Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kit, zaren sarƙar baƙi ne, pendant ɗinta kuma wani abu ne me kama da key, kuma daga ganinsa an ƙera shi ne da gold. Tsabar muhimmanci da darajar sarƙar a keɓe take a cikin shagon, an sanyata cikin wani glass me ɗaukar ido.
“Wannan ta kai kimanin nawa?”
Ya tambaya yana ɗaukan glass ɗin da aka sakata a ciki, me kantin ya yanko maƙudan kuɗaɗe ya faɗa, duk da sarƙar ta yi tsada hakan bai sa Adam ya fasa siyawa Arman ita ba, domin ko da zai ƙarar da kuɗin da yake da shi zai yi domin faranta ran Arman. Ita kuma Ivana sabon takobin fencing ta sai masa, da wasu ƙanun kyautuka da ta san za su burgeshi.
*Dubai...*
“Ina zuwa!”
Faɗin Maama dake wanke hannu a sink, yayin da take kallon ƙofar gidan da ake ƙwanƙwasawa. Hannunta ta goge, sannan ta nufi ƙofar ta buɗe, mamaki ya kamata, ganin Sayyid Iƙbal Alhadi da matarsa Zahra, da kuma 'yarsu Gulzar.
“Barkanku da zuwa... Ku shigo ciki mana”
Ta faɗa tana murmushi, tare da buɗe ƙofar gaba ɗaya, Abby ya ɗan yi murmushin yaƙe yana mata sallama, ta amsa yayin da yake shiga falon, ita kam Immi babu wata alamar walwala tare da ita, ta yi sallamar kamar da aka mata dole, sannan ta shiga falon ita ma, Gulzar kuwa bayan ta yi sallamar sai da ta gaida Maama sannan ta shiga. Su duka ukun a falo suka zauna, yayin da Maama ta koma flat kitchen ɗinta ta ɗauko abin sha, ta aje musu a center table suna sake gaisawa.
“Shin Adam yana nan?”
Abby ya tambaya, mamaki ya sa Maama ta kallesu, kafin cikin kokwanto tace.
“Adam? Ai jiya suka tafi Regen, Germany, kuma yace min tare da Arman za su tafi, ko dai Arman ɗin bai samu zuwa ba?”
Abby ya dafe kansa. Yayin da hawaye ya zubowa Immi.
“Arman guduwa ya yi ya bar gida ba tare da saninmu ba, yanzu haka ba dan kin faɗa ba da ba mu san inda yake ba”
Maama ta yi shiru, ta san irin haka sam ba daɗi. Da ace ita ce a matsayinsu da yanzu ita ma nata hankalin a tashe yake.
“Sayyid Iƙbal ka yi haƙuri, haƙiƙa abu irin wannan babu daɗi, amma su yaran yanzu idan har suka yanke hukunci babu wanda ya isa ya tablnƙwarasu, dan za su iya aikata abin da suke so a ɓoye ba tare da sun sanar da kai ba, ku yi haƙuri ku ci gaba da masa addu'a”
Abby ya dubi Maama, sannan ya yi murmushi kawai. Dan shi tun da har ya san inda yake matsala ta kau, Arman ba ƙaramin yaro ba ne da zai ɓata, ya sha yin tafiye-tafiye irin wannan, kuma shi kaɗai, dan haka yanzu hankalinsa ya kwanta, domin ko ba komai idan ya gama kwanakin nasa a Regen dole zai dawo gida!...
“Allah ya kareka shugaba!”
Shi ne kawai abin da ya furta. Dan ba ya jin yana da wani abin cewar bayan wannan.
*Regen, Germany.*
Adam ya ja tsaki a karo na barkatai, yayin da suke duban ƙofar hotel ɗin da suka kwana ciki, tsaye suke shi da Ivana da kuma Arman, a jikin motar da suka yo hayarta yau, domin yau ne za su shiga Bavarian forest. Ga shi rana ta kusa faɗuwa, amma har yanzu Hans bai zo ba.
Ivana na sanye cikin purple crop top, me ɗauke da ratsin baƙi-baƙi, da kuma wideleg bleach jeans, takalminta farin orthopedic sneakers ne. Gashinta ya sha gyara cikin style ɗin side braid pony tail, ta saka wani purple hair clip a karshen side braid ɗin. Yayin da ta ɗora baƙar wide brim hat a kanta, wadda za ya sauƙaƙa mata zafin ranar da ake, idonta manne da shade.
