Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta shiga har baya misaltuwa, dan da yanzu dabarar yin wanka ba tazo mata ba da tuni ansha da ita an gama. "Ba dai ya maidaki ba naga kina murna tun yanzu Salma?.. Yanzu ke bazakiyi kishin kanki ba har kin bada kai daga fita bori ya hau?.. Ina laifin ya samo Abbanki da maganar in dai da mutunci aciki... "Au dariya ma na baki koh Salma?.. Ga shash.. "Mama ni fa ba aure a t'sakanin mu da Alhaji yanzu,dan tau nai iddah ta.... Baki sake take kallonta,dariya tasa ta bata labari,sai ga Mama na tikar dariya. "Lalle yarinyar nan da wayo ki ke,kwarai kinyi dabara, dan sam mutumin ya sane min, dan ban fad'a miki bane,ba'a fi sati da dawowarki gida ba muka had'u da dan talikinnan,d'auke kai yai kamar bai ganni ba fa,bayan sarai mun had'a ido.. "Shi yasa yaron nan Ja'afar nake ganin kimarshi har kullum,dan koh bayan rabuwarku yana daraja mu,musamman zai sa azo har gida abokinshi yai mana goma ta arziki in sun d'au Miemie... Shiru tayi tana sauraran maganar Mama, wai Ja'afar take ma ya6o haka da kirari?.. Farin cikinta a yau bai misaltuwa,ina Miemie na nan ta rad'a mata itama suyi tare,tasan dai duk inda take yanzu tana neman gida,dan tun dazu tai mata kwalliya da kayan Abbanta kaninshi yazo ya d'auke ta. Murmushi tai tana jijjiga kai. Lalle ne *Duniya Labari ce* By Feenat Ja'afar. feenat-jafar.my wapblog.com Feenat Jaafar's Mobile Blog feenat-jafar.mywapblog.com Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 9 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 43_Waya yake d'annawa a nitse yana duba sakon waya kamar bayaso,kamili ne,da hasken shi,sajenshi a yanzu shine sirrin 6oye kyanshi na ainashi, sanye cikin kananan kaya da glass manne a idonshi,da gani yana ji da ajinshi a dai- dai lokacin nan,dan miskili ne yanzu na karfi da yaji. A yanzu ne yake tsone idon y'an mata musamman na jami'a, dan ya iya t'sare kai da tsare gida. Rayuwarshi ta sauya,dan ya dawo ainashin halaiyar shi ta da,koma yafi da din, Ja'afar kenan,namijin duniya. Dago kai yayi yana duba yanayin garin da yadda kowanne shago suke hadahadarsu,sai ya sauke kai kan Abdull mai tahowa dauke da baby a kafad'a tana ta washe baki tun kan ta karaso. Tuni fara'a ta maye g'urbin rashin walwalar shi,kashe wayar yayi tare da ajiye ta gefe dan tarar gudan jininshi,duk Abba dake gefe kad'an yana kallo. "Abbaaa... Miemien ta fad'a lokacin da yake k'ar6ar ta,murmushi yayi mata tare da shafo fuskarta "Na'am Miemien Abba.. Sai ta washe baki. Ciro changi ya mika ma Abdull, "Kan magriba kazo ka maidata kaji?... Kai ya kad'a tare da amsa yayi godiya. Zama yayi tare da d'aura ta cinyarshi, Tasha kwalliya da rigar da ya yo mata tsaraba cotton ja da pink,kan nan kamar an mata shampoo sai kyalli yake yasha ribbons.. Hannu yakai kan dan beauty point nata ya latsa sai ta sa mishi dariya. A hankali shima yayi har hakorinshi suka baiyana. Tashi yayi zuwa gun Abba dan mishi sallama,kai ya kad'a Miemie na mishi bye-bye tana dariya. Kamar kullum nai yai ta yawo da ita suka sai ice cream suka nufi gidan Garba nan suka