Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba mai rigima bace, tabbas da abinda ke damunta yau,yawan kukan ji take kamar itama tasa kukan koh taji sa'ida. Dak'yar ta samu tai shiru,sai ajiyar zuciya take halamar tai bacci. Buta ta d'auka ta shiga band'aki kenan sai gashi kamar an hulloshi gidan,fatanshi yau ya rit'sata garin satar fita. Bintu ya kalla wacce ke murmushin ganinshi,sai taunar cingam take tana kas-kas,kai da ganinta da yanayinta kaga na mai shirin kulla wani sharrin. "Sannu da zuwa.. Kai ya daga mata, kamar kullum zai tambayi Salman sai yaji bud'e band'aki. A fusace ya kallo Bintu, "bayan fita ta Salma ta fita?.. Ki fad'an t'sakani da Allah. Kwai tayi kan ta fasa tare da yin kas dashi, "Eh ta fita,mey ya faru? Yanzun bud'e dakinta ta shiga band'aki ka shigo. Gadan-gadan Salma tayi kanta da butar data cika zatai alwala anjima,kansu farga ta rot'sa mata aka tana huci,bai isa ba ta rufeta da duka baji ba gani,fad'i take "Sharrin naki ya wuce bayan idona yanzu a gaban idona ma yi.. Mari ya d'auketa dashi shima yana fad'in ta sake ta. A fusace tace bazata saka ba,ita kam tamkar wawiya ta bari Salman na jibgarta,ganin da gaske take yasa da sauri ya finciko Bintun tare da kara mata wani marin. Kunci ta rike tana K'allonshi, "ki sani na gaji da halinki a gidan nan, karan nan zan d'au mummunan mataki akanki wall... "Ka sallame ni in ka gaji dani Ja'afar.. Dan ni tuni na gaji da zaman gidan ka, ka sallame ni ka huta toh.. "Haka ki ka ce?.. A fusace tace "eh haka nace.. Tuni shedan ya shiga cikin zuciyar kowa,musamman Ja'afar da ya rufe ido tamkar bashi ba. "Ki je gida sai na neme ki toh... Cikin kuka tace ''Ban isa zuwa musu ba sheda ba,dole ka bani sheda.. Ba tare da jin komai ba mugu(shedan) yasa ya rufe ido. "Kije na sake ki toh.. Chak! Taji kukan ya t'saya sai na Miemie data tashi dan hayaniya. Baki sake take k'allonshi fuska wanke da hawaye. "Ja'afar ka sakeni kace fa?.. Muryarta na ka'rkarwa ta tambaya. Da sauri ya bud'e ido ya dawo hankalinshi kanta. K'allon-k'allo suke ma juna cikin rashin sanin abin fad'a, musamman Ja'afar dashi ya furta. Ido ta rufe a hankali, sai ga hawayen da ya makale sun zubo. A hankali ta bud'e idon ta k'alli Bintu. "Allah ya biya ki da dai-dai abinda ki kamin Bintu.. Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai dawo gun maishi.. Jiki a sanyaye ta juya gun Ja'afar. "Shikenan abin nema ya same mu Ja'afar.. Aure ya kare a t'sakanin mu..igiya uku ka rusheta Ja'afar.. Ka rushe su.. Hannu tasa ta share idonta. "Ba ka da bukatar na t'saya maka bayani yanzu kam,dan ka zuba katanga a t'sakanin mu. Cikin nut'suwa tai hanyar waje ba tare da ta koh waiwayi d'aki ba. Da k'allo ya bita, ilahirin jikinshi ka'rkarwa yake,ya kasa tattara kalma daya da zai ambata, har Salma ta 6ace wa ganinshi. 