zato sai kiran sallar azahar suka ji. "Wai har k'arfe 1 ta yi.,"Naseer ya duba agogonsa, ya fad'a. Ta ce,"Ai babu wai a ciki. Lokacin ne ya gangaro irin na k'arshen zamani komai a gurguje, shi yasa kafin D'an-Adam ya farga, ya cinye lkcn sa a duniya cike da dogon buri fal zuciyar sa, domin shi yana ganin kamar jiya aka haife shi. Mutane k'alilan suke gane kanana alamomin k'arshen duniya, suna ta tabbata a fili, har su kan yi k'ok'arin su gyara halayen su, su koma ga Ubangiji. Amma da yawa daga cikin mu. Yanzu ne suke bude sabon faifan cin duniya da tsinke, ta ko wacce hanya. Ubangiji ya shiryi zukatan mu ta yadda za mu gane cewar mun fa kusan zama abin tausayi. Kwarai mahaifiyar su Yakubu ta kashe jikin yaran, kowa numfashi ya sauke Naseer ya ce,"Allah yasa mu dace." Suka ce,"Amin." Ya mik'e ya ce,"Bari in yi sallah in koma gida." Shi ma dayan Naseer d'in, ya sakko yana fad'in,"Mu je ni ma in yi sallar." Suka fita tare, ita ma Mama alwalar ta shiga yi.A harabar asibitin suka had'u da Yakubu na fakin. Gun sa suka nufa suka yi masa barka da zuwa, sannan suka gaisa da matarsa da ke tare da shi. Shi ma masallacin ya bi su. Uwar gida kuma ta wuce cikin asibitin. Fitowar su masallaci, babu 6ata lkc k'anin Yakubu ya fesa masa lbrn hirar da su kayi da Naseer, baki har kunne ya jawo kafad'ar sa, ya ce,"Haka na ke so Naseer A. Daga yau na sanya maka Naseer A. Wannan kuma ya zama B, tunda ragon maza ne. Insha- Allahu wasan polo kamar ka iya shi. Zan koyar da kai sukuwa, idan har ka mai da hankalin ka kwarai, to kuwa zan ba ka mamaki. Yaushe ka ke son fara zuwa koya?" Wannan albishir ba k'aramin kid'ima Naseer yayi ba, ji yake tamkar an biya masa aikin hajji. Bakin sa ya k'i rufuwa,"Ai ni ko yanzu ka ce in zo mu je da gudu zan bi ka yaya, domin ni a rayuwa ta, ba ni da burin da ya wuce min in zama d'an wasan polo." Yakubu ya ce, "To yanzu yadda za'a yi, gobe idan Allah ya kai mu, aka sallami takwaranka, bayan sallar la'asar, sai mu had'u a fili. Har wannan kalalan ma sai ya hau ba kyale shi zan yi ba." Suna dariya Naseer B ya ce,"Kai yaya, tunda dai ka sami wani Naseer d'in, ba shi kenan ba. Sukuwar nan fa da zan iya da tuni ina Kaduna ana fafatawa da ni..............." "Shiru don Allah! Nan ka fi auki wajen maida zancen. Doki kuwa hawan shi ya zama dole yaro." Suka shiga yi amsa dariya, yadda suka ga ya marairece baya son hawan doki. ****************** Abin nema ya samu wajen Naseer, mafarkin sa ya tabbata gaskiya. Yau ga shi a filon sukuwa bisa doki ana koya masa sukuwa. Abin ya ba su Yukubu mamaki ganin yadda Naseer ke sakarwa doki linzami kamar ba hawan sa na farko ba kenan." Lallai za'a da Naseer," Haka Yakuba Jah-Jah ke fad' a zuciyar sa. Nan take ya dorawa Naseer kyakkyawan zato. Nan suka wuni filin sukuwa, sai gab da kiran magarib suka dawo. A daran ranar, suna tare da Sageer bisa hanyar su ta zuwa wajen Zarah. Sageer ke fad'in,"Gobe ne fa za mu fara zuwa shagon koyon d'inki." Naseer ya ce,"Taf, ai ni gobe tun safe Jah-Jah ya ce in fito, zai