Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yace tana nan ta fito,wai sai had'a rai yake,shi yasa ta bar mishi gidan, nan ta daura kan na Maman Ummi, Zuwa chan Maman ummin tace "Kiyi kok'ari hudu ki biyo min zuwa 5 dawo. Da wannan suka baje har ta wuce ka'idar Ja'afar. *Washegari*. "Wai dan Allah Salma na tambaye ki zaki ban amsa? Y'atsine fuska tai kan tace "ina ji.. "Shin dad'i ki ke ji in kin t'saya muna musayarya magana dake?.. "Mey yasa in na ce ki bar abu sai dai nai son ranki,amma ni ban isa ba? "Ita maijegon ta ta6a tako kafarta cikin gidan nan da sunan tazo gunki?.. Ki ban amsa? Baki ta saka,kan tace "oho,kana nufin gyaiyar sod'i zani kenan?.. Tunda ga areni muje biki koh?.. Kai ya kada, "Ke ki ka kira kanki haka,ba Ja'afar ba,abu daya na sani,ko na fita ba jimawa zanyi ba, saboda in ma kin fita,toh kisan inda dare ya miki... "Mey ka ke nufi? Kana nufin yau ma zaka ce a bakin auren nawa Ja'afar?.. Da sauri ya kada kai, "K'warai,tunda abinki naga na yanzu har so yake yafi na da, in har kam kin fitan,toh kisani,kin fita *A BAKIN AURENKI*... Sai ki zabi wanda ya fi miki, aure? Koh gidan suna?... Kofar ya bugo mata yai waje tare da barinta baki sake. "Eh lalle yau zan nuna ma tabbas ba tsoron ka nake ba Ja'afar... Wannan kurin bakin wallahi bazai hanani fita sunan ba,daga yau kalmar nan ta *A BAKIN AURENKI* tabar bakinka. Daki tai tana balbalin masifa ita kadai kamar yana k'allonta. Kaya ta fito dasu tana duba wanda zata sa, _lace_ din sunan Ummi ta dakko wani karamin _swiss_ da aka sashi siyanshi dan dole. Sunan na manya ne, dan haka sai da kure adaka. Ba koh shakku ta fice, yau tun dazu taji gidan su Maman Ummi t'sit kamar ruwa ya shanye su,halamar mai gidan yana nan kenan,amma tunda ta fara jiyo hayaniya tasan yai waje. Gidan suna kam ya kayatu, sun samu abinda ake so tuni aka baje a faranti ana ci ana kora wa gulmar wata. Kan ta farga har 5 da yan mintina. Haka kawai taji gabanta na fad'uwa hankalinta yayi gida. Tashi tai ana fad'in ta t'saya k'ulli ya kare a k'ulla mata tana a bawa Maman Ummi. Sauri take ta zubawa, dan da y'ar tazara a t'sakanin su. Adu'ar ta daya,Allah sa Ja'afar bai dawo ganin koh ta fitan ba. Ta rasa dalilin da ya sa hankalinta ya tashi,bayan ita ta zabi hakan. Lekawar da zatai shine taci ka'ro da Ja'afar suka had'a ido. *WAIWAYE*... *************** ************** Haka yai ta juyi har kusan k'arfe biyu. Washegari haka ta tashi sukuku, ga fargabar Abba yau zai dawo,ga wani mugun mak'on Ja'afar da yake taso mata. Kai in ma ba wai bata kula bane gani take zazzabi ne a jikinta. "Salma... Dagowa tayi ganin mama a kofa,da mamaki fal fuska ta karaso ciki. "Wai har yau kukan nan ki ke Salma?.. Mey yaron nan yai miki ne haka?.. Hannu ta kai kan fuskrta,sam ba tasan tana kuka ba, da sauri ta goge tana k'ak'alo murmushin dole. "Mama ina k'wana.. Kai kawai ta kada mata. "Haba Salma,kar fa ki rako mata duniyar nan...kar ki zamo mace mai kulafucin D'a namiji duk k'wa wulakancin da ya mata man... Ashe ni ina chan jiya nai baccin farin ciki da aka rabu lafiya ba rabo bare ya kawo cikas a zawarci ashe ke kina nan kina kukan an rabu? Haba Salma, karan nan ne fa ki ke da dama ta biyu,tunda har ya sallame ki. "Maza goge hawayenki ki biyoni daki yanzu. Kai ta kada,a gaskiya ta fara mamakin irin kiyayyar dasu mama suke ma Ja'afar, wato har ma godiya ake ta rabu da alakakai?... Allah yaga tafi jin haushin kanta sama da haushin Ja'afar, in ma taji haushin shi toh bai wuce yadda ya k'ulle mata gida ya kuma tafi koh ajikinshi. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 22_"Toh wa ya jawo?... T'sam tai yayin da zuciya ta tambaye ta, "Ni ce... Tabbas ni najawo, amma ba laifi na bane. Kuka ta fashe dashi,tabbas anci k'arfinta,ta ko'ina an mata dabaibayi da huduba gur6atacciya. "Gashi na jawo wa kaina saki biyu ba tare da na samo kan ba(kan Ja'afar).. "Oh ni Salma.. Ina tunani na yake da har na aikata wannan wautar?.. Ina son da nake ikirarin ina ma Ja'afar?.. Ina ya je... "Salma... Mama ce ta kat'se mata tunanin gaskiya da kira. Hannu tasa ta share hawayen ta,ta daga kai tare da fitar da iska dan daidaita nut'suwar ta. "Na'am.. Ta amsa kan ta tashi tai waje. "Gani mama, Kan gado ta nuna mata kan tazo ta zauna. Ba musu ta karaso. Kafad'arta ta dafa kan ta numfasa, "Kina ji koh Salma? Kai ta daga mata. "Baban ki yau nasan zai dawo,tabbas ya rit'saki nasan zai cid'a ki ne a banza. "Yanzu abinda nake so kiyi shine,ki je gidan A'i,dan mijinta baya gari ya tafi sari,ki barni in na gama lalla6a shi sai ki dawo,dan karan nan kam sai dai ai wacce za ayi, amma aure kin gama... G'wara a chanja hannu,tunda wannan d'in ba fus, bare ass,sai dan banzan dacin rai ba koh gidan kai... Hawaye ne ya zubo mata,ba da ban suna matukar kama da Mama ba,da tayi shakkun akan haihuwar ta... Mama na da kamasho a ta6ar6arewar aurenta kashi 70 acikin dari... Tabbas uwa uwa ce, amma su kam tasu uwar sai g'yaran Allah.. "Au,au,kuka ki ke? Dan nace baida gidan kanshi?.. Koh shi ya siya ya gina da gumin ajin?.. Yarinya ki duba yadda ake harka,y'an uwanki na shiga ta alfarma amma ke kin zama y'ar k'allo.. Ki farka a bacci Salma,dan rayuwar nan ta zo mu fafata ce. Kai ta k'ada tana goge ido,sai ta mike tai hanyar waje, "Bari na shirya zuwa gidan Aunty A'in, naga 10 tayi. Kai Maman ta daga harda washe baki, "Yauwa,ko ke fa.. Maza aje a shirya,ga nan abincinki a kitchen. Kai ta k'ada kan tai waje, da kallo Maman ta bita, ba abinda y'arta ya gaza a gareta,wa ma zai ce ta ta6a aure in ta fito da ita gari?.. Dole kud'in da ba taci ba da yanzu taci gun Salma. *************** ************** A k'wance take kan _3sittern_ Aunty A'i,in banda ciwan kai ba abinda take, "Tashi ga maganin kisha... Kai ta dago,Aunty A'i rike da kofi da _paracetamol_. Bayan tasha ta g'yara zama,d'uk gidan bata jin da wanda bai ta6a kushe mata Ja'afar ba sai Abba da Aunty A'i. Hawaye ne ya zubo mata,kan kai duk'e tace "ban san mey Ya Ja'afar ya t'sarewa su Mama ba da sam basa kaunarshi... Yanzu ki duba Aunty A'i Mama yau tace murna take an sake ni.. Harda fad'in g'wara da bamu samu rabo ba... Kuka ne yaci k'arfinta,tuni ta hau yi ba kakkautawa. Taso wa Aunty A'in tayi zuwa kusa da ita ta hau