Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 11
in yi tafiya ta kawai?" Sosai ma." To Zarah fa? Ai ita ina son ta ba zan iya barinta ba." Ya ce,"Ita ma ta hada na ta komatsan ku sa kai." Takaici ya kara lullube shi ya buga tsaki ya ce,"Abin kuma ya zama iskanci. Ba fa Indiya ka ke kallo ba, wannan zahiri na ke gaya maka. Ina za ni da 'yar mutane? Ya ce,"Idan kuwa mafita ka ke nema, dole cikin biyu ka dauki daya, ko ka hakura da su duka, ko ka aure su gaba daya har da wacce ba ka son. Ka kuwa ce ba ka son ta, yaya za'ayi ku zauna tare? Ransa ya kara baci ya ce,"Yaya za'ayi kuwa? Kai ka na da mafita, amma suna da kamar wuya. Ka dan nemo mai sauki ne, zai fi.." Mai sauki bai wuce ka yi tafiyar ka, ka ba kwana 2. Alhj zai ji haushi, ya soke zancan. Idan ka dawo, a nemi Abba gafara, ka ga shi kenan, waccan magana ta tashi, dole a bar ka da Zarar ka. Wallahi ta ma fi dacewa da kai, duk da ban ga waccan ba." Ya nisa ya kwanta a katifa rigingine, sakwan 2, bai ce kala ba. Yana zancan zuci ya kafin ya ce"Yau din nan zan 6ace masu kuwa. Ya 6alla masa harara, ya ce a ransa,"Ai sai ka 6ace, tunda a wajen ka masifa ce ta same ka. A dakin yayi sallar la'asar, duk irin kiran wayar da Abba ke yi, babu wacce ya amsa. Kira na karshe daya shigo, shine na Zarah, misalin hudu da rabi, shi ma bai dauka ba, don bai san ma ta inda zai fara yi mata bayani ba. Take nan ya kashe wayoyinsa duka biyun. Karfe biyar dai-dai Yakubu ya dawo, su biyun suka fito tarbar sa,"Bakin sa har kunne ya fito, "Ah! Jah-Jah. Dama ka na nan? Ban ga kafafuwan ka ba? Yayi dan murmushi ya ce,"Tana gida." Jaja ya miko masa hannu su kai musabaha, Yakubu ya ce,"Congrats! Sai na ji daddan lbr wajen Alhj. You're so lucky Naseer. Nusaiba akwai hankali ga natsuwa. Ka zama dan gata, mata 2, lokaci guda. Allah ya tayaka rikon su. Yake yayi, domin tumi zuciyar sa ta kara firgita. Watau Alhj har ya fara shela 'yar sa tayi miji. Lalai zai ji a salansa. Bai ce komai ba. Ya ce,"Na gode yayanmu. Amma yayanmu ai ina ganin kamar bn isa rike mata 2 ba." Ya ce,"Why not, kai ba namiji bane? Babu abinda zai gagare ka, dukkan su a karkashin ikon ka za su zauna, illa iyaka ka sa ido akan ko wacce, ka fahimci halin ta. Sannan ka yi iyakar yin ka, ka tabbatar da cewa babu gutsiri tsoma a cikin gidan ka. Daga karshe kai karan kanka ka tsaida adalci. Shakka babu gidanka za'a zauna lafiya. Ko dama na gaya maka Nusaiba bata da matsala. Kafin in taho ma, na je mun gaisa ina mata tsiya, ta gudu. Ya dafa kafadar sa, ya ci gaba," Ka yi sa'a Naseer. Alhj na kaunar ka. Ka rike masa amana, ka ji? Da kyar ya hadiye miyau, don ya fahimci Yakubu ba zai gane ba, saboda haka yayi masa ta 'yan duniya, ya washe baki ya ce,"To na gode yayanmu. Dama zan wuce kenan sai gobe." Ya ce,"Allah ya kai mu. Ina fatan ka shirywa wasan mu da (Kano Horses) jibi? "Sun aiko da takarda ne? Duk dazu Alhj ke shaida mi." Ba matsala, kullum a shirye mu ke." Yayi murmushi, yana masa kirarin ," Jah-Jah! Ba wani bayanka." Su kayi sallama. Yakubu ya