Adam kuma na sanye da maroon chinos trouser, da farar shirt, wadda ya ɗora mata ash hoodie a sama. Shi ma ya saka shade, saboda duk da rana ta kusa faɗuwa akwai zafinta har yanzu. Ƙafafunsa kuma na cikin farin huaraches.
Yayin da Arman ke sanye da gray khaki trouser, da farar shirt, wadda ya ɗorawa black bomber jacket a sama. Saɓanin sauran da suka saka shade shi glasses ɗinsa na kullum ne a idonsa. Ƙafafunsa na cikin farin canvas. Shi ma tsakin ya ja yana shafa sumar kansa, sannan ya dubi su Adam.
“Ya kamata mu tafi fa, dan da alama wannan ba shi da niyyar zuwa.”
“To da kake cewa mu tafi mun san hanyar ne?”
Cewar Adam, ya musu banza ya buɗe driver seat na motar ya shiga, har ya tada motar Ivana da Adam na kallonsa. Ganin ba su da niyyar shigowa motar yasa ya kallesu.
“Dare ne yake shirin yi, da dare ya mana a hanya mu ɓata, gara daren ya mana a cikin dajin. Matambayi ba ya ɓata, kuma Bavarian forest sannanne ne a ko ina, ba za mu rasa wani ɗan rakiyar ba a hanya... Dan haka ku zo mu tafi kawai”
Ivana da Adam suka haɗa ido, kamar kar su bi shawararsa su bari sai Hans ya zo, amma da yake tsautsayi ba ya wuce rana sai suka amince, suka shiga mota suka ɗauki hanyar Bavarian forest. Da ko wani taƙi da suke wucewa domin nufar dajin ƙaddararsu suke tunkara ba tare da sun sani ba. Domin da ace sun san abin da suke tunkara da sun yi tariyar zamanin baya, sun cire ranar da suka yanke shawarar zuwa Bavarian forest a cikin kwanakinsu na duniya.
Kasancewar ba su san hanya ba ya sa suke tambaya, har Allah ya sa suka samu damar kutsawa cikin dajin sosai, dan ma suna tsayawa jiran Adam ya ɗauki hoton abubuwan birgewa dake dajin, da haka suka iso inda hanya ta rabu biyu. Kokwanto ya sa Arman ya tsayar da motar, dan a cikin hanyoyin biyu bai san ta ina zai bi ba, ga shi kuma babu kowa a wurin bare su yi tambaya.
“Ina ya kamata mu bi?”
Ya tambayi Adam dake zaune a gefensa, Adam ya ɗaga kansa ya kalli hanyoyin biyu. Kuma a lokacin abin ya faru, a lokacin ƙofofin ƙaddarorinsu suka buɗe. Domin zuciya ɗaya Adam ya ɗaga hannunsa ya nuna hanyar da ta yi dama.
“Wannan hanyar ta maka kama da ana binta? Ji yanda ciyayi suka rufe hanyar fa, kuma sam babu alamar ana bin hanyar a yanzu”
Cewar Ivana dake baya. Arman da Adam suka dubeta.
“Ai dole hanyar ba za ta yi kama da ana bi ba, saboda an fi shigowa dajin a mota, so ba lalle ta nuna wata alama ba... Kuma ni jikina ya na bani cewar wannan ita ce hanyar”
“Arman kar ka saurare shi, saboda ni dai na ce waccan ita ce hanyar.”
“Ivana bari mu fara bi ta nan ɗin, idan ba ita ba ce sai mu dawo”
Cewar Arman da shi ma tasa zuciyar ta raya masa cewar hanyar da Adam ya nuna ita ce wadda za su bi. Ya tada motar, sannan ya juya kan motar zuwa hanyar da za ta sauya rayuwarsu. Har motarsu ta shige hanyar, a cikinsu babu wanda ya lura da allon sanarwar dake gefen hanya, wanda aka rubuta ‘CHEETAHS AHEAD. KEEP DISTANCE!’.
*Da misalin 10:22 na dare.*
Tantina (tent) uku ne kafe a tsakiyar wani fili, domin wurin da babu yawan dogayen bishiyu suka samu suka kafa tent. Yayin da motarsu ke fake kusa da tents ɗin, sun aje wasu gingimen bishiya guda uku wanda suke zaune a kai, yayin da wutar da suka hura domin ƙarawa daren nasu armashi ke a ci.
