Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
had'a jiki da karya irin Bintu,haukar nake son sauke miki aka yau ai, gaba kin d'aina irin kuskuren nan ina zuba miki ido kawai,yau dole na fidda ki cikin gona ta. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31 Feenat Ja'afar Novel's "Karya ki ke wallahi ki iya koyan hankali Salma,ai fad'a da makami tsoro ne,ki ajiye bokitin mu gabza da hannu in kin is... "Meye hakan ke kuma Bintu?.. Juyawa tai da sauri,tana ganin Ja'afar ta sau kukan munafurci harda kank'ame shi,wai Salma tace in ta shigo sai ta kashe ta da duka da bokiti bayan ta jika su ita da bakin da zata raka... Ciki yai gadan-gadan gun Salman,tana ganinshi ta mike t'saye rike da bokiti,bai watawataba kawai yai kanta da niyar mari tai baya. Kunci ta rike har tana halamar yin baya zata fad'i, "Kin haukace ne Salma ko mey?.. Gidan ki ne da har zaki kafa dokar wa zai shiga ko ya fita?.. Cike da mamaki ke d'auke a fuskarta, ganin yadda ya rufe ido yake zazzaga mata bala'i harda yunkirin mari. "Ni zaka mara da akan waccan karyar Ya Ja'afar?.. A tuzare yace "eh wallahi, da da halin duka ma sai na miki,kuma daga yau kar in sake jin kin kamanta matata da sunan kare a gidan nan.. Kai ta k'ada, kan tai baya tana g'yara t'sayuwa tai d'aki. Code wear ta ciru, a masife ta fito tana mika mishi, "Amshi waya, yau in ka cika kaine Ja'afar ka dake a gidan nan sai nasan na ta6a maka y'ar g'wal dinka Ya Ja'afar, amma ni in naci sunan Salma,toh wallahi babu mai takani ya k'wana lafiya,zaman lafiyarta a gidan nan kawai ta fita harkata... "Bazata fita ba d'in, haba. Wannan wace irin masifa ce wai?.. Kullum ke kenan cikin dacin rai?.. Ba wanda yake t'sallake masifarki in ta motsa.. Haba Salma,yarinyar nan tun tana miki kawaici har sai kin kaita bango,koh tausayin yanayin da kike ciki ba k'ya yi?.. G'walo Bintun ta sakar mata tana a bayan Ja'afar. Kawai sai tai murmushi tai d'aki ta dakko hijabi da kud'i ta fito. Cikin sanyin murya tace "kamin izini zan fita Ya Ja'afar.. Harara ya sau mata!kan yace "Da in zaki fita ba kina gaban kanki ba?.. Wato ga shashasha yana magana dole ki fice,toh kije duk inda zaki ai kin saba... Dak'yar ta iya shanye kukan dake son subuce mata,ga Bintu sai dariya take mata a boye,da sauri ta zira hijab dinta tai waje. K'wafa yayi shima kamin yace Bintu ta shiga ciki yana zuwa. Waje yayi da sauri,har ta samu mai Napep ta shige tana hawaye, a tunzure yai gun mey Napep din, "Kar ka kuskura ka jata cikin Napep dinnan in kana son kekenka ya tsira.. Sauketa tun wuri.. A masife ta rufe ido tana mishi balbalin bala'i kan bazata sauka ba din. Shi dai mai Napep duk ya tsorata,jin ta dawo kanshi yasa ba shiri ya tada Napep,magana yake mata amma ina,da sauri ya juya shima yai gun nashi machine din yabi bayanta. "Hajiya wannan binmu yake a baya fa,wallahi kar ya tafkan asara.. Murya na rawa tace "Dan Allah ka kara gudu sabuwar gandu zaka kaini.. Kan ta karasa kukan har ya taho mata,kawai sai ta jingina kanta ta hau yi kamar ance mata Mama ta mutu. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 27_Tun kan Napep ta t'saya ta mika mishi kud'in, da sauri ta shige gidan Aunty A'i fuska duk hawaye. "Toh kiyi min bayani man ba kuka ba Malama,mey aka mi... Wayan Aunty A'in ne ya hau ruri Aslam ya miko mata. A takaice ta k'alli Salman sai tai waje dan amsar wayar. Tana ji tana waya da Abban Aslam kan zata shigo da Ja'afar. "Dan Allah karki shigo dashi,wallahi ban san ganinshi,gwara in na huce da kaina zan koma. Baki sake take k'allonta hijab a hannu, "Ok,kina nufin yaji kika yi kenan?.. Shiru tai mata tana ci gaba da goge hawayenta. Bata kara bi ta kanta ba tai waje. Ba'a jima suka shigo tare,kai ta kautar gefe, tana jan hanci,ido yayi luhu-luhu dan kuka. Abinda ya faru ya t'sarawa Aunty A'in, tuni ganin duk ita ya d'aurawa lefi yasa ta hau musu bori ba shiri. Ido kawai Aunty A'i ta sa mata. "Auntyn mu kin gani koh? A gabanki ma kenan,wallahi na rasa rikicin Salma sam yanzu,abu kadan yanzu zata hau balbalin bala'i sai dai ni na bar mata. "Yanzu da banzo ba Allah kad'ai yasan mey zatai ma y'ar mutane,k'alli a halin da take fa,amma Salma taki k'wantar da hankalinta ai zaman lafiya.. "Ni fa kar ma ka zata kishi nake da kai koh kuma waccan amaryar taka,sam ba haka bane,ni mud'in za'a tada min hankali toh lalle na kowa zai tashi... _period_. Aunty A'i ya k'allo halamar tasa baki. Tambayarta take mey ya had'a su?.. Amma fur taki magana a gaban shi,har aka gama sulhu yace ta taso su koma tace sai dare. Da kai Aunty A'in tai mishi kawai kan ya k'yaleta. Ba musu ya tashi kan sai ya zo,yana fita ta mike tai kitchen. Tana cin abinci Aunty A'i na mata fad'a, kan ta d'aina fada Ja'afar na fada,dan ta fuskanci Bintu ta iya bariki. Nan ta fad'a mata ainashin abinda ya faru,harda irin habaici da sharrin da Bintun ke mata kullum. Baki ta ta6e. "Ni fa Aunty A'i Bintu bata gabana, abu daya na sani na tsani a gabana yana biye mata tana mishi abinda taga dama.. Yana konan rai ne,shi yasa yake rasa kaina. Murmushi tai mata, "Lalle Salma kina so Bintu ta kai ki ta baro, kin kuma yi saken da kika bari kishiya har ta gano lagon ki,dole yai ta ganin bakin ki ke kadai,dan ke kadai ki ke iya daga jijiyoyin wuya agabanshi akanta,in sharri ma ta miki ki barta da Allah kawai,shi zai isar miki,kar ki manta igiya daya tai saura a t'sakanin ku da Ja'afar, kuma kince ta sani,toh wallahi ki sani ingiza mai kantu ruwa kawai zata miki,so take tai ta tunzuro ki har ki tafka kuskuren da za ai mai dika, kinga taci galaba kenan. "Gaba koh abinsu suke kina d'auke kanki a kansu, sannan abu in kinga zai ja ki fad'i wata magana musamman kan Ja'afar kiyi shiru kar ki tanka dan Allah Salma. "Ja'afar na sonki,kiyi amfani da hakan sai ki ci galaba kan Bintu.. Har ta gama mata fada tana ta nazarin abin,toh Allah yasa ta iya k'auda kan. Ita kwa Bintu murna fal rai,dan tana lekensu ta k'auran zauren, fatan ta Allah yasa yadda ya figi machine din nan in yaje kawai ya dankara mata saki. Shi yasa tun kan ya dawo taje ta t'sant'sar wanka ta hau kananan kaya, duk da ba ita ke dashi ba. Ita a ganinta an sau Salma an gama,.. K'warai ta gode da shawarar su Aunty Ladi ta waya da ta yau,tabbas da BARIKI kadai zata mallaki Ja'afar ba boka ba Malam. Sai dai har dare ba Ja'afar ba