tare da aje wayar, sannan ya yi wa motar key yana kunna wata waƙar Sa'ad Lamjarred da Elissa me taken Min Awal daƙiƙa. Da haka ya koma gida, ya je ya ɗauko 'yar rigimar tasa, sannan ya nufi Dubai Mall. Sai a lokacin ya lura da shigar da Gulzar ɗin ta yi. Wasu pink Chickankari (Pakistan) ne a jikinta. Rigar kayan da ta kusa taro wandon tsayi na ɗauke da ratsin sea green daga ƙasa, hakan yasa mayafin kayan ma ya kasance net sea green, wanda ta yafa shi a kanta, ammma duk da haka bai hana dogon gashinta bayyana ba.
“Gul”
Ya kira yana duban hanya, ta ɗago daga barin kallon wayarta ta dube shi.
“Umm”
“Su kuma waɗannan kayan fa?”
Ta dubi jikinta.
“Mi ye laifinsu?”
Ta tambaya, ba tare da ta hangi makusar kayan nata ba.
“Amma Aii (Mahaifiyar Immi dake Pakistan) ce ta aiko miki da su?”
Gul ta ƙanƙace ido tana kawar da gashin da ya kwanta mata a gefen fuska.
“Wato ni ba zan iya siyan Chickankari da kaina ba sai Aii ta aiko min ko?”
Arman ya yi dariya, dan da ma abin da yake so ke nan. Ita ma da ta gane cewa kunnata yake son yi sai ta ɗauke kai tana duban wurin da suke nufa.
“Akhi ni fa Mall of the Emirates zan je ba. Dubai Mall ba”
Ya dubeta.
“Shi Dubai Mall ɗin mi ye laifinsa. Na ga ko Immi a nan take siyayya”
“La (No) ni ba zan je can ba, yau Mall of the Emirates nake son zuwa”
Arman ya girgiza kansa. Sannan ya juya kan motar zuwa wata hanyar da za ta fi saurin sadasu da Dubai Mall ɗin da take son zuwa. Siyayya ta yi kamar ba ta masu hankali ba, dan kaya ta yi ta jibgowa kamar da za'ayi bikin aure ba na ƙarin shekara ba. Shi dai Arman bai isa yace ƙala ba, tun da Abby ne ya ɗaure mata gindi, don hatta da kuɗin siyayyar ma shi ya biya, yau da safe tace za ta je siyayya, dan haka ya bata ɗaya daga cikin ATM cards ɗinsa.
Yayin da kowa na ahalin Alhadi da sauran 'yan uwan mahaifiyar Arman da suka samu zuwa tun daga Pakistan ke shirya masa kyakkyawar liyafa ta taya shi murnar ƙarin shekara. Shi da su Adam kuwa na can suna shirya tafiyarsu zuwa Germany. Shi da kansa yay musu booking flight, daga Dubai zuwa Germany, wanda zai tashi a daren da zai cika shekaru 32 a duniya. Kuma a ɓoye yaje ya yi siyayyar wasu kaya da zai buƙata a tafiyar tasa ba tare da ya bar kowa na ahalinsa ya sani ba.
Hannu ya sa ya buɗe wata drawer dake kusa da dressing mirror ɗin ɗakinsa. Ban da glasses iri-iri babu komai a ciki. Gaba ɗaya glasses ɗin cikin drawern irinsu ɗaya, domin duka farare ne, masu ɗauke da square frame, banbancinsu kawai shi ne rims ɗin da suka zagaye frame ɗin glasses ɗin. Dan kaloli ne birjit, kuma ko wace kala akwai kayan da yake sakawa da shi, shi yasa adadin glasses ɗinsa suka wuce ɗaya, amma kuma ya fi saka mai farin rims da kuma mai baƙi.
Glasses biyu kawai ya ɗauka, dan ba ya jin za su yi wata daɗewa a can da har zai ɗaibi sama da uku, har wanda yake tare da shi a yanzu. Wani kit ya ɗauka ya saka glasses ɗin duka biyu a ciki, sannan ya dawo kan gadonsa, inda jakar kayan da yake haɗawa take, ya saka kit ɗin a ciki. Kuma yana saka shi ya zuge jakar, domin ya gama saka duk wani abin buƙatarsa a ciki.
