Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
suna da aikin yi sai ke kad'ai ce bakki shi?.. Salma ki nemi mutuncinki da hannunki,a ganina zai fi mu.... "Ka ga malam,ba sai ka zage ni ba zan san dama kana kule dani ba,daga fita nan da nan din shine har zaka na cemin wata gantalalliya?... Haka kawai,in ma kayan ne naga kai zan sawa ba wani ba,toh meye abin zafi aciki?. Kai ya k'ada kan yace "babu... Amma wallahi kar gobe ki sake ki kara fita gun wata mai gumama,in ba haka ba zan mugun sa6a miki... Waje yai rai 6ace, "Ja'afar?... Ni zaka sa6awa?... Chak! Ya t'saya ya kasa gaba, a hankali ya juyo fuskarshi d'auke da mamaki. "Salma... Yau ni kike kama sunana garangatsai ba koh rufi?... K'ugu ta rike tana girgiza, "ai sunan ka ne naga.. Kuma muna kama sunan Allah ma bare wani chan... Na gaji ne da hancini. Kai ya k'ada yana murmushi, tabbas ba abinda yai saura da gantalin Salma bai gur6ata ba,ciki kuwa harda iya fit'sara. Sai ya k'ada kai ya fice,dan yasan komai zai iya faruwa in ya tanka. ~~~~~~ Washegari haka aka tashi kowa rai ba dad'i, yau ce ranar farko da har aka waye gari ba'a shirya ba. Ga yau week end,yana gida yaki fita shago. Har yamma ba bayani, sai dai yai bacci,ya je masallaci ya dawo. A sama take,dan gani take da gayya yaki fita dan ai ba ita gidan gumama. Ya dawo daga masallacin la'asar ya shiga wanka. Maman Ummi ta turo tazo suje kan a za6e,yana jin lokacin da tace dan aiken yace tana zuwa. Yazo fita ta biyo shi,dan tambaya a ganinta ta wanke lefin jiya ya barta. "Ya Ja'afar zamu gidan wannan mai kayan Maman Ummi na jirana. Ja yai ya t'saya, kan ya juyo ya koma parlour,ba musu ta bishi ai wacce za ai. "Tun jiya ai mun gama magana dake,babu fita... "A gaskiya sai na je, gashi nan ai kai ka ke jawo komai, da lallami na tambaya ba zaka barni ba,sai na fita cibi ya zama kari... Haka kurum yanzu haka jirana ake ka ce wani bazani ba..ta karasa tana kunkuni. "Sai kinje koh?.. Cikin fusata tace "eh.. Murmushi yai ya k'ada kai, "Bazan hanaki ba toh, sai dai wallahi ki sani, mud'in kika sa kafa kika fita,toh *A BAK'IN AURENKI*.... Bai jira komai ba yai waje,yana jiyota tana ai wallahi bazaka sani kaffara ba,fita kam nayi na gama. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Like 路 6 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Ummu Maryam Tahir Sannu da qoqari 6ter Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Kareema Wakeeli Tnx Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 25 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 18 _Kitchen_ kawai ta leka,ta d'aura guntun ruwa a tukunyar silver a _hot plate_ nata karama nepa suka d'auke wuta. Kamar zata kashe,kawai ta bari,a ganinta ba komai. Kan su kai gidan gumama kuwa 5 tayi,fatansu Allah sa ba'a za6e ba. Kaya kam gasu masu k'yau, tuni ta fara daddagawa tana ware na wara. "NEPA"... Cewar yaran gidan, sai dai da halamun su Salma hankali yayi kan gumama. Suna nan a gidan har kusan k'arfe 6,amma basu gama da mai kaya ba. Kamar ance daga kai sama,sai ga nan dan hayaki na yin sama halamar daga nesa ana gobara a wani gu. "Ina ga wutar dazu tai ma wasu aiki,hayakin nan