yada zangon su. Miemien Garban ya kallo yadda take tsalle kan Abban nata shikam sai murmushi yake mata. "Abokina ina so yau dai daya ka saurare batu na,sama da wata hud'u dana fara ma magana zaka ce a'a kai baka so.. Kallonshi yake jin inda yake neman dosa,tuni ya fara sauya kama. Ba tare da yabi ta kanshi ba Garban yaci gaba "Salma fa au... Cikin t'sananin fushi ya rufe ido tare da daga mishi hannu. "Dan Allah ka d'aina dawo min da hannun agogo baya,ina a cikin farina yanzu,banson jin sunan wata Salma chan.. Gefe yayi da kai yana chunkune fuska,kai Garban ya kad'a kan yai y'ar dariya, "Karyar banza kenan,yanzu da zance Salma tana gida an sakota da nasan ba wanda zai farin ciki a yau,kaine fa.. Baki sake yake kallonshi, "kana sanin abinda zaka fad'a man malam.. Matar mutanace fa yanzun. Murmushi yayi yana mishi k'allon bakasan komai. "Toh auren Salma ya rabu tun wata hud'u da ya wuce,sai ka kurbi ruwan sanyi ka huce.. Baki sake yake kallonshi ba koh kiftawa. Baya Garban yayi da kai yana shafa ha6a tare da daga mishi gira,ya dan jima a kame kamin ya d'auke tare da wayance wa. "Wannan bazai sauya komai ba kama ji da wai,dan ban manta abinda ta dirka min ba a baya.. Kama d'aina wata dariya.. Kafad'a Garban ya make,kan yace "Daga baya kenan kuma,chan ta matse ma,dan nasan yau sai kafi kowa farin ciki a garin nan,karyar kawai. Tashi yayi yana daukan Miemie tare da hararar shi, "Kanka ake ji,ni nayi kaga tafiya ta.. Dariya yai kan ya mike dan sauke su, "Kaima an kusa jin naka soon. Harara ya sakar mishi kan suka fice yana ta mishi t'siya. ***** "Mama zan tafi,a min adu'a Allah yasa kar na samu mat'sala kamar yadda principal yace.. "Amin kam, in Allah ya taimaka zasu karbi uzirin.. Kai ta kad'a, ''Amin toh, na tafi kan wannan ta farka. Da sauri ta fice ganin zatai latti. Allah yasota tana zuwa wata Napep zata tashi ta d'au wani da dan sauri ta t'sayar ta shiga ba tare da ta dubi na ciki ba. "Dan Allah ka taimaka school of... Shiru tai jin wani kamshi da ya bigeta,turaren da koh ajikin wani taji,toh mutum daya ke zuwa ranta. A hankali ta waiwaya dan ganin waye masanyin turaren. K'yam tayi tana kallonshi da murmushi ba koh kiftawa, shima hakan take,kan da sauri ya d'auke kai kamar ma bai ganeta ba yake nufi.. Dad'i ne..koh farin ciki a ranta a safiyar yau.. *Ja'afar* Wannan shine yaushe gamo. Kokarin mishi magana take yace da mai Napep ya t'saya. Ba musu yaja ya t'saya, da mamakinta taga yana kokarin sauka a Napep d'in, da sauri mai napep yace "Kazo gaba toh. Ba tare da ya kalle yace "Kai hakuri,bana shiga keke da mata... Gaba yai ya batta baki sake.. Kuturu,wa ya ga turnuku... Ji tai tamkar ta d'aura hannu a ka ta kurma ihu,wai ita Ja'afar zai haka?. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:44 AM - Queen Safiyyert馃憫: Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 45_Washegari kowa da farin ciki ya tashi kamar ma ance an shirya. Yau tana son ta koma Salmanta ta da ne. Yau shima yana son komawa Ja'afar d'inshi na Salmateen shi,dan haka tun wuri yaje yai g'yaran fuska,ya rage sumar kai,tuni ya hasko kamar zamanin angoncinshi da Salma. Gun Garba yaje yasha kwalliya kamar wani sabon ango. "Ya mutumina nayi kyau kuwa?