Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kinfi k'arfin shi kima ji da wai,gaba ake son ci ba baya ba wallahi,d'uk da ban san wacce iriyar amsa kika bawa Muzammil ba... Da harara Salma ta bita, kan tai k'wafa, "ina ruwan ki da sha'anina? Ke har kin isa ki fad'a min wanda ya dace dani Ummi? Baki Ummin ta ta6e, "ke dai kika sani,dama ni meye nawa? Ni koh ana saurayi mey zanyi da Ja'afar mai shegen dacin ran t'siya... "Wai ku baku zama inuwa d'aya ne da juna Salma? Mey yasa baki iya daga ma Ummi K'afa sai kin tanka mata kullum kuna sa makota na jin ina daga murya.. Kasa Salma tai da kai kawai,tasan yanzu in mama taji ta kad'e.. Kamar k'wa wacce Ummi ta karanci zuciyarta ta amshe.. "Wai fa mama daga shawara ta tsaya min masifa,yau akan wannan dan gidan Malam Kabiru mai shago ta kori Muzammil,daga fad'a mata gaskiya ta hau ni da masifa.. Dan Mama daga ganin yadda Muzammil ya tafi rai 6ace nasan cewa tai bata son shi... "Eh bana son shi,koh ana son dole?.. Ja'afar d'in da kika rena ni shi ya min ki ji da wai.... "Kunga ku min a hankali,koh yanzun nan na sa6awa mutum... Shiru sukai,yayinda Salma taci ka tai dam. "Ke ummi wani dan wajen Malam Kabirun kike fad'a? Da harara Ummin ta k'allo Salma kan tai ma Mama bayani,"yanzu haka mama Malamin makaranta ne wallahi yana chan yana kokawa da alli.. Jim Maman tayi kamar mai tunani,chan ta nisa tace "Ikon Allah..anya yarinyar nan Salma ba'a min misanye dake ba a layin jarirai a haihuwa ba?... Mutum arziki na binshi yana ki?...Ina laifin yaran nan?har kasa suka gaida ni,ga mota ga boko..amma in banda abinki mey na sama yaci bare ya bawa na kasa? Da shagon uban zaku dogara koh da kud'in malami?..... Shiru Maman tayi ganin yadda Salman ke hawaye... "Au,au,Salma kuka? Daga fad'an gaskiyar? Kai ta k'ada ma Maman. "A ni tawa mai sauki ne Salma,ina d'ai hanga miki gaba ne kawai... Amma banga abin kuka.... "Wa ke kuka?... Assalamu Alaikum. Shiru sukai salman na goge ido,sai Mama da ta amsa mishi sallama. "Sannu da zuwa Abba. Kai ya daga musu kan ya amsa. D'uk suka tashi sim-sim sukai d'aki. Sai da Abban ya gama komai yasa Mama ta kira su. Kowa tai ladab kai kasa suna saurarar Abba. "Ni ke Ummi na ma kasa gane alkiblar da ki ka kama sam,kullum da wanda za'a ga yazo gunki,sai aukin shegen zance a titi ba wanda ya iya yazo ya samu iyayen ki.. "Ga nan yayarki yau d'in nan yaron nan na wajen Alhaji Kabiru yasa Baban shi yazo muka zanta kan yana son Salma da aure,kuma har sun sasanta da ita.. "Koh ba ai haka ba Salma?... Kai duk'e cike da kunya ta daga kai halamar anyi. "Haka shine musulunci, ta haka kuma ake gane da'ar yaron da zai auri y'arka... Shiru kake ji Ummi anyi lakwas. Nan ya kara ja ma Ummi k'unne kan tara samari da zancen waje,ya kuma ja mata k'unne kan ta fidda na aure koh ya fiddawa mutum. ***** *** Zancen aure dai ya kank'ama tsakanin Ya Ja'afar da Salma. Itama Ummi Isma'il yace da gaske yake.. Mat'sala d'aya tafi damun Salma,yadda komai Ja'afar ya bata na alheri a rene yake gun su Mama, barin Ummi. Dan ita fachaka isma'il yake mata kamar ba gobe. Tun abin bai damunta yau da gobe har ta fara ganin kamar Ja'afar mammako yake mata. Zuciya bata kashi. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 24 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 14_Anyi bikin su Garba. Ana haka saurayin Ummi ya d'allo mata wata sabuwar waya,ita kam tun wata Zain da ya bata,nan habaici ya karu gun Ummi. Biki ya kusa sukai shirin zuwa Borno dangin Abban su. Sunyi sallama da Ja'afar ta shigo gida rike da farar ambalan,d'uk suna zaune t'sakar gida har Aunty A'i da yaronta. Hannunta Ummi ta k'alla, kan cike da shakiyanci tace "ta Ja'afar mey aka samu ne haka har a farar takadda?.. Harara ta dan mata kan ta mikawa Mama. Kai Maman ta k'ada, kan tace "a rabani da kayan haushi,rike abinki kawai ki kirga... Dariya Ummi ta sa,wanda tuni ta kara kular da Salma. "Mama ba ma sai ta kirga ba,dan wallahi ba kaffara nasan kud'in nan bai fi dubu biyu ba... Kanta Salma ta yiwo a tunzure mama tai musu iyaka. "Meye na jin haushi?.. K'yautar tashi tana wuce nan ne?... Ba dai d'an d'an kasuwa zaki aura ba? K'wafa tai,kan tace "baki fara ganin komai ba ma Salma. Aunty A'i ce ta k'ar6a ta kirga,ai kam sabbin hamsin hamsin ne ta dubu biyu. Mama tace "Ahab,na sani ai. D'aki Salman tai tana hawaye,sam bata kaunar abinda ake ma Ja'afar,amma shima da laifin shi,dubu biyu ina zata kaita? ****************************** Biki kam yazo,gashi yau har anje jere, k'warai sunyi mamakin gidan Ja'afar da gina kuma da kanshi. D'uk da ba wani babba bane,dan koh t'sakar gidan karama ce,babban _parlour_ ne sai _bed room_ da band'aki aciki,ga _kitchen_ a ciki karami,sai d'aki d'aya daban a waje, d'ai d'ai zaman mutum d'aya de,rufin asiri dai ak'wai shi,Alli da shago sunyi rana. Sa6anin Ummi mai tafkeken gida da mai gate yasha alatu. Yanzu lefe ake wat'sa ido aga na Ja'afar, dan tuni na Ummi yazo san barka,sai zuzutawa ake. Salma in ta tuno gabanta har fad'uwa yake,fatan ta Ya Ja'afar ya fitar ta a magana. Dan tun a kud'in anko taga tasku,dan isma'il ankon k'yauta yai ma k'awayen Ummi da dubu ashirin nata na fitar biki. Shikam sai hakuri yake bata,kan shi bai d'aura ma kanshi abinda bazai iya ba,bare daga baya ya dame shi. Kawai sai ta toshe k'unnenta gun su mama,komai ta samu ta samu,wanda ta rasa tasan bai da hali. Mamaki kam Ja'afar ya bama su mama, dan ak'wati shidan nan y'ar yayi sai da aka bat'se ta da kaya, ga uban _cosmetics_ har a jakar Ghana must go. Aciki da swiss d'aya, holland biyu,engla biyu,sai su code dav'ior,sauran kam duk kana na ne su dangin material. Salma baki har k'unne jin ba wanda ya kushe a dangin sai d'ai ace na Ummi yafi t'sada. Anyi biki lafiya kowa ya wat'se an bar amare da halin su a gidan su. Kauna ziryarta taga gun Ja'afar mai t'sayawa a rai,sosai sukai amarcin su cikin kula da tarairayar juna,musamman ga Ja'afar d'in. _kitchen_ tare,wanki tare,shara tare,duk aiki in dai ba ya fita bane yana a makale da Salman sa, d'uk wata kulawa tana ganinta a gun Ja'afar,shi yasa sai abinda yace take aiwatarwa matukar bai sa6a Shari'a ba. Yadda ta fuskanta ma kamar bai kaunar tai nesa dashi,koh dan ganin har wata biyu kenan da bikinsu amma ba