yi wuya zuwa na koyon d'inkin nan." Sageer ya dube shi,"Ka fasa kenan?"Ya ce,"Zan iya cewa hakan, don ka san da abin nema ya samu a guna." Amma kuwa bai kamata ka fasa ba, kuma a ganina sukuwa ba za ta hana ka koyon wata sana'ar hannu ba." Da wutsiyar ido ya kalle shi, ya ce,"Ita sukuwar ba sana'ar hannu bace? Idan na kware. Yakubu yayi min hanya manyan su. Allah ya taimake ni, a na haye." Ya ce,"Haka ne. Allah ya tabbatar da alkhairi. Ina ganin ma dai zan bar ka anan, bari in wuce shagon, in yi masa tuni, ina nan zuwa gobe." Sarai Naseer ya gane ya yi fushi ne, amma ya share, ya ce,"To, sai mun had'u." Take nan Sageer ya yanke hanya, shi kuwa Naseer ya mik'e zuwa gidan su Zarah. Zarah na ta wanke-wanke, yayin da Inna ke tankad'an garin tuwo. Sallamar Naseer suka amsa, ya shigo da fara'ar sa mai tattare da albishir cikin zuciyar sa. Sau guda Zarah ta kalle shi, ta maida kai bisa aikin ta. Innar ke fad'in,"Ah, d'an Inna." Ya k'araso gabn ta ya tsugunna,"Sannu Inna, ina yini?" Ta amsa tana duban sa, sannan ta tambayi mutun gida? Ya ce suna lafiya. Ta ce,"To yaya an je sukuwar?" Ya amsa,"Na je Inna, kuma Yakubu ya yaba da kamun ludayi na. Sai a taya ni da addu'a. Allah ya tabbatar da alkhairi." Ta ce,"Insha-Allahu za mu yi maka d'an Inna. Allah yasa ka na da rabo ciki. "Kullum yana jin dad'in kalaman Inna, kuma har da hakan ke k'ara masa soyayyar Zarah cikin ran sa. Ya amsa da,"Amin Inna." Sannan ya dubi inda Zarah ke aiki, kanta sunkuye yake, dad'e duniya bata san da shigowar sa ba, amma gaba daya hankalin ta ya taru ya koma inda Naseer ke tsugunne. Ya juya kan Inna ya ce,"Inna kin san wani abu! Zarah ta daina gaishe ni, ko sannu da zuwa bata min, ni ba yayan ta bane? Bata da kunya ko Inna?" Murmushi Innar ta yi kafin ta ce,"Wannan kuma ai tsakanin yaya da k'anwar sa ce, ni na shiga?" Ta sunkuci kwanon garin ta tayi kicin, ta bar Naseer nan yana kallon yadda Zarah ke kwad'o masa harara. Yana ganin Inna ta shige kicin, ya sunkuci kujera ya nufi gunta ya zauna. "Baki da kunya ko? Ni ki ke harara?" Ta aje kai k'asa, ta ce,"Na ji ka na min sharri ne, ni ce bn gaishe ka?"Ya ce,"Ai da, da zarar na shigo gidan nan, ke za ki fara tarba ta.Ni kuma abinda na fi so kenan kodayaushe in rink'a ganin fara'ar ki. Idanuwanki suna duba na. Da kin san irin farin cikin da ki ke sanya ni, da ba ki daina ba. To wai ma sbd me ki ka sauya?" Akaikace ta dube shi,"Ni ina zan sani, ni ma haka kawai na ji ba ni iyawa." Ya ce,,"Ni kuwa na san dalili, in fad'i?" Ta ce,"Fad'i mana." Ya dubi hanyar kicin. Inna ta raja'a bisa aikinta. Sannan ya duk'o k'asa-k'asa ya ce,"Saboda Baba ya ce ke mata ta ce, ko ba haka bane?" Bata dube shi ba, ta amsa,,"Yaushe Baban ya fad'i hakan? Ai ni bn da labari." Murmushi yayi ya d'an yarfa ruwan d'auraya, don ta zolaye shi, yayi jim, yana kallon yadda ruwan ke gangara bisa kyakkywan kuncin ta. Take nan zuciyar sa ta d'auki zugi, sbd tsabar son da yake wa Zarah. Jin yayi shiru yasa ta bude shi. Yanayin da yake zahiri ya nuna ya shagala, d'an