shige gida." Naseer ya dubi Naseer B, ya kwa6e fuska ya ce,"Yayanmu ya shagala. Ka ji Alhj Feshi ya ke yi 'yar sa ta yi miji." Dariya yai cikie da hassada,"Zai sha mamaki." Manta kawai. Ni zan wuce,sai mun waya." Suka wuce yana taka masa, jimawa kadan ya sami dan aca6a ya hau, yayi gaba. Naseer B yasa hannaye aljihu, yayi hucin zafi, ya ce a ran sa,"A sauka da nauyi. Gara6asa ta wuce ka Yaro." Ya juyo ya dawo gida ran sa cike da tunanin ko shi ma ya koma Sukuwan ne? Dan aca6a ya aje shi kofar gidan su Zarah. Ya sauka ya shiga zaure, ya dau lkc cikin zauren yana tunanin iska. Da kyar yayi karfin hali ya shige tare da sallama. Amma da ka dube shi, za ka tabbatar babu kuzari a tare da shi. Inna kadai ke tsakar gida a zaune. Ta bi shi da kallo, tana fadin,"Ka kyauta. Kuma sai ka bar ni da dambu cikin kula. Ya karaso gefenta ya tsugunna ya gaishe ta. Bayan ta amsa, ta ci gaba da fadin,"Me ya hana ka zuwa tun danbun na da mutuncinsa? Nan da nan idanuwansa suka fara ja." Ina ba zan iya cin sa bane, shi yasa." Ta ce, "Don me? Ita rayuwa ba shirin Ubangiji bace? Kar ka damu kanka dan Inna, kai dai ka roki Allah ya sanya alkhairi. In don ta Zarah ne, na riga na yi mata bayani, na kuma kwantar mata da hankali. Ita fargabar ta daya ce. Wulakanci take gudu. Nace........ Yayi fit! ya katse ta,"Inna ni fa ban so, su kyale ni mana. Ko kuwa ana auren dole ne? Ni babu abinda ya dame ni da kudin Babanta. Ga wacce na ce ina so, kowa ya san maganar nan, ai bai kamata Abba yayi haka ba. Saboda haka ni gas............... Yi min shiru don Allah. Me yasa ku yaran yanzu ba ku da kawaici ne? Sai ku ce dole-dole abinda ku ke so, shi za'ayi? Abba bai da iko da kai ne? Na ce su iyayenka ba isa da kai ba ne? Ya sunkuyar da kai, saboda kunyar da nauyin Inna kawai, ba don wai jawabinta ba. Sam bai ratsa zuciyarsa ba, balle ya saduda. Ta sassauta murya,"Haba dan Inna, yanzu kai ka na ganin yadda Alhj ya taso da girman sa da komai, ya tunkari Abbanka da wannan maganar, har yana da abin cewa bayan wannan? To ina son ka sani, ba haka dattijo yake ba, kuma Abba yayi abinda ake so, kamar yadda Alhj ya nuna halin girma. Abu na karshe, shine ka ba mara da kunya, ka nuna wa duniya ka fito gidan mutunci, ka yi kawaici irin na mutan da, ka amshi wannan kyauta da zuciya daya. Ai Malam ya jima nan yana jiranka har ya sa Zarah ta kira ka a waya, amma ka ki dauka. Ko dama bayanin da zai maka kenan, kai dan mu ne, duk ci gaban daya same ka, muna farin ciki da shi. Allah ya taya ka rikon su bisa adalci. Inna sarewa kawai take yi, domin shi a wannan lkcn tunanin sa wane gari zai 6oye. A neme shi, a rasa? Abuja tayi masa kusa, sai dai Lagos ko Fatakwal. Shi yasa jawabin Inna ko ince nasihohinta, ba dayan da ya ji. Ko da tayi shiru ma, sai da ta sake maimaitawa,"Ka ji ko dan Inna? Sannan ya dawo hayyancin sa, ya dan daga kai ya ce,"Na ji Inna." Ta ce,"To shi kenan, tashi ka shiga daki. Zarah ta kawo ma abincin." Ya mike ya shiga dakin. Zarah na zaune bisa kujera, tana sauraron komai. Daga shigowar