Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
k'ada kai, "toh Bintu.. Salma Bintun ta k'alla jiki a sanyaye ganin ko in kulan da Ja'afar ya mata,"shiga za kiyi ne Salma? kai ta kada mata, jiki a sanyaye tai gaba Salma ta daga musu hannu halamar sai anjima tana murmushi. Da k'allo ya bita cikin wani yanayi, da ko shi kanshi bazai iya fassara wa ba. Kai ya k'ada kan ya k'allo Garba wanda k'wachokam ya maida K'allonshi kan abokin yana dariya kasa-kasa. Harara ya maka mishi kan ya juya,sai k'wa Garban ya kara sa dariya yabi bayanshi. "An fad'a tarko makal ana hura mana hanci,sai anyi magana kace wani "mey nene so? Ni ban sanshi ba.. Karyan kawai,koh makaho ya laluba yaji ka afka so ai yanzu kam. Chak! Ja'afar ya t'saya tare da juyo wa gun Garba. "Mey kenan haka ke nufi?.. Harara Garban ya k'wada mishi kan yace"kar ka maida ni yaro fa malam,kana nufin baka san kana son Salma ba ko mey?.. K'allonshi kawai Ja'afar ke yi cike da mamaki,a hankali ya furta *"SO"*?... Hararar shi Ja'afar ya kara,gani yake kamar ya raina mishi hankali ne. "Kaga Malam kawai kai saranda haka,tuni tun yadda ka ke ta yawan fad'in Salma nasan a rina,ka bar wani k'wane-k'wane. Shi dai Ja'afar ya t'sunduma tunani maganar Garba,wai So? Salma kuma?. *By* *Feenat Ja'afar* 庐NWA. 9/29/16, 8:56 AM - Queen Safiyyert馃憫: [7/21, 12:28 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 8-Har Ja'afar yazo k'wanciya yana tunanin kalaman Garba,tabbas biri yaso kama da mutum, dan yana jin sauyi tun ranar farko da ya dora idonshi a Salma bayan dawowar shi. "So"... Ya furta a hankali, murmushi yai kan ya k'ada kai,dan yana da aiki a gaba,dan bai san kom ba game da lamarin. Tun daga ranar ya zamto kusan kullum da yamma yakan raka Salma islamiya,koh da yana shago zai zo ya ganta kawai,hakan na sashi nishad'i, yau da gobe har ta fara sakin jiki dashi a karo na biyu. Sai ya zamana itama in bata ga Ya Ja'afar a ranar ba batajin dad'i sam,haka zata k'wana sukuku. Shirye-shiryen bikin Aunty A'i suke,duk sun shiga _busy_. Da yamma sun fito bak'in shagunan su Abba siyayyan kayan fitar biki, tasan kuma d'uk layin ba inda ya kai shagon su Ya Ja'afar kawo kayan k'yali, amma da tayi magana Ummi sai ta tanka. Kai duk'e yana duba takaddu,kamar _papers_,chak ya t'saya da abinda ya yake yana murmushi kai duk'e, ajikinshi ya ji kamar Salma na kusan shi,itama dai satar k'allon shi take,tana ganin zai dago tai sauri ta juyar da kai tana murmushi. Fara'ar shi ta karu dan hango Salman. A hankali ta dan kara K'alloshi,sai k'wa suka had'a ido,da azama tai kasa da kai tana murmushi har suka karaso. Tuni Ummi ta had'e rai ganin Ja'afar a shagon,a takaice ta dan harari Salman ganin sai wani munafukin murmushi suke sakar ma juna,baki ta ta6e kan a ciki ta gaidashi tai cikin shago ta barsu nan. _"My_ kanwa,.. Kai ta kara duk'ar wa tana gaidashi,sai ya k'ada kai,ya rasa irin kunyar Salma gare shi yanzu,abu kad'an duk'ar da kai. "Biki ya karato ba? Kai ta daga mishi tana dan k'allon _net_ d'in gefenshi da murmushi. Tashi yai zuwa gun inda take k'alla ya fara saukar mata dasu. A hankali ta tako gun dan zabi,d'uk sun mata k'yau. Sai ta dan kallo shi, "malam Garba fa? Murmushi yai yana k'allonta, "yaje inda