murmushi ta yi, da gangan ta tsunduma kwanon da ta wanke cikin ruwan daurayar, ruwan ya fantsale har bisa fuskar sa. Yayi lallausan ajiyar zuciya, sannan ya lumshe ido, ya bud'e a natse yake fad'in." "Kin rama ne? Kamar ma ba ita ta aikata ba, ci gaba ta yi da aikin ta. Ya d'auraye kwanon ya kife mata shi."Ba ki ganni a doki ba yau." Ta ce,"Na gan ka mana." Ya k'ara duban ta, kamar yaya? Biyo ni ki ka yi?" Ta karkada kai," A raina na ke ta aiyana ka, ka tsere Yakubu Jah-Jah. JUMAT KAREEM Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-05 Posted by ANaM Dorayi on 11:18 AM, 06-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . ." Ya ce,"Wane ni, rufa ni ki saya." Ta ce,"Ai na san yayana ba shi da wasa, yau da gobe za'a kira ka Jah-Jah. Ta d'an dube shi,"Ko ba haka ba?" Yana murmushi ya amsa,,"Komai ya fito bakin ki alkhairi ne, Insha Allahu don haka nace haka d'in ne." Ta ce, "To Allah yayi yagora." Ya ce,"Amin." Ta jima da gama wanke-wanken yana yi mata d'auraya. Amma suka ci gaba da zama wajen suna hirar har gob da kiran magariba. Sannan ya sallami Inna ya koma gida. Sati 2 sun yi wa Naseer yawa, domin a cikin 'yan wad'annan kwanakin ya kasance sai Yakubu yayi da gaske yake tsere masa bisa doki.Ba k'aramin mamaki ya ba kowa ba, musamman Yakubu da k'anin sa Naseer B. Haka ya burge abokinsa Sageer da Zarah, ranar da suka ziyarce shi a filin sukuwar, don ganin yadda atisayen ke tafiya. Tabbas Naseer gwarzo ne kuma Allah yayi masa baiwa cikin jinin sa. Safiyar lahadin yau, ita ce ranar da Yakubu ya ajiye, don gabatar da Naseer ga uban gidansa a Kaduna, sbd sosai ya tabbatar da Naseer ba zai ba shi kunya ba. Tsaf! Naseer ya kammala shirinsa, ya fito cike da albarkar iyayensa. A k'ofar zaure suka had'u da Sageer tare suka gangaro har zuwa marabar da za ta kai Sageer shagon da yake koyon d'inki. A nan su kayi sallama Naseer ya wuce gidan su Zarah. Suka yi sallama da juna, don bai iya wucewa, ba tare daya salleme ta ba. Nan ma ya sami k'arin addu'a daga iyayen ta. Sannan kai tsaye d'an acaba ya aje shi k'ofar gidan Yakubu Jah-Jah da ke Tudun-Jukum. Babu 6ata lkc suka damki hanyar Kaduna, cikin motar Yakubu. A cikin tafiyar awa 1 kacal! Suka iso k'ofar katafaran garejin siyar da motoci wanda yake d'auke da sunan (DABAI MOTORS'! Cikin kallon tsoron da Naseer yayi wa garejin, yayi zaton akalla akwai sababbin motoci na gani, na fad'a sama da 200. Domin kuwa motoci ne fululu! Wannan na zagin wancan. Yakubu yayi masa jagora zuwa 6angaren ofishin wajen inda suka fara magana da sakataran sa, wanda a fili ya nuna sun jima da sabawa da Yakubu. Nan take ya sada su da ogan sa. Tare da sallama suka shiga k'aton ofishin daya amsa sunan ofis. Kyakkywan Alhajin wankan tarwada na zaune bisa lafiyyar kujerar sa. Sanyin A.C na ratsawa ta ko'ina cikin ofishin gwanin dad'i. Cikin fara'a da walwala ya amsa sallamar su, sannan ya ce,"Yakubu kun iso? Bismillah ku zauna mana." Kujera 2 da ke gabn d'in, su Yakubu ya jawo ya nuna wa Naseer ya ce ya zauna. Duk sun