'By Feenat Ja'afar. [8/2, 10:40 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 31_"Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un.. Allahumma Ajurni fi Musibati,wakhluf li khayran minha... "Salma ki ce min ba gaskiya ki ke fad'a ba Salma?.. Dan Allah ki ce wasa ki ke.. Murmushi take,wanda da zatai kukan zai fi mata alkairi, amma ta kasa,tun zuwanta gidan Aunty A'i ido ya kafe,tunani ya t'saya.. Dabara ta ka re,sai kallo da ido da murmushi da yafi kuka ciwo. Waya Aunty A'in ta d'auka dan kiran Ja'afar, tayuwu koh shi ya mata bayanin da zata gamsu tunda Salma ta zama kurma. "Ja'afar.. "Bashi bane.. Tsam tayi dan tasan Bintu ce ta d'auka. Da karfin hali ta tambayi in yana kusa ta bashi man, t'saki tai mata kamin ta kashewar. Kasa tai da wayar tana mai tabbatar da kalaman Salma na aure babu,ya ka re. A hankali ta sakko ta t'suguna gaban Salman tare da dafa kafafunta. "Salma kimin magana ba shiru ba dan Allah.. A dunkule kika bani, dan Allah kiyi magana, shin da gaske ya sake ki cikon na ukun?.. K'allon Aunty A'in take cikin ido,tabbas wannan kalmar ita ta 6acewa tunaninta. Kan ta ankara ta sau mata wiwi,baji ba gani. "Bintu ce... Wallahi itace.. Ban mishi komai ba..ya raba aurenmu.. Allah banyi komai ba karan nan Aunty A'i,ki yarda dani dan Allah, koh su Abba baza su yarda ba... Kamar karatun yara haka take had'a kalaman cikin kuka. Jiki a sanyaye Aunty A'in ta tashi tazo kusa da ita,sosai ta gane sambatu take,cike da tausayin y'ar uwartata ta rungumo ta, ta abu daya take gane gaskiyar Salma tun a yarinta, shine fad'in abin da batai ba cikin kuka. "Na yarda Salma,na yarda dake karan nan.. Ki bar kukan haka, Allahu yasa shi yafi zama muku alkairi. Ita dai kukanta take. Ina Ja'afar ya gano abinda Aunty A'i ta sani game da rayuwar Salma, da bai bawa CID na fitar ta ba, da ya fuskanci ta sauya tun sa'ilin da in yace ta fita take kuka,da ba ayi hakan ba. ******************* "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'una... Ja'afar mai ya kai ka wannan yanke d'anyen hukuncin kan ku?.. Mey ya kai ka?.. Abinda ya faru yake sanar mishi,gaba daya ya rasa abin yi. "Shin ka tambayi ta fitan koh bata fitan ba?.. Koh har yanzu kai baka hango hankalin Salma ba ne.. Kai ya k'ada mishi "Ba wannan ne karon farko ba,ni nasan Salma fiye da zaton ka.. "Ka kuma yarda da Bintu fiye da yarda ka bawa Salma yarda koh ka ke nufi?.. Murmushi yayi na takaici, "Ja'afar bakasan sharri irin na mata bane.. Da baka ba Bintu amanar aurenka sukutum ba Allah. Tayu ka tafka babban kuskure na fahimtar Salma karan nan.. Amma ka yi bincike, shine t'sarin Shari'a.. Ni na shiga gida. Da kallo yabi bayan Garban, duk maganar shi gaskiya ce,kuma ba daya daga ci da ya aiwatar kamin komai. Yau daya yaga fushin Garba karara kwance a fuska,tabbas haushin shi yake ji shima,kamar yadda shima yake jin haushin kanshi da kanshi. Jiki ba kwari ya tada machine yai gida. Dole ya tit'siye Bintu ta sanarshi gaskiya. Bata d'aki,ga nan wayarshi da ya manta da tata akan gado halamar tana sana'ar tata ta charting. A garin ya d'auki tashi ya danno screen na Bintun, haske ya baiyana halamar tana ma kan charting din tai wani waje. Kwanciya yayi da bayanshi jiki duk a sanyaye,bazai iya bawa wannan ranar suna ba. Ido ya kura ma wayar Bintun kirar _Techno_, zai so yau yaga mey ke debe hankalin ta zuwa Facebook. *Bintu U*. _"ke an saki shegiyar fa,ki tayani murna zan sakata in wataya_.. *Shining star*: _"Kai matar nan baki da dama,a bani satar amsa dan yanzu na dawo makarantarki_.. Da azama ya mike zaune dan ganin charting din. *Binta U* _"Hhhhh,tuggu dai kamar kullum nayi,sai dai na yau mai zafi ne,dan jiya an bani sa'a har gida, take ina fad'in ta fita ya d'anna mata saki,baiwar Allah