Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 11
da kishi, ga mari ga tsinka jaka. Kin fa san mu maza mun fi ku zafin kishi, illa iyaka na mata ne ya fi bayyana. Dole Salis ya rasa na yi, tunda kin ce ba ki tare da shi. Yayan ki, ki ka fi so ko?" Ta saci kallon sa tana d'an murmushi ta ce,"Kai wanne ka ke ra'ayi?" Yayin da wata bus ta tsaya gaban su. Ya ce,"fad'a 6ata baki. Shiga mota kawai mu isa gida." Suka shige cikin mota, ta sauke su inda suke son sauka. Sageer ya biya kudi. *************** Washe gari Sageer na tare da Naseer a gidan yari, kuma ya samu nasarar ganin sa. Zaune suke suna nemar wa juna mafita.Gaba d'aya hankalin Naseer a tashe yake kuma ya fi karkata ga k'aunar jefa Sageer cikin maganar da babu hannun sa a ciki. Saboda haka ya dage yana fad'in,"Koda wasa Sageer kar ka kuskuara ka amince da laifin da ake so a k'aga ma. Don na lura Lauyan nan, shegen kan sa ne. Saboda haka ka lura da laffuzan da za su fito bakin sa. Sannan ka ba shi amsa." Ya ce,"Ni ma d'in kai na fi ji Naseer, na san ka ba ka da tsoro, don girman Allah kar ka fad'i abinda zai 6ata ran Alkali, a zo kuma abubuwan su k'ara rikicewa."D'an murmushi yayi." Ai taka tsan-tsan na ke yi, sbd ba na son Zarah ta dauwama a kuka, ba don haka ba, da tun shekaranjiya na amsa da wukar na je, ka ga Alkali ya huta, take a nan zai yanke hukunci." Naseer kenan, to Allah dai ya fida mu lafiya. Bari in lalla6a gida, me zan cewa mutuniyar?" Ya ce,"Ka gaya mata idan har ta san tana sona, to ta daina min kuka, lafiya lau na ke, damuwa ta 1 ce, yanayin da take na rashin kwanciyar hankali. Muddin kuwa ta natsu, ta maida hankalin ta a makaranta, shakka babu, ni ma zan sami nutsuwa.." Suka mike yana fad'in,"Zan isar da sak'on insha- Allahu. Sai mun had'u a kotu." Ya wuce Sageer na tsaye na kallon sa. Gandiroba ya bi bayan sa. Kafin ya fice, ya juyo suka had'a ido,"Ka gaya mata ta ci gaba da lissafin kud'in (Break) d'in ta Insha Allahu da na fito, zan biya su." Murmushi Sageer yayi ya ce,"Zan fad'i." Yasa kai ya fice, tare da ,mai tsaron sa. Sageer ya sauke numfashi cike da tausayin abokinsa, sannan ya fito yana fad'in cikin ran sa, "Da yardar Allah sai ka bar gidan nan." 27 ga wata kotu ta cika mak'il! Kasancewar litinin ce masomar aiki, ko nasara na tsoronki. Ci gaba da shari'ar su Naseer aka fara saurara. Gaba d'aya kowa ya hallara har da shedun da lauyan Salis ya ce zai gabatar. Ba wasu bane, illa abokan Salis da aka yi abin akan idanuwan su, amma maimakon su fad'in gaskiyar lamarin, sai suka goya wa k'arya baya, suka tabbatar wa Alkali tabbas Naseer ya sumar da Salis, sannan yayi k'ok'arin da6a masa shar6e6iyar wuk'a. Bayan Alkali ya gama sauraron shedun lauya, kai tsaye yasa aka shigo masa da Sageer cikin akurkin kotu. Bayan yayi rantsuwar zai fad'i gaskiyar abinda ya sani. Alkali ya tambaye shi, Me ka sani a game da fad'an Naseer da Salis?" Ya gyara tsayuwa, ya fed'e bayani kamar yadda ya faru. Alkali ya ce,"To ina wukar da ka tsare da ita?" Ya kad'a kai, fuska yamutse ya amsa,"Naseer bai je da