natsu a zaune. Shi dai Naseer haryan muzurai yake yi irin na bak'unta. Sun kwashi gaisuwa cikin girmamawa, haka shi ma Alhj ya amsa yadda yakamata. Daga nan Yakubu ya ce,"Alhaji wannan shine Naseer, ina fatan babu wata matsala." Yakubu ya amsa,"Insha Allahu ba na haufi a kan sa, sai dai ka gani da idon ka.'a Murmushi Alhj yayi, sannan ya ce ,"To shi kenan, ina son k'arfe 2 mu had'u a fili." Ya juya kan Naseer ya ci gaba,"Naseer, ka saki jikin ka, za mu had'u k'arfe 2 a fili, don ganin yadda ka ke gudanar da sukuwar ka. Ba wani abu. Sai mun had'u d'in ko?" Ya ce,"Shi kenan Alhj. Na gode." No problem." Alhj ya fad'i yana jawo dirowar gaban sa. Makullai ya d'auko, ya mik'awa Yakubu,"Don Allah ka tabbatar da su Musa sun dawo da dawakan nan guda 3 akan lkc. Kuma a ba su abinci a kyale su su huta." Ya ce,"To Alhj. Muna iya tafiya ko?" Ya ce, "Yes, ai ina ganin babu wani abu, idan ma akwai. I will call you." Ya amsa da, "O.K Sir." Suka mik'e suna fad'in,"Mun bar ka lafiya," Sun kai k'ofa. Alhaji ya sake kira, "Naseer!" Ya juyo da sauri tare da amsawa. Ya ce,"Kar fa ka ji komai, cikin ranka, tunda Yakubu ya yarda da kai, ni ma na amince da kai. Kawai gwaji ne, don in gani da ido na." Naseer yayi murmushi, kafin ya ce,"Babu komai Alhj. Ai gwaji dole ne a ko'ina haka k'a'idar take na gode kwarai." Shi ma Alhj murmushin yake yi, yana duban Naseer, sannan ya ce,"K'arfe 2 insha Allahu." Yakubu ya janyo kafad'ar Naseer yana fad'in,"Allah ya kai mu lafiya." A haka suka bar ofishin. Cikin mota bisa hanyar su ta zuwa bargar dawakin Alhj. Naseer cike yake da farin ciki tare da doki cikin zuciyarsa. Kwarai ya k'osa karfe 2 tayi su hadu da Alhj a filin sukuwa. Yakubu ya dube shi ya ce,"Ka ga oganmu ko?" Ya amsa,"Kwarai na gan shi, da gani kuma Alhj zai yi saukin kai." Ya ce,"Kwarai kuwa. Alhj Basheer Rufa'i Dabai kenan. Wanda ya gaji d'umbin arziki daga mahaifinsa Alhj. Rufa'i Dabai. Su 2 ne shi da kanwar sa, ita tana Jordan tare da mijin ta. Yayi aiyukan gwamnati da dama. Daga baya ne ya aje, ya ci gaba harkokinsa na kasuwan cin da ya gada. Bayan wannan garejin motocin, yana da wani a Mando, wanda ake siyar da manyan motoci zalla. Yayi k'arfi sosai a harkar polo, dan kusan zan iya ce maka duk Arewa babu club din da ya kai na sa ingattatun dawakan polo. In dai ana maganar polo, idan aka ce maka (DABAI RIDERS), to anyi maka kankat! A gaskiya na ci gajiyar Polo kuma babu abinda zan cewa Alhj. Sai Allah ya saka masa da alkhairi. Shi ya kai ni Makka, yayi min aure, ya ba ni gida. Sau 3 yana can zamin mota. Da zarar ya ga ta tsufa, ta soma ba ni matsala, zai sa aban wata. Saboda haka na ke son ka kwantar da hankalinka, ka natsu ka nunawa Alhj Jarantakarka. Insha Allah wata rana za kayi dariya. Naseer ya cire tagumin daya zabga, ya sauke numfashi, kafin ya ce,"Lallai yayaka mori Polo. Allah yasa muna da rabo muma. Kuma yarda Allah ba zan ba ka kunya ba." Yayi yar dariya ya ce,"Ai na sani kai ne Naseer Jah- Jah." Ya ce,"Me ake nufi da Jah-Jah?" Alhj. Ya soma lak'aba