Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Allah yasa kafi haka   Ameen ngd sosae Juyawa yay yakama hanayar barin tashar      Taba dadeba aka saka mota nan aka fara loda kayanta sannan suka shiga ita da Nauphal xama tae tana dan dudduba kafarta da take mata xafi gani tae duk taji ciwo sosae akafar      Sae wajen 6:00am Sannan motar tafiya KADUNA tacika suka kama hanya     Kudin mota akace musu tadauko xata bayar sae wani mutum akusa da ita yace aa bari in bayar     Kallonsa tae taga bata san saba amman yabata kudin mota godeeyah tae masa     Yace babu komae Haka sukaeta tafiya vasu suka isaba sae wajen 10:30pm sannan    Suna sauka aka sakko mata kayanta dauka tae tayi shiru tana tunanin ina tace akaeta tunda ita batasan ko inaba      Bakin wata inuwa suka xauna tacewa nauphal tsaya anan in samo maka abunda xakaci  kaji dan kirki      Toh Ummerh saekin dawo Tafiya tae wajen wata mae koko da kosae ayar rumfarta tace abani koko da kosae     Toh na nawa Kokon 50 kosan 100 fanken 50    Dari biyu tabata kar6a tae tafara daura mata kosan tae da panke sannan tadauki leda xata saka mata Kokon aciki     Hapsatu ce tace aa kixubamun aroba yanxu xamusha acan mukawo miki      Toh dan Allah inkunsha ki kawomin dan 6ata suke wlh     Toh in sha Allah amsa tae taje wajen Nauphal tashimfida xanin data goyo nauphal dashi  sannan tace xauna yaraon kirki inkawo maka ruwa kawanke hannun ka     Toh Ummerh ai nayi alwala yanxu nayi sallah da wannan ruwan na butar can dana gani     Toh inga hannun naka mana Nuna mata yay     Tae murmushi tace toh xauna kasha kaji     Xama yay yace Ummerh musha tare kinji Ummerh ta     Toh saka hannu tae tafara cin kosan tana shan Kokon     Koda suka gama tashi tae takae mata robar    Har wajen 12pm lokacin ma babah mai kosae tagama wanke wanke takeyi dakanta     Hapsatu ce taje tace mata dan Allah koxan iya yimiki wanke wanke     Aaa aaa barshi kawae Kawo intayaki toh Mika mata tae tacigaba da wankewa ita kuma tana saka sauran kayan acikin shagonta      Haka har suka gama Hapsatu ce tace mata dan Allah babah ina xan samu gidan haya Koda daki dayane da bandaki     Aaaa kajimu da tsiya wani irin gida keda baku da  matsugunni kika kamo hanyar xuwa KADUNAH IYEEEE 🤔 🤔 🤔       A'a dolece tasani xuwa babah Toh muje gidana daganan sae afara nema muki........    🍃🍃🍀🍀🍃🍃🍀🍀🍃    *DASHEN🍃ALLAH* *WRITING ASSOCIATION* * *DAN* *HAKIN* 🍃 *DAKA* *RAINAH😏** 🤔              Nah   💕Ummuh fateemah💞 🆓 *page*    Page 2⃣9⃣&3⃣0⃣ *Wata* katuwar motace tadaki wannan nafef din nasu ta cillasu can cikin dajin daga gefen wata bishiya     Ko minti uku basuyi dafadawa gurin ba bala da baba mai kosai suka fara yunkurin futowa aikuwa kafun sukarasa futowa nafef din yakama da wuta gaba daya saici yake    Ihu suke suna neman tai mako Amman babu kowa agurin koh alamar motsin mutane babu bare susaka ran ceto....... Wata motar hayace tazo wucewa hapsatu tasa hannu tana tsaydata Amman ko sauraran su basuyi ba suka wuce abunsu    Komawa sukayi bakin Titin suna jiran ko xasuga wata tazo wucewa     Suna zaune sukaga wuta ta kama bawwww     Dasauri takama hannun yaran tace kutashi mutafi wuta    Dahanzarinsu suke tafiya gashi duk sun gaji sosai gurin data saba kwanan anan taje ta kwanta ita da yaran     Basu dadeba bacci yadaukesu suduka dan amugun gajiye suke    Basu suka farkaba sai da gari yawaye Nauphal ne yafara tashi yaga ummerh