inda taje sai barkar Aunty A'i da makotansu da taje tun tana sati daya da zuwa. Sai dai tai ta jiyo shewar su ta katangar gidan halamar ana ta _chapter_. *Farin Bacin komai* Yau tun tashinta sallar asuba ta kasa komawa bacci,sakamakon tun dare da yace yau ta shirya da wuri zata gida. Dan farin ciki ji take kamar a wani garin zata je musu. Waya tai da Ummi kan zata fito yau gida. Gaban madubi take tana yi tana k'allon agogo har sha d'aya saura. Karar _machine_ d'in Ya Ja'afar taji a kofar gidan,sai ta cigaba da shiryawa. Sallamar shi taji,daga d'akin ta amsa tana fara'a. Yana shiga ya jingina da kofar d'akin yana mata murmushi,ta mudubin ta mishi tana d'auri. Kan ya tako gaban madubin ya t'saya ta bayanta. "Sannu da dawo wa.. Kai ya daga mata,sai kare mata k'allo yake, kayan sun mata k'yau, "Kinyi k'yau... Tashi tai da jin dad'in kalaman shi,sai ta dan ja mishi kumatu kan tace "na gode... Muje koh?.. Ta fara nad'a lifaya. Sai ya rike mata daya gefen tana nad'a dayan da murmushi. Da kanshi ya yafa mata akai ya rufe ko'ina ruf. "Ba dan kin nace sa abar nan ba da hijab d'inki za ki sa zai fi min k'wanciyar hankali.. Murmushi tayi kan ta lang'wa6e kai, "ai ba g'yale bane Ya Ja'afar, Allah ina son lifaya. Kai ya k'ada mata yana d'aukar mata jaka. "Toh naji,amma ni banga maraba ba. Murmushi kawai tai tana d'aukan mukulli. Machine d'in ya karkata mata kirar lifan,a hankali take ko'k'arin hawa sai ya dan girgiza machine din,da sauri k'wa ta dafa kafad'arshi suna dariya. In kagansu g'wanin k'yau suna ta nishad'i har suka zo gida. Tana g'yara lifaya tace "bazaka shiga ba?.. Kai ya girgiza mata da murmushi,"ki gaida su Mama, anjima in nazo d'aukan ki zan shiga, yanzun makaranta zan koma. Kai ta k'ada mishi,kan ta bashi hannu,sai ya bata suka gaisa suna dariya. "Abincin ka yana a kitchen a bisa faranti,na had'a komai, a dawo lafiya... Kai ya daga yana mata murmushi,jin yaki tafiya tace "kaje man.. Kafad'a ya make yana nuna mata gefen fuskanshi, kai ta k'ada mishi cikin kunya. "A layi muke fa... Shima sai ya kada kan tukun ya tada sukai sallama. Har ya kule tana daga mishi hannu,kan tai cikin gida. Da dan gudunta ta shiga tana kiran Mama. D'uk suna d'aki, Ummi an hakimce a kujera ana d'anna waya. "Har kun rigani ashe d'uk saurin nan nawa?.. K'allonta Ummi take ganin tana since lifaya,ga flasks da jaka an ajiye. "A ina zaki zo da wuri,ke dad'i miji ce ai.. Banza tai da ita tana gaida Mama, itama Maman a dan ciki ta amsa mata. D'uk sai taji ba dad'i, jikinta yai sanyi,da murnar ta tazo amma sun dakushe mata. "Sai ya barki ki waiwayo mu?.. Maman ta k'alla, kan tai kasa da kai, "ai na zata irin ta y'an da zai miki,sai kin shekara koh kin fito yawan arba'in.... Baki Ummi ta ta6e,kan tace "d'uk mai irin halin Ja'afar ai dole yai k'ulle Mama,in banda haka wata biyu wai sai yau za kizo gidan ku,ni nazo yafi a girga,wallahi tun wuri ki mawa tufkar hanci.. Dan in kika sabar mishi da haka zai mike. Dagowa tai da niyar yi wa Ummi magana Mama ta tari numfashinta. "Y'ar uwar ki ce,dole ta fad'a miki gaskiya, ke zaki nema mana mutunci a gun miji ki ma ji da