min. Da zarar na hau d'oki, shi kuma ya shiga yi min kirari kenan, Jah! Jah!! Mu je Yakubu! Ina jin dad'in kirarin Alhj, Sannu a hankali sunana ya zamana ba'a kiran sa zalla, sai an lak'aba Jah- Jah." Ya ce,"Gaskiya ne, ba kai kad'ai ba, ni kaina kirarin yayi min, tun ina yaro k'arami na ke begen sunan." Dariya Yakubu yayi. Shi kuwa Naseer tambaya yake," yayansa ba sa yin Polon?" Ya amsa, "Ai 'yar sa guda 1 ce a duniya, tana ma can Jordan tare da k'anwarsa can take karatu. Kawai tausayin Alhj ya ji ya kama shi. Shi yasa ya ce," Allah Sarki, yanzun duk dukiyar nan 'yarsa 1? Allah ke nan." Ya ce,"Wallahi kuw. Oh, har ta shiga jama'i. Nusaiba sunan ta, ni na ke kiran ta Baby N. Tana ce min Jah-Jah, kamar ita ta rad'a min sunan. Gaskiya yarinyar na da tarbiya ga ilimi. Shekarunta 15 ta sauke Kur'ani, ga sanin harshen larabci ko yanzu ma abinda take karantawa kenan a can Jordan din "Arabic and Islamic Studies)." Naseer ya nisa, ya ce,"Amma ya kyauta daya banbanta da wasu masu kudin ko kuma in ce wasu 'yan boko ma sun maida kan su tamkar Yahudawa, saboda takamar abin duniya." Ya ce,"Ai Allah ya taimake shi,"Ubangiji ya k'ara shirya mana zuri'a." Naseer ya amsa da Amin." Ba k'aramin mmk Naseer ya sha ba bargar dawakin Alhj Basheer, domin dakawai 12 ke harbin iska, sun kai sun kawo a girma da koshin lafiya. Ya kubu ya zaga da shi ko'ina tare da gabatar da shi ga jama'ar da suka iske a wajen. Daga bisani Yakubu ya bude wani k'aton falo mai kunshe da kayan alatu, kuma da gani an tanade shi ne, don hutawa da gudanar da taro. Anan suka zauna. Yakubu ya ci gaba da gudanar da aiyukkan sa, kamar yadda Alhj ya umurce shi, ko kuma ana iya cewa ya saba yi a kodayaushe. K'arfe 2 bayan salar azahar. Su Naseer na filin sukuwa, ba jimawa Alhj Basheer ya iso cikin tsaddadiyar Jeep din sa. Bayan sun kwashi gaisuwa, sai suka rankaya wajen da wasu yara ke rike da dawakai guda 2. Naseer ya hau 1. Alhj ya ce Musa daya daga cikin yaran sa ne, shi ma ya hau 1. Suka dai-daita sahu, kafin Yakubu ya hura usur, watau ya ba su umurni tashi. Alhj Basheer ya sha mmk, domin Naseer yayi wa dokin Musa Fintak'au! Wanda shi ma Musan yana 1 daga cikin wanda suke taka rawar gani a (DABAI RIDERS). Alhj ya dubi Yakubu, ya ce,"Za'a da Naseer, gaskiya shi ma yana Jah. Kuma kawai yaron ya shige min rai, tunda ku ka tafi, na ke ta tunanin sa." Yakubu yayi murmushi, ya ce,"Haka ne,"Naseer na da hazak'a ba k'aramin mmk zai bayar ba, nan gaba, idan ya k'ara gogewa." Yana rufe baki. Dokin Naseer na isowa. Ya ja ya tsaya gaban su Alhj. Alhj da kan sa ya rik'e masa, ya sauka,"Good! Sukuwa tayi yadda ake so Naseer. Saura mutum 1 na ke so ku kara. Ina Dogara? Yakubu kira shi ya hau doki." Kowa ya san Dogara, shi yake rufa wa Yakubu baya, kuma shine na 2 cikin wadanda Alhj Basheer ke ji da su ko'ina." Amma ko alama gaban Yakubu bai fad'i ba, da kiran Dogara. Domin yana da yakinin Naseer zai iya karawa da shi kan sa Yakubu." Don haka kai tsaye ya kwala wa Dogara kira. Daga gefen da suke tsaye. Ya