Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su dakko mishi Mimi Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 4 Feenat Ja'afar Novel's Su Salma an samu gurbi a school of hygiene,da shawarar baba ta cike ba Polly ba. Ranar da ta fara fita da personal zata kai takaddun ta. Ba yadda zaka ga Salma ka gane itace da lokacin tana budurwa, yanzu Salma ta daban ce,ta gaban goshin Mama, dan ta dage dole sai tayi kara'i da zawarci. Kwanar su Ja'afar ta shawo,tasan yanzu haka yana makaranta dan sha d'aya na safe. Sosai tai k'yau cikin doguwar riga ruwan kwai mai duwatsu,da g'yale karami ta nad'a fari,ta ritaya jaka karama mai (chain),ba wata k'walliya tayi ba ta azo aga,dan wannan ma Mama na t'saye tayi ta,ta kuma rantse ita da hijabi sai a sallah. Zai wuya kace ta ta6a aure har da rabon Miemie, dan yanzu ne take shekarunta na (22) a duniya. Kanta kasa take tafiyarta cikin nut'suwa, sai dai ji take duk ta tsargu,tamkar Ja'afar na kofar gida yana kallonta. Dak'yar ta kai kanta bakin kwalta tana sauke numfashi, ashe feeling take... "Kin k'yauta Salma kenan?... A razane ta juyo jin mai maganar.. Rai had'e yake kallonta tamkar bai ta6a dariya ba. Duk da ta tsorata da ganin yanayin da yake amma ta cije itama ta ci kunu. "Da nai mey fa? Rai 6ace yace "Ina Miemie?.. Kai ta k'autar gefe,kan tace "Gida".. A fad'a fad'a yace "Wato bakiji abinda nace ba koh?.. Kalli shigar ki,kamar wacce zata party,sam baza mu shirya dake ba in.. "Tafiya ne?.. Wani mai keke napep ya tambaya, kallo irin na baka isa ba tamai, kamin tace ma mey keken "Eh tafiya ne. Tana kokarin shiga tace "ba ruwanka da shiga ta,cos I know what i'm doing.. And ni ba y'arka bace, na fad'a ma ka rabu dani. Sam taki k'allon fuskarshi bare ta sare gun taka mishi burki. Baki sake yake binta da k'allo har mai napep yaja kamin ya samu k'warin ya tanka. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:28 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/7, 11:03 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 34_Jingina tai a jikin Napep din tana sauke ajiyar zuciya. "Kai hakuri Ya Ja'afar, ya zama dole na koya ma nisa dani,kai hakuri,ina sonka wallahi.. "Hajiya magana ne?.. Kai ta dago jin mai Napep na tambaya, ashe maganarta ta fito fili. Ta gama komai Monday zata fara zuwa,kwarai taso ta yaye Miemie sai dai ba hali,dole tabi yadda uban y'ar ya t'sara. Shikam Ja'afar tun daga wannan ranar kullum zata makaranta sai yai mata maganar wani abu,koh yace k'walliya tayi yawa, koh yace uniform ya d'ame ta. Wani sa'in har ta wuce tana dariyar zariya irin ta Ja'afar, tabbas gani take ya zare. Shima kamar yadda Abba yace haka dole ya fara _processing_ dan tafiya masters a B.U.K,sai dai fur Abba yace garin zai bari,a Zaria zai yi,kar ya damu an ma kusa shirya masa komai ba koh kwandalar sa. Tamkar ya aza hannu aka ya kwala ihu yake ji ranar,yana nan ma ya ya k'are da Salma bare ya mata nisa?.. Tafe suke ita da wata y'ar makarantar su da tazo zata rakata bakin kwalta, ta gama shirinta kenan zata gidan Aunty A'i sai fasawa tayi. Tai kyau,fatar sai shining take taji mai da sabulun Mama. "Allah ba wanda zai ce kin haifi Miemie sis Salma,kin ganki kuwa?.. Murmushi tai ma kawar tata lokacin da take t'sayar mata da Napep. "Haka dai kuke cewa kullum.. Murmushi tai mata