Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
saka ranar aure!’
Mahaifin yariman ya faɗa, Iqrah ta kalle shi, sannan ta kalli mahaifinta Malik Cangaz da shi ma ke zaune a ɗakin cin abincin. Amma shi sai ya ƙi ya kalleta, ya yi murmushi me kyau, sannan yace.
“Babu buƙatar sai mun ji daga gareta, dan haka yanzu ma za mu iya saka ranar da za'a yi auren”
Maganarsa ta tarwatsa duk wani fata da Iqrah ke da shi, kuma dalilin maganarsa yasa ta ƙudiri aikata abin da ba zai musu daɗi ba daga ita har shi. Ta kalli yariman tana jin kamar ta shaƙo wuyansa ta maƙure shi a bango har sai ya daina numfashi, sannan ta kalli mahaifinta, sai dai ba ta da ikon cewa uffan. Har suka gama yanke abin da za su yanke, aka sallameta.
Champa da sauran hadimanta suka mata rakiya zuwa ɗakinta. Sai da suka sadata da ɗakinta, sannan ta sallami sauran hadiman, ta dakatar da Champa kawai. Sannan ta dubeta tana faɗin.
“Gobe ki tabbatar kin zo min da kayan da kika saba kawo min na saka a duk lokacin da nake son na yi shigar ɓadda kama na fita, kada ki bari kowa ya san cewa gobe zan fita domin ganawa da Eid!”
Kan Champa a ƙasa ta jinjina shi.
“An gama gimbiyar kyawawa”
Daga haka ta mata lamunim fita daga ɗakin. Tana shirin zama a bakin gadonta ASRA ta shigo ɗakin, kamar kullum, sanye ce kin shigar yaƙi, domin a ko da yaushe ita tana cikin shirinta na yaƙi. Kallon juna suka yi, kafin Iqrah ta ɗauke kai ta zauna a kan gadon cike da damuwa. Asra ta ƙarasa cikin ɗakin, sannan ta zauna kusa da 'yar uwarta me matuƙar kama da ita.
“Ina kika tafi tsawon kwana uku bana ganinki?”
Iqrah ta gefo mata tambayar bayan wani lokaci. Asra ta yi murmushi.
“Malik ne ya tura mu yaƙar wani ƙauye dake cikin dajin Urf al-tawul... Tafiyar ta taso a bazata, shi yasa ban sanar miki ba kafin mu tafi!”
Iqrah ta kalli 'yar uwarta, ita ke nan rayuwarta ba hutu, a ko da yaushe sarki na bata ayyukan da suka girmi hankali, har suna ganin kamar ya manta a mace aka haifeta ba namiji ba. Domin ya mayar da ita tamkar namiji, hatta da muryarta ta fi ta mata girma, yanayin tafiyarta da kuma shigarta ya banbantata ta mata, duk da ta kasance mace.
“Darvesh (Holy man) yace min ya zaɓa miki mijin aure, hasali ma nan da mako guda za'a yi aurenki... Faɗa min kina farin ciki?”
Asra ta tambaya, Iqrah ya juya idonta.
“Bana farin ciki Asra, saboda bana son zaɓin Abbu, ni ina da wanda nake so, amma na san ko da na sanar masa da hakan ba zai goyi bayana ba”
Asra ta dafa kafaɗar ƙanwarta.
“Haka ƙaddarorinmu suke Iqrah, daga ni har ke ba za mu iya sauyasu ba, dole ne mu bi abin da Malik yake so, ko da kuwa mu ba ma ra'ayin hakan!”
Iqrah ta miƙe tsaye.
“Na daɗe ina bin duk wasu dokoki da zai kafa min, amma ba zan bi wannan ba...”
“Me za ki yi ke nan?”
Asra ta kasteta tana miƙewa ita ma.
”Zan gudu tare da wanda nake so!...”
Ba ta rufe bakinta ba Asra ta sharara mata marin da ya yi sannadiyar fitar jini daga bakinta, sannan cikin zallar ɓacin rai ta nunata da yatsa.
“Ki yi komai ba komai, amma yin kuskure irin wanda Sana ta tafka ba zan bari ki aikata shi ba...”
