Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wuni zakuyi koh    Wuni wlh a'a yanzuma zan siya wainar shinkafane da kuma sweet     Laaa dama bani kikazo ganiba Kalis ce ta amshe dacewa bake tazo ganiba gurin wa.........    Bata 'karasaba Nusy tadoke bakinta, Kai wlh bazai yuyuba saina fad'a kuma, tazo ganin saurayintane   Zaro ido Bintu tai tace saurayi kuma🙄🙄🤔    Allah yatsareni wlh, waina nazo siya, yasin wannan baikai saurayi naba wlh     Aaaaaa tome garesa wai naga yanada kyau😏😏    Tukunna ma kalis wanne kuke nufi Takedai nufi    Hhhh muke nufudai, ina wani wanda zakiga sumarsa mai yawa yana gyarata fari mai 'karamun baki wanda zakiga kamar yashafa pink d'in lips 💋 gloss     Ok Yeah Nauphal zakice Ta66 wlh wannan bazaima sokiba ingaya miki dan mata dayawa sunsha rubuta masa letter ya yagata ingaya miki, shi sam bayasan ma soyayya arayuwarsa    Gaaaa shegen miskilancin tsiya inba da yayansa ko maman suba baya magana wlh, saiki gama wuninki agidan su bazai kula kiba gaisuwar kima da'kar yake amsawa    Kalis ce tace kindaiji ko Kinji dai ni ai bagurin sa nazoba abu nazo siya kunga tafiyata    Juyawa tai tashiga gidan da sallamarta abakinta     Amsa mata Baba mlm yayi yace sannu dazuwa     Yawwa Baba ina wuni Lpy qlu yarinyar kirki      Murmushi tai tace baba ummerh tana nan    Ey tana ciki Shiga tai tana 'kara sallama amsa mata Hapsatu datake d'aki tayi    Aaaaaaa lale sannu dazuwa   Yawwa Ummerh ina wuni Lpy qlu, kwana da yawa   Wlh Ummerh makaranta muke zuwa A'a masha Allah, shiyasa najiki shiru    Ey wlh Ummerh, akwai wainar shinkafa da Pepe sup din nan irin wanda nata6a siya     Ey da akwai "yar gidan Ummer Yawwa abani wainar ta d'ari biyar, Pepe sup d'in kuma da dubu d'aya, sai kunun aya na d'ari biyar shima      Aaa 'yar ummerh keda wa zakuci wannan abuncin    Wlh Ummerh makaranta zanje dashi nace zan siyo musu suci yau    To shikenan, kulolin tami'ka mata,  Amsa tai tafara zuba mata komai na yadda tafad'a harda 'kari da wainar ta 1k tasaka naman na 2k tasa mata sannan ta mi'ka kulolin       Kud'in ta mi'ka mata tana russina wa, A'a barshi kinji 'yar Ummerh    Habadai Allah Ummer ki amsa Wlh bazan kar6aba abunda ba kullum kike siyaba sai anganki     A'a nidai to Allah zan daina zuwa Hhh tofa dana nemo ki ai    Maza d'auka indai ni Ummerh takice da gaske ba tsokana ba     Kai Ummerh Ey mana maza d'auka kigaida mutan gidan    Toh Ummerh angode, Allah ya'kara arzi'ki    Ameen yaravval alameen 'yata ngd     Murmushi tai tad'auki kayan harda kunun aya sannan tafuto      Kallonta su Bintu sukai suna dariya Had'e rai tayi tace lpy meye nadariya kuma     Kinjedai kinga da gaske bayanan ko, kinga yanzu ai saikiji dad'i basai mun 'kara dawowa ba     Allah yasawwa'ke wlh inje ganin wannan yaron    Wai yaro kike cewa, in aka had'aku ad'akin zai nuna miki aikin yarinta           Kai wannan d'an 'karamin yaron Allah yasuttura wlh    Wlh zanga mijin dazaki aura kedai Yana nan zaku ganshi ingaya muku Hhhh Allah yasa karki auro yaron wanda yafi Nauphal 'kan'kanta    Allah yakiyaye ai in sha Allah saiyafi wannan yaron in gaya muku    Wai baku kallesa