aka tura shi _service_ nashi yaga gun,gobe zaki ganshi. Kai ta k'ada, d'uk sai taji ta kasa za6a ganinshi kusa da ita. Kamar ya sani ya kara s'akko mata da wasu. "Bari na tayaki za6a. Kai kawai ta k'ada mishi tana k'allon kayan,kan wani _purple_ idonta ya kai,a hankali ta kai hannu zata ja shima ya kai zai d'akko shi yana fad'in _"purple_ zai miki k'y... Shiru yai ganin itama shi ta rike,ya rike rabi ta rike rabi. D'uk sai suka k'alli juna ba koh kiftawa da wani yanayi... Tamkar wanda aka lika _poster_ a gun haka suka kame da k'allon juna. Ummi ce ta kat'se su da fad'in "Ga nan wasu materials y'an leda Salma masu kaman _lace_.... Shiru tai ganin wani ikon Allah,baki sake take k'allon su,tuni Salman ta sakar mishi tai baya tana sunke kai da murmushi tare da amsar kayan hannun Ummin tana sunyi k'yau ba dan ta gani ba. Murmushi ya sakar mata shima,har yanzu yana rike da _net_,ya rasa mey ke damun K'wak'walwar shi akan Salma. *By* *Feenat Ja'afar* [7/21, 8:05 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 9_Baki ta dan ta6e,kan a y'atsine tace ma Jafaar d'in "mun zabi wannan, zamu nuna ma Baba sai ya bada kud'in. Murmushi yai yana k'allon gun Salma,itama idonta na kusan hannunshi. "Koh na tafi ne Salma? K'allo Ummin tai,kan ta k'ada kan suka yi hanyar fita a shagon,a hankali ta dago mishi hannu halamar _bye_. Kai ya k'ada mata shima ya dago mata nashi. Tai k'walli da Ja'afar ta ji dad'i,har aka je gida bata umm ba um um,sai Ummi ke ta zuba kamar kanya, yadda zata zuba wanka a bikin Aunty A'i har ta kule. Da dare sai ga yaro wai ana kiran Salma. Rai had'e ta k'allo yaron, "je kace bana nan... Shiru tai ganin yadda mama ke mako mata harara, "anya yarinyar nan kalau kike kuwa? Wato sai dai ai ta min asarar hoda da kazal a banza ina tufka kina min warwara koh? "Farin jini Allah ya bayar kina ma kanki bak'in ciki? Haka zan ta barar miki ni baki ban bare na maida g'urbin abinda na fitar Salma?.. Maman ta k'allo da mamaki,toh rokon samari mama take so ta fara komai? Allah yaga ta t'sani fita zance. Amma ganin yadda mama ke wanke ta yasa ba shiri tace ma yaron "yace ma waye?.. Kai ya daga mata,"wai ince inji "Ja'afar in kin tambaya... Ai koh karasa wa nai ba ta mike,tuni murmushi ya maye g'urbin 6acin rai, da k'allo mama ta bita, kamar ba ita ce yanzu ba. Yau kam ga su Salma harda mit'sika hoda da _lips stick_ har ta d'au hijab ta kara k'allon madubi,kawai sai ta janyi g'yalen Ummi tai waje. Shine kuwa yana jingine da gidan,wani murmushi ta saka na farin cikin kara ganinshi a daren. Da sallama ta karasa d'uk da ba wani haske gun sosai,amma sai dan sinke kai take kamar rana. Bayan sun gaisa kowa yai shiru kamar basu abin fad'a. Chan dai ya nisa ya miko mata ledar hannunshi. Kamar mai neman ba'asi ta t'saya bata k'ar6a ba. "Ajiya na kawo kimin zuwa gobe ne,ba wani abun ba naga kina tsoro. Murmushi tai kan ta amsa tana k'allon Ummi zata wuce,koh ci kanku bata ce ba ta shige gida. D'uk sai Salman taji wani iri,Ummi sam taki jinin Ja'afar ta rasa dalili. Ba jimawa yai mata sallama dan ya rasa abin fad'i shima. Dama da Garba ne yau kam da zai iya fad'in komai ga Salma. *** Tunda daga lokacin Ja'afar ke zuwa gun Salma jefi-jefi,d'uk da har yanzun