sa akwance tana bacci     Murza idonsa yayi yace ummerh nah kece ummerh     Jin ana shafa mata fuska yasata bude ido cikin Sauri tana mikewa tsaye     Ganin Nauphal ne yasata murza nata idon itama dan ganin shine ko kuwa gizau yake mata     Shidinne dai wata muguwar runguma takai masa tana kan kame shi gam ajikinta kamar za'a kwace mata shi     Kuka suka saka atare dan sun rasa mezasuyi idan ba kukanba     *FAHAT* dayake bacci kukansune yata sheshi yazauna yana kallon ikon Allah dan shi dai yakasa gane musu     Duk da yafi Nauphal girma dan zaikai shekara 15 Nauphal kuma yanzu yake 13 banbancin kadanne    Shima hapsatu kamosa tayi tarungumesu gaba daya tanaci gaba da kukan sosai saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru     Cewa tai kujirani anan inje in samo mana ruwan alwala kunji     Toh ummerh Tafiya tai tasamo musu ruwan alwala dayake babu nisa da jama'a fiyo wata tasiyo musu Leda daya sannan tadawo alwala sukayi sannan sukai sallah tanajin kunyar yin sallah gari yayi haske amman yanzu babu yadda ta iya haka tayi tanata istigfari     Ce musu tayi mukoma can dinnan ko kuma muzauna anan dan niyanzu tsoron mutane nake     Cewa sukai A'a muzauna anan kafun musamu gurin zama     Toh bari inje in siyo mana abunda zamuci    Tafiya tai cikin garin tana duddubawa har taga inda ake shinkafa da miya ta tsaya ta siya musu ta dari biyar sannan ta siya ruwan shayi dauri uku da bread sannan tadawo     Zama sukayi sukaci suka koshi sannan tace muje gidan wanka muyi ko    Kunga mafi kyau shiga cikin mutane neman inda zamu zauna     Aikuwa haka akayi gidan wanka sukaje sukayi wankansu tadauko kayan *Nauphal* tabawa *FAHAT* yasaka itama tasaka wasu kayan suka daure wanda suka cire aleda suka saka abakkonsu    Shago taje ta siya musu takalma da man shafawa sannan suka shafa     Shiga suka farayi cikin garin suna dan zazzaga garin *KADUNA* kozasuga inda yayi musu sukama haya    Wani mutum suka gani yatsufama sosai suka gaidashi sannan sukace masa dan Allah suna tambayar shin ina xasu samu gidan haya agarin nan koda mai daki dayane da ban daki    *Babah sa'idu* yakallesu yace 'yata inake ina iya kama haya    Tace Babah zan iya insha Allah Yace to shikenan ni dillaline ina bada hayar gida amman muje kiga wanda suke ahannuna kozasuyi miki saiki za6i daya daga ciki     Toh *Baba* muje tafiya sukayi mai dan nisa kadan sannan suka shiga cikin gari sosai unguwace ta jama'a     Nan yafara nuna mata gidajen kowanne da mutane acikin sa sannan kuma yakaita wasu Gidajen     Sukuma daya mutum dayane aciki dayan kuma mutum biyune aciki amman matsalar duk vandaki dayane dasu   yace toh acikinsu wanne ne yayi miki Toh baba duk sunyi amman matsalar ta bandakice wlh Baba daso make dasan samune ko zamu samu mai ban daki daban    Ey Yar nan zaku samu amman da tsadafa sosai dan duk wadannan gidajen dana nuna miki dukkansu dubu 10 ake biya duk shekara    Amman mai ban daki daban da phalo da daki biyu da kicin shikuma dubu 20-30 ne duk shekara     Yakike gani shidin zankaiki ko kuwa Toh baba muje in gani    Nafarkon da sukaje d'aki biyu, ban d'aki, kicin, babu phalo kuma part biyune kowa da nasa shine dubu ashirin #20    Shikuma dayan d'aki biyu, phalo, ban d'aki, kicin sai dan karamin tsakar gida shikuma part 4 aciki shine me dubu 30# kuma akwai mutane aciki guri dayane ba'akama ba inda ya nuna mata     Toh gurin yayi amman