harda dan guntun wa'azin ta ta min hhhhh_.. *Shining star* _"ina ma zan iya irin wannan sharrin naki dana huta, sai dai tawa tasan takan duniya,ina mata take dawo min da abu na_.. *BINTU U* _"ba gari daya muke ba,da wallahi taci karya,ni zan baki maganin y'ar banza_... "Ya Allah... Kai shafo cikin ranar jiki hawaye na zuba, da sauri ya d'anna _previous chat_ Sai gata kamar an jehota da buta a hannu tana zare idano na munafukai. Sam bataji koh dirin machine dinshi ba,sai arbawa tai da takalmanshi. Da d'ukkan hannu biyu ya dafe kanshi yana hawaye,mey zai ma Bintu ya huce da bala'in da ta jawo mishi?.. A hankali kalaman Salma ya dawo mishi, _"Allah ya biyaki da dai-dai abinda ki kamin Bintu..Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai dawo gun maishi_... Gashi tun kan a kwana ya dawo ma Bintu bata shirya ba... "Ka dawo..yaushe ka shigo..ban banji shigowar ka ba.. Da in'ina take maganar, ganin yadda hawaye ke diga a kafafunshi ga kuma wayarta a hannunshi tasan yau karya ta kare. Ido ya goge kamin cikin nut'suwa ya ajiye wayar kan gado ya k'allota. "Tabbas kinyi nasarar rabani da d'ukkan farin cikina Bintu.. Kinyi nasara,tanan kam nasan kin ma Salma fincinkau,dan ita bata sharri.. "Na baki d'ukkan wata amana,ki mayarni shashasha.. Ki nunan yau abinda Salma take gudu a kishiya,"makirci".. "Amma ki sani,wallahi!,wallahi!!.wallahi!!! Uku,yadda kikai sanadin 6allewar aurenmu da Salma kinyi naki. "Kamin nan zaki ji jiki kamar yadda ki ka sa taji t'sawan zaman ku.. Kan tai kwakwaran mot'si ya hard'o ta, ta ko'ina mari yake bata iya karfinshi tana ihun jama'a su ceceta.. Sai da tabbatar ya taga wuta dan mari kamin yana haki ya nuno ta. "Kije kema,na yanke igiyar aurena dake kanki har guda uku... "Tun kan ki kwana maganar Salma ta kar6u gun Allah... Ihu ta saka tana bashi hakuri kan ta daina, "dan Allah karka sake ni... Hanyar waje yayi yana sa waya a aljihunshi. "Ki tabbatar baki kara awa d'aya cikin gidana ba,dan saki uku na furta. Waje yayi ya ja ya t'saya a zaure,tamkar wani yaro ya rushe da kuka mai tsanin ciwo.. Yayi kuskuren da dak'yar ya g'yara shi cikin rayuwarshi.. Yayi kuskuren da ya bari Salma tai mishi nisa... Yayi kuskuren kin kar6ar shiryiwar Salman sa.. Tabbas ya tafka babban kuskure a rayuwa. "Allah ya isa t'sakani na dake Bintu... Ubangiji yai ma Salma sakayya akanki daga yau har ranar sakamako... Allah ya isar mata cikin sauri.. Ganin hakan ba mafita bace gareshi yasa ya d'akko waya hannu na ka'rkarwa zai nemo Garba yaga kiran Aunty A'i na dazu. Garban ya kira,dole ayi wacce za ai,Aurenshi da Salma mutuwa ce kadai zata raba. Da Allah ya had'ashi cikin muryar kuka kan yazo gidanshi yanzun nan.. "Isha'i ake kira fa Ja'afar.. "Dan Allah kazo,in bakazo ba komai zai iya faruwa... Ba'a fi minti goma ba yazo,fatattakar arziki yai ma Bintu ta bar gidan ya rufe ya fad'a mota. Da t'sananin mamaki yake k'allon abokin nashi, a iya abotarsu bai ta6a ganin koh da hawaye na Ja'afar ba bare kukanshi mai sauti irin haka. Dan Ja'afar namijin duniya ne,Jarumi, kuma jajirtacce, yasan komai ya sashi kuka ayau ba karami bane. "Gidan Aisha zaka kai ni yayar Salma.. Baki sake yake k'allonshi, "Yayar Salma kuma?.. Ido jajir ya kalloshi ba halamar wasa,dole ya tada mota suka d'au hanya. Waya yai