dalilin sa,kawai sai ta zata bai gama hucewa bane,tasan mutumin ak'wai saurin zuciya. Dirin machine dinshi taji,da sauri ta kara fesa turare ta haska touch light tai zauren da zummar taro shi yasha Bariki. Turus taja ta t'saya gabanta na fad'uwa, ganin ya mike yana fad'in ma Salma "Dafani man toh,ban san ki fad'i ne garin sauka. Da kamar kar ta kulashi,amma ganin hasken fitilar Bintu yasa ta hau shagwaba. "Toh ni kam tsoron sauka fa nake tunda cikin nan yai girma,in zaka iya ka sauke ni toh... Ta karasa da kalar tausayi. "Toh toh,amma ki kokarta,ki rikeni gam, koh ki bari na fara sauka... Kofar Bintu ta saka da sauri ta koma ciki dan bakin ciki. Tana jiyo su a t'sakar gida Salman na fad'in "Wash.. Allah Ya Ja'afar kafata rikewa take fa.. Tuni gogan ya hau rikicewa abinda aka jima ba'a mishi ba yau yake gani,bar zuciya da abinda take so. "T'saya na d'auke ki toh ai kina ma kok'ari.. Tana jiyo Salman na fad'in "kai Ya Ja'afar, anya zaka iya kuwa?.. Nayi nauyi fa yanzu. A zabure ta mike ta tana lekensu ta window ta cika tai ham. Dariya suke k'yak'yatawa kan yace"bari ki ga,nawa ki ke.. Da sauri ta sau labulen ganin ya k'wa daga Salman ya dauke kamar y'ar tsana suna dariya. Har d'aki ya dire ta suna nishad'i kamar ba su bane dazu an bar Bintu da kukan d'aki. Sai yanzu ya tuna ai koh sallama basuyi ba suka shigo. Murmushi tai mishi lokacin da yace bari yaje ya dawo. K'wafa tai tana kada kai, "kowa ya iya BARIKIN ai,in na baje tawa sai kin ji jiki Bintu. Yau da sauri-sauri yai ma Bintun sallama yana ta zumudin sun dinke da ta k'arfen. Kuka wiwi tai tayi bayan fitarshi. A gaban mudubi ya tarar ta tana g'yara gashi,kowa farin ciki fal ranshi,ta baya ya sakalo cikin yana shafawa harda sakar ajiyar zuciya. Murmushi tai mishi,tare da shafo siririn sajen shi ta bayan, sai ya k'wanto da kanshi wuyanta suna ma juna murmushi ta jikin mudubin. Yaushe rabon su kasance haka shi da Salman sa?.. Ga y'ar shagwa6ar nan yau yana shanta,duk sai ta mantarshi komai. A hankali ya rad'a mata a kunne "I love you... Murmushi tai kan ta juyo tana lumlumshe ido jin dad'in kalmar, lafewa tai jikinshi tana fad'in ''Me too.. Sosai yasha mamakin Salman shi yau,komai yi mishi take cikin kauna da kulawa, kamar farkon aurensu kamin komai ya wargaje. Hakan yasa washegari kowa fuskar nan kamar gonar audiga dan fara'a, amma banda Bintu Lol. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 28_Tun daga ranar aka dinke da Salma da Ja'afar d'inta, sam ta d'aina sanya da abinta, shima abin nema ya samu,wai ! Matar falke ta haifi jaki. Kan kace k'wabo,tuni tsohuwar soyayya ta dawo d'anya,sai ya zama kamar kamar yanzu ma tafi yawa. A cikin wata guda duk sun sauya,takanas zaice su fito aje siyayyar kayan baby,fur Bintu take kin zuwa,sai suyi tafiyarsu a kafa suna tadin su,sai jiran EDD. Kwana biyu Bintu an tsiri zaman d'aki,sai ta kule ka rasa abinda take aciki ita daya. Ranar tana bacci da safe wajen k'arfe goma taji kwkwazon maigidan yana tayi ba kakkautawa. Tashi tai ta fito parlour. "Na fita ban karya ba,yanzu ma na dawo ashe baki tashi ba, bayan tun asubar fari kika fara wannan charting din danaki jini a