bane ba amman kuke had'asa dani Yaro nefa d'an 'karami ma kuwa narainashi sosaima kuwa in gaya muku, zakuga mijina       Dan Allah nikizo mutafi in kuma bazakiba in 'kara oil ni    Gurin da suke hawa napep taje tatsayar tagaya masa inda zasu, shiga tai, aiko da gudu kalis tabiyota tashiga suka tafi    Motar........................... Keep waiting my fan's🤗🤗🤔🤔 Hallmarth ce💕💖💕 [04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨ ✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨ WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7 🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️ بسم الله الر حمن الر حيم ✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨ 💞NAH💞 SADIYA ABDULLAHI UMAR 💞UMMUH FATEEMAH💞 🅿---      6⃣1⃣&6⃣2⃣ ...................Motar mom d'anta tagani tana shirin yin perking a 'kofar gidan su Nauphal    Gabanta ne yafad'i rass dan tasan yau baza'a kwashe 'kalau ba, dakatar dame napep d'in tai tace yatsaya dan Allah       Yana tsayawa tasauka tabar kalis aciki, dasauri taje tasha gaban mom d'in tata, kallonta tai tace ashe maganar da aka fad'amun gaskiya ne cewar kinzo ganin saurayinki da kuma siyan abunci     Kallon mom tayi tace waya fad'a miki mom     Body guard 💂 d'inki Body guard 💂 kuma mom Yesss  ko kina shakkune, to nabaki tsaro sosai sbd wannan matsiyatan da kike san kulla ala'ka dasu     Kinsan dukkan family d'inmu babu matsiyaci dan haka ki kula    Mom kizo mutafi gida mayi maganar acan gida in munje Dallah can wawuyar yarinya kawai,  Anan zamuyita kauce kiban guri, kafun in sabauta ki yanzun nan     Tureta tai ta shiga gidan babu ko sallama ta banka musu 'kofa      Kuna ina ahalin matsiyata wad'anda basusan komai ba sai tsiya dangin fa'kirai       Baba mlm ne yafuto yace lpy "yar nan    Wani mugun Kallon banza tai masa tace "yar nan kuma, wlh Allah yakiyaye inyi uba dakai Allah yatsareni wannan aikin dana sanin, kalli kanka ka kalleni kaga nayi kama da irin 'ya'yanka eyeeee      Ko amafarki bana fatan wannan masifar ingaya maka, dan had'a abota da matsiyata baiyiba      Talakawa dangin fa'kirai Allah yasitiri bu'kyuuy inji kishiyar mai doro      Annabi ma ya nemi tsari da talauci, nikuma saina jaji 6owa kaina        Kuka Nusaiba tasaka tace mom wannan d'iban albarkar ya isa haka, duk akan menene     Kuma wani laifi suka aikata mikine mom     Menene aibunsu, mom  aiba su sukai kansuba inda mutum keyin kansa dabaza'a samu talaka ko guda d'aya ba aduniyar nan     Mom karki manta Allah shiyake azurta wanda yaso kuma shiyake talauta wanda yaso, badan baya sansuba saidan yagwada imaninsu     Kuma karki manta da talaka da mai kud'i duk d'aya suke awajen Allah babu wanda yafi wani sai wanda yafishi tsoron Allah 'Dauketa da wani gigitaccen mari tayi tace dan ubanki nizaki gayawa Allah Tunkan kisansa nasansa kuma tunkan in haifeki nake bauta masa kina fahimta kokuwa      Duk wannan ha'kilon dabe akan wa nakeyi komai danakeyi ai akanki nakeyinsa ba'akan komai ba    Saboda inasan kisamu gobe mai kyau arayuwarki    Amman kike za'kal 'kalewa kina gayamun magana san ranki akan matsiyata    Sannan hakan bai ishekiba