Iqrah ta dafe wurin da ta mareta hawaye na bin kuncinta tace.
“Tun da ke kin bari ya gurgunta miki rayuwarki sai ni ma na bari ya ruguje min rayuwa ta hanyar rabani da Eid? Duk abin da zai min sai dai ya min, amma ba zan taɓa rabuwa da Eid na auri wani ba...!”
Asra ta sake ɗaga hannunta za ta sake marinta, amma sai ta fasa.
“Mutuwa ce kaɗai za ta shiga tsakanin da dakatar da ke kan abinda kike son aikatawa... Zan yi komai domin ganin ban barki kin aikata irin abin da Sana ta yi ba, na gwammaci ace ni na kasheki da hannayena da na bari Malik ya saka miki ciwo irin wanda ya sakawa Sana...”
Tana gama faɗin hakan ta fita daga sashin Iqra rai a ɓace. Yayin da Iqra ta kwanta a saman gadonta tana kuka.
Salma

Ahmad

Isah

✍️
_______________
_Book one ya ɗauki hanyar ƙarewa, dan bai fi pages 5 ne suka rage a gaba ba._
_Idan kun shirya bibiyar wannan tafiyar sai ku biya ₦400 regular group. Akwai V.I.P ₦800._
_Za ku tura kuɗinku ta wannan account ɗin._
5487270431
Salma Isah
Monie point
Sai ku tura shaidar biyanku ta wannan lambar 08130172702.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.

🪄

...JUYIN

KWAƊO...🪄
©️Salma

Ahmad

Isah

SalmaAhmadIsah

@ArewaBooks
SalmaAhmadIsah

@Wattpad
Page-11
ƘAUYEN ASKAR.
Mamaki ne yasa Ivana ta sandare a tsaye, sakamakon ganin wani mutum me kama da Uwais Fazil wanda ta sani a Dubai, kuma a zamaninsu, yanzu sai ga shi suna ganinsa a matsayin wani Uwais ɗin, amma Uwais bin Dhaakir. Banbancin wancan Uwais ɗin da wannan da take gani kawai shi ne dogon gashin dake kan wannan, sai kuma yanayin shigarsu. Amma za ta iya rantsewa da Allah kan wannan Uwais ɗin da ta sani a Dubai ne.
“...Ivana!”
Adam ya kira sunanta yana taɓata, a ƙokarinsa na dawo da ita zahiri, dan ya ga kamar ta lula duniyar tunani, firgigit ta yi ta kalle shi tana amsawa.
“Me ya sameki?...”
Ta kalli Adam, sannan ta juya ta kalli Arman, ta sake tsayar da dubanta a kan yarima Uwais dake tsaye a gabansu, shigar jikinsa ta ƙara kalla, sannan ta sake duban fuskarsa. Shi ma sai kallonta yake kamar ya santa a wani wurin, wata ƙila kuma shigar jikinta yake kallo...
“Ku ci abinci”
Cewar Tsohuwa Feroza tana aje musu wani tray dake ɗauke da Mujaddara, wani nau'in abinci na wancan ƙarnin, wanda ake yinsa da shinka, kayan lambu da kuma nama. Kasancewar suna jin yunwa yasa ba su musa cin abincin ba a wannan lokacin. Suka fara cin abincin a ɗarare, kamar suna cin dutse, dan sam abincin ba shi da ɗanɗano mai daɗi a baki, na kamar wanda suka sana ci ba. Shi dai Adam a ransa mamaki yake na yanda aka yi mutanen da suka rayu cikin farin ciki. Har suka ƙare cin abincin Ivana na satar kallon Uwais, kuma daga zarar ta kalle shi za ta ga shi ma kallonta yake. Har Arman ya fara lura da hakan. Amma bai mata magana a lokacin ba har suka kammala cin abincin, suka samu damar yin wanka, sannan suka sauya tufafi.
