Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani harafi hakkinsa yace.
“A halin yanzu kun bar zamaninku matasa, a yanzu kuna zamaninmu ne, a ƙalla shekaru 1000 baya!”
Wani abu ne ya bada sautin tau a ƙirjin Adam, dan zai iya cewa ya riga kowa sauraron shekaru dubu ɗayan da aka furta. Ita kuma Ivana sai ta ji kamar ba ta fahimci abin da yake faɗa ba, saboda kalar larabcin da yake ya sha banban da nasu, nasa kyakkyawan larabci ne irin wanda ke cikin Alkur'ani me girma. Su kuma ba da shi suke magana ba, dan haka kalaman nasa suka mata wuryar ganewa, duk da taso ta gane, amma da ta ɗora maganar a mizanin hankali sai ta ƙi yarda da gaskiyar. Shi ko Arman idonsa ya lumshe kawai, domin tun da ya kalli mutumin ƙwaƙwalwarsa ta fara raya masa hakan, amma ta ya ya ke nan? Ta ya mutumin da yake rayuwa a 21st century zai dawo 11th century?... Taya hakan za ta kansace?...
“Na san cewa ba lalle wannan maganar ta zauna a kanku ba, domin kuna ganin kamar hakan ba me iyuwa ba ne... To yau ya iyu a kanku, kuma wata ƙila ku zamto ababen misali, domin gagarumin abin da za ku tunkara a gaba!”
Dattijo ya sake faɗi. Arman ya buɗe idonsa, sannan ya kalli tsohon.
“Ya za'ayi mu koma gida!?”
Ita ce kawai tambayar da ta zo ransa, dan bayan ita kuma ba ya jin yana da abin faɗe. Tun da ya furta tambayar Ivana ta gaskata abin da datijjon ya faɗa ɗazu, amma ta yaya su da suke rayuwa a zamanin da dogayen gine-gine suka yawaita a ko ina, da wayoyin hannu, da kafafen sada zumunta, da ababen hawan zamani, da ci gaban technology za su dawo rayuwa a zamanin da babu skyscrapers, babu wayoyin hannu, babu ababen hawan zamani, babu... Babu... Babu, babu komai sai yaƙi da rigima a kan mulki!. Shi ko Adam ko motsi bai kuma ba, ya ƙame ne ƙam yana kallon mutumin, saboda shi yana iya jin kyakkyawan larabcin da dattijon ke yi.
“Dogon labari ne, amma zan yi ƙoƙarin gajarce shi, kafin ku koma gida yana da kyau ku san manya manyan masarautu ukun dake mulkin wannan duniya a wannan zamanin!...”
Ta farko MAMLAKATUL MAJDAL, Babbar masarauta ce, wadda a zamanin nan sam babu kamarta, masarautar na da girma da yawan al'umma na ban mamaki. Mutanen masarautar na rayuwa cike da farin ciki da kuma samun ci gaba a ko wani lokaci, domin sun yi sa'a da samun adalin sarki da ya dace da mulkarsu. Masarautar na da tattalin arziƙin noma, kiwo da kuma ma'adanan ƙarƙashin ƙasa, kana gari ne da ya zamto cibiyar kasuwanci.
MAMLAKATUL MAJDAL tana a ta yammacin saharar Majma, ginin masarautar ya sha banban da sauran masarautu, domin a zamanin za'a iya kiran masarautar da ta zamani. Masarautar na kewaye da ganuwa, wadda aka ginata da duwatsu da kuma taɓo.
A batun yaƙi kuwa sun zarce tsara, domin a ƙalla masarautar na da kimanin mayaƙa dubu goma, waɗan da suke a shirya ga mutuwa, ga kuma kayan yaƙi masu firgita abokin gaba. Rayuwa a MAMLAKATUL MAJDAL tana da sauƙi...