lallashi,chan ta numfasa itama harda hawaye ta fara fad'in "Kinyi wauta Salma matuka,samun irin Ja'afar a yanzu wallahi sai kin tona,irin halin da kika dinga karta mishi duk na samu gun Abba,kinsan nima ba wai Mama nayi dani bane sosai,dan ban fiya shiga irin shirgin nan ba. "A gantali har gida sukutum ki ka kona mishi Salma.. Naji ance ya kuma shiga cikin y'an _missed call_..Bana tunanin har yau ya gama tattare takaddun da ya rasa kuma duk a dalilinki fa,amma dai dai da rana daya bai ta6a hanaki ci koh sha ba?.. Duk da baki san ta ina yake samu ba. "Maimakon ki zama mace ta gari mai k'wantar mishi da hankali har ya manta bakin cikin da yake ciki na rasa aikinshi,a'a sai ma kara hura mishi wutar masifa ki ke a gida. "Salma kina da ilimi fa,kinsan d'ukkan hukunci a game da matar da take sa6a umarnin mijinta, bare ke da kusan kullum cikin shi kike?.. Ina ki ka bar islamiyar taki Salma?.. Da har kika bari rudin su Ummi da chan wasu jahilan makotan suke hure miki k'unne,wanda in zaki titsiye su ba mai iya rashin mutuncin da ki ke Salma.. "Nayi imani zaman cikin gidan ki ya fiye miki alkairi sama da zaga makota yawan gulma da ki ke.. "Ya sanar ni shi sai a shafe wata nawa,baiga makotan naki na zirya gidan ki ba sai dai aiken bani taliya bani mai, shin sun fiki sanin ciwan kansu ne Salma? "K'wanaki haka har gida na samu yana fad'a kina fad'a, amma dana shiga nai miki fad'a, sai kika nunan wai maza sai da wuta.. "Kan kiyi aure Salma ni nayi da shekara hudu, ba zaki fad'an halin maza ba,amma a lokacin na biki da murmushi ne kawai. "Ki dube ni nan Salma... Dago tai ido jajir hawaye na zuba. "Wallahi tunda nake akan fita unguwa ban ta6a sa'inasa da Abban Aslam ba,kar kara in naja,ya ja,hakura nake na barshi,wani sa'in sai kiga har ya fita,amma sai ya dawo yace in shirya ya sauke ni,ina fara'a za'a gama komai ba bacin rai, duk wanda zai fad'a miki ana tank'wasa namiji ta fad'a da bala'i wallahi karya yake miki,sai dai ma kullum yai ta baud'e ga uwa uba sane mishi da ki ke. "Zuciya nason d'ukkan mai k'yautata mata Salma,sannan a kullum tana kara nisa ga wanda ke munana mata... Ki gane wannan, tunda dama taki,shine ya koma miki ta hagu, ki fita a bakin aurenki Salma, tun da kuruciyar ki wai har kin zama bazawarar k'arfi da yaji? Ranar da kanshi Ja'afar din yazo gidan nan,akan irin yadda ba k'ya jin maganarshi,nai mishi alkawarin zanje har gida na miki fad'a sai gashi Allah ya kawo wannan. Sosai tai mamakin Aunty A'i,da yau ta zauna fed'e mata biri har wut'siya.. Tai imani duk maganganunta ba wanda ba ita ke da laifi ba tabbas. Wata muguwar nadama ce ta sakko mata,kuka kam ba kama hannun yaro, har sai da taji ba dad'i. Bataki koh yanzu ta nemi gafarar Ja'afar ba kan ya maidata aurenshi,tai alkawarin d'auwama acikin dakinta har sai yace Salma fito. Aiya Salma, Ja'afar baya tataki,yanzu ta Bintu yake.. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 23_Zazzabi harda amai take,duk zatan Aunty A'i akan kukan da taki dainawa ne. Washegari ba zato ba t'sammani Aunty A'i ta t'sinkayi sallamar Abba a t'sakar gida. Lokacin dawowarta daga band'aki kenan ta gama zuba ma Salma ruwa a amai na tun jiya da yaki t'sayawa,sai dai tana jin Abba ne ta mike tare da yin waje da sauri. Hannu Aunty A'i ta d'aura aka,ganin zabga- zabgan bulalin da Abban ya shigo dasu gidan, fad'i yake "Ina take Aisha?.. Tuni idonta ya raina fata,fatan ta Salma taji ta buya. Cikin in'ina tace "Abba wa d'in?.. Hannu daya marar bulala ya nunota dashi, "Kinci gidan ku... "Bani hanya na wuce,yau mai rabani da Salma sai Allah a gidan nan.. Da k'arfi Aunty A'i tace ta gudu,hayaniyar ce ta fiddota a band'aki ta had'a uban zufa dan azabar amai, har bata danji sosai, lekawa tai ta labule jin an ambaci sunanta... Ido waje ta koma da baya tana neman ma6oya,tuni ta ware tai bayan kujera tana rufe baki da duk hannunta biyu jin Abba a parlourn. "Dan Allah Abba kai hakuri,wallahi bata da l... "Aisha,koh ki fito min da ita koh bulalinnan su kare a kanki... Ido Salma ta rint'se da sauri,kirjinta sai d'ukan tara tara yake. Sai dai mey? Kamshi turaren kayan Abba ne ta busu hancinta,take taji amai ya taho tai kokarin ta mat'se sai dai ta kasa,tuni k'ak'arin aman ya taho sai dai ciki ba komai. Bata zata ba sai jin magiyar Aunty A'i tai tana dan Allah yai hakuri... K'wak'waran mot'si batai ba taji saukar bulali tai ajiki ta ko'ina. Ihu take da iya guntun k'arfin daya rage mata tana Abba zan mutu, ina,kawai lafta mata yake,da Aunty A'i ta rike sai ya cika ya hau zuba mata wata. Makogaro ba ruwa,duk ya tafi a amai,tuni har muryarta ta dashe,sai k'ak'arin amai da take. Kamar an hullo mama sai ganinta sukai a kid'ime,ganin yadda yake jibgar Salman ta bala'in tsorata, da sauri tai waje dan kara kiran yayanshi Ganin Abba zai kisa,yasa da sauri Aunty A'i tai ma Salman rumfa tana yai hakuri cikin kuka,ganan Salma koh k'wakkaran mot'si batai,bai bi takanta ba ya hau zuba musu tare, "Abba ciki ne da ita,wallahi zai zube.... Chak ya t'saya da bulala a hannu sai zufa yake, yai dai dai da shigar Mama tai katari da zancen Aunty A'in. Bulala ya yarda yana haki,tamkar yasa kuka dan bakin ciki,tunda yake basshi da fadanshi amma bai ta6a sa hannu ya dakesu ba sai akan Salma,wannan shine karo na biyu gareta. So take tafi k'arfin kowa a ganin shi,toh shi bazata fi karfinshi ba. "Ba mai fin karfina a gidana ban maganin shi ba... Yau kin t'sira a dalilin zancen A'i,da na lahira ya fiki jin dad'i.. Duk da laifin nafi daura ma uwarku data zuba ido kuna abinda kuke so... "Mun shiga uku... Da sauri Maman tai kan Aunty A'i mai magana. Jijjiga salman take tana kira. "Salma!... Salma!!.. Mama bata mot'si wallahi... Tuni suka hau jijjigata Aunty A'i na kuka. "Shikenan Malam ka kashe min Y'a ka huta... Babu yadda banyi da kai ba akan kai hakuri kar kazo,kar kaje,ga nan irinta ka... "Ki rufe mana baki, koma meye ke kika jawo, ruwan k'anin Aslam ya gani a jarka da sauri kuma ya dakko wai su mat'sa agun,ido duk hawaye suka mat'sa. A hankali ya dagota tare da yayyafa mata, a hankali ta kawo numfashi sai dai ido a rufe. "K'unnen k'ashi gare ki ne Salma,shi yasa baza mu shirya ba sam sai kin g'yara hali. Kuka ta fara kad'an kadan lokacin da suke