Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsaye min a rai ba. Kasancewar Uwais da Feroza a raye shi ne babban abin da yake damuna... Idan har Uwais ya ci gaba da kasancewa a raye ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba, domin mulkina zai kasance cikin haɗari, wanda ni kuma ba zan lamunci hakan ba!”
Anser ya sake matsawa kusa da ɗansa, sannan ya dafa kafaɗunsa.
“Rabuwarka da Uwais shi ne abu mafi alkairi, idan har ka ce za ka ci gaba da bibiyar rayuwarsa to fa ni da kai duka ba za mu ji daɗi ba. Dan haka a shawarce ka ƙyale shi zai fi!”
Safraz ya ture hannayen mahafinsa dake kan kafaɗunsa, sannan ya tashi sama ya fara yawo a iska yana faɗin.
“Ba zan ƙyale shi ba, dole cikin biyu a yi ɗaya, ko dai shi ya mutu, ko Feroza ta mutu!...”
Yana gama faɗin hakan ya ratsa rufin falon ya fice ta wurin.
MALIK CANGAZ.
Kallon kallo aka shiga yi tsakaninsa da Boka Jalis dake sanar masa da wurin da matasan da yake naima suke. Can kuma sai ya kwashe da dariya yana cilla kansa baya.
“Tabbas zan taƙaita musu kwanakin tafiyar dake gabansu!”
Ya faɗa bayan ya gama ƙyaƙyata dariyar tasa. Cikin rashin fahimta boka Jalis yace.
“Ban fahimceka ba shugabana!”
“Tun a daren yau zan shirya dakaru, sannan na turasu suje su tarbesu kafin su samu isowa nan!”
Malik Cangaz ya bawa Boka Jalis amsa. Shi dai boka bai cce ƙala ba, dan shi ya hango abin da ya hango. Har suka gama tattaunawa da bokan bai sanar da shi wani abu bayan nasara ba. Da wannan farin cikin ya koma fada, duk da akwai manyan baƙi dake zuwa domin halartar bikin gimbiya bai sa ya fasa sawa a shirya dakaru domin turasu ƙwatar mukullin dake hannun baƙin matasa uku ba.
Sai da ya gama da wannan fannin, sannan ya dawo cikin fada ya fuskanci lamarin baƙinsa, a gefe guda kuma shirye-shiryen bikin gimbiya na ci gaba da wanzuwa a fadar, domin duk mutanen gari sun san cewa za'ayi biki a gidan sarki.
EID.
Hannu ya miƙa ya karɓi sabbin tufafin da ya siya a wurin wani mutum dake cikin kasuwar ƙauyen Aban, domin ƙauye aban shi ne ƙauyen da ya zaɓa domin gudanar da ɗaurin aurensa da gimbiya Iqrah. Auren da zai yi amfani da shi wurin tarwatsa zuciyar Iqrah, auren da zai yi amfani da shi wurin rama kwatankwacin abin da Malik Cangaz ya aikata masa.
Sai dai kuma ta wata hanyar wannan auren ya taɓa rayuwarsa, tun farko shi ba son gaskiya yake yi wa Iqrah ba, hasali ma komai yake faruwa tsakaninta da shi duka shiri ne. Domin hatta da farkon haɗuwarsu shiri ce, shirin da ya taso shi tun daga nahiyarsu zuwa Mamlakatul Jiyad.
Domin asalinsa ba ɗan garin ba ne, babu wani abu da ya haɗa alaƙarsa da ta daular Jiyad, cin burin ɗaukan fansa ya sa ya yi takekeniya ya bar nahiyarsu ya kutsa zuwa wannan gari. Lokacin da ya zo garin duka tsarukansa sun tafi dai-dai, ciki har da sawa Iqrah soyayyarsa a ranta. Kuma hakan ma ya tafi yanda yake so, sai dai kuma wa gari ya waya? Domin a ƙarshe shi aka bari da jinyar zuciya.