“Akwai sanyi sosai a wurin nan”
Faɗin Ivana tana ƙara nannaɗe hannunta cikin zip hoodie ɗin dake jikinta. Arman ya yi dariya yana shan drink ɗin dake hannunsa, yayin da Adam ke duba hotunan da ya ɗauka jiya a cikin garin Regen.
“Adam!”
Ivana ta kira tana dubansa, shi ma ya kalleta cikin alamun ya aka yi?. Da ido ta masa alama, take ya gane abin da take nufi, dan haka suka miƙe a tare kowa ya shiga tent ɗinsa, yayin da Arman ke binsu da kallo yana tambayar abin da ya faru. Cikinsu babu wanda ya amsa masa, dan haka ya miƙe yana kallon tents ɗin nasu, har suka fito, kowa a cikinsu hannunsa riƙe da gift box.
“Barka da ƙarin shekara abokina, ina tayaka murna”
Faɗin Ivana tana miƙa masa box ɗin kyautukan da ta sai masa, Arman ya yi dariya yana kallonsu, sannan ya saka hannu ya karɓa yana mata godiya, shi ma Adam ya miƙa masa nasa box ɗin guda ɗaya, wanda silar ƙaddararsu ke ciki, Arman ya aje wanda Ivana ta ba shi kusa da inda yake zaune da, sannan ya karɓi na Adam, ya masa godiya yana rungume shi.
“Na gode sosai abokina...”
Ya kalli Ivana dake kallonsu, sannan ya mata alama da hannu tare da faɗin.
“Taho mana”
Ta yi dariya sannan ta shiga space ɗin da suka yi creating ma ita, su duka abokan suka rungume junansu, a lokacin kuma kunnen Adam ya jiyo wani sauti me kama da kukan damisa. Hakan ya sa ya firgita ya janye jikinsa yana waige-waige.
“Hey lafiya?”
Ya kasa amsawa Arman, sai bin zagayen wurin da suke yake da kallo.
“Adam”
Ivana ta faɗa tana dafa shi, banda bugu babu abin da ƙirjinsa ke yi, kamar mace.
“Me ya faru?”
“Kamar... Kamar kukan damisa”
Ya amsa a tsorace.
“Damisa kuma? A nan ɗin?”
Arman ya tambaya, sannan ya kunna wata touch light ɗinsu me haske, ya shiga haska dajin, amma shi bai ga komai ba.
“Kai babu komai fa a nan”
Adam ya haɗiyi yawu yana girgiza kansa, in dai baiwar ji to Allah ya hore masa kamar maciji. Dan haka ba ya jin cewa kunnensa ne ke haihuwa, yana da tabbacin ya ji kukan damisa. Amma da su Ivana suka ƙaryata shi sai ya haƙura ya zauna yana baza ido kamar ɓera a tarko. Yayin da Ivana ta ɗauki guitar ɗinta ta soma kaɗawa, saboda Arman da ya buƙaci hakan.
Duka kyautukan da suka ba shi sai da ya buɗe su a lokacin, amma duk ciki babu wanda ya fi burge shi sama da makullin ƙaddararsu, wato sarƙar da Adam ya ba shi, dan sam kasa jurewa ya yi sai da ya saka sarƙar a wuyansa yana ta jin daɗi.
Sun ɗau lokaci sosai a wurin suna hira tare da cin abinci, kafin suka yanke shawarar kowa ya shiga ya kwanta, kasancewar Adam a tsorace yake yasa yace dan Allah Arman ya yarda su kwana a tent ɗaya, amma fir Arman ɗin yaƙi.
“To wai kai yanzu da kake haka ta ya za ka zama jarumi? Shi fa namiji da jarumta aka san shi, kalli Ivana, ita ma ita kaɗai za ta kwanta, mi ye zai cinyeta? Da har kai da kake namiji za ka ji tsoron kwana kai kaɗai”
Da wannan batu dai ya ƙwararawa kansa gwiwa ya shiga tent ɗinsa yana karanto duk addu'ar da ta gifto cikin tunaninsa, dan a tsorace yake matuƙa. A lokacin da kowannensu ya shiga tent ɗinsa, Cheetah ɗin dake laɓe a cikin daji ta juya zuwa wata hanyar!... 😳
Salma