Lokacin da suka gama shiryawa suka dawo 'yar farfajiyar gidan Feroza, inda suke tsaye ita da Uwais. Shi ma da jakarsa a tare da shi, alamun dai ya gama shiryawa za su ci gaba da tafiya. Tsaye suka yi suna kallon uwar da ɗanta suna sallama, da alama duk tsawon shekarun da suke rayuwa tare ba su taɓa rabuwa da juna ba sai a sannan karo.
“Ka tabbatar sun isa inda suke son zuwa cikin aminci!”
Faɗin Feroza tana danƙawa ɗanta taswirar da su Arman suka bata, Uwais ya karɓa yana murmushi, sannan ya sakata cikin jakar kayansa, kana ya rungumi mahaifiyarsa.
“Ki min addu'a ya Umma”
Ya faɗa suna sakin juna, Feroza ta shafa kansa.
“Addu'ata za ta kansace tare da kai a duk inda ka sa ƙafa yarimana”
Ya yi murmushi me kyau, sannan ya ɗauki jakarsa.
“Sai Allah ya mana dawowa Umma”
Feroza ta share ƙwallar da ta zubo mata, tana kallonsu har suka fita daga gidan, ta cikin ɗan ƙaramin ƙauyen suka bi, mutanen ƙauyen suka yi ta binsu da kallo, sakamakon yanayin shigarsu Arman, dan ba su yi kama da mutanensu ba. Shi ko Adam hotunan ginin ƙauyen da kuma na mutanen ƙauyen ya shiga ɗauka, yayin da Ivana da Uwais suka ci gaba da satar kallon juna.
Har suka fita daga ƙauyen suka nausa cikin daji, sun yi tafiya me matuƙar tsayi, kafin suka samu yada zango a cikin dajin, suka zauna suna hutawa, yayin da Uwais ya tafi naima musu abin da za su ci, sai a lokacin Arman ya fasu ya tambayi Ivana abin da ke ransa.
“Ivana kin san Uwais a wani wuri kafin nan?”
Duk da tambayar ta zo mata a bazata sai da ta yi murmushi, yayin da take karkaɗe jakar guitar ɗinta.
“A ina za ta san shi? Ita da mai tafiya a tsakanin zamani ba?”
Adam ya rigata bawa Arman amsa, amma sai ta girgiza kansa.
“Ko kaɗan, mun taɓa haɗuwa da wani Uwais ɗin da ban a Dubai!”
Adam ya zaro ido yana kallonta.
“Kun taɓa haɗuwa? Ke nan har a zamaninmu yana raye bai mutu ba? Da ma fa aljannu suna da taurin rai, shi yasa nake kaffa-kaffa da shi, dan Wallahi tsoronsa nake ji”
Ivana ta yi dariya.
“Ba lalle ace shi ba ne, amma wancan zai iya kasancewa me kamarsa ne”
Arman ya gyara zaman glasses ɗinsa yana jinjina kai.
“komai zai iya kasancewa, kuma shi ma sai kallonki yake ta yi, kamar ya sanki”
Ivana ta sake darawa.
“Ban sani ba”
“Ga shi can ya dawo”
Cewar Adam yana nuna Uwais da ya nufo wurin da suke.
“Barkanku da hutawa”
Cewar Uwais yana aje jakar da ya zo da ita. Su dai kallonsa suke, an ce musu rabinsa mutum ne kuma rabinsa aljani, amma su dai mutum suke gani.
“'Ya 'yan itaciya ne na samu, da fatan za ku iya ci”
Ya ƙarashe yana duban Ivana, Ivana ta ɗan yi gajeren murmushi tana kallonsa ita ma.
“Me zai hana mu iya ci”
Arman ya ja jakar yana faɗa, Uwais ya zauna a gefe yana nasa murmushin, suka fitar da kayan dake ciki, har suka fara ci amma shi Uwais sarewarsa ma yake gogewa.
“Kai ba za ka ci ba?”
Cewar Arman yana dubansa, sai ya kalle shi.
“Ba na jin yunwa yanzu, daga zarar na ji yunwar zan naimi abinci”
“A ƙalla kana iya kwana nawa ba tare da ka ci abinci ba?”
Adam ya tamabaya.
“Mako guda”
“Mako guda sati ɗaya ke nan?”
Adam ya zaro idanuwansa cike da mamaki.