kinasan had'ani da matsiyata dangin fa'kirai ahalin talauci,salan kije ki kwaso mana cuta ko wata masifar, kina ganin gida kamar kangon acijiyar sharar gidan mu   To inasan kisani daga yau inkika 'Kara shigowa wannan kangon wlh sai nasa an 'konashi yadawo toka Tayadda babu wata halitta dazata 'Kara rayuwa acikinsa ko da kuskure Bare harkisakamun ciwon kai ki'kara dawowa gidan da annobane atare dani da rayuwata gaba d'aya    Baba mlm ne yace dan Allah kiyi hakuri hakan bazata 'kara faruwaba rashin sani ne Rashin sani kuma, agidan uwarwa yazama rashin sani, bayan nazo nayiwa wannan "yar iskar matar bayani akan ta, amman tadanne sani ta'karayi Kiyidai hkr hakan bazata sake faruwaba in sha Allah nayi miki al'kawrin nan, kotazo baza'a 'kara siyar mata ba    Dalla mlm matsamun daga gani, ku matsiyata har wani al'kawri kukeda bayan kuna halin talauci, daga kunga kud'i ai kar6ewa zakuyi     Tunda daman fatarar su kukeyi Kuna neman nasawa abakin salati       Wai ina ita shugabar matsiyatan take ne, muna fuka, tashige d'aka ta'ki Futowa     Toki futo ko kuma insa afuto dake yanzun nan   Shiru taji,  Kallon d'aya tai daga cikin body guard 💂 d'inta tace jeka d'auko mun ita tunda bazata futoba   Kama hanyar d'akin yay, sai Baba mlm yataresa, aikam mom d'in Nusaiba tun kud'esa tayi yakusa fad'uwa tace maza jeka d'auko min ita Shiga yayi d'akin yaga tana sallah    Juyowa yay yafuto   Kallonsa tai tace tana ina   Cewa yay  sallah take To tagama ta futo maza    Hapsatu ce tayi sallama ta futo da hijab d'inta da carbi a hannunta tace lpy hjy mekuma yafaru wanna d'iban albarkar yayi yawa haka     Uwar kice banyi miki kashedin karki 'kara siyarwa da 'yata wannan gur6a taccen abuncin ba kuma bana gaya miki cewa ba tunda bazakiyimun aikiba banasan sakejin kina saida wani abu ba    Nusaibace, tace haba mom wai meyake damun kine     Tayaya zakice tadaina san'arta, adalili dame yasaka    Adalilin ubanki nace adalilin ubanki,inaga yanzu kin fahimta ko,  ina han'koro akan lpyr ki ke kuma kina neman cimun mutunci agaban mutane, saboda kinuna ban isaba   Hapsatu ce tayi Murmushin takaici tace, kiyi hkr in sha Allah zan kiyaye, Nusaiba kidaina yiwa mahaifiyar ki musu su iyaye lalla6a su ake arabu lpy    Banasan in 'Kara ganin kinzo gidan nan siyan abu ko gaisheni, kinji ko    Toh Ummerh Ummerh kan ubanki Allah yasuttura Wuce mutafi    Baba mlm ne yace Allah mai iko Allah yasa mucika da imani........... Ai bai kammala fad'aba yaji wani saukar wawan mari wanda tunda yake bai ta6ajin irin saba     Yana d'agowa yaga babar Nusaibace, cewa tai Allah dama ai da iko yake, kuma kullum zakana ganin sababbi indai kana raye     Ina sake sanar daku indai baku fita harkar "yataba, to yanzu muka fara nidaku wlh    Kuka Nusaiba tasake fashewa dashi ta tako zuwa gaban mom d'in tata tace, "yata³ saida tafad'a sau uku sannan tace Allah yakiyaye ni da'kara zama "ya agareki, wlh nayi ba'kin cikin kasancewa "ya agareki nayi dana sani da nadama wlh nazamanki uwa agareni, ina takaici da ba'kin cikin hakan wlh     Allah yamun tsari yakuma kiyayeni daga irin wannan arzi'kin mara anfani     Indai wannan