k'yau. Kasa tai da kai tana murmushi, duk da a zuciyarta bataji dad'i ba sam. "Mama baza'a a sake ba inshaAllah. Da haka aka ware kuma zancen nawa ta tara a banki. "Ni fa ba'a ban kud'in cefane Mama, komai yana kawo min har katin waya,sai dai in ina da bukata yana cewa na mai magana... Baki Ummin ta ta6e,kan ta zuge jaka, sai ga nan kud'i tumi. "Kinga kud'in cefane na,nima ai ba abinda na rasa,ina ruwana da wani ni kud'in kati? Kawai naji dumus ni... Gashi nan na banki ne dana sa Mama ta sai min. Kai Maman ta k'ada, tabbas Ummi tasan ta kan maza,shi yasa take burgeta sosai. Itade Salma an sata duhu,dan sun raba hankalinta biyu. T'saka mai wuya kenan. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:00 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 15_Sai dare yazo a dalilin yadda take fad'in bata gama ba,har cikin gidan ya shiga,kawai kuma sai yake ma Mama k'warjini, dan fuska sake ta amsa mishi,kan suka tattara suka tafi. Koh da Salma tazo k'wanciya maganganun su Ummi take ta tunawa. Ita babban haushinta ma yadda aka fa fad'in koh tsoron Ja'afar take. Washegari ma haka ya yakaita gidan su Abban shi,nan ya wuni suka biya gidan Garba. Yau tun (7:30) ya fita, sakamakon an fara jarabawa a makarantu. Sha d'aya ta gama aiki ta fara jiyo hayaniyar y'an unguwa a makotanta,halamun sun hallara za'a fara chapter. D'uk yau sai hankalinta yai gidan,duk da ba sabawa tai dasu ba. Waya ta d'auka,ta d'anna kiran Ja'afar _no answer_.. Ji take kamar ta zaga in ya dawo ta fad'a mishi,sai dai ta daure. Da yamma kam kamar kullum yazo fita shago tace zata leka makota. Jim yai ba amsa,sam tarbiyar matan unguwar bata mishi ba,baya so Salma tai sabo dasu a samu mishkila,amma kawai sai ya k'ada mata kai, "Sai kin dawo. Cike da murna ta rakoshi har bak'in kofa ta koma d'aki. Da sallamarta ta shiga,tun daga bak'in kofar gidan zaka fara jiyo karad'in matan. Da fara'ar su suka amsa,d'uk sun baje a tabarma, wasu ba koh dank'wali. A dan kunyace ta gaida su, dan ganin duk sun girme ta,sai wata mai kamar shekarunta da D'a a goye. Chan hira taci gaba, zabiyar ciki sai karanta musu makamin kama wuyan maza take. Salma tai shiru tana jin su,tabbas babban burinta shine Ja'afar ya so ta har karshen rayuwa. "Su amarya yanzu ai farin take gani kan a juya mata bak'in bayan.. K'allo matar tai,bata gane nufinta ba,sai dai bazata iya tambaya ba. Haka firar yau ta tashi kan makamin rike miji har Salma ta fito. Tunda ta zauna a gida take tariyo firar sun. Tabbas shawarar nan tayi ta makamin rike miji, ta hakan kam ba yadda Ja'afar zaiyi ya raina ta... Toh amma Ja'afar yana sonta,batajin zai mata dabi'a irinta mazajen sauran Matan da ke fad'i. Nan ta jefar da dayawa a hudubar da taji a makota tai kitchen dan k'unna ritio. Sai d'ai Washegari ma da yamma Salma ta sake tambayar shiga makota. Karan nan kam kir ya fito yace mata a'a, da ido kawai take binshi, "Ya Ja'afar yafi zaman kad'aici ne,ba jimawa zanyi ba ka ji... Ta langwa6e kai. Ba dan yaso ba ya k'ada mata kai. Minti biyar bata kara ba tai makota,gidan chapter. Yau kam a sa'a taje,dan suna a kan firar rashin fitar