Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta goge hawayenta ta tashi, "Billy" taga a rubuce. Da sauri ta saita kanta kamin ta daga. "Sarauniyar kirki kina gida ne?... Dariya ta danyi kan tace tana nan.. "Toh ina kofar gidan ki yanzu haka. Da sauri ta tashi dan g'yara fuska tana fadin gata nan zuwa. Sai da ta tabbatar da ba mai gane tai kuka kamin ta fita kofa shigo da Billy. "Matar nan kinganki kuwa?.. Kin zama big madam da gaske fa. Murmushi tayi tana kar6an Ilham. "Kai Billy banda fa sharri.. Dariya tai tana "ba wani sharri, koh dai mun karu?.. Miemie tayi k'ani? Shiru tayi tana murmushin iya le6e. Bayan sun gaisa take ce mata ai daga wajen Miemie suke,tai ta kukan zata zo tana jin tace gun Auntyn ta zata. Murmushi tai tai kasa da kai,Allah sarki Mimi. "Yau Miemie aka kaima ziyara kenan?.. Murmushi Billy tai kan tace "ai duk sati sau biyu Abban Ahmad (Garba) ke zuwa dan dubo ma Abban Miemie lafiyarta. "Shine yau muka je tare,Miemie akwai wayo,kusan wata shida amma bata manta Abbanta ba,tana jin muryarshi a waya ta fara murna.. Shiru tai tana nazari,ba dai ace tun tafiyar Ja'afar ya zuciya ya bar garin nan ba?.. "Ja'afar kanar wasa,kinga wata shida muke nema yaki waiwayo mu,sai kulafucin a dubo mishi gudan jininshi... "Rayuwa kenan fa,kana naka Allah na nashi,in kai hakuri sai ka ga na Allahn ne dai dai a gare ka. "Amma Abban Miemie namijin duniya ne,mai ra'ayin kanshi,tunda ya jima haka nasan alhinin aurenki ne bai sake shi ba. Shiru tai tana jinta,a hankali ta fara jin nadamar wulakancin data kartawa Ja'afar, Abban y'arta. Yau Billy ta kawo fitina,dan har ta tafi bata da sukuni,har sai da ta tiki kuka son ranta taji dad'i,yanzu burinta Miemien ta dawo gare ta. Koh da maigidan yazo yaga yanayinta yasan tasha kuka,da ya tambaye ta sai tace Miemie take son gani ta d'akko ta. Anan ya tada mata bori,har sai da tai da na sanin maganar Miemie. Ba abinda yafi kona mata rai sama da yadda tanaji tana gani yai mata haramiyar makaranta,sannan Mama ta goya mishi baya,abu goma da ashirin sun had'e mata. Adaddafe akai shekara, lokacin tuni ta jima da d'akko y'arta,dan bazata iya da rashinta ba a irin yanayin da take na son yaran nan. Sai sai wani abu,fur Miemie taki jinin Alhaji, ko abu take in zai kwan dubu yana ta bari bazata koh k'alleshi ba,asalima har wani kumbura baki take in ta ganshi,Salma tai magana tasa mata kuka,ga bala'in Alhaji na wai yarinya tun kan ta girma ta rainashi shi da gidanshi, har harara wai take mishi... A tunaninta kamar Miemie wane harara ta sani bare wai kumbura mishi baki?.. Amma dan a zauna lafiya yasa kullum take kwa6ar ta. A gaban kowa har su Nabila zatai wasa harda k'yak'yatawa, amma fa koh a nan bangaren taci ka'ro da Alhaji zata d'unkume,tamkar ba ita ba,shima kwa da harara zai bita, wani sa'in harda t'saki.. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:33 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 39_"Aunty A'i na rasa yadda zanyi ne,yadda yake nuna t'sanar Miemie karara yafi damuna,abu kadan tayi sai ya hantara,t'sawa, ga kullum yai ta surutun wai tana hararar shi,koh fa wai turo mishi baki,nawa take fisabilillahi?... "Allah bansan haka agolanci yake sai gun Miemie. Murmushi tayi "bari muga,ke dai sa ido... ta kallo Miemie dake chan gefe tana mota da motar wasa. Da k'arfi Aunty A'in tace "ke Miemie... Rai had'e, itama ta dago tare da 6ata rai tana kumbura ma Aunty A'in baki. Sai Aunty A'in tai mata murmushi tare da mika mata hannu, "zo Miemie naga kitso, waya miki?.. Kafad'a ta make halamar bazata zo ba kenan. Cikin wasa Aunty A'in tace "haba Miemie ta,zo zan baki sweet fa.. Da sauri ta taso har tana dariya ta d'are ta tana kiran sweet. Baki sake Salma take k'allonta,Allah yaga banda yau ta gani da idonta bazata yarda Miemie zatai haka ba. Gira ta daga ma Salman halamar ta gani ai. Miemien na fita tace "Ikon Allah Aunty A'i, ashe dai gaske ne Miemie na mishi hakan. Kai ta kad'a, ''amma in ya mata irin yadda na mata,kila koh wasa take yana mata ne,yaro kamar Miemie dan lallabi ne,shi yasa tun farko banso kin karbi yarinyar nan ba Salma,gudun irin matsalar nan.. Ba magiyar da Abbanta bai min ba shima a waya kan baison ya'rshi ta zama agola, Gashi in bakiyi wasa ba shi kenan ta gama raina miki miji. Cike da damuwa tace "Nikam ta rufan asiri karta kashen aure Allah.. Dariya Aunty A'i tayi,lalle ma Salma,wai karta kashe mata aure? "Haba dai ke kuma,sai kace wata babba,kawai dai ita tata salon fad'an ne haka,amma zata daina. Ajiyar zuciya ta sau,kan tace "Bazaki gane ba Aunty A'i,wallahi in Abban su Nabila zai kwana yana cewa Miemie bari koh kallonshi bata yi,wannan nasan tana dashi,shi kuma sai ya kule,baya duba yarintarta,sai ma ki ga ya hauni da sababi. "Toh ki dinga sata misali kai mishi abu haka,kina kuma kula d yanayinta in yana mata magana,sai kina sata a hanya. Har magriba suna abu daya,matsalar gida Alhaji har ta tafi. Washegari a ita ke da shi,tun wuri ta shirya Miemie ta d'auke duk kayan 6arna duk dan a zauna lafiya. Chankula chankoto take mata tana dariya,ta sunkuya tana mata "aci ladan gabe" tana dan mata duka yai sallama. Kallo daya ya musu ya d'auke kai, dagowa Miemie tayi,in ba idonta ke mata gezau ba kamar harara ma ta mishi,tuni ta gintse fuska ta daina dariya. Ya salam, Miemie tai nisa a tsanar Abban su Nabila. Yake tai kan ta tashi dan binshi d'aki, "Miemie tashi muje gun Abba koh?... Kafad'a ta mak'e tana turo baki, sai tai kamar bata gani ba ta kinkime ta,a ranta tana fad'in "sai nayi da gaske a kanki Miemie. Ihu ta fara tana zazzamewa,a dole ita bazata je ba,jin suna iyowa dakin yasa da sauri yace "Kar ki shigo min kina min wannan kukan dama.. Chak ta tsaya tare sauke ta,kafadar ta kara makewa tana kallon Salman,sai ma ta fita tayi bangaren su Ja'afar. Kai ta dafe tana mai mamaki ita kam,Miemie,toh mey take so da ita?. *DAN KUKA...* ************************** Dube yake zai k'alli news amma baiga d'ayan remote ba, ga Salman ta shiga wanka, Kamar ance diba hannun Miemie dake chan gefen corridor tana wasa sai ga shi kuwa,yau shine motar ta ma. Da zafin nama ya tashi ya nufi gunta.. "Jiyinnnn" take dashi cikin tsawa yace "Wannan ne abin yin motar?.. Dagowa tai tana t'sareshi da ido cikin had'e rai, "Bani nan ni labarai zai wuce ni sarauniyar 6arna. Kafad'a ta mak'e mishi tare da yi da remote din bayanta tana zunguro mishi da baki. Cikin zafin nama ya dagota, dai-dai