sukai sallama. Tana kula da wani mai mota yana ta kallonta ya t'saya siyan Apple. Kokarin tsallakawa yake ganin zata wuce da sauri,kai ta kada dan sarai tasan yau ma za'a tafka dirama irinta ranar chan da Ja'afar, dan tana kallon yadda yake maka mata harara a kofar gidan su suna zaune shi da Garba da wani,tasan darajar kawarta taci da yanzu ya taso bambami dan tasa g'yale a kafad'a, kai ta girgiza dan yanzu abin dariya yake bata ma... "Assalam Alaikum.. Waiga wa tayi jin an mata sallama. Da dan sakin fuska ta amsa tana mai cigaba da tafiya a nut'se. "Gunki nazo fa y'an mata dan Allah. Kai ta daga aikwa idon Ja'afar kyar kanta. Da murmushi ta juya badan taso ba sai dan yakice dan gudanta, duk da tasan baza a wanye lafiya ba. Tuni dad'i ya kama saurayin dan da har ya fara d'ari-d'arin mata magana,sai ya ga kamar matar manya ce. "In bazaki damu ba dan Allah ki ban numbern ki,wannan ne gani na biyu da na miki a layin nan yanzu ina sauri zan kira ki... Ta gefen ido ta sato k'allon Ja'afar ai kwa a suk'wane yake zuwa gun nasu. Da sauri ta karbi wayar mutumin da zummar sa mishi ya iso. Su dai su Garba ido ne nasu,dan abin Ja'afar ya daina bashi dariya yanzu tsoro yake bashi. "Bashi wayarshi ya kauce tun kan na dagargazata a gun nan.. Banza tai dashi tana cigaba da latsa wayar karya,bata aune ba taji ya warce da karfi. "Karbi wayarka ka bar layin nan Malam, koh kaga tayi sa'ar tsayuwar ka?.. Baki sake saurayi yake kallonshi,shi a tunanin shi koh yayanta ne ma,dan shima haka yake ma samarin k'annenshi baraza,dan haka bakin shi alaikum ya kar6a yana kallon Salman. Cike da tsiwa ta kallo Ja'afar din, "Malam wai ina ruwanka da samari na ne eyeee?.. "Kimin shiru tukunna, kema zan dawo kanki ne ai. Da hannu ya nuna ma saurayin hanya halamar ya ware,ba daban yaga Ja'afar din ba na wasa bane ba da ba yadda za ai ya bar wannan sankaceciyar budurwar. Da sauri ganin zai tafi tace "Malam ina zaka ne?.. Kai ya kad'a mata yana murmushi kan ya kara gaba. A fusace ta nuno shi da hannunta "Wallahi Ya Ja'afar na gaji da wannan abin fa,dan wallahi na kusa kai karar ka gun Abba ya mana t'sakani,mey ruwanka dani wai?... Shiru tai tare da matsawa da sauri ganin ya mika hannu bayan gyalen ta. "Wai kai lafiya ka ke?.. Harara ya sau mata kan yace "Tun muna sheda juna ki daina sarar nan ta sauke g'yale a kafad'a Allah... "Bazan daina ba din, na fad'a ma bani ba kai, tunda kai har yanzu bakasan Annabi ya faku ba... Shiru tai ganin Garba. "Haba Salma,haba,a titi fa ku ke?.. Tunda kinsan halin kayanki sai ki gaba ki barshi ya karata, dan Allah ki daina biye mishi. Harara ya sakar ma Garban, "ina ruwan ka toh kai ma,kowa dai yasan da matata nake t'saye ba kowa ba.. "Mtsww... T'saki taja rai 6ace, duk suka kallota.. "Wallahi you are sick.. "Ni matarka ce, amma fa a da, kai istigfari ma tun wuri,dan wallahi za kayi sa6o... "Kimin shiru fa Malama..dan kwanciyar hankalinki wallahi kibi abinda na ce kiyi,period.. Shiru tai tana kallonshi,karfin hali sai gun Jafar,tabbas sai tayi da gasken gaske,dan abinshi gaba yske,shima Garban k'allonshin yake,abu dai kamar wasa yake gani yanzu zai zama babba. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:07 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 35_Drama sosai sukai kan ta wuce gida rai 6ace duk rai a dagule, dabarar ta ta kare kuma a akan Ja'afar, duk hanyar da zai zuciya ya daina kulata tabi ba nasara,tamkar ma zigi take mishi. "Mtsww... Taja t'saki,Tabbas so so ne,amma na Ja'afar son kai ne,dan shi yaja komai.. "Ke kuma ke da wa kike t'saki haka?.. Ba tare da ta dago ba tace "Ja'afar man.. Ya hanani sakat a unguwar n... Da sauri ta datse harshenta dan jin Mama fa ke tambaya, "Au har yau yana nan yana bibiyar taki koh?... Kai ta girgiza da sauri, zarar bunu.. "A'a, ni nasan hanyar maganinshi,ki ban nan da gobe. Da sauri tace "A'a Mama ba komai bane fa,kiyi hakuri zai daina... Shiru tai ganin harar da take aiko mata. Tun daga ranar Mama ta zama y'ar rakiyar Salma hanya,sai ta tabbatar ta hau abin hawa zuwa makaranta zata juyo tana aika mishi harara,da tai na sati sai ya bar tare hanya kuma ya dawo waya. Ana haka shima admission nashi ya fito shima,tuni ya shiga kunci,dan yasan ya kusa yin nisa da Salma,hakan yana nufin komai zai iya faruwa. Ranar da yamma ana washegarin zai tafi yazo mata sallama duk da sunyi fad'a. Taimakonshi daya Mama bata nan ranar ma,dan yana ga ita kad'ai zata iya tsaida shi a yima Salma kashedi. Shigarshi zauren kenan sukai kicibis zata fito,harara ya sakar mata kan yaja ya t'saya. Fita take shirin yi ya ruko gyalenta da sauri har yana zamewa,don haka a fusace ta juyo da niyar balbaleshi ya marairaice mata fuska. "Saken g'yale toh.. Murmushi yake yaki saka, ''ka saken gyale koh na fuce... Da sauri ya cika yana tare kofar fitar. "Maganar fahimta nake so muyi dake,dan Allah ki t'saya.. Hannu ta hard'e a kirji ta k'alleshi,itama zata so su fahimci juna. "Ina wuni toh,tunda har gaisuwa kin soke dani. Da kalar tausayi ya kara yana sukui da kai har taso yin dariya kamin ta gaishe shi. "Ina Miemie?. "Da Mama suka fita,kayi kai maganarka kan su dawo fa. Tsayuwa ya gyara tukun ya kira sunanta, rai sake ta amsa,fatan ta yasa zancen azziki zai mata ba wai shirme ba. "Salma".. A karo na biyu ya kara kiranta, bai jira amsarta ba ya cigaba, "Gobe zanje Zaria kan batun makaranta da zan fara, kima Allah Salma ki yi kamar ina nan dan Allah,banda kula tsagerun samarin nan wanda har yau basu mallaki hankalin kansu ba dan Allah. "In ma aure naso kiyi ina ga ni ya dace na baki mijin aura,bare a agendar mu bamuyi haka dake ba... T'sam tai tana kallonshi da halamun ya zare tana murmushi, amma zata bishi a haka a wanye lafiya. "Toh naji,zan kuma kiyaye,happy?.. Kai ya kad'a da murmushi, "yauwa koh ke fa,dan Allah Salma ki riken alkawari nan.. Kai ta kad'a tana taji ai.. Da haka suka rabu ya bata kayan zakin Miemie, murna fal ranshi suka rabu ranar. K'warai ta samu sakewa sosai bayan tafiyar shi,tuni ta kara bud'e shafin zawarci sabo,duk da kasan ranta tausayinshi take ji sosai. A wata daya tai samari biyu irin son Mama, barin Alhaji Usman Dan chanji. Kud'i sosai yake kar mata kamar ba gobe, albarka kwa kullum samunta take gun Mama,yace shi ba yaro bane,dan haka yana so ai auren cikin k'ank'anin lokaci. Ya sanar mata yana da mata daya da yara biyu kachal,aurenshi uku,sun rabu da biyu sai Hajiya ta k'arfen. Tunda suka rabu tazo gida tana tuna abu uku, tabbas a yanzu bata da ra'ayin auren mey mata,dan taga aya akan Bintu. Sannan bata son mutum mai irin kud'in Alhaji Usman sam a rayuwarta. Gwara ma Kamal dan shi