Duk taka tsantsan ɗin da yake na gujewa soyayyar Iqrah an yi rashin sa'a shirinsa ta wannan fannin bai yi ba. Domin a halin yanzu shi kansa ya san cewa yana sonta, amma kuma ya yi rantsuwa kan ba zai bari soyayyarta ta hana shi ɗaukan fansarsa ba, ko da kuwa hakan zai sake raunata zuciyarsa ne a karo na biyu...
“Eid!”
Kamar kullum, kamar yanda ya saba tunaninta haka yau ma muryarta ta kutso cikin tunaninsa. A hankali ya zauna kan wata bishiya, yana kallon wasu yara dake wasa kusa da bishiryar. Hannu ya kai ya sauƙe Aafa dake kafaɗarsa, sannan ya ajeta a gefensa yana ci gaba da kallon yaran.
Haka kawai murmushi ya suɓuce masa, domin ya tuna da nasa ahalin, da ace har yanzu matarsa Maryam na raye, da ita ma ta haife masa ɗan cikinta... Ɗansa, jin zuciyarsa na ɗacin tunowa da mutuwar Maryam xa ta mahaifinsa ya sa ya kawar da kai daga barin kallon yaran, gudun kada ya haɗiyi zuciya ya faɗi ya mutu ba tare da ya ɗauki fansa ba.
“Daga gobe ba za ka sake kwanan farin ciki ba Cangaz! Zan tabbatar da na ƙuntata maka dai-dai da yanda ka ƙuntata zuciyata!”
Ya furta yana haɗe haƙwaransa na sama da na ƙasa, zuciyarsa na tabbatar masa da cewar zai iya!.
ADVENTURERS.
Bayan shafe tafiyar awa uku a ƙafa, suka yanke shawarar zama su huta a wani daji. Yayin da suke hutawa Uwais yace zai je ya naimo musu abinci, amma sai Arman yace kada ya je, shi ma ya zauna ya huta, tun da shi ma zai gaji ne.
“Ba lalle ba! Shi da mu akwai banbanci!”
Cewar Sana da yanzu ita ma ta zama abokiyar tafiyarsu. Lokacin da suka gane cewa ita ce sun sha matuƙar mamakin ganin matar sarki 'yar saki a wuri irin wanda suka haɗu, bayan ta sanar da su cewa tafiya ce ta kamata har ta kai ga mutanen nan sun kamata, sai suka cire ko wani kokwanto, su ka ci gaba da tafiya da ita har zuwa yanzu.
“Me ya sa na zama ba ɗaya da ku ba?”
Uwais ya tambaya yana murmushi.
“Saboda kai ka kasance ruwa biyu, aljani kuma mutum!”
Sana ta amsa shi, har zuwa yau fuskarta na a rufe da mayafin da take rufe kanta da shi, domin ba ta cika buɗe fuskarta ba.
“Uwais!”
Adam dake yi wa Ivana tausa a ƙafa ya kira sunan. Hakan ya sa Uwais ya dube shi.
“Ya ka ji lokacin da aka ƙwace mulkin mahaifinka, sannan ya kake ji idan ka tuna cewa abin da yake mallakinka na tare da wani da ba kai ba!?”
Adam ya tambaya da biyu, dan lokacin da ya cilla masa tambayar sai da ya saci kallon Arman, kuma ya lura da tambayar ta sa shi cikin nazari. Ivana da ta fahimci inda ya dosa ta daki kafaɗarsa cikin gargaɗi, duk da yau a gajiye take liƙis, saboda ita ne ma suka yada zango ba dan dare ya yi ba, ga ƙafafunta dake mata mugun ciwo, shi ya sa ma ta saka Adam ya mata tausa.