“Wannan fa, mi ye a hannunka?”
A wannan karon Ivana ce ta yi tambayar, sai ya kalleta.
“Sarewa, takobi kuma baka!”
“Sarewa, takobi kuma baka duka lokaci guda?”
Faɗin Arman.
“Eh, na kan iya yin busa da ita a lokacin da nake bukata, na kan iya juyata ta koma baka idan ina son kare kaina, amma kuma ainahinta ta kasance takobin mahaifina!”
“Ke nan wannan ita ce takobin sarautar da sarki Safraz yake naimanta?”
Cewar Adam.
“Ƙwarai, ita ce, kuma na san yanzu haka zai samu labarin bayyanar takobin, sannan zai iya yunkurin ƙwaceta daga hannuna ta ko wace hanya”
Matasan uku suka dubi junansa, a lokacin da tunani ɗaya ya ziyarci ƙwaƙwalansu. Sun fuskanci cewa haɗuwarsu da Uwais ba sauƙi zai kawowa lamarinsu ba face ƙarin wasu ƙalubale da kuma matsaloli. Da ace Malik Cangaz kaɗai za su yaƙa abin zai iya zama da sauƙi, tun da shi bil adama ne, amma faɗa da aljani ai abin ya girmi tunanin me hankali!.
MAMLAKATUL AFSAH.
Fadar masarautar cike take da 'yan majalissar sarki, yayin da sarki ke zaune a kan karagarsa, ana ta gudanar da sha'anin mulki. Sarkin na bayar da wani jawabi a kan wata matsala da ta kunno kai a masarautar. Cak ya tsaya da jawabin da yake, lokacin da ɗaya daga cikin masu gadin babbar ƙofar shigowa fadar ya shigo fadar da sauri, ya zube a gaban sarki ya kwashi gaisuwa.
“Sarki ya amsa bafade, faɗi abin da ke tafe da kai kanka tsaye!”
Cewar waziri, Ba fade ya risinar da kai, sannan ya furta.
“Ya shugabana yanzu muke samun masaniya daga dakarun ɓoye dake bibiyar lamarin takobin mulki da kuka aika... Cewar suna jin alamun an fito da takobin daga maɓoyarsa”
Babu shiri sarki ya miƙe tsaye a kan ƙafafunsa, domin haƙiƙa batun ya girgiza tunaninsa, ba ma shi kaɗai ba, hatta da sauran fadawansa sai da batun ya saka suke miƙe tsaye. A ƙalla yanzu an kwashi shekaru sama da ashirin, babu wani batu daga masu biciken takobin sai yau...
“Ina wakilan ɓoye suke? Duk inda suke a tabbatar an naimo min su, an kawosu nan”
Hadimin ya miƙe a kan ƙafafunsa yana risinar da kansa a gaban shugabansa tare da faɗin.
“An gama adalin sarki!”
Har hadimin ya fita daga fadar idon sarki na kan ƙofar shigowa fadar, yana saƙa mabanbantan abubuwa a ransa, shin me zai sa Feroza ta fito daga maɓoyarta bayan wasu shekaru masu tsayi? Imma dai ya kasance takobin ya bayyana ne ba tare da saninta ba, ko kuma ta bayyanar da shi da gayya, domin akwai wani abu da ta taka. Ko ma dai mene ne, shi ba zai sauka a daga kan ƙudirinsa na son ganin ƙwatar takobin daga gareta ko ɗanta.
IQRAH.
Tun a safiyar yau ta shirya tsaf a ɗakinta, tana jiran zuwan Champa domin ta kawo mata tufafin da ta saba sakawa a duk sanda take son ta yi fitar ɓadda kama ba tare da sanin kowa a fada ba. Lokacin da Champa ta kawo mata kayan yi ta yi kamar za ta sumbaceta dan farin ciki, cikin hanzari ta saka baƙaƙen tufafin a jikinta.