wuk'a wajen ba, balle har in gudu da ita. Hasali ma, Naseer bai ta6a yawo da makami ba." Yana sa aya. Lauya ya mik'e, "My Lord! Ina da 'yan tambayoyi ga Sageer." Na take ya sami izini." Gaban Sageer ya tsaya suka kare wa juna kallo, kafin ya ce,"Hujja 1 na ke so ka gaya min, menene dalilin gudan ka, ka bar k'ofar gidan su Salis?" Sageer ya amsa,"Gidan iyayen Naseer na je, don sanar masu halin da ake ciki." To da ka garzaya ka sanar wa iyayen na sa, sun zo wajen?" Yayi shiru, na 'yan dak'ik'ai, sannan ya kad'a kai,"Ba su zo ba." Me yasa?" Lauyan ya tambaya cikin sauri. Gaban Sageer ya ci gaba da fad'owa, kamar ma ba zai ce komai ba, saboda tsawon shirun sa, ya nisa a natse ya ce,"Cewa suka yi babu ruwan su." Lauyan ya gyara tsayuwa ya ce,"Ah! Naseer ba d'an su bane? Don me za su ce ba ruwan su? Nan kam Sageer ya kasa amsa wannan tambayar, ya aje kai k'asa, idawuwan sa suka cika da k'walla. Barista ya dai-daita zaman kot dinsa, ya dubi mai shar'ia ya ce, "My Lord! Bayanan Sageer sun nuna a fili ko a gidan su Naseer ya ishe su, sun kuma tabbatar da zai aikata abinda ake tuhumar sa da gasganta min binciken da na yi cewar har kwana 2 yau, babu mahaifin Naseer a cikin kotun nan. Ya mai girma shari'a. Iyayen Naseer ma sun tabbar da d'an su zai aikata laifin,My lord, banda wannan ya dade yana dauko wa mahaifin sa magana, wanda shine babban dalilin da yasa ya tsame hannunsa akan d'an sa. Bincike ya nuna ko cikin makaranta Naseer bai da biyayya, domin har makaranta ta ta6a korar sa na sati 2. My Lord! Ga shedu na na ga hujjoji na na, ga kuma k'wafin shedar koran Naseer daga makaranta na sati 2. A tunani na sun isa su tabbatar da cewa Naseer shaharrare ne wajen aikata laifuka iri-iri. Saboda haka ina rok'on wannan kotu mai adalci da ta duba ta fidda wa Salis hakkinsa, na neman kashe shi da Naseer yake shirin yi. Na gode."Ya mik'a takarda. Aka mik'awa Alkali.Sannan ya koma mazauninsa ya zauna. Kotu ta yi tsit! Yayin da Alkali ke duba takarda. Can 6angaran 'yan kallo inda su Malama Lawal da M. Umar ke zaune, tuni ransu ya gama 6aci, da ka dube su, ka san akwai tashin hankali a tattare da su. Zaune kawai suke, amma zukatansu babu abinda bata sak'awa. Alkali ya dubi Naseer da ke tsaye cikin akurkin tuhuma, cikin madubin idon sa fari sol ya ce da shi,"Ina fatan duk ka ji bayanan da suka gabata. Ya ce,"Ka ji Me za ka k'ara a kai?" Ya amsa, "Babu." Ya ce,"Duk ka amince da abubuwan da aka fad'i kenan?" Kai tsaye Naseer ya amsa,"Dole duk abinda aka fad'i, ya zama gaskiya, saboda ni ba ni da wani sheda sai Allah, domin haka babu amfanin wahalar da kotu, duk hukuncin daya dace sai ayi min." Na amince da kowane irin adalci da mai shari'a zai min." Alkali shi kan sa, sai da kalaman Naseer suka sa shi ya jima yana yana kallon sa. Haka su M.Umar ke kallon Naseer cike da tausayi. Sun sani dole dama haka za ta kasance, sai dai kawai addu'ar Allah yasa hukuncin ya zama mai sauki. Bayan kammala rubucen-rubucen Alkali, sai ya yanke hukunci. Bayan ya karanto dokokin kundin shari'a, sai ya zarce