gobara ce duk yadda akayi.. Kai Salma ta k'ada, "koh taya ake konawa ba... Sai dai kan su farga ihun gobara har kusan layin da suke. Maman Ummi tace suzo su je,in yaso daga baya sa dawo suyi bayanin. Da sauri Salma ta tare, "A'a Manan Ummi,nasan yanzu Ya Ja'afar na hanya 6 saura. "Muje dai koh gobe tunda ta kirga wanda muka d'auka ma dawo ai sabon lissa... "Umma!..Umma!!... Da gudu yaron mai gumama ya shigo, matar tace "lafiya irin wannan gudu? Ince dai ba daga gun gobarar ka ke ba? Yana haki yace "a gidan Aunty Salma ne fa Umma.. Ana ta neman inda za'a shiga a k'ulle, yanzu aka kira Malam Jaaf... "Na shiga uku... Ni Salman koh wa?.. Kai yaron ya daga,ai ina,da gudu ta fice ta wat'sar da kayan a nan ta bar Maman Ummi da kira. Kamar wata sabuwar kamu haka ta iso wajen,kofar gidan cike da jama'a wasu na kok'arin sanya t'sani su haura. A ka ta d'aura hannayenta d'uk biyun,tama rasa ihu zata kurma koh kuka. Baban Ummi ne yace ina mukullin gidan?.. Nan ta fara tunanin mukulli?.. Innalillahi, ta barshi shima gidan gumama... Baya ta fara yi ganin Ja'afar da Garba sun faka mota a chan gefe, a gigice suka karaso, "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un"... Itace kalmar da Jaafar ya iya fad'i. Ina kan ta farga sai ga hawaye na zuba tana girgiza mishi kai,mukulli Garba ya tambaya, kan cikin azama ya lalubo a aljihu ya bashi. Salman ya k'allo cikin tausayin kanshi, har yanzu hannu na ka tana k'ada kai tana kuka. "Shikenan kin zaunar mu Salma... Burin ki ya cika sai ki zuba ruwa a kasa ki sha.... Tuni ta kara fashewa da kuka. Fad'in "A kashe meter... Ne yasa yai cikin gidan da sauri. Ba ka ganin koh ina sai dusu-dusu dan hayaki. Da taimakon Maman Ummi ta bar kofar suka shiga daga cikin gida. Sai dai har yanzu kuka take baji ba gani. Yau tasan ta kad'e har ganyenta. Motar kashe wuta ce ta iso,da taimakon dak'yar wuta ta mutu. Ilahirin kitchen da bedroom ya kone ya laso parlour ta silin Allah ya t'sayarta. Fito wa tai bayan taji komai ya dan lafa ta leka gidan,sai ga nan Ja'afar din sun fito rike da barbadin _documents_ nasa a hannu. Kamar munafuka ta dan ra6a ta shigo kai duk'e tana jan hanci. Sai da yazo dai dai ita ya t'saya. Kanta kasa tana sharar hawaye,a hankali ya saki burbudin takaddun ya fice jiki duk yayi sanyi. **************************** Zaune suke a bak'in masallaci shi da Garba bayan komai ya lafa yana tausarshi,yan unguwa sai jajanta mishi suke suna tafiya. "Dan Allah ka'r ka ce zaka d'au mummunan mataki akan Salma, kai hakuri,ubangiji ya mayar ma da alkairin da ka rasa. Shiru Ja'afar d'in yai,zuciyar shi sai tafasa take,dan ma yana ta kok'arin neman kariya daga zugar shedan. Zuwa chan dai ya nesa, "Babban ni takaici na Garba Takaddu na ne,tun jiya ake _verification_ gobe ne namu,ni bana ta Salma,dan a bakin aurenta ta fita... "Ni ga nan d'akin waje zan iya maleji. Kafad'arshi Garban ya dafa,lalle kowa da jarabawar shi a rayuwa,shi kuma abokinshi ta mata Allah ya bashi. "Yanzu toh ya za ai?... Murmushi Ja'afar d'in yai wanda yafi kuka ciwo... "Ya k'wa zanyi Garba?.. Kana sane da gamnatin nan tamu, wa zai k'ar6i uziri na gobe?.. Shiru