Ahmad

Isah

✍️
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.

🪄

...JUYIN

KWAƊO...🪄
©️Salma

Ahmad

Isah

SalmaAhmadIsah

@ArewaBooks
SalmaAhmadIsah

@Wattpad
Page-8
*Bavarian forest, Germany.*
Yayin da hasken rana ya mamaye duniya, matasan uku suka shirya tsaf, domin zaga dajin da suka kwana ciki. Tun bayan da suka yi karin kumallo suka nannaɗe tents ɗinsu. Suka haɗa kaf kayansu cikin wasu dogayen backpack irin na matafiya.
Arman na sanye cikin wani 3qtr milk color, da farar hoodie mara nauyi, wadda ya ɗorawa black denim jacket a samanta. ƙafafunsa cikin takalmin timberland. Adam kuma na sanye da blue jeans da baƙar shirt, ya ɗora casual Oxford shirt a saman rigar, sai bakar p-cap da ya saka. Yayin da Ivana ke sanye da Orange T-shirt, sai jeans overall (corpenta) da ta saka, gashin kanta kuma na cikin French braid.
Kowanne a cikinsu na goye da jakar kayansa, yayin da suka kutsa cikin dajin cike da farin ciki da annashuwa, duk da har yanzu shi Adam a ɗarare yake, dan a tsorace yake ɗaukan hotunan wasu wuraren da suke da ban sha'awa. Duk da sam inda suke kutsawa a dajin bai yi kama da mutane na yawan bi ba bai sa sun fasa shiga ciki ba. Har suka iske wani kyakkyawan dausayi dake tsakiyar dajin, akwai nau'ikan bishiyoyi da tsirrai a wurin gwanin ban sha'awa, sannan akwai kogi dake a ta gefe, a gefe guda kuma akwai wani babban dutse da yake bayar da ruwa, wurin ya haɗu matuƙa.
“Wow wow wow! Amma wurin akwai ban sha'awa”
Faɗin Ivana tana ɗaga kanta tare da ƙarewa wurin kallo, yayin da shi kuma Arman ke gefe ta wurin kogin yana kallon yanda ruwan wurin ke gudana, shi kuma Adam ya riga ya fara ɗaukan wurin a hoto da camera ɗinsa.
“Ivana gyara na ɗaukeki hoto”
Ya faɗa yana saita camera ɗin a kanta, Ivana ta gyara tana murmushi, ya ɗauki hoton yana dariya, shi ma Arman ya matso yana faɗin a ɗauki hoton da shi, ya dafa Ivana Adam ya ɗaukesu tare. Suka sauya style suna jiran Adam ya ɗaukesu hoto, a cikin camerar Adam ya hango mutuwa.
Dan haka ya sanƙare yana wangale duka idanuwansa, jiki a saɓule ya sauƙe camerar yana rawar jiki kamar an jona masa lantarki.
“Ka ɗauke mu mana, ka wani tsaya a nan kamar saƙago”
Faɗin Arman yana gyara glasses ɗinsa, Adam ya soma ja da baya, sannan cikin karkarwar hannu ya ɗaga ɗan yatsansa, ya yi nuni da bayansu, hakan ya sa cike da mamaki Ivana da Arman suka dubi juna, kafin Ivana ta juya tana faɗin.
“Wai me ka gani da ka...”
Haɗiyewa sauran kalaman ta yi, tare da binsu da yawun bakinta tana zaro ido, kamar yanda ta yi kyakkyawan gani haka shi ma Arman ya yi, dan yana juyawa suka yi ido huɗu da Cheetah ɗin dake saman dutsen da yake zubar da ruwa.
Ba su tsaya ɓata lokaci ba suka ce ƙafa me na ci ban baki ba? Kowa a cikinsu ya ranta a na kare, gudu suke Cheetah ɗin na binsu, Adam ya fi koea ruɗewa, dan a gudun ma shi ne a kan gaba, dan tun da ya zo duniya bai san wani abu da ya firgita shi sama da wannan ba, sanin cewa Ivana me rauni ce ya sa Arman ya ruƙo hannunta yake janta suna gudu tun ƙarfinsu.