da cewa,"Kotu ta yankewa Naseer d'aurin wata 3 a gidan yari, ko tara ta 3000. Haka kuma shi zai biya kud'in asibitin da Salis ya kwana, wanda a yanzu haka (Bill) yake a hannun kotu, na naira dubu biyar da d'ari biyar da hamsin 5,550. Shi kuwa Sageer taimakawar da yayi wajen ta'addancin, kotu ta ba shi tarar 1500, ko sati 2 gidan yari, tare da gargadin mai tsauri, idan har aka sake kamasu da laifin irin wannan. Kwarai za su had'u fushin hukuma. A karshe ina jan kunnunwan Naseer da Sageer da cewa kar wanda ya sake nemaan wani da fad'a. Tare da fatan dokar kasa za ta zama abar biyayya ga kowa. Nan take ya sallami wannan shari'a ya kama wata.Waje aka fito da su Naseer, duk jama'ar su suka biyo su, yayin da gayyar su Salis da Lauyan su suka wuce cike da farin cikin samun nasara. A nan take su M.Lawal da M. Umar suka had'a kud'i 1500, don biyan kud'in tarar Sageer, shi kuwa Naseer suna ji, suna gani aka wuce da shi gidan yari, don babu yadda za su yi. Gaba d'ayan su babu mai adadin kud'in tarar sa da na asibitin Salis, jimliar dubu takwas da dari biyar da hamsin, kamar su zubda hawaye, saboda 6acin rai. Shi kam Sageer sai da ya zubda hawayensa, a haka suka nufi kasuwa, runfar M. Balarabe suka sheda masa yadda shari'a ta kaya. Kawai kad'a kai yayi, ya ce,"Allah yasa ya zama darasi a gare shi." Malam Lawal ya ce,"Yanzu matsalar kud'in asibitin nan da aka ce sai an biya. 8,550." Mala, Balarabe ya ce,"Ai da ma Alkali ya maida su dauri. Wa zai biya? Ni dai bn da wannan adadin kudin. Dukkan su shiru suka yi na 'yan dak'ik'ai, kafin M. Umar ya ce,"Allah ya rufa asirin, ni zan k'arasa gida."Balarabe ya mika masa hannu,"To ka gaida gida, Allah ya saka da alkhairi.." Amin." Yake fad'i, yana mik'ewa tsaye. Suka yi sallama da Malam Lawal, ya fito ya bar su tare da Malam Balarabe. Gida ya nufa, lkcn 10:15 na safiya. Inna na zaune tsakar d'aki cike da tunani, har wani gyangyad'i takaici ke son d'ibar ta. Sallamar M. Umar ta sa ta, ta wartsake." Ka dawo?" Ya k'araso cikin d'akin yana fad'in,"Na dawo." Ya zauna rai 6ace, yayin da take masa sannu da zuwa, ya amsa,"To yaya, me ake ciki?" Ya ce,"Anyake hukunci. Wata 3 zai yi gidan yari ko tarar 3000. Sai kuma kudaden asibitin da suka ce sun kashe, 5550. Kin ji yadda aka yi. Shi kuma Sageer da yake na sa babu yawa, mun had'a kud'in mun biya tarar. Inna ta aje numfashi, ta ce,"Yanzu shi Naseer din gidan yarin zai yi? Ya amsa,"To yaya ki ke so a yi? Ba mu da adadin kudin nan A'i. Dama ace 3000 ne kawai, da sai ayi 'yan buge- buge a samu. Amma babu komai. Allah zai rufa asiri, zan yi iya kokari na mu gani." Ta ce,"Sati mai zuwa zan amshi adashina 3500 ne, sai in hakura da tafiyan kauyen, zan ba ka a harhada mu ga abinda za'a samu." Ya nisa kafin ya ce,"Allah ya kai mu lkcn. Ni bari in koma kasuwa." Ya mike ya fice Inna na fadin,"Idan Zarah ta dawo zan leka wajen gidan su Naseer din in yi wa Umman ta sa jaje.Ya ce,"Sai kin dawo." Ya fice ya bar ta da jimami. Tamkar d'an cikin ta take jin Naseer a zuciyar ta, sbd yadda ya kular mata da Zarah lokcn da take buk'atar kulawar. Watau sa'ilin yarintar ta. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-04 Posted by ANaM Dorayi on 10:59 AM, 06-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_____________ Karfe 3 ta gota, awa 1 bayan dawowar Zarah daga makaranta, amma har yanzu tsiyayar hawaye take yi. Tunanin ta me take da shi wanda za ta siyar, don taimakawa iyayen ta wajen fiddo Naseer daga gidan yari! Tsaf! Ta mike ta nufi d'an akwatin kayanta ta bud'e, ta za6o tsala-tsalan ciki, watau k'arshen adakar. Kala 6 ta aje su bisa gado, ita ma ta nemi wajen ta zauna ta ci gaba da tunanin adadin kudin da kayan za su bayar. Can cikin zuciyar ta kuwa, tsabar kewar yayanta ke addabar ta. Ji take tamkar sun shekara goma rabon su da juna. ******************** Cikin kwanaki 3 bayan yanke shari'a Umman Naseer tare da taimakon su Malam Lawal da M. Umar da Inna suka had'a kud'ad'en da kotu ta buk'ata, watau Naira 8,550. Suna biyan kud'in kai tsaye kotu ta aika da takardar umurnin sakin Naseer. Yana fitowa yayi arba da su M. Umar da abokinsa Sageer. Da sauri suka nufo juna Sageer, ya rungume shi suna yi wa juna barka tare da nuna tsananin godiya ga Ubangiji, sannan ya juya wajen su M.Umar ya gaida su. Su ma cike da farin ciki su ke, fuskokinsu tsaf, suke d'auke da fara'a suka amsa gaisuwar sa. Daga nan gida suka wuce da shi. Umman sa na jin sallamar su, ta mik'i da hanzarin ta, amma kuma sai ta kasa aiwatar da komai, haka ta tsaya kame da ha6a tana kallon Naseer. Kwarai ta tausaya masa ganin ya sauya ba kad'an ba. "Malam!" Ta kwala wa Malam Balarabe kira, yayin da su Naseer ke karasowa daf, da ita. Ta koma bisa tabarma ta zauna suka zauna suna fad'in,"Sannu Umma." Ta ce,"Kai ne abin sannu, manya d'ibar fari. Allah ya shirye ka." Ya sunkuyar da kai, dai-dai lkcn Malam Balarabe ya fito daga d'aki. Sageer ya gaishe shi, sannan ya ce,"Su Baba na nan zaure." Bai saurari gaisuwar Naseer ba, yayi gaba abin sa, ya nufi zaure.""Ku shigo mana M.Umar! Kun tsaya daga nan kamar bak'i?" Ya koma ciki suka biyo bayan sa. Umma ta k'ara baza tabarma kowa ya zauna suna 'yar raha. Bayan gaisuwa. M.Lawal ya ce,"Malam Balarabe babu wato doguwar magana tsakanin ka da Naseer, face ka sanya wa ranka ruwan sanyi,ka yafe masa laifin da yayi maka, tunda Allah ya tak'aita wannan wahalar. Shi kuma tun a hanya mun jajja masa kunne, yayi alkawarin ba zai sake maimaita laifin makamacin wannan ba. Ina fatan za ka karbi tuban sa ka sanya masa albarka? Malam Balarabe yayi d'an jim, sannan ya dubi abokan sa ya ce,"Hakika kun nuna min kauna tsakani da Allah, kuma wanda na yi imani ko banda rai za ku iya rike min iyali na. Saboda haka ba ni da wata kalmar godiyar da zan muku, illa in ce Allah ya saka maku da mafificin alkhairi, ya bar mana zumuncin da ke tsakanin mu, har zuwa gidan aljanna. A game da Naseer kuwa, ni na yafe. Ubangiji ya shirya mana dukkan zuri'a baki d'aya. Kowa ya ce,"Amin. Kan Naseer na sunkuye, kuma har cikin ran sa yana jin tausayin iyayen sa, sai yanzu yake nadamar ta6a Salis da