鈥� banda shakiyanci pls. Daga sama har kasa yake kallonshi,yai kokakarin 6oye dariyar shi. "Kayi man,ina zuwa haka da sanyin yammacin nan haka?.. Da zumudi yace "gun Salmatee hayatee man. Da rashin fahimta yace mishi "wace haka?.. Harara ya sau mishi tare da fad'in "Ban sani ba, kaima ramawa zaka yin?.. Dan Allah ni taso muje.. Kai Garban ya juyar yana fad'in "ba inda zani bansan mace ba, haka kawai, Da zumudi yace "Salma ta fa,kar kace baka gane ba mana mun dinke.. Kunu yasha yace "ban gane ba,yaushe aka dinke?.. Koh ka manta kalamanka?.. Lallami ya fara yana kasa da kai,tuni Garban ya ware yana dillika mishi dariyar mugunta. Shi dai yau bata tashi yake ba,burinshi kawai su isa ga Salman shi. Yau d'aya ta zauna zaman kwalliya duk da bata da tabbas din ganinshi,har Mama na mata t'siyar ina zuwa?. Murmushi kawai tayi ta ciro wani arnan purple swiss tana kallo, shafashi tai tana tunano colorn da Ja'afar yafi kauna ya gani ajikinta. Riga da zani ne single, dinkin yai mata kyau tsam ya kama jikinta, da gaske yau ta fito a Salmanta. Tana daga d'aki ta jiyo yaro yazo wai Salma tazo,tana jin Mama na fad'in inji wa?.. Bataji amsar yaron ba taji Mama tace kace tana zuwa. G'yale ta rufa fari da ratsin flower purple tana k'allon kanta a mudubi,ina ma Ya Ja'afar ne man... "Ki fito ana kiranki a waje Ja'afar yanzu... 6ata rai tayi tana gunguni, "Ja'afar kuma Mama?.. Ni fa ba danshi zan fita ba fa.. Harara ta sakar mata,kan ta juya tana fad'in "magulmaciyar kawai,ni zakiyiwa alaye?.. Da gani shigar Ja'afar daban take gunki ai... Dariya ta kunshe kan ta kara k'allon kanta a madubi ta fita. Suna tsaye sun rike hannun Miemie da suka dakko chan gidan su jaafar suna mata y'ar dage tana dariya. Murmushi ta tsaya yi musu da sallamarta. Ido ya zira mata,yayinda itama take kallon sauyawarshi a yau kadai kamar sabon ango. Murmushi ya sakar mata yana daga mata hannu halamun tayi k'yau, da sauri ta d'auke kai a kallonshi tana cinkune fuska. Kai ya kad'a yana murmushi, karya kuma ai ta kare, tunda har shigarshi an mishi. Ha6a Garba yake shafawa yana kallon wani fulakon karya gun Salma da Ja'afar. "Kaganta ni dai ya kamata nayi fushi bisa abinda ta dibga min,amma kaga an dakeni an hanani kuka... Harara ta sau mishi,kan ta kau da kai, "lefinka ai dayawa,bar tunatune kawai. Kai Garba ya kad'a,kan ya kallo Salman. "Salma.. Kalloshi tai,bata tunani ta ta6a ganin Garba ya zama serious haka, hakan yasa ta bashi hankalinta gaba daya. "Nasan nima har yanzu kina ganin baki na sakamakon zuwanmu na karshe gunki. Rantsuwa ya mata,kan yace "Ja'afar baizo ranar gunki da neman auren kisa wuta ba sam,asalima yazo ne danya sadaukar miki da farin cikinshi gare ki sakamakon sanin waye Alhaji Usman.. Kai ta dago tana kallonshi. Sai ya kad'a mata kai, Ja'afar din ta kalla,shima itan yake kallo. Yacigaba, "yana son ki samu farin ciki ne Salma,wanda yasan a gidan Alhaji dak'yar ki sameshi,dan kaf halin Alhaji ba wanda ba'a karanto