itakam tsoron mutane take sosai dan haka yasa tace suje dayan wanda bashi da phalo suzauna kawai tunda shi kofar shiga part dinkama daban take data daya 6angaren kuma akwai katanga data shiga tsakaninsu kowa kofarsa daban    Nan taza6a tace masa nan yayi Baba bari muzauna anan kawai    Toh shikenan amman kinsanfa nan dubu #20 ne koh duk shekara    Ey baba zan biya yanxu bari in baka rabi zuwa nan da sati biyu zan cika maka to shikenan     Shiga sukayi da kayansu taduba tadauko masa dubu goma acikin kudin ta sanann tafuto tace gashi Baba    Yace A'a Yar nan bari in kira dayan abokina sai mu amsa kinga saboda yanayi na rayuwa yau kaine gobe ba kai bane ko yakikace     Hakane kam Wayarsa yadauko yacdanna kira wata number aka dauka nan yayi masa jawabi sosai yadda zai gane sannan yace gashinan zuwa    Bai dadeba  yakaraso nan akayi komai akan idonsa    Nan sukace taciko dubu biyar kawai tarinka biyan dubu shabiyar 15 duk shekara taji dadi sosai kuwa    Baba sa'idune yakalleta yace yata kije asibiti aduba miki kafar nan taki dukta kumbura gashi taja ruwa ko kuma kiduba kiga ko sartse kikayi    Toh baba IN SHA ALLAH zanduba in gani kafun inje koda chemins ne    yace mata yanxu kingani kowa yanada nasa shaidun koh ke da danki daya da Malam baba    Nima nida danki daya koba hakaba Kinga hakan yafi kai waye    Ey Babah ngd sosai A'a karki damu ai duk wanda yataimaki wani shima Allah zai tai makesa    Hakane kam ngd Sosai Allah yasaka da alkhairi    Ameen tafiya sukayi itakuwa Hapsatu suka fara duba yaya zasu fara aikin gidan yanzu     Cewa su Nauphal tai ina zuwa kujirani zanje in siyo mana tsintsiya da allura in duba wannan kafar     Toh Ummerh saikin dawo Toh ngd    Futa tayi taje wani shago data gani acan bayan unguwar su tasiyo abunda duk zasu bukata sannan tadawo gidan     Lokacin sukam harsun fara futo da "Yan tarkacen da suke cikin dakin harda wasu kodaddun labulaye da tar kacen kwanuk da tukwane da farantai da wasu fasassun robobin ruwa da kuma jarka guda 6 yalaye nazuba ruwa    Cewa tayi toh wadannan kayan banamu bane amman bari inje in gayawa Babah sa'idu cewa munga kaya yaya zamuyi dasu    Toh ummerh kibari muje mugaya masa mana    A'a kubari inje dan yanzu nikam tsoron garinnan nake sosai wlh    Toh ummerh Futa tayi tana futa tag........... ***     ***      *** A6angaren su *Balaraba* kuwa haka suka koma gida babu wani farin ciki ko kwanciyar hankali atare da ita    Koda gari ya waye sun shiga tashin hankali sosai dan dukkan tashoshin garin Rano lungu da sakonsa saida suka duba amman babu su Hapsatu babu dalilin su ko kuma alamun su    Hankalinsu yayi matukar tashi dan Alhaji daya dawo yatambayi Hapsatu    Sun rasa mezasu ce masa    Kawai sai fauziyya tai katsa landan tace muma bamusan inda ta tafiba    Tun jiya mun kasa bacci sbd nemanta da muke    Wlh mun gaji da halin wannan banzar yarinyar ta tafi yawon karuwancin ta sanann tabarmu da nema haka kawai       Kema dai kyafad'a haka kawai muyi tafaman wahala akan karuwa    Wlh mama wadda batasan ciwon kantaba ma kuwa wadda bata da aiki sai karuwan..........    