Sannan ta rufe fuskarta, ta jawa Champa kunne kan kada ta kuskura ta fita daga ɗakinta, kuma duk wanda ya zo ganinta ta sanar da shi ita tace ba ta buƙatar ganin kowa. Da haka ta samu ta silale ta fita daga ɗakin, ta yi ta ratsawa ta faluka da wuraren hutawa dake cikin fadar. Har ta samu ta fita harabar fadar babu wanda ya ganeta, dan kanta a ƙasa take tafiya, yayin da ta sauya salaon takunta.
Duk yawan masu gadin fadar da hadimai dake kai kawo babu wanda ya iya ganeta, da haka ta kutsa cikin gari, kyakkyawan birnin Jiyad na da kyawawan gine-gine irin na waccan lokacin. Sanda ta shiga cikin gari aka fara kiran sallah a babban masallacin garin, hakan yasa kaikawon mutane ya ƙaru, kowa na shirin tafiya masallaci.
Kuma hakan kyakkyawar dama ce a gareta, wadda za ta yi amfani da ita wurin isa ga abin da take burin cimmawa. Can ƙarshen ganuwar garin ta bangaren yamma ta yi, har sai da ta fara nisa da gidaje, sannan ne ta fara hango shi a jikin wata bishiya ya jingina.
Matashin saurayin SA'EID ALI, na sanye cikin tufafin Dishdasha, wasu nau'in kayan larabawa na wancan ƙarnin, wanda ake saƙa shi da zaren lilin, kayan ba masu tsada ba ne, hakan ya sa kowa kan iya saka shi a rayuwar yau da kullum. Rigar Dishdasha doguwa ce, haka ma wandon rigar. Kansa babu rawani, hakan yasa kyakkywan gashin kansa kalar (brown) bayyana. Mujiyarsa da ya yi wa laƙabi da Aafa na a kan kafaɗarsa ta dama.
Tun da ya hangota ya fara murmushi, ya gyara tsaiwarsa har ta iso gabansa, suka tsaya kallon juna, duk da shi kwarmin idanunta kawai yake gani, dan gaba ɗaya ta rufe fuskarta, bayan idanuwanta ba ka ganin komai. Hannunta na dama ta saka ta buɗe fuskarta, hakan ya bayyanar da kyakkyawar hallitar fuskarta gare shi.
“Tsawon lokacin da na ɗauka ba tare da na ganki ba ya sanya na ji kamar duniyar nan ba ta juyawa sarauniyar kyawawa, da fatan kina cikin ƙoshin lafiya”
Cewar Eid cikin muryarsa me sanyi. Murmushi Iqrah ta yi, sannan ta jinjina kanta, domin ba ta ji tana da amsar maganar tasa ba, dan haka kai tsaye ta tafi kan maganar da ta haɗasu a wurin.
“Ban sani ba ko labarin auren da Abbu yake son haɗawa tsakanina da yarima ɗan sarkin Mamlakatul Azad ya riskeka!”
Lokacin da ta kai ga ƙarshen maganar tata fuskar Eid ta sauya launi, daga farin cikin ganin abar begen zuciyarsa zuwa baƙin ciki mabayyani.
“Gimbiyata me ya sa za ki bari su fara ƙoƙarin rabani da ke?”
Ya tambaya a dugunzume, Iqrah ta girgiza kanta, sannan ya yi taku biyu zuwa gareshi, sannan ta saka hannunta ta kamo hannayensa.
“Ko da numfashina zai rabu da gangar jikina ba zan taɓa bari wani ya rabani da kai ba Eid, domin kai nake so, ba na son wani bayan kai, kuma kai kaɗai nake so a matsayin ABOKIN RAYUWA!”
(Anty Candy's new book, lolz).
Eid ya girgiza kansa, tare da ƙwace hannayensa da ta riƙe, ya juya bayansa yana kallon birnin Jiyad, murya ɗauke da damuwa ya furta.
“Ba haka ba ne Mehbuba. Ƙoƙarin haɗa aurenki da wani bayan ni na nufin zan rasaki har abada, kuma rasaki a rayuwata na nufin zuwan ƙarshen numfashina!”
Iqrah ta sake girgiza kanta, sannan ta zagayo ta sake tsayawa a gabansa.