sa, suka hada ido, gaban sa kawai ya ji ya fadi. Da sauri ya kauda kai, ya hanzarta zama. Shiru suka yi, kowa ya rasa mai zai ce wa dan- uwansa. Inna ta kwala kira. Zarah ta amsa, ta tashi ta fice, bai ko iya cira kai ya dubi fitar ba, illa wani tukuki da ransa ke yi, ko alama ba shi da ra'ayi daya da su Abba.."Sallama tayi, ta shigo da kayan abinci a tire, ta aje gaban sa.Ta bude kula ta dauki filet da cokali za ta zuba. Wata shakakkiyar murya ta ji ya ce,"Kar ki zuba." Ta dube shi idanuwan nan jajur! Suke ta ce," "Don me?" Ba zan iya ci ba." Ta ce,"Zan gaya wa Inna." Ya dauki murfin ya rufe kular ya ce," Je ki gaya mata din." Ta koma da baya ta zauna dirshan! Ta kare masa kallo, tayi dan murmushi ta ce,"Kai yanzu mece ce matsalarka? Abincin ma ba za ka ci ba? Ko zaton ka za ka sami matsala ta waje na?Ta dan kauda kai kafin ta ci gaba,"Ina jin na ta6a gaya ma wannan maganar, har ka yi fushi. Alkawarin a hurumin da ba na mu ba, kuskure ne. Ga shi ba'a je ko'ina ba, ta fiya ta sauya salo, sai dai ina baka tabbacin cewa ina tare da kai a ko wane yanayi, ni ce uwargida." Ya watso mata gwalagwalan idanuwan sa jajur! Ya nuna ta da yatsa,"Yanzu na gane ba kya sona, tunda ba kya kishi na. To ina son ki sani, ganin nan da ki ke min, sallama na zo miki, domin gaba daya na hakura da auran."Ban gane sallama ba? Ya ce,"A zaton ki zan auri yarinyar nan ne? Ban jin zan iya, na kuma lura babu wanda zai fahimce ni, balle ya goya min baya. Babban abin bakin ciki, wai har da ke. Shi yasa na hakura da auran gaba daya. A yau din nan zan bar ma ku garin, sai ku nemi wani miji." Tayi dan murmushi, yana lura da ita. "Wannan zancan 'yan dirama yayana ka ke yi. Maganar kishi kuwa, ai babu wani kishi daya wuce na bin iyaye. Ni gaskiya na ke gaya maka yayana. Muddin ka ce za ka aikata wani abu wanda zuciya ta shirya maka, to ina mai tabbatar maka da na sani ne zai biyo baya. Zai yi kyau ka sami lokaci ka yi tunani kafin ka yanke hukuncin. Idan kuma ba ka yarda ba, to ni din ma ina iya cewa na hakura. Wata kila hakan shine mafi alkhairi.."Zuru yayi mata, yana kallo, ta . Sannan ya ce," Ci gaba mana." Ta ce,"Ai na gama, sauran za6in na ka ne." Ya ce,"Ina lura da ke har wani murmushi ki ke yi, watau magana ta busa ce, shi yasa ki ke rattafo wadannan kalaman.Tuni na gaya miki za6i na, na hakura da auran, meneme ma 6ata lkcn wa'azinki? Tunda ba shi zai sa na so yarinyar nan ba? Da muguwar rawa, gwamma kin tashi, ina kakkaucewa, kowa yana jawoni da wa'azi. Alhali masu wa'azin ba su za su zauna da 'yar ba.Kin fi kowa sani na, idan na tsani abu sam- sam ba na waiwayar sa, haka kuma in na so shi, kamar zan mutu na ke ji, saboda tsabar kauna. Haka jini na yake, babu mai iya canza min shi. Ina son ke ma ki yi tunani akan magana ta. Ni zan wuce, watakila ban iya mancewa da ke." Tsoro ya fara kamata. Me Naseer ke naman jawo masu? Tabbas ta fi kowa sanin halin yayanta, na kafiya akan ra'ayinsa. Amma maganar da aka ce iyaye na ciki, ta fi gaban a zauna ana jayya da ita. Idanuwanta suka raina