🪄...JUYIN KWAƊO...🪄
_Daga ruwa zuwa ruwan zafi_
From the writer of:
YADDA ƘADDARA TA SO
LABARINSU
HASKE
ƘADDARA CE
ArewaBooks @SalmaAhmadIsah
Wattpad @SalmaAhmadIsah
*Gabaki ɗaya labarin JUYIN KWAƊO, da littafin kansa. Na sadaukar shi zuwa ga ZAHRA ROYAL STAR and NAINARH KD NKD'S. Your love and acceptance mean everything to me. Thank you for being my safe space and my forever friends.*
بسم الله الرحمن الر حيم
*Page-01*
*MK Fencing Academy,19th Floor, The Binary by Omniyat, Business Bay, Dubai, UAE.*
ARMAN IƘBAL.
Babu abin da yake tashi a ko ina sai hayaniya da iface-iface, sai kuma sautin sara da sukan takkuba. Kuma ko ina jini ne ke zuba... A tsakiyar wannan hatsaniyar yaƙin yake tsaye, can ya hango wani mayaƙi ya taho da gudu ya iyo kansa, hannunsa riƙe da wani takobi me tsananin kaifi, ya kawo masa sara da ita...
Tahowar sukan takobin cikin tunaninsa ya yi dai-dai da tahowar sukan takobin abokin karawarsa a tsakiyar filin hall ɗin koyon wasan takobi na MK fencing academy. Cikin zafin nama ya buɗe idonsa, sannan ya yi azamar kaucewa sukar takobin wasan. Cike da ƙwarewa kuma ya yi amfani da nasa takobin ya kaiwa abokin nasa farmaki, farmakin da ya yi nasarar kai shi ƙasa, hakan yasa ya zamo zakaran wasan, domin shi ne ya lashe!.
Malamai da ɗaliban wasan na takobi suka shiga tafa masa, hakan yasa ya juya kansa ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a hankali yake fitar da numfashi, domin wannan mafarkin da ya saba yi ido biyu yau ma ya raɓe shi, ya rasa mece ce alaƙarsa da wannan yaƙin da yake yawan yin mafarkinsa ido biyu ko cikin bacci. Ba ya jin ya taɓa tsallake sati ɗaya ba tare da ya yi mafarkin wannan yaƙin me firgitar da ɗan adam ba.
Shi dai ya san ba a haifeshi a ƙarnin da aka yi yaƙin ba, amma kuma ya rasa dalilin da yasa a ko da yaushe yaƙin yake raɓar rayuwarsa. Hannu ya kai ya taɓa farin glasses ɗin da ba ya taɓa rabuwa da su duk rintsi, kasancewar yana fama da lalurar rashin gani, wadda aka haife shi da ita. Da ace kuɗi yana samar da lafiya ya tabbatar da mahaifinsa Sayid Iƙbal Alhadi zai ƙarar da duk dukiyar da ya mallaka domin sama masa lafiyar ido.
Amma tun yana ƙarami ake fafutukar naima masa maganin da zai warkar da idon har zuwa yanzu da yake da shekaru talatin da ɗaya a duniya ba'a dace ba. Hakan tasa aka haƙura aka ƙyale maganin, ya ci gaba da amfani da glasses ɗin da da taimakonsu kaɗai yake iya ganin abin da Allah ya yassare masa ya gani.
“Muna tayaka murnar lashe wannan gasa Arman! Fatan nasara!”
Faɗin ɗaya daga cikin malaman dake koyar da su wasan takobi cikin harshen larabci. Yayin da yake miƙa masa award ɗin da aka tanada domin zakaran da ya lashe wannan gasa da aka saka a tsakanin ɗaliban makarantar. Hannu bibbiyu yasa ya karɓi award, sannan ya yi murmushi me kyau, tare da furta.
“Na gode”
Ya juya ya kalli abokansa da yake koyar wasan tare da su, ya ɗaga musu award ɗin, suka saka tafi har da masu ihu, shi dai murmushi kawai yake, har ya sauƙa daga kan stage ɗin wasan. Ya nufi ɗakin sauya kaya dake cikin hall ɗin, a nan ɗakin da ya shiga ya sauya kayan fencing ɗin da suke jikinsa, ya mayar da kayan da ya zo da su. Wato black plain hoodie, wadda ya ɗorawa red bomber jacket a sama, da blue jeans sai baƙaƙen canvas ɗinsa.