mata kan ta fito yana kofar gida. "Malam mijina ya fita..kai hakuri.. Kit ta kashe wayarta,yau Aunty A'i ta d'au zafi ya sani,tabbas kuma Salma na gidan.. Murfin motar ya bud'e a fusace ya fice Garba na kira.. Kofar a bud'e take,kawai ya tura ya shiga, nufinshi a d'aureshi bayan yaga Salman. "Salma!,, Salma!!.. A tunzure Aunty A'i ta fito a parlourn dan tsayarahi shiga mata parlour. Yadda taganshi bata isa hana shi ba ganin Salman, dan g'wiwa biyu ya zube gabanta tamkar yaga Salman. Hanya ta bashi ba musu,da zafin nama ya mike ya shiga parlourn, bata zata ba taga mutum a kanta,da sauri ta zabura ta mike tana kwad'a kiran Aunty A'i da sauri. Bata nufa ba taga mutum zube a gabanta kanshi a kasa. Ido ta rint'se tare da kawar da kanta,koh kadan bata son kara ganin Ja'afar a rayuwarta Abadan. Juyo wa tai da niyar surfa mishi ruwan bala'in da ba shiri zai bar gidan,sai dai mey? Da t'sananin mamaki take kallonshi tana k'allon Aunty A'i. Hawaye ke malala a idonshi kamar wanda ya rasa jin dad'in rayuwarshi,abin g'wanin ban tausayi. Ja'afar?.. Kuka ma?, a namey toh?. "Salma gani gabanki, a matsayin wanda ya tafka miki laifi cikin rashin sani,da kuma sharrin Bintu..Salma kiyi hakuri,wallahi _am really really sorry.. Kar ki barni dan Allah.. Zan tagaiyyara Salma.. Zan zauce.. sharrin Bintu ne,kuma itama ta amshi hukunci,dan na saketa kamar yadda ta jawo mana, _please_ Salma _forgive me_... Wallahi _I can't live without you anymore_,ki tausaya ma mijinki uban yaranki... Baya taja da sauri ganin yana kara kusantota. Da sauri Aunty A'i tai waje jin kuka zai kubce mata.. Dole haka zata kasance dasu Salma,ranar rabuwa, rabuwar da ba a da tabbacin za'a dawo ta.. Tabbas tausaya wa rayuwar su,dan a irin soyayyar nan ita ce ake kira *Mutu ka raba*.. Gashi yanzu K'ADDARA ta raba masoyan biyu. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:24 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 32_Kuka take yanayi iya karfinsu, tabbas K'ADDARA ta rigayi fata, duk kuma yadda ka t'sara rayuwarka sai ka ga ba haka ya tafi ba,tabbas ta Allah itace daidai. Baya tai ta zube kan kujera da6ar.. Duk sunyi kuskure, kowa na da laifi,meyasa ma tace ya saketa?.. Mey yasa?.. Le6e ta cije tana mai sa d'ukkan hannunta biyu zuwa fuskarta, kuka kam yau har sunji ba dad'i. A hankali ta dago tana K'allonshi ido yai luhu- luhu,duk ya marairaice mata hawaye na zuba, tafi tausayin kanta sama dashi, Kokarin magana take su Aunty A'i sukai sallama ita da maigidan da taima waya. Fuska Ja'afar yai saurin gogewa ganin yadda Abban Aslam ya sau baki yana kallonsu,bai tunanin abin ya kai haka ba, kuka a gaban mace da zubewa g'wiwa biyu?.. Lalle yasan abin babba ne. "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Itace kalmar shima da ya fad'i bayan yaji mai ke faruwa.. "Dole aje gida kowa ya samu labari,dan wannan ba abin a 6oye bane koh da za'a nemi sulhu,saki ya cike na uku abin yafi karfin zama anan Ayush.. Zamu tafi da Salman kai Ja'afar sai ku taho da abokin ka. Har kusan goman dare ana abu daya akan zancen saki. "Ka ce kayi saki,ita tace ya zama uku, sannan kana zancen ai sulhu koh? Kai ya daga da sauri, murmushi Abban yayi,abin yaso ma bashi dariya, "Wato Ja'afar... "Malam Umar wannan zancen ba zancen da za'ai wa sakwakwa