Sauƙewa jakar ya yi daga kan gado, ya jata zuwa ƙofar bathroom ɗinsa, da nufin idan an jima kaɗan zai saka ɗaya daga cikin masu aikin gidan ya fitar masa da ita waje.
“Aki Wainak? (Yayana kana ina)”
Da sauri ya fito daga wurin, jin Gulzar na ƙwala masa kira, tsaye ta yi tana kallonsa. Dan alamu sun nuna cewa wani abu yake ɓoyewa.
“Mi ye?”
Ya tambaya cikin son waskewa tambayoyinta. Ita da yake akwai abin da ya kawota sai ta manta da wannan batun, tace.
“Su Rahma ne suka zo...”
Cikin rashin fahimta ya kalleta.
“Wace ce Rahma?”
“Mts ƙawata da take Riyadh, ta zo ne domin tayaka murna”
Sai ya dage girarsa duka yana kaida kai.
“Ohh na gane”
“Me kake ne?”
Ta tambaya tana kallon dressing table ɗinsa da yake a hargitse, domin gujewa zargi sai ya ɗauki hair dryer ya shiga busar da gashin kansa da babu ruwa yana faɗin.
“Gyaran kai nake, ke yaushe za ki je a rage miki tsayin wannan gashin naki”
Gulzar ta kalle shi tana taɓa dogon gashinta.
“Ai ba zan taɓa yanke wannan gashin ba”
Ya taɓe baki yana aje dryer, sannan ya ɗauki comb ya shiga taje sumar da take sama, kafin ya juyo ya kalleta.
“Su waye suka zo kuma bayan ƙawarki? Na ji hayaniya ta ƙara yawa a ƙasa”
Ta ɗage kafaɗunta.
“Ban sani ba, amma mu je mu gani”
Ta ƙarashe maganar tana juyawa, ya aje comb ɗin da ya ɗauka ya bi bayanta. Ko da suka sauƙa ƙasan ba kowa suka ga ba face 'yan uwan Abby na Qatar da suka samu isowa. Duk dangi sun zo, kai kace bikin aure za'a yi ba na ƙarin shekara ba. Duk waji abu da suke Arman kallonsu kawai yake, dan gani yake kamar ihu suke bayan hari, a ganinsu bai san abin da suka shirya ba, shi ya sa wasu daga cikinsu ke farin cikin zai zama shugaba ba tare da sun furta ba. Amma shi ya san farin cikin na miye, kuma zai musu albishir na wannan burin nasu ba zai taɓa cika a yanzu ba...
Tunanin nasa na tafiya kafaɗa da kafaɗa da ƙaddararsa, domin kamar yanda yake ganin cewa ba zai karɓi shugabancin Alhadi yanzu ba yabbas ba zai karɓa ɗin ba, kuma hakan zai faru ne sakamakon ƙaddarar dake jiransu a Bavarian forest. Wadda za ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwarsu, daga ruwa zuwa ruwan zafi.
*House
No.
34,
Street
12,
Al
Mankhool,
Bur,
Abu
Dabhi,
Dubai.*
ADAM POV.
Tsaye yake a gaban Maama wadda ke masa addu'ar Allah ya tsare shi, hannunsa riƙe da jakarsa ta kaya, yayin da yake murmushi yana dubanta.
“Zan yi kewarki Maama”
Ya samu bakinsa da furta hakan. Domin a ganinsa kamar sati ɗaya ya yi kaɗan da zai sa ya riƙa jin kewarta a ransa irin haka, Maama ta yi dariya.
“A sati ɗayan? Na ga ka sha yin tafiyar da ta fi wannan tsayi, kuma kana daɗewa, sai wannan ta sati ɗayan ne zai sa ka yi kewata?”