Wani wawan mari aka dauketa dashi wanda yadauke dukkan wani jinta kanta ankara aka kara dauketa da wani marin saida yayi mata kwarara guda 4 sannan yakyaleta shima ganin tafadi kasane hancinta yana futar da jini shine yasashi kyaleta    Duka yakai mata da kafa yana fadin akwai wanda yakaiki karuwanci ne eyeee    Tunda anriga angur6ata miki rayuwarki    Kuma kisani wlh dukkan sharrin da ake kullawa akan Hapsatu kanku zai koma     *WLH IN GAYA MIKI* *DAN HAKIN DAKA RAINA* *SHINE ZAI TSONE MUKU IDO*    Karkuyi tunanin kuna cutar da ita da kaninta dan ganin bata da kowa    Toh ina mai tabbatar miki da cewa Allah yana tare da su akoda yaushe     Kuma dukkan wanda Allah yatsaya masa to bashi dasauran Kuka     Har lokacin dukanta yake kamar jaka Da gudun tsiya s....... Hallmarht ce💞💖💞 [04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: ✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨ WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7 🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️ بسم الله الر حمن الر حيم ✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨ 💞NAH💞 SADIYA ABDULLAHI UMAR 💞UMMUH FATEEMAH💞 🅿--- 3⃣1⃣&3⃣2⃣ 🆓 page    Da gudun tsiya sukayi kansa suna cewa bazaka denan dukan taba ANAS wannan wani irin haukane eyeee Gajiya sukayi dan sunkasa kwatarta daga Alhaji har mama Balaraba sunkasa amsarta dukan ta yake kamar an aikoshi    Balaraba ce tace wlh ANAS idan baka daina dukan taba saina tsine maka kaji narantse wlh kuma baka isa ka karyamun rantsuwata ba    Jin hakan ne yasashi tsayawa da dukan nata Amman fa tadaku sosai dan bakaramun duka yayi mata ba     Dan tunda take aduniya bata ta6ajin irin wannan dukan ba gashi kuma yau ta d'an d'ana     Kamata sukayi itada Alhaji sukayi waje dan zuwa asibiti dan tahancin ta, tabakin ta, ta goshi, duk jini zuba yake     Sannan  gawani nan yana zuba ta kasanta kamar an6alloshi     Dak'ar take iya taka kafarta saboda muguwar azaba     Amugun wahale take dan jitake kamar jiri zai dauketa babu yadda suka iya dole yasasu suka je chemist dan afara dubata kafun suje asibitin    Da'kar suka shawo kan Baba iyabo yadubata sosai yayi mata kokari sosai nan yake sanar da Balaraba tana da ciki dan Allah yataimaka sun kawota da wuri dabasu kawota da wuriba daya zube Tashi tayi amugun razane tana fadin CIII MEEEEEE............ ***        ***        *** Tana futa taga abokin Baba sa'idu gaisawa suka karayi take gaya masa kayan dasuka gani acikin dakin nan yace mata wlh matar data kama haya agidan ce tayi arziki shine tace duk kayan dasuke shiki tabar mana tofa shine muka tsinci na tsinta mukabar sauran    Kiyi amfani dasu kawai in kina so Wanda basu da amfani kuma ki xubar    Toh Baba ngd sosai Allah yasaka da alkairi   Amen "Yar nan Komawa tayi cikin gidan ta tarar harsun fara sharo dakunan da ban dakin sunata cire yanar    Ita ma fara tayasu tayi aikin dansu gama da wuri saida suka share ko Ina nan suka kwashe sharar suka saka abuhu    Lokacin da suka bude kichin dinne sukayi mamaki dan jerene aciki nakomai tsaf Ba'ata6a ba harda sababbin kuloli acikin sa fara dubawa sukayi ahankali nan sukaga harda shinkafa buhu 2 da taliya da maka roni    Kayan avunci sosai ne acikin gurin harda mai doyarce dai tafara hun huna da dankali saidai 6ura da sukasha sosai     Ce musu tai bari inje in gayawa Baba kayan dayawa sosai fa    Sukace Toh Tafitai gidan tayi sallama Amsa mata sukayi nan take fada masa komai akan kayan dasuka gani sosai dana abunci      Babane yace mata kiyi amfani dasu Hapsatu wlh muma mun samu arziki sosai acikin wannan gidan    Wadannan Allah yayi rabon kine Hapsatu karki damu kinji    Toh Baba ngd sai anjima Sannan ko kinga wani abun ma