dagata, sosai ta lillisu,duk jiki ciwo. Wayar Aunty A'i,da Ja'afar suke magana wai yaji Abban su yace Mama ta bugo kan Abba zai kashe Salma... Cikin kuka tace "Kazo gidana suna nan. Duk ya kuma kid'ime, tabbas ba d'ukkan wasa yasan Abba yake ma Salma ba,tunda Aunty A'i take kuka. Garba ya kalla,"dan Allah kaini gidan Aisha yayar Salma. Da mamaki yake K'allonshi, "amma dai kasan yanzu _chairman_ zai zo yama signing koh?.. "In bazaka kaini ba na fita na hau abin hawa. Kafad'a ya daga, "a muje, ni meye nawa. Mijin Aunty A'in ya kira koh yana gidan,yace su shiga kawai,Abba ya sanarshi komai tun dazun. Abba ya fita lokacin da suka zo,mama ta tafi nemo abin hawa. Aunty A'in ce ta shiga dasu,ganin bulalin wajen duk sun kakkarye ji yai kamar yasa kuka,yanzu duk bulalin nan a jikin Salman sa ta kare? Jiki a sanyaye suka je parlourn,duk ta kudindina tana rawar sanyi,da sauri ya karasa gunta yana kira,tana jinshi ta kara rushewa da wani kukan. Hijabin ya yaye mata,yana ko'k'arin cicci6ota ya tuna da sakin dake t'sakanin su,sai ya zame hannu tare da zama. Bai san wani irin so yake ma Salma ba,wanda har yake rawar jiki akanta duk da abinda ta mishi, gashi har taja jiya ya bada kai gun Bintu bori ya hau. "Mey yasa Salma?.. Mey yasa ki ka zabar mana irin rayuwar nan?.. Gashi yanzu kin dasa min son kara aure koh na samu maslaha aciki... A zabure ta tashi,duk da yadda take jin jiki tana cije le6e dan azaba. "Mey kace Ya Ja'afar?.. Aure?.. Da sauri ya k'allo ta,sam bai tunanin zancen ba a ciki yai ba. Ganin bai bata amsa ba yasa ta yarda da abinda taji,hannu tasa duka biyu ta dafa kan ta zamo kasa tana cije baki,g'wiwa biyu ta durkusa duk tai kalar tausayi. "Ka rufamin asiri Ya Ja'afar dan Allah,wallahi, na rantse bazan kara ba..Dan Allah kar kamin kishiya.. Dan Allah, wallahi bana sonta.. Allah zan g'yara..nai alkawari,.. Ido ya rint'se, had'i da cije le6e,ba yau Salma ta fara mai magiya da rantsuwa kan ta d'aina ba,amma ba abinda ya sauya zani.. Yanzu komai ya kare musu,aure gareshi ya zama dole. By Feenat Ja'afar. Juma'@ Mubarak. 9/29/16, 9:07 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 24-Kai ya kada tare da mikewa, "kiyi hakuri Salma.. A baya na baki d'ukkan wata dama taki kinyi watsi da ita.. K'arfi da yaji so ki ke ki mayarni wani iri,dame zanji Salma?.. Na fita waje na samo 6acin rai,sannan na shigo gida nan ma wani 6acin ran ne,maimakon a lallashe ni..A'a ni kullum ni nake lallashi. "Kiyi hakuri,Allah ya baki lafiya.. Garba ya k'allo yai mishi halamar su tafi. A hankali ta mike tana jin wata irin hajijiya na debarta. "Nasan ni na ja ma kaina komai Ya Jaafar... Ja yai ya t'saya, jin taci gaba yasa ya juyo. "Tabbas na chanchanci d'ukkan wani hukunci da zaka min in dai zaka yafe min.. Kasa tai da kai,tai matukar zama abin tausayi a gunshi,sai dai kawai ya kasa gane nadamar Salma a yau,dan ta saba, ga kafa sai ka'rkarwa take. "Amma dan Allah wa zaka aura?.. Ba dai Bintu ba?. A yadda ta t'sareshi da ido yasa ya kasa magana,sai ya kalli Garba,kafad'arshi ya daga mishi halamar ba ruwan shi. Sai da ta maimaita kan ya daga mata