mana ba,hakan yasa ya gwammaci ya baki ni,duk nai imani sai ya fi mishi ciwo sama da auranki a waje.. Ya kallo Ja'afar da murmushi, "nasan abuna. Murmushi sukai ma juna,tabbas hakane,dan da Garba ya auri Salma,da yana gani bashi ba sake ganinshi bare hulda da gidanshi. "Dan haka banajin da wanda ya kai Ja'afar son farin cikin ki,ki d'aure ki bawa abokina second chance a zamanku kamar yadda bukaci haka. Nan yai ta musu fad'an rayuwa sai y'ar hakuri ce,da sanya tsoron Allah a lamari,gashi sunji dad'in tawakallin tunda suna fatan in Allah yaso su maida aurensu. Kan Garba ya tafi sai da ya tabbatar kowa ya yafe. Zaure suka koma ta sa musu taburma. Kallonta yake suna ma juna murmishin so cikin kauna. Sai wani dan sinke kai take halamar kunya. Hatta Miemie ta gane iyayen sun dinke, sai kallonsu take tana murmushi. "Assalam Alaikum.. Kai suka dago,Ja'afar ya amsa. "Aunty Salma wai ana kiranki a waje.. Kallon Ja'afar d'in tayi, Shima ita yake kallo,sai yai mata murmushi. "Tashi muje naga wane tsageren ne wannan... Miemie ya d'auka itama ta tashi tana murmushi suka fita. Alhaji ne yasha gayu da babar riga da wata katuwar mota yana murmushin ganinta. Fuska ya tsuke ganin fitowar Miemie da Abbanta suna wasan su. Tana ganin Alhaji Miemie ta g'imtse fuska,murmushi Ja'afar ya mata tare da shafo fuskarta suka karasa. Hannu ya bashi dan su gaisa Alhaji ya juyar da fuska gefe. "Gunki nazo fa. Kallonshi tayi tana murmushi, "toh Alhaji,gamu ai.. Da halamar tambaya ya k'alleta. "Ban gane ga ku ba?.. Kina nufin dashi zan ganki?.. Ja'afar d'in ta kallo tare da Miemie dake kallon Alhajin duk rai had'e daga shi har y'ar. Murmushi tayi tare da matsawa kusansu suka jeru mishi a gaba. "Alhaji, kai hakuri, kai hakuri,ka daina zuwa,InshaAllah aurenmu zamu mayar da Abban Miemie.. Ka d'auka zaman mu yazo karsh.. ka d'auka rabuwar aure na da kai da auran duk had'i ne na Allah... Ja'afar ta kalla tai mai murmushi tare da shafo fuskar Miemie. "Kai hakuri na na zauna da iyalina, ka yarda sune farin cikina, ni ce tasu,kai hakuri pls... Kai ya kad'a,tare da kallonsu,duk daga gani suna a farin ciki.. Tabbas yasan yai sake,gashi ya tashi a tutar babu,ba Halima ba Salma,ba su Nabila ba Miemie... Wa zai gane a jiya yayi nadama?.. Ya zasu gane yasan dad'in jin motsin D'a kusanshi a yanzu?.. Wa zai gane ya hakura yanzu kam yana son zuri'a?.. Murmushi yayi yana d'auke kai,kila haduwarshi da Salma sanadin shiryuwarshi ne,koh yanzu ya gode Allah. Kai ya kad'a tare da masu fatan alkairi, k'warai tai mamakin jin harda mata godiya a bisa gaskiya da take tsage mata. Hannu ya mikawa Miemie fuska d'auke da murmushi. Kafad'a ta mak'e tare da lafewa a kafad'ar Abbanta. Mota ya shiga tare da fitowa da leda cike da shopping na chocolate da ice cream.. Alawa daya ya fito dashi tare da fad'in "Zan baki sweet fa,zo mu gaisa mana Miemie.. Salma ta kalla kamar mai jiran umarninta. Murmushi tai mata tare da daga mata kai,abin kai sai taje ba musu,yau sai ga Miemie harda ma Alhaji dariya. Da zai tafi hannu ta daga mishi tana mishi bye-bye tana dariya. Duk sai Alhajin ya bata tausayi Alhajin,har Ja'afar na daga mata gira halamar tambaya. Marairaicewa tayi tare da shagwa6e fuska. "Y'arka ta rabani da Alhajina shikenan kunji dad'i.. Harara ya sakar mata kamin yace "toh bishi, Allah yai ma y'ata albarka yarinya mai kishin Abbanta koh? Kai ta daga mishi tana dariya,da murna ya shillata sama ya chafe suna dariya. Gwalo yai ma Salman,sai Miemie ma ta hau mata,tuni ta fara chunno musu baki suna cikin shagwa6a. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 11 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 46_Ba sauran jira,dan karara suke nuna ma fitsara a gidan Mama, su Ja'afar abin nema ya samu,ba guntun fulako,ba shiri ta bama Abba shawarar ayi a mayar da auren nan. Wata daya aka sa suka sha biki kamar ba gobe.. Nan take jin labarin auren Bintu a gidan mai mata uku,tana chan ta zama bora. Su Maman Abba duk sun halarci bikin nata,nan take tsurkuta mata labarin Maman Ummi kan ranar ta fita gantali miji ya dawo,bayan ta dawo yace ta nemi inda dare ya mata,karshe dai akai saki. Murmushi tayi,tasan Allah ba azzalumin sarki bane,dole yadda taga tasku Maman Ummi tagani itama. Jingina yayi a jikin bango yana kare mata kallo,fuska rufe ruf da g'yale,murmushi yayi dan tunawa da daren farkonsu a wanchan gidan. Karasawa yayi tare da g'yaran murya kad'an yana leka fuskarta. Zama yayi tare da sauke ajiyar zuciya. A hankali ya kai hannunshi tare da daga mayafin da ta rufe fuskar. Tsam yayi yana kallonta ido cikin ido,tuni ya marairaice mata fuska,kuka fa?.. Hannu yasa yana share mata wani na zubowa,duka ya hayo gadon tare da janyota yana shafo bayanta halamun tai shiru. Sai da tai shiru kan ya dago kanta. Ido suka zuba ma juna ba koh kiftawa. Chan ya nisa cikin murya kamar mai jin bacci yace "Kin tuna kalaman da na ta6a turo miki na karshe cikin text message dina kuwa?.. Tunowa ta fara,sai yai murmushi tare da zamewa kan katifa da ita a kafad'arshi. Ajiyar zuciya suka sauke tare da kamo y'atsunta. "Na ce miki _" a heart dat truly loves never loses hope..but always believes in d promise of love,no matter how long d time and how far d distance,at d right time,love will fine a way".._ "Hope kin yarda da maganar ba wai soki burutsu Masoyinki bane?. Kai ta daga mishi halamar ta yadda,tunda ga nan K'ADDARAR wani zama ya kara had'a su waje daya. Yau kam ya gama gasa mata jiki da d'anyun kalaman da ya tanadesu kawai da Salmanshi,fatanshi Allah ya kare sa6ani a tsakani. Washegari da t'sant'sar farin ciki suka tashi,suna kitchen had'a break fast sai nannan yake da ita. Tashin Miemie suka ji tana kiran Aunty cikin kuka taga sabon waje. Ganin iyayen waje daya ita kanta sai binsu take da kallo, mot'si kad'an ta kallesu,kamar wacce bata so su rabu da juna suyi rayuwarsu tare. ********** Yau ziyara aka fito ta sallah ita dasu Ummi, Sun zaga duk inda ta tambaya saura gida 1 taga sun karkata zasu shiga gidan kawunsu wanda jiya sunje. Ja tai ta tsaya tare da ce musu su shiga su fito dan yau bata tambayi nan ba. Murmushi Aunty A'i tai tare da kad'a kai,a lalle kullum Salma hankali na