rayuwa,na hana kin ki hanuwa,toh ina gaf da fasa wayarnan a gidan nan Allah. Baki ta ta6e tare da tashi a hankali tayi d'aki dan fita wanka. Tana kallo ta fito wai yai hakuri ta daura mishi indomie,koh ta kanta bai bi ba yai waje yana huci. Kamar jira take,da dan gudunta ta koma d'aki ta dane Facebook cikin group din su na KI G'YARA DA KANKI. Kusan duk anyi katari masu kishiya sun da yawa, nan zatai ta samun shawarwari mey kyau da marar k'yau,dak'yar ta tashi ta d'aura jalof ta koma. "Wato sai yanzu nake hangen maganar ka abokina, dan yanzu abinda Bintu take har yafi mai na gantali ciwo,in ta hau wannan Facebook din nata,sam bata ji bata gani,abinci a kone, in ma ta samu d'aurawa kenan,sallah a kure,bacci sai biyun dare,da asuba ta d'aura a inda ta tsaya,ga in ka shigo kaji tana dariya ita kad'ai, Allah zaka zata Bintu sabon kamu ce... Dariya ya fara mishi harda k'yak'yatawa,har ya fara k'uluwa,yasan haka zata biyo baya, amma shi yanzu shawara yake nema ya zai da sabon halin Bintu?. "In ka gama kai magana sai ka bani shawarar abin da zanyi. Dak'yar Garba ya takaita dariyar ya fara magana. "A lokacin chan baya ai bakaji zance na ba,dake idon ka a rufe yake,na sanarka baka san mey wani irin hali zaka jajubo ba,kace kai fa gaji ka gani sai Bintu.. "Malam ni shawara zaka bani,in babu zanyi gida. Dariya ya cigaba dayi,kawai sai ya zuciya yai gaba. "Ma had'u in ka gama,dan hankalina yai kan Salmatee. "Wash Allah bayana,Bintu!...Bintu!!.. Tamkar ba kowa a gidan ka ke ji sai karar fankar sama dake kadawa a parlourn wacce bata hana gumi t'satsafo mata ba. Rarrafo wa tai zuwa kofa,iya karfinta ta kwalawa Bintun kira,ji take tamkar zata mutu dan azabar ciwo,tuni ta fara kuka tana ambatan Allah,tasan koh zata mutu Bintu bazata taimake ta ba,fatan ta Allah ya hankad'o mata Ja'afar koh wani ya ceceta. "Wayyo Ya Ja'afar, Innalillahi.. Bintu.. A razane ya karaso cikin gidan dan jin ta ambaci Bintu cikin kuka. "Subhanallah.. Salma.. Ina Bintun toh?.. Da sauri ta dago,tana ganinshi ta kara fashewa da kuka tana cije le6e. gaba daya ya tallafota yana aikin sannu sannu. Waya ya ciro dan neman Garba ya kaisu asibiti, tana ta ringing shiru.. Da rigarshi ya goge mata gomin dake tsatsafo mata, "Bari na ga koh bacci waccan take na taso ta. Hannunshi ta rike gam tana girgiza mai kai, Kanta ya shafa, "ki d'aure Salma,bari na kirata kinji. Dak'yar ta cika shi yai dakin Bintun, dan ji take yana tafiya zata mutu. Bata parlourn, sai ya bankad'a daki,tana mike a kan gado taja rabin bargo tana dariya kasa-kasa tana charting hankalinta yai gaba. A sukwane yai kanta,bai wata-wata ya sinketa da mari mai rai da lafiya,a gigice ta mike tare da dafe kunci,wayar ya warce, "Lalle haukar nan taki karuwa take Bintu,yanzu dama kina cikin gidan nan Salma take ta kakarin kiranki kamar zata mutu?.. "Toh ki biyoni yanzun nan waje, tana turo baki ta sakko kan gadon tana gunguni. Nishi take ta dafe d'ukkan hannunta a kasa, sannu yake mata da tausayawa,da harara Bintu ta bita da jin haushin akanta an mare ta. "Ka kira min Iya Shatu dan Allah Ya Ja'afar kar na mutu.. Bintu ya kallo dake maka musu harara, "Kizo ki