Masarauta ta biyu ita ce MAMLAKATUL AFSAH, Babbar masarautar Aljannu dake a cikin gajimare, Masarautar tana da kyau da tsarin gine-gine masu ban sha'awa irin nasu na waɗan da suke ba bil adama ba. A fagen yaƙi su ma ba'a barsu a baya ba, domin suna da dakaru da kuma kayan yaƙin tunkarar duk wani abokin gaba idan yaƙi ya taso.
Masarauta ta uku kuma ta ƙarshe ita ce MAMLAKATUL JIYAD. Babbar masarautar da a masarautun bil adama ta kasance ta biyu. Masarautar da na kyau da kuma albarkatun ƙasa, sai dai kuma sun yi rashin sa'ar shugaba, domin Allah ya hallata musu mugu kuma azzalumin sarki.
Babban sarki me daraja ta farko, wanda bayan shi a iko ƙasaita izza da mulki babu wani a cikin sarakunan wannan zamani, shi ne Malik WASIMUDDEN BIN ABDUL ADAL. Kyakkyawan matashi kuma jarumin yaƙi, sadaukin sarkin da babu me taka shi ya wuce... Shi ne yake mulkin MAMLAKATUL MAJDAL.
A ƙalla shekarunsa talatin da biyar a duniya, ya gaji mulki ne a hannun mahaifinsa, Malik Abdul Adal Abu Wasim, wanda shi ma ya gada daga wurin nasa mahaifin. Ya fara gudanar da mulkinsa tun yana da shekaru asibirin da biyar, hakan ya faru sakamakon mutuwar mahaifinsa a wannan lokacin.
Malik Wasimudeen ba shi ne kaɗai ɗan Malik Abdul Adal ba, domin bayan mahaifiyar Wasimudeen Malik Abdul Adal yana da wata matar, wadda ita ma take da ɗanta na miji guda ɗaya Amir Ehan Ibn Abul Adal.
Malik Wasimudeen adalin sarki ne, wanda yake gudanar da mulkinsa cikin adalci da tausayinsa ga talakawansa, sannan kuma shi dodo ne ga maƙiyansa, ba shi da imani wurin hukunta mai laifi, kusancin dake tsakaninsa da kai ba zai sa ya ɗaga maka ƙafa ba idan har aka kamaka da laifi. A halin yanzu yana da aure, sunan matarsa DANEEN SANAH (Princess Sanah)...
Tarihin yanda wannan aure ya kasance kaɗai abin mamaki ne, domin Daneen Sanah ta kasance 'ya ga abokin gabar MAMLAKATUL MAJDAL, tun zamanin mahaifin Malik Wasimudeen ƙiyayya da mahaifin Sanah ta samo asali. Kuma har zuwa zamanin yanzu da Wasimudeen ke shugabantar masarautar ƙiyayyar ba ta ƙare ba, duk da ya auri 'yarsa kuwa.
Ta wani ɓangaren ma wannan auren shi ya ƙara rura wutar ƙiyayyar, domin Malik Wasimudeen ya auri Sanah ba da son ran mahaifinta ba, amma kuma ita da Wasimudeen suna son juna.
Sarki me daraja ta biyu kuma shi ne MALIK SAFRAZ BIN ANSER, wanda yake mulkin MAMLAKATUL AFSAH. A tashin farko ba za'a kirashi da adalin sarki ba, kuma shi ba mugu ba ne, amma za'a aje shi a sahun masu yin mulkin taka haye. Wanda bai gaji mulki ba, sannan bai iya gudanar da shi ba.
Asalin sarautar ba tasa ba ce, ba kuma ta mahaifinsa ba ce, sarautar ta kasance ta MALIK DHAAKIR BIN AQEED. Babban sarkin aljannu da ba'a taɓa kamarsa ba. Kaf duniyar nan Malik Dhaakir ɗansa ɗaya, wanda matarsa ta haifa masa shi. UWAIS BIN DHAAKIR, Feroza mahaifiyar Uwais ta kasance bil adama, yayin da Dhaakir ya kasance daga jinsin jinnu, hakan ya sa Uwais ya mallaki ƙudurat guda biyu. Ya kan iya yin duk abin da bil adama za su yi, sannan ya kan iya yin wasu abubuwan na aljannu, amma kuma jinsinsa ya fi ƙarfi a bil'adama,
domin

