Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 11
abinda matarsa tayi min sai naji inama son auran.
DUTSE
A wajan Nahrna kuwa ba yadda ta iya haka ta nufi gidansu sosai y'an gidansu suke binta da kallo Mamarta dake kwance ba wani cikakkiyar lafiya ce da ita da sauri ta tashi tace "wa nake gani Nahrna badai auran kika k'ara kashewa ba yanzu tunda kika aure ko k'iyarki bamu sake gani ba haka rayuwa zata yuwu kuwa?" Ta ida maganar tana kallon Nahrnah kuka Nahrnah ta fashe dashi tana cewa "wallahi Mama ya sake ni kuma ninaja ma kaina dan Allah ki yafe min nayi nadama" k'ananta dake kallonta a banzace dan kuwa haushi take baso kwata-kwata Nahrnah bata da mutumci in yau akace ta zama wani abu Mamarta kuwa salati take tace "yanzu Nahrna da kika kaso auran naki kika zo nan mi kike so inyi miki ai gaki ga gidan nan badai zaman gidan nan ba gaki gashi sai kizo kuyi maleji da k'annanki" sosai Mamar tayi mata fad'a inda ta fara zaman gidan nasu a d'aki d'aya suke kwana da k'annanta wani lokacin su tabka mata rashin kunya dole tayi hakuri ba damar tayi magana kud'in kashewa ma gagararta suke sai dai ta dawo tana wankau ko surfe shine zata samu y'an kud'i wadda ba wasu bane sosai Zuby take d'an taimaka mata ganin tayi nadama Nahrnah sosai ta gaji da zaman gidan sosai take so tayi aure ko waye ma indai zai rufa mata asiri ganin tana son auran yasa Hamza abokin Malam dama shi ya had'a auran Malam d Nahrnar yayi bak'in cikin abinda tayi yace "ai wallahi ba k'aramar asara kikayi ba mutuwar auranki da Malam amma yanzu ga wani nan na kawo miki sunan sa D'anliti matansa uku kice ta hud'u dan haka in kina so gashi in kuma zaman gida kikafi so to?" Ya ida maganar yana kallonta d'ago kai tayi tana kallon D'anliti dake washe mata baki duk goro ya batasa ga wani uban tunbi batasan sadda ta fashe da kuka ba lallai tayi asara wallahi ba kowa zai samu kamar Malam yayi wasa da damarshi ba da sauri Hamza yace "au baki ra'ayi ne kika wani tasamu gaba kina kuka?" Da sauri tace"a'a wallahi ina so Allah yasa alkhairi" dan kuwa inta ce ma bata so to zaman gidansu kwata-kwata bata jin dad'insa gara ko yayane tayi auran zai fiye mata kwanciyar hankali sosai D'anliti ya washe wangameman bakinsa yana murnar samun mata, haka aka d'aura aure aka kaita gidan D'anliti k'annanta kowa gani tayi sunfi kowa murnar matsawa ta basu waje sosai take ganin rashin ta ido ga uwar gidan D'anlitin dan kuwa sai ubanda take so shi ake yi sosai take nadama haka dai take tsantsar hakuri zama a gidan D'anlitin dan kwata-kwata intace tana son D'anliti to tayi k'arye kwata-kwata k'azami ne gaba d'aya gidan nasu da matansa k'azamai ne gasu sun had'e mata kai ita kad'ai ke harkarta ba wadda keta tata.
WANNAN KENAN
***** A can Kano kuwa sakinta Maryam tayi jin su Ummeeta na salati cewa Hjy Sa'adha ta suma saboda tashin hankali ganin abun take kamar a mafarki sosai suka shiga tashin hankali wayar suka d'auka suka dannawa Dr Aysha kira koda ta d'auka jin Kukan Hanan yasa cike da rud'u tace "mi yake faruwa ne?" Hanan dake kuka ta sanar mata iya abunda suka sani sosai ta shiga tashin hankali da mamaki kai tsaye gidan ta taho ta d'auke su sai Asibiti sosai ta k'ara mamakin rashin ganin Alhaji Mustapha mi yake nufi ne?.
Bayan an kwantar da ita an samata k'arin ruwa likita yace "ta tsorata ne shi yaja mata suma dan haka su barta tad'an huta" Dr Aysha kuwa amsa maita kawai tana kiran Mahaifiyar Hjy Sa'adha wadda suke kira da INNEE Sosai Innee ta rud'e ta taho asibitin tana tabbayar miye musabbabin abinda ya faru sai dai Dr Aysha ta kasa fad'a mata dan kuwa Innee bata d'aukar shirme tana tsayawa inda gaskiya take ne dan sam zatai masu abinda basu tunani.