matashi ne kamar su Ja'afar, kuma yafi kwanta mata a rai,gashi da saukin hali da saukin kud'i. "Oh ni y'an nan,ashe arziki ke binki Salma a rayuwa?.. K'allon Maman take yadda take daga abubuwan da Alhaji ya bata,ita dey nata ido. "Bana jin koh lokacin y'an matancinku kun ta6a had'uwa da irin wannan, babbar harka ai tayi y'an nan... "Mama ni fa mutumin nan bai kwanta min ba sam Allah,gashi har ya fara maganar aure tun yanzu,ga yana da mata fa,ga ni sam irin kud'in nan baya... Baki sake Mama ke k'allonta,tuni ta tsayarta cikin fad'a. "Rufe baki ni sauraniyar y'an iya t'sari, ashe har yau kina nan da halin nan Salma? Arziki na binki kina zura da gudu?.. "Ina ruwanki da matarshi?.. Koh a kanta zaki zauna?.. Kai ta girgiza zatai magana ta dakatar ta. "Koh dai Salma hudubar yaron chan tai tasiri akanki?.. Kai ta kad'a, "Allah Mama ba haka bane,ni ina tsoron kishiya ne,kinaji fa wai aurenshi uku suna rabuwa sai ita ke zama... "Sai mey toh?.. Kar ki bada mata mana Salma?.. Baki sake take k'allon Maman,kamar ba ita ke fad'in ba mai zama da kishiya ba a yaranta tunda itama bata zauna ba,wace daga ce ba'aci ba lokacin auren Bintu da Ja'afar amma yanzu kud'i ya warware Mama?... Kat'seta tai, "Saboda haka komai yace ki ce toh, in ma ita ke fidda su toh ke zama daram,dan wannan ba gidan fita bane in an shiga... Hawaye ke zubar mata yayin da tazo k'wanciya tana tariyo zancen Mama, dole in dai tana son faranta mata wai ta ba wa Alhaji dama. Waya ta d'auka jin shigowar text message,tasan na Ja'afar ne. _"Salmatee,remember, a heart dat truly loves never loses hope..but always believes in d promise of love,no matter how long d time and how far d distance,at d right time,love will fine a way".._ ki rike alkawarin ki,love you.. *Ja'afar* Kukanta ne ya karu sosai bayan ta gama karantawa, tabbas in ta cigaba da sauraran kalaman Ja'afar zasu sa ta karaya har ya ci galaba akanta.. "Bani da kamar ka har kullum Ya Ja'afar, sonka gareni ba mai misaltuwa bane,amma kai kaja mana koma meye... Fuska ta goge sakamakon jin tahowar Mama da Miemie na kuka. Washegari kanta t'saye ta bawa Alhaji damar ya turo magabatanshi kawai koh ta huta da dawainiya da son Ja'afar. Sabon sim ta siya tasa a sabon wayar Alhaji da ya bata,a haka suka raka wata kusan biyu, duk da tai kewar text da kiran Ja'afar din. Shikam yana chan hankali tashe na rashin samun wayar Salma, ga Abba ya sanarshi kar ya sake ya dawo sai an nemeshi a makaranta, Duk da an sanarshi ana kawo Miemie gidansu ta yini. A jikinshi yaji abu na faruwa,duk sai yaji bai da nut'suwa sai ya je gida dan tabbatar da zarginshi. *** Tunda daga d'anno kanshi layin su Salman ya ja ya t'saya. T'saye take da dan murmushi a fuskarta, sanye cikin favorite dinshi riga da skirt na atamfa purple, tai kyau matuka gyalen nan a kafada,daga inda yake zai iya gano bakin gashinta a tufke ta chan kasan dankwalinta, tasha ado tamkar zata party. Wani abu ne yazo dai dai makogwaronshi ya tsaya,kishi... Bai san ya isa gun ba sai da yaji ana "lafiya?.. Kallo shi yayi, duk sai yaji yau baida ma k'warin g'wiwar fad'a,Salman ya kalla,da sauri ta kawar da fuskarta gefe ta had'e rai. Sai ya dawo kan Alhajin,tsaf sai ya haifi Salma,sai t'sabar kud'i da jindadi da suka 6oye shekarunshi. Kallonshi yake tun daga sama har zuwa kafa, so