A yunƙurin ceton rayukansu suka faɗa cikin wani kogo dake bayan dutsen da Cheetah ɗin take, kuma suna shiga cikin kogon ba su tsaya wata-wata ba wurin naiman maɓoya, Arman ne ya fara ganin wata tsohuwar ƙofar katako dake cikin kogon, dan haka ya yi azamar saka duka hannayensa biyu, tare da ƙarfin da Allah ya wadata shi da shi ya buɗe ƙofar.
“Ku zo ku shiga”
Ya faɗa ba tare da ya tsaya duba abin da yake a bayan ƙofar ba, ya janyo hannun Ivana ya turata, an ce idan ka ga mutuwa idonka rufewa yake, tabbas idanuwansu sun rufe, domin har suka gama shigewa ƙofar sam ba su lura da ina suke shiga ba.
Abin da zai biyo bayan shigarsu wannan ƙofar sai ya fiye musu su tsaya wannan Cheetah ɗin da ta biyosu ta cinye naman jikkunansu ɗanye. Domin masifa da bala'in da zai biyo baya babu hankali ko tunanin da zai iya hasaso shi...
Yanzu ne labarin zai soma, sai a yanzu ne za mu kama ainahin hanyar da labarin yabi, yanzu ne muka saƙo zaren labarin, domin gane warwararsa, sai kun ji abin da ya biyo bayan shigewarsu cikin wannan ƙofa...
*Wani Zamani...*
Wani zamani na nufin zamanin da ya shuɗe kafin samuwarmu, ko kuma wanda zai zo bayan wanzuwarmu, zamani na zuwa ya wuce kamar wucewar damina da rani... Sannan zamani ya kan shuɗe, har a manta shi a duniya, matsawar babu masu bada labarin wannan zamanin... Sunan zamani na wakiltar shekaru 100 da suka suɗe a baya, ko waɗan da za su zo a gaba... A kan iya gane bambancin zamani ta hanyar tufafinsu, abincisu, gine-ginensu da kuma kalar yarensu...
*
Wani kyakkyawan daji ne, ko ina ka kalla koren ganye ne ke kaɗawa a cikin iskar Allah, dogayen bishiyu da ciyayin da suka ƙawata ƙasa su ne a ko ina. Kuma duk girman dajin babu komai cikinsa sai ginin wata bukka ƙwara ɗaya tal, wadda aka yi ta da busasshiyar ciyawa. (Budu)
Daga bayan bukkar, wani farin dattijo ne durƙushe, yana tsinkar 'ya'yan itaciyar da suka nuna har suna faɗowa daga jikin bishiryarsu. Wasu kayan saƙi ne sanye a jikinsa, wanda za su shaida maka daga zamanin da yake, gashin kansa dogo ne, domin har ya sauƙa gadon bayansa, duk da rawanin da ya yi a kansa.
Wata iska me matuƙar ƙarfi ce ta fara kaɗawa a dajin, hakan ya sa dattijon ya miƙe tsaye yana kallon dogayen bishiyun dake wurin, waɗan da ke kaɗawa da ƙarfi, sakamakon ƙarfin iskar da ake. Kansa ya juya ta ɓarin damansa kaɗan, nan ya ga wani jan kyalle dake ɗaure a saman bukkarsa na shirin sulmiyewa ya faɗo.
Hakan ya sa ya firfito da idonsa cike da abin da ya zarce a kira shi da mamaki. Bakinsa na rawa ya juya ya shiga bin dajin da kallo, amma bayan iskar dake ƙara ƙarfi babu kowa babu komai. Mamaki bai ƙara kama shi ba sai da ya ga jan ƙyallen ya kunce ya faɗi ƙasa...
A nan ne ya tabbatar da wani abu guda, lalle ranar da ya daɗe yana jiran isowarta ta zo, ranar da ya shafe sama da shekaru ashirin na rayuwarsa yana rayuwa a wannan dajin domin ta zo, ranar da za a yi wasu baƙin matasa uku, daga wani zamanin zuwa nasu...
“Tabbas!