Ya aje jakar hannunsa, sannan ya rungumeta yana jin kamar ya fasa tafiyar, shi dai ba ya ce ga dalilin da ya sa yake jin cewa zai yi nisan gaske da ita ba.
“Sakeni haka mana, sai ka karya min ƙashin tsufa”
Faɗin Maama, sai ya saketa yana murmushi.
“Allah ya tsareku, ya dawo da kai lafiya”
“Amin Maama”
Ya amsa yana ɗaukan jakar da ya aje. Sannan ya ɗaga mata hannu, ya juya zai fita, cikin raha Maama tace.
“Kett!”
Ya tsorata yana juyowa tare da kallonta. Maama ta kwashe da dariya, shi ma da ya gane cewa zolayarsa take sai ya yi dariya.
“Ai zan daɗe ba na nan, sai na ga wanda za ki zolaya kuma”
Ya faɗa yana fita daga gidan. A bayan motarsa ya saka jakarsa, domin sun yi da Ivana da kuma Arman kan a motarsa za su tafi airport. Domin shi Arman ba ya so kowa ya san cewa ba ya gida a lokacin da suke gudanar da shagalin ƙarin shekararsa. Shi ya sa ba zai ɗauki ɗaya daga cikin motocinsa ba.
Kai tsaye gidansu Ivana ya nufa, da yaje gidansu ma ya daɗe, domin Ivana dake sallama da Yumma da kuma 'yar uwarta Hala. Kamar wata wadda za ta bar duniya haka ta fara hawayen bankwana da su Yumma. Sai da ban banki sannan ya samu ya ɗauketa suka tafi gidan Iƙbal Alhadi, a bayan gidan ya tsayar da motarsa, sannan ya kira Arman...
ARMAN POV.
Tsaye yake a balcony ɗin ɗakinsa, hannayenssa zube cikin aljihu, yana kallon masu aikin decoration na decorating garden ɗin gidan, dan daga nan inda yake yana iya ganin duk abin da ke wakana a garden da kuma wurin swimming pool ɗin gidan.
Haka kawai yake jin kamar bankwana yake da kowa da komai, kamar wannan hukuncin da ya yanke ya yi tsauri da yawa, kamar idan ya aikatawa ahalinsa hakan sam ba za su ji daɗi ba, daga can ƙasan zuciyarsa kuma akwai wani abu da yake marmari da son tafi Bavarian forest, ba zai ce ga dalili ba, domin bai taɓa zuwa dajin ba, hasali ma sau ɗaya ya taɓa zuwa Germany...
“Wai har yanzu ba ka shirya ba Arman?”
Ya jiyo muryar Immi na faɗin hakan a bayansa, hakan ya sa ya juya ya kalleta, hannayensa zube cikin aljihu. Tsaye take a tsakiyar ɗakin nasa, hannunta riƙe da wani box me faɗi, wanda ya san cewa tufafi ne sabbi a ciki. Ta sha adonta cikin wani maroon chickankari, me ɗauke da ratsin golden. Wuyanta kunnenta da hannayenta duka ta saka jewelry masu tsada, fuskarta ta sha kwalliya, wadda ke ɓoye yawan shekarunta.
“Shu? Ka'annak mu farhan ibini?”
(Miye? Kamar ba ka farin ciki ɗana?).
Ta tambaya ganin yanayinsa, ya girgiza kai yana nufota. Yana zuwa kusa da ita ya kama hannunta.
“Kin yi kyau fiye da kullum Immi. Kamar yayata ba mahaifiyata ba”
Immi ta aje box ɗin da ta shigo da shi, ta daki kafaɗarsa, ya yi dariya yana kallonta.
“Sai ga shi kuma ni mahaifiyarka ce ba kakarka ba.”
Ya kalleta yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya dafa kafaɗarta.
“Da gaske kin yi kyau”
Immi ta yi murmushin jin daɗi, Arman ya dawo gefenta yana dafa kafaɗarta ɗaya, tare da zaro wayarsa a aljihu yana faɗin.
“Bari na ɗauki hoto”
Ya ɗaukesu a hoton, sannan ya nuna mata.