kai. Murmushi tai da yafi kuka ciwo,a hankali take neman juyawa wani kanta ya sara gami da ganin duhu. "Kar ki min fassara Salma,ba abinda ya had'ani da Bin... Luu ta fara halamun zata fad'i, cikin zafin nama yai taku daya ya taro ta. Gaba d'aya jikinta ya saki,ga wani irin zafi kamar garwashi. "Salma.. Jijjiga ta ya fara,da sauri Aunty A'i ta shigo,sai ga Mama na fad'in ta taimaka su sa Salman a Napep gashi ta nemo.. "Mey zan gani haka... Da sauri suka juya ganin Mama da tai turus ganin yadda ya mammakale Salman,ita k'wa k'allonshi kawai take hawaye nabin gefen idonta. Garba ke mishi da hannu kan ya saki Salman amma kamar yana zigashi,sai kara naneta yake. Gaida Maman sukai da girmamawa tai banza dasu. Sababi Mama zata fara Aunty A'i ta jata sukai waje. Garba ne ya tsayarshi ganin yana neman cicci6ar Salman. "Kasan dai yanzu ba a mat'sayin matarka Salma take ba,kar ka nemo mana magana dan Allah.. Harara ya sakar mishi,kan cikin fusata yace "na mayarta toh.. Koh da magana? Kai ya k'ada mishi, kan ya bud'e mishi labule, "Dan Allah kaimu asibiti... "Auntyn mu.. Aunty A'i ya k'wada ma kira, da sauri suka fito ita da Mama dake huci. "Asibiti zamu kaita, dan Allah Mama ki yi hakuri na kaita.. Harara ta sakar musu kamin tabi bayansu ta sallami mai Napep sai asibiti. Murna ta koma ciki,da d'ukkan hannu biyu mama ta dafe kai,jin rahoton likita kan tabbatar da cikin Salma,dan haushi ba tasan tai waje ba. Shikenan an 6ata mata shiri, ciki?.. Kai amma an sha da ita, sam ta zata fad'in A'in ne dan a bar Salma. "Mama kiyi hakuri zata samu lafiya,bari naje na siyo allurori mu dawo. Kala bata ce musu ba, asalima ji tai kamar ta rufeshi da duka koh ta huce. A gun Garba ya k'ar6i kud'i,basu juma da tafiya ba sai ga Ummi da Aunty A'i sun zo,tuni k'wa ta ware tana surfawa Ja'afar Ummi na tayata. Kai Aunty A'i ta k'ada, fatan ta a kullum Allah ya ganar dasu Mama alkairin Ja'afar, alkairin da batajin koh su wanda suka auri masu halin suna musu. "Mama Salma fa matar Ja'afar ce har yanzun,don musulunci ya mallaka mishi,matukar batai idda ba,bare da kunne na naji yace ya mayarta wallahi, dan Allah Mama ki sassauta, in har da mey lefi aciki toh fa Salma ce.. "Ke dama ina kika ga kishin kai?.. Ai guntunki ta tsotsa, shi yasa sam kusan halin ku daya... Aure kuwa in dai ni nai nakudar Salma toh ya kare ya gama.. Ba ruwana da wani ya mayarta,sakaryan yaro kawai,sam bai da zuciya wallahi. Ummi ce ta amshe tana k'wafa. "Ai wallahi dad'i yake ji dan yaga Abba na jibgarta,dama garin d'ukan yaja ya rasa cikin ai da shi ya jiyo... "Ummi mey yasa ke sam baki da mutunci ne?.. Baki Ummin ta turo, "Ja'afar fa ba sa'anki bane,in bazaki g'yara ba toh kar ki 6ata... Salma ita ta chanchanci komai ba Ja'afar ba,gashi taja yace aure zai kara... A zabure Mama ta jiyo, "Aure?.. Shine ki ke kuma fad'a min ya mayarta?.. Kai ta k'ada, "eh lalle Ja'afar, toh k'wa zama da kishiya ba dai y'ata ba, karan nan zamu banje da Malam wallahi akan maganar komen nan,sam naki jinin yaron nan wallahi.. "Ni kam Mama bana ganin aibun Ja'a.. "Kimin shiru,kar ki gani din,amma aure