bane,kan Ja'afar ya dawo. "Kai kuma in dan baka tashi mun wuce ba zan mugun sa6a maka yanzun nan.. "Kana hauka ne?.. A wane garin ka ta6a jin anyi saki d'ai daya har uku kuma ana neman sulhu?.. "Ai baka fara ganin komai ba Ja'afar, ba dai zuciya ba?.. Za ta sa ka dana sani, "Malam Umar ai hakuri bisa wannan K'ADDARAR da ta sakko mana,zamani ne yanzu muke ciki da yara basu dauki saki a bakin komai ba.. Tashi yayi yana bawa Abban Salman hannu,kan ya kallo Ja'afar,har yanzu sautin kukan su ke fita shi da Salman. "Muje koh?.. Salma ya dago ya kalla da sunkuyar da kai, "Salma dan Allah ki basu hakuri kar su rabamu,kin san bazan iya rayuwa ba ke ba,Abadan Salma...Please. Kuka ta kara saka mai karfi, t'saki Abba yayi ya karkade riga yana nuno shi cikin fad'a. "Hauka kenan wannan, dan koh a musulunce Salma ta haramta a gare ka..ta haramta har abada,dan kai kam ka nuna mana bazaka ta6a iya rike aure ba, saki tamkar wasan yara? Itama waccan wai ka mata saki uku?.. Toh koh aure Salma tayi na fad'a maka ta haramta a gare ka har abada,kaje kaci zuciya. Da gudu Salman ta tashi tai d'aki tana kuka.. "Haba Alhaji, abin bai kai haka ba,kuskure ne kowa yana iya tafkawa a rayuwa.. Anji bai k'yauta ba,amma kar hakan yasa kai mishi baki,kai hakuri. "Hakuri shine ya biyo ni yanzun nan.. Wace iriyar haukace wannan kamar a jahiliya?.. Wani yai mishi sakin?.. Haka Ja'afar naji na gani yai waje yana waiwayen dakin da Salma ta shige yana hawaye. Tun daga ranar duk suka zama sakwa- sakwa, barin Ja'afar da baida kuzari,ga Abba ya sako shi gaba ta ko'ina.. Dan har gida iyaye Bintu suka zo sukai ma Abba rashin k'yauta wa akan yadda bayan saki uku sai da aka kumburawa ya'rsu fuska,harda ikirarin koto,dak'yar aka basu hakuri kan suka debe kayanta, ranar Abba yayi takaici har yaji ina ma da ya barma Umman shi Ja'afar,kila da baici karo da bacin ranshi ba. Sai dai yace kayan Salma koh sama da kasa zasu had'e ba mai diba, ashe ma in ya bari aka diba sun rabun kenan... Ja'afar mat'sala. Anyi ban baki, Abba yayi fad'an ya dawo lallashin amma Ja'afar ba sauki,kawai sai Abban Salma yace a rabu dashi,dole in ta tashi aure zai bari a diba da kanshi. Kullum ta Allah yana kan jelar gidan su Salma,a wata guda har kama ya sauya,ba aski,ba g'yaran fuska,ya zama tamkar zararre. Sosai Abba yake tausaya mishi,Mama kadai ke shafawa idonta toka ta hana ya ga Salman,sai dai a bashi Miemie, haka zai gaji har ya tafi,sai dai tai ta ganin text na ban hakuri,gobe ma zuciya zai dawo. *************** *************** Rayuwa irin ta kunci kam sun ganta a wata hudu da ta gabata. Salma ta saduda sosai akan Ja'afar,dan har yanzu shi yana kan bakar shi. Sam in ka ga Salma ta sauya,ta dawo shiru shiru sosai,kullum zaka same ta a daki,koh ta dukufa tunani, koh tana k'allon Miemie tana hawaye. "Salma... Gefe tayi da sauri da kanta tana goge hawayen jin maganar Mama akanta. Dole yau ta kawo karshen matsalar nan. Zama tayi a gefen gadon tana kare mata kallo. "Rayuwa fa kullum sauyi take Salma,amma banda taku, ni dai ban ta6a cin karo da kulafucin D'a namiji irin naki ba, wata hudu ba kwana hudu bane Salma.. "Lokaci yayi da za ki cigaba da rayuwarki ki manta da kashin Ja'afar.. Ki d'auka Rabon Miemie kawai ya had'a ku,ki manta da rayuwar da,dan ta wuce,ki