“Ya yi kyau. Ga su nan, kaya ne da na saka aka maka tun daga kamfani, ka yi maza ka shirya ka fito, masu kawowa cake sun kusa zuwa.”
Ya kalli box ɗin yana jinjina kai, sannan ya maida hankalinsa kan wayarsa da kiran Adam ke shigowa. Bai ɗaga kiran ba, ya jefa wayar a aljihunsa, ya samu ya lallaɓa Immi ta fice daga ɗakin, paper da pen ya ɗauka, ya yi rubutu a kai, sannan ya aje papern a kan box ɗin kayan da Immin ta kawo masa. Sannan ya ɗauki wayarsa ya kira mai aikin gidan da ya bawa ajiyar jakarsa, yace masa ya kai motar Adam, tana bayan gida. Daga haka kuma shi ma ya saɗaɗa ya fice daga gidan, ba tare da ya bari kowa ya ankara da shi ba.
*11:40 na wannan daren.*
Ko ina ka kalla a garden ɗin gidan Iƙbal Alhadi mutane za ka gani, cikin shigar da za ta sanar da kai tsadar kuɗin kayan da suka saka. Kuma ko ina na garden ɗin an ƙawata shi da kayan decoration wanda suka sa daren ya ƙara armashi.
Daga can wajen kan wani table kuwa, cakes ne kala-kala, manya da ƙanana, ban da wasu nau'ikan drinks da snacks. Immi da Abby da kuma Gulzar ne tsaye a kusa da wurin, kowa ka kalla a cikinsu za ka ga yana cikin farin ciki. Kuma haka wasu daga cikin 'yan uwan Abby ma. Amma wasu daga cikin waɗan da suka san shirin da Abby ke yi na miƙawa ɗansa ragamar kamfanunuwan Alhadi akasin farin cikin suke.
Musamman Anwar da yaransa, kai da ka kallesu ka san dole aka musu na zuwa wurin shagalin, dan Jadda ce ta kafawa kowa tsatssauran warning kan kada wanda ya kuskura wannan shagalin ya wuce shi, shi ya sa suka zo ba dan suna so ba, sai dan an musu dole. Ganin sha biyu saura ya sa Abby ya kira Gulzar gefe.
“Ina ɗan uwanki ne? Tun ɗazu ban ga gilmawarsa ba. Kuma ko ɗaya daga cikin abokansa ban gani ba, duk da na turawa kowa katin gayyata, kuma shi ma na san ba zai kasa sanar da su ba”
”Yana ɗakinsa fa Abby, kuma wata ƙila su ma su Adam ɗin na tare da shi a can, bari na je na kira shi”
Cewar Gulzar.
“Ki yi maza ki kirashi ya sauƙo, dan sha biyu ta kusa cika”
“To Abby”
Ta amsa, sannan ta nufi hanyar falo, da ƙyar ta samu ya hau sama, sannan ta shiga ɗakin Arman. Tris ta ja ta tsaya a ƙofar ɗakin, ganin babu kowa a ciki.
“Akhi! Akhi?”
Ta kira tana leƙa kanta, jin shiru yasa ta ƙarasa shiga ɗakin, ta tsaya dube-dube, kafin ta nufi bathroom ta ƙwanƙwasa, amma shiru, babu alamar ma akwai mutun ciki, sai ta buɗe ƙofar bayin ta leƙa tana kiransa. Ganin baya cikin bayin yasa hankalinta ya fara tashi.
Dan haka ta dawo ɗakin da gudu, tana shirin barin ɗakin ta yi arba da box ɗin dake kan hadonsa, kuma ta lura da wata paper dake kai, dan haka ta dawo jiki a sanyaye ta ɗauki takardar ta shiga karantawa. Ai ba ta gama karantawa ba ta fashe da kuka, sannan ta fita daga ɗakin da gudu, ta koma garden.
Tun da Abby ya hangeta daga nesa ya gane cewar ba lau ba, dan haka ya yi saurin isa gareta yana tambayar abin da ya faru, kuka kawai ta sake fashewa da shi ta faɗa jikinsa tana rufe bakinta, kukan da take da tambayarta da Abby ke yi na me ya faru ya janyo hankalin baƙi da 'yan uwa.