yayi. Sai dai ba laifin sa bane, kaunar da yake wa Zarah, ita ta kai shi ga aikata abinda zuciyar sa ta sak'a masa. Amma in kwana dubu yana wannan bayanin, iyayensa ba za su ta6a daina ganin laifin sa ba, Musamman Abban sa. Ya sauke numfashi, na jin dadin furucin Baban sa. Tsam! Ya taso ya tsungunna gaban sa, ya ce,"Abba na gode." Ya dube shi a raunane ya ce,"In kunne ya ji, gangar jiki ta tsira Naseer. Ka sani kullum shekaru na tafiya suke yi, za'a wayi gari wata rana ace babu ni, shi yasa kodayaushe kokarina ka dan sami ilimi dai-dai gwargwadon k'arfi na, amma kai hankalinka ba shi a nan. B'acin rai na kodayaushe, idan na tuna cewa ba ka sami rubuta jarabawar ka ba, ga shi ance saura guda 3 a kammala ta. Wannan babban rashi ne, don ko banza sai wata shekarar za ka sake wanda ya kamata ace katafi wani mataki na gaba. Haka Allah ya so." Wannan dogon jawabi ya sanyaya jikin kowa, duk sukai shiru na 'yan dak'ik'ai kafin M. Lawal ya ce,"Lokaci kam an 6ata shi.Amma babu wuya a wurin Ubangiji, wata shekarar za ta zo ne, sai ya sake. Allah dai ya kai mu dai rai lafiya." Suka ce,"Amin." Malam Umar ya muskuta, ya ci gaba,"Akwai wata magana da na ke ganin zai yi kyau in fade ta wannan zaman, don kowa ya zama shaida. Allah ya sani, ba ni da abinda zan yi wa Naseer in iya saka masa akan hidimar kuluwar da yayi wa Zarah, wanda shine silar kullawar zumuncin mu, face in ba shi auran Zarah. Don samun d'oruwar zumuncin mu. Ina fatan kowa zai amshi wannan kyauta tawa da hannu biyu. Saboda haka Naseer, ga Zarah nan matar ka ce insha Allahu. Za ta ci gaba da karatu har zuwa lkcn da Allah ya hore mana d'an abin yi. Haka kuma ina son kowa ya shaida ko bayan raina, ban ce a tada wannan magana ba, koda za'a sami wani akasi ta 6angaran Zarah, wanda ba na fatan faruwar hakan, ban jin Zarah za ta iya juya wa yayanta baya. Ko akwai kuskure a zan ce na? Gaba dayan su farin ciki ke bayyane bisa fuskokin su, musamman uban gayyar wanda yake jin tamkar an tsunduma shi a al-janna. Kiris ya rage ya riga iyayen sa magana. Sageer yayi sauri ya toshe bakin sa. Umma ta ce,"Kyale shi mana mu ji abinda zai ce maras kunya, dama tunda aka fara maganar bakinsa ya k'i rufuwa. Ai sai mu kyale shi, ya amshi auran da kan sa." Da sauri ya mik'e, yana dariya yayi zaure. Sageer na bin sa, yayin da iyayen ke masa dariya. Malam Lawal ke fad'in,"Yaya za ki maida shi kamar mace? Ai mata aka sani da wannan kunyar. Gaskiya abu yayi dadi, kuma mun amshi wannan babbar kyauta taka. Allah ya sanya duban albarkun tare da fatan ran mu ya kai had'e da koshin lafiya." "Amin." Duk suka amsa Malam Balarabe ya mik'awa M. Lawal hannu su kai Musabaha, "Mun gode! Mun gode!! Allah ya bar zumunci. Malam Umar ya ce,"Naseer d'a na ne, ni kad'ai na san irin gudumuwar daya bai wa rayuwar Zarah, na kuma fahinci dalilin fadawar sa wannan fitinar. Zarah yake so, ni kuma naba shi. Allah ya tabbatar mana." Umma kan ta farin ciki ya hana ta cewa k'ala, illa ta amsa da amin, ta zarce ta sawa abin albarka cikin zuciyar ta, sun dan jima suna