“Da ace ka mutu kai kaɗai gara ace tare muka mutu, mu mutu ba tare da mun mallaki juna ba na nufin ba mu cimma burin soyayyarmu ba, dan haka ni na yanke shawarar mu guda kawai mu je domin a ɗaura mana aure!”
Eid ya mata wani irin kallo, sannan ya girgiza kansa.
“Ba na so Malik ya cutar dake Mehbuba ba zan iya zuba ido ina kallo a cutar min da ke ba”
“A'a Eid, zan iya yin komai a kan soyayyarmu, dan haka na yanke shawarar za mu gudu tare da kai a ranar da za'a ɗaura mana aure da wancan yariman, kuma a wannan ranar nake so a ɗaura mana aure ni da kai masoyina”
Eid ya tsaida dubansa a kanta.
“Kin tabbata abar sona?”
Ta gyaɗa kai. Daga haka suka shiga tsara yanda shirinsu na guduwa daga birnin Jiyad zai kansace. Ba tare da sanin abin da hakan ka iya jawowa ba. Sai da suka gama tsara shirin nasu, sannan ta masa sallama ta tafi.
Sai da ta ɓace masa da gani, sannan Eid ya sheƙe da dariya, har da hawaye, kafin lokaci guda ya haɗe rai. Ya saka ɗan yatsansa ya ɗauke hawayen da ya zubo masa.
“Dole ne Malik Cangaz ya biya bashin da ya ci... Kuma wannan kyakkyawar dama ce da zan yi amfani da ita wurin rama abin da ka min!”
Lokaci guda kalar zaluncin da Malik Cangaz ya aikata masa ya shiga dawo masa, amma sai ya yi saurin ture komai, ya sauƙo da mujiyarsa dake kan kafaɗarsa, bayanta kawai ya shafa, ta rikiɗa ta zama ƙatuwa. Ya kama bayanta ya ɗale, sannan ta buɗe fukafukanta ta tashi sama da shi.
Salma Ahmad Isah ✍️.
_____________
_Ta ko ina littafin nan ya kama da wuta, dan ƙiri ya rage papers ɗin book ɗin su ƙone!🤣._
_Na ce muku tafiyar bana ta sha bamban da sauran_
_Dan haka sai ku sake shiryawa, domin jarumanmu na cikin tuƙeƙiyar matsala._
_Sannan kar a manta da biyan kuɗin book, regular group ₦400, VIP ₦800._
_Ku tura kuɗinku ta account details ɗin da zan rubuta a ƙasa_
5487270431
Salma Isah
Monie point
A tura shaidar biya ta 08130172702.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
🪄 ...JUYIN KWAƊO...🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad
Page-12
ADVENTURERS.
Tafiyarsu ta miƙa a cikin dajika da tsaunika, sun yi tafiya irin wadda ba su taɓa yi ba a rayuwarsu, hatta shi kansa Uwais bai taɓa yin doguwar tafiya irin wannan ba, dan ko shi kansa ba sanin hanyoyin ya yi ba, ta hanyar wannan taswirar da suke ɗauke da ita ne kaɗai suke iya gane hanyoyi. Batun abinci kuwa tun kafin su ji yunwa Uwais yake kawo musu abin da za su ci, tun abincin ba ya musu daɗi har ya zamto sun fara sabawa da abincin.
Ranar da suka cika kwanaki biyar da barin ƙauyen Askar cif, suka shiga wani daji me yawan dogayen duwatsu. Su huɗun cif suna tafe a tare, Arman da Adam na kan gaba, yayin da camera ɗin Adam ke rataye a wuyansa, dan ba ya rabo da ita, daga zarar ya ga abin ɗauka zai ɗauke shi a hoto. Ivana da Uwais kuma na daga baya suna hirar da suka saba yi a lokuta irin wannan.
“Me yasa kake yawan kallona?”
Ivana ta jefa masa tambayar, dan za ta iya cewa daga zarar tana wuri Uwais ba shi da abin kallon da ya wuce ita.