bai furta mata so ba,amma ita a ganinta d'uk acikin so ne. A k'wan a tashi gashi har ta kammala secondary, wannan itace tafiya mafi tsawo da Salma tai bata ga Ja'afar ba,kusan wata bakwai. Tun tana damuwa har ta hakura ta rungumi karatun ta na fita. Gasu yau sune a gida,d'uk an rame anyi baki. By Feenat Ja'afar. [7/21, 10:10 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 10_Babban tunaninta bai wuce d'uk t'sawan lokacin nan da aka diba ba Ja'afar ba labarin shi ba,tasan yakan je mata ziyara makaranta koh a t'satt'saye ne,ga ita ba waya ba balle ta neme shi koh lafiya? K'wana biyu da dawo wa yau d'ai ta kudiri niyar fita jin ba'asi,koh Garba in ta gani. Hijab d'in _mss_ d'inta har kasa ta sa harda nikaf. Sai d'ai har ta gama zagayen layin ba wanda ta gani ciki,kawai burinta ganin Ja'afar ne. Iyanzu kam tasan tai nisa kan sonshi ba kad'an ba,sai d'ai ita yanzu ta fara tantama. Har zata juya ta tuna da shago,d'uk da tasan yanzu ba kasafai yake zama ba tunda ya samu g'urbin koyarwa. Sai dai tai chan d'uk bata tunanin ganin nashi. Daga d'an nesa ta t'saya kusa da wata bishiya ta d'an kare ba mai ganinta, da sauri ta juya tare da dafe kirji,zuciyar ta sai bugawa take da k'arfi. Yanzu ta samo amsarta da kuma kokwantan ta da ya zama gaskiya... Bata aune ba sai jin hawaye tai na bin kuncinta cikin nikaf d'in. A hankali ta fito daga bayan bishiyar tare da kara k'allo shagon. Murmushi yake harda darawa, ita kuma budurwar sai washe mai baki take tana ta mai zuba,rike yake da hannun wata y'ar k'yak'yawar yarinya fara kamar yayarta. Ji tai wani abu ya tokare mata kirji,da sauri tasa hannu ta dafe gun,ga hawaye yaki ya d'aina malala. Lalle tai wautar kin kula kowa sai Ya Ja'afar da bai furta mata so ba. Ido ta rint'se ganin ya d'akko mata wani had'adan net purple yana bata,wato har kalar da yasha sanar mata yana so ya bata? Tai imani mai irin wannan zankadediyar budurwar fara ba abinda zai da ita Salma baka. Hannu tasa ta cikin nikaf d'in tana goge hawayen dake zuba mata. K'allo sun da zatai taga Ja'afar ya zuba ma inda take ido,har budurwar na k'allo itama,da sauri ta juya gabanta na fad'uwa, kar dai ace ya gane ta? Tab,da k'wa ta bada kanta wallahi. Juyo wa ta kara,sai karaf suka kara had'a ido da Ja'afar. Ba shiri ta tare mai adaidaita ta shige,tana k'allo ya bi napep d'in da k'allo yana girgiza ma budurwar kai. Kawai sai ta sa kuka mara sauti tare da cire nikaf d'in. Lalle tai wautar zurmuwa ga soyayyar Ja'afar, soyayyar da ba'a ma bayyana mata ita ba... Ya Ilahii. ************************** "Oh! Man Ja'afar, dama kana k'allon mata har haka? Bafa koh kiftawa? Murmushi yai mata tare da girgiza kai, "Hala tai kama da Salma ne? Danma da hijab ga kuma nikaf.. "Kusan hakan ne, jikina ya bani kamar Salman ce kam..amma nasan ba ita ba ce ma. Dariya ta danyi har hakorinta farare suka baiyana,kan tace "sannu _Romeo_ toh, ni sallameni kan Amal ta fara neman mamanta, amma ina mamakin yadda ka iya zaben kaya da color, halama kana son _purple_? Murmushi kawai yai mata,kan ya k'ada mata kai halamar eh. Ita kam Salma tana zuwa gida ta taho da yaro a kofa ya kaima mai Napep kud'in shi. Allah yaso ba kowa t'sakar gidan mama na d'aki. A katifa kawai ta