fata. Take nan suka kawo kwalla, a raunane." Ta ce,"Yayana saboda ni ka ke son bijirewa su Abbba? Ba ka yi min adalci ba, domin ni har ga Allah ba zan bijerwa iyaye na, saboda kai ba. Komai son da na ke maka, zan hakura. Balle wannan maganar mai sauki, ka hada mu, ka aura menene a ciki? Lallai gata ya yi maka yawa, ka je din duk abinda ka ke so, ka aikata dai-dai ne." Bai ce uffan ba, ya mike yai waje abin sa. Babu kowa a tsakar gidan, don haka ya kara sauri, ya bar gidan. Zulumi bisa zulumi. Tunani. Haka Zarah ta kasance har bayan sallar isha'i. Haka abin ke daurewa Inna kai. Ita gani ma ta rinka yi kamar Naseer wasa yake yi. Malam Umar na shigowa, ta maida masa bayani. Bai 6ata lkc ba, ya sake shura takalmansa ya nufi gidan su Naseer. Ya jaddawa Malam Balarabe halin da ke ciki da irin shirin da Naseer ke kullawa zuciyar sa. Al'amarin ya daurewa su Malam Balarabe kai, har yayi fushin da bai ta6a yin sa ba, domin a gaban Malam Umar ya ce," Idam kuwa har Naseer yasa kafa ya bar garin nan, har abada ban yafe masa ba. Malam Umar bai ji dadin wannan kalami ba. Yayi rarrashin duniya. Malama Balarabe ya ki sakkowa, sai ma kara tafasa zuciyarsa ke yi, ransa 6ace ya dawo gida. Al'amarin ko alama bai yi dadi ba. Haka Umma ke ta wahalar tunani cikin ranta, ko bata furta komai ba, fushin da ke zuciyar ta, ya ishi Naseer. Karfe 11 dare, ko gyangyadi ba wanda yayi, don sun hakikance Naseer ya aikata abinda zuciyarsa ta shirya masa. Tunanin Malam Balarabe, shine bai san da wane ido zai kalli Alh. Basheer ba, balle abinda zai ce da shi? Ya zuwa yanzu ya ci ace Naseer ya je sun gaisa da yarinyar nan,Me Alh. Basheer zai dauka cikin ransa? Lallai ko alama Naseer bai daraja shi ba, bai kuma ta6a tozarta shi ba, irin na yau. Kawai hawaye Umma ta gani suna zuba daga idon Malam Balarabe. Hankalinta ya kara tashi, muryar ta na rawa ta ce,"Don Allah Malam ka daina zubda masa hawaye, bakin da ka yi masa ma kadai ya ishe shi." Bai iya cewa komai ba, ya goge hawaye. Ta sake cewa,"Kwanta ka sami barci, ka barwa Allah komai." A cikin dakin shirun da suka yi, na juyayi suka tsinkayi motsi kamar ana ta6a k'ofa. Umma ta ce,"Malam ba ka kulle k'ofar gidan bane?" Ya ce, "Oho, ni ban sani ba, amma ina ganin kamar na kulle.." Motsi na ke ji." Malam Balarabe ya mike a hankali, ya bude kofa ya fito. Umma na biye da shi. Naseer suka gani rataye da jaka, yana sanda zai fice. Umma ta ce, "Naseer! Ya tsaya cak! Bai juyo ba. A zaton sa sun yi barci, don ba su ji shigowar sa ba. Abba ya ce,"Dama ka daina sand'a ka saki jikin ka, ka yi tafiyar ka yadda ka saba, babu abinda muka isa mu yi ma ka. Maganar barin gari kuwa, in ka so ka koma bangon duniya ka zauna. Ba zai ta6a damu na ba, saboda ba ka da wani amfani a gare ni." Sai dai ina son ka san wani abu. Duk inda za ka je, ba za ka ta6a ganin alkhairi ba. Ka aje wa ranka har abada na sallame ka, kar ka yi tunanin ka na da iyaye., Alh. Basheer kuma ina iya zuwa gobe, in ba shi hakuri. Ka na iya tafiya, in kulle gidana." Tsaye yayi, ya kasa