yake ya gano ta inda ya fishi har Salma ke mishi murmushi haka. A zuciya yace "Babu... Sai dai kud'i kawai da sa kaya masu t'sada. "Kai fa,daga ina ba koh sallama?.. Cike da haushi ya kallota, "baki sanarshi ko ni waye ba ne?.. Kan Alhaji ya dawo,ba shakku yace "matata ce ita,zaifi mana k'yau in ka daina zuwa gunta Alhaji. Murmushi yayi Alhajin,kan ya kallo Salman, "sai kinji ni kawai.. A takaice ya k'alli Ja'afar din,ba sai an fada mishi waye ba,halamu ya nuna tsohon mijinta ne,har zaga wa tai ta rufe mishi tana daga mishi hannu d'auke da murmushi, har ya kule tana daga mishi hannu kan ta d'au kayanta koh ta kanshi bata tai hanyar gida,da zafin nama. "Wato abinda ki ke kenan tun bayan tafiya ta shine yasa ki ka kashe waya? Salma mey yasa kike son ki 6ata min rai wai?.. Jibi fa shigar ki,ji gashi a waje,wace iriyar rayuwa ki ka za6a mana? Cike da fada tace "Wace iriyar ka za6arwa kanka dai Ja'afar.. Ya zaka zo kana fad'an wata iriyar magana mijin da zan aura?.. Karan nan bazan dau abinnan naka ba wallahi, aure zamuyi dashi nan da wata biyu... Sai kayi abinda zaka yi. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:07 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 36_Kan yai k'wak'waran mot'si ta shiga gida tare taru kofa harda sa sakata. Jiginna tai hawaye na neman zubo mata,daga yar bular dake jikin kofar ta leka waje,kofar gidan yake kallo jiki a sanyaye kamar yasa kuka,juyawa tayi hawayen dake makale mata ya zubo,dak'yar ta seta kanta ta shiga ciki rai cike da tausayin Ja'afar. Kusan kullum zai zo ba zuciya dan bata baki akan Alhaji tana mishi wulakanci,shi kam Alhajin har dariya yake bashi wani sa'in, dan baijin da abinda zai iya rabashi da Salma a dai dai lokacin nan,sai dai jin saki uku ne kawai sai ya bar jin komai,iyaka ma yai ta tusa ma Ja'afar din bakin ciki in ya gansu da kalamai ma Salman. Biki ya karato ga makaranta,amma haka duk week end daga Zaria zai zo kan batun Salma ta janye zancen bikin nan. Duk ya fita a hayyacinshi duk akan auren Salma. Da halamu ya fara hankalin daina zuwa gun Alhajin,sai dai in yazo ya tsaya chan gefe sai tazo shiga ya tare ta da magiya. Yau saura k'wana biyu biki, sai gashi shi da Garba,dawowarsu daga gidan g'yaran jiki kenan ita da Ummi. Turus ta ja ta t'saya ganin Ummi ta wuce ita ya tare mata hanya. "Ka ga yau bani da lokacin jin wannan mahaukatan zantukan naka,jibi iyanzu na d'aura aure, ya kamata kasan inda dare ya maka, sabuwar rayuwa zan fara,saboda haka kai yanzu ya rage ma,danni yanzu baka gabana... Kai ya kad'a mata, "Karan nan bazan hanaki aure ba Salma,sai dai ba da Alhaji ba. Baki sake take kallonshi, Garba ya nuna, "Garba zaki aura Salma,kimin wannan alfarmar. Kai ta dauke daga kallonshi ta k'alli Garban wanda shima ya cika da al'ajabin kan maganar Ja'afar. Sai ta girgiza kai da murmushin takaici. "Tanan kuma ka bullo min?.. Auren kisan wuta Ja'afar? Lalle kayi nisa ba zakaji kira ba. Bayab hannunta tasa tana goge hawayen idonta. "Wai ka zata ni din auren kisan wuta zanyi da wanda zan aura?.. Kai ta kara kadawa, "Kai kuskure toh,dan ni aure zanyi na tsakani da Allah,ba wai nayi na fito ba Ja'afar.. "A'a Salma,ba haka ne nufi na ba.. Da muryar kuka ta tareshi, "Hakane man,haka kake nufi,wato ka kawo min abokin ka na aura bayan wani lokaci ya sake ni