Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nutsuwa, yanayin yanda kike magana, yanayin da kike tafiya, da duk wani abu da ya shafeki na musamman ne”
A wannan karon murmushi ta yi me faɗi, har haƙwaranta na bayyana.
“Kin yarda ke nan? Tun ga shi har kina murmushi”
Sai ta rufe bakinta, tana mamakin yanda aka yi ya san ta yi murmushi, tun da murmushin ba me sauti ta yi ba.
“Zan sauƙa daga kan layi. Ina fatan sake haɗuwa da ke”
“Sai anjima”
“Na gode da lokacinki”
Uwais ya sauƙe wayar, a lokacin da mahaifiyarsa ta shigo katafaren falon gidansu. Murmushi ta yi tana kallon ɗanta, tana zama kusa da shi ya kama hannunta ya sumbata. Ita kuma ta shafa kansa tana sanya masa albarka.
“Da wa kake waya? Ko yarinyar da zata zama sirikata ce?”
Ya faɗaɗa murmushinsa yana kallon mahaifinsa da shi ma ya shigo falon.
“Ai da gani ba sai an faɗa ba. Tun da kika ga yana yin irin wannan murmushin.”
Mahaifinsa Inayat Fazil ya faɗa yana nasa murmushin. Ƙudsiyya mahaifiyarsa tace.
“Wace ce?”
“Wata ce”
Ya basu gajeriyar amsar yana kwasar wayoyinsa, sannan ya bar living arean yana murmushi me kama da dariya.
*House

No.