cira koda kafa daya ce. Ilahirin jikinsa babu inda zufa baya ratsawa. Umma ta ce,"Ka wuce ka tafi, ka bar mu a tsaye." Jakar da ke kafadar sa ta zamo ta fadi k'asa, saboda tsabar rashin kuzari, yasa hannu ya d'auko ta, ya juya a hankali ya koma 6angaransa, ya bude ya shige. Malam Balarabe, ya wuce, ya kulle kofar gida. Suka koma dakinsu. Labarin zuciyar Naseer abin ba'a cewa komai. Kansa cikin guiwa tamkar ya hadiye zuciya, ya mutu. Yanzu shikenan ya tabbata za'ayi masa auran dole? Bai san lokacin daya daddage ya kwarma ihu ba, "Dole! Umma ta tashi zumbur! Tana fadin, "Subahanallah! Menene wannan?Abba ya ce,"Menene kuwa, daya wuce mahaukacin dan ki." Ta nufi kofa tana budewa. Ya ce, "Me zai dame ki? Ki kyale shi ya hadiyi zuciya ya mutu. Kafin safiya, sai in tabbatar daya cika dan halas." Allah Sarki uwa! Bata saurari Abba ba, tayi waje can sashin Naseer. K'ofar falon wangame take, tana zuwa, ta cusa kai. Shi kadai yake madedewar sa tsakar falo, ya dunkule waje daya tamkar mai tsananin ciwon ciki." Ta isa da sauri ta cicci6o shi, fadi take,"Naseer! Kai Naseer tashi ka ji." Da kyar ta samo hankalinsa yayi zuru, yana kallonta. Naseer ka na hauka ne? Daga abin arziki, sai ya zama na tsiya? Kai ba Yaro bane Naseer, ka yi hankali da za ka gane muhinmancin mu a gunka. Amma ka ke kokarin aikata abinda Yaro karami ba zai yi shi ba. Yau har kuka sai da Abbanka. Yayi a kanka, me ka ke zaton zubdar hawayensa zai haifar maka? Yau ko ba ka son yarinyar nan, ai ka dubi girman Babanta daya ce ya ba ka ita. Sannan ka dubi darajar mu iyayenka da mu ka amsa. Ban ta6a tunanin za ka yi mana haka ba Naseer. Don a zota na ka yi hankali, ka daina shirmen baya. Ka sani in har Alh. Basheer ya sami labarin ba ka son 'yar sa, ran sa ba zai masa dadi ba, wannan kuma shine karshen cin mutunci da tozarci a idon jama'a. Saboda haka yanzu na ke so ka bani amsa, shin ka amince za ka auri yarinyar nan? Ya dube ta a yamutse, kwalla ne sharkaf bisa kuncinta. Jikin sa ya k'ara sanyi, zuciyarsa ta raunana, bakin sa na rawa ya ce,"Umma ki share hawayen nan, komai ya wuce. Zan je Kaduna gobe." Ta ce,"Ta so mu je ka roki Abban ka gafara, ran sa 6ace yake da kai. Yayi kuka, yayi maka baki. Hakan bai dace ba, kuma masifa ce babbab a gareka." Ya mike suka fito tare, suka sami M.Balarabe zaune yana juyayin takaici. A natse ya aje guiwoyinsa a k'asa gaban Abba, "Abba ka yi hakuri, ka yafe min." Ya cira ido ya dube shi,"Me zan ce da kai Naseer? Ka riga ka ban kunya, rashin zuwan ka Kaduna a yau, wata magana ce a lullube. Na kuwa san tuni Alhj ya gane nufin ka. Ban yi zato ba,ko ba son yarinyar nan, kamata yaui ka bi umurnina.Idanuwansa suka kara ja. Tabbas yarinya baya son ta, idan ma ana maganar, ji yake kamar ana k'ara dasa masa kiyayyar ta cikin zuciya. Kawai daurewa yayi, ya k'ara k'asnk'antar da murya, ya ce,"Abba na yi kuskure, amma zan gyara, ka yi hakuri don Allah." Ya ce,"Taashi ka koma dakin ka, komai ya wuce., Sai dai ina son ka sani, hankali na ba zai ta6a kwanciya ba har sai ka