Zaune suke a d'akin da aka kwantar da Hjy Sa'adha Innee dake kallon yadda d'iyarta ta lokaci guda ta rame tace "Aysha kindai k'i gaya min miya faru ko bari na kira mijin nata naji ko miye tunda naga ban gansa asibitin nan ba tabbas itace bata da gaskiya" ta ida maganar tana danna mai kira cike da tsoro Dr Aysha ke kallon Innee shikenan sun shiga uku yau da jarabar tsohowar nan sosai sukai magana da Innee da Alhaji Mustapha gyad'a kai kawai take daga k'arshe tace "kayi min dai-dai daka auri yarinyar ita kuma zata tashi ne zata had'u dani" tana gama fad'ar haka ta hanke wayar tana kallon Dr Aysha datai k'asa da kai su Maryam dake sauraran wayar da take da gaske dai ya aure Khaleesat innalillahi wa'inna ilaihir raju'un shikenan su sun d'auka duk tsoratar da ita kawai yake ba gaskiya bane ashe da gaske yake tashi Maryam tayi ta fice daga d'akin dan kuwa zuciyata kamar zata fashe lallai saita tsaya taga ranar da Khaleesat d'in zata tare taci alwashin saita mata rashin mutumci kana tabar gidan dan kuwa izuwa yanzu ta riga da tasan Alhaji Mustapha yayi mata nisa nisan da bazata iya taddashi ba.
A d'akin da aka kwantar da Hjy Sa'adha kuwa sosai Innee ke surfa bala'i inda take shiga bata nan take fita ba cewa take "au dama ke dai ba k'awar arzik'i bace kenan harda ke za'a had'a baki a cuci baiwar Allah kinsan baccin kin kasance y'ar uwa ga Hjy Sa'adha ta b'angaran uba da yau sai kinbarta har haba da ai ko tayi wannan tunanin ke mai hana ta ne kuma y'ay'a da take so a haka ake neman yaran ne saita rok'i Allah ai baya bacci ko yasan damuwar kowa ko kuma ko a shari'a wannan cikin da kuka k'ak'uba ma yarinyar da bata ji ba bata gani ba ba wadda zai rabata da abinda zata haifa dan kuwa ko koto kukaje bazata amshi wannan abunda ta haifa ta bata ba bari ta tashi ita kuma zata gamu dani ne ai ba haka na koya mata tarbiyya ba" ta ida maganar rai a b'ace Dr Aysha kuwa ita dai hakuri take ta ba Innee ganin hakurin da take bata ma k'ara zugata take yasa tayi shuru da bakinta wannan haniyar ce tasa Hjy Sa'adha fara motsawa da sauri suka matsa kusa da ita banda Innee dake jin haushin d'iyartata ganin ta farka sai sambatu take akan auran da Alhaji Mustapha yace yayi da sauri Dr Aysha ta rik'e hannu ta tace "sannu kinji ya jikin naki?" Kallon Dr Aysha tayi tace "Dr Aysha kice min ba gaskiya bane please wallahi bazan iya had'a ko wacce mace da mijina ba kice min mafarki nake dan Allah" ta ida maganar tana fashewa da kuka Innee dake kallon ta cikin b'acin rai tace "kware kuwa da gaske ne ke sadda kikai rashin imaninki wani ya sani ne to dan haka yanzu ki shirya amsar ta a matsayin kishiya" wani irin kuka ne ya k'ara zo mata da wata irin masifaffiyar tsanar Khaleesat lallai saita hana Khaleesat zaman lafiya indai tace zata zauna da mijinta ganin kukan da take basu ankara ba ta k'ara sumewa dan kuwa sosai Allah yasama Hjy Sa'adha tsananin kishi ganin ta k'ara suma yasa Innee jikinta yin sanyi su Ummeeta kuwa kuka suke sosai Dr Aysha ke bata taimako gaggawa ganin data farka saita k'ara suma yasa Dr Aysha ficewa a firgice ta kira likita sosai yayi fad'a kan cewa mi yasa data farka ba'a kirasa ba dukansu fita sukai waje allurar bacci akai mata ganin yadda take farkawa ba'a cikin hankalinta sosai yanzu Innee ta d'an nuna damuwa tasan d'iyarta da kishi amma ai ita taja ma kanta komiye shi kansa Alhaji Mustapha kasa hakuri yayi saida yazo asibitin sosai ya shiga damuwa ganin halin da take ciki amma ita taja harya sanar da ita ta wannan hanyar yasan tabbas kanta bazai iya d'auka ba yaso sanar da ita a tsanake ne amma laifin tane ai,
Dr Aysha ce zaune ta amsa number Laure sai danna mata kira take amma ba'a d'auka wayar Ummeeta ta amsa ta sake kira nanma dai k'arshe ma akace mata a kashe take sosai ran Dr Aysha ya b'ace dan wallahi duk inda nake sai sun nemo ni sunmin gargad'i mai zafi karna sake na shigo cikin gidan nan wai a matsayin matar Alhaji Mustapha ina ni ina had'a kishi da Hjy Sa'adha...........✍️
*Wai gsky Hjy Sa'adha akwai kishi akwai k'ura nan gaba fa banga laifin bafa miji kamar Alhaji Mustapha son kowacce mace dole a murza kishi*🥱
*FATEEMAH RABI'U (ZAHRA ROYAL STAR CE)*