fitowar Salma dan jin fad'anshi, binta yake daga zaunen tana matsawa taki bashi,kawai sai ya fizgota da niyar kwata ta tun karfi, kai cikin fushi ta kwada remote din a kasa tana kuma mishi ihun kukan ya hanata wasa.. Dagashi har Salman suka bi remote din da kallo wanda kowanne part yai nashi gun battery ya cire. Da sauri Salman ta karaso ta kwada mata mari,sauke ta yai kasa yana sababin ai wai ita tasa ta raina mutane yai waje,k'allon da baiyi ba kenan ya fice. Harara ta kwada mata kan ta kamo kunnenta ta murde tana kuka, "Baki isa ki chazan matsala ba ja'irar nan,wato bakin hali ki ke son kowa koh?. Kashen aure zakiyi ne?.. Kullum baza'a aji kanmu da mijina ba sai akanki?.. Cikata tai tare da dan rangwashenta, "Toh baki isa ba,dole kizo ki koma gurin Mama koh dangin Abbanki da zama... Bata karasa ba Miemie ta fad'i tana burburwar fad'in taki,ita bazata ba. Ido kawai ta sa mata,kan tai kwafa tai d'aki,da gudu itama ta bita tana kukan bazata ba Salman ta rufe kofarta ta batta da bugun "Antee,Antee bata cho. Anan tai ta mitarta tanaji daga dakin tana "Ai sai kinje... Tuni ta kara jiniya, kuka harda shudewa amma tai burus da ita tana kwalliyarta. Zuwa chan taji shiru,sai tai murmushi, Miemie matsala. Fito wa tai dan ganin koh fita tayi,sai ta ganta kwance bakin kofa sai sauke ajiyar zuciya take tai bacci. Sunkuyawa tai ta leka,ido har ya kumbura, duk sai ta bata tausayi,batasan lokacin da ta d'akko abarta ba,batajin tunda Miemie take ta ta6a dukanta haka tai kuka. Kwantar ta tai a gado tana goge mata fuska da tissue,baki ta kai fuskarta, "am sorry kinji... kamar ta sa kukan itama,Miemie taurin kai toh,Alhaji hancini,ya suke so tayi da ranta ne? By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:34 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 40_Washegari bayan la'asar tace mishi zata maida Miemie gidan Mama dan Allah ya batta taje daga nan sai tai barkar Ummi data haihu cikin dare. Da har zai hana,ganin kayan Miemie a akwati yasa bai gardama ba ya batta,kwarai tasha mamaki,dan rabonta da fita har ta manta,amma dake wacce bai kauna za'a mayar ya batta. "Ga driver in kin gama ya kaiku,kar kuma ki dad'e.. Kai ta daga tace ta gode. Rayuwa kenan,da ya batta ma taji dad'i,koh ba komai zata leka gida yau. Gidan Ummi suka fara zuwa,sai ta6e baki take tana korafin yadda ta zama matar k'ulle. "Aure sama da shekara wannan ne zuwanki na biyu gidana,wannan wace iriyar rayuwa ce,mutum sai shegen kullen t'siya.. Tana jinta tai shiru,tana tunanin hali irin na dan Adam,mai wuyar gane hali,lokacin Ja'afar mai barinta fita haka ta gurza,yanzu kuma ta had'u da dai dai kowa,ga kud'i ga cima, amma ba fita ba haihuwa.. Zaman lafiya wai yafi zama Dan Sarki. Ita kanta Miemie murna take sun fita yau,sai dai suna zuwa gidan Mama taji Salman na maganar zamanta ta d'ane cinyarta ta riketa tam. Ban6are ta Mama take ajikinta tana ihun kiran Aunty,ita kuka Salma kuka, ga magriba ta sawo kai. Suna haka Abba ya shigo, duk ta rike gyalen Salma kam tana ihu. Dak'yar ta fizge tai hanyar fita da gudu tana kuka. "Subhanallah... Ta shid'e fa wannan... Chak ta tsaya jin daina kuka Miemien,da sauri ta juyo taga Abba na jijjiga ta. Ba shiri tai gun