hatta

suffarsa

ta

bil'adama

ce.

A
ƙa'ida

Uwais

shi

ke

da

gadon

wannan

kujera

ta

mulki.
Amma sai Safraz da mahaifinsa Anser suka shirya maƙarƙashiya, domin ƙwace mulki a hannun Malik Dhaakir. Sun shirya kashe shi yayin da suke tsaka da wani yaƙi. Kuma shirin nasu ya tafi yanda suke so.
Domin sarki Dhaakir ya mutu a wannan yaƙi, bayan mutuwarsa kuma suka shiga aiki kan shirinsu na biyu, wato yanda za'a yi mulki ya dawo hannunsu. Lokacin da 'yan majalissar sarki suka zauna suna tsara wanda ya kamata ace ya zama sarki bayan rasuwar Malik Dhaakir Safraz da mahaifinsa Anser suka bijiro da wata magana.
Ta cewa a shekarun Uwais a wannan lokacin bai kamata ace ya zama sarki ba, domin a lokacin bai fi Shekarau 9 ba, kuma suka ƙara da cewar sam bai kamata bil'adama ya mulki aljannu ba, ai hakan ma zai zama kamar cin fuska ne ga jinsinsu, sannan hakan zubar da ƙima ne.
Haka suka hurewa aminttatun sarki kunne, waɗan da suka ƙi kuma suka basu cin hancin dukiya, har sai da aka amince da sarki na gaba shi ne Safraz. Lokacin da wannan labari ya iske Feroza sai ta ɗauki ɗanta ta gudu ta bar Masarautar.
A lokacin babu wanda ya damu da tafiyarta, sai a ranar da za'a tabbatar da Safraz a matsayin sarki aka zo naiman takobin sarki na mulki aka rasa. Domin Feroza ta ɗauke shi ta gudu, Kasancewar tun kafin Malik Dhaakir ya rasu ya mallakawa ɗanta Uwais shi.
Hakan ya sa aka naɗa Safraz mulkin, amma kuma har yanzu bai zama cikakken sarki ba, domin sai ya mallakai wannan takobin ne zai zama cikakken sarkin MAMLAKATUL AFSAH. Hakan ya sa har zuwa yau hankalinsa ya kasa kwanciya, domin bai huta ba ya ci gaba da naiman Feroza a duniya ruwa a jallo, domin ya ƙwace wannan takobin da ta gudu da shi.
Sarki me daraja ta uku shi ne MALIK CANGAZ, wato mahaifin Daneen Sanah, matar sarki Wasimudeen, kuma shi ne yake mulkin MAMLAKATUL JIYAD. Babban burin Malik Cangaz a duniya bai wuce kada ya tsufa ba, ko kaɗan sarkin ba ya son ya tsufa, duk da a shekaru a ƙalla ya kai sittin da ɗori.
Hakan ya sa idonsa ya rufe ya shiga naiman bokaye da nalaman tsubbu, domin naima masa maganin tsufa a duniya. Duk da magungunan da ake ba shi na sakawa ya dawo yaro ba hakan ke hana jikinsa nuna tsufa ba a wasu lokutan. Domin idan yau ka ganshi yaro, gobe sai ka ga ya rikiɗa ya dawo tsoho.
Kuma sam shi hakan bai masa ba, shi yasa ya ci gaba da naiman maganin tsufa a duk inda yake, da haka har ya samo wata ƙofa, wadda aka sanar masa da cewa daga zarar ya buɗe ƙofar nan ya shiga, da zarar ya fito babu shi babu komawa tsoho har zuwa lokacin mutuwarsa.