“Saboda irin shigar da kike, da farko na ɗauka cewa ke ba musulma ba ce, sai da na ga yanda kike suturta jikinki lokacin da za ki yi sallah, amma kuma bayan kin idar sai ki yaye ki koma shigarki mai nuna tsaraici!... Sai na cewa kaina, idan har za'a suturta jiki yayin yin ibadar Allah, me zai hana a ci gaba da suturta jiki ko ba lokacin da za'a bauta masa ba, domin zamanki da irin wannan shigar na cikin saɓa masa!”
Hatta Adam da Arman sai da suka tsaya suna dubansa, saboda ya yi magana ta hankali. Ganin suna kallonsa yasa yace.
“Ku yi haƙuri fa, na fuskanci kamar hakan ba komai ha ne a zamaninku... Amma ni gani na yi ya kamata ace na faɗa mata gaskiya”
Ivana ta dubi shigar dake jikinta ta slacks trouser peach color, da farar blouse, wandon sam bai kai idon sawunta ba, har gwanda ma rigar na da ɗan tsayi, kuma duk sai ta ji jikinta ya yi sanyi, domin ita kanta ta san cewa abin da suka yarda da shi a matsayin wayewa kauce hanya ne...
“Ki yi haƙuri idan maganata ta sa kin ji ba daɗi!”
Uwais ya sake faɗa yayin da suka ci gaba da tafiya, ta girgiza masa kai tana murmushi, alamun ba komai, sannan ta gyara zaman jakar guitar ɗinta dake goye a bayanta, dan yanzu Arman ne yake ɗauka mata kaya.
“Mi ye sunan abin da yake cikin jakar nan, na ga kina yawan kulawa da shi”
Uwais ya tambaya. Ivana ta kalle shi, amma kamar yanda wancan Uwais ɗin yake mata magaba ba tare da ya kalleta ba shi ma wannan haka.
“Guitar sunanta, kuma ana yin kiɗa da ita, kamar dai sarewarka!”
Ya jinjina kansa.
“Ina son kiɗa sosai”
Ya faɗa, kamar yanda wancan Uwais ɗin ya taɓa faɗa mata cewar yana son kiɗan guitar.
“Ka iya busa sarewa?”
“Sosai, ko kina so ki ji?”
Ta gyaɗa kai, sai ya saka hannunsa ya zaro sarewar tasa dake saƙale a ƙugunsa, sannan ya kafata a bakinsa, ya soma busa sarewar cikin sauti me daɗin saurare, wanda ya cakuɗe da yanayin sanyin dajin da suke ciki. Hatta su Adam kansa busar sarewar tasa na musu daɗi.
Hakan yasa tafiyar tasu ta ƙara armashi, suna tafe yana musu busa me kwantar da hankali, a lokacin kuma suka yi kiciɓis da tawagar wasu mutane, sanye cikin shigar jajayen kaya. Hakan ya sa suka tsaya suna kallon yawan jama'ar, kafin su yi wani yinƙuri har mutanen sun musu ƙawanya... Kuma sam ba su da kataɓus, dan sarkin yawa, ya fi sarkin ƙarfi.
ASRA.
Tsaye take a cikin dakarun da take da alhakin koyar da su salon yaƙi na masarautar Jiyad, yayin da suke a wani babban fili da aka tanada domin koyar da faɗa a cikin masarautar, wani lallausan yashi ne zube a ƙasan wurin, yayin da muggan makamai na koyon salon yaƙi ke aje a ko wace kusurwa na wurin. Ta harɗe hannayenta, yayin da take kallon yanda ɗaliban nata ke nuna mata abin da ta koyar da su.
Tun daga nesa suka fara jin takun sawun masu gadin Malik Cangaz, hakan yasa ta dakatar da ɗaliban nata tun kafin ƙarasowar sarki wurin. A kan idonsu aka buɗe ƙofar filin, Malik Cangaz tare da masu tsaronsa suka shigo cikin filin. Hakan yasa Asra da ɗalibanta duka suka durƙusa domin kwasar gaisuwa.
Sai da sarki ya amshi gaisuwar tasu, sannan kowa ya miƙe kan ƙafafunsa, hakan ya bawa Asra damar matsawa kusa da Malik, domin jin abin da ke tafe da shi. Yau ma kammaninsa sak na matasa, ba za ka ce shi ne mahaifin

Chapter 11 of 13