Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 9/27/16, 7:56 PM - Messages you send to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info. 9/29/16, 8:34 AM - Queen Safiyyert馃憫: A BAK'IN AUREN KI... 漏Feenat Ja'afar. 1_Sauri take tamkar taci da k'a, kai daga ganinta ka ga marar gaskiya, a d'ai d'ai layin da zai sadata da gidanta ta t'saya tamkar munafuka ta d'an leka, da sauri ta komar da kai tare da dafe kirjinta mai barazanar fashe mata... "Na shigesu.. Ja'afar? Ta fad'a tana mai sake lekawa, sai karaf sukai ido hud'u dashi,tuni buguwar zuciyar ta ya k'aru, bata ta6a ganin shi a irin wannan yanayin ba. "Mey yasa kika fita bayan yace ka'rki fita?... Bak'in g'yalenta tasa tana t'sane gumin dake t'sat'safo mata, cikin jihadi ta fito daga inda ta boye harda d'aure fuskarta tamkar bata ganshi ba. Kanta na k'allon gefe tazo d'ai d'ai kofar gidan zata shige ba tare da ta k'alli yanayin nashi ba.. Turus taja ta t'saya, ganin yadda ya d'aura wani mukulli kan wanda ta rufe gidan dashi, cikin k'arfin hali fuskarta na gefe tace "ya haka? Wanda bai nan ma yafita,hakan yasa ta kara fad'in "Ya Ja'afar ya haka?.. Tamkar kububuwa yake cika, ji yake tamkar ya rufeta da duka dan takaici, Ashe d'uk uban rat'suwar Salma ta mai kan ta d'aina a fatar baki ya t'saya?.. Mota ya bud'e yana ko'k'arin shiga ta mot'so da sauri, "Ja'afar magana nake fa... A tunzure ya juyo da nufin kifa mata mari tai baya da sauri gabanta na fad'uwa. Lalle yau ta ta6o ran y'an maza, cikin bacin rai yai mata k'allon banza, "kin za6i gidan suna sama da sharad'i na koh? Toh mey kika dawo yi min gida? Koh kin manta da sharad'in da na baki na in kin fita toh kin fita "A BAK'IN AURENKI?... Ido ta zaro tana dubenshi, kawai sai ta dake, cikin k'arfin hali tace "A BAK'IN AURENA fa kace Ja'afar? Daga gidan sunan shine har kake wannan kumfar bak'in?.. Ta karasa tana y'atsine mishi fuska,kawai sai ya k'ada kai ya shige mota. Ganin da gaske tafiya zai yasa da sauri t ajiye t'siwar ta fara kiranshi, ina,tuni ya juya a kalar motarahi cikin zafin nama, da sauri ta mat'sa ganin sai ya iya bi ta kanta.. Tana ganin da gaske yake hakan yasa tuni ta t'sure, hannu ta aza bisa kanta cikin nadamar fitar da tai sunan da ba'a ma gaiyace ta ba, "na shiga uku ni Salma.. Na ja ma kaina wani bala'in.. "Yanzu igiyar Aure na biyu ta t'sinke kenan?.. Tuni zufa ta kara zubo mata dan tunawa da kalaman Babanta, "d'uk randa zaki kara maimaita haka Salma sai na 6alla kafarki in kin doso gidana.... Fad'uwar gabanta ta t'sananta,t'saf Baba zai aikata mata hakan, ta k'alli gabar,da yamma, ta ma rasa ta ina zata fara? Gefen dakalin gidan ta d'an dosana, da d'ukkan hannunta biyu ta dafe kai,tuni kalaman Ja'afar ya dawo mata, "in kin fita kin fita A BAK'IN AURENKI.... Ku biyoni Bayan sallah dan jin yadda zata kaya... By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 8:46 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. *3*- Kai ya k'ada mishi, _"aure ba shine mafita ba Ja'afar,ka g'yara wacce ke hannunka tukun,bana tunanin wannan shawara ce_. Murmushi yai tare da k'ada mishi kai _("I know)_.. _"Amma ka gane ba dan dad'i zanyi ba,nasan d'uk duniya ba abinda Salma taki jini irin nace zan kara aure,dole na d'andana mata mad'acin da ta d'andana min