matar gidan,sai bata dabaru suke akan yadda zatai mijn ya rika barinta fita. "Kar ki fara tambayar unguwa kina fara'a, sosai zaki dake mishi,mud'in yaga 6acin rai toh jiki na bari zai barki. Ni da farko haka Salisu ya t'siro min da k'ulle,tun farko nai ma tufkar hanci,da yace A'a yana fita zan arce, gashi yanzu har ya saduda yana barina duk inda na tambaya. T'sam Salma tai,tana tariyo maganar Ummi da Mama ta ranar,ga nan ta makotanta. Daga ganinsu sun san takan duniya. Tabbas ta yarda itace tun yana d'anye ake tank'wara shi. Tun yanzu ya dace ta takawa Ja'afar birki koh dan ta t'sira daga zargin wai tana tsoron shi. *Wasa farin Girki.* Daga ranar Salma ta tsiri dan hali,fita makota,tambayar fita gida,ga wani t'sarewa da take in tana tambayar. Kamar kullum tazo rakiya taja ta t'saya a gefe, "Ya Ja'afar... Jiyo wa yai shima rai ba dad'i,tare da zuba mata ido,yasan abu daya zata tambaya. "Zan leka gidan Maman Ummi gobe suna za ai k'ulli... K'allonta kawai yake, yadda tasha mur tamkar wanda take bashi umarni. "Anya Salma wani abu bai shiga kanta ba kuwa?.. Gaba daya ta sauya mishi hali k'wana biyu in dai akan fita ne.. G'wara tun wuri ya taka mata burki dan yaki jinin yawan fita sam shi. "Kiyi hakuri Salma,ki bari ki leka goben tunda suna ne... Tuni ta k'ank'ance ido, "gaskiya kar ka maidani saniyar ware a unguwa ya Ja'afar, yau k'ulli kowa ya je sai ni ce bazani ba?.. Ai sai a chake ni gobe dama suna fad'in ni dad'i miji... "Kuma ma ba wannan ba,nima sai ina zuwa za'a zo min in nawa yazo ai.... Shiru tai ganin yadda ya zuba mata ido yana kallo, chan ya nisa "amma Salma kin fuskanci kin fara sauya hali kuwa?... Kin koyi ja dani,kin koyi gantali k'arfi da yaji.. K'alloshi tai a wani iri, "au gantali ma nake Ya Ja'afar?.. Fisabilillahi wace fita ce nake yi ba dalili? A satin nan sau biyu koh uku ne fa na fita kuma dubiyar Ummi ne ba wani waje ba, koh shi ka ke nufi da gantalin? Kai ya k'ada,"kar mu rika ja in ja dake Salma,kiyi hakuri kawai gobe ki je... Juyawa yai ganin tana neman wata maganar yai waje, baki ta ta6e,kan tai cikin d'aki. Tana jin tashin machine d'inshi ta zaro hijabi ta k'ulle gida tai cikin gidan k'ulli. "Ai na zata bazaki zo ba,da har zanyi aike naga machine din maigidan. Hijab ta cire ta jawo jarka, "bari ke dai Maman Ummi,dak'yar na fito fa.. Murmushi tai kan ta d'akko wani abu a bakar leda,"yanzu saratu ta fita an kawo sabbin kaya dakakku wallahi,tai ta jira baki zo ba zata tafi na dau miki wannan... K'ar6a tai tana dubenshi kan ta kunce ledar,roba ce karama da wani abu mai d'anko. "Takalmin Kaza ake fad'a miki,nasan yafi haka,kawai ta mana sauki ne.. Amma abin ba magana,sai an g'wada akan san na k'warai... Dariya suka sa aka tafa harda shewa. "Wannan ne kawai makamin wulakancin D'a namiji,tunda kuka d'aurani kan _network_ nake son raina Allah. "Dari biyu ai ma yai araha... Bari yazo dari biyar zan tat'sa, dan asusu nake kan zuwa watan haihuwar Ummi na tara da yawa... Sai da aka gama k'ulli ana firar duniya,a debo gulma har aka gama,ana kiran magriba ta tuna Ja'afar, da sauri-sauri tai gida dan yau abinci ta zarce