kamamin ita na kira Iya Shatun, kamar bata so ta matso kusa,yana fita ta mat'sa tana jan tsuka,"aikin banza,dan kina wata shegiyar nakudarki akan hakan kika ja aka mare ni, wallahi za... "Eh dan Allah kazo yanzu mukaita asibiti.. Shiru tai jin Ja'afar na kokarin shigowa tare da matsawa gun Salman da sauri zata ta6ata tana sannu. A hankali ta janye daga hannun Bintun tai dan ciki kad'an tana nishi, da sauri ya karaso dakin yana mata sannu. Nishi take iya karfinta sukaji sallamar Iya shatu,tana dubata tace ai haihuwa ce tazo gadan-gadan, ya basu waje, ya siyo reza da sauran abin bukata. Gam hannunta na cikin nashi,ji yake tana cikawa in ya tafi zata mutu. Kanta ya tallafo yana ta d'aure, iya shatu sai k'allon ikon Allah take. "Kai hakuri Jafaru,zata haihu lafiya dan ina jin kan D'a, yanzu bazata ji komai naka ba sai adu'a. Kai ya kada harda guntun hawayenshi yai waje,yana fita Bintu ta d'aura a bayanshi. Iya shatu tsuhuwar ingozoma ce mai ritaya, da guntun hand gulf din zuwa awunta ta karbi haihuwar Salman. Allah ya taimake tazo mata da sauki inji Iyan,sai shigowa yai shi da Garba yaji ihun jariri,baki wangale zai dakin iya shatu ta fito k'ar6ar reza. Ummanshi ya fara mawa albishir sai Aunty A'i,tuni ya fesa cikin gidan su,da ance mey ta samu? Sai yace bai gani ba. Har aka kintsa komai basu kara ganin keyar Bintu ba,sai da zasu asibiti ta fito,shi kam baiya ma ta ita. Suna fita su Aunty A'i suka zo da Ummi,lokacin Bintun na t'sakar gida tana yankar farce,ita dey Iya sai mamakin karfin hali irin na Bintu take. Sallama suke ta manna musu bajon hauka,tuni Ummi taja dogon t'saki, taki jinin Bintu a rayuwa. "Banza y'ar bakin ciki kawai,toh sai ki had'iyi zuciya ki mutu ai.. Hannu Aunty A'i ta daga mata halamar tai shiru,ita k'wa da harara tabi su har suka shige. Sun dawo an duba suna lafiya ita da babyn ta,Ja'afar baki har kusan k'unne dan murna,yana makale da yarshi. "Um,Baban baby ba koh dan karar nan ma ta manyan yayu.. Kai ya sosa yana ma Aunty A'in murmushi, ba dan yaso ba ya mika mata ita. Kan kace mey gida har ya cike da dangi yan barka da yan unguwa. Sai dare ta samu tasa hakarkarinta dan hutu. K'allon babyn take mey kama da Abbanta, gashi kadai da dan _beauty points_ (dimples) tai gadonta. Murmushi tayi tana kai hannu kan kumatun babyn, Allah mai halitta. Murmushi yake musu yayin da ya shigo d'akin, sai ta daga kai ta k'alleshi, kai ta girgiza tana dan murmushi. Sallama ta uku yana musu kenan yana dawo wa,ta rasa wani irin kulafuci yake musu musamman babyn. Zama yayi yana shafo sumar babyn da farin ciki. "Oh ni kam,koh zaka je da ita in tai kuka sai ka kawo ta. Murmushi yayi yana kai baki kan dimple din babyn yana kissing. "Ba kinki barina na k'wana anan ba?.. Da kalar tausayi yace "yau dai daya naji dumin y'ata kinji? Sai ya marairaice fuska. Dariya ta dan mishi,kan tai magana ta jiyo Babah mai zamar mata tana ya fito zata zo ta k'wanta,taga sallamar bata karewa. Dariya suka sa kamin ya tashi yai waje. "Maza ki rika biye mishi ki debo ma kanki magana da kazamin goyo ai. Da rashin fahimta ta k'allota tana neman karin bayani. ***** ***** Yau suna,baby taci sunan