karki dawo kidauka kawai     Toh Baba Tashi tayi danta futa kafarta ta rike gam takasa takata    Salati tasaka Baba Hasiyace tace lpy "Yar nan meyasameki    Wlh Baba kafatace nakasa taka ta Assha LAHAULAH    BARI MUGANI zuwatai tafara tai maka mata tazauna sannan tace muga kafar taki     Mika mata tayi Inna lillahi ni Hasiya mezan gani haka saikace ba mutum ba dawannan katon hakin akafa fuwanki har kusan 3 Amman kina tafiya haka nan     Binta Binta kina inane Ganinan Babah lpy nikam wannan kira haka    Dauko mun matse fata da leta da kuma allura maza kinji yi sauri    Dauko mata tayi dan aleda take ratayesu tasa asaman sip    Yawwa daukarsu tai ta konasu da letar nan sanan tadauki wata auduga tagogesu tas    Ahankali tafara cire mata sartsen duk inda tacire sai yayi feshin ruwa sosai     Haka saida tacire mata su tsap sannan tafara buda gurin da allura tana yankewa da sabuwar rezar data bude yanzun     Hapsatu jitai kamar ancire mata wani mugun nauyi daga kafarta    Danjitae sakayau kafar tata Baba hasiyace tace muga dayan kafar taki dubawa tayi nan guda dayane sartsen Amman yajah ruwa yakumbura sosai     Shima matseshi tayi tana fad'in sannu kinji "Yar nan kinyi jarumta sosai    Nan kamar tar gad'e mlm zoka duba mata dan inajin nan kam tar gad'e ne    Toh tasowa yayi yafara duba mata Yace ey wlh tar gad'ene kam    Wai nikam "Yar nan a ina kikaji Wadannan ciwukan sai kace wadda tai ya'ki     Murmushi tayi kawai batace komai ba Sannu sukaita binta da ita sannan   Baba Hasiya tace dan huta kafun kitafi    To Baba zama tai tadan huta har wata gajiya taji tana saukar mata     Takai kusan minti 40 sannan tace bari in tafi Baba   Haba dakin kara hutawa itama kafar tasamu salama ai ko    Bari ma in kira binta ta tai maka takai miki ruwa ki watsa ko kyaji dadin jikin ki    Aa babah.... Wani A'a    Kina inane Binta   Gani nan Baba kayan make up din nan nake kwashewa   Ok toh yiki kwashe kizo Toh Baba Bata Jimaba tazo   Yawwa "Yar kirki  kawo mata ruwan dumi tadan watsa   Ki saka mata aban d'aki    Aa Baba bari inje aiki mukeyi nabarsu sukadai karsu zata ko 6ata nayi sufuto Aaaaaa"aaaaaaa 'aaaaa wlh hakane kam bari inkun gama Binta takawo muku ruwan zafin kawai kuyi wankan    Toh Baba ngd sosai Allah yakara lpy Ameen "Yar nan    Wai nikam yasu nan kine Murmushi tai tace Hapsatu sunana     A'a kice mesunan sirikatace ALLAH yabar kauna sirika    Murmushi ta'karayi tace amun Babah   Futa tayi taka ma hanyar xuwa gida Lokacin dataje gidan sun gama share ko'ina sun wanke ko ina dan tayal ne ako ina acikin gidan    Sunsa tsunman dasuka gani sun goge ko ina ya tsane     Kayan kiching ma sun wanke sun goge komai Doya, da dankalin dasukaga sun lalace suka futar suka saka abuhun shara     Dan watan ta d'aya da tashi Amman saboda yanayin sanyi ga iska ga 6ura kota ko ina shiyasa gidan yayi futu futu sosai    Yadda kasan an shekara ba'a shiga gidan ba     Mamaki tai ganin sun gama komai har wankin kaya sunyi shaya     Tarar dasu tayi suna iban ruwa dayake akwai rijiya acikin gidan kuma akwai guga aciki      Wai harkun me Mun gama Ummerh   Sai kace wasu injina gaskiya kun aykatu sosai Allah yasaka muku da gidan aljannah    Amen yarab Ummerh FAHAT ne yakalleta sai kuma yace Ummerh mujefa cigiya har INDA RANKA, BBC NEW'S MUJE    Amman shiru bamu ji bayani ba Murmushi tai tace Allah yashirye ku wlh   Ummerh munjefa sai kafun nashiga