shine arzi'ki bana fatan samunsa har izuwa 'karshen rayuwata Arzi'ki dabakasan darajar kowaba saita kud'i² wanda ake samunsu aduniya abarsu kuma aduniyar ummmm   Dattin duniya, daud'ar duniya, wanda bazaka ta6a tafiya dasu kabarinkaba     Saidai inkayi aikin alkairi dasu sai yabika    Amman kud'in baza'a ta6a sakaka acikin kabarinka dasu ba    Kuma daga yau nayanke duk wata ala'kata dake karki 'Kara tunanin kina da "ya Nusaiba arayuwarki, ragowar "ya"yanki sun isheki rayuwa amman nikam nagama daga yau    Kuma zama agidan nan yanzu nafara, daga yau wanan gidan shine gidan mu,  kuma family na, dangina, ahalina kuma, abun alfaharina, kuma zanyi tutiya dasu agaban kowa afad'in duniyar nan    Daga yau niba "yarki bace ko family d'inki    Kuma wanda yace miki nazo ganin saurayina to yayi 'karya danni bani da saurayi agidan nan    Nazo siyan abunci ne agidan nan, amman tunda ance miki harda saurayi nazo gani to nazo ganin saurayin, kuma saina aureshi kodan tabbatar miki da zargin ki      Juyawa tai takama hannun Baba mlm tace Baba muje sakashi tai ad'akin datake zaton nasane tace kayi hkr baba ni naja muku     Babu komai 'yar nan haka rayuwa take dama yau da dad'i gobe kuma akasinsa Hakane baba ina zuwa    Futa tai ad'akin ta kalli mahaifiyarta Tace ina kinji menace      Sannan takama hanya danta shiga d'aki    Jitai andan'kota zuwa baya, mom d'intace tace daga kikace kinyanke ala'ka dani ko     Ey tace babu tsoro atare da ita Toh kisani karki 'kar....................... ✍🏻✍🏻✍🏻     keep waiting my fan's 🤗🤗🤔🤔 Hallmarth ce 💕💖💕 [04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 🍃✨🍃✨🍃✨ ✨🍃DASHEN 🍃ALLAH🍃✨ WRITTER'S✍🏻 ASSOCIATION https://chat.whatsapp.com/BHqoOEHjWQz26cyXRvt9V7 🍃ALKALAMI ✍🏻YAFI TAKOBI🗡️ بسم الله الر حمن الر حيم ✨DAN HAKIN🍃 DAKA RAENAH😏🤔✨ 💞NAH💞 SADIYA ABDULLAHI UMAR 💞UMMUH FATEEMAH💞 🅿---          6⃣3⃣&6⃣4⃣ ....................... Toh karki 'kara kusantar koda hanyar gidanane      Kuma  dukkan abunda nake miki najin dad'in rayuwa nayankeshi daga yau      Dukkan wani kud'i danake baki daga yau nadaina baki     Sannan makarantar islamiyya koh boko duka najanye hannuna daga biya miki kud'in makarantar ki       Kuma komai wahala karki sake kidawo cikin family na    Babu ni ba ke sannan karkiyi tunanin kina da iyaye arayuwarki kodai-dai da minti d'aya      Kisa aranki wad'annan sune iyayenki nahar abada, kinajin na ko ina fatan kin fahimta sosai    Cikin rashin tsoro ko nadama tace nafahimta sosai      Dukkan abunda yadanganceki zansa ayi waje dashi akawomiki shi gidan ahalin matsiyatan nan kuma koda pics d'inkine sai nasa akawo miki dan bana bu'katar ko tsinkenki, zan fahimtar da mahaifinki, ragowar yaranmu sun ishemu rayuwa, ke kuma kije na sallamaki wa ahalin matsiyata har abadaaaa Na yadda na amince kuma wannan ahalin da kike ciwa mutunci kika RAINA WATA RANA ZAI TSONE MIKI IDO, Kobadad'e ko ba juma nasan wataran zakiyi nadama mom Fuuuuuuuuuu tajuya tafuta tana banda other akan ayi sauri atashi mota    Suna shiga takama hanyar gida babu 6ata lokaci tasa aka rin'ka kwaso mata kayan Nusaiba ana shiryawa a akwatunan ta, dukkan wani abu daya