Sai dai wannan ƙofar a kulle take, kuma babu wanda ya san inda makullin ƙofar yake. Babu wanda ya taɓa buɗeta, ballantana har a san abin da ke cikinta. Sai dai duk da haka Malik Cangaz bai sare ba, ya sa an kawo masa ƙofar, ya ajeta a cikin masarautarsa, yana naima tare da binciken inda mukullin ƙofar yake, amma har zuwa yau bai samu ba.
Malik Cangaz azzalumi ne na gaban kwatance, domin ko kaɗan ba shi da imani. Bai san tausayin takala da na ƙasa da shi ba, ba shi da wata suffa ta shugaba na gari. Tsabar zalunci irin na sarkin haka kawai sai ya bushi iska yasa dakarunsa su je su tashi wasu ƙauyinka da ba'a yankinsa suke ba, domin kawai a samo masa bayi, ko a samo masa albarkatun ƙasa.
Yana da dakaru na ban mamaki, waɗan da ya shayar da su ruwan zalunci, domin kamar yanda yake haka ya horesu. Uwa uba kuma kuma ga ƙarfin tsafi da yake amfani da shi wurin yaƙar duk wani wanda ya gagare shi.
Tsabar son duniya da son mulki irin na Malik Changaz ya sa ya kashe matarsa a ranar da ta haifa masa yaransa mata 'yan uku, domin bokansa ya sanar masa da cewa yana buƙatar jininta domin haɗa masa wani tsafin da zai dawo da shi matashi. Hakan ya sa har wa yau ba shi da mata, sai yaransa mata 'yan uku.
Ta farko ita ce Daneen SANAH, wadda soyayya ta ƙullu tsakaninta da Malik Wasimudeen har ta kaisu ga aure, sai kuma Daneen ASRA. Wadda son zuciya irin na Malik Changaz ya sa ya tsafaceta, ya sauya mata tunani da kuma alƙibila. Ya mayar da ita karen farautarsa, domin ko yaƙi zai je tare da ita yake tafiya. A cewar bokansa idan har ta ci gaba da zama a matsayin me ba shi kariya babu wani mahaluƙin da ya isa ganin bayansa.
Duk da ita sam Daneen Asran ba ta so, domin yana juya mata tunani da hankali ne kawai. Ya mayar da ita jaruma, domin kaf cikin su ukun babu wanda ya kaita iya sanin salon yaƙi da kuma faɗa, Daneen Sanah ita ce kawai za ta iya kaita a wurin sanin makamar yaƙi, domin ita ma jaruma ce ta gaske.
Ta ƙarshen kuma ita ce Daneen IQRAH, wadda ita ce ta kasance zinariya a 'ya'yansa, domin ita ko faɗa da koyon yaƙi bai bari an koya mata ba, a cikinsu ita ce shalele, ita ce wadda aka shagwaɓa da gata da kuma riritawa irin ta 'ya'yan Sarauta, hakan ya sa ta zamto gimbiyar ta gaske.
Duka yaran Malik Changaz babu wadda bai tsaface ba, su duka ukun suna da ƙarfin tsafi a jikinsu, musanman ma Asra, domin ita nata ya fi na kowa, ita kuma Iqra ba ta da shi sosai, domin ba ta cika amfani da shi ba. Yayin da na Sanah ya zame mata alaƙaƙai, domin a halin yanzu so take ta rabu da shi, amma ta kasa, saboda ta hanyarsa Changaz yake aiko mata da jinya iri-iri. A cewarsa yana hukuntata ne a kan laifin da ta aikata na bijire masa...
“...Waɗannan su ne masarautu da kuma sarakunan da suke mulkin wannan duniyar a wannan lokacin”