naji ana cewa kizauna kidan huta shine nadawo nace masa kina nan muci gaba da aikin mu Au ainazata bakuje nemana ba    Haka kawai kuke ta zaune Haba mu mafara   Dariya sukayi gaba d'aya suka cigaba da dibar ruwan tana tayasu cika wasu abubuwan    Atare sukayi jeran kicin din dakuma sauran ayyuka     Kallon su tai tace toh yanzu mezamu siyo muci kuma ice zaku siyo muhura wuta azaure ko kuma magal zaku siyo mana da gawayi dan naga acan kofar gidan wasu makera anayi    FAHAT ne yace Ummerh ga gass nan aisaimu kunna muyi amfani dashi    Gass kuma ni Hapsatu ina na iya aiki dashi ko kunnashi ban iyaba     Hh Hh Hh ummerh ni na'iyafa wlh agida nikeyin girki kullum    Toh maza shiga kayi Meza'adafa ma Wai Ai sai abunda kikace Tohhh🙄🙄 kubaku da za6i sai nawa   Ey mana Ummerh kifada Toh nikam banasan komai    Nauphal ne yace toh muyi shinkafa da wake tunda akwai     Saimu daka yaji koh yayah Yawwa kumafa hakan yayi mudaura     Hapsatu ce ta tafi dakanta tasiyo barkono da salat, tumatir, kokumba, da albasa duk sannan tasiyo musu kankara daruwan sanyi leda daya, da tiara, da so6o, cotta, kanin fari da danyan kifi na dari biyar sannan tadawo gida    Lokacin sun zuba wake Adayan kuma sun daura ruwan zafin wanka har Nauphal yashiga yayi Fahat kuma zai shiga ta shigo    Zuwa yay zaitayata aikin tace a'a maza kayi wankanka bari ingyara     Tafiya yayi yay wanka yashirya Lokacin ta gama komai ta tattare gurin ta gyara    Itama wankan tashiga Lokacin harya sauke abuncin yajuye akula Nauphal yakama wanke-wanke shikuma yahad'a sauran kayan abuncin yakai daki ya ajiye     Kifin yasoya sannan yasoya man dazasu ci abuncin dashi     Saida suka kammala komai sannan suka zauna cin abuncin ababban plate 🍽 tazuba musu abuncin suka saka hannu suka faraci      Koda suka gama saida suka tattare komai sannan suka dawo dakin suka zauna     Hirar su suke Sai Hapsatu ta kalli Fahat tace nikam Fahat inane gidan ku    Saida yanayin fuskarsa yacanja dakar ya kwa'kulo murmushi yace Ummerh meyasa kika tambayar gidan mu     Haka kawai kuma yakamata musan gidan ku dan mumaidakai koh yakake gani    A'a Ummerh dan Allah karki maidani gidan nan wlh banasan komawa gidan nan ko amafarki wlh    Meya faru haka Fahat? Kabani labarinka in babu damuwa? Toh Ummerh bazanki gaya miki koni waye ba da kuma asalina ba.............. ***      ***       ***    A6angaren su fauziyya kam Mama Balaraba anugun razane ta tashi tace ciiii meeeeee na shiga uku yanzu fauziyya cikine dake inna lillahi wa inna ilaihi raji'un nabani     Tayaya akayi fauziyya tasamu ciki Am nace ba dan Allah tayaya za'ai acire wannan cikin    Zaro ido Baba iyabo yayi yace minana kike cewa hajiya   Kazubar mana da cikin nan nakeso Niii nini nii Wlh bazan iya aikin sa6an nan ba badani ba hjy   Nace kadauka d'anka kubarmin chamist Wlh konayi maka ihu yanzu jama'asutaru    Haka kawai ni nace d'anka yaje yayi ciki   Tashi Balaraba tai tace katai makamun karkamun ihu yanzu zamu tafi   Yawwa yafi dai kam Amman kaban kudina maza kafun nama rashin mutunci Wlh kagane ko?   