“Ke Gul mi ye haka?”
Immi ta tambaya tana nufo wurin da suke tsaye ita da Abby, amma sai ta kasa amsata, ta shiga girgiza kai kawai.
“Gul! Gul! Ina yayanki?”
Jadda ta tambaya tana ɗagota daga jikin Abby, yanzu ma bata yi magana ba, sai takardar dake hannunta da ta miƙawa Abby, Abby ya karɓa hannunsa na rawa, dan sam zuciyarsa ta kasa gaya masa abu me daɗi a kan Arman a halin da ya ga Gul ta dawo bayan ta tafi kiran shi.
_“Ina da tabbacin a lokacin da za ku riski wannan takardar jirginmu ya tashi. Dan haka kada ku sha wahala wurin naiman inda nake. Na daɗe da sanin shirin da kake a kaina Abby, kuma kamar yanda ka yi hasashe, ba zan taɓa baka kunya ba, babu wanda ya san gaibu, amma ina me tabbatar maka da cewa da ban san da wannan maganar ba da na saka hannu a takardun da za ka bani yau a wurin shagalin ƙara shekarata. Amma kuma tun da na riga na sani ba zan bar hakan ta faru ba Abby, na rasa ta wace hanya ya kamata ace na fahimtar da ku abin da nake son ku gane, na rasa da wani yare zan muku magana dan ku fahimta. Na zaɓi barin ƙasar Dubai ne ba dan komai ba sai dan nisanta kaina daga duk wani abu da ya shafi Majmu'at Shirkat Alhadi. Kuma ina me muku albishir da zan dawo bayan sati ɗaya. Abby kada ka shiga damuwa, Immi kada ki yi kuka, ki min addu'a, Gul kada ki zagi yayanki a kan abin da ya yi na ɗauki wannan hukuncin ne bayan dogon nazari.... Arman Iƙbal Alhadi!”_
Abby na kaiwa ƙarshen karatan takardar ya dunƙuleta a hannunsa, idonsa na sauya kala nan take.
“Kai Iƙbal me ya faru?”
Jadda ta tambaya tana riƙe shi. Cikin wani hali me kama da abin da ya fi tashin hankali ya kalleta.
“Jadda me yasa kika faɗa masa abin da muke ɓoyewa?”
Tun da ta ji wannan tambayar ta tabbatar da abin da take zargi. Shi kuma Abby ya san babu wanda zai sanar da shi face Jadda, ko Anwar ko ɗaya daga cikin 'Yayansa. Jadda ta sunkuyar da kanta.
“Ban yi hakan da wata manufa ba Iƙbal, sai dan na gargaɗe shi kan kada ya bijire mana”
Abby ya kasa magana, ya dafe kansa da ya fara juyawa, ita kuma Immi da ta kasa gane inda zancen ya dosa ta yi saurin ɓanɓare takardar daga hannun Abby domin ta karanta. A lokacin da ta gama karantawa sakin takardar ta yi, jikinta ya shiga rawa, haka idonta ya soma zubar da ƙwalla.
“Iƙbal ɗana ya gudu!”
Shi ne kaɗai abin da ta faɗa tana shirin faɗuwa. Abby da Gulzar suka yi azamar riƙota, suka tsayar da ita, Gul na bata haƙuri. Jin batun guduwar Arman ba ƙaramin faranta ran Faisak da mahaifnsu ya yi ba. Kuma duk da ya ga halin da mahaifiyarsa, ƙaninsa, matar ƙaninsa da kuma 'yar ɗan uwansa suka shiga bai sa ya fasa faɗar baƙar magana ba.
“Da ma me kuke tsammani daga wurin nakasasshe kamar wannan?... Nakasasshen ma wanda ya fito daga jinin Indiyawa”
Wata daga cikin 'yan uwan Immi ta nufo shi a zafafe, dan ta gane cewa magana ya yada musu.