A lokacin da ya kai ƙarshen dogon tambihin nasa Adam ya fashe da kuka yana dafe kansa, dan tun da ya fara jin labarin ya san cewa shikenan kuma, shi tasa ta ƙare, domin ba makawa sai ya mutu a cikin wannan duniyar. Ita ko Ivana hawaye ne suka soma zubo mata, na tunawa da Yumma, Hana da Imran, da kuma Uwais, dan ta fara tunanin shikenan ta yi bankwana da su. Arman ne ya daure ya sake tambayar tsohon.
“Ya za'ayi mu koma gida?”
Ya sake nanata tambayar da ya yi ɗazu. Tsohon ya nisa, sannan yace.
“Na san abin da zan faɗa yanzu zai firgita ku fiye da zato... Wannan ƙofar dake cikin masarautar Malik Changaz ita ce ƙofar da za ta mayar da ku gida!”
Arman ya rintse idonsa, domin da ma shi ne abin da yake hasashe.
“Ta ya za'ayi mu buɗe ƙofar da ba'a taɓa buɗeta ba?”
Ya sake yin ƙarfin halin yin tambayar, a wannan karon dattijon murmushi ya yi, sannan ya nuna Arman da ɗan yatsa.
“Wannan sarƙar da ke wuyanka, ita ce makullin ƙofar!”
Ivana da Adam dake kuka suka dube shi baki buɗe, shi kansa sai da ya yi mamaki, sannan ya kai hannu ya taɓa mukullin dake jikin sarƙar.
“Kana nufin wannan?”
Adam ya tambaya yana nuna sarƙar, datijjon ya jinjina musu kai.
Cike da ƙarfin hali Arman ya miƙe tsaye.
“Zan je, kuma zan fuskanci Malik Changaz, zan tabbatar da na buɗe wannan ƙofar, domin mu koma gida.”
“Ka yi hauka ne Arman? Saboda kai sirikinsa ne sai ka je ka ce masa ya buɗe maka ƙofar kai da abokanka za ku koma gida, ai ku matafiya ne, kun ɓata a hanya, saboda shi kuma shashashan afirilu ne sai ya matsa ya baka ƙofar cike da girmamawa?...”
Faɗin Adam yana miƙewa, sannan ya nuna shi da ɗan yatsa.
“Yanzu fa ba a 21st century muke ba, mun dawo zamanin baya ne, zamanin da ake kisan wulaƙanci a kan mulki! Zamanin da uba zai kashe ɗansa a kan mulki. Mutumin da bai ƙyale 'ya'yansa na cikinsa ba shi ne zai ƙyale mu saboda mu ba daga zamaninsa muke ba? Ka yi tunani mana!”
Arman ya yi shiru kawai, a idonsa yake hango wahala tare da tarin ƙalubalen da za su fuskanta kafin cimmawa komawa gida. Ya kalli Ivana.
“Ivana shin kin yarda da ni?
Ivana na goge hawayenta ta gyaɗa kanta har sau biyu, ya juya ya kalli Adam.
“Adam ka yarda da ni?”
“Na yarda da kai amm...”
Ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu.
“Eh ko a'a?”
Adam ya jinjina kai.
“Na ɗauki alƙawarin tunkarar Malik Changaz, ko da kuwa zai kasheni, ruwa, iska sanyi ko guguwa ba za su dakatar da ni ba wurin cimma hakan. Tabbas zamu fuskance shi, idan ta kama zan yaƙe shi, domin mayarda ku gida, zan sadaukar da raina domin ku rayu, na ɗauki wannan alƙawarin, kuma babu abin da zai dakatar da ni wurin cika shi....”
_The game starts now!🔥_
Salma