Mama tun ran huduba amma ya 6oye mata. Sosai yau daya Ja'afar ya biya mama,harda mishi waya tana kwarara mishi godiya ba iyaka. Maijego tai ras abinta da Baby Miemien ta,sun fito sunyi k'yau sosai. By Feenat Ja'afar. Ai hakuri da wannan dan zani gidan Suna Salma.. Zuwa yamma in na dawo zakujini Lol.. 9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 29_Suna ya wat'se kalau,maijego tai goshi,ak'wati guda Mama ta mata na suna sai na baba,ga Umman Ja'afar nata daban da tazo suna,chan gidan su Ja'afar su ma sun mata karamci,sai son barka. Wankansu suke cikin g'yara na musamman da Mama ta zage yi ma y'arta, albarkacin Miemie mama ta sakko sosai. Shirya Miemie take tare da taimakon Ja'afar din suna ta nishad'in su yau za ai yawan arba'in. Ta chakare sosai kamar yau ne sunan ita da Miemie. Baya ta juya mishi yana goya mata ita, "D'aure ta dakyau,dan kinga machine zamu hau.. Kai ta kad'a tana murmushi, Sai da ya zaga ko'ina yaga yayi kan ya bata majanyi tana mishi dariya, "A'a toh in baki iya ba ni sai na goya abata kawai... Dariya tai kan tace "Da kwa kabar abin fad'i agari kuwa. Jakar ya d'au mata ta d'au mukulli sukai waje,shima yasha sabuwar shadda abinshi. Bintu na t'sakar gida tana d'anne-d'anne a wayar da dak'yar ya bata. Da harara ta bisu harda dan t'saki a hankali. "Toh mu zamu fita sarauniyar charting.. Sai kisa mana mukulli a gida dan gudun kar a dirko kina sana'ar taki koh.. Tuni ta kara k'uluwa kuwa,ita dai an mayarta borar karfi da yaji a cikin gida. Hannu Salman ta dago mata halamar sai sun dawo,da harara ta bisu har sukai waje. "Jishi kamar wani dan daudu rike da jakar mata. K'wafa tai tana tashi t'saye, "Ba dai kin fara fita ba?.. K'wanan nan zaki yabawa Aya zakinta wallahi. ** K'wana biyu yau tayi tana fita yawan arba'in, yau ne na uku,yau kuma aka tafka t'siya da maigidan,dan fur yace ba inda zata je. "Bazaki k'waso ma yarinya rana ba fa,kiyi hakuri kawai. Iya wuya Salma ta kawo dan takaici, tayi magiyar yaki kuma,kawai sai ta raya mata tunda dama taki bari ta koma hagu. "Amma gaskiya baka min daidai ba Abban Miemie in har ka hanani fita yau. "A ka'ida sati ake fita yawan arba'in fa,amma ni na yarda zanyi ukun shine har na gama shiri amma kace bazani ba... Gaskiya da sake. Gefe tai da kai tana kunkuni,tuni ta kular dashi shi zuciya kusa. "Toh ban hanaki ba kije d'in, amma ki ajiye min y'ata ki tafi ke kad'ai. Baki sake take k'allonshi,ganin yadda ya fidda waya yasha kunu ya barta. A zuciyarta tace "Eh lalle,da gani abin Ya Ja'afar yazo da wulakanci... "Kasan dai ba yadda za ai na tafi na bar Miemie a gida,dan Allah in wasa ka ke ka bari,dan kam nasa rai da fita yau.. A tunzure ya mike da niyar magana cikin masifa,sai yai shiru yana k'allonta. "Kiyi toh gaban kanki kawai.. Sai yai waje da zummar barin gidan ma dan haushi. Sai dai mey?.. T'saye yayi yana binta da k'allo galala, ganin yadda ta fara kame-kame dan ya kamata tana musu la6e ta window. "Ke kuma lafiya kike abu kamar marar gaskiya?.. Dakewa tayi tai ganin kamar bai ramfota ba. "Dama zuwa nayi ina son na leka nan na dawo ne... "Ba mai fita yau acikin gidan nan in dai ni ne mijin, wacce ban