zube ta sau kuka,sai da tai mai isarta tai shiru tana maida numfashi. Chan kuma kamar wacce aka t'sikara ta mike zaune. Tabbas Ja'afar bai ta6a nuna yana sonta ba kam,d'uk zuciya ke yaudarar ta. Asalima da "K'anwata" yake kiranta, kila hakan ne tun da,ita kad'ai ke kidanta, gaba d'aya ta gama kore masu sonta ita a dole ta riki Ja'afar. Hawaye ne ya kara zubo mata tunawa da yadda yake washe ma budurwar nan baki. Tasan yadda Ja'afar yake a gaban mata baya wargi,baya sake fuska ma bare har yai musu irin wannan tad'in. "Tabbas budurwar sa ce,nai wauta ni Salma... "Lafiyar ki kuwa kike maganganu ke kad'ai ya sabuwar kamu? Kai ta dago jin batun Ummi tana wannan y'atsine matan. Sai dai ganin irin yadda idon salman yadda yai ja,ga kuma hawaye yasa ta mat'so "Mey ya faru kike kuka haka?.. Ai kamar mai jira a ta6ota ta kara sa wani kukan mai sauti. Tuni kuma sai Ummin ta zauna tana lallashi da fad'in lafiya? Ita de sai kukanta take baji ba gani. Tashi Ummin tayi,"bari na fad'o ki da mama toh,kila k'ya fad'a mata ita... Da sauri ta rike mata riga, "ni ba komai.. Marata ke ciwo da bayana kawai. T'saki Ummin tayi, "Allah kina da aiki a gaban ki Salma,kukan jinya sai kace wata yarinya. Ita dai tana jinta ta karaci kardinta tai waje,a hankali ta zame ta k'wanta,sai sauke ajiyar zuciya take. *By* *Feenat Ja'afar* 庐*NWA* [7/22, 12:02 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 11_Kan safiya har ta gama tunanin abin da zai fisshe ta. Hakan yasa t'saf ta tashi kamar ba ita taci kukan nan ba. Aunty A'i yau za'a kaima wuni,tun (12) suka fice ita da Ummi. Chan suka yini har dare,a kafa ta ratso ita kad'ai sakamakon Ummi da ta biya kar6an _style_. Tunda tazo layin su Ja'afar d'in taji gabanta na fad'uwa, duk da bata koh k'alli hanyar gidan ba. "Abokina ina ka tafi ne daga lissafi kai shiru? "Ba kaga kamar Salma ba waccan mey tafiyar? Ido Garba ya k'wara, da mutum,amma a duhun nan bazai tantance ba,kawai sai ya k'ada mishi kai, "A cikin duhun daren nan ne har zaka gane wake tafi.... Shiru yai ganin Ja'afar d'in yai gaba,da sauri yace "wai mey ke damunka ne? Ina za ka?.. Binshi yake shi kuma yana bin mai tafiya a duhun. "Salma"... Chak! Ta t'saya dan jin kamar an kira ta,a hankali ta juya,da dan tazara a tsakanin su kad'an, amma hakan bazai sa ta kasa gane ya Ja'afar ba koh a cikin dubu,hakan yasa cikin sauri ta juya ta chigaba da tafiya,har dan gudu- gudu sauri-sauri take. "Mey zai fad'a min kuma? Ta fad'a cikin ranta. Har kusan layinsu ya bita, tsammanin shi koh tsorata tayi,amma tabbas wannan Salma ce,kawai sai ya t'saya a dai-dai layin nasu yadda bazata ganshi ba,da hasken inji a layin, yana gani ta t'saya ta waiga,kan da sauri ta shige gida. "Amma fa baka aiki sam Jaa, wai har nan ka biyota kage ma koh aljana ce a daren nan? Juyawa yai yana girgiza mishi kai,"Allah Salma ce,toh yaushe ta dawo?.. Baki sake Garba yace "hadda rantsuwa? In Aljana ce fa mai siffar ta?. Harara ya sakar mishi kan ya juya suka tafi. Ita kam tana zuwa gida Abba da Mama suna t'sakar gida ta shigo sai haki,tuni k'wa Abba fad'a ya karu, kan mey yasa sukai dare? Tuni tai zuru zuru,fad'a sosai tasha,saura Ummi,d'uk da laifin Ummin har sukai daren. Washegari kusan yamma sai