sai ka halartawa kanka ni koh?.. Baki sake duk suke k'allonta,ganin yadda hawaye ke zubar mata. "Jahilcina bai kai nan ba Ja'afar, a bazan ta6a abinda ka ke so ba, a gareni yanzu k'allon Yaya nake ma,da kuma uban yarinyar dana haifa, bayan haka.. Kai ta girgiza, kan tace "you mean nothing to me a yanzu kam.. Jin baice komai ba yasa taci gaba. "Banzaci haka daga gare ka ba Garba,a ganina in shi ya 6ata kai mey dawo dashi kan hanya ne, wallahi auren t'sakani da Allah zanyi, ku sani kuma auren so zanyi,wanda nake fatan mutu ka raba ne,dan Allah,dan kaunar ka da Allah ka bar bibiyata,dan Allah.. Shiru tai dan ganin shima idonshi ya taru da hawaye,da sauri ta shige gida tana goge hawaye.. Har ta shige yana binta da ido ba magana, sai hawayen da ya zubo mishi shar, da sauri yasa hannu ya share. Kafad'arshi Garba ya dafa, "kaji zancenta, tai mana fassara baibai,ya kamata kai hakuri ka bar kulata in har kana wa Allahn data had'a ka dashi. Kai ya daga, "InshaAllah.. ~~~~ Taro ne iya taro,taron shedar auren Salma da Alhaji Usman, daga inda yake t'saye a chan nesa da kofar gidan yana k'allon komai har aka shafa. Juyawa yai da jaka biyu hannunshi tare da sanya bakin glass dan 6oye sirrin dake idonshi. Yasan yanzu kam Salma ta mishi nisa. "Mama taki ta bud'e dakin fa,daga ina jiyo sautin kukanta Allah. Ta window Ummi ta leka,gata k'wance ta tasa tsohuwar wayarta a akan fuska tana razgar kuka, So ba karya bane Salma. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:08 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 37_Har aka kai amarya gidanta bata bar kuka ba,dayawa sun zata kukan na Mama ta cire Miemie ne, dan basa ji koh auren farkonta tayi haka. Kowa ya wat'se sai ita kad'ai, ko'ina take kallo a dirare, gida ne iya gida,tun bata fita ba ta zaga,yau gata a gidan da ba Ja'afar, ba kuma Miemie,tuni ido ya cika da kwallar tuna baya. Anya tai ma Ja'afar adalci kuwa?.. Anya bata ci amanar so ba kuwa?.. Ta sani da takai Ja'afar bango,hakan yasa bai kara waiwayarta ba,ta yuwu yai zuciya... Ido ta goge da sauri jin motsin za'a bud'e d'akin. Ango ne yasha babbar bunjima da rike da leda, bakin nan har kusan kunne,jan mayafinta ta kara yi ta rufe fuska. "Amarya! Amarya!!.. Ba k'ya laifi wai koh kin kashe dan maigida koh?.. Murmushi ta k'akalo mishi, zama yayi a gefenta tare da ajiye ledar a gefen bedside, bata aune ba taji ya yaye mata g'yale yana kallon fuskarta. Alwala yace ta d'auro suyi nafila,dan wai agareshi babbar kyauta ce ita daga Rabba. Sun gabatar da duk wani al'ada,sai dai har ango ya d'ane gado amarya tana t'saye a gaban madubi sai sininiki take,gabanta sai mugun fad'uwa yake tamkar wacce tai auren fari. Murmushi yayi da kanshi ya taso ya karaso har gaban madubin tare da kamo hannunta. "Muje ki kwanta haka dare nayi sosai.. Kamar yarinya ya kwantar ta gefen shi yana kallo da murmushi. Salon ya sauya,tuni ta fara digar da hawaye,shi kadai yake kid'anshi yana rawarshi,sai dan sautin kukanta dake fita kad'an-kadan,wanda a gareshi tamkar zigi take mishi. Kai ta juya ta kallo Alhajin dake bacci hankalinshi k'wance,abu uku sun hanata bacci,na farko kukan zamanta ta wani ba Ja'afar ba,na biyu tunawa da Miemie, na uku minsharin Alhaji.. Har gari ya waye bacci sai jefi-jefi-jefi ke dibanta,sam taki jinin minshari kusa da