34,

Street

12,

Al

Mankhool,

Bur,

Abu

Dabhi,

Dubai.*
ADAM POV.
Tsaki ya ja yana ci gaba da danna system ɗinsa, sakamakon binciken wurin da ya kamata ace ya je ya ɗauki hotunan da aka saka shi da yake. Amma ya shafe sama da awa uku bai samu wurin da ya kwanta masa ba. Arman dake zaune a gefensa yana cin tuwon da Maama ta ba shi ya ce.
“To wai duk wannan tsakin da kake wa mutane na miye?”
Adam ya juyo ya kalle shi, sai lomar tuwon shikafa miyar kuka yake, kamar wani bahaushe, ko irin ya saba da cin abincin nan. Kuma dan tsabar yana son tuwon yasa a wasu lokutan yake tattaki ya zo gidansu Adam, dan kawai Maama ta ba shi tuwo, yace a cikin abincin hausawa tuwo ya fi komai daɗi.
“Ya zalame (Man) na rasa wurin da ya kamata ace na je na ɗauki hotunan da za su ja hankalin mutane, irin hotunan da ba'a saba gani ba ka gane?”
Armaan ya gyara zaman glasses ɗinsa, sannan yace.
“Ka je ka ɗauko hotunan Creek harbor, ko Dubai Fountain show, ko Museum of the future...”
“Ina maganar abin da ba'a saba gani ba kana lissafo min wuraren da babu wanda bai sansu ba a Dubai. Duka waɗannan wuraren da ka lissafo ɗaiɗaikun mutanen garin nan ne kaɗai ba su taɓa zuwa ba, in ma ba su je ba sun san wurin. Kuma me zan nunawa mutane a wurin da suka riga suka sani?”
Adam ya katse shi. Arman ya gyara zama yana aje bowl ɗin hannunsa a kan center table.
“To ka je Bastakia, Deira, ko ka ɗauko gaba ɗaya Palm Jumeirah...”
“Dakata Arman, hotunan wuraren nan tuntuni an riga an ɗauke su, imfact ba na son ɗaukan hoton wani abu a Dubai, na fi son na fita wajen Dubai dan na zo musu da sabon abu.”
“Ina za ka je to?”
Ya tambaya yana gyara zaman glasses ɗinsa. Adam ya yi shiru kawai, dan har yanzu ya kasa tsayar da shawarar inda ya kamata ace yaje.
“Me zai hana ka je Nigeria, ka ɗauki hotunan masarautun gargajiya da al'adun Hausawa?”
Maama dake tsaye a kitchen, tana sauraron duka hirarrakinsu ta bada shawarar. Kusan a tare suka juya suka kalleta.
“Kyakkyawar shawara... Idan za ka je zan rakaka, dan ban taɓa zuwa ƙasarku ba, ko ba komai ka ga ni ma zan buɗe ido”
Adam ya yi murmushi.
“Zan duba na gani”
Arman ya kai masa dukan da a ɗan ƙanƙanin lokaci ya sa ya razana. Dan sam bai zaci dukan Arman ɗin a wannan lokacin ba.
“Miye ne?”
Ya tambaya yana zaro ido.
“Me za ka duba ka ga?. Ai tun da Maama ta riga ta bada shawarar nan ta karɓu, ko kai ba ka karɓa ba ni na karɓa maka, dan haka ni zan ɗauki nauyin tafiyarmu Nigeria. Dan a private jet ɗin Alhadi za mu tafi”
Adam ya yi dariya.
“To ya kamata mu sanar da Ivana, dan ita ma ba za ta kasa zuwa ba”
“Zan faɗa mata”
Arman ya faɗa yana ɗaukan wayarsa dake ruri, alamun shigowar kira, ganin lambar kakarsa ‘Jadda Nahila’ (Kaka Nahila) yasa ya ɗaga kansa yana girgizawa. Dan tun da har ya ga kiranta ya san wani abin aka ce mata ya aikata.
“Shu sar (Me ya faru?)”
Adam dake rufe system ɗinsa ya tambaya.
“Jadda ce ke kirana”
Ya faɗa yana nuna masa wayar.
“To ka ɗaga mana”
Sai ya girgiza kansa yana miƙewa.
“Babu amfanin sai na ɗaga, na san cewa za ta yi duk inda nake, duk abin da nake na bari na tafi gidanta”
Adam ya yi dariya yana kallon Arman ɗin da ya nufi kitchen, ya wanke hannunsa, sannan ya dawo falon ya ɗauki Denim jacket ɗinsa ya saka. Sannan ya ɗauki keyn motar da ya fito da ita.
“Na tafi... Maama na tafi”
Ya musu sallama yana nufar ƙofar fita daga gidan, wadda ta kasance ita ce ƙofar falo.
“To Arman ka gaida Imminka”
“Za ta ji”
Daga haka suka fita tare da Adam. Motarsa silver color ƙirar RR (Rolls-Royce) sweptail. Na fake a ƙofar gidan. Kallon motar kawai idan ka yi za ta baka labarin kuɗinta. Dan sam motar ba ta yi kama da ta ƙananun masu kuɗi ba. Shi kansa Arman ba ya hawa mota ɗaya, idan yau ya hau Bugatti La Voiture Noire, gobe za ka ganshi da Lamborghini Venone Roadster.
“Idan na dawo daga gidanta zan kiraka a kan maganar tafiya Nigeria ɗin nan”
Arman ya faɗa yana buɗe ƙofar motarsa. Adam ya amsa masa da to, suka yi sallama, sannan Arman ya ja motar zuwa gidan kakarsa, wadda ta haifi mahaifinsa, dan duka 'yan uwan mahaifiyarsa suna can Lahore, Pakistan.
Salma Ahmad Isah ✍️
_______________
_Shin a ganinku me Arman zai yi ifan jar ya san abin da iyayensa ke shiryawa?._
_Wata alaƙa kuke hasasowa tsakanin Uwais da Ivana?._
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.
🪄