tayi. Kamar kullum ya dawo bayan magriba ana kiran isha'i, sai dai sam ranshi ba dad'i,nan tasha jinin jikinta,koh ya dawo bata gida ne? Har yaje masallaci akai isha'i bai dawo ba har ta gaji da jiranshi ta k'unna inji. Sai chan kusan tara ya shigo,har yanzu jiya iyau,sam kuma sai taji ba dad'i, tun kan ya fad'i lefin da tayi,amma de sai ta dake. Komai yayi,dan har abinci ya ci,sai dai fur yaki sakar mata. "Wai Ya Ja'afar mey nai ne ka ke ta shan kanshi?.. K'allonta yake da mamakin anya Salman shi ce wannan?.. Bai da amsa,sai a gunta kawai,saboda haka ya tashi yai hanyar d'aki. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:03 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 16-Ya fito a band'aki ya ganta zaune a gad'o,kai ya dauke yana goge jiki da _towel_,d'uk sai jikinta yai sanyi,tabbas tasan Ja'afar kila zuciya yayi,har ya gama shirin bacci uffan bai ce mata ba,tuni ta fara kuluwa ganin ya ja filo bai bi takanta ba. "Wai mey in ma ina ta maka magana tun dazun?.. Kai ya dago ya k'alleta da tuhuma, "mey kika ce ban amsa miki ba?... Baki ta turo gaba kad'an, kai ya kada,tukun yace "Salma!... Salma!!.. Dagowa tai ta bashi hankalinta dan jin kiran da yawa. "Na'am.. Ido ya tsura mata,sai tai gefe da nata. "Ina kika fita dazu har magriba?.. Jin tambayar tai ta bazata,hakan yasa ta kasa K'allonshi, sai da ya maimaita tukun ta amsa a hankali da "gidan k'ulli... "Gidan k'ulli?.. Mey mukai dake toh kan na fita?... Duk t'siya ta ki jinin kuma taga ran Ja'afar ya 6aci, sai dai an rinjayi zuciyarta. "Kai hakuri... Itace Kalmar da ta fad'i. Tashi yai ya jingina da pillow,kan cikin nut'suwa ya fara mata magana. "Ba wannan ne ba karon farko da ki ke fita ba'a son raina ba Salma,nasha aiko yaro da sako yace gida a k'ulle yake,amma nai ta daga miki kafa. Duk gantalin da take bada yardar shi ba sai da ya sanarta,ga t'sinuwar mala'iku dake binta har ta dawo... "Sam wannan ba Salman da nasani a wata 5 d'in baya ba... Wannan cikin wata d'aya ta sauya,bata jin magana ta,duk abinda tasa kanta take ganin shine d'ai dai shi take... Sosai ya kasheta da kalamai,har ta fara hawayen wai bata jin magana. Murmushi yai kawai,kan ya dan taso ya janyo ta ya hau kuma lallashi,da alkawarin bazata kara ba,sosai ya ji dad'i,dan yana son mutum mai gane kuskure in ya yi. Washegari _week end_suna ma haka tai shiru,sai dai kasan ranta ji take kamar tai filfilwa taje gidan. Tasan iyanzu an kusa sauke abinci ana ta cin chapter ba ita. Sai dai tai ko'k'arin ganin bata tambaya ba. Shi kuma ganin haka yasa yaji dad'i,fatanshi yasa Salma ta g'yara ne. Ce mata yai yana zuwa,yana fita ta kasa zaune ta kasa t'saye. Anya bazata leka ba kan ya dawo?.. Dan tasan yanzu ana chan an kafa da ita uwar son miji. Sau biyu tana k'wata fita tana dawo wa,a na ukun taji dirin machine d'in Ja'afar ta koma. Sai gashi da leda baka a hannu. Sannu da zuwa ta mishi,burinta ya fita ta fice, amma fur yaki. A jima kadan ta k'alli agogo,kafarta har kaikayi take,da ya k'allota ta sai ta sau mai murmushin dole. Kamar ya kula sai yace bari yai wanka,yau sha biyu yake son yaje shago. Ita dai ta