“Lokacin da aka sanar mana da cewa mahaifina ya mutu ji na yi kamar ni ma zan mutu na bi shi. Har ina jin kamar na samu Safraz da Ammi Anser (Kawuna Anser) na ce da su su kwashe komai da muke da shi, amma su bar min Abi. Na ji haushi sosai lokacin da na fuskanci cewar a kan kujerar mulki suka kashe min mahaifina. Bayan kuma sun fara shirin ƙwace abin da yake nawa sai na ji cewar na rasa komai, wannan kujerar ita ce kaɗai abin da nake ganin cewa Abi ya bar min... Lokacin da ya mutu ina ƙarami sosai, amma duk da haka ba na mancewa abubuwan da suka shefi shi, a ko da yaushe yana yawan cewa babu wanda ya dace da zama sarkin Mamlakatul Afsah bayan Uwais!...”
Ya ɗan yi fasali yana murmushi me ciwo, ya shafa kansa sannan ya ci gaba da faɗin.
“Ashe hakan ba zai zama gaskiya ba, ashe wani bayan ni ne zai zama sarkin! Ashe ba ni da rabon gadar mahaifina...”
Lokacin da ya kai ƙarshe duk hankalin Adam da Ivana na kan Arman da jikinsa ya yi sanyi, ba komai yake tunowa ba face Abby. Ta wani ɓangaren zai iya cewa rayuwar Uwais na kamanceceniya da tasa rayuwar. Idan aka kwatanta Anser da Ammu Anwar, Safraz kuma da Faisal, Malik Dhaakir kuma da Abby, Uwais kuma a matsayin shi!... Ke nan son abin duniya zai iya sawa Ammu Anwar da Faisal su haɗa hannu wurin kashe Abby?...
“Arman!”
Kiran da Ivana ta masa ya katse masa tunani, sai ya kalleta, sannan ya gyara zaman glasses ɗinsa.
“Lafiya?”
Ta tambaya tana taɓa shi, ya girgiza mata kai, sannan ya miƙe ya nufi cikin daji, sai da ya yi nesa da su sosai, sannan ya jingina da jikin wata bishiya, kewar ahalinsa na mamaye masa ruhi. Wayarsa ya ɗauko, ya buɗe, sannan ya shiga gallery, ya dubo hoton da suka ɗauka shi da Immi ranar da zai gudu daga gida.
Ƙwalla ya ji na taruwa a idonsa, hakan yasa ya kai hannu ya cire glasses ɗinsa, sannan ya goge idonsa, ya mayar da glasses ɗin, kana ya dubo hotonsu shi da Abby, wani tsohon hoto da aka daɗe da ɗaukansa...
“In Allah ya sa ba ni da rabon dawowa gida ina fatan ka yafe min Abby, idan kuma har Allah ya nufi dawowata ina me baka tabbacin zan yi abin da kake so, zan karɓi shugabancin da ake fata da tuƙuburin na karɓa... Domin a yanzu na gane cewa kuskure ne bijire maka da na yi ta yi a baya, ka yafeni Abby!”
Ya furta wani hawayen na zubo masa. A dai-dai lokacin kuma ya ji ihun Ivana, hakan tasa ya buɗe idonsa da sauri, sannan ya juya yana kallon bayansa, domin ta nan ya jiyo ihun.
*
“Kamar akwai abin da yake damunsa!”
Cewar Uwais lokacin da Arman ya tashi daga wurin. Adam ya girgiza kansa.
“Ta wani ɓangaren rayuwarka da tasa tana kamanceceniya. A zamaninmu mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, sannan yana da manyan kanfanunuwa, kuma shi mahaifin nasa yana da ɗan uwa, wanda yake da ɗa namiji, shi ma ɗan nasa yana da burin zama shugaban kamfanin. Kasancewar shi Arman na da nakasar gani ya sa kawun nasa ya yi amfani da wannan damar wurin cusa masa ƙiyayyar shugabancin kamfanin. A halin yanzu kuma mahaifinsa ya fara gazawa, tsufa ya fara masa sallama, yana buƙatar Arman ya maye gurbinsa, amma sam Arman ya ƙi aminta da hakan... Hatta da wannan tafiyar da muka yi ta samo asali ne daga gujewa karɓar shugabancin kamfanin!”