...JUYIN

KWAƊO...
🪄
©️Salma

Ahmad

Isah

SalmaAhmadIsah
@ArewaBooks
SalmaAhmadIsah

@Wattpad
Page-5
A ƙofar gidan ya faka motarsa, sannan ya fito yana kallon kyakkyawan gidan da tsohuwar ke ciki, dan kakansu ya daɗe da rasuwa, ita Jaddan ce kaɗai ta rage, sai jikokinta da kan zo tayata zama jifa-jifa. Dan bayan mahaifinsa da Anwar Jadda na da 'ya'ya mata huɗu, waɗan da suka kasance ƙannen mahaifinsa.
Ba tare da knocking ko danna door bell ba ya buɗe ƙofar gidan ya shiga, a ɗan hall ɗin dake bakin ƙofa ya tsaya ya cire takalmansa, ya saka wasu da ya ga a wurin, sannan ya shiga falo yana dube-dube. Bai ga kowa ba bayan wata kyakkyawar budurwa da ta fito daga ƙofar da ya san cewa kitchen ne. Hannunta riƙe da tray, wanda kallon kyanta bai sa ya san miye a ciki ba. Da alama ta ji buɗe ƙofar tasa ne shi yasa ta fito dan ganin wanda ya zo.
“Marhaba”
Ta faɗa tana kallonsa da murmushi, dan ita ta san shi, shi ne dai alamu suka nuna cewa bai santa ba. Kansa ya jinjina kawai yana ƙare mata kallo, ba zai yi ƙarya ba, yarinyar tana da kyau.
“Aina Jadda” (Ina Jadda)
“Bi gurfatah, kallini nadilah. (Tana ɗakinta, bari na kirata)”
Ta amsa da muryarta me daɗin saurare. A living room ya zauna yana ci gaba da kallon matashiyar, har ta nufi corridor ɗin da zai sadata da upstairs. Sai a lokacin ya ɗauke idonsa a kanta, yana zaune a wurin har ta dawo, ta sanar masa ga Jaddan na sauƙowa, sannan ta koma kitchen ɗin.
Tun da Jadda ta fito take wurga masa harara, har ta iso living room ɗin, ta zauna a gefe da shi tana kallonsa a kaikaice. Kuma duk da ya lura da hakan bai sa ya fasa dariya ba.
“Masa'ul khair ya Jadda. (Barka da yamma Jadda)”
Jadda ta masa banza ta ɗauke kai tana girgiza ƙafa.
“Ƙira nawa na maka?”
Ta tambaya bayan wani lokaci.
“A ƙalla goma”
Arman ya amsa.
“To me yasa ba ka ɗaga ba?”
“Saboda na san maganar da za ki faɗa, shi yasa na zo tun kafin ki ce na zo”
Jadda ta kuma yin shiru.
“Arman zo nan”
Ya dubeta, sai ya miƙe ya koma gefenta ya zauna.
“Magana nake so mu yi...”
Ya jinjina mata kai, yana kallon yarinyar nan da ta dawo falon ɗauke da kayan taɓawa, ta aje a kan center table, sannan ta juya ta koma kitchen.
“Jadda wace ce wannan?”
Ya tambaya. Jadda ta harare shi, dan ta lura tun da ta shigo falon yake kallonta har ta koma inda ta fito.
“Gufran sunanta, ita ce yarinyar gwaggonka Bilƙisa, wadda ke Qatar.”
“Ohh na gane. To ina jinki”
Ya amsa yana jinjina mata kai.
“Da Anwar da Iƙbal duka 'ya'yana ne. Da kai da Faisal jikokina ne, haka Gulzar da Sakina. Amma Wallahi har cikin raina na fi son ka zamto magajin Alhadi fiye da Faisal Arman...”