nima_. Murmushi Garba yai yana K'allonshi,wai yau Ja'afar ke maganar zai d'andanawa Salman sa mad'aci?.. Kai ya girgiza, lalle Salma tai wasa da damarta, dan yasan irin dimbin son da Ja'afar ke mata, sai dai gashi za a kaita a baro,dan ta fara sane ma abokinshi.. _"Bana tofa tawa ba nikam,nasan da kai da Salma sai Allah,ni d'ai kai tunani abokina,kar ka yanke hukunci cikin fushi azo daga baya ai nadama_... Baki ya ta6e, kan ya ciro mukulli a aljihunshi ya mika mishi, _"k'ar6i mukullin motarka,dan aure kam nayi na ma gama,kuma *Bintu* zan aura kasa ido_.. Ido waje Garba yake k'allonshi,kan ya k'yalk'yale da dariya, _"lalle ka d'ebo aiki..za kuma ka dasa ma Salma zargin ka cikin ranta tunda kasan komai_... T'saki yai kan yace _"zanso hakan ya kasance, dan zata fi jin haushi sosai_.. Kai Garban ya k'ada yana kunshe dariya, _"muje na sauke ka toh na Salma da Bintu,kai (scene) din nan zai dad'in k'allo wallahi_.. Ya karasa da dariyar keta. Murmushi kawai yai suka shiga mota,har suka isa gida Garba na mishi t'siya..da ya had'o shi da Salma zai kicin-kicin. ************************ A wajen Salma kuwa,sai da dare yai tana k'wance d'akinsu na da sai juyi take,wanda ita kanta ta rasa dalili,har yanzun haushin Ja'afar na kasan ranta na ya mata wulakanci, sai dai da ta tuna rabuwar igiyarta d'aya sai taji fad'uwar gaba. Yau gata a katifa ba ta ita da Ja'afar d'inta ba?..yau d'aya ta raba alakar matashin kanta(kafad'ar Ja'afar) sai pillow... Hannu takai kuncinta,da mamakinta hawaye take,kawai sai ta ida karasawa ta fashe da kuka.. Wanda kai da gani na k'ewar Jafaririn ta ne da t'sant'sar nadama,amma ina,zuciya taki amsar hakan.. Ga uban sauro da ya damu k'unnenta da ihu duk da da Katanga a t'sakaninta dasu(net), ga uban zafi ba wuta ba (Gen), d'uk t'siya tasan da a gidanta ne da yanzu tana shan iskar injin da Ja'afar ke k'unna mata d'uk dare ta k'wanta dan bata bidar zafi.. Ga mama tace ba mai tada mata inji Babanta baya gari, kuma bata kud'in mai... ***""* Shima hakan take ga Ja'afar, kusan a hali d'aya suke,sai dai shi kawai ya kura ma fankar d'akin da ke kad'awa a saman d'akin ido. Tabbas har yanzun baida sama da Salma koh a kasan zuciyarshi.. Yana sonta, so marar misali,duba ga yadda suka gina soyayyar tasu kamin aure.. Da za'a ce mishi a da Salma zata sauya hali gaba d'aya musamman akanshi da zai mu sa... Juyi yai ya jawo filo,d'uk t'siya tanan yai k'ewar Salma.. Dan karamin t'saki yai kamin ya tashi yai waje dan kashe inji. *By* *Feenat Ja'afar* 9/29/16, 8:48 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 4- Salma Umar Y'a ce ta biyu gun Mama(Haj Rabi'a) da Baba(Malam Umar),y'an asalin Yobe ne,kasuwanci ya kawo kakansu Kano da rabon su Salma. Su biyu kawai ne a gun kakan su Malam Bukar Mai buhu,baban su Salma ne karami, sai yayanshi Baba Aji, yaranshi a kallah za suyi (16),yayin da Baban Salma ke da uku,Aisha (Aunty A'i)dan tafi Salma sosai,Salma,sai Ummi. Kasuwanci ne gadon su Baba,dan koh bayan rasuwar kakan su Salma sun cigaba da juya abinda ya rage musu. Suna taimakon juna sosai,hakan yasa kansu yake a had'e, duk da rufin asiri ne kawai na Allah. Sannan d'ai-d'ai iyawa sun bama yaran su karatu da tarbiya,suna da t'sanani musamman Baban su Salma. Sai dai fa ita Maman su gani take kakarsu