danganceta saida aka kwasheshi tsap aka saka mata shi ajakunkunan ta da akwatunan ta ----------- Suna tafiya tashiga d'akin da Hapsatu ta futo, binta Hapsatu tai dan ita takasa magana ma sam      Zuwa tai ta zauna akusa da ita ta d'aura kanta akan cinyarta tace yarinyar kirki meyasa kikaiwa mahaifiyar ki haka bayan kinsani Kuma kin karanta alittattafai da dama illar bin umar nin iyaye musamman ma uwa, wadda Annabin rahama dakansa saida ya ambaceta sau uku tukunna ya ambaci uba    Meyasa yarinyata, dakin sani bakiyi mata hakaba kin kyaleta tayi dukkan abunda tai niyya inta gama sai abata hkr    D'agoda kanta Nusaiba tai ahankali ta kalli Hapsatu fuskarta tayi jaaa jaaajurrr idanunta sun kumbura sunyi luhu² saboda tsabar kuka da ba'kin cikin abunda yafaru abunka da farar fata duk tafuta hayyacinta sosai, cewa tai Ummerh nah, mom bazata fuskanta ba kikalli yadda ta bangaje Baba ta tunkud'esa sannan hakan bai ishetaba ta wanka masa mari    Koba komai yaci ace taduba girmansa sannan taduba yanayinsa dakuma yaddda yake bata hakuri ko kaffara bazanba wlh nasan baba yagirmeta yayi jika da ita tunda kakana baikaisa girma ba    Ita gaba d'ayanta mom wahaka take bata ganin girman kowa ko mutuncin kowa asangarce ta taso ita kad'ay ce awajen iyayenta sam bata jin nauyi ko Kuma damuwar ta wulakanta mutum matu'kar akace miki bashi da kud'i to zance ya'kare    Ita awajenta mutuncin ka kud'inka shine kad'ay darajarka idan baka da shi wlh zakasha wula'kanci ba kad'anba   Ummerh ki kyaleta watarana zatayi nadama mukuma zamu zame mata 'DAN HAKIN🍃 DAKA RAINA In sha Allah Ummerh karki damu    Hawayenta tashare mata tace kidaina kuka kinji yar Ummerh, gani nake kamar bazaki iya rayuwa acikin wannan gidan namuba, sbd mu Talakawa ne bamasu 'karfiba    Murmushi Nusaiba tayi tace karki damu Ummerh ta in sha Allah zanyi rayuwa tare daku komai wahala komai d'aci bazan guduba    Allah yasa yarinyar kirki "yar Ummerh ta shafa mata kanta takeyi tana kuka tanata lallashinta    Sallamar kalis ce ta katse mata kukanta dantamanta ma tare suke, shigowa tai har cikin d'akin dataji su suna magana    "Karasowa tai ta rungumeta suka 'kara saka kuka, kalis ce tace meyasa kikai haka Nusy     Kinsan halin mom kalis ki kyaleta Allah yasa hakan shiyafiye min alkhairi arayuwata    Amman kalis batun makarantar ki fa kinga bamu dad'e da fara zuwa lecture ba      Murmushi tai tace zancigaba da zuwa har kud'in wannan shekarar ya'kare daga nan saina ha'kura kawai     Haba Nusy kiyi hakuri ki koma wajen mom d'inki kodan karatunki     A'a ilimun da nake Dashima ya isheni haka, indan dan tabiyamun kud'in makaranta ne bazan komaba wanan ma ilimun danake dashi Allah yasanya masa albarka     Kuka suka cigaba dayi, Hapsatu ce tabasu hakuri da'kar suka ha'kura sukai shiru   Tom 'yanzu kitaso mutafi makaranta kinji    A'a bazani yauba kikai muku abuncin kawai nisai gobe zani Gaskiya indai bazakiba nima babu inda zani      To shikenan, dawowa da Ummerh abuncin kawai, dan nidai babu inda zanje yau ina tare da Ummerh ta sainaji d'umunta    Murmushi Hapsatu tai ta'karaso gurinta kama mata hannu kawai tai suka ''karasa bakin fanfon da aka saka musu atsakar gida tacire mata hijab d'inta tasa'kale akan igiya sannan ta tsugunnar da ita awajen ta saka sabulu ta wanke mata face d'inta tsap sannan tasa Hanki ta goge mata ita tsap    'Dankwalinta ta kunce tagyara mata yarwatacciyar sumarta ta'kara yi mata parking da band sosai sannan tagyara mata d'aurin d'ankwalin tasaka mata hijab d'inta      Lip gloss tad'auko ta shafa mata sannan tace maza kutafi makaranta kinji "yar Ummerh ta, karkice a'a kinji indai kinasan Ummerh ki maza kutafi makaranta ayi karatu banda wasa banda tunani Kuma kinji ko    Murmushi tai tarunguneta tanajin wani dad'i da sanyi aranta dan tunda take ba'a ta6a yi mata abunda Hapsatu tai mata ba    Thank you thank you thank you soooo muchhhh Ummerh na Rakosu tai suka hau adai-daita sannan tayi mata kiss agoahinta tace akula sosai fa yarinyar kirki   Toh Ummerh ta saimun dawo Allah yay muku albarka gaba d'aya Ameen Ummerh   Saida taga tafiyarsu sannan takoma gida, tattare komai tayi tashare sannan ma masu aikinta aunzo sukai mata wanke² tad'aura musu fried rice wadda taji vegetables da naman rago     Sannan tasaka turaren wuta mai 'kamshi tashiga wanka    Bata dad'eba ta futo shiryawa tai tana sauri dan kar abuncinta yakama zuwa tai tajuyesa acikin kularta sannan ta wanke tukunyar     Tadawo tana had'a musu so6o kenan taji anbanko 'kofa,gabanta ne yafad'i ta tashi tana kwashe kayan juice d'in tad'aura akan fridge d'inta wanke gurin tai taji anan duddure akwatuna kamar za'asauke akanta     Kallonsu tai saita d'auke kanta suka gama ajiyewa sannan suka futa, mom d'in Nusaiba ce tashigo itama tana fad'in kina ina, danki tabbatar da da gaske nake kuma kinsanni idan nayi al'kawrin yin abu bana fasawa dan haka gashinan babuni babu ke komai naki nahad'o mikishi Itakam Hapsatu tama kasa magana dan gani take anya kuwa wannan matar tanada hankali, kodai tasha wani abun    "Yarta tacikinta takewa wannan d'iban albarkar, kai Allah yakyauta      Kina inane wai Hapsatu ce tace sun tafi makaranta ai tun d'azu    Toh gashinan kisanar da ita ahalin matsiyata kawai   Fuuuuuuuuuu kamar wata iska tayi waje    Itakam Hapsatu tattara akwatunan tai tashiga dasu cikin ad'akin ta tana mamakin wad'an nan kaya saikace lefen 'yar birni akwati har goma 10 da bakko 4 saida takaisu uwar d'akinta sannan tadawo taci gaba da aikinta Saida tagama sannan tadawo tashimfid'a tabarma tafara karatun al'kur'aninta      Basu d'auki wani lokaci ba suka dawo, dan lecture biyu garesu suna gamawa kuma suka kamo hanya suka dawo gida,  abakin 'kofar gida suka rabu ita da kalis me nafef yayi gaba da ita, ita kuma tashigo gida da sallamarta abakinta, wani dad'i taji jin sautin 'kira'ar Ummerh ta    Wanda tunda take acikin gidansu bata ta6a ganin mom d'inta tayi ba saidai daddy'nta taji yanayi da asuba koda yamma ranar da babu aiki Shiga tai ta zauna kusa da Hapsatu tana Murmushi, itama tana kai aya ta rungumeta tace andawo kenan     Umm Ummerh Sannu da dawowa   Maza garuwan wankankican a flask kije kiyi wanka ad'aki, kayanki suna nan ankawo miki kisaka  saikizo in baki abunci maza     Kinga yamma