dai dai Miemien ta kawo wuta ta kar6e ta. Kuka na fitar hankali take tana bata hakuri, ''Ni bansan mey yarinyar nan zata tsare miki ba in ta zauna achan gunki ba,kullum sai da kuka koh jinya za'a rabu?.. Ki bar y'arki a kusa dake man tunda ita mai kulafuci ce... Kai ta daga tana share ma Miemien hawaye tana tai shiru toh.. Dole tana ji tana gani ta koma da Miemie, dan yau fir taki yadda tunda ta d'andana zama da ita. Kanta take shafawa,ita kam ta tasata gaba tana ta kallo ba koh kiftawa. A hankali tace "Miemie.. Idonta a kan Salman tace "Uhmm. Kwanto wa tai a gefenta tana g'yara mata kwanciya, kamar wata babba ta fara mata fad'an ta zama mai ji dan Allah. "Ban san matsala Miemie, ki rufan asiri ki daina halin nan naki na kumbura ma mijina baki,kinji?.. Kai ta daga mata kamar gaske. Sai tai murmushi tai kan tace ta taso suje suyi girki a kitchen. Shikam Alhaji da murnar yau Miemie ta tafi ya shigo gida,shi kanshi ya rasa mey yarinyar ta tsare mishi a gidan,duba ga su Ja'afar na gidan. Sai dai tun daga bud'e kofar parlourn farin cikin ya kau. Dariyar Miemie ya fara cin karo yana shigowa ta kitchen,dan haka da sababi ya isa. "Mey ya zaunarki har bayan magriba baki dawo ba?... Mey kuma ya dawo da wannan? Duk ido suka zuba mishi,mai hali kuwa Miemie tuni ta chunno baki gaba tana mishi wani irin kallo jin ya fara sababin nashi. "Wallahi har kusan suma tayi dan kuka yau,tausayi ta bani shine na dawo da ita,kai hakuri duk ita tasa muka kai magriba. K'allon Miemien yayi da kamar harara kamin ya kad'a kai dan takaici ya fice. Ajiyar zuciya ta saka,ta tsalake rijiya da baya da k'yar,kan ta dawo kan Miemie ita tuni har ta cigaba da sabgarta. Sai dai ana zuwa kwanciya yace daga yau Miemie zata bar kwana dakin su,koh ta koma kasa. Ya ta iya,dan a zauna lafiya ta sauke Miemie kasan,dan ba yadda za ai ta luluka yarinya chan wani waje ita tana wata jahar,a ganintq Miemie nawa take. ******* Fur yanzu ta daina ganin fuska gun Alhaji, in ya shigo ba wanda ya isheshi kallo,asalima ya daina zama bangarenta sai cin abinci koh bacci. Yau dai ta d'au damarar fara koyawa Miemie sabo da Alhaji. "Abba ki ne kinji Miemie nah?.. Ki dinga mishi oyoyo kina mishi dariya kinji?, banda harara,banda turo baki,kina ji na? Shiru tai tana binta da kallo kawai,chan sai ta yak'e mata hakori. Cikin farin ciki Salman tace "yauwa,koh ke fa,be a good girl ba? kai ta daga mata tana dariya. Alhaji yai wanka ya shirya yaje parlour yana duba abu a system nashi su kuma suna daki gun shirya Miemie. Daga parlourn ya kwada ma Salma kira wai ta fito mishi da agogon shi na kan mirrior. Murmushi tai ta k'alli Miemie,tasha parking da ribbon sanye da gown ja da baka iya g'wiwa, dake fara ce sai tai mata k'yau sosai. Agogon ta d'akko ta kamo hannun Miemie, "Kai ma Abba a maza yana parlour,ki nutsu dan Allah kinji Miemie nah.. Kai ta daga tana dariya ta karbi agogo tai parlour. Bayanta ta biyo dan ganin ya zata kaya, daga yau ne zata fara koya musu kusanci da juna shi da Miemie. A dunkume ta isa gunshi yana duba abu a laptop, mika mishi tayi ba koh magana, sai ya dago ganin itace,tai mishi kyau sosai,ga sai kamshi take,ba abinda ta bari na babanta a ganin shi har dacin ran,in