Ahmad

Isah

✍️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.

🪄

...JUYIN

KWAƊO...🪄
©️Salma

Ahmad

Isah

SalmaAhmadIsah

@ArewaBooks
SalmaAhmadIsah

@Wattpad
Page-9
“Wannan shi ne kaɗai abin da zan iya taimaka muku da shi”
Cewar datijjo me ban al'ajabi yana miƙawa Arman wata takarda dake naɗe, wadda aka yi ta da fatar akuya. Kansa ya juya ya kalli Adam da Ivana dake tsaye a gefe, kowannensu goye da jakarsa, dan sun ɗauki ɗamarar tafiya yanzu ba sai anjima ba. Hannu ya sa ya karɓi takardar, kafin ya buɗe takardar tsoho ya soma faɗin.
“Wannan ita ce taswirar da za ta nuna muku hanya...”
Adam da Ivana suka matso suna kallon taswirar da Arman a buɗe.
“Duk wata hanya ko daji da kuka ga a kan takardar nan sai kun bi shi, za ku tsallake abubuwa masu tarin yawa a hanya, ban ce babu ƙalubale ba, ban kuma ce akwai zallar wahala ba, ban ce babu farin ciki ba, kuma ban ce akwai baƙin ciki ba... Abu ɗayaa na sani, hi ne kafin ku kai ga gaci za ku sha baƙar wahala!”
Su duka uku suka dubi juna, kafin Adam yace.
“Mu da za mu nufi Masarautar Jiyad me ya haɗa hanyar mu da Masarautar Majdal?...”
Ya tambaya domin ya ga zanen sunan masarautar a cikin taswirar cikin harshen larabci. Dattijo ya yi murmushi.
“Har Mamlakatul Afsah sai kun je, babu buƙatar na faɗa muku ta yaya kuma yaushe ne hakan zai faru, wata ƙila hakan zai rage muku armashin tafiyar, na tabbatar nan da wani lokaci ku da kanku za ku bani labarin abin da ya faru daku idan Allah ya nufi saduwarmu da ku a nan gaba, sannan akwai wani abu gudu...”
Ya ɗan yi fasali yana shafa farin dogon gemunsa, sannan ya ci gaba da faɗin.
“Ƙauyen Askar shi ne ƙauye na farko da za ku fara shiga bayan kun bar nan, tafiyar dake tsakanin nan da garin a ƙalla ta kai kwana uku a ƙafa, idan kuma a doki ne kwana ɗaya da yini ɗaya... Abu mafi muhimmanci shi ne mutumin da za ku haɗu da shi a can. A farkon garin akwai wani ɗan ƙaramin gidan ƙasa, nan za ku fara shiga, idan har kun shiga za ku iske wata tsohuwar mata, sai ku bata wannan taswirar, daga zarar ta ga taswirar ita za ta sadaku da abokin tafiya!”
Suka yi shiru, domin duk cikinsu babu me abin faɗi kuma, tun da har rayuwa ta yi JUYIN KWAƊO da su sun riga sun karɓi hakan a matsayin ƙaddara. Tsoho ya ɗauko wata jaka ya miƙawa Adam, Adam ya sa hannu ya karɓa cike da naiman ƙarin bayani.
“Akwai dabino da busasshen nama da kuma kubuz a ciki, zai isheku ku ci har na tsawon kwana uku da za ku yi kuna tafiya. Idan har kun isa Askar kuma naiman abinci ya ƙare, domin abokin tafiyar da za ku haɗu da shi a can shi ne zai ci gaba da kula da cikinku da ma lafiyarku!”
Adam ya rataya jakar a kafaɗarsa, lokacin da tsoho yake bawa Arman wani takobi dake cikin gidansa.
“Za ku buƙaci wannan a hanyarku, na san kai kaifi dacewa da iya sarrafata, ka kula JAGORA!”
Ya ƙara kiransa da sunan da ya kira shi da shi ɗazu, tun da Arman ya kalli takobin abu ɗaya ne ya faɗo ransa, wata rana, wata magana da ta taɓa shiga tsakaninsa da Gulzar.
_
“Daga an yi magana sai ka ce kana zuwa fencing class, bayan ko takobin gaske ba ka taɓa riƙewa ba!...”_
_
“Wata rana zan riƙe”_
Ita ce amsar da ya bata a lokacin, yanzu kuma ga ranar ta zo, cike da martabawa ya sa hannu biyu ya karɓi takobin, wani abu mafarkinsa, wani abu burinsa, wani abu da yake matuƙar son ya cimma a rayuwa, wato mallakar takobin da ba na fencing ba. Ya ɗan ɗaga takobin sama kaɗan, sannan ya zaroshi daga cikin gidansa, ƙyallin takobin ya haska a cikin rana, hakan ya sa ya dalle masa ido da har sai da ya rintsesu, a hankali ya sauƙe takobin yana ƙare masa kallo...