Arman ya yi murmushi, dan ya san tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi.
“Jadda me yasa kowa yake son na zama shugaban Alhadi?”
Ya matambaya.
“Saboda kai kafi cancantar zama shugaba... Alhadi kamfanin mahaifinka ne, Anwar hannun jari kawai yake da shi!”
Jadda ta ba shi amsa, ya girgiza kansa yana murmushi.
“Jadda bani da suffofin shugabanci, saboda inada nakasar gani, ba zan iya shugabanci ba”
“Arman! Ka ga wannan kujerar dake cikin office ɗin Iƙbal? Ka ɗauketa tamkar kujerar wata babbar masarauta a zamanin baya. Wadda ake yaƙi da zubar da jini duk domin a mallaketa, wannan kujerar na dai-dai da kujerar katafariyar fada a zamanin baya!”
“To wai duk me ya kawo wannan zancen?”
Jadda ta yi murmushi.
“Saboda ba ma so ka bamu kunya. Nan da kwana uku zagayowar ranar da aka haifeka. Iyayenka na shirya maka babban shagalin taya murna. Kuma a wurin shagalin mahaifinka ya ɗauki niyyar baka takardun shugabancin gamayyar kamfanunuwan Alhadi, domin ka sa hannu a matsayinka na shugaba na gaba. Kuma ba na fatan ka bamu kunya Arman!.”
*Maison De Curry, Souk Al Bahar, Sheikh Mohammed bin Rashid Blvd, Downtown Dubai, United Arab Emirates.*
*10:52 na dare.*
THE ADVENTURERS.
“Wai me ya faru ne?”
Ivana ta tambayi Arman da ya tarasu a restaurant ɗin, kuma ya zauna ya yi shiru ba tare da yace komai ba. Arman ya juya kansa ya kalli Fountain show dake nan kusa da restaurant ɗin, kuma ta tsakanin Fountain ɗin yana iya ganin dogon ginin Burj Khalifa.
“Yau saura kwana biyu zagayowar ranar da aka haifeni. Abby da Immi suna shirya shagalin zagayowar ranar”
Ivana da Adam suka dubi juna. Sannan suka kwashe da dariya suna tafawa, hakan ya sa Arman ya kallesu da mamaki.
“To ai duk mu ma mun san wannan. Dan mu ma muna shirya namu shagalin... Mi ye na damuwa a ciki”
Arman ya saka hannu ya shafa ganshi kansa dake a nannaɗe, sannan yace.
“Ba wai batun shagalin ne abin da yasa ma taraku a nan ba. Abby yana shirin danƙa min takardun shugabancin Alhadi... Kuma kun san cewa wannan shi ne abin da bana so”
Cak Adam da Ivana suka dakata da dariyar da suke, sannan suka dubi juna. Kafin Adam ya kalle shi.
“Man! Ni fa da za ka ji shawarata da ka karɓi shugabancin kamfanin nan. Kasancewarka shugaba shi ne burin mahaifinka na ƙarshe. Bayan duk abubuwan da ya mallaka maka a rayuwa kuma sai ka kasa cika masa wannan burin?... Burin da a ƙarshe kai ne wanda za ka amfana da shi”
Ya gyara glasses ɗinsa, sannan yace.