kara zuwar mata. Tuni Ummi kam tai gaba tana t'saki. Tana nan tsaye kawunsu ya fito a gidan,bayan sun gaisa yace mata ya bata shiga ba ga y'an uwanta suna ciki? Kai a kasa tace "Abba ban tambayi nan ba ne,dan jiya munzo yini. Murmushi yayi na jin dad'i, "hakane kinyi tunani mai kyau,Allah ya miki albarka. Kai ta kara kasa kamin ta amsa. Kud'i ya ciro daga aljihu ya kirga dubu ya bata,dan sosai Salma tana wa mutane bazata,yana matukar son mutum mai gyara kuranshi. "Sannu da jira uwar y'an ka'ida... Juyawa tayi daga kallon wani a mota sun tsaya da Kawunsu da ya wuce yanzu,sai dai kan ta tantance su Ummi sun fito. Murmushi ta mata tare da basar da zancen suna tafiya. "Wannan ai wahala ce,ace duk inda zan shiga sai miji ya ban izinin shiga?.. Kai ta girgiza, "gaskiya da sake.. Hararar da Aunty A'i ta mata ne yasa tai shiru. Kallo Ummin tayi da murmushi, a irin hudubar nan a baya suka dilmiyarta,ita kwa yanzu a shirye take da yima Ja'afar biyayya matukar bazata sa6a Allah ba. Har akaje gida nan ma Ummin ta hau zaiyyanawa Mama halin da Salma ta tsiro, tuni Mama tai mata kacha-kacha,Ummi harda kukan takaici ranar. Da dare yazo ya dauke su,sai taga a motar Garba da kamar ta ganshi dazun. Taga anje gida yana kokarin rufe mota da abin rufa sai ta kasa d'aurewa ta tambayi nan zata kwana? Murmushi ya mata tare da bud'e gida. Sai da akazo kwanciya yake sanarta ai shine albishir din dazun da yace sai sun zo gida. "Ya sai sabuwa ne,sai mukai cinikin wannan dashi tawan, munyi abin hawa. Murna tai ba kadan ba tana k'allon mukullin motar. Ido ya zuba mata yana kallo ba koh kiftawa. Baki ta kai kan idon tare da hurewa. "Salma.. Hankalinta ta bashi tana murza yatsunshi cikin nata. "Daga yau na yard'e miki koh ba idona ki taka ko'ina u r free... "Dazun naga komai Salma,ina horn bakiji bane,kin sani farin ciki dazun kinsa naji ni din na isa gun matata.. Duk inda ta tambaya nan zata jefa kafarta. "Sai ganan kuma kawu shima ya labarta min yadda kuka yi sai murnar wai kin san ya kamata yake.. "Nagode sosai,yau har kawu yasan ni mai fad'a aji ne a gidanshi.. Murmushi tayi tana kara ruk'unk'umo shi. Ta gode Allah da yasa ta gyara dabi'ar ta maras kyau ta maye mai kyau. Fatanta duk wata mace mai irin halinta ta daina,dan ita taga misali akanta. Dan a yanzu rayuwarta ta fi mata dad'i da kwanciyar hankali, ta gane yanzu kulle ma wasu matan ke ja ma kansu, tana fatan kowacce mace ta guji fita a bisa sharad'in *A BAKIN AURENKI* da suke yi,dan gudun haifar da saki irin nata mai gabadaya. Alhamdulillah.. Nan na kawo karshen littafin A BAKIN AURENKI.. Ina rokon Allah kuskuren da nayi ya gafarta min. Da fatan darasin ciki ya isar masu halin Salma za kuma su gyara,Allahu ya datarmu aikin kwarai a gidajenmu. Gareku dubin masoyan Feenat Novel's, na gode kwarai da kaunar ku gareni,Feenat na son duk mai sonta, dama wanda bai yinta.. Luv you all. Sai kun sake jina a sabon littafi mai sunan... *RABO IN YA RAT'SE*... Nafisa Bashir Tanko, (Feenat Ja'afar) ke muku fatan saduwa da alkairi. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 11 of 11