“Mu ba Indiyawa ba ne. Dan haka kada ka sake cewa mu indiyawa ne”
“To yanzu da kika iyo kaina dukana za ki yi? Na ce dukana za ki yi?”
Nan fa cecekuce ya kaure a tsakanin dangin Abby da na Immi.
“Ya isheku haka!”
Faɗin Immi cikin ƙaraji. Hakan ya sa wurin ya yi tsit.
“Ku barmu mu ji da ɓatan ɗanmu mana. Bayan wannan abin da ya faru da mu kuma me yasa kuke son ƙara mana wata damuwa?”
Ta ƙarashe tana kwantar da kanta a kafaɗar mijinta da ta jingina da shi, sannan ta fashe da wani sabon kukan.
“Ko kana ina yanzu haka ɗana?”
°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°
A hankali Arman ya leƙa windown dake a ta gefensa, ya kalli gajimare dake ƙasan jirginsu da ya tashi sama, kafin ya juyo ya kalli Ivana da Adam dake kusa da shi, dan tikitin kujeru ukun dake kusa da juna suka siye, kasancewar jirgin da suka hau babba ne.
Ita Ivana kallo take a system, yayin da Adam ke cin abinci hankali kwance, amma shi sam ji yake hankalinsa ya ƙi kwanciya, da ko wani ƙarin daƙiƙa da jirginsu ke nufar birnin Regen dake ƙasar Germany, wanda ya kasanci gari mafi kusa da Bavarian forest ji yake kamar yana ƙaura daga duniyarsa zuwa wata duniyar da bai sani ba.
Idonsa ne ya kai kan agogon dake tsintsinyar hannunsa, a hankali ya furzar da iska daga bakinsa, sannan ya gyara glasses ɗinsa tare da tura sumar dake kan goshinsa baya. Ya lusmhe makafin idonsa yana jin wani abu na rashin daɗi na masa yawo a zuciya.
“Arman? Shu fi (Me ya faru)”
Adam da ya lura da shi ya tambaya. Amma sai ya buɗe idonsa yana girgiza kai. Sannan ya ɗauke kansa ya jingina da kujera yana kallon window, kasancewar shi ne a window seat. Adam ya kira ɗaya daga cikin flight attendant. Jim kaɗan ta iso seat ɗinsu tana murmushi, kamar yanda aka saba ganinsu, cike da girmamawa ta risina tana faɗin.
“Me kake buƙata yallaɓai?”
“Ruwa me sanyi”
Adam ya amsa.
“An gama yallaɓai”
“Sannan ki tafi da wannan, na kammala”
Ta sake amsawa, sannan ta ɗauke trayn da ya gama cin abinci da shi, ta juya ta tafi, sai da ta kawo ruwan, sannan ya bawa Arman.
“Ka sha”
Arman ya kalli ruwan, sannan ya kalle shi, ya sa hannu ya karɓa, ya sha sosai, sannan ya aje yana sake ɗauke kai ba tare da yace komai ba. Hankalinsa gaba ɗaya yana kan agogon hannunsa, dan jira kawai yake 12 ta cika. Kuma a dai-dai lokacin da ta cika, ya lusmhe idonsa, a hankali ya furta.
“Eid Milad sa'id ya Arman (Happy birthday Arman)!”.
Salma
Ahmad
Isah
✍️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.
🪄
...JUYIN
KWAƊO...
🪄
©️Salma
Ahmad
Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah
@Wattpad
Page-7
*Furstlich zeil Hotel, Lower Town, 168, Regen, Germany.*
*11:04 na rana.*
IVANA POV.
A karo na uku ta sake ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin Arman, sannan ta janye hannunta tana jiran ya buɗe. Jiya bayan jirginsu ya sauƙa a birnin Regen kamfanin da Arman ya ɗauka musu domin su kaisu duk wasu wuraren buɗe ido ne suka aiko wakilinsu ya ɗaukesu a airport. Kuma shi ne ya kawosu wannan hotel ɗin, inda suka kama musu ɗakuna uku, kowa da ɗakinsa.