Baƙin

matasa

uku

sun

samu

shigowa

duniyarmu.

Domin

zama

silar

kawo

ƙarshen

mulkin

zalunci.

Sun

zo

domin

tada

gagarumin

yaƙi

da

yake

dai-dai

da

yaƙin

duniya...

Ƙaddara

ba

ta

da

siffa,

ta

kan

juya

rayuwar

ɗan

adam

ta

ko

wace

siga,

sannan

ta

kan

iya

maida

sama

ta

dawo

ƙasa

cikin

abin

da

bai

fi

ƙiftawar

ido

ba.

Lalle

ƙaddara

ita

ce

ta

zamto

silar

wanzuwar

waɗannan

matasa

a

wannan

duniya

tamu...

Wannan

ƙaddara

ita

ce

ta yi JUYIN KWAƊO da rayuwar waɗannan matasa, daga zamaninsu zuwa namu...”
Kwandon kayan marmarin dake hannunsa ne ya suɓuce ya faɗi, yayin da ya ga haske ya fara mamaye dajin, saurin durƙushewa ya yi a ƙasa yana me godiya da mai duka...
*
Yashe suke a kan ciyayin dake kusa da wata ƙatuwar bishiya, idan ka musu kallo ɗaya sai ka ce a mace suke, amma kuma ba a macen suke ba, wani dogon bacci suke me kama da suma. Arman ne ya fara motsawa, kafin ya buɗe idonsa yana dafe kansa da ya sara lokaci guda.
Idonsa ya rufe ya sake buɗewa, amma saboda glasses ɗinsa a fashe suke ya sa ba ya gani da kyau, a daddafe ya miƙe zaune yana yarfe hannu, saboda Adam da ya danne masa hannun nasa, glasses ɗin ya cire, ya kamo ƙasan rigarsa ya goge shi, sannan ya mayar idonsa, a nan ne ya gane cewa glasses ɗin ne ya fashe. Tsaki ya ja, dubansa na kaiwa kan Adam dake kwance, ya sake jan wani tsakin tare da saka hannunsa ya ɗaka masa duka.
“Mun mutu... Damisa ta cinyemu!”
Ya farka da wannan batu a tsorace, amma ganin Damisar ba ta cinyesu ba ya sa ya fara son kwantar da hankalinsa, kusan a tare suka dubi Ivana dake can nesa da su, hakan ya sa Arman ya miƙe ya nufi inda take, ita ma ya tasheta.
“Wai a ina muke ne?”
Adam ya tambaya yana miƙewa tsaye, yayin da Arman ya cillar da tsohon glasses ɗinsa da ya fashe, Ivana kuma ta ba shi wani domin ya saka, sai da ya saka glasses ɗin sannan shi ma ya tsaya ƙarewa wurin kallo, daji ne fetal, ba gida gaba ba gida baya.
“Kai! Ina ƙofar da muka shigo?”
Cewar Ivana tana waige-waige, amma sam babu alamar ta a wurin, shi ko Arman shiru ya yi yana wani lissafi a cikin kansa, idan zai iya tunawa bayan wannan Cheetah ɗin ta biyosu sun buɗe wata ƙofa sun shiga, bayan da suka shiga ƙofar kuma ba su iya ganin komai ciki sai haske, sai wani abu me kama da iska da suka ji ya kwashesu, to daga nan ne ba su sake sanin me ke wakana a duniya ba sai yanzu...