fuskanci zahiri a rayuwar gaba Salma.. Fad'a Mama ke ta mata tana kuka, taya zata mance Ja'afar?.. Taya zata mance zaman su?..Soyayyar ta da Ja'afar had'i ne na Allah a ganinta ba wai wani rabon Miemie ba... In har Ja'afar na bata haushi bai wuce yadda ya dankara mata saki ba ba ji ba gani,amma bacin hakan,tabbas bata da sama da Ja'afar a zuciyarta kawo iyanzu.. "Nasan da kin gama iddar ki sarai... Da sauri ta k'allo Mama da t'sananin mamaki, kai Maman ta kad'a mata. "Tunda ki ka zo gidan nan ina fuskance dake Salma,kin gama iddah tun wata uku da suka wuce. Kasa tai da kai tana goge hawaye,tasan Mama gaskiya ta fad'a, dan shayarwa bai hanata period ba.. "Nasan ma hakan ne Salma,yanzu abinda nake so dake shine, "Dole ki fara fita,dan saki ba takaba bace, bazai yu kiyi ta zama a gida ba kamar matar kulle,tun yanzu zaki fara fuskantar cigaban rayuwa,bana son musu koh taurin kai Salma a zuwan nan daga gunki, dole komai nace kiyi kiyi, kina jina koh?. Shikenan kuma,ta faru ta kare,wai an ma mai dami daya sata.. Shikenan ta shiga sahu,yanzu sai jiran bazawari.. Kuka ta sa mai sauti,yi take ba kakkautawa,har ta kular da Mama ta bar lallashi ta hau sababi. Dole kam in dai ta yadda da K'ADDARA ta maida komai ba komai bane.. Dole ta daina yaudarar zuciyarta,tana biya zancen Ja'afar a kullum akan tashi ce shi kad'ai.. Hannu tasa ta share hawayenta,kan ta g'yara zama. "Na shirya bin umarnin ki Mama matukar bai sa6a shari'a ba.. Baki Maman ta washe, "Koh ke fa,yanzu naji batu,ko ke fa Salma. Kasa tai da kai tana murmushi, sosai taga farin cikin Mama. Washegari da dare bayan Abba ya dawo taje gunshi suna zaune da Mama,yai mamakin sauyawarta faradd daya,shima sai murmushi yake mata. "Abba.. Zama ya g'yara da murmushi ya amsa. "Abba makaranta nake son shiga dama... Da sauri Mama ta kallota, ji zata kwafsa musu kuma,wai makaranta? Baki ya washe dan murna. "Toh Salma,kinyi tunani mai k'yau, Allah yasa a shiga a sa'a. Kai kasa tace "Amin Abba... "Anjima ina son zan k'waso akwatina na a gidan Abban Miemie koh da y'ar makota ne.. Kai ya kad'a mata "A'a,ki bari zan ma shi Ja'afar din magana zai kawo miki har gida. Sosai sukai fira Mama na jinsu bata ce kala ba,tana shiga d'aki Maman ta bita. "Ya zaki min haka Salma?.. Wace makaranta kuma ana zaune lafiya?.. Shiru tai sai da ta gama kan tace ba abinda karatunta zai tsare mata,tai hakuri tasan zai mantar ta wasu abubuwan. Ba dan taso ba ta yarda. Ta gama da Mama, saura Ja'afar. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:25 AM - Queen Safiyyert馃憫: A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 33_Washegari Abba da kanshi ya samu Jafar din a shago,duk da yai jim,daga baya ya tuna da wannan ne damarshi na ganin Salma a yau dan tuna mata da alkawarin shi. Da yamma k'wa yasa Garba ya k'waso mata akwatinan ta da sauran sabbin kayanta marar dinki. Da sallama ya shigo gidan, ya k'wa taka babbar sa'a Mama bata nan. T'saye yayi ganin Salman t'saye a gaban famfo Miemie na mata kukan kunu tana dauraye murfin feedern. "Sam baki da jimirin yunwa Miemie,kimin hakuri yanzun zan... Itama shirun tai dan jin sallamarshi. Da dan rarrafe da tafiyar da batayi kwari ba ta nufi gun Abban da murna. Ganin Miemien ne yasa shi dawo da hankalinshi kanta,sama yai da ita kamar