“Adam ina so na cika burin Abby, saboda ban taɓa neman komai a wurin Abby na rasa ba. Duk abin da na naima cikin gaggawa Abby ke mallaka min shi, dalilina na ƙin shugabanci shi ne, duk wani abu da zai sa a na min kallon nakasasshe ba na sonsa. Duk wani abu da zai zama silar da za a muzantani gudunsa nake, bana so ana aibanta ni Adam. Kuma ku duka kun san cewa ta dalilin wannan kamfanin Ammu Anwar da Faisal da kuma Sakina ke aibantani a ko ina... Shi ya sa nake gudun Alhadi”
Shiru ya ratsa tsakaninsu, dan duk abin da ya faɗa gaskiya ne.
“Arman”
Faɗin Ivana tana kama hannunsa.
“A ganina maganar mutane bai kamata tasa ka sare da rayuwa ba. Allah shi ne me bada lafiya, kuma idan ya so a yanzu zai iya baka lafiya. Kuma tun da kana iya gani da taimakon glasses me zai hana ba za ka jarraba bin abinda iyayenka ke so ba”
Ya girgiza kansa, Ivana da Adam suka sake duban juna. Sun san abokinsu da taurin kai, tun da yace a'a to fa ba zai sauya ra'ayinsa ba.
“Yanzu mi ye shirinka?”
Adam ya tambaya. Ya kallesu su duka biyu.
“Kamar yanda suke zato. Sam ba zan taɓa basu kunya ba, domin da ace ban san da batun shagalin nan ba da zan amince na je wurin shagalin, kuma idan ya bani takardar a gaban kowa zan saka hannu. Amma tun da har na sani ba zan je wurin shagalin ba”
“Me kake nufi?”
Ivana ta tambaya a mamakance.
“Zan bar Dubai a ranar da suka shirya shagalin, yayin da suke shirya shagali a nan ni kuma zan yi nawa shagalin a wata ƙasar”
Adam ya girgiza kai.
“Hakan bai kamata ba Arman. Da wannan abin da za ka yi sai ka fi basu kunya, fiye da ƙin amincewa ka sa hannu a gaban jama'a.”
“Adam ya zan yi?... Sam ba na son abin da suke so, na kasa fahimtar da su, ya suke so na yi?”
Suka yi shiru, tausayin abokinsu na kama su.
“Shikenan. Mun yarda da shirinka, amma ba za mu barka ka tafi kai kaɗai ba, duk inda za ka je za mu kasance tare da kai”
Faɗin Ivana tana kallon Adam, shi ma Adam kansa ya jinjina, alamun ya amince. Arman ya yi murmushi yana kallon abokansa biyu.
“Amma ina kuke ganin za mu tafi?”
“Tun da ni zan je ɗaukan hoto me zai hana mu tafi Nigeria?”
Adam ya tambaya. Arman ya girgiza kai, a lokacin da idonsa ya kai kan allon da zai sauya akalar labarin gaba ɗaya, kuma allon dake ɗauke da zanen ƙaddararsu. Wadda za ta yi juyi irin na kwaɗo, daga ruwa zuwa ruwan zafi. Lokacin da ya gama karanta sunan wurin a jikin allon, fatar bakinsa ta furta sunan dajin a hankali.
“Bayericher wald (Bavarian forest)!”
“Germany ke nan?”
Cewar Adam, Arman ya gyaɗa kansa.
“Dajin yana da kyau sosai. Sannan za mu shaƙata a cikinsa, kai kuma za ka samu abubuwan da za ka ɗauka a cikin dajin... Kamar dai wancan hoton!”
Ya ƙarashe yana nuna musu wani allo dake ɗauke da hoton Bavarian forest ɗin. Suka waiga suka kalli board ɗin a tare, allon dake ɗauke da zanen sauya labarin kowanne a cikinsu.
*House