ga nan yaro kan ana kiran Ummi da Salma inji su isma'il. Harara Salman ta k'wada ma Ummi, kan tace "yanzu sai da kika fad'i ma mutanan gidan mu kika huta koh? Allah ban san yayi6e ni. Hararar itama Ummin tai mata,"arziki na binki kina guduwa,kowa yazo kice bai miki ba,ki mayi karatun ta nut'su wallahi,dan aure zanyi ni ba jira.. "Keai Kowanne dan chaburos ma yazo Ummi a shirye kike, toh ba dani ba. Yankan farcen Ummin ta bari tai hanyar d'aki tana fad'in"sai kiyi ta zama kar kiyi aure,har mahadi ya baiyana. Cikin kuluwa zatai magana sai ga Mama ta fito a d'aki, ashe d'uk tana jin su, "toh k'wa maza ki wuce ki je tun kan na sa6a miki,daga yau na d'aina zuba miki ido ba fus bare ass Salma... Yarinya sai taurin kai,ace koh kishin yadda y'ar uwarki take shiga take fita da y'an k'wabai ba kiyi? Toh na gaji da gafara sa dan ban hangi kaho ba... Maza ki shiga daga ciki ki g'yara ki wuce... Kai kasa Salma tace "toh.. Ita kam tana mamakin halin Mama har kullum akan su,sai dai tana tuna Ja'afar tuni taji tana da muradin fita,tunda wanda take danshi bai ma san tana yi ba. G'walo Ummi tai mata,kan tai waje tana sai ta fito. Bata aune ba taji mama a d'akin nasu, bani waje ki ga,da kaina sai na g'yara ki... Baki sake take k'allon Maman,aikwa ta zage ta hau cha6a ma Salma k'walliya irin wacce bata ma san mama ta iya ba. Fad'i take "na rasa gane wace iri ce ke Salma,arziki na binmu kina zura da gudu,d'uk wani buri da na sa kanki kin rushe shi, in banda haka a jiya kad'ai kina ga irin bajintar da Ummi ta shigo dashi daga gun isma'il yake ko wa? "Haba k'alle ki a madubi man,san kowa kin wanda ya rasa... Tana yi tana g'yara mata d'aurin dank'wali. "Maza ki fita kan Abban ku ya dawo ya hana ruwa gudu.. Kai ta daga zata d'au hijabi,da sauri Mama ta warce, "g'yale zaki sa matar Malam,koh a Shari'ar a haka ake son a ganki,ta ina za'a yaba in kin maka hijabin? Toh ba walima nace kije ba.. Kai ta k'ada, ta zama tamkar rakumi da akala,sai yadda mama tace. "A'a, ko ke fa,k'alli kanki a madubi ki ga man,ai da banbanci, maza je ki... Kai ta kara k'ada mata, har zatai waje da sauri Mama ta kara kiranta. Turare ta fesa mata,kamar tace ba k'yau mama,sai dai taja tai shiru. "Ki murmusa man Salma,haba..murmushi ma ado ne ga fuskar Y'a mace... A yadda maman take yi bata ma san sanda abin ya bata dariya ba. Allah ya gama su da uwa "LASHE MONEY", har ta fita kuwa tana murmushi, mama sai barta. Suna t'saye gaban wata jar _CRV_ tare da Ummi,d'uk dinsu sun zubo mata ido. Ita kanta tasan tayi ne, fari da manyan ido kawai budurwar Ja'afar zata fad'a mata tasan. Doguwa ce ita dai dai misali,farin jinin samarin zamani,fatarta a goge take mai launin Wankan Tarwada(black beauty), tana gashi ga gashin ido,gata fuska doguwa,gata tana da diri dai dai so,d'uk komai ya ji ba bau ba. Ya dace kam tai amfani da lokacinta tun yanzun. Cikin takun da ba irin na Salma ta da ba ta karasa gun su Ummi,ga murmushin nan dan _beauty point_ din nan sai lot'sa wa yake. Tuni ta kara tafiya da imanin Muzammil,har yake ji kamar ya taro ta kan ta iso. By Feenat Ja'afar. [7/22, 4:57 PM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 12_Ita kanta Ummi tai mamakin Salma da sakewar ta. Sun gaisa da