amshi kyautar Alhj da zuciya daya. Ka so ta kamar yadda mahaifinta ya kaunace ka." Da kamar wuya. Wai gurguwa da aure nesa. Abinda yasa shi yake jinjina kai kenan. Ya ce,"Insha Allahu gobe zan je Kaduna." Kullin da ke zuciyar Abba ya dan warware, ya dube shi da kyau ya ce,"Je ka kwanta. Allah ya kai mu goben lafiya.." Ya mike yana fadin,"Amin. Umma sai gobe." Ta amsa masa. Ya wuce sa shin sa." Karfe takwas na safiya. Sageer ke sallama tsakar gidan su Naseer. Umma ta fito daga kicin tana amsawa." Sageer, in ce dai lafiya ko? Ya ce,"Lafiya lau Umma. Jiya da daddare Naseer yayi min waya ya ce zan raka shi Kaduna." Ranta yayi fari sol! Ta ce, "To madalla." Suka gaisa, sannan ya wuce falon su, ya gaida Abba. Shi ma ya ji dadin abin. Take nan zuciyarsa ta yarda da Naseer. Daga nan sashin Naseer din ya wuce. Kofar a bude, yayi sallama ya shiga. Yana zaune saye da bugaggiyar shadda, ruwan ganye mai duhu.Duk da fuskar sa babu walwala, kallo daya za kai masa, ka tabbatar da yayi kyau ba kadan ba. Safa yake sawa a lkcn da ya amsa sallamar, ba tare daya kalle shi ba. Haka kuma daga nan bai sake cewa da shi komai ba. Shi ma Sageer din shiru yayi yana kallonsa, ya gama sanya safa, ya janyo bakaken takalmansa koba, ya sa. Hular sa da ke gefe, ya mika hannu ya dauko, ya riqe ta a hannu. Mu je ko? Ya cewa Sageer, yana duab sa. Ya ce, "Dora hular mana." Ya dora. Sageer yayi dan murmushi, ya ce,"Ko yau ka ke angwanci, iyakar ta kenan. Babu makusa na Zarah angon Nusaiba." Fuska daure ya ce,"Ka yi shiru, ya fi alkhairi akan zancan da ba za ka faranta min rai ba." " 'Yar fara'a yayi. kafin ya ce,"Naseer kenan.A zatona maganar ta wuce, sai zancan shagalin biki za mu sa a gaba?.. Zaharaddeen Shomr Whatsapp 08168575100 Ajininsa yake 1-11 Posted by ANaM Dorayi on 11:36 PM, 11-Nov-15 Under: Ajininsa yake _______ NA ZULAIHAT SANI KAGARA_______ . .Ya ce,"Biki kuma shine a gaban ku, tunda Naseer ya bi umurni. Za ku rabashe na ke gaya ma, bikin 'yar (Dabai Motors) tilo. Amma zuciya ai dole a bar wa mai ita ko? Sageer bai son jin maganar, don haka ya ki tankawa, haka bai hana shi Naseer din yayi shiru ba,"Ba ka ce komai ba? Yakamata ka ce wani abu, magoya bayan karya." "Karya? Karya ce mana. Ni kuwa na fi son duk abinda za'a yi, a rinka fede gaskiya komai dacin ta. "A'a ba dama ka nuna ra'ayinka, sai ayi ma baki, da zarar an sami matsala kuma, ace ban kyauta ba. Ko ba haka bane? Ya ce,"Haka ne, amma a iya sani na, rakiya Kaduna ka ce zan ma, ban san dalilin wannan musayar ra'ayin ba. Tunda za ka Kaduna. Ina ganin maganar ta k'are, a ba shi a ka amince kawai,. Idan ka gama shirin ina kofar gida." Ya mike ganin zai fita. Naseer ya sha gaban sa, amma kafin ya ce wani abu. Umma ta sawo kai cikin falon. Ita ma haka tayi tsaye, tana kallon su cirko-cirko, kamar zakaru na fada. Sageer yayi sauri ya kar6i katon filas din silba da ke hannun ta. Ta ce,"Menene? Hada baki su kayi,"Babu komai Umma." Naseer ya zarce da fad'in"Anya kuwa za mu tsaya karyawa kuwa? Ta ce,"Ya zama dole, ai da