ita,tsaf yake hanata bacci. Shikam da farin ciki ya tashi irin na sabbin ango,ita kam da ido kawai take binshi. Tara sai ga yaron uwargida ya kawo abinci,da fara'a ya gaida ta,kanshi ta shafo kan tace ya sunan shi? "Sunana Ja'afar".... Kallonshi take da mamakin jin sunanshi, koh dai bataji dakyau bane?... Kat'seta yai da fad'in "K'anwata kuma Nabila,Umman mu tace sai anjima zamu shigo kar mu tashe ki a bacci. Murmushi tai mishi yace ya tafi.. "Ja'afar... Ido ta rint'se jin maigidan ya kira sunan,ba shiri ta d'au abincin tai kitchen. Bayan sun gama komai yace suje bangaren uwar gida zai magana dasu. Batai zatan da kishiyoyi masu kaunar kishiyar su ta ra6e su sama da matar Alhaji ba,sosai tai mata bazata,tun tana d'ari-d'ari har ta saki jiki da ita da yaranta, musamman Ja'afar.. Yau Miemie ce tazo mata,sai murna take taga Auntyn ta. Duk babyn ta rame,yaye bai amsheta ba. ''Miemie, ga nan Abdul yazo ku tafi gun Mama koh?... Kafad'a ta make halamar taki tana neman kuka, "Yi hakuri gobe zanje gida mu taho koh?.. Kuka ta saka mata baji ba gani, sai mak'e kafad'a take tana ita "um-um. Sai ta sallami Abdullahi kan gobe yazo ya d'auke ta, har ya jima da tafiya Miemie bata bar kuka ba. Sai um-um kawai take fad'i, suna haka Alhaji ya shigo,duk yai kicin-kicin da fuska, cikin fad'a- fad'a yace ta lallasheta man,shi baison hayaniya bare ta yaro... Baki sake take kallonshi,kaya ya ajiye ya juya ya fice harda dan tsakinshi,toh mey yake nufi?... Y'arta ta d'auka ta sa6a a baya sukai kitchen tana fad'in tai shiru ba inda zata toh,kan aje ko'ina sai ga nan Miemie harda dariya tana bata labarin Mama cikin gwaranci. Har dare ba Alhaji ba duriyarshi,abinci ma sai Ja'afar ya turo ya d'auka. Suna k'wance Miemie sai k'allonta take,gani take kamar guduwa zata yi ta barta. Kanta ta shafo tana mata murmushi, "Yi baccinki my Miemie, ina nan fa tare da ke kinji?. Kai ta daga mata tana k'allonta. "Antee... Kai ta dago kan tace "Na'am Miemie nah... "Abba... Tsam tai tana k'allon Miemien,Abba? Ta nanata a ranta. Murmushin dole ta k'akalo tana fad'in Abba yana nan Miemie,bata aune ba taji ta kara fad'in Abba... Hawayen da take makalewa ne suka zubo mata,da halama yanzu Miemie ce matsalar ta,dan zata dawo mata da hannun agogo baya. Da dabara ta d'auke hankalinta daga tunanin Abban ta hau lalla6ata har tai bacci. Photocopyn Ja'afar ce Miemie,barin yanzu data kara girma, tunani take koh dai Ja'afar har yanzu baya zuwa gida, laifinta ya shafi Miemie? Dan tasan sai Miemie ta kwana biyu bata ganshi ba take nemanshi haka. Tana nan har maigidan ya shigo,sai wani k'allo yake aikama Miemie wanda ta kasa fassara shi. Tun daga ranar ya zamana in dai Miemie zata zo,toh fa zata rasa gane kan maigidan, ta rasa dalili, musamman in tai la'akari da hadithn hausawa na Duk mai son uwa toh yaso d'iyanta. Ranar har ta kasa d'aurewa tai mishi magana, amsar da ya bata ta jima tana sata hawaye. Ga Miemie da kulafuci bare tace kar a sake kawo ta,asalima duk randa tazo fara'arta karuwa take. Sa6anin in tazo mata,data gane sai take d'akko ta duk randa bata da girki su k'wana, ranar da maigidan yake da ita su wuni ai rabuwar kuka har uwar. Allah yaga Miemie kadai take gani taji sanyi a ranta. Ranar suna fira a bangaren uwar gida take mata korafi kan halin maigidan akan