“Arman a ina muke ne?”
Adam ya tambaya yana riƙo Arman, shi kansa Arman ba shi da wannan amsar, domin bai san a ina suke ba, bai san ya aka yi suka zo nan ba. A hankali ya ɗan matsa bayan bishiryar da suke kusa da ita, nan ya hangi wata bukka guda ɗaya tal.
“Ga wani ɗaki can, mu je mu duba”
Ya faɗa yana ɗaukan jakarsa, tare da goyata a bayansa. Suma nasu kayan suka ɗauka, sannan suka bi shi, shi dai Adam ya san cewa ɗakin bukka ce, su kuma sauran ba su san wani abu me kama da hakan ba. Shi ya sa tun kafin su ƙarasa kusa da bukkar suka fara taradaddin a duniyar da suke.
Ko da suka iske bukkar sai aka tsaya kallon-kallo, dan ba su san me za su iske a ciki ba. Arman ne ya fara ƙundun balar nufar ƙofar, yana taku a hankali, hannunsa ya sa ya ɗaga wani abu me kama da labule da ya saya ƙofar, hakan ya ba shi damar ganin cikin ɗakin.
Babu komai a ciki face tarin littattafai irin na da, da kuma wasu takardu da aka yi su da fatar dabbobi, sai wani gadon ciyawa dake a gefe, sannan wani gajeren teburi, wanda a kusa da shi wani farin dattijo ne zaune.
“Barka da zuwa JAGORA”
Su ne kawai kalaman da dattijon ya furta yana ɗora ido a kan Arman. Shi kuma Arman tsaye ya yi yana kallon tufafi da kayan ɗakin mutumin, ko kusa ko alama bai yi kama da wanda yake rayuwa a zamaninsu ba, mutumin ya fi kama da irin mutanen da suka rayu a baya.
Shiru suka yi su ukun, yayin da suke zaune gaban dattijo, banda kallonsa ba abin da suke, suna jiran ya amsa musu tambayoyin da suka soma masa, shi kuma sai murmushi yake musu, kamar wanda ya san da zuwansu.
“Ina ne nan?”
Arman ya sake nanatawa datijjon tambayar da Ivana ta fara masa tun ɗazu. Kuma sai yanzu ya samu damar ba shi amsa.
“Hayy al- Umda!”
Arman Ivana da Adam suka dubi juna cike da kokwanton da ya zarce na da, su har yanzu sun kasa gane abin da yake faruwa, amma Arman ya fara fuskantar wani abu guda...
“Ban taɓa jin sunan dajin nan ba, kuma mu a Bavarian forest muke ba Hayy al- Umda ba”
Cewar Ivana. Dattijo ya yi murmushi, sannan cikin larabcinsa me matuƙar daɗi da bawa ko

Chapter 8 of 13