Sannan ya nufi backpack ɗinsa ya buɗeta ya saka award ɗin da aka ba shi, kafin ya ɗauki wayarsa dake ciki, ya buɗe da fatan ganin missed call ɗin abokinsa ADAM, amma babu alamar ma ya kira, dan haka ya ja tsaki, ya buɗe wayar ya nemo lambarsa ya sake aika masa kira, a karo na barkatai a ranar, dan tun kafin ya shiga fencing class ɗin yake ta kiran wayarsa.
*House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.*
ADAM ALI ABBAS.
“Adam! Adam! Adamm! Wai ba za ka buɗe ƙofar nan ba!?”
Wata bahaushiyar mata ke faɗi, cikin harshen hausa, yayin da take tsaye a jikin ƙofar ɗakin da take a kulle, yanayin shigar dake jikinta kaɗai zai sanar maka da ƙabila da kuma ƙasar da take. Duk da su mazauna ƙasar ta Dubai ne bai sa ta daina saka kayan al'adarta ba, a matsayinta na ainahin 'yar ƙasar Nigeria, kuma bahaushiyar arewacin ƙasar.
Daga cikin ɗakin da take buga ƙofarsa kuwa, wani matashi ne tsugunne a ƙasan desk, ya lulluɓa da blanket har kansa, yanayin tsoro shi ne kwance a kan fuskarsa, ban da rawar ɗari ba abin da yake, kamar wanda ya kwana a cikin fridge.
Ɗakin
bai
cika
girma
ba,
amma
yana
ɗauke
da
kaya
masu
kyau
da
sauƙin
kuɗi, kallo
ɗaya
za
ka
yi
wa
ɗakin
ka
san
cewa
na
mai
ɗaukan
hoto
ne. Dan
ko
wace
kusurwa
ta
ɗakin
na
ɗauke
da
hotunan
mabanbanta
abubuwa,
da
kuma
hotunan
cameras
da
ma
cameras
ɗin
na
zahiri, tarkacen
da
ɗakin
ya
cika
zai
sa
ka
san
cewa
ɗakin
matashi
ne.
Daga wajen ɗakin, matar nan ta ɗazu da take ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta girgiza kanta cike da takaicin halin ɗan nata.
“Allah ya raba bawa da wahala!”
Ta faɗa kawai, sannan ta juya ta dawo ɗan ƙaramin falonsu dake ƙasan gidan, wanda ke ɗauke da kyawawan furnitures masu kyau. Tana shirin wucewa kitchen ɗin dake haɗe da falon wayar Adam ɗin dake a falon ta yi ringing kamar ɗazu. Dan yawan kiran wayar da ake run ɗazu ne yasa ta gane cewa Adam ɗin bai fita ba, shi ne ta je domin duba shi, amma sai ya ƙi buɗe ƙofar ɗakin.
Wata shawara ce ta faɗo mata a rai, hakan yasa ta nufi wayar tasa ta ɗauka ‘Bin Iƙbal’ shi ne abin da aka rubuta a matsayin sunan wanda yake kiran, kuma ta gane cewa abokinsa Arman ne, dan haka ta ɗaga wayar, ta sanarwa Arman ɗin halin da Adam ɗin ke ciki.
Daga ɗayan ɓangaren, Arman ya sauƙe wayarsa ƙirar iPhone 'yar yayi yana dariya a nutse, ba sai Maaman Adam ta yi dogon bayanin abin da yasa ya shiga ɗakinsa ya kulle kansa ba. Dan ya san dalilin ba zai wuce ya kalli wani horror ko Zombie movie ba, ya san abokinsa da tsoro kamar farar kura. Kuma ga shi da naci, dan duk yadda ya kai ga tsoron horror film ɗin sai ya kalla daga zarar sabo ya fito, Allah yasa yanzu haka bai kwanta zazzaɓi ba.
Kansa ya sake girgizawa yana ɗaukan backpack ɗinsa, ya goyata a bayansa yana kama hanyar barin Business Bay, sai da ya fita daga building ɗin sannan ya fara dialing numbern ɗaya ƙawar tasu wato IVANA!.
*Repton school Dubai, Nad Al Sheba 3, Abu Dabhi, United Arab Emirates.*
IVANA SAGAR.
Zaune
take
a
kan
maroon
bowl
chair,
sanye
take
cikin
farar
hoodie
da
baƙin
distressed
jeans,
ƙafafunta
cikin
farin
canvas,
baƙin
dogon
gashin
kanta
kwance
a
gadon
bayanta,
yayin
da
hannayenta
ke
kaɗa
guitar
ɗin
dake
kan
cinyarta.