isa ba ta fita nagani.. A fusace ya fice yabar gidan,duk sai ta Salma tafi zafi. Ita kam Bintu dariya tasa harda shewa, "Yau karya ta kare,sai a za6a zaman gidan miji koh fita yawan gantali gard'i... Tana jiyota tai banza da ita tana hawayen bakin ciki. Waya ta d'auka ta kira Aunty A'i kan abinda Ya Ja'afar ya mata. "Salma kiyi biyayyar aurenki, dan Allah kiyi hakuri da fitar kawai. "K'wana biyu ai yayi ma,tunda kin zaga ko'ina ai har gidan su... "Aunty A'i ban fa wuni a gida ba kullum a ziyara muke wuni. "Ai duk fita kina zuwa,dan Allah kar ki dawo muku da hannun k'yauta baya man,kuna cikin zamanku abin sha'awa. Baki tai ta bata sai da ta tabbatar mata da ta hakura kamin sukai sallama. Haka tanaji tana gani ta hakura da fitar tai zamanta a d'aki. Koh abincin rana kin zuwa yai yaci a gidan sai gidan Garba yaje. Kawai zuciya ke raya mishi Salma ta fita,bazai so yaje gida yaga tabbas ta fitan ba,kawai sai yai zamanshi har yamma tukun ya koma gida. Dakin Bintu ya nufa har yanzu baida walwala sai ya tabbatar da Salma bata fita ba,yasan Bintu kat ce,bata t'sallaka doka akan fita,in yace A'a, toh ta hakura. Sannu da zuwa tai mishi tana fara'a, a ranshi yana aiyana da Salma ce yasan sai ta cika tai fa kan ta mishi sannu da zuwa duk akan ya hanata unguwa,amma kullum y'ar uwarta ko ajikinta. "Yau bayan fita ta Salma ta fita?.. Kai zata girgiza, sai tai saurin kwa6ar kanta, dole yadda tasa taga bakin ciki har yau itama ta gani. "Eh,bata jima da dawo wa ba ai,baka sani bane?.. Hannu ya daga mata,cike da jin haushi yace "ya isa ni,tambaya na miki kawai. Waje yayi tana binshi da g'walo, yana yin nisa ta tuntsire da dariyar mugunta. Kamin cikin sand'a tai waje jin ya zata kaya. Ba koh sallama ya shiga parlourn, ganan takalmin a gefen kofa wanda ta fitar zata sa dazu. Tana zaune tana _feeding_ din Miemie ya shigo yana binta da kallo,da fara'arta tai mishi sannu da zuwa. Kekam yayi yana k'allonta ba koh kiftawa, tabbas Salma ta fita,dan mud'in bata fita ba bazata tare shi da wannan fara'ar ba haka,yasan kayarshi. "Wato kin fita hankalinki ya kwanta koh?.. Ban isa ba ashe har yau halinki yana nan baki sauya ba koh Salma?.. Baki sake take K'allonshi da tsananin mamaki,sai d'aure ta yake da jijiyoyinta. Cikin nut'suwa tace "Ni fa ba inda naje tun fitar ka,dan Allah ka d'aina tun.. Malama ki amshi laifi kawai,kinsan nafi t'sanar musu sama da komai, koh kina nufin Bintu karya zata miki?. K'allon mamaki take mishi,a hankali ta maimaita "Bintu".. Yaki ma bari tai mishi bayani sai zazzaga mata yake kan bata maidashi abakin komai ba. Kawai sai ta sau mishi kuka,tama rasa abin fad'i,wai Bintu ce ta fad'a mishi,wato ita ba abin yarda bace sai kishiyarta indai kan fita ne. "Haka ki ke ai,da kukan rashin gaskiya Salma..sam bana son ki dawo mana da hannun agogo baya,ina ta murna komai ya wuce ashe albarkar ciki ne yasa ki zaman dole. Ganin kukanta na karuwa yasa ya fice ya koma d'akin Bintu. Har da bawa kura ajiyar nama,wai duk randa Salma ta fita dan Allah karta 6oye mishi. Tun daga ranar ya sauya mata,sam in ya shigo sai dai ya d'au ya'rshi ya fice,itama daga gaisuwa shikenan ta gama,dan a