baxai manta ba yanzu ne zata shiga shekara uku,amma duk ta tara dacin rai wai da fitsara. Kai ya d'auke ya cigaba da abinda yake, Salma har ta fara murna ganin bai mata dan halin ba yau. Ita kwa Miemie sai ta ajiye agogo kan hannun kujera ta juya tsautsayi agogo ya fad'o kasan tiles sai glass din ya fashe. Da azama ya juya,ganin agogon akasa a fashe Miemie ta juya ta mike ya fara sababi. "Duk wani mugun hali irin na ubanta yarinyar nan ta iya,agogon nawa zaki saka da gangan ki fasa min?.. Waje Salma ta fito ganin ya yo kan Miemien a sukwane, duk tana k'allon abinda ya faru. Kumatun Miemien ya ja tare da kai mata rangwashi akai yana sababi,tuni ta hau kuka jin zafin abin,da sauri Salman ta karaso dan bashi hakuri. "Shegiyar yarinya kawai,kin san kud'in agogon da kika fasa kuwa?.. Ja Salman tai ta tsaya tare da rintse ido. Ga ihun Miemie tana kiran Aunty,ga sai zagin y'arta yake harda sheganta mata ita? "Alhaji.. Cikin fusata ta kira shi tare da bud'e, Rai 6ace shima ya dago da niyar huce haushin shi kanta ta rigashi. "A gaskiya ka daina sheganta min yarinya, dan da ubanta gaskiya,haka kawai, ina fa kallo tana mika maka ka d'auke kai,ta ajiye ya fad'o kasa,toh meye lefinta aciki har irin wannan zagi?.. A'a toh gaskiya... Kai ta kawar ranta 6ace. Cika Miemien yayi yana kallonta, wannan ne karo na farko da ya fara ganin fitsarar Salma,shi zatai wa tsawa akan Miemie? By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:37 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 41_Da gudu ta karasa tana kama hannun Salman,d'aukarta tayi a ta sa6a a baya, "Yi shiru kinji.. Muje daki... "Kar ki kuskura ki shigar min d'aki da wannan yarinyar.. Chak taja ta tsaya tare da juyowa tana kallonshi. "Kema kar ki shigar min d'aki,ni zakiyi wa rashin mutunci kan y'arki?.. Toh baki isa ba,dan ba ayi macen da ta isa daga min murya ba ki sani. Cikin karfin hali tace "Toh mey ka ke nufi da hakan?.. Daga fad'in gaskiya?.. Haba Alhaji,Kullum ina fuskantar yadda ka ke tsagwamar yarinyar nan,shi yasa sam bata shiri da kai ai... "Ba wani nan,bakin halin yarki dai irin na tsohon mijinki dai,da kuma shegen taurin kanta irin nashi,koh kin zata na manta da waye shi zamanin neman aurenki? Da sauri ta tare mai numfashi harda sauke Miemie kasa da sauri, "Ba ruwan Ja'afar cikin maganar nan tamu,zai fi kyau in ka daina sakoshi ciki..kuma na fad'a maka y'ata bata da wani mugun hali,sai dai naka mugun halin rashin son yara, da kuma.. Shiru tai tare da ja da baya ganin ya zaburo kanta, "wallahi kar ma ka soma,dan ba yadda za ai in zuba ido kullum kana aibanta min yarinya wallahi, nawa Miemie take? Amma k'arfi da yaji so ake ta iya dan hali.. "Salma ni nake fad'a kina fad'a?.. Ashe baki da mutunci?.. Kai ta kad'a tare da juyar da kai, "Nikwa nake da mutunci tunda a cikin gidan ubana ka auro ni kuma... "Subhanallah,haba ku k'wa.. Juyawa tayi taga Maman su Nabila na shigowa dakin. "Tun ina shanya nake jiyo ihun Miemie da naku,bai dace ba Allah,kuna abu a gaban yarinya.. "Ba ruwanki cikin zancen nan,in ba so ki ke ya taso da kwantaccen naki ba ke ma.. Shiru taja bakinta tayi tuni idonta ya fara zubar da kwalla, ya cigaba "Yara nawa ma basa gabana bare ta