baro sauran, ya iso gun su Alhj. Alhj ya ce ya hau dokin da Musa ya sauka. Cikin ji da kan sa ya kama doki ya d'are, kamar yadda Naseer yake tsaf! Bisa na sa. Suka ja sahu. Yakubu ya bada umurnin tashi. Kowa ya baza wuta, suka sakar wa dawakai linzami. Me zai faru? Kafin wani lkc Naseer ya 6ace 6at! Sai k'ura. Duk Jama'ar wajen shewa suke yi. Alhj kuwa rungume hannayensa yayi ya kasa cewa komai, amma cikin zuciyar sa ba karamin alfahari yake yi ba da samun Naseer. Musamman ganin Yakubu ya fara manyanta, yana buk'atar hutu nan d'an lkc k'ank'ani. Bai gama tunanin dogon burin da ya d'ora akan Naseer ba, Naseer din ya iso cikin sassarrafa ya diro. Yakubu ya rungume shi. Duk Jama'ar wajen suka yayyame shi ka dauka gasa ce ake yi.Alhj. Ya kamo kafad'un sa, ya juyo sosai ya dube shi, bakin sa har kunne. Alhj ya mik'a masa hannu, suka yi musabaha, sannan ya ce,"Welcome to DABAI RIDERS.Daga yau ka zama Naseer Jah- Jah." Dai-dai lkcn da Dogara ke k'arasowa wajen, gaba d'aya jikinsa babu kwari kamar an zare masa laka. Duk 'yan wasan da ke wajen sai hannu suke ba Naseer suna taya shi murna don haka shi ma Dogara yi mika masa ya ce,"Congrats." "Na gode." Inji Naseer yayin da shi tuni Dogara ya bar wajen dauke da wata irin hassada cikin zuciyar sa. To ai dama haka D'an-adam yake, tara ne bai cika goma ba. Duk inda ka kai ga dumbin masoya, dole ne ka sami wanda a rayuwa ba ka yi masa ba. Wani lkcn kuma zai iya zama hassada. Muna iya cewa zuciyar Dogara ta shiga wani garari na musamman take yanzu akan Naseer, ganin yadda Alhj yayi maraba da shi, domin burin sa duk lkcn da Yakubu ya zama tarihi a (DABAI RIDERS), to shine zai maye gurbinsa. Sai ga shi da rana tsaka wani ya zo daga sama kuma take yanke Alhj ya kira shi da Jah-Jah. Suna mai tsada da muhimmanci a gun Alhj Basheer. Lallai Naseer yayi wa Dogara shigar sauri a bisa dukkan alamu kuma ya zama kishiryarsa, sai dai ce Allah ya tsare sharrin shaid'an. Ba kankanin farin ciki Naseer yake ciki ba, a tarihi rayuwar sa kaf! Yana jin ba shi da wata rana da ta fiye masa ta yau. Don haka ne ma yake ganin ba shi da wata kalma wacce zai yi wa Yakubu godiya da ita, balle Ubangiji daya nufe shi, ga kai wa wannan matsayi da ke cikin ran sa, ga cimma wannan matsayi da ke cikin ran sa tun yana yaro karami. Saboda haka ya kara kaimi fiye da ko wace rana, don ganin ya ba maras da kunya. ******************* Kafin shekara 1 Naseer ya wuce duk inda tunanin mai karatu zai kai a duniyar wasan polo. A kowane lungu gabas da yamma kudu da arewacin Nijeriya. Dole ne ka ji sunan Naseer Jah-Jah a bakin masoyan wasan tseren polo. Wannan ba karami matsayi ya samawar Naseer ba a cikin zuciyar Alhj Basheer. Wanda ta kai ga akan dole Dogara ya sakar wa Naseer ragamar (DABAI RIDERS), ya tattara kayan sa ya canza sheka, don ba zai iya ganin irin gatan da riritawar da Alhj Basheer yake wa Naseer ba.Ana iya cewa ko Yakubu bai sami irinta ba. Domin ko kafin Naseer ya hade watanni 6 a wasan Polo. Alhj Basheer da kan sa ya

Chapter 5 of 11