Wani mafarki da ya saba yi na yaƙin nan da yake na tariyowa kansa a cikin tunaninsa, wato dai wannan mafarkin da ya daɗe yana yi yana da nasaba da wannnan JUYIN KWAƊON da rayuwa ta yi da su?. Daga ruwa zuwa ruwan zafi, takobin ya mayar gidansa, sannan ya kalli datijjo dake ta fara'a.
“Mun gode sosai”
Ya girgiza kansa.
“Ni ya kamata ace na gode muku, domin zuwanku yau ya sa na sauƙe nauyin dake kaina, fatan nasara”
Ya ƙarashe yana dafa kafaɗar Arman guda ɗaya, Arman ya gyara zaman glashinsa, sannan yace.
“Mene ne sunanka?”
A wannan karon kuma dariya ya yi.
“Babu buƙatar sanin sunana yanzu, domin akwai yiyiwar sake haɗuwarmu a nan gaba, ku je, Allah ya bada sa'a.”
Daga haka suka juya suka fara tafiya a kan hanyar da ya nuna musu, kowa a cikinsu jikinsa a sanyaye yake, ban da Arman, wanda ya sa fata da yaƙinin cewa ko ba yau ba tabbas za su koma gida, kuma zai tabbatar da hakan!.
Sai da suka yi nisa sosai, sannan datijjon nan ya soma ja da baya, ya tsaya a gaban bukkarsa, ya lusmhe idonsa yana taɓa jikin bukkar, nan da nan bukkar ta ɓace, kamar ba'a taɓa hallitar wata bukka a wurin ba. Ya buɗe idonsa yana murmushi, sannan ya daka tsalle, kafin ya dire ya bi iska ya ɓace.
Sun ɗauka cewa tafiyar mai sauƙi ce, dan tun da suka kama hanya ba su tsayawa sai idan sun lura da lokacin sallah ya yi, kuma daga sun tsaya sun gabatar da sallahr za su ci gaba da tafiya, duk da jikin kowanne a cikinsu a sanyaye yake, Arman ne kaɗai ke ƙokarin ƙarfafa musu gwiwa. Ba su tsaya yada zango ba sai da dare ya yi, shi ma a cikin dokar daji suka kafa tantinsu guda uku.
Amma ba su shiga sun kwanta ba, suka zauna a waje suna jin ɗumin wutar da suka hura. Sai a lokacin Adam ya buɗe jakar abincin da tsoho me abin al'ajabi ya basu, ya shiga fitar da kayan ciki.
“Ni dai ba na jin zan iya cin wannan abincin”
Faɗin Adam yana nunawa Arman, Arman da ya nutsa duniyar tunanin 'yan uwansa ya dube shi.
“Za ka ci idan har abincin da muke da su suka ƙare”
Adam ya yi shiru kawai... Ita kuma Ivana na gefe tana duba service ɗin wayarta babu ko ɗaya, chajin wayar ma ya kusa ƙarewa.
“Ba service, ba wutar nepa, babu abincin da muka saba ci, babu komai na more rayuwa!”
Cewarta tana aje wayar, dan ta ga babu amfanin da za ta mata.
“Ba ki da chaji ne?”
Adam ya tambayeta, ta jinjina masa kai.
“Ina da solar, gobe sai ki yi chajin”
Ta sake jinjina kai tana shan tea ɗin da suka dafa.
“Ban taɓa tunanin cewa zan wayi gari na yi rayuwar da babu abubuwan ci gaban zamani ba, wai ashe akwai lokacin da rayuwa za ta juya mana mu kasance a halin da ba mu isa mun yi communicating with wani ba?”
Faɗin Adam yana rufe system ɗinsa.
“Duk abin da zai faru damu a gaba ba mu da masaniyarsa, ba mu da ikon canza komai”
Arman ya ba shi amsa.
“Kuma ka san ina ga kamar wannan babbar dama ce na samu da zan ɗauki hotunan abubuwan da babu photographer ɗin da ya taɓa gabatar da su, masarautun mutanen da, al'adu da shigarsu da ma abincinsu!”
“Ƙwarai, kuma ina ga kamar wata dama ce da za ta sauya tunanin Arman a kan Alhadi!...”
Adam da Arman suka dubi Ivana da ta yi wannan furuci cikin mamaki...
“Ke! A wannan duniyar fa ba su san masana'anta ba ballantana babban kamfani kamar Alhadi, ta ya za'a samu wani kamfani da zai sa Arman ya sauya ra'ayinsa kafin mu koma gida?”
“Masarautun zamanin nan suna kama da kamfanunuwan zamaninmu!”
Ta basu amsa, suka sake duban juna, amma shi dai Arman bai ce komai ba. Har suka gama zaman hirar suka koma cikin tent ɗinsu suka kwanta, cike

Chapter 9 of 13