isma'il saurayin Ummin su kuma suka zaga dayan bangaren motar, Kusan kawai d'aurewa take tana mishi yake, amma ita sam taki jinin saurayi mai shegen surutun t'siya. Hakan yasa d'uk taji ta gagu su k'auce, ga tasan Abba gaf yake da zuwa da magriba tayi. Kamar ance daga kanki, Ja'afar tagani kusan su kad'an, tamkar gunki yaja ya t'saya, ga nan wannan budurwar da ta ta6a ganin su itama tana k'allo su,sai ta k'alli Ja'afar, kawai sai ta d'auke kai kamar bata gansu ba. Harda kara bawa Muzammil wani _attention_ na daban tana murmushi. Cikin sanyin jiki ya juya,tana dan satar k'allon shi,a baya budurwar tabi shi tana waiwayen Salman,ji tai kamar ta k'wada mai kira,So ba k'arya bane Salma. Da k'allo Ummi ta bisu lokacin da suka zago ita da isma'il, sallama sukayi,suna kokarin jan mota sai ga wata bakar mota ta _parker_. Ganin su Garba yasa da sauri Salma ta daga ma muzammil hannu tana mishi murmushi. Ja'afar dake k'allonta ta glass din ya rint'se ido da sauri. Ganin zata juya yasa Garba fad'in "Salma" da sauri. Juyo wa tai lokacin da yake yafito Jafar da hannu halamar ya fito. Koh ta kansu Ummi bata bi ba tai gida. Yake tai mishi lokacin da suke karasowa,sai dai koh inda Ja'afar yake bata k'alla ba shi da budurwar shi. Cikin barkwanci Garba yace "duniya da alkawari kuwa Malama Salma?.. Murmushi tai mishi iya le6e, "ashe kin dawo amma koh mu sani.. Karon farko ta k'allo gun Ja'afar, idonshi k'wa a kanta girrr...ba koh kiftawa. Da sauri ta d'auke kai daga kanshi. Gaidasu tayi,budurwar na mata an dawo. Lafiya? A ciki ciki ta amsa,Garba yace "yaushe a gari? An gama lafiya _hope_? Da mamaki take k'allon shi,yanzu dama da wanda zai ce bai san y'an makaranta sun dawo ba? Kawai dai sai ta maze, "yau kusan satin mu da dawo wa. K'allo Ja'afar d'in Garba yayi,kan ya dawo da K'allonshi ga Salman. Ba wannan dawowar ba,yau k'wana uku da zuwan mu K'anwarki tace mana kinyi tafiya... Da sauri ta dago kai da mamaki,tana k'allo gun Ja'afar d'in ya d'auke kai. Garba yaci gaba, "zuwan mutumin kenan daga Zaria yace sai ya zo ya ganki ya miki murna,ashe ke har kin ma fice a garin. Batta bakin magana,dan bata san amsar basu ba,amma Ummi tana mata daya a rayuwa..wai tai tafiya? "Ga nan mutumin jiya har sururu yake yaganki da dare ina mishi t'siya, ashe ke ce. Kai ta daga,kan ta kara k'allon Ja'afar, d'anna wayarshi yake kamar bai wajen. Cikin wasa Garba yace "toh ni zan gabatar mata da ita ko mey da kai mikis?..kasan ba kunya zan ba ni. Murmushi budurwar tayi kai duk'e, dan sam bata ga fuska gun Salman ba. K'allon Ja'afar din take,yayin da yake k'allon Garba yai shiru. "Toh,mu bama sanya, sai ya juyo gun Salman, "Salma ga nan budurwa,kuma matar... Da sauri ta rint'se ido,kan ta karasa da "Ja'afar"... Na sani Malam Garba... D'uk ido suka zuba mata har Ja'afar baki sake,jin shirun yasa ta bud'e ido akansu,yadda suke k'allonta tasan tai su6ul da baka... Cije le6e tai,amma ta bada kanta wallahi.... Dariyar keta Garba yasa harda k'yak'yatawa, sai ta dago tana k'allonshi. Sai da yai mai isarshi kan ya k'allo Billy, "Haba,Yanzu na ji batu,ni fa naga kowa yana sassahan kamshi,ashe-ashe...uhm uhm _Jealousy_... "Toh wannan Matar Garba ce bata Ja'afar ba,sassauto