Miemie. Murmushi tayi kamin tace "Sai kinyi hakuri da halin Alhaji Salma,ba tone- tone ba,a'a kawai dai ya kamata ki sani, Alhaji sam baya son yara,musamman hayaniyar su,hakan yasa ya d'aurawa kansa kin haihuwar k'arfi da yaji, nayi ta zaman takaicin halin nan na Alhaji har t'sawan shekara bakwai,a lokacin aka tada kayar baya kan sai ya kara aure tunda ni sun zuba ido shiru. "Hanna ta shigo itama ta shekara biyu shiru, ni dai nasan kusan kullum yakan tasa ni da Hanna dan shan maganin daukan ciki. Ana nan ranar wata kawar Hanna tazo suna jajanta ko dai matsalar gun mijin ce,toh a ranar dai asirin Alhaji ya tonu,dan kawar Hanna taga magani tace na hana d'aukar ciki ne. "Ranar muka mishi tawaye har Hanna,in takaice miki yace shi bai shirya haihuwa ba yanzun,anan sukai baram-baram da Hanna ya bata takardar ta. "Haka sauran mata biyun kowa tazo zai fad'a mata ra'ayinshi, da taga bazata iya ba zata fice, duk kuwa da tarin arzikin shi,a lokacin muna da shekara kusan sha uku da aure,koh mai zaiyi na daina shan magani, hakurina ya kare,nan na kai kara gun Hajiyarshi. "Ya saduda muka haifi Ja'afar, yace daga nan ta isa haka,wai incigaba shan magani,a gabanshi zanyi kamar nasha, daya kauce zan zubar. Koh shekara Ja'afar bai ba na samu cikin Nabila,cikin da a kullum sai naga tasku gun Alhaji,gar da gar zai nuna bai kaunar su,barin in Ja'afar na kuka,haka nai ta hakuri har na haifi Nabila. "Yanzu kam magani sai dai shi yai tasha,amma banda ni,kinga Nabila har ta shiga shekara ta biyar. Tsam tai tana tunani bayan kammala bata labarin waye Alhaji, ita ba kullen ne yafi damunta ba sama da rashin son haihuwa.. A kalla yanzu ta doshi wata na biyar a gidan nan amma ba bayani,sam bata kawo wani abin ba,ashe wannan ne dalili?.. Bazata iya tuna ranar fitarta ta karshe a gidan nan ba,tun kwa bayan aure sau daya taje gida sai dai aukin waya koh azo mata, lalle duniya labari. "Zaman hakuri kawai zamuyi Salma,sai adu'ar shirya in da rabon zai gane, amma shawarata gareki ki rike y'arki, dan kar kiyi sakiyar da babu ruwa tun kina yarinyar ki dake,shi ba ruwanshi. Kai ta kad'a mata,Allah sarki Ja'afar, ta tuno lokacin data fara period tana kukan samun ciki yana murna. Ta tuno da abinda yace mata "Allah sa Miemie ta samu k'ani a kusan nan... Ta tuna data hau bori ya hau lallashinta, harda alkawarin shi zai mata reno in bata shirya ba... "Ba kuka zakiyi ba Salma,muyi ta adu'a. Hannu takai fuskarta, ashe kuka take bata sani ba. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:08 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 38_Ranar sakwa-sakwa ta yini tana tuna halin Alhaji, bai da mugun hali koh daya sai na bakin kulle da kin yara,bayan nan baza tace ga mugun halinshi ba. Zataso sanin wane hali Ja'afar yake ciki a yanzu,dan tabbas tasan ya zuciya da ita,tunda gashi ance koh wajen Miemie baya zuwa sai aike?.. "Mey nai kenan?.. Mey nayi ni Salma?.. Mey yasa ban iya jure zama ba aure ba a rayuwa kamar yadda yaso muyi..mey yasa?.. Juyi tayi tana hawaye, Kila rabon Miemie kadai take dashi a duniya,tasan kuma aure dai ana yinshi ne dan abu biyu,samun zuri'a na daga ciki, gashi ita anan ana son a haramta mata. Tabbas d'aukar y'arta shine babban mafita a game da yadda take jin son ta haihuwa a yanzi.. Wayarta ce tai ruri, a hankali

Chapter 9 of 11