A'a Baba iyabo basaikayi rashin mutunci ba yanxu zan baka kudinka nawane   Yawwa yika kawo maza dubu biyar da d'ari tara da hamsin da biyar   A'a nashiga uku harda biyar Baba iyabo baza'abar mun biyar dinba   Ey bazan bari ba dan tashegen zan yiwa ragi kaban kud'ina tsaf sannan kafuta anan Wlh    Balaraba saida ta irga masa kudinsa tass sannan takama hannun Fauziyya suka futo daga chemist din   Kama hanya tayi sukayi wani chemist din ma nan ma babu wani sauki sai wula 'kanci data tarar Saida sukaje chemist yakai 5 amman babu wani bayani haka suka dawo akan zasuje cikin garin kano gobe dan samun mafuta     Mama Balaraba kuwa tashiga tsananin tashin hankalin daba'a zato bare tsammani dan ta gigice ta razana dajin wannan zancen har yakai kunnen.......... Ina ganin comment dinku masoyana ina godeeyah sosai da sosai    ALLAH yabar kauna Love you all my fan's 💞💞💞💞💞💞💞💖💖💖💖💖💖😘😘😘💋💋💋💖💖💖💖💖💖💖❤❤❤😍😍😍😍😍😍😘😘😘 Hallmarth ce💞💖💞       [04/02, 7:56 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨ ✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨ WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7 *🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️* بسم الله الر حمن الر حيم *✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏* 🤔✨ *💞NAH💞* *SADIYA ABDULLAHI UMAR* *💞UMMUH FATEEMAH💞* 🅿--- Page 3⃣3⃣&3⃣4⃣ Danjin zancen yakai kunnen Anas da kannensa shiga sukai cikin gidan ad'arare suka wuce d'akinsu     Zaunar da Fauxiyya tai tace dan uwarki a ina kika samu ciki nace miki eyeeeee     Uban waye yayi miki ciki Kifad'amun nace kafin yanzunnan in yanka ki wlh kinajina ko Cikin tsananin tashin hankali da rud'u take maganar      "Dan tuno da maganar da likitan nan yamusu akan karta kara samun ciki dan in takara samun ciki tofa saidai tarasa mahaifarta gaba daya"    Ma'ana bazata kara haihuwaba kwata kwata yanzu kuma gashinan tayi wani cikin wannan na 4 kenan     Kuma ita gaskiya bata da burin "yarta taja mata abun kunya acikin garin toh yanzu yayah zatai kenan     Haka Balaraba taita masifa tana tambayar Fauziyya wayay mata ciki amman ko ajikin ta tayi mata buruss    Tana zaune kamar bada ita take ba     Saida Balaraba tadauko wata katuwar wu'ka tace wa Fauziyya koki gayamun waya miki wannan cikin ko kuma na yankaki     Sannan cikin rawar baki tafara fad'in wlh mamah zan gaya miki ki ajiye wukar nan wlh zan fad'a     In kinga na ajiye wu'kar'nan toki tabbata kin fadamun Gaskiya wlh inba hakaba Wlh saina yankaki, kinjini koh ba kijiba    Tunkarota tai gadan gadan da wukar zata luma mata    Tana fad'in kin manta abunda doctor yace koh akan karki kuskura kisake daukar ciki sbd mahaifarki bata da lpy in aka 'kara yimiki abortion zaki rasa mahaifarki    Yanzu yaya kike so inyi Kuma dawani idon kikeso in kalli yayyenki da jama'ar gari eyeeeee     Ma..... Ma.... Ma.... M... Mama..... Wlh wannan cikin na jaz.... ja...... z.. u.... l.. i... J.. azuli..... ne Wlh    Jazuli.....  jazuli....  kuma bangane ba jazuli.... dana bawa kudi yayiwa Hapsatu fyade    Eyy Eyy Wlh shine Yanzu kuma haukar taki kan jazuli takoma   Inna lillahi wa inna ilaehi raji'un kice hauka nake tayi nice keda abun kunya agari    Toh wlh daga ke har Jazulin saina kasheku    Kan Fauziyya tayo da gudun Ihuuuu taraf ka tana fadin atai makamun jama'a    Za'ai kisan kai Wayyo Allah n............ ***      ***       *** ALHAJI UBAH SHEHU Shine mahaifina yakasance mutum mai tarin dukiyane    Dan shahararren d'an kasuwa ne shi babu abunda baya siyarwa kama daga kayan abunci sutura motoci mashina da kekuna da saida gidaje yana siyan fili yagina yasiyar    Wannan dalilin ne yasa shi yin suna acikin garin kano kota ko ina ansansa har wasu suna masa kirari da SANA'A GOMA MAGANIN

Chapter 5 of 16