hirararrakin raha, kafin suka yi sallama suka fito.Naseer da Sageer na cikin dakinsa su ma suka fito suka yi rakiya tare da k'ara godiya, sannan suka dawo d'aki. Bisa katifa Naseer ya zube a ringine. Sageer ya zauna kusa da shi ya ce,"Yanzu ba washe hak'ora ba, mice ce shawarar ka?" Ya juya ya dube shi." Ta me? Ya ce,"An ba ka Zarah, wane shiri za ka yi na dogaro da kanka, don ci gaba da kulawa da ita?" A natse ya taso, ya dube shi kafin ya nisa, ya ce,"Akwai fa sauran aiki, amma ai Allah na nan, shi yasan yadda za'ayi ko? Haka ne, sai dai yakamata kai ma daga (Next year) ka dai- daita jarabawar ka, don na san ka da shiririta akan karatu. Wani lkcn har da laifin ka." Ya kwada masa harara, ya ce,"To zigziglar baturan ilimi! Cewa na yi ba zan sake (Exams) d'in ba ko yaya?" Ya ce,"Ka ji tsiyar ka, sai ana maganar arziki, sa ka fand'are. Ni bari in wuce gida, tun kafin mu hau rimi mu fad'o karyayyu." Ya mik'e zai fice, "Naseer ya janyo hannun sa,"Kai banza ne Wallahi, duk ka 6aci da bakar zuciya, yanzu kuma me na yi? Ya sanya masa ido suna kallon juna. D'an murmushi Naseer yayi, ya saki hannun sa cikin damuwa ya ce,"Je ka ma kawaia anjima idan na yi wanka, zan fito mu je gangare." Ka wuce kawai, kar ka biyo min." "Me yasa?" Ya ce,"Shi yayi saniya, d'an rainin wayau. Kasan in yi maka rakiya, amma ba ka san in ba ka shawara, ka ji ba. Ka tafi kai kad'ai, ba Zarah bace? Kun san.............." Ya katse shi, saboda fizgo shin da yayi, ya zauna dabas! "Bani shawara Sageer, me ne zan yi? Faskare ko dako? Yasar masai ko kuwa in fara turin kura?" Ya ce,"Ko wanne ka d'auka yayi, idan ma gatse ka ke min, ina son ka sani duk sana'a ce, kuma da su mutane da yawa suke ciyar da iyalan su. Sana'ar hannu aba ce mai kyau, wanda duk me yin ta, ya wuce raini. Sai anjima." Ya ce,"Tsaya mana, ai ka fad'i gaskiya Malam Sageer. Ba gatse na ke yi ba. Yanzu menene abin yi? Ya ce," Akwai shagon da na yi magana zan rinka zuwa koyon d'inki. Nan shagon Alh. Hassan, idan ka na so, ka zo mu rink'a zuwa tare. Me ka ce?"Kai tsaye ya amsa,"Dai-dai wallahi. Yaushe za mu fara?" Ya ce,"Ka ga ranar Wednesday za'a gama (Exams),zuwa alhamis ko juma'a, sai mu fasa kawai." Ya ce,"Dole a fasa ko a sami na auran Zarah. Komai zan iya yi, sbd ita, don jin ta nake tamkar rai na. Anjima za ka raka ni d'in ko? Yayi d'an murmushi,"Shi yasa ka yi saurin amsa min? To bn zuwa, ka je kai kad'ai, kafin laifin ka, kai kad'ai.............." Umma ce ta katse hirar da ta kwala wa Naseer kira. Ya mik'e yana naushin kafad'ar Sageeer. Jim kad'an ya dawo da kwanon abinci. Sageer ya ce,"Umma har ta gama abinci k'arfe 11?" Ya ce,"A'a, waina ce Abba ya bada kud'i, maimakon ta kira ni, mu siyo shine ta shiga nan gidan wainar ta siyo da kan ta." Sageer ya kad'a kai, ya ce,"Su Umma na son ka Naseer, ka yi wa Allah ka rink'a gudun 6acin ran su." "To, na ji." Haka ya fad'i yana bud'e wainar, komai yayi. Suka fara ci, sai dai Sageer ya lura kamar Naseer bai son yin magana, don haka ya tambaya,"Me ka yi?" "A'ina?" Shi ma ya tambaye shi. Ya ce,"Kamar