ta yanke saka,tunda Allah ya hore mata yara mata uku setin samira ta zuba jari,shi yasa d'ukkan wani abu akan A'i yake karewa dan ita tasa a lokacin. Ba lefi,ak'wai dan k'yau irin na ainashin mutan kanuri,sai kuma Maman dake asalin Shuwa,ba farare bane,za dai mu iya kiransu da _"black beauties"_sirrin su kuwa,diri ne da yalwar gashin ka da _"beauty point"_ _(dimples)_.. Wanda tamkar kowa diga mata ake. Hakan yasa kasuwar Aunty A'i ta daga da sauri,tuni k'wa Mama abin nema sai ya samu,hakan yasa ta kara sa ma sauran Burin da yafi na Aunty A'in.. Barin Salma dake doguwa ce cikin su. Ita kam Salma bata san ma ana yi ba. Kasantuwar shagonsu Baba ya zama biyu sai ya zamana aiki yai musu yawa, har bai samun damar dawo wa gida cin abinci sai d'ai Ummi koh Salma su kai mishi. Ranar kaiwar Salma ne,tai shirin Islamiya ta doshi shagon su Baba. Tunda ta ajiye abinci taki gaba taki baya,kamar dai da alamun an mata abu daga gida. Murmushi Baban yai kan yace tazo.. _"mey aka miki uwata?_ Hawaye ta dan matso halamar 6aci. _"Mama ce ta hana ni kud'in tara_. Kai Abban ya k'ada yana murmushi kan ya sa hannu a aljihu ba chanji,gudar naira dari ya fitar kan ya nuna mata shagon kusa dasu taje tai chanji. Da sallamarta ta shiga,ta gaida shi,shago ne na kayan k'yallin mata na sawa, attamfofi da laces,ga materials kala kala,d'uk zuwanta bata ta6a shiga shagon ba sai yau. _"Salamatu y'an mata,ina su Ummi?_ Murmushi tai mishi,dan tana ganin shi gun su Baba, dattijon na da kirki da fara'a, banda yaron shagon shi da koh k'allo bai mata ba, _"suna gida,Baba ne yace aban chanji_. Kai ya k'ada, kan ya k'allo na zaune a acikin shagon rike da littafi halamar yana dubawa. _"amm *Ja'afar*_.. Kai ya dago karon farko, _"Na'am Abba_,, sai lokacin ya kula da Salma, _"Ba wa Salma naira ashirin ta tafi kar tai latti_. Kai ya k'ada kan ya kara k'allo Salman wacce sai hange take koh za taga wani dan islamiyar su tana mika hannu. _"k'ar6i man_.. Juyo wa tai taga yana miko mata kud'i fuska ba fara'a, da sauri ta k'ar6a tana tafiya tana fad'in _"na gode Abba_. Da k'allo Ja'afar ya bita,yana ganin Ummi ce mai rawar kai ashe sauran ma haka suke. _customers_ ne suka tada shi ya shiga shagon. Washegari ma sai ga Salma,wannan karan koh shagon su Baba bata je ba tai shagon su Ja'afar. Da mutane da kusan d'uk y'an mata ne suna siyayya, yana ganin Salma ya had'e rai, sam yaki jinin a 6ata yaro da kud'i, ita kam Salma harda mishi murmushi tana dago mishi hannu da kamar abu aciki. T'saki yai,kan ya cigaba da abinda ya ke,sai da ya sallami kowa kan ya ganta tana gaida Abban shi da ya fita yana nuna mata cikin shagon. Da dan gudinta ta shigo,a tunanin shi kud'i Abban yace ta kara k'ar6a gun shi,dan da zumudinta ta gaida shi. _"dama Abba ne yace in_..... Cikin fad'a-fad'a ya katseta, _"bani da chanji nima yau,jiya an baki kinji dad'i shin_.... Shiru yai sakamakon idonta da yaga ya cika da k'walla tana k'allonshi. D'uk kuma sai jikinshi yai sanyi.. A hankali ta ajiye masa gudar naira ashirin akan benci ta juya tana goge hawaye. Ba dai kud'in shi ta biya shi ba dan ya mata fad'a? Da sauri ya d'auka da niyar k'wada mata kira ya mayar mata sai dai tuni tai nisa sosai. D'uk kuma sai yaji bai k'yauta ba. Yana nan zaune har Abba ya dawo, _"kaga Salamatu wai kud'in ka na jiya ya hau shine ta dawo ma dashi ba"_.. K'allon Abban yai da sauri, _"Abba kud'i kuma?