sauran lokaci, don nan da Kaduna, in Allah ya yarda nan da nan ne. Ga ruwan zafi nan, zo ka kwaso sauran abincin." Ta fice. Naseer ya dubi Sageer ya ce,"Zauna in kwaso." Ya zauna yana fadi cikin ran sa," Dan rainin wayau." Tire ya dawo da shi, ya aje, kofuna ne, sai soyayyen dankali da kwai ga biredi a ledar sa. Cikin daki ya shiga ya kwaso gwangwanayen madara da Bonvita. Babu wanda ya tanka wa wani. Ya gama hadawa, ya mika wa Sageeer na shi. Cikin zaman kuramen suka kasance zuwa wani lkc. Shirun Sageer kuma ya dami Naseer, don haka ya ce,"Rabo na da abinci tun karin safiyar jiya. Kamar bai ji shi ba, ya ci gaba da kurbar shayinsa Naseer ya dube shi a dage,"Ina magana, ka na banza da ni. Ni na fi ka iskanci Wallahi. Ya kwado masa harara, ya ce,"Dama ni ba dan iska bane, kai ma ka san wannan. Allah daya hada ni da kai, shi zai raba ni da kai, in huta."Ya ja dogon tsaki,"Sai me, sai me kuma? Mts...............Ya aje kofin, ya mike," Ka same ni waje." Ya ce,"Ko kuma na same ka Kaduna ba, na lura duk ka kosa." Ficewa yaui, bai tanka masa ba. Cikin mota haka suka zauna dunkum! Sageer ke tukin, abin yayi masa dai-dai, domin gaba daya ya tattara hankalinsa ga tukin, shi kuwa Naseer tunanin sa me zai cewa Nusaiba? Ta yaya zai fuskance ta? Yadda ba za ta gane komai ba, don gudun wata matsala? Wadannan tambayoyi sun sa shi yana jin kamar ya ce wa Sageer su juya. Amma babu hali. Ransa ya kara kuna, ya cika da kunci. Zarah ce kadai za ta iya share masa zuciya, ga shi tana makaranta, babu halin daukar waya, balle ya kira ta, ya dan ji sanyi a ransa. Saboda haka ya bude sakwanin (Text) din ta, yayi ta karantawa. Kawai ji yayi Sageer na fadin,"Ina mu ka nufa ne? Ya cira kai, ya duba, suna cikin Kawo. Ya duba agogansa k'arfe 10:30am. Ofishin Alhj suka nufa. Bai jima da isowa ba, lokacin. Suna ta musayar fara'a, har suka zauna. Gaisuwa cikin mutunci da girmamawa suka yi wa Alhj. Shi kansa Alh cikin jin dadi yake a yanayin da ya ga Naseer, tun daga shigar da yayi ya zuwa dauko abokin sa da yayi. Abin ya burge shi. Hakan kuma ya nunar ,masa da amincewar Naseer dari bisa dari. Wani dadin farin cikinsa, shine samun goyon bayan Nusaiba da mahaifiyarta, baya dawowarsa, yayi masu bayanin s 2 ne 'yan matan da Naaseer din zai aura lokaci guda. Shi yasa yake cikin nishadi, zuciyarsa kamar gonar auduga. Cikin kunya Sageer ke cewa." Da tun jiya muka so zuwa, to ni ina makaranta, shine nace yayi hakuri, yau mu zo in taya shi godiya. Gaskiya mun ji dadi Alhj. Mu kuma ya ba mu Ikon rike amana." Alhj ya ce,"To Amin. Ni ma na ji dadi,." Ya maida kallon sa kan Naseer ya ci gaba,"Akwai gida a (Hanwa Low-cost) nawa, shi zan ba ku, ku zauna. Akwai motoci guda 2, su ma sai ranar tarewa za'a tare da su. Sannan kar ka manta da maganar da mu ka yi akan makaranta, ina jiranka."A lokacin da yake kara nuna kaunar sa ga Naseer. Shi dan gogan tunaninsa daban ne. Domin kuwa cikin ransa yake saka wadannan kalamai,"Lallai Alhj dan siyasa ne. Ai na dade da sanin wannan wayon masu kudi. Da za'ara 