Tun a daren jiya ita da Adam suka tsara cewa za su je siyayya, dan haka ne ma yanzu suka shirya domin fita, kuma wakilin kamfanin da kan zaga da masu yawon buɗe idon na tare da su, dan shi ne wanda zai zaga da su a cikin gari, kafin zuwa gobe kuma su nufi Bavarian forest, inda kaddararsu ke jiransu a cikinsa.
Kallon Arman ta yi, wanda ya buɗe ƙofar a kasalance, sanye yake da sweate shirt eggplant color, da farin chinos trouser, idonsa saye cikin glasses ɗinsa, wanda rims ɗinsa ya kasance white color. Babu ko takalmi a ƙafarsa, hatta da gashin kansa a hargitse yake, alamar bai ga gyara ba. Shi ma kallonsu ya tsaya yi su duka ukun, sannan ya bar ƙofar ɗakin a buɗe, ya juya cikin ɗakin.
Ivana da Adam suka shiga ɗakin, yayin da ɗan rakiyarsu me suna Hans ya tsaya a waje. Ivana da Adam kallonsa kawai suke, har ya zauna kan sofa yana ɗauke kai, ba tare da ya bari sun haɗa ido ba. Ivana da Adam suka dubi juna, dan sun gane cewa kamar abokinsu na cikin damuwa.
“Za mu je siyayya ne, idan kana da ra'ayin zuwa”
Cewar Adam. Kansa ya girgiza yana shafa sumar kansa, tare da ƙifta idonsa a hankali, kuma bai bari ya kallesu ba.
“Arman”
Ivana ta kira tana zauna a gefensa. Dubanta kawai ya yi yana aje wayarsa dake riƙe a hannunsa, dan ba amfanin komai yake da ita ba, hasalima a kashe take, domin ba ya so wani na gida ya kirashi.
“Kamar akwai abin da yake damunka?”
Ta tambaya tana son su haɗa ido, amma ya ƙi bata damar hakan. Tun jiya da suka baro Dubai har zuwa yau ɗin nan ba ya jin daɗi sam, duk tsayin awa shidan da suka kwashe a jirgi kafin su iso Regen sam bai ji daɗinsu ba, hatta yanzu haka da yake zaune ba ya jin daɗi. Kuma jinyar ba a jikinsa take ba, a zuciyarsa take.
“Ka ga Arman! Idan har kana jin hukuncin da ka yanke bai maka ba muna tare da kai. Idan kana jin cewa ka yi nadamar abin da ka aikata za mu kasance tare da kai, wannan rayuwarka ce, kuma lokacinka ne, ka yi abin da ya dace a lokacin da ya dace, ka yi tunani me zurfi a kan wannan hukuncin, duk abin da ka yanke za mu amince da shi. Ko da kuwa kana so mu koma Dubai a ranar yau ne za mu koma, mu dai burinmu shi ne ka yi farin ciki!”
Cewar Adam yana dafa shi, ya ɗaga kai ya kalli Adam, sannan ya kalli Ivana dake jinjina masa kai, alamun abin da Adam ya faɗa haka ne. Ya sauƙe ajiyar zuciya me nauyi, sannan ya shafa kansa yana rinte ido.
“Mu za mu tafi siyayya. Ka tabbatar ka yanke hukunci kafin mu dawo”
Cewar Ivana tana miƙewa, tare da ɗaukan bag ɗinta, ta bubbuga kafaɗarsa sau biyu, sannan tace da Adam su tafi, suka tafi suka bar shi cikin tunani me zurfi.
Ivana da Adam sun zaga sosai a cikin garin Regen, kuma tun a cikin garin ma Adam ya samu ya ɗauki wasu hotuna. Sun shiga manyan kantuna da gidajen abinci, domin sun ɗauki alƙawarin shiryawa abokinsu babban bikin ƙarin shekara. Ta hanyar siya masa kyautuka da dama.
Yayin da suke siyayya a cikin wani shagon da ake saida kayan tarihi irin na da can. Adam ya yi arba da wata sarƙa a cikin wani