Farar
balarabiya ce,
kyakkyawar
gaske,
me
manyan
idanuwa
da
dogon
hanci da
madaidaicin
baki
me
ɗauke
da
farar
fata
me
haske.
Murmushi
ne
kwance
a
kan
fuskarta,
yayin
da
take
kallon
ɗalibanta da
take koyawa
kiɗan
guitar
zaune
a
gabanta.
Dukansu
sun
nutsu
suna
sauraron
daddaɗan
kiɗan
guitar
ɗin
da
take...
Wayarta
dake
aje
a
gefenta
ce
ta
kaste
musu
darasin,
ta
hanyar
ringing
ɗin
da
ta
fara.
Hakan
yasa
ta
dakata
da
kaɗa
guita
ɗin,
ta
kalli
wayarta
dake
ruri,
alamun
shigowar
kira
‘Rafiƙi’
(Abokina)
shi
ne
rubuce
tare
da
heart
emoji
a
gaban
sunan,
kuma
kaf
duniya
mutum
ɗaya
ne
ta
yi
saving numbernsa
da
hakan.
“A'aziruni
lahza!
(Excuse
me
please)”
Ta
faɗi
cikin
harshen
larabci
tana
duban
yaran
ɗabilan
nata.
Sannan
ta
juya ta
ɗauki
wayarta,
ta
ɗaga
kiran
Arman
dake shigowa.
“Shu wainak
halla?
(Yanzu
kana
ina?)”
Ta
tambaya
ba tare
da
ta
bari
ya
yi
magana
ba,
dan
ta
san
sun
yi
da
shi
a
kan
yau
yana
da
gasa
tsakaninsa da
abokan
koyon
wasan
fencing
ɗinsa.
“Ai
dai
kya
bari
mu
gaisa
ko?”
Arman
ya
faɗa
daga
ɗayan
ɓangaren,
sai
ta
yi
murmushi, tana cire
handle
ɗin
guitar
ɗin
daga
wuyanta, sai
da
suka
gaisa,
sannan ya
sanar
mata
da
dalilin
kiranta.
“Na
kira
Adam
Maama
ta
ɗaga,
ta
sanar
min
da
tun
jiya
ya
kulle
kansa
a
ɗaki,
ya
ƙi
fitowa.
Da
alama
ya
kalli
wani
horror
film
ɗin
ne”
Ivana
ta
kwashe
da
dariya
tana
rufe
bakinta,
dan
ita
ma
ta
sa
halin
abokin
nasu.
“Yanzu
kana
ina?”
“Na
baro
business
bay
a
motata”
“Mashi
(Okay)
ka
biyo
ta
nan
sai
ka
ɗaukeni”
“Ɗayib
(Okay)”
Ya
amsa,
sannan
ya
aje
wayar.
*
Arman
ya
kwashe
da
dariya
yana
kallon
Adam
da
yay
tsuru-tsuru
da
shi,
saboda
yanda
yake
a
tsorace.
Ivana
ta
ɗan
yi
guntun
tsaki
tana dafa
kafaɗun
Adam dake
basu
labarin
film
ɗin
ban
tsoron
da
ya
kalla
daren
jiya,
wanda
ya
hana
shi
sukuni
har
zuwa
yau
ɗin
nan.
“Shifti?
Huwa
am
yadhak
alaiyyi”
(Kin
ga
ba?
Dariya
mayake
min)
Adam ya
faɗi
yanayinsa
na
nuna
damuwar da
yake
ciki, dan
har
yanzu
a
firguce
yake.
“Armaan
la
ad
tadhak!”
(Armaan
kada
ka
sake
dariya)
Ivana
ta
gargaɗe
shi,
sai ya
ɗora
hannunsa
a
kan
bakinsa,
yana
son
toshe
dariyar
dake
cinsa, amma
ya
kasa.
Ivana
ta
girgiza
kanta,
sanan
ta
tura
Adam suka
fara
tafiya
tana
kwantar
masa
da
hankali.
Arman
ya
biyosu
yana
ci
gaba
da
ƙyaƙyatawa
Adam dariyar
mugunta.
Da
haka
har
suka
shiga
Cavo Espresso Bar dake
kusa
da
inda
suke, har
suka
zauna
Arman
bai
daina
dariya
ba,
ko
ya
so
ya
danne
daga
sun
haɗa
ido
da
Adam zai
ji
dariyar
da
taso
masa.
“Ivana
kalli yaskut!
Wa
illa
rah
irja'a
ala
bait”
(Ivana
ki
saka
shi
ya
yi
shiru,
idan ba haka
ba
zan
koma
gida).