yai mishi,dan tabbas yasan bai da abin fad'a ma abokin. Gida suka koma,tana nan inda suka barta a durkushe ta tasa takaddun a gaba tana shesshekar kuka. Ja yai ya t'saya yana k'allonta, muryar ta har ta dashe. Abin haushi wai kuma zuciyarshi ta fara tausayinta. Da sauri ya d'auke kai daga k'allonta dan jin zuciya na ingiza shi yaje ya lallaso ta, Salma ce fa... Dake wa yai ya daure tukun yace "toh meye ne na kuka kuma Salma?..ki tashi kawai kije gida dan sharad'in dazu yana kan ki.... Da sauri ta dago ta k'alleshi, tuni taji kukan ya kafe,sai ido da ta kafe shi dashi, shaf ta manta wani sharad'i ne ma? Tuni ta tafi duniyar tuna abinda ya afku ka ta fita. Garba ne ya katse mata tunani da fad'in "haba dai dan Allah? Wannan sharad'in bai k'yautu a gun ka ba Ja'afar.. Aure ya fice wasa fa.. Ka janye sharad'in nan tun kan kowa ya ji ku koma auren ku.... Da sauri ta k'allo Garba,duk ta kasa ta6uka komai, Mey Garba yake nufi da su koma auren su? Yaushe Ja'afar ya sake ta?.... Bai furta ba sai dai in yanzu.. Cikin muryar kuka tana ka'rkarwa tace "bai sake ni ba Garba, auren mu na nan... Koh yanzu ya furta?.. Banji ba Allah... Ni bai sake ni ba...bai sake ni ba.. Sai ta karasa tare da fashewa da wani kukan mai ban tausayi. Ido kawai suka zuba mata, tamkar zararriya haka take magana. Duk sai ta karya musu zuciya, barin gogan,har bai san ya je gareta ba,da zummar dago ta yaje ya lallashi abarshi,sai dai kamar wanda aka t'sayar ya d'auke hannunshi, baya ya koma yana rint'se ido... Tabbas yanzu saki ya gifta a tsakani,bai da _right_ na ta6ata,tabbas bai dashi. A hankali ya furta "Salma kin cuce mu... Kin fara dasa katanga a tsakanin mu... Ban san da abinda na rage ki ba Salma...ban sani ba, dazu a yadda nake jin zuciya ta,wallahi dan banzan doka naso na miki,Allah ya kareni da yin kuskure. Baya ya juya mata,kan ya k'allo Garba. "Dan Allah ka kaita gida gani nan zuwa... Waje yai ya barsu nan,Shikenan ta tabbata,ba makawa Ya Ja'afar ya sallama ta.. Ai tuni ta kara jiniyar kuka,dak'yar ta tashi sukai waje da Garban. Sai duba Yayan nata take koh zata ganshi. "Muje Salma,InshaAllah komai zai daidaita,.. Juyowa tai ta sadakar da yai nisa... Yana k'allon su har suka kule kan ya fito a inda ya 6oye a bayan bishiya. Harda goge y'ar k'walarshi... Salma kinyi aiki. By Feenat Ja'afar 9/29/16, 9:06 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 19_"Toh a garin yaya haka ta faru? Fita kukai?... Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima. Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita sakin, kuma yaushe ya mata?. "Salma komai mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi adu'ar Allah maida muku alkairi kinji... Kai ta dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar, kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba cewa yai fa ya sake ni... Wallahi ba dagangan na bari haka ta faru ba.... A zabure Mama tace "ya sake ki?.. Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da yai shiru yana k'allonta. "Ni dai banji lokacin da ya saken ba kuma.. Ta karasa da dan kukanta. Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar, "Mey take fad'i ne Ja'afar?... Sam ban gane inda ta dosa ba.. Kai ya kara d'ukrawa,kan ya dago,mama in banda harara ba abinda take sakar mishi. Ya sani da dole su Abba suji. Cikin nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama, kawo yau da abin ya faru.. Tsananin mamaki Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da wannan d'anyen aikin? Chan dai ya numfasa tare da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Kuma kin fita d'in Salma?.. Baya ta fara ja tana k'ada kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba... Murmushi Abban yai na takaici.. Ya ma rasa mey zai wa Salma ya ji dad'i.. Duka? Kai ya k'ada. "Ni meye nawa? Ba dai kin fanshi fita sama da aurenki ba?.. "Wannan shine sakin Salma... Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN AURENKI*.... Kai ta dago da sauri.. Saki kuma? Daga fad'in hakan?... Kawai sai ta sa musu kuka, "Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara ba,Abba kai hakuri... Cikin t'sawa yace "tashi ki bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce... Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da haka sai da mummuka mata. Dak'yar Ja'afar ya lallaso shi. "Kin wa kanki toh Salma,dan dole kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min ba... "Haba wai Malam dan Allah.. Waye baya kuskure a rayu.... "Kimin shiru kema, dan duk laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au mataki.. Jan Salman tai d'aki tana bashi hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita. Sai da ya gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na rasa abin yi ne shi yasa nai hakan.... "Ni fa banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai.. Gaba nasan bazata kara ba. Shi dai kawai hakuri yake bama Abba. Abba ya tambaye shi kan saki nawa ne? Yace daya. Tashi yai yace ya jira shi,sai yace bari yaje gida shima ya d'au machine sannan ya sanar musu. D'aki Abban ya shiga bayan Ja'afar din ya fita. "Amma kin bani mamaki Allah Rabi... Ashe ba zaki zama mai g'yara wa ba sai dai kiyi shiru? T'sawan lokaci yaro yana hakuri da halin yarinya amma kina sane?... Shiru tai,sai da ya gama chake ta ta hau bashi hakuri. "Ke kuma tun yanzu har har kin kone tun kamin ki tafasa koh Salma?... Kai ta k'ada tana yai hakuri, "A'a, ni ai nawa mai sauki ne,koh dai ki g'yara halin ki,koh ki shiga hannu na... Bansan lokacin da kika sauya k'yak'yawar dabi'ar ki ba Salma?.. Sosai yai mata fad'a cikin zafi zafi kan ya kara da ta shirya,dan ya rantse bazata k'wanar mishi a gida ba... "Haba malam,ina zata toh?... Cikin fad'a yace "gidan mijinta... Koh da magana?.. Kai ta kada,kan tace "sakin fa?.. Sannan wane gida bayan ya kone?... "Eh a konan nan zata zauna akwai daki a waje yace da bai kone ba,sannan ki sani igiya d'aya babu a tsakanin ki da shi. "Ki gode Allah kin samu mai sanki,yau da wani ki kai wa haka sai ya tabbatar da ya miki shegen duka kan ya baki saki... Amma shi kok'ari yayi ma a take yace min ya mayarki. "Abu d'aya zan iya fad'a miki Salma... Wallahi, duk ranar da zaki maimaita haka,ki kuma k'waso kafa ki zo min gida sai na 6a66alla kafarki... Baki sake Mama ke K'allonshi, ita kam yau kad'ai ta kara mugun tsoron Abba,tasan a yadda yau ya daketa tsaf zai iya 6alla tan. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Zeenat Yakubu tnx 1st 2 cmmnt Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 19_"Toh a garin yaya haka ta faru? Fita kukai?... Tambayar da baba ya jeho musu kenan bayan Garba ya kawo ta ya dakko Jaafar shima. Kukanta kawai take,ita burinta ya kara maimaita sakin, kuma yaushe ya mata?. "Salma komai mukaddarine fa daga Allah,ba kuka zakiyi ba, kiyi adu'ar Allah maida muku alkairi kinji... Kai ta dago,ido duk yayi luhu-luhu, ta dubi Ja'afar, kanshi na kasa,cikin muryar kuka tace "Abba cewa yai fa ya sake ni... Wallahi ba dagangan na bari haka ta faru ba.... A zabure Mama tace "ya sake ki?.. Kai ta k'ada tana dan k'allon Abba da yai shiru yana k'allonta. "Ni dai banji lokacin da ya saken ba kuma.. Ta karasa da dan kukanta. Abban ta d'aure mai kai, chan ya k'allo Ja'afar, "Mey take fad'i ne Ja'afar?... Sam ban gane inda ta dosa ba.. Kai ya kara d'ukrawa,kan ya dago,mama in banda harara ba abinda take sakar mishi. Ya sani da dole su Abba suji. Cikin nut'suwa ya hau zayyanawa Abba halin da Salma ta t'sirar mishi,har zuwa kawo kararta gun Mama, kawo yau da abin ya faru.. Tsananin mamaki Abba kasa cewa komai yayi,wai Salman sa ce da wannan d'anyen aikin? Chan dai ya numfasa tare da fad'in "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Kuma kin fita d'in Salma?.. Baya ta fara ja tana k'ada kai, "Abba dan Allah kai hakuri,bazan kara ba... Murmushi Abban yai na takaici.. Ya ma rasa mey zai wa Salma ya ji dad'i.. Duka? Kai ya k'ada. "Ni meye nawa? Ba dai kin fanshi fita sama da aurenki ba?.. "Wannan shine sakin Salma... Tunda har kin fice bayan yace *A BAKIN AURENKI*.... Kai ta dago da sauri.. Saki kuma? Daga fad'in hakan?... Kawai sai ta sa musu kuka, "Dan Allah ya Ja'afar kai hakuri, Allah bazan kara ba,Abba kai hakuri... Cikin t'sawa yace "tashi ki bar wajen nan kamin nai miki lilis koh na huce... Kasa motsawa tai,ai da zafin nama Abba yai kanta da takalmi,Mama ta tare, amma duk da haka sai da mummuka mata. Dak'yar Ja'afar ya lallaso shi. "Kin wa kanki toh Salma,dan dole kizo ki bar gidana, wallahi ba zaki k'wanar min ba... "Haba wai Malam dan Allah.. Waye baya kuskure a rayu.... "Kimin shiru kema, dan duk laifinki ne,tunda kinsan irin shegantakar da take aikatawa, amma wai ki kasa sanar ni na d'au mataki.. Jan Salman tai d'aki tana bashi hakuri,dan sai ya iya had'awa da ita. Sai da ya gama sababinshi kamin Ja'afar ya hau bashi hakuri, "InshaAllah bazata kara ba Abba, nima na rasa abin yi ne shi yasa nai hakan.... "Ni fa banga lefinka ba Ja'afar, kamin dai dai.. Gaba nasan bazata kara ba. Shi dai kawai hakuri yake bama Abba. Abba ya tambaye shi kan saki nawa ne? Yace daya. Tashi yai yace ya jira shi,sai yace bari yaje gida shima ya d'au machine sannan ya sanar musu. D'aki Abban ya shiga bayan Ja'afar din ya fita. "Amma kin bani mamaki Allah Rabi... Ashe ba zaki zama mai g'yara wa ba sai dai kiyi shiru? T'sawan lokaci yaro yana hakuri da halin yarinya amma kina sane?... Shiru tai,sai da ya gama