No

27,

Street

45,

Mirdif,

Dubai*
IVANA POV.
Sanye take da yellow maxi skirt, da farar shirt, wadda a samanta ta saka denim jacket. Tana zaune a kan gadonta, yayin da take goge guitar ɗinta da hanki, Yumma kuma na shirya mata kayanta a cikin jaka, dan ta riga da ta sanar mata da cewar za su yi tafiya tare da su Arman.
“Ivana”
Yumma ta kirata tana saka wasu takalmanta a cikin jakar da take shirya mata kayan.
“Na'am Yumma”
Ta amsa tana ɗaga kanta, tare da kallon Yumman.
“Me ya sa Arman ba ya son ya karɓi abin da yake nasa?”
Ivana ta girgiza kanta tana murmushi, ta saka hannu ta ta saƙala gashinta a bayan kunnenta, sannan tace.
“Tun yana yaro kawunsa da wasu daga cikin 'yan uwansa suka raunata masa zuciya. Bayan nakasar ido da yake da ita sun ƙara masa da nakasar zuciya Yumma. Abokina yana da zuciyar zinare, yana son taimakon wanda ba shi da shi, duk da tarin dukiya da Allah ya yi wa mahaifinsa sam ba ya dubawa, domin ba ya nuna banbanci tsakanin mu da shi. Amma wannan raunin da suka yi a zuciyarsa yasa sam ba ya son zama shugaban Alhadi...”
Ta ƙarashe tana ɗaga kafaɗunta tare da taɓe bakinta.
“Da ace Arman zai karɓi shugabancin nan Yumma da an yi shugaban da ba'a taɓa yin irinsa ba”
Yumma ta girgiza kanta.
“Allah ya karkato da zuciyarsa kan kamfanin, su kuma Allah ya musu abin da suka masa”
“Amin”
Ta amsa dai-dai lokacin da wayarta dake chaji a kan side drawer ta fara ringing, hannu ta miƙa ta ɗauki wayar, ganin lambar Uwais Fazil ya sa ta ɗaga wayar, tare da karawa a kunnenta.
“Marhaba”
Muryarsa me sanyi ta faɗa daga ɗayan ɓangaren.
“Alo”
Ta faɗa tana murmushi.
“Shin zan iya ganinki?”
Sai ta kalli Yumma da ke shirya mata kaya, da alama sam ba ta lura da wayar da take ba. Sai ta sauƙa daga kan gadon tana saka toe wrap shoes ɗinta dake kusa da gadon, sannan ta fita daga ɗakin. Sai a sanda take sauƙa downstairs sannan ta amsa.
“Zan so hakan, domin ina sa ran zan yi tafiya nan da gobe...”
“Yanzu haka ina ƙofar gida me lamba 27, titi na 45, a tsakiyar unguwar Mirdif.”
Ido ta zaro tana rufe baki, sannan cikin sanɗa ta isa jikin windown dake kusa da ƙofa, ta ture curtain ɗin dake jikin windown ta leƙa. Daga nan inda take ta samu damar ganinsa, jingine a jikin motar da ya zo da ita. Yana sanye da baƙin sweat blazer trouser, me ratsin ja a gefe, da farar crew-neck sweater, wadda ya saka baƙar shirt a ƙasanta. Ƙafafunsa cikin garin sneakers. Gashin kansa na cikin askin high pade, sannan wayarsa kare a kunnensa, kuma suna haɗa ido ya ɗaga mata hannu, sai ta yi saurin sakin curtain ɗin tana dariya ƙasa-ƙasa.
“Ina jiranki”
Ba tare da tace komai ba ta sauƙe wayar, sannan ta koma sama da gudu. Har Yumma na tambayarta shin lafiya, ta amsa mata da tana zuwa. Guitar ɗinta kawai ta saka a cikin jakarta, sannan ta ɗauki canvas ɗinta ta saka a ƙafarta, ta tsaya a jikin mirror ta gyara gashin kanta. Sannan ta goya jakar guitar ɗin a bayanta, ta fita ba tare da mayafi ba, dan ta saba yin hakan kullum.
Ba ma ita kaɗai ba, a muslman 'yan matan larabawa ba kowacce ce ke saka mayafi lokacin da za ya fita ba. Mafiya yawan waɗan da za ka ga da mayafi a waje to matan aure ne, dan 'yan matan ba su cika yin hakan ba, shi ya sa idan aka gansu a waje za a ɗauka cewa ba musulmai ba ne, dan duk wasu ɗabi'u na turawa sun ɗauka sun yafa a jikinsu.
“Ina ya kamata mu je?”
Uwais ya tambaya yana duban Ivana dake zaune a kujerar gefensa. Yayin da yake tuƙa motarsa cikin nutsuwa, kuma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana kan bakinsa. Ivana ta kalli hanya tana murmushi.
“Duk inda kake ganin zai yi kyau da zama a lokaci irin wannan”
Ya sake dubanta, sannan ya ɗauke kai yana dariya, bluewaters island shi ne wurin da ya fara zuwa ransa. Dan haka ya nufi wurin, a gefe ya samu wuri ya faka motarsa, sannan suka fito daga motar, yana riƙe da bag ɗin guitar ɗinta. Yayin da suka jera suna tafiya a cikin yammacin.