ganinta wulakanci ne wannan babba. Ga wani fi'ilin mutunci da Bintu ta koya da kissa,kullum faram faram take mata,harda gaisuwa in antashi. Ta d'au Miemie ta goya a bayanta in Baban ya d'akko ta. Ba karamin dad'i kwa Ja'afar din yake ji ba,dan yana karrama mai son Miemien shi,ita kam Salma nata ido,sai ta dukufa gun kai kukanta ga Allah. Dan tabbas tasan tai saken da har mijinta yai mata mummunan tambari. Bintu kuwa kullum rokon ta Allah duk wani sharrin da take nemanta dashi Allah ya mayar mata kanta. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:20 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/2, 2:29 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 30_Sai ya huce kamar sati ana mutunci da ta tambayi fita unguwa zai kicin-kicin,yace tai son ranta,haka zata hakura tanaji tana gani,in ya dawo kuma tasha fad'an da batasan laifi ba. Kawai Allah ya d'aura mata wani irin hakuri,daga Ja'afar din har Bintun ido tasa musu kawai. A haka har Miemie tai wata hudu Salma na zaman hakuri, musamman ga saurin fushin Ja'afar gareta,ga tai alkawarin daina kai kara gun kowa sai gurin Allah. Ana haka Maman Abba ta haihu. Ganin yau y'an mutuncin na kanshi yana zaune ya shagala da yiwa Miemie wasa tana wage mishi baki tana dariya. Da fara'arta ta zauna kusa dasu tana k'allonsu. "Abban Miemie... K'allota yayi tare fad'in yana jinta,cigaba yayi da wasan su. "Inda hali dan Allah zani barkar Maman Abba yau kwananta hud'u da haihu banje ba. Kai ya kad'a, "wace Maman Abba?.. Da zumudin zai batta ta sanarshi makociyarta ta unguwar su ta da. Abinda yake ya t'sagaita yana k'allonta ba koh kiftawa. Tuni ya zata an rufe babin y'an tsohowar unguwar su a gidan,ashe har yanzu tana makale dasu. Bazai manta dasu ba,dan sune ummul aba'isin wargaza gidanshi. Kai ya girgiza mata, "Kiyi hakuri ba halin zuwa.. Baki ta sake tana K'allonshi, a gaskiya bazata zuba ido tai ta zaman gida na y'anci ba,da takura gaskiya. Amma sai ta bishi da lallami. "Dan Allah ya Ja'afar ka barni naje,nima dana haihu fa sau biyu tazo min har suna uku,kaga ba dad'i ace ni koh sau d'aya banje ba barka ba sai suna. "Sunan ma ki fidda a ranki,dan inda mu'amular dana fi tsana,toh mu'amular ki da y'an unguwar chan ne,kin gane ai?. Kasa tai da kai,sosai take d'aure irin halin da Ya Ja'afar ya tsiro mata,yanzu da ta kara tambaya zai ce tai gaban kanta,hakan yasa tai shiru. Shi kuma yadda yaga batai gardama ba yasa yai tunanin zancen bai shige ta ba ne. Miemie ya ajiye kusa da ita ya bar mata d'akin. A hankali ta zame ta kwanta,sai ga hawaye ya zubo mata. Zaman gidan nan ya fara isar ta,hakurinta ya fara karewa. Tana ji yai ma Bintu sallama ya fice,kawai sai ta sau kuka a hankali marar sauti. Wato a dake ka a hanaka kuka?. **** Tun bayan fitarshi bayan ta gama kukanta Miemie ta fara,kukan har ya wuce kima, komai tayi taki shiru,kawai sai ta goyata tasa hijab akai suka fita t'sakar gida dan sanyin magriba. Bintun na t'sakar gida tana saita abin fad'i kan Ja'afar ya dawo tambayar Salma koh ta fita,dan komai a k'unnenta ya wakana. Jijjiga ta take tana yawo daga t'sakar gida zuwa zaure da ita,tasan Miemie

Chapter 7 of 11