chake ta ta hau bashi hakuri. "Ke kuma tun yanzu har har kin kone tun kamin ki tafasa koh Salma?... Kai ta k'ada tana yai hakuri, "A'a, ni ai nawa mai sauki ne,koh dai ki g'yara halin ki,koh ki shiga hannu na... Bansan lokacin da kika sauya k'yak'yawar dabi'ar ki ba Salma?.. Sosai yai mata fad'a cikin zafi zafi kan ya kara da ta shirya,dan ya rantse bazata k'wanar mishi a gida ba... "Haba malam,ina zata toh?... Cikin fad'a yace "gidan mijinta... Koh da magana?.. Kai ta kada,kan tace "sakin fa?.. Sannan wane gida bayan ya kone?... "Eh a konan nan zata zauna akwai daki a waje yace da bai kone ba,sannan ki sani igiya d'aya babu a tsakanin ki da shi. "Ki gode Allah kin samu mai sanki,yau da wani ki kai wa haka sai ya tabbatar da ya miki shegen duka kan ya baki saki... Amma shi kok'ari yayi ma a take yace min ya mayarki. "Abu d'aya zan iya fad'a miki Salma... Wallahi, duk ranar da zaki maimaita haka,ki kuma k'waso kafa ki zo min gida sai na 6a66alla kafarki... Baki sake Mama ke K'allonshi, ita kam yau kad'ai ta kara mugun tsoron Abba,tasan a yadda yau ya daketa tsaf zai iya 6alla tan. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 20_Koh da Ja'afar din yazo haka ya kara bashi hakuri kan suka d'au hanya. Zaune take a d'akin da ya rage musu,duk ta dawo kalar tausayi. Waya yake amma yana k'allon yadda ya takure kanta tana K'allonshi. D'anna wayar ya cigaba bayan ya gama, cikin nut'suwa ta hau bashi hakuri, kan Allah bazata kara ba. Sannan bazata kara fita ba izinin shi ba. Shiru yayi,hakan yasa ta fara kuka tana rantsuwa kan haka. Sauka yayi akan 1sittern dake a d'akin ita kad'ai sai karamar katifa da filo daya da ledar t'sakar d'aki. Yasan dan so yana ma Salma,sannan yana matukar ganin darajar Abba cikin idonshi, sannan yana mutunta soyayyar da ta mishi a da chan baya. "Salma kin d'aina so na yanzu sam,shi yasa ki ke ganin damata a yanzu... Ki duba kiga abinda yawan ki ya wanzar mana...nayi imani a garin saurin ki fita ne har kika manta wani abu a k'unne a kitchen... Ki duba irin kinjin magana ta abinda ya jawo... Salma takadduna sun kone kaf...sai guntu, sanin kanki gobe muna da _verification_ da za'a gunar mana. "Ba wanda zan je ma hannu Rabbana ya k'alle ni... Kinga meyiwa na rasa aiki,dan zan shiga _miss call_... Kinga kin zaunar mu... Ba gida ba aiki.. Cikin kuka ta mat'so tana bashi hakuri, "kai hakuri banzan kara ba Allah.. Murmushi yayi kamin ya janyota da sigar lallashi. "Ina sonki Salma,kisa a ranki komai zanyi zanyi ne _for your own good_... Bazan ta6a miki abu dan tuzarci ba... _cos I love you_... Kank'ameshi ta kara cikin jin dad'i... Tabbas tana son mijinta, zata jure komai dan 6acin rana irin wannan. Koh da yazo k'wanciya ita tana gefe yaga bata niyar k'wanciyar tunda ta fito a bayan gidan waje. Daga k'wancen ya mika mata hannu halamar tazo. Har wata kunyarshi ce ta da tazo mata yanzu. Da rarrafe ta isa gareshi,sai ya nuna mata kafad'arshi kamar kullum,nufunshi ta sa kanta. Da murmushi ta g'yara, kan cikin nut'suwa ta zame ta k'wanta. Duk kusan tare suka sau ajiyar zuciya, bata ta6a saba bacci a kafad'ar Ya Ja'afar ba... Haka shima bai ta6a