angama. ****************************** Yau k'wananta biyu aka sallame ta,fur Mama taki bawa Ja'afar fuska,daga ina wuni lafiya shikenan. Su Abban su Ja'afar harda y'an cikin gida sunzo sun jajanta abinda ya faru. Kowa ya bawa bangarenshi rashin gaskiya, take Baba yace ya mayarta. Kai duk'e yace ai tun ranar chan ya mayarta,nan ya ja mishi kunne kan sarar ki fita A BAKIN AURENKI. A gaban su Abba ya kara tasa zancen zai kara aure,cikin fusata Abbanshi yace "Ba mun gama maganar nan da kai tun jiya?.. Wane aure kuma bayan wannan da aka mayar? Kai yai kasa dashi yai shiru, murmushi Abban su Salma yayi,kamin yace "Kamin dai dai Ja'afar, fatana Allah yasa auren shi zai zaunar da Salma a dakinta ta rungumi ibada. Ja in ja sukai tai t'sakanin Abban Salma da Abban Ja'afar, dak'yar Abban Ja'afar ya yardewa Ja'afar kara aure. Ana watse wa koh gama jan mota basuyi ba Mama ta fara sababi,ita a fafur ba inda Salma zata,bata zauna da kishiya ba,saboda haka ba mai zama da ita a yaranta. Itade Salma bata um bata um- um,sai hawaye kadai ke zuba,ita kad'ai tasan ya zuciyarta take hautsina mata,ta faru ta kare,tunda har manya sun amshi magana. "Ja'afar? kishiya? Kuma da Bintu kawarta?.. Tab da matsala. By Feenat Ja'afar 9/29/16, 9:10 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 24_Daaga sosai akai da Mama akan komawar Salma,sai da Abba ya bud'e mata uwata sosai kamin harda Yayanshi ta saki aka ta koma din. Ita kanta Salman yanzu ba kaunar komawar take ba sai ta mot'so mata ga laulayi. Ga Ja'afar tunda ya ji batun ciki ya kasa sukuni,kullum yana zaryar dubiya da leda. Shi dai bai mat'sa da sai ta dawo ba lokacin, dan g'yaran gida sosai yake wanda Ummanshi ta bashi ya zauna aciki. Har gida yau Abba yaje gun Abban sun kan lalle yau Jafar yazo ya dau Salma. Da dare k'wa ta koma dakinta. G'yaran nan gidan ya t'saya chak,sakamakon aikinshi da aka mayarshi aka bashi albashin da ya wuce shi,bai da mat'salar kud'i yanzu,auren shi kawai yasa a gaba. "Ina k'wana.. Cikin sanyin murya ta gaida shi kai duk'e, kai ya daga kamin yace "ya jiki?.. Shiru tai ba amsa. "Ki tashi ki zauna man.. Kai ta dago ta k'alleshi kamin ta kada mishi, "A'a magana nake son muyi da kai. Zama ya g'yara yana sauraranta. "Mey yasa ka ke son auren Bintu?.. Da ido ta kafeshi tana jiran amsa. Murmushi yai kan yai baya kad'an harda d'aura kafa daya kan daya. "Saboda tana so na ne Salma.. Kai ta kada, ''kaima kana sonta?.. A bazata tambayar tazo mishi,ga takafeshi da ido hawaye taro a idonta. "Ki gane Salma, ba wai.. "Eh koh A'a?.. Amma nake son ji kawai. Ba koh shakku yace mata "eh.. Amma.. Hannu ta daga mishi tana hawaye, "Barni haka dan Allah,amma kasan Bintu k'awata ce da koh?.. Ya zaka min haka? Kai ya kada harda dariya, "A sani na banta6a ganin Bintu a gidan ki ba,asalima... Sallamar Aunty A'i ce ta kat'se mishi maganarshi,sai ya tashi dan dan bud'e mata kofar,da kallo ta bishi tana mamakin kalamanshi,sai kawai ta k'ada kai ta mike tana goge ido. "Bissmillah mana Auntyn mu.. Yana gaba ta biyoshi a baya, sosai suke dasawa da Aisha,dan tasan abinda take sosai,shi yasa baya 6oye mata