wani, saboda haka akan yaro ba mai sani ciwan hawan jini,dole yau ki mayarta gun ubanta,koh ki san nayi da ita. Cikin kuka tace "Bazan iya rabuwa da y'ata ba,kai hakuri raina ne ya 6aci.. Malalacin murmushi yayi,kan yace "Daga baya kenan,amma dole ki za6a zaman dani koh da yarinyar ki... Maman Ja'afar ta kallo da itama ke hawaye tana kallonta,sai ta cije le6e da takaici. Juyawa tayi ta d'au Miemie, kan ta kalloshi ido na fidda kwalla. "Ni kam na kasance daga masu taya annabinmu kishin Al'ummar shi,dan haka ina son haihuwa,bi ma'ana zan iya rayuwa da Miemie kad'ai mud'in Annabin mu zai alfahari dani... Cikin zafin rai yace "Kimin hausar da zan gane Malama ni.. "Annabinmu yace kuyi aure dan ku hayaiyafa,domin go6e kiyama nai alfahari daku.. Kayi aure,amma baka fatan tara zuri'a, hakan yana nufin kana tarjiya a bisa umarnin manzon Allah.. A tunzure yai yo kanta, "Kimin shiru fitsararriyar kawai,koh yayarki bata isa ja ina ja ba wallahi, dole ne yau ki za6i d'aya.. Cigaba tai da batun ta ido rufe, "Nai ma biyayya ta t'sawan shekara guda ina bin yadda kaso,toh ka sani ni Sunnah na dauki aurena,kuma zan cikashi ne ta hanyar tara zuri'a, dan zanyi alfarhari idan na kasance a daya daga wanda Annabi zai alfari da ita... Mari ya de6eta dashi jiki na 6ari,da sauri ta dafe gun tare da bud'e ido,kuka Miemie tasa ganin an daki Auntyn ta, "Mutuniyar banza kawai,ni zaki mayar jahili?.. Murmushi tayi kan ta kad'a kai. "A'a,dan kuwa kafi jahili,danshi dama bai sani ba bare take,kai kuwa ka sani amma kana taya shedan rawa,dan baka kaunar.. Shiru tayi ganin zai kara mata wani,da sauri ta rintse ido tana hawaye,jin shiru bataji saukar mari ba yasa ta bud'e ido. Hannunshi rike a hannun Maman su Ja'afar, "Lalle lokaci yayi da ya kamata in tanka maka Alhaji,lokaci yayi da zan daina bin umarnin ka ina 6ata.. Ashe har alfahari ka ke cewar yaranka ma basa gabanka?.. Jiran amsa take tana kallonshi, da borin kunya yace "Cika min hannu... Ba musu ta cika, Salma ya nuno "Ke kuma ki tafi gidan ku,na sake ki saki daya,na koyan hankali,in kin koyo kofa a bud'e take ki dawo.. Ido ta rintse gabanta na fad'uwa, wai ya saketa?.. Daga fad'in gaskiya. Kan Maman su Ja'afar ya dawo, "Wato zuwan fitsararriyar yarinyar nan ta sa kin fara sauya hali Halima koh.. Kai ta daga da sauri.. "Kwarai kwa,dan yanzu na gane kuskuren dana tafka a zaman baya da nayi da kai, nima ina son zuri'a, ina son su Ja'afar sama da komai yanzu,kuma zanso wanda duk yake son su,zan kuma yi fad'a da duk mai kinsu, aciki kuwa harda kai usman... Baki ya saka yana mata k'allon mamaki "Usman?.. Babbar magana.. Halima yau ke kike kama sunana ba ma Abban Ja'afar bare Alhaji?.. Shiru tayi tana kallonshi,sai sababi yake daga karshe itama yace taje sai ya nemeta. T'saki sukai mai lokaci daya ita da Salma,duk da kallo ya bisu Salma tai d'aki. "Ai nima ka sallame ni kawai,dan bazan zauna da mutumin dake kyankyamin zuri'a ba,dole yau na barka,Allah ya yafen baya,amma yanzu kam ta kau,ka sake ni nima kawai... "Bazan saki ba,amma dole ki fuce min a gida,dan ba mai sa min hawan jini... Kuka Salman take tana jiyo sababin da Alhajin ke yi.. Hannu Miemie ta kai tana girgiza mata kai itama tana kukan,gaba daya ta rungumo y'arta tana kuka mai cin rai,ita kuma haka Allah yayi ta marar sa'a a zaman aure,gashi yau a dalilinta auren shekara sama da ashirin na neman tsinkewa bayan ta t'sinke nata. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:39 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 42_Jugum Abba yai bayan jin bayanin Aunty A'i,ita dai Salma sai kuka take,dan tasan yau kam sai ta Allah,fad'a kam sai dai ta toshe kunnenta. Amma da mamakinta sai ji tai ya sauke ajiyar zuciya tare da fadin "Allah ya kyauta toh,dama tun farko ni mutumin nan ba wai ya mun ba ne. "Yadda naga kowa na yinshi a gidan musamman Babar taku yasa nabi yarima nasha kid'a, sai fatan Allah yasa haka shi yafi alkairi.. Mama ce ta riga kowa saurin fad'in "Amin,ni nasan naso shi,amma daga baya sam mutumin ya fice min akai,dan daga gani ba wai zaiyi wani mutunci bane,ga dankaran kulle,yanzu kuma an kara da rashin son haihuwa.. Dame yarinya zata ji?.. Kallon mamaki suke ma Maman musamman Salma, yau mama ke fad'in aibun Alhaji da bakinta?... Lalle abu ya 6aci. Da dare suna kwance ta tasa Miemie a gaba tana kallo,itama ido ta sa mata, tunaninta zancenta ya tabbata. A dalilin Miemie aure ya 6alle.. Murmushi tai kan ta gyara kwanciya. "Miemie.. Kai ta daga tare da fad'in "Uhmm.. Sai ta mirgino kusanta tai rub da ciki "Kina murna kuwa?.. Baki ta yage mata ba dan ta fahimci nufin Auntyn ba. Sai ta kad'a kai,ta rasa wane irin nishad'i ke shigarta da yamman nan zuwa daren yanzu.. "A k'ya kam yi murna,wato kin rabu da alakakai koh? Kai ta daga mata tana dariya.. Itama tana dariya ta fara mata chakulkuli su na k'yak'yata dariya har su Abba dake waje suna jiyo su. Mama ya kallo,itama shi take kallo, "kina jin mutananki koh?.. Kamar yau take Sallah.. Murmushi tai tana sadda kai kasa, sai ya girgiza kai yana tuna wani abu. ****** Tun daga wannan lokacin hankalinta ya koma kan makaranta, babban bakin cikinta bai wuce yadda Alhaji yai burus da maganarta ba,a ganinta in har da mutunci koh Abbanta ya samu da zancen.. Gashi a kalla yanzu ta kusa cinye kwanakin iddar ta. Duk suna waya da Maman su Nabila tace yana zuwar musu,sai dai ita baya samun ganinta. "Aunty!.. Aunty!!.. Da dan gudunta ta shigo gidan tana k'wada mata kira rike da leda tana ja,bakin nan har kusan kunnen Miemie. Kamar a mafarki taji kira ana ta6ata,a hankali ta bud'e ido dan bata jima ba da bacci ya debeta sakamakon ciwan period da take. "Uhmm Miemie.. Ya akai?.. Ledar hannunta ta hau bud'e mata tana mata magana duk a hard'e dan murna. Riguna ne y'an kanti masu kyau da tsada da takalma, sai teddy guda biyu da y'ar tsana mai feeder a baki. A zabure ta mike tana duben Miemien,tasan ba mai irin ma wa y'arta tsarabar nan sai Abbanta,yawu ta had'iye kamin tace "Miemie,ina kika samo kaya haka?.. Dagowa tayi kamin tace "Abba ne... Tsam tai tana kallon irin farin cikin da Miemien take,wato in zai shekara bata ganshi ba tasan Abbanta. K'allota tayi tana mata yake ganin yadda take cire feedern a bakin y'ar t'sanar tana fad'in Inya.. Inya. Da sauri ta tashi tare da zarar gyale tai waje. A kalla zataso ganinshi koh dan ganin yadda yake a t'sawan shekara guda da d'auri. Sai dai har ta gama leke bata koh hango