madam. Wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyar ta,har batasan sanda murmushi ya su6uce mata ba. A kunya ce ta k'allo Billy,sai ta mat'sa kusan da ita kan tace "sannu da zuwa... Dariya suka sa mata banda Ja'afar da ya dan dara,idonshi kir a kanta,bazai iya fassara mey hakan yake nufi ba, shin Salma na son sa da kishin sa ne koh mey? Ita dey sai dan satar K'allonshi take,amma bazata iya fassara ina ya dosa ba. Mota su Billy sukai suka barsu,ga nan magriba ta gabato,gaidashi ta kara yi itama ciki ciki,t'sayuwa ya g'yara kan ya amsa,tare da mata murnar kammala karatu,shiru ba mai cewa uffan,kowa miskilin kanshi,kawai sai sukai sallama kan gobe zai zo. Tana shiga gida dan takaici kasa ma Ummi magana ta cikin fad'a."yanzu Ummi kina k'yauta min kenan a rayuwa? Mey Ya Ja'afar ya t'sare miki ne ki ka ki jinin shi? Rai ta had'e, kan tace "oho,kawai bai min bane... Ga nan sakon daga Muzammil,kinga in da ake harka ai... Kai ta k'ada dan takaici tai d'aki batabi koh ta kayan ba. Washegari dan kalata sai ga su sun dawo, ana la'asar, mama ta fita unguwa. Ado Ummi ta ciwo da tafi na jiya,sakare tai ganin Salma koh mot'sawa batai ba. "Koh ba zaki bane Salma? A tunzure tace "ba zani ba.. Baki Ummin ta ta6e,kan ta daga kafada, "mat'salar ki ce wannan kuma... Sai tai waje. Aiko yaro sau biyu ana yi daga waje daga Muzammil amma fur taki fita. A ka'ro na uku ne yaron suka shigo da Mama da ta dawo daga unguwa. Dole ta tashi badan rai naso ba,sai dan ganin Ummi ta shigo ta had'a ta da Mama kan taki zuwa gun Muzammil. Tana had'a rai ta fito,sai dai da mamakinta taga Ya Ja'afar t'saye yana aiken yaro kan tazo. Da sauri ta koma cikin zauren kan ya ganta. Jim tai kad'an bayan fitar yaron kan ta fito,kanta t'saye tai gun Ya Ja'afar, kan tace ya bata minti biyu dan Allah. Kai kawai ya k'ada mata,sai tai gun su Ummi,a mutunce suka gaisa,kan tace da Muzammil sakon shi sai gobe.. Bata jira amsa ba tai gaba. Shi kam Ja'afar k'allonta kawai yake,amma tuni har yazo wuya. Tabbas dole ya bayyanawa Salma yau ranshi ba sai an k'wana ba,dan wannan samarin tsaf sai su iya kasa shi yana k'allo. "Bissmillah, muje zaure... Bai yi musu ba yabi bayanta. Har ya dan saki fuska, dan sam ba kaunar zaman ta a layi yake ba. Bayan sun gaisa yake bata labarin abinda yasa bai je mata ba. "Kinsan Mamana tana a Zaria ne,sun rabu da Abba tun ina dan shekara biyar,hakan ya zamana Abba ya k'ar6e ni a dalilin tai aure,nakan kai mata ziyara haka,sannan dan ita na zabi zuwa Zaria karatu. A _time_ d'in da za ai _visiting_ aka aiko bata lafiya,chan naje har t'sawan wata uku. "Taji sauki sosai,har tana ta fad'an na koma bak'in aiki na,ana haka y'arta K'anwata ta dawo sun gama makaranta,hakan yasa na tuna da Salma.. Nan nai shiri na dawo,duk dan na ganki,sai aka samu akasi, Ummi tace kinyi tafiya... Shiru yai kai duk'e, itama tai tsam tana sauraren shi. "Salma"...kai ta dago ta dan k'alleshi, shima idonshi a kanta. "Yanzu kam lokaci yayi da zan sanar ki wani sirri,sai d'ai ina fatan wani bai rigani yad'awa ba... "Salma"... Cikin wata siga ya fad'i, kan yace "na jima ina dakon son ki azuciyata,tun ma kan Salman tasan itace... K'allonshi take baki sake,shikam ya zage sai tona sirrin ranshi yake a gare ta ido bud'e.. Dad'i, farin ciki har ya kasa misaltuwa a gun Salma,So d'aya ne, tasan Ya Ja'afar tai ma. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 8:59 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 13_Har yai shiru ita kam idonta na kanshi,kan dafa bisani tai kasa da kai cike da kunya,kawai shima sai ya zuba mata na mujiya yana murmushi. Magana suke jiyo wa kasa-kasa,duk sai suka zuba ma kofar ido. "Ba mutunci ace kowa yana wuce wa yana ganin ku a t'saye a titi, gaba na fad'a miki ki nemi koh zaure ne koh cikin gid... Shiru Abban yai dan ganin Ja'afar a zauren da Salma. D'ukawa ya danyi kan yai ma Abban sannu da zuwa. Cikin sakin fuska Abban ya amsa,Salma ma ta mai kai duk'e. Sim-sim Ummi tazo ta wuce,dan duk iskancin ta tana bala'in tsoron Abban su sosai. Yana shiga gida shima yai mata sallama da alkawarin gobe zai zo dan jin amsar shi. Da t'sananin farin ciki ta shiga yau, haka dashi ta tashi. Tun jiyan Ummi ke ci mata kunu, tasan kuma d'uk akan Muzammil ne,shi yasa koh bi takanta batai ba. Washegari tun kan Ummi ta shiga wankan yamman ta na kullum Salma ke gaban mudubi, sosai take k'yali, yau d'aya ta bata lokaci dan Ja'afar d'inta. Ummi da tun dazu ta fito tana jira ta ta6e baki, ''kiyi kare ni ki ban waje na zauna Malama... Juyo wa tai da tana yage mata baki, "dan Allah Ummi nayi k'yau?.. Bar zancen wasa. Baki ta ta6e kan ta juyar da kai gefe, "oho miki ni kar ki daman. Murmushi tai kan ta tashi ta bata gu. Bincike ta fara,a babu babu Mama kala 5-5 ta musu kayan _candy_ na ke ce sa'a, ciki masu ruwan _purple_ ne kusan duk. Cikin nishad'i ta ciro attamfa wata mai _purple_ da rat'sin _yellow_ riga da siket, murmushi tai dan tuna wa da kalar da Ja'afar yafi so kenan. Tunda ta zura kayan ta nad'a d'auri take bin kanta da k'allo a mudubi ta gefen Ummi. MashaAllah tai k'yau, gashin da ya fito ta kasa take turawa cikin dank'wali,ta kai dubenta ga Ummi wacce sai ko'k'arin fiddo nata take tabi dank'wali ta kansu. Murmushi kawai ta mata,tasan da tace ta mayar su ciki ma a iska. Sai dai tana d'akko turare ta hau feeeee ba ko kakkautawa. "Haba Ummi,turaren nan kinsan haramun ne sashi ki fita koh?.. Ga gashi kullum sai ance ki alkinta shi.. Allah kina *TABARRUJ* da yawa.... Galala take k'allonta, kan ta ja t'saki tai waje. Iya wuya Salma tazo, ta bala'in t'sanar t'saki. Ba'a jima ba Ja'afar yazo.. Tabarma yau ta d'aukar musu,shima yasha wankan farin kaya da farin takalmi _half cover_ sosai yai mata k'yau. Yadda yake fara'a da bin k'allonta tasan itama ta wanke shi. Suna t'saka da gaisawa cikin nishad'i yaro yazo,wai tazo a waje inji Ummi. Tuni ya sauya,dan yaga zuwan su Muzammil. "Minti biyu kawai.. Kai ya k'ada mata da dan yake. Tana fita suka ware gefe,tsakani da Allah ta fad'a mishi yai hakuri. Baki sake yake binta dashi har ta kule cikin gida. Amma Ja'afar ya bala'in k'wada shi da kasa,dan haushi koh isma'il bai jira ba yai gaba. Ita kam tana zuwa ta bashi amsa gamshasshiya, wanda tasa fara'ar Jafaririn ta dad'u ba shiri. Tad'i suke kamar ba gobe, mot'si kad'an yace "kinyi k'yau..... Itama cikin kunya tace yayi shima. *************** ************** "Naga sai zarmewa kike fa akan Ja'afar salma,sam

Chapter 2 of 11