wani abu ya dame ka?" Ya dube shi da kyau, ya ce,"Har yanzu babu wanda ya fahimce ko ni wanene, shi yasa aka min kallon maras ji. Alhali ni ina son duk abinda zan yi, ina da dalili na. Kuma wallahi ina tausayin iyayena. Amma abinda ke ba ni haushi, ku ba ku fahimtar halaye na A JINI NA SUKE. Sannan shin wai ma, me na ke yi na 6atanci, wanda ya taka shari'a?" Sageer yayi shiru, yana kallon sa. Naseer ya kad'a kai, manyan idanuwan sa suka fara kad'awa, ya sanyaya murya,"Amma tunda kai ma ka na ganin ina sa6awa su Abba, yanzun nan zan je in nemi gafarar su, ni kuma zan nemawa kai na mafita, duk da na san cewa ban aikata komai ba, don ran su ya 6aci. Sageer nisa ya ce,"To ka yi hak'uri, idan magana ta bata yi maka bane." "A'a, ka fad'i dai-dai, abinda ka fahimta ne tsakanin ka da Allah so ba matsala na gode, mu ci abinci kawai." Suka ci gaba da cin abinci, suna hirarraki har suka kammala. K'arfe 12 Sageer ya koma gida, ya bar Naseer tare da su Abba yana sake neman gafarar su.K'arfe 4 bayan sallar la'asar, ya fito fes! Cikin k'anana kaya. Shagon aski ya fara shiga, aka yi masa, gaba d'aya ya k'ara tsaftacewa kamar wani ango. Daga nan gidan su Sageer ya nufa, yana zaune bisa dakali ya na karatu. Naseer ya jira shi, ya mayar da littafin ya kulle k'ofa, suka wuce gangare. Cikin zaure ya tsaya ya dubi Sageer ya ce,"Zan iya shiga gidan nan kuwa?" Ya ce,"Me yasa?" Kunyar Inna na ke ji............."Bai gama zancensa ba, sai ga Inna ta kawo cikin zauren. Take nan Naseer ya daburce, tsanananin kunya ta kama shi tamkar bai ta6a sanin Inna ba. Shi kan sa ya rasa dalilin hakan. Hannun sa a k'eya yana ta sosawa,"Sannu Inna. "Dukkan su suka ce. Bakin ta har kunne ta amsa. "Allahu Akbar Naseer, yanzun nan gidan ku na nufa in duba ka. Sannun ku!"Suka tsugunna suka gaida ta, ta amsa, sannan ta zarce da fad'in,"To ku shiga. Zarah tana nan a ciki, sai na dawo." Suka amsa, "Adawo lafiya." Amin." Ta wuce tana fad'i. Su kuwa ciki. Suka yi sallama, kamar su take jira, domin kuwa ta zuba adonta da wani material ruwan hoda da farin furanni. Ko ba'a tambaya ba, adonta ya nuna tsaf, tana cikin farin ciki irin na bege. Amma maimakon ta tarbi yayanta kamar yadda ta saba, sai ta kasa, saboda wata sabuwar kunyarsa da ta mamaye idanuwanta, masu sa yayan nata neman zarewa. Sallamar kawai ta iya amsawa, ta k'ara sunkuyar da kai, ta d'ora idanuwanta bisa tiran da take gyaran wake. Kujeran tsakar gida suka ja suka zauna, sannan Sageer ya ce,"Zarah, yau kuma ba za'a kalli yayan bane?" Sageer ta duba fuska cike da murmushi, "Ina ruwanka?" Ya ce, "Au, haka ne? Saboda na kawo miki shi ko? Ba laifin ki bane. To ya ki ke?" Ta ce," Lafiya lau, ya mutan gida?" Ta amsa,"Su ma k'alau suke. Yau dai kuka ya k'are ko? Ga yayan ki nan. Allah ya taimake mu ya fito."Ta ce,"Allah ya kare na gaba." Amin, sai ki yi masa fad'a ya rink'a danne kishi." Ta karkad'e kai. Duk suka fara dariya,"Kin goye bayan sa kenan?" To babu ruwa na, kinfi kowa sanin halin yayan ki."Ta ce,"Akwai k'arya k'ashin wuya ko? Ai ya bada darasi, ka