samu ya fice,Allah koh satar hanya sai taje gidan sunan Maman Abba. Toh sai ma ya barta harda mika mata ledar riga ta barka. Abu kamar gaske Salma kamar anyi hankali, sai hali ya dawo sabo. Shiga makota kam Ja'afar har yai hakuri ya zuba ma Salma ido, Gashi yanzu su Salma har ketare ana t'sallakawa,kusan duk yanzu unguwar sun san da Salma,ga surutu da t'sabar manyance da ta koya zama cikin manya. Ranar Garba suka zo gidan a 6ame da mukull,sai ya d'au waya ya kira Ja'afar din. "Ba kowa fa a gidan nan Aboki,dan da mukulli a 6ame.. Daga chan Ja'afar yai t'sam, kan yace "oh,sorry pls,na manta tace zata je dubiya, ga wayanta ba chargy... Kai Garban ya kada "toh dai mun fita,dama ita ke mitar madam shiru,yanzu kam ma had'u suna. Murmushin dole ya k'akalo,yana cewa ace Billy tai hakuri. Bayan sun gama ya ajiye waya,Salma tasa ya tafka karya,dan da abin kunya ace yana mai gida amma bai san matar gida bata nan ba... Toh mey zai wa Salma ne?.. Ya mata d'ukkan nasiha,yayi fad'a, yai lallami,amma tamkar a iska yake zubawa. Sai tayi kamar ta d'aina, gobe ta fidda sabon hali. "Assalam Alaikum... Kai ya dago,ganin mey sallama yasa ya fad'ada murmushin shi, cikin girmamawa yace "a Abba,sannu, yana sunne kai, murmushi Abban yayi,kan yace ''yauwa Ja'afar,ka ga na dawo,zan dan zaga ne, baya,dayan shagon nan ba kowa ne, nazo arar Sadi minti biyu.. Kai kasa yace "Bari na zauna kan ka dawo nan bana komai. Yasan zai samu ma damar yau amar da abin da ke ranshi. Yana shagon Baban ya k'wance ya d'aure, ya fad'a ya je gida ya shiga uku gun Salma.. Shawara d'aya ya yanke, gun Mama, dan yaga ita batta zafin Baban. Tun yamma ya tashi,bayan sun gaisa da Maman faran faran yake sanarta halin da Salma ta t'suro mishi. Kamar abin kirki harda bashi hakuri,da fad'in zata t'sawatar mata. Sai d'ai tana fita Ummi da tun shigowarshi tai zamanta a d'aki ta fito. "Kai amma mama mutumin dan rainin hankali ne,wai kinji fitar Salma tai yawa? Matar da sai tai sati biyu wataran ba tazo gidan nan bama bare har fitar ta tai yawa.... K'wafa Maman tai,kan tace "ke lefin shi ki ka ga?.. Ai lefi na gun Salma da ta zauna yake juyata kamar waina... A zamanin y'ancin kai ake yanzu, bana tsawalawa dana.. Kaza kaza,har Abba ya shigo zaure ya dan t'sinci wani zancen,amma bai gane kanshi ba. Kullum Ja'afar na sa ran yaga Salma ta sauya,sai dai shiru,sai yai tunanin fad'an Maman ma bai shige ta ba. Ranar Garba yace a gidanshi zai magriba yace Salma tai musu irin gurasar nan tun tana amarya. A gabanshi ya kirata, a lokacin an zube ana ta firar kashe wando a makota bayan layinsu, Koh da ta sauke waya ta cigaba hirarta. Chan kusan magriba ta kusa ta tuna da zancen Ja'afar,kusan ma d'uk y'an firar an wat'se amma Salma matar gida ta riketa wai suna firar su zata tafi? Yaron gidan tasa yai gudu bayan layinsu ya siyo mata gurasa mai siga ta karbi kud'i gun matar gidan. Cikin nishad'i suka zo sai dai gida a 6ame,ga yau ta bar mukullin shi a ciki. Ranshi in yayi dubu ya 6aci,basu jima ba sai gata tanan,duk tabi ta burkice, duk da koh k'allon inda take Ja'afar bai ba. Sai da Garba take magana tana ko'k'arin bude gida. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 17_Shi dai Garba har suka shiga gida yana zungurar abokinshi kan ya saki fuska. D'aki ta shiga tana mai adu'ar Allah yasa a samu gurasar nan,in ba haka ba yau ta kad'e har ganyenta a gun Ja'afar. Suna t'sakar gida suna alwalar magriba sai ga yaro yai sallama rike da k'wano,da sauri ta fito ta amsa,har ta shiga Ja'afar na bin bayanta da ido,k'wafa yai kamin yai ciki, shi dai Garba duk ya gane da wata a kasa. Kitchen ta sameta tana jera su a faranti. Tasan shine amma fur taki daga ido ta k'alleshi. "Nagode Salma, kinji? Na gode,amma ba zanci gurasar titi ba ki sani... Kofar kitchen din ya rufo sukai waje. Ita kam koh a jikinta,tunda de ta t'sallake fad'a ai shikenan. Yau dai ya kasa d'aurewa, har sai da ya sanar da Garba halin Salma ba ragi. Sosai yai mamaki,wai Salma ce da halin nan? Sai dai kawai ya bawa abokinshi hakuri, da kuma ya rage saurin fushi... Haka ya wuce gida ba tare da shima yaci ba. Da dare ya d'au pillown shi ya koma parlour,baki ta ta6e tai k'wanciyar ta. Sai dai koh minti ashirin ba ai ba ta hau juyi,ta ture pillow,dan Allah yaga bata saba k'wanciya ba'a hakarkarin Ja'afar ba,duk fad'a kuwa. Ba shiri tazo bada hakuri dan tasan ya bala'in jin haushi. Shi kuma haushin shi d'aya da hakurin Salma,tunda ba wai zata g'yara bane. Kuka ta fara mishi harda shura kafa kan wai ya juya mata baya yaki kulata. Juyo wa yai yana k'allonta, duk da a kule yake da ita amma har kusan dariya yaso saka. "Ba nace kai hakuri ba,Allah kasan ban ta6a kin yi maka abinci ba da gangan... Tashi yai ya zauna a kusa da ita. "Toh naji na hakura,bar borin...ya sa hannu zai goge mata hawaye sai dai kamas... "Au kukan ma na karya ne ashe?... Dariya ta fara ta d'au mishi pillow sukai d'aki. "Ina a gidan nan Allah ba kai ba k'wanan parlour. Murmushi yai yana mai tausayin kanshi, ina ma Salman shi ta da ta dawo mishi... Ina ma zai yuwu ace kullum yaso ganin Salma zai sameta a gida haka?... Ya sani da yana son Salma,so ba na wasa ba,amma k'arfi da yaji so take tafi k'arfin shi,ga ko kadan bai kaunar yaga fushin ta. Ina ma itama haka take nannan da nasa fushin... Yasani da *Mai Hali Baya fasawa* **************************** Sauri take tayi,dan yau gidan mai gumama suka je,tasan kuma tabbas Ja'afar yana hanya. Aikwa tana zuwa ga nan machine d'inshi a kofa halamun yana ciki. Duk da tana jin dan shayin shiga su ar'ba, haka ta d'aure ta shiga. Takaddu yake nema, da sallama ta shiga, a chan ciki ya amsa yana cigaba da abinda yake. "Sannu da zuwa... "Uhmm.. Kawai yace, sai ta ta6e baki. "Gidan fa mai gumamar nan da na fad'a ma jiya ta aiko mana za'a kawo muka je..kaga zuwan banza mukai ma wai sai gobe. A dirare ya k'alleta lokacin da yake tashi, ganin yai banza yasa tace "ni fa nan kad'ai naje,sai gidan Maman Ummi dana biya mata muka tafi.. Kai ya k'ada, kan yace "yayi k'yau... Maman Ummin ce mijin ki koh mai gumamar?... Ido ta zaro,sai ya kada kai, "no ba wannan ba ma, wai d'uk inda kike azarbabin zuwan nan wa kike gani yana zuwa gidan ki yafi minti goma aciki?... Koh d'uk

Chapter 3 of 11