Ya
faɗa
yana kallon
Ivana.
Ivana
ta
ɗakawa
Armaan
duka
a
baya
tana
faɗin.
“Da
ƙyar
muka
saka
shi
ya
fito
daga
gida,
yanzu kuma
idan
ka
ci
gaba
da
masa dariya
ko
zai
koma
gida
ba
zan
yi
ƙoƙarin
hana
shi
ba”
“Asif
(Ku
yi
haƙuri)”
Faɗin
Arman
yana
toshe
bakinsa.
Ivana
ta
sake
dafa
kafaɗar
Adam da
har
yanzu
yake
a
dame.
“Laik
Adam!
Shabah
mu
haƙiƙi!
Killu
mazah!
Wa
ma
bi
kaffu!”
(Ka
ga
Adam,
fatalwa
ba
gaskiya
ba
ce,
duka
shiri
ne,
kuma
ba
su
da
ban
tsoro).
“Me
ya sa
za
ki
faɗi
haka?
Bayan
ni
na
ganta
da
idona,
wata
doguwa,
me
dogayen
farata,
idonta
ja...
Wayyo
Maama”
Ya
ƙarashe
yana
rufe fuskarsa,
saboda
fuskar
fatalwar
da
ya
hango.
Ivana
ta
sake
dafa
shi.
“Ihda!
Halla
rah
jiblak
shai.
Biddak
shai
mu?”
(Ka
nutsu,
yanzu
zan
kawo
maka
shayi,
kana
son
shayi
ko?)
Ya
jinjina
mata
kai
yana
kallon
Arman
dake
ta
ƙoƙarin
danne
dariyar
da
ke
ciyo
shi.
Ivana
ta
gyaɗa
kai,
sannan ta
miƙe
ta
zagaya
ta
nufi
wurin
da
zata
yi
order.
Cup
uku
na
shayin
ta
karɓa,
sai
dai
a
yayin
da
take
shirin
juyawa
ta
yi
karo
da
wani
mutum
da
shi
ma yake
ƙoƙarin
zuwa
wurin.
Farko
kofunan
shayin
dake
jere
a
kan
tray
ta
fara
kalla,
da
ta
ga
ba
su
zube
ba
sai ta
kalli
mutumin
da
ta
yi
karo
da
shi.
Wani
kyakkyawan
matashin
balarabe
ne,
wanda
ke
sanye
da
baƙar
suit,
kalar
farar
fatar
jikinsa
me
ɗaukar
hankali
ce, haka ma kammaninsa,
dogo
ne,
kuma
me
matsakaicin
jiki,
yana
da
faffaɗan
ƙirji,
sannan
sumar
kansa
na
cikin
asken
high
pade. Yana
da
buɗaɗɗen
ido,
wanda
yake
ɗauke
da
shuɗiyar
ƙwaya,
sannan
hancinsa
dogo
ne
sosai,
ga
bakinsa
dai-dai
wa
dai-dai,
yana
da
saje
da
kuma
gemu,
wanda
suka
ƙara
masa kyau.
“Ana
ba'atazir!
Ma
intabahat!”
(Ki
yi
haƙuri
ban
lura
da
ke
ba
ne).
Ta
ji
muryasa
me
daɗi
ta
furta,
sai
kawai
ta
jinjina
kanta,
alamun
ba
komai,
sannan
ta
raɓa
shi
ta
wuce,
har
ta
koma
table
ɗin
da
su
Armaan
suke bai
daina
kallonta
ba.
“Rifaƙ
(Guys)
ko
kun
san
cewa
yau
Chris Brown
zai
yi
live
performance
a
Coca-cola
Arena?”
Faɗin
Arman
yana
nuna
musu
takardar
sanarwa
a
cikin
wayarsa.
Adam
da
Ivana
suka
dubi
juna.
“Wai
yau?”
Adam ya
tambaya
yana
aje
cup
ɗin
dake
hannunsa.
“Eh
yau,
duba
ka
gani”
Ya
miƙa masa wayar ,
Adam
da
Ivana
suka
haɗa
kai
suna
karantawa.
“Za
mu
je
ne?”
Cewar
Ivana.
“Akid!
(Of
course)”
Arman
ya
bata
amsa.
Domin
duk
inda
za
su
je
ko
za
su
fita
shi
ne
ke
biyan duk kuɗin da za'a kashe, ko
cinema za su
je
shi
zai
sai
musu
ticket.
Saboda
kaf cikin
su
ukun