mai kamar Ja'afar fa sai sawun mota. Zaure ta koma tana lumshe ido tare da dafe kirjinta. Babu makawa Ja'afar ya shigo zauren nan.. Dan ga nan kamshin turarenshi ciki tana iya shakarshi. Jiki a sanyaye ta juya ta koma cikin gida, a chan d'akin Mama ta jiyo karad'in Miemie na ba ma maman labari tana dariya. Da murmushi ta samu ta dan dosana tana kallonsu kamar ta sa kuka. "Na fuskanci yarinyar nan in dai tai arangma da Abbanta tana kwanan murna, haka kwanaki dak'yar na ban6areta jikinshi ashe bata manta shi ba tana kuka,shima harda y'ar kwalarshi yana daga mata hannu... Ido ta kurawa Maman ba koh kiftawa.. Ba dai Mama na nufin Ja'afar yana zuwa garin nan ba kuma har gidan nan?... Mama ce ta kat'se mata tunani da fad'in "Ban tunanin yaron nan koh a hanya ya ganni zai gaidani ba sam bayan aurenki, duba ga yadda na rika mishi fatattakar arziki.. Zuwan shi biyu gidan nan ashe makaranta ya koma kinji.. Murmushi tai Maman da iyakar shi le6e tare da daga kai. Tuni ta zurfafa tunani,har bata jin mey Mama da Miemie ke fad'a,kan ta farga har idonta ya cika da kwalla,da sauri ta juyar da kai tare da goge wa kamin su gani. Sakkowa tai tana taya Miemie rad'awa teddy suna suna dariya. Kallonsu kawai Mama take tana wani tunani, kai ta kad'a kamin ta tashi ta basu gu dan tasan Abba yana gaf da zuwa. Washegari da yamma tana kokarin shiga wanka akai mata sallama. Hijab ta zira harda shafa powder da zumudin Ja'afar ne ma,kila ya samu labarin tana gida. Turus tayi tare da chunno baki kamar Miemie ganin Alhaji da abokinshi. Baki ya washe mata yana fad'in ta karaso man kusa... Murmushin mugunta tai kan ta kalloshi "Dan bani minti biyar na fito a gida... Kai ya daga yana mata murmushi, ashe bazai yi wahalar shawo kan Salma ba kamar Halima. Ruwan da ta zuba na wanka ta d'auka da wani a buta dan tsarkake kai in tai wankan t'sarki. Tana yi tana murmushi har ta gama. D'aki ta shiga ta tsane kanta da towel kan ta dan shirya a gaggauce ta fita. Yadda take murmushi ne yasa Mama tambayar waye yazo, a tunaninta koh Ja'afar ne,tana cewa Alhaji ne ta 6ata rai. "Ki dai kama kanki ki saiwa kanki mutunci,dan sam mutumin ba nagari bane,kinjini ai? Kai ta kad'a tana murmushi, lalle Mama, yau Alhajin guda?.. Sai ta kad'a kai, "adu'a bata fad'uwa kasa banza. Bayan sun gaisa yake zungurar abokin nashi sarkin iya t'sari, duk tana jinsu tana murmushi dan feleke harda tambayar Miemie,sai da suka gama tass tana jinsu tana kad'a kai. "Ai yanzu na fita sahun matarka Alhaji,sai dai kabi sahun zawarawa na..dan nayi iddah ni... Fuska ya g'imtse yana kallonta, "haba kar muyi haka dake man,ina fa lissafi,yau watanki biyu da kwana uku rabonki da gida na, kinga ai bakiyi wata uku bare ace kinyi iddah koh ba haka ba abokina? Kai ya jijjiga yana fad'in "kwarai kuwa,dan haka muka sani a al'adan ce. Kai ta kad'a tana murmushin takaici, wato ga babyn roba,a hular a lokacin da akaso a d'auka a randa aka ga dama.. 6aro-6aro tai mishi dalla-dalla kan ita ai duk bayan sati uku take period, kuma ya sani sai dai ya take. A fafur yace shi baisan zance ba,kawai ya maida ta dakinta. Juyawa tai ta koma gida,tana ji sai kwad'a mata kira yake tai mishi banza. Da farin ciki

Chapter 10 of 11