ta kusa 5:00pm yanzu harda yan mintina     Toh Ummerh ta ngd sosai Tashi tai taje tana duba kayan taga ankawo mata komai harda littattafanta da dukkan wasu tarkacenta, wankanta tafara yi sannan tashirya cikin doguwar rigar atamfa blue da fari tayi kyau sosai    Lokacin data gama ma anata kira  sallar magariba dan haka ta futo sukai salla itada Hapsatu    Karatun suka cigaba dayi saida akai sallar isha'i sannan sukai sallah    Abuncin su tad'auko musu takaiwa Bb mlm nasa sannan tazau tafara bata abaki, tun lomar farko talumshe idanta sbd dad'in dataji sosai     Haka taita bata harta ''koshi sannan tabata juice d'in tasha sannan itama tafara ci saida suka 'koshi sannan suka tashi    Nusaiba ce ta wanke kwanukan harda na Bb mlm sannan tadawo kusan Ummerh ta ta zauna      Hira suke mai dad'i sosai anan take gaya mata in sha Allah komai zaiyi normal   Koda dare yayi ad'akin Hapsatu suka kwana atare, da'kar ta kwanta akan bed d'in Hapsatu shima saida taga tayi mata jan ido sannan Washe gari kwa tin sassafe suka kama aiki inda Hapsatu tari'ka mamakin yadda Nusaiba take aiki kamar ba 'yar masu kud'iba Itada 'yan aikinta suka kammala komai suka gama kafun 7:30 sun gama komai, sa6anin da dasai 9:00pm suke gama wasu ayyukan    Sallama sukaji anayi abakin 'kofa, gaban Nusaiba ne yafad'i rass dan ko amafarki tasan mai wannan muryar.......... ✍🏻✍🏻✍🏻 Keep waiting my fan's🤗🤗🤔🤔 Hallmarth ce💞💖💞    [04/02, 8:02 AM] Ummuh Fateemah🥰💖🥰: 👑👑👑👑👑👑👑👑👑 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 *DASHEN ALLAH* *WRITING ASSOCIATION* *'DAN HAKIN🍃DAKA RAINA😏🤔* _Story and written by_ *SADIYA •A• UMAR* *{UMMUH FATEEMAH*} 🅿---          6⃣7⃣&6⃣8⃣ ...............laaaa Ummerh kingan su, mamaki ne 'karara akan fuskar hapsatu tace too🤔 Kuce kuna kan hanya     Murmushi sukai suka shigo shikam gogan naka babu alamar wasa akan fuskar sa mamaki yake meya kawota gidansu da daddare kuma harda wani kwanciya akan 'kafar kummansa     Ajiye jakar datake bayansa yay akusa da Hapsatu     Kallonsa tai ta kauda kai tasan halinsane muskilanci      Fahat ne yashiga d'aki da kayan nasu yace waya gaya miki mu mukeyin girki da kanmu     Ey mana baku damai muku ai ku kukeyi, ba boarding school 🚸 bace bare Kuce za'ai muku    Wannan university 🎓 ce fa Ai dai muna siyane ko kuma musaka adafa mana     Hmmm 🤔 🤔 lallema brother waye zai muku biyansu kukeyi    Ey mana Waya baku kud'in dazaku biyasu to   Allah ne yabamu     Kaiii    Kamar daga sama taji yace Keeeee kin ishemu da zance da Allah tunda mukazo sai zuba kikeyi tsayyy³     Kallonsa tai ta watsar sannan tace "NI INBAN DAMU DA KASUWA BA KO SAUTUN CIKINTA BANA BAYARWA"    Kai ni kike gayawa haka Ko kallonsa bataiba tace brother wanka zakayi ko kuma abunci za'akawo maka    Aa baridai afara wankan ko Sai aci abuncin     Toh Mamaki Fahat yake dan shidai sau d'aya yata6a ganinta amman kuma tana masa hira kamar sunsan juna    Kuma baisan maiya zaunar da ita agidan ba    Amman komadai menene yasan Ummerh 'nsu bazata 6oye musu ba      Haka sukai tayi har sukayi wanka sukaci abuncin, su amman magana bata 'kara had'asuba saidai harara kawai     Hapsatu