Daddaɗar iskar da ruwan wurin ke badawa tana busawa a ko ina, akwai kaikawon mutane a wurin, kowa yana harkar da ta kawo shi. Da haka suka samu wani bench suka zauna. Kafin Uwais yace bari ya siyo musu abin sha, tana zaune a wurin har ya siyo ya dawo, ya bata drink ɗin, ta masa godiya tana kallonsa yayin da yake zama, a lokaci guda ta saƙala gashinta a bayan kunnenta, sakamakon iskar wurin dake kaɗa gashin nata.
“Ina za ki je?”
Uwais ya tambaya. Sai ta kalle shi tana shan drink ɗin da ya bata, sannan ta jinjina kanta.
“Akwai abokina da zamu taya murnar ƙarin shekara. Dan haka muka shirya tafiya zuwa Germany”
Ta ba shi amsa tana kallon wheel ɗin dake wurin. Uwais ya jinjina kansa.
“Kamar kwana nawa kike ganin za ki yi?”
Ta ɗan juya idonta, sannan ta tura gashinta baya tana faɗin.
“A ƙalla sati ɗaya... Da wani abu ne?”
Sai ya girgiza kansa yana kallon bottle ɗin drink ɗin dake riƙe a hannunsa, sannan ya sake dubanta.
“Idan kin dawo akwai wani abu da nake so na sanar dake”
Ivana ta yi murmushi me faɗi.
“Me ya sa ba yanzu ba?”
“Saboda ba na so wani abu ya katse ƙudirina a kanki, na fi so sai kin je kin dawo...”
Ta yi shiru kawai, dan ba ta san me za ta sake cewa ba kuma.
“Ina son kiɗan guitar, ko za ki kaɗa min?”
Ya katse shirun yana ɗaukan bag ɗin guitar ɗinta.
“Akid (of course)”
Ta aje bottle ɗin hannunta a tsakiyarsu, sannan ta karɓi guitar ɗin, ta cireta daga cikin jakar, ta ɗorata a kan cinyarta, sannan ta riƙe neck ɗin guitar ɗin tare da ɗora hannunta a kan frets dake jikin neck ɗin. Ɗayan hannun nata kuma na kan body ɗin guitar ɗin, yayin da yatsun hannun ke kan sound hole na guitar ɗin, sai da ta dube shi, sannan cike da ƙwarewa ta soma kaɗa guitar ɗin.
Cikin wani irin sauti me daɗin gaske, me sanyayawa tare da kwantar da hankalin mai sauraronsa. Ko daga nesa ka jiyo kiɗan dole ya ɗauki hankalinka. Dan ba ta daɗe da farawa ba masu wucewa suka fara tsayawa kallonta, har da wasu yara da suka tsaya a gabanta suna rawa, ba ita kaɗai ba, hatta Uwais abin ya ba shi nishaɗi.
Salma Ahmad Isah ✍️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
. 🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad
Page-6
*MK Fencing Academy,19th Floor, The Binary by Omniyat, Business Bay, Dubai, UAE.*
ARMAN POV.
Tun yana cikin hall ɗin horar da wasan takobin Gulzar ke kiran wayarsa, amma bai ɗaga ba, har sai da ya je office ɗin shugaban wurin, ya ɗauki izinin hutu na sati ɗaya, dan sati ɗaya shi ne tsawon lokacin da suka tsara za su yi a tafiyar tasu, ba tare da sanin abin da zai biyo baya ba.
Sai da aka lamince masa, sannan ya yi godiya ya fito daga office ɗin yana jan tsaki, saboda wani kiran Gulzar ɗin dake shigowa wayarsa. Tafiya ya fara a cikin business Bay, yana gyara zaman glasses ɗinsa. Sanye yake da plain hoodie ash color, da kuma baƙar denim jacket da ya ɗora a saman hoodie ɗin. Sai ligh blue baggy jeans, ƙafafunsa na cikin farin huaraches, ya saka baƙar p-cap a kansa, wadda ta taimaka wurin rufe sumar kansa da a kullum take cikin curly top, amma duk da haka sai da gashin ya fito ta jikin hular, kasancewar ya juya rumfar hular ƙeyarsa. Sai da ya shiga motarsa sannan ya ɗaga kiran Gulzar.
“A ƙalla na maka kira ya kai ashirin! Amma sai yanzu ka ga damar ɗagawa?”
Ta soma da ƙorafi, Arman ya rufe motarsa ƙirar Rimac C_two, jar kala, dan yau da ita ya fito.
“Ina class ne, ni ba na son ƙorafi, faɗi me zan miki?”
“Shopping za ka zo ka kaini”
Ta amsa daga cikin wayar, Arman ya saki baki.
“Duk direbobin gidan nan a rasa wanda zai kaiki shopping sai Arman?”
Ya tambaya yana nuna ƙirjinsa da keyn motar dake hannunsa.
“Eh kai nake so ka zo ka kaini, saboda akwai wasu kaya da zan sai maka kaima”
Sai ya yi dariya.
“Gani nan zuwa”
Ya katse kiran,

Chapter 6 of 13