kullum suna dariya. A hankali ta rufe idonta tanajin zuciyarta na bugawa da sauri,kusan wata 2 rabonta da ta sashi a idonta,jin takunshi na kusanto ta yasa ta juya da sauri tare da had'iye hawayenta. Ya sauya mata,duk ba g'yara, har wata kasumba ya had'a ta dole ta rashin g'yara fuska. Da t'sananin murnar ganinta ya karaso sai washe baki yake,da sauri tai baya ganin abinda yake shirin yi tai gun taburma ta d'akko,sai ya bita da kallo baki sake, tabbas Salma batai kewarshi kamar yadda ya mato a kewarta ba.. Koh irin d'aukin nan na ganinshi t'sawan lokaci haka bata yi. Dan dukan da Miemie take mishi ne yasa ya kallo ta,da hannu take nuna mishi kan feedern dake hannun Salman. Kan taburmar ya nufa tare da zama,so yake sai ya fassara yanayin Salman,shi yasa yake ta k'allonta. Feedern ta mika wa Miemie tana dan satar kallonshi kan ta kau da kai tace "Ina wuni.. Shiru yai mata,sai ta dan kalloshi cikin ido,shima ita yake kallo,bazata iya kallon kwayar idonshi ba,zata chaza mata matsala,da sauri ta kara dauke kai tana maimaita gaisuwar. "Mey yasa kwana biyu ba k'ya d'aukan kira na Salma?.. Ba k'ya ban amsa koh na miki text?.. Gefe ta kara yi da kanta tana kallon wani waje, kan tace "Ban gani ba ne.. Da mamaki yake kallon yadda tai maganar cikin nuna ko'in kula. "Salma kin daina so na yanzu koh?.. Yadda yai maganar yasa jin wani iri da dan tausayinshi,da jihadi ta juyo ido cike da kwalla. "Ya Ja'afar, ya dace mu fuskanci zahiri fa yanzu,mu daina yaudarar kan mu dan komai ya afku..Dole nai aure ka sani,ban maka alkawarin zama ba aure ba,bazan maka alkawarin kin kula wani ba.. Yanzu haka karatu zan koma,ka d'auka rayuwar da ta shud'e a mafarki muka yi ta, yanzu mun farka... Dole akwai cigaba a rayuwa.. Kai hakuri, amma bani da alaka da daukan kiran ka yanzu,ka manta Salma dan Allah,mu fuskanci rayuwar gaba.. Kai ta kautar tana goge hawaye, shi kam k'allonta kawai yake ba koh kiftawa. "Ke nan kina nufin son da nake miki karya ne?... Soyayyar mu hasashe ce Salma?.. Zaman mu da rayuwar auren mu wasa ne?.. Kina nufin Miemie ma mafarki ce?... Da fusata yake tambayarta,kai kawai take girgiza mishi tana hawaye. "Ba haka nake nufi ba.. "Toh mey ki ke nufi?.. Shiru tai tana cigaba da kukan ta,sai ya kada kai cikin takaici. "Salma kin d'aina so na kam.. Girgiza mishi kai tai "Ina sonka Ya Ja'afar, har karshen rayuwata.. Abu daya nake son ka gane,yanzu komai ya sauya,alakar Mimi ce kawai ta rike mu... Ka cire son zuciya aciki, dan bazan iya haramtawa abinda Allah ya halasta min ba.. "Assalam Alaikum, wannan akwatunan fa a zau... Tsaye tai ba tare da karasawa ba, kai kasa ta amsawa Mama sallama,ciki Maman ta karaso,ya gaida ta kai kasa,duk shiru sukai ba mai magana, sai muzurai Mama take ma Salman kan ta shiga daga ciki. Jiki a sanyaye ta tashi ta shiga ciki,a hankali ta sa kanta a kan katifa tana hawaye. Ba dan yaso ba ya tashi yai fita,tare da shigo mata da akwatunan ta. Har zauren Mama ta bishi ta sa sakata tana sababi kan tai gun Salman. "Wai ke baki da hankali ne Salma?.. Meye had'inki da wannan da har zai shigo cikin gida ki bashi taburma, har ki zauna a gabanshi kina wannan shashancin cin?.. Mey fa rabawa(K'ADDARA) ta raba ku har abada. Shiru tayi har Maman ta gama tana ta kok'arin shanye kukanta, ta