komai. Bayan sun gaisa ya mike yana zai fita, kai kawai ta k'ada mishi,sai Aunty A'i ce tai mishi a dawo lafiya. Zama Aunty A'i ta g'yara tana ma Salman k'allon tuhuma. "Ashe Salma baki fara g'yara ba har yanzun?.. Da rashin fahimta ta k'allo ta tana hawaye, "Fita fa yayi jiyan nan dawowarki amma har kin fara nuna mishi baki sauya ba. "Aunty A'i ba abinda na mishi fa Allah.. Katseta tai da fad'in "Amma zai fita babu koh a dawo lafiya?.. Haba Salma,nan ki ka dinga rantsuwar kin shiryu, koh har kin leka makotar ne yau d'akko sabon darasi?.. Kuka ta sa mata tana girgiza kai, "Haba Aunty A'i,k'awata fa zai aura fa,taya bazanji zafinshi ba?.. Da mamaki tace "wacce kawar taki? Cikin kuka tace "Bintu,dalibar shi ce a Day school fa. Ita dai ta hanga bata gano wace Bintu bace a k'awayen,tasan sarai k'awayen Salma basu fi biyu ba wanda tasan su. "Wace Bintu kuma cikin k'awayen naki? Amma basan ta ba koh?.. Kai ta daga mata, "islamiya mukai tare fa.. "Mtsww, t'saki Aunty A'in tai tana k'auda kai, "har wata kawar islamiya K'awa ce?, bana jin ko hanyar gidan ku ta ta6a zuwa balle ta zama kawarki, koh ta halarci bikin ki?.. Kai ta kada mata tana goge hawaye. Cikin lallami ta fara lallashinta. "Kar fa ki bari tun kamin ta shigo taci galaba akanki Salma, yanzu ba lokacin t'sayawa kishi bane a gunki, lokacin g'yaran kuranki na baya ne Salma... Ki d'auka baki ma ta6a sanin wata Bintu ba rayuwa,dan ba gaminki da ita sam. "Ki kuma fidda zancen auren nan a ranki,dan koma meye ke ce sila Salma. Nasiha tai ta mata tana kuka har ta gamsu da bayaninta. Ta bata shawara masu k'yau, ta kuma d'auka. Da ya dawo ya ga chanji,sannan bata kara mishi maganar Bintu ba. Yau satin ta daya da dawo wa,amma banda Maman Abba ba wanda ya leko mata har Maman Ummin, Ga sai wani kama mata kai Ja'afar din yake bare tace zata leka,abu daya ta sani,shine ta daina zuwa gidan kowa sai in ta kama. Washegari har kofa ta rako shi zai fita tace zata leka gidan Maman Ummi.. Yana fita yace mata sai ta dawo kawai. Da k'allo ta bishi,sai ta ga kamar gat'se ya mata,dan haka ta koma ciki tai k'wanciyarta. Mukullin gidan da ake g'yara zai fitar musu dashi sai ya dawo. A k'wance ya sameta ido rufe a parlour,sai yai jim,ganin bata fita ba har ya dawo. "Har kin dawo ne?.. Kai ta girgiza mishi,sai yai d'aki yana tunaninta, haka ta saba mishi kan gaba ta fand'are mishi,shi dai yasan yai alkawarin mud'in ta tambaye shi fita ya d'aina hana ta,yasan duniya makaranta,da sannu zata gane abinda yake gujar mata. Koh da zai fita sai ya kara nanata mata kan taje kawai. Bai jima da fita ba ta fito,tana dan jin hayaniyar su kasa-kasa. Har zatai Sallama sai ta ja ta t'saya jin wata gulmar da suke. "Ai yanzu ya zamarta mai gadinshi, tunda ta dawo ba inda taje tana d'aka,koh duk sururin zai kara auren ne?.. Tana jin Maman Ummi tace "oho mata,ba ita areni muje biki ba,mijina baya fad'a.. Muryar Maman Abba tajiyo tana fad'in ''ni tausayi ma take bani wallahi, ranar chan dana shiga duk ta rame tai baki,kana yaronka da kai an ma saki 2.... Baya tai cikin sanda danjin wani na shirin fitowa. Gida

Chapter 5 of 11