'ya'yan su sun rasa miji, sai a sami wani mai yunwa a lika masa, a ba shi gida da mota. Shi kenan an kama shi a hannu, sai yadda aka yi da shi. Allah ya hada ka da Naseer, mu je a siyasar." Kayataccen murmushi yayi, suna kallon juna da Sageer kafin ya ce,"Ban san avinda zan ce ba Alhj. Na gode." Ya fadi yana dan rankwafawa, Sageer ya taya shi godiya. Bakin Alh. Basheer baya rufuwa, ya ce,"Kauna ce Naseer, kar ka ji komai ni Babanka ne. Yaya sunan ita waccan 'yar tawa? Ya shafi keya, ya ce, "Zarah." Yayi murmushi ya ce,"Ashe kanwata ce, shi ke nan ga Nusaiba ga Antin Jordan. To Allah yasa albarka." Sageer ya ce, amin. Suka yi shiru na 'yan dakikai, kafin Alhj ya lura, kamar kunya duk suke ji, don haka ya ce,"Za ku karasa gidana ne? Sageer ya amsa, "Eh." Ya ce, "O.K., to ku na iya tafiya, zan kira Nusaiban, in gaya mata ku na tafe." Sageer dai ke magana,"To mun gode." Suka mike, suna k'ara godiya, suka yi waje. ******************* (Go slow) ne ya 6ata masu lkcn bisa hanyar su ta zuwa unguwar Rimi, sakamakon mutuwar wata babbar mota akan titi. Naseer ya ja dogon tsaki, saboda takaicin zaman da suke a mota, ga rana ta fara zafi. Sageer ya dube shi ya kauda kai. Tuntuni yake son yi masa magana a kan alkawuran da Alhj yayi masa, watau gida da canjin mota, amma yayi shiru, saboda yana gudun 6acin rai. Shi yasa ko yanzu da ya ci birki da yin dogon tsakin sa, kallon sa kawai yayi, ya kyale. Da kyar da ji6in goshi suka sami wuce dogon cunkoson motocin. Sannan suka fada titin da zaikaisu kayatacan gidan Alh. Basheer. Nusaiba ma gab da kammala shirin ta, lkcn da Baba Mai gadi yayi sallama ya kira Mariya mai aiki, ya ce ta gaya wa Hajiya bak'i sun zo. Sama Mariya ta haye ta shaidawa Ummi, ita kuma ta umurce ta da kira mata Nusaiba. Jimawa kadan Nusaiba ta shigo, ita kanta Ummi sai da gaban ta ya fadi, saboda tsabar iya adon Nusaiba,Komai ta sa yana amsar jikin ta. Wani lallausan farin les ne ke jikin ta, wanda aka yi wa ado da zare kalar samaniya. Shi yasa hatta abin wuya, da 'yan kunnenta, kalar samaniya ne. Haka nan warwaraye, sai bungus din su da ke hannunta na hagu. Haka takalmin kafar ta suke irin daya da gyalen da ta yafa, wanda gaba daya ta tattara launanin farin ciki, ga duk wanda ya kalle ta. Tamkar yadda ko wace zuciya ke a ji a duk lokacin da samaniya tayi luf-luf! Cikin wannan launin mai sanyaya idanuwa. Ummi ta dafa ta ta ce,"Naseer ya iso, ki maza ki kai shi babban falo, a kai masa duk abinda ya dace. Ta ce,"To Ummi." Tana kallonta. Ki tafi mana, ko sai na ce kin yi kyau? To kin yi kyau Bebin Abba." Da sauri ta juya cikin hanzari ta bar dakin dauke da murmushi, bisa fuskarta. Ummi ta kada kai ta ce,"Allah sarki Bebin Abba. Allah yayi miki albarka.." Su Naseer na tsaye jingine da mota, inda suka yi fakin a harabar aje motoci. Nusaiba ta danno, tana takawa d'ai-d'ai. Gaba dayan su sai da suka rasa kuzari. Kwarai Nusaiba tayi wa Naseer kawarjini a idonsa har yasa jikinsa yayi sanyi, sai dai cikin zuciyar sa Zarah ta riga ta kame, ko

Chapter 10 of 11