ga babu mai sake kwatantawa. Suna ta k'yalk'ya dariya. Naseer kamar ya lashe ta, sai lkcn ya fara magana, "Kinyi min dai-dai my sister, jarumta adon namiji, kuma ai kishi halas ne, duk wanda ya shige maka hanci, ka daddage ka fyato shi, har sai ya balle k'ashin wuya. Idan ya suma, ya farfad'o ya gane kuskuren sa ko tawan?" K'ara aje kai tayi k'asa tana murmushi. Sageer ya ce, "Ok, irin na ku tsarin kenan? Lallai jiki magayi, gara shi da ke mai kukan tsiya." Wasa na ke Sageer,ai yayana yayi min babban laifi. Shekaru nawa mu ke tare da shi? Koma dai menene, sai ya gaya min, ba wai ya je ya jawo mana tashin hankali ba. Babu wanda ran sa bai 6aci ba akan abinda ka aikata.........." Ta d'an dube shi a raunane ta ci gaba,"Don girman Allah yayana ka rink'a gudun abinda zai rik'a 6ata wasu Abba rai." Gaba d'ayan jikin Naseer yayi sanyi, ta jefa shi cikin damuwa. Yayi d'an shiru kafin ya numfasa." Ya ce,"Na ji Zarah. Insha Allahu ba za'a k'ara ba. Kuma na rok'i su Abba sun ce komai ya wuce. Ina fatan ke ma za ki min afuwa, ki d'auka cewa kishin ki ne yayi min yawa har idanuwa na suka rufe ruf! Ba na ganin kowa a gaba na, balle ya gaya min in ji. Ki yi hak'uri, kin ji?" Ta d'an rausaya kai tana murmushi,"Ya wuce,"Sai harkar soyayya ko?" Kunya ya bata sosai, ta rasa madafa. Sageer ya ce,"To in d'an jira daga zaure ne? Yadda ka so." In ji Naseer ya sanya hannu cikin tiran da ke cike da wake ya shiga taya ta. Ta ce,"Yimin wulank'anci, don na rako ka." Zarah ta amshe,"Kyale shi Sageer, yi zaman ka ai kai yayana ne."Maigida na ke, komai sai da izini na." Ta ce,"Haka ka ke gani, amma ni na san sabon yayana ya fi power, don haka ka bi shi a hankali. Ya dubi Sageer ya ce,"Allah ko? To sannu yaya ina yini?" Sageer dokar masa kafad'a, suka ci gaba da hira cikin farin ciki.Daran wannan ranar Naseer bai iya barci ba. Ba waai k'aunar Zarah ke masa tuk'uk'i ba, don wannan ta dad'e masa cikin zuciya. Ammamaganar da ta zame masa sabuwa, ta kuma hana shi sukuni, ita ce maganar da kowa yake masa, watau ya rink'a gudun abinda zai rink'a 6ata wa iyayensa rai. Ko Inna da ta dawo, ta same su a gidan. Sai da ta fad'i wannan maganar sbd haka abin yayi matuk'ar tsaya masa a rai. Kuma ya rasa mafita, domin shi a ganinsa bai aikata komai ba, don ran su Abba ya 6aci, akan gaskiyar sa yake kuma ko a yanzu ba don kotu ta shiga tsakanin sa da Salis ba, da Salis ya gane shayi ruwa ne, madara ake zuba masa yayi kauri. Duk da cewar Baban Zarah ya share masa hawaye kuma ya hana Salis zuwa wajenta. Wannan ba zai hana shi k'wato hak'k'in sa ba. Amma magana ta kau, tunda kotu na tsakani. Ya juya rigingine, ya numfasa, "Mece ce mafita a waje na ni Naseer? Na san ba ni da hak'uri, amma ai sai anyi min na ke ramawa. Sai kuma a rink'a ganin laifi na." Ya ja tsaki, ya kada kai mai cike da takaici. Har aka kira assalatu idonsa 2, ya fito yayi alwala, suka fita masallaci da Abba. Bayan cin abincin safe, ya fito k'ofar gida yayi shiru a tsaye, kusan layin yayi tsit! Saboda duk wani yaro daya isa zuwa

Chapter 4 of 11