“Abin tausayi!”
Cewar Uwais.
“Me ya sa yake saka wani abu a saman idonsa?”
Sana ta tambaya. Adam da Ivana suka yi dariya.
“Glasses ake kiransu, kuma su ne suke taimaka masa wurin gani, ba tare da su ba ba zai iya ganin ko da tafin hannunsa ba!”
“Na gane!”
Cewarta tana waigawa tare da kallon hanyar da ya bi.
“Adam taimaka min na miƙe!”
Cewar Ivana, Adam ya taimaka ya ɗagata.
“Ina za ki je?”
Ya tambaya ganin ta yi hanyar kogin dake gefe da su, Ivana na ɗingisa ƙafa tace.
“Zan wanke fuskata ne”
Da haka ta ƙarasa bakin kogin, ta tsugguna ta fara wanke fuskarta, sai da ta gama ta miƙe, tana shirin komawa inda su Uwais suke ta ga wani abu ya faɗo gabanta tim!. Razana ta yi ta ja baya tana ƙarewa budurwar da ta faɗo gabanta kallo. Kafin ta yi wani yunƙuri budurwar ta ruƙo wuyanta, sannan ta buɗe fuska-fukanta ta tashi sama da ita, hakan yasa ta ƙwala ihu domin naiman ɗaukin abokanta.
Lokacin da Su Adam suka iso bakin kogin har budurwar ta yi nisa da ita a sama.
“Ivana!”
Cewar Adam cikin matsanancin tashin hankali.
“Me ya samu Ivana?”
Cewar Adam da ya ƙaraso wurin da gudu, shi ma kuma sai a lokacin ya lura da Ivana dake sama.
“Wace ce waccan?”
Arman ɗin ya tambaya yana kallon budurwar dake tare da Ivana. Kafin wani ya amsa masa Uwais ya buɗe nasa fukafukan zai tashi sama, Arman ya dakatar da shi.
“Uwais! Zan tafi tare da kai!”
“Zo mu je!”
Kawai Uwais yace, sannan ya riƙe hannun Arman ɗaya, ya tashi sama da shi, suka bi bayan budurwar da ta ɗauke Ivana.
...End of book 1...
____________________
_
Humm! Shin wacece wannan wadda ta sace Ivana?_
_Shin kuna ganin cewa Uwais da Arman za su iya cetonta?_
_Wata ƙiyayya ce tsakanin Eid da Malik Cangaz?_
_Wani abu ne ya samu matar Eid da ahalinsa da har ta kai ga yana son ɗaukar fansa!_
_Me Malik Safraz yake shiryawa?_
_Wani ƙudiri ne ya sa Sana matar Malik Wasimudeen shigowa cikin ADVENTURERS?_
_Shin kuna ganin dakarun Malik Cangaz za su iya riskar ADVENTURERS?_
_Mece ce makomar auren da Malik Cangaz yake shiryawa?_
_Yaushe ADVENTURERS ɗinmu za su riske ƙofar Malik Cangaz?. Shin za su iya samun nasarar buɗe ƙofar? Shin za su koma gida ko a'a?_
Domin ci gaba da karanta book 2 za ku biya ₦400 for regular group. ₦800 for VIP to.
5487270431
Salma Isah
Monie point
Shaidar biya kuma ta 08130172702.
Sannan za ku samu complete book one and 2 on Arewabooks, kada ku manta ku yi following ɗina domin samun notification da zarar na yi update.
Ina me tabbatar muku da book 2 is giving 🔥🔥🔥. A har kullum, godiya ta musamman zuwa ga masoyana a duk inda kuke. I ❤️ like WUJIGA-WUJIGA 💋. See you in book 2.
Best regards
Salma Ahmad Isah ✍️
A.k.a Candy🦋
A.k.a Bahaɗejia🐎
2024...

Chapter 13 of 13