kam saidai ta kallesu ta girgiza kai kawai      WASHE GARI Koda gari yawaye tunkan sutashi tayi ayyuka dayawa dan lokacin da suka dawo daga masallaci ma ta kammala wasu ayyukan saura kad'an     Mamaki suke sosai akan yadda take aiki babu kasala ko nuna gajiyawa     Saida tagama sannan tai wanka tai shirin tafiya makaranta, kalis kawai take jira      Tana zaune itada Hapsatu suna hira tana nuna mata wasu pics d'in 'yan ajinsu da sukai birthday 🎊 d'insu sunyi kyau sosai    Hapsatu ce tace kefa yaushene aka haifeki    Ummerh awannan watanne 23 gawata    Kice anyi naki ma ey Ummerh      To Allah yakai mu shekara mai zuwa sai musakeyin wani koh    Ameen Ummerh na Sallamar kalis ce tasasu suka katse hirar tasu   Tana shigowa tagaida Hapsatu sannan tace bestie wlh wannan d'an iskan mlm chemistry d'in yaturo assignment kuma yace duk wadda bataiba bazatai test d'insaba ta gobe kuma agoben zai amsa inkika bashi kishiga d'akin test inbiki bashiba kuma shikenan kiji asalansa     Tooo fa yanzu yazamuyi Mugani, mi'ka mata wayar tai tagani tace ta6 mun bani wlh yanzu yaya zamuyi    Kuma yasin niban ganeba Kodai muje mucire masa kawai Haka za'aima    Amman fo komun cire yace shi bayasan na computer    Na rubutu yakeso To kawai muyi Googling mana Hakane kam    Fahat ne yace muga aikin naku Yawwa kagani brother amsar wayar yay yafara dubawa     Ok bari Nauphal yayi muku Kubada paper guda biyu Cirowa sukai suka bashi sunata murna     Yanzu kunada lacture ai ko Ey bro    Toh maza kutafi tunda bayau zai kar6a ba inyaso in kuka dawo yagama    Kusaka sunayenku akan paper's d'in Amsa sukai sunata jin dad'i suka rubuta sannan suka tafi        Ummerh zamu tafi To yaran kirki, Nauphal maza jeka sakasu a nafef katabbata sun shiga sun tafi sannan kadawo     Ummerh kuma ni Haka nace ko bazakaba A'a am sorry 🙇 mom    Oya maza kutafi Mom yanzufa nashigo gidan bari ind'an d'auki ruwa saimu tafi     Ok Tafiya yay yad'auki ruwan sannan suka futa yana gaba suna binsa abaya     Sai murgud'a masa baki Nusaiba take     Shikam baima san tanayiba Saida yatsayar da me nafef sukai masa bayani sannan yabiya suka shiga sannan yajuya yatafi yanata sakin tsaki      Fahat ne yabashi assignment d'insu yace yay musu    Yeahhh meyasa ka amsa daka bari an mata dukan tsiya ai    Duka sai kace wata pri-sec University fa sukeyi waye zai dakesu kuma     Amman yaya saidai inyi na 'kawarta amman bazanyi na mara kunyar nan ba     Ni nace kayi ko itace tace kayi Shagwabe fuska yayi yace haka yeahhhh Allah bata da kunya jiya kanajin takama mun rashin kunya amman bakace komai ba   Ajiye masa takaddun yay yafuta yace in kaga dama kayi inkuma bakaga damarba kabarshi zanyi musu     Tashiyay yasha gabansa yakama kunnensa yace am sorry 🙇 my big bro     Allah zanyi musu kamar yadda kace kaji bro    Ok yayi matsamun to     Cikin muryar shagwa6a yace A'a am sorry fa nace    Toh naha'kura mana Amman ka'kiyimun dariya    Kama kunnensa yay yamurd'a sannan yace naha'kura to Ashhhh yeah akwai zafi ba wlh    'Dan dukan kansa yay yace ai gwara kaji zafin     Rungumesa yay yace yeah to mukoma ciki kaji

Chapter 10 of 16