_ K'allonshi yai kan ya k'ada mishi kai, _"sai da nace ta tafi wai A'a tana da wani,Salma ak'wai hankali, ashe batai ma magana ba?_ Shi dai Ja'afar yai shiru yana jin Abba,sai ya kara jin wani iri. *By* *Feenat Ja'afar*. 9/29/16, 8:50 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAK'IN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. *5*- Washegari sai zuba ido yake yaga Salma shiru,dan d'uk jiya ji yake bai k'yauta mata ba. Sai d'ai Salma har k'wana biyu shiru ba koh kalar ta sai Ummi ke zuwa kawo abinci. Ranar Ummi ta kawo zata tafi ya t'sayar ta da tambayar ina Salma k'wana biyu? "tana gida Yace "ya bata kawo abinci sai ke?.. Tana zungura baki tace "sai gobe ne nata kawowar. Dan koh ita Ummi Ja'afar ke hanata zuwa gun Abba mai k'yautar naira biyar goma.. Sam baida fuska,shi yasa taki jinin shi. Washegari kuwa tun da ya ga lokacin kawo abinci yayi yake k'allon shagon su Baba,yau ga k'ananan shi a shagon baida mat'sala. Kamar ance ya dago,sai gata kuwa sanye da kayan islamiya,sai dai duk tai kicin kicin fuska ba walwala. Yana k'allon yadda ta t'suguna ta gaida su Abba kamar kullum, tana da nut'suwa ba kamar Ummi uwar bankaura ba. Tashi yai kamar mai tafiya wani gun,dai dai k'wanar da take bi gida ya t'saya,sai gata kuwa,har zata wuce ya kira ta,suna had'a ido ta had'e rai,sai ta bashi ma dariya. Hannu yasa ya ciro naira ashirin d'in ya mika mata yana murmushi, a dan sace ta k'allo shi kan ta kawar da kai tare da girgiza mishi kai. *"Salma*..K'all onshi ta kara,ganin yana murmushi sai abin ya bata mamaki,bata t'sinke da lamarin ba sai ji tai yace tai hakuri, kai ta kawar kawai, kin huce? tana wasa da hijab d'inta ta daga mishi kai, "toh ki k'ar6a in kin huce,na bar miki.. Kai ta kara girgiza mishi,kan tace "A'a ka barshi fa.. "baki hakura ba kenan Salma?.. Kai ta k'ada mishi, yace "toh ki k'alle ni ki amsa maza kar kiyi latti kinji K'anwata.. Da lallami yasa ta sakko harda dariya,har kusan makaranta ya rakata ya dawo,yana mai mamakin fara'ar shi yau ga yarinya Salma,sam shi baida sakin fuska musamman ga mace d'uk k'ank'antar ta k'wa. Tun daga ranar ya zamo in Salma ta kawo abinci sai Ja'afar ya rakata ya kuma bata ashirin d'uk bayan k'wana biyunta. Sosai sun saba,har in batazo ba baya jin dad'i, har su Abba suka kula da sabon kawancan Ja'afar da Salma,ana haka Baba yasa ya dinga ma wa su Salma _lesson_ tare da kannenshi tunda ya gama _secondary_ _admission_ yake jira. Koh a gun _lesson_ misalin Ja'afar a Salma yake t'sayawa, in k'wa duka ne koh t'sawa Salma bata ciki,sai dai yai ma k'annenshi, hakan yasa tun tana karama yaran suke ce mata Salma budurwar Ya Ja'afar. A lokacin takanyi bori kan bata so,har takai da ta kai kara gunshi,sai dai mamakinta dariya ma yai mata,yau da gobe har Salma ta saba da tsokanar k'annen Ja'afar . Karatu ake sosai za ai _coming interest_, sai dai ba Ja'afar dan ya tafi Zaria sakamakon _admission nashi da ya fito. Sosai Salma tai k'ewar shi,har hakan yasa ta d'aina kai abinci shago sai almajiri,a hankali har k'ewar ta sake ta suka gama jarabawa sai zaman jiran sakamako... Sai dai Ya Jaafar na chan k'wance kasan zuciyar ta. Yau ga Salma a _boarding_ babban burunta kenan makarntar k'wana. ************************** Lokaci ya shud'e, kamar wasa yau ga nan Salma an zana _J.S.C.E_, hutun mai dan nisa ne na yau. Mai nut'suwa ce a d'uk y'an gidan su,a layin su,dama unguwar gaba d'aya, Salma abar k'watance ce,musamman rashin yawanta,kullum kaje in tana hutu toh za ka samu Salma a gida. Batta k'warafniya irin ta y'an mata masu tashen tashi,asalima fitar ta in tai yawa toh islamiya ce ta yamma, sa6anin su Ummi da tuni tun kar ta far ta kone, dan wanka iya wanka Ummi ta iya,hakan yasa Mama ta kara d'aure mata gun siyan kayan k'arya. Dan a ganinta ta gama da kason Aunty A'i tunda har an kawo sadaki, kuma irin wanda mama ke da muradi. Ita kam Salma zai wuya ka ga tama sanya g'yale bare har ta zauna k'yali. Gata dai mama ita tafi sawa buri, ga ta kuma y'ar _boarding_. *By* *Feenat Ja'afar*. 9/29/16, 8:52 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 6-A dai-dai k'wanar su Ja'afar take,dawo warta daga islamiya kenan,sanye take da dogon hijab ruwan kasa mai yashi har kusan kasa,rataye da jakar littafai da Qur'ani a hannu,sai dan asirin _skirt_ nata na attamfa da ya fito _green_ da ruwan kasa, duguwa ce,ba zangal ba,tana da kaurin jiki,dan ta fita sahun ramammu,tafiyarta a nut'sue tafi komai d'aukar hankali. Kamar kullum ta daga kai dan k'allon gidan su Ya Ja'afar kamar yadda ta saba k'ewar shi ta kawar da kai, sai dai taku biyu taja ta t'saya tamkar an t'sayar ta. Kanta duk'e dauke da murmushi,cikin nut'suwa ta kara k'allon kofar gidan dan tabbatar da wanda ta gani.. *"Ya Ja'afar*?...ta fad'a a zuciyarta lokacin da ya taso yana mata murmushi. Ikon Allah,wai kunyarshi kuma take ji,cikin nut'suwa ta d'auke kanta daga gareshi ganin ya karaso. "Assalam Alaikum Malama Salma.... Wani irin buguwar zuciya taji ya ziyarce ta,shekara uku da wani abin ba wasa ba,hatta muryar Ya Ja'afar ta sauya mata. Cikin nut'suwa ta dago da murmushi ta amsa mishi,kamin ta gaida shi a kunya ce, shi dai kawai k'allonta yake yana murmushi, kamar mai mamakin kara girmanta,ga wata nut'suwa da ta kara shigarta. D'uk sai ya kara yaba Salman nashi,ganin shirun yai yawa yasa da hannu ya nuna mata hanya halamar su wuce. Dan satar K'allonshi tai kan ta sunne kai suka fara tafiya. "Salma koh murnar gani baki yi,ba koh tambayar yaushe nazo? Kai duk'e tace "yi hakuri,yaushe kazo?.. Kai ya k'ada da murmushi,kan yace "jiya. Tambayar yaushe gamo yake mata, yadda take kunyar tata gun bashi amsa d'uk sai ya ji shi wani iri,mace mai kunya itace muradinsa. Da haka har kofar gida ya rakata yana mata tad'in makaranta da yadda suka juma basu gamo ba. Ummi ya k'allo achan dan nesa dasu tana tad'i, sai ya tuna mata yasha zuwa ai. Ita dai daga murmushi sai k'ada kai da Umm,a'a,d'uk ta takure yau a gaban Ja'afar d'inta. Ganin haka yasa yai mata sallama tai gida.. A katifa ta zauna tana cire hijabi,ta rasa wani irin farin ciki take ciki na ganin Ya Ja'afar d'inta yau. Sai murmushi take saka cike da kunya ita kad'ai kamar yana ganinta. A haka har Ummi ta cimmata, dan harara ta sakar mata gami da had'a rai. "Yanzu Ummi kinyi dai dai kenan? A y'atsine ta k'allo ta tana ninke g'yale, "da nai miki mey? Iya jaraba.. Kai Salma ta k'ada kan tace "dan t'sabar wulakanci ashe Ya Ja'afar yasha zuwa gidan nan nema na in yazo gari muna sa6ani sau biyu yana fad'a miki amma koda wasa baki fad'an ba? Allah kin ban haushi.. "Mtsww.. T'saki Ummin tai kan ta ta6e baki,tuni Salma ta kule,sam ta t'sani t'saki, bare ga Salma K'anwar ta. "Na zata wani abin kirkin ne wallahi, toh meye nawa dashi da zai mayarni y'ar aiken shi?.. Anki a fad'a miki d'in ki d'au mataki toh.. A tunzure Salma ta tashi tayo kan Ummin sukaji Mama na magana a kofar d'aki, "Kun fara cin kan koh? Yara kamar masu ganin hanjin junansu? Baya Salma tai tana harar Ummi, "Mama kimin tsakani da ita toh,ta fita harkata dan bata da kunya sam wallahi.. A y'atsine Ummi ta harare ta,"ka ga kunya manya,akan wannan mai dan uban d'acin ran kike wannan kumfar bak'in?...baki ta ta6e kan tace "Kin k'wa kama abga in dai Ja'afar ne.... "Ke Ummi... Bana son fit'sara fa,kullum ina sanarki Salma yayarki ce,dole ki bata girma, koh nai mugun sa6a miki.. Maza bata hakuri. Tana chunno baki ciki ciki ta bawa Salma hakuri,ita kam har ta fara hawayen bak'in ciki. "Toh fito ki biyoni.. Mama ta nuna ma ummin kofa da hannu.. *By* *Feenat Ja'afar* Like 路 Reply 路 Report 路 Jul 20 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 6-A dai-dai k'wanar su Ja'afar take,dawo warta daga islamiya kenan,sanye take da dogon hijab ruwan kasa mai yashi har kusan kasa,rataye da jakar littafai da Qur'ani a hannu,sai dan asirin _skirt_ nata na attamfa da ya fito _green_ da ruwan kasa, duguwa ce,ba zangal ba,tana da kaurin jiki,dan ta fita sahun ramammu,tafiyarta a nut'sue tafi komai d'aukar hankali. Kamar kullum ta daga kai dan k'allon gidan su Ya Ja'afar kamar yadda ta saba k'ewar shi ta kawar da kai, sai dai taku biyu taja ta t'saya tamkar an t'sayar ta. Kanta duk'e dauke da murmushi,cikin nut'suwa ta kara k'allon kofar gidan dan tabbatar da wanda ta gani.. *"Ya Ja'afar*?...ta fad'a a zuciyarta lokacin da ya taso yana mata murmushi. Ikon Allah,wai kunyarshi kuma take ji,cikin nut'suwa ta d'auke kanta daga gareshi ganin ya karaso. "Assalam Alaikum Malama Salma.... Wani irin buguwar zuciya taji ya ziyarce ta,shekara uku da wani abin ba wasa ba,hatta muryar Ya Ja'afar ta sauya mata. Cikin nut'suwa ta dago da murmushi ta amsa mishi,kamin ta gaida shi a kunya ce, shi dai kawai k'allonta yake yana murmushi, kamar mai mamakin kara girmanta,ga wata nut'suwa da ta kara shigarta. D'uk sai ya kara yaba Salman nashi,ganin shirun yai yawa yasa da hannu ya nuna mata hanya halamar su wuce. Dan satar K'allonshi tai kan ta sunne kai suka fara tafiya. "Salma koh murnar gani baki yi,ba koh tambayar yaushe nazo? Kai duk'e tace "yi hakuri,yaushe kazo?.. Kai ya k'ada da murmushi,kan yace "jiya. Tambayar yaushe gamo yake mata, yadda take kunyar tata gun bashi amsa d'uk sai ya ji shi wani iri,mace mai kunya itace muradinsa. Da haka har kofar gida ya rakata yana mata tad'in makaranta da yadda suka juma basu gamo ba. Ummi ya k'allo achan dan nesa dasu tana tad'i, sai ya tuna mata yasha zuwa ai. Ita dai daga murmushi sai k'ada kai da Umm,a'a,d'uk ta takure yau a gaban Ja'afar d'inta. Ganin haka yasa yai mata sallama tai gida.. A katifa ta zauna tana cire hijabi,ta rasa wani irin farin ciki take ciki na ganin Ya Ja'afar d'inta yau. Sai murmushi take saka cike da kunya ita kad'ai kamar yana ganinta. A haka har Ummi ta cimmata, dan harara ta sakar mata gami da had'a rai. "Yanzu Ummi kinyi dai dai kenan? A y'atsine ta k'allo ta tana ninke g'yale, "da nai miki mey? Iya jaraba.. Kai Salma ta k'ada kan tace "dan t'sabar wulakanci ashe Ya Ja'afar yasha zuwa gidan nan nema na in yazo gari muna sa6ani sau biyu yana fad'a miki amma koda wasa baki fad'an ba? Allah kin ban haushi.. "Mtsww.. T'saki Ummin tai kan ta ta6e baki,tuni Salma ta kule,sam ta t'sani t'saki, bare ga Salma K'anwar ta. "Na zata wani abin kirkin ne wallahi, toh meye nawa dashi da zai mayarni y'ar aiken shi?.. Anki a fad'a miki d'in ki d'au mataki toh.. A tunzure Salma ta tashi tayo kan Ummin sukaji Mama na magana a kofar d'aki, "Kun fara cin kan koh? Yara kamar masu ganin hanjin junansu? Baya Salma tai tana harar Ummi, "Mama kimin tsakani da ita toh,ta fita harkata dan bata da kunya sam wallahi.. A y'atsine Ummi ta harare ta,"ka ga kunya manya,akan wannan mai dan uban d'acin ran kike wannan kumfar bak'in?...baki ta ta6e kan tace "Kin k'wa kama abga in dai Ja'afar ne.... "Ke Ummi... Bana son fit'sara fa,kullum ina sanarki Salma yayarki ce,dole ki bata girma, koh nai mugun sa6a miki.. Maza bata hakuri. Tana chunno baki ciki ciki ta bawa Salma hakuri,ita kam har ta fara hawayen bak'in ciki. "Toh fito ki biyoni.. Mama ta nuna ma ummin kofa da hannu.. *By* *Feenat Ja'afar* Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 20 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 7_Washegari ma ta fito zata makaranta sai gashi shi da abokinshi Garba suna tafiya. Ido ya kura mata ganin tai kasa da kai tana murmushi. Sai ya k'ada kai suka karasa,cikin sanyin murya ta gaida su,Garba kad'ai ya amsa,shikam Ja'afar k'allonta kawai yake yana murmushi, kamar mai son sai sun had'a ido. "Malama Salma fa kar tai latti a mata bulala abokina.. Kasa ta kara da kai tana dan dariya, shikam gogan sai binta yake kawai da k'allo,kan ya nuna mata hanya kan wai su rakata hanya. Ba musu ta wuce suka jera,Garba sai shakiyanci yake zuba musu,murmushi kad'ai ne nasu har suka zo bakin _gate_ d'in islamiyar. Ka'ro na farko suka k'alli juna cikin ido,da sauri ta K'awar da kanta tana murmushi, shikam harda k'ada kai, tuni Garba ya harbo jirgin nasu,sai ya hau shafa ha6a yana k'allonsu,musamman abokinshi da yace bai san so ba.. Hannu Ja'afar ya kai aljihu yana lalube,ita kam sai ta hau satar k'allon shi ganin mey zai yi. Da mamakinta k'wa sai gashi ya fito da naira ashirin yana mika mata. K'alloshi tai tana kunshe dariya,sai ta k'ada mishi kai, "Kud'in tara ne fa Salma, ki k'ar6a ki sai hambididi... Dariya Garba ya fara harda rike ciki,itama wacce take rikewa ta fito fili, sai ta sa hannu a baki dan rufe sautin ta.. Shikam Ja'afar kawai sai ya hard'e hannu yana K'allonsu, musamman Garba yadda yake k'yak'yata dariya. Shikam ba kasafai ya iya dariyar keta ba irin ta Garba,shi yasa wataran yakan kularshi a abu. "La Malam Ja'afar...... Gaba d'ayan su suka juya k'allon mey magana. Ja'afar take k'allo tana murmushi halamar jin dad'in ganin shi, shikam tuni ya had'e rai yana k'allon ina ma ya santa. Kamar tasan mey yake tunani tace *"Bintu*(Na Rufaida Omar) ce,dalibar ka a day... Salma ya k'alla wacce itama ke kallon Bintu,kan ya

Chapter 1 of 11