sani da koh tayi bayani Mama bazata gane inda ta dosa ba. "Kiyi hakuri bazan sake ba. Kai ta k'ada tuni har tai laushi. "Ina kuje miki yaudara irin ta D'a namiji ne Salma,gaba in kina mishi haka sai ai abin kunya. Shiru tai tanajin wa'azin Maman kawai. G'yale ne kusan kala 5 had'add'u,tana washe baki ta fito dasu daga leda. "Ki zabi na za6a ki darje,dan zawarcin ki sai yafi y'an matanci a komai Salma, gobe kayan k'walliya zasu zo dan na bawa Hajiya Jidda kud'in kayan g'yaran jiki,ga wata yayi nisa da komai kin samu akan lokaci.. InshaAllah sai mun cike gurbin da muka rasa.. Ni da zakiji shawarata ma da an yaye Miemie a satin nan a mikata ga gidan su chan ya karata... Da sauri ta dago tana kallon Mama, Kat'seta tai da fadin "Eh man,bashi yake ikirarin yana kawo shi ba?.. Toh zamu mayar mishi da abarshi kawai. Kai ta hau girgiza ma Maman,Allah yaga ba mai rabata da Miemie sai aure. "Mama Miemie fa karama ce,kawai tai saurin tashi ne,koh fa wata tara bata cika ba.. Dan Allah kiyi hakuri,dan ba abinda zata t'sare min koh a makaranta. Harara ta aika mata, "Kina nufin da ita zakina fita?.. Kallonta take ta rasa amsar ba Maman. "Toh da sake wallahi, ba yadda za ai ina tufka kina bin bayana da warwara.. Zawarci da goyo?.. Toh da sake,dan ba mai gani ya kulaki alhalin kina sa6e da y'a. "Aikina fitarshi ta naga dama ce,in ma kince baza'a mayarta ba ni zan na miki renon,aje a dawo lafiya. Shiru tai tana jinta kawai. Washegari sai ga kayan k'walliya jibgi,su mascara, eye shadows,su sabulun g'yaran fata harda su man gashi,ga haddun man gyaran jiki,lalle Mama da gaske take. Shi kam tunda ya koma da yazo k'wanciya yake tuna dazu,lalle in Salma tasan wata toh bata san wata ba. Tazo k'wanciya taji karan wayanta,agogo ta duba, tasan ba mai mata haka sai mutum daya. Badan taso ba ta d'auka, sai dan jin dame yazo. "Naji kije makarantar, amma bisa sharad'i uku.. Baki ta bud'e cike da mamaki,wai koh ya manta bata karkashin ikon shi ne yanzun? Dan dai taji sharad'in tace tana ji. "Good. "Na daya kafarki toh kafar Miemie duk inda zaki shiga. "Na biyu ba zancen yaye sai Miemie ta cika shekara biyu kamin kiyi komai. "Na uku,fitar ki sai da nikaf da hijab,sannan ni zan sama miki mai kai ki a Napep ya d'akko ki in kin gama, dan ba ko wanne kato zai na d.. "Ka ga malam,ka bari ka fad'awa Miemie wannan dokar taka ba wai ni da nake Salma ba... Dan ba y'ar ka bace ni,ni nake da damar t'sara rayuwata yanzu ba kai ba. "Abu daya nasan na yarda zan iya shi,shima dan hakkin ka ne dole,shine yaye Miemie,zanyi yadda kace, sauran kuwa ba huruminka bane... Wayar yabi da kallo baki sake jin ta kashe kit.. Lalle Salma ba ta so zaman lafiya ba a garin nan, amma zata jidi mamakin shi. Dan shi tai mishi daidai ma da zata tafi makaranta. Tun daga ranar ya daina kiranta a ganinshi zata damu ta bashi hakuri ayi yadda yaso,sai dai ta daure ita. Ana haka ranar Abba yace ya batun makarantar da yace zai koma?.. Kanshi t'saye yace ya ma Abban ai ya fasa. Nan ya bud'e mishi wuta kan bai isa ba,duk haukar da yake ranar ya samu labari gun Mama,dan har gida tace ai mishi t'sakani da Salma,sai dai yazo za'a bashi Miemie in dan ita ne. Sosai yaji haushi,yasan aikin Salma ne..shi yasa ya d'auke mata wuta,sai dai ya tura k'annenshi

Chapter 8 of 11