sa6a bacci,ba tare da Salma na hakarkarinshi ba. A daren ta tabbatar mishi da lalle har yanzu tana son nashi,har ma tai kok'arin mantarshi wasu abubuwan. *Hmmm..Allah sa da gaske ne Salma*... *************************** "Haba dai? Yaushe?.. T'salle ta doka lokacin da ta sauke wayar a k'unnenta... "Ya Ja'afar.... Da sauri ya katseta da "Ummi ta haihu... Yana murmushi. Hannunshi ta kamo,sosai tana a farin ciki. "Yaushe zamu ganin baby?.. Murmushi yayi,kan ya k'alli agogo, shida da rabi,harda wasu y'an mintuna. "Yanzu kam dare kinga ya gabato... Gobe da safe kan ma an sallamota sai kije koh?.. Kai ta k'ada tana wani tunani... Jin ya kai hannu cikinshi yasa ta dan murmusa.. Gira ya daga mata,kamin yace "saura mu koh?... Murmushi tai mishi ta k'ada kai. "Mun kusa ai...k'wantar da hankalin ka sarkin son yara... Dariya sukai,kan yace "sosai ina son su kam...in naje yaron Garba kamar nace su bamu aro... Kai ta k'ada, "lalle a gaishe ka.. Ni kam nafi son mu shekara kan na haihu da... Murmushi yai yana kada kai kawai. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~ "MashaAllah, ganshi kamar dan larabawa... Ta g'yara mishi hular kanshi... Dagowa tai cikin wasa tana"um um,su Ummi an iya haihuwa... Shiru tai ganin yadda Ummin ta 6ata rai. "Mey akai kuma ki ke wani 6ata rai ina magana?.. Baki ta ta6e,kan ta ja k'wanon namanta ta fara ci. A y'atsine tace "ya bazan bata rai ba?... Saboda t'sabar wulakanci tun jiya na haihu amma sai yau zaki wani zo kina nad'e taburmar kunya?... K'allonta take ba kiftawa, sam Ummi batta kunya.. Sai dai kawai ta basar. "Dadina dake Ummi baki bada uziri a koman ki.. Yanzu ina laifin kin haihu da magariba nazo da sassafen nan?... Baki ta ta6e kan ta had'iye naman bakinta. "Ki ce kinbi order mijinki dai Malama, amma bare nawa ne suka zo tun a jiyan?.. Karara tsoron mutumin yaci k'arfin ki k'wana biyu na fuskanta... Shiru tai dan bakin ciki, ba abinda ta t'sana irin a dinga cewa tana tsoron Ja'afar...K'wafa tai cikin ranta. Zuwan Aunty A'i ne yasa aka dawo mutunci kuma. Kullum tana gidan Ummi,duk dan gudun magana. Yau kam Ja'afar yace ta hakura gobe tunda aiki jibi kuma suna,yau masu g'yaran gida zasu zo. Ba tace toh ba,haka bata ce a'a ba. Sai dai duk ta sauya,tunaninta muddin yau take zuwa gidan Ummi,toh ba makawa sai sunce chaketa,hakan ya tabbata kenan ita mai tsoron Ja'afar ce. Tabbas lokaci yayi da zata nuna musu bata tsoron Ja'afar. Hakan yasa da k'warin g'wiwarta ta tashi ta bishi d'akin waje. Shiri yake yana son fita wajen ciciku cikun neman takaddun shi da ya kone. Yanayin da ya ganta ta dan kama kai yasan yau abin ya mot'so. Kawai sai ya kau da kai. Zama tai gefen gado tana k'allon shi ta gefe, "Haba Ya Ja'afar dan Allah... Yau daya kar kamin haka dan Allah, ka barni naje tunda an g'yara kitchen ga kuma d'aki muna dashi a waje bayan suna suyi aikin.... Ido kawai ya zuba mata,sai da ta kai Aya tukun yai magana. "Ke mey yau din zata miki in baki fita ba?.. Kullum fa tun haihuwar nan kina fita Salma,dan yau kad'ai nace ki hakura sai gobe shine ba zaki iya ba Salma? Fuska ta y'atsine, kan tace ita dai kawai ya barta ta fita toh. K'allonta yake,abu yai sauki yanzu tana son dawo da hali? "Son ranki za'a bi yanzu koh nawa Salma?... A gida na ban isa nace ga abinda za ai ba sai ace a'a?.. Meye haka kike son kawo wa kuma da ya wuce?.... Hawaye ta fara mishi,tabbas yau in bata fita ba,toh gobe fa sai dai ta toshe kunne. Haushi tai bala'in bashi,akan wannan shine harda kuka?.. Sam bai son abin da ya wuce a dawo dashi. Nan ta zaune mishi tana mishi kukan gardamar sai ya batta. Haka yanaji yana gani sai shi ya sauke ya barta yace ta shirya su je. Da murnarta ta shirya suka fita ya sauke ta. Sai dai shi sam baida walwala. Haka tai ta fita har ran suyar nama,washegari ma wai zata wanke gida,anan suka hau suka fad'o.. Ya ja ta ja,harda fad'in dama ance tsoronshi take ji. Ya rant'se da in har ta fita,toh zai maimaita mata abin ranar,wato ta fita a bakin aurenta. Tuni ta nut'su ta dawo hankalin ta. Tuni ya kashe bakin t'sanya,har ya fice ya barta tana kuka,harda dariyar mugunta... Ya k'wa gano lago ai. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 21_Ranar ta fita a Napep ta layin su Ja'afar taga wani kamar shi tare da wata, har zasu wuce ta gane Bintu ce,da sauri tace mai Napep ya t'saya. Sam a yadda suke ba kace ba masoya bane,dan sai wani sunne kai take kasa halamar kunya. Tuni zuciyarta ta hau tafasa,ba shiri tai wajen gadan-gadan,dai dai suyi sallama harda dago mishi hannu. Kan ta karasa har ya juyo itama ta tafi... Ganin yanayinta shima ya dan tsorata,amma sai ya maze. "A'a, har kin fito?.. Harara ta sakar mishi kan ta k'allo Bintun da har tai mata nisa. "Ban sani ba... Ashe dama zance ka fito shine kace na hau adaidata koh?.. Kuma da Bintu?.. Har kana wani yage mata baki... Hannu ya kai kan bakinshi halamar tai shiru yana duba layin, "Haba Salma,a titi fa muke,kiyi hakuri ba abinda ki ke zata bane ba... Harara ta kara sakar mishi,kan ta farga har ido ya ciko da hawaye. Tabbas yau ya tabo jaraba... Dan sarai yasan Bintu kam sonshi take,kuma Salma ta sani. Akan kishiya k'wa, yasan sai Salma taki ci taki sha. Tuni ya hau lallami harda rantse rantse kamin ta yarda bayan anje gida. Wataran yakan yi tunanin koh Salma na da Aljanu,in ta tashi sauya hali tafard daya ne,sai dai in ya bud'e mata wuta su shirya. ~~~~~~~~~~ "Shiru ake jinki makociya,koh dan ziyarar yamman nan an daina zuwar mana sai jefi-jefi, koh mutumin har yau yana nan da kullen?... Baki ta dan ta6e,kan ta bawa maman Ummi amsa. "Ai sai abinda yai gaba, yanzu tunda akai abinnan na farko abu kadan sai ya kafan sharad'i kan in na t'sallaka a bakin aurena, ina gudun rabuwar mu,yanzu ma minti goma ya ban na dawo. Baki Maman Ummin ta ta6e, "lalle kina da aiki in dai mazan nan ne, saf zasu mayarka marar y'anci in bakai ma tufkar hanci ba,harda lokaci? Tab aiki.. Ga gobe sunan _nurse_ din layin chan (Maman Nuwaira),ke koh barka baki je ba, ke kinsan za'a watsa karya kiyi kok'ari ya barki muje. Kai ta k'ada, "Ai dole,dan wallahi baza ai bani ba,ko bai bari ba naje koh minti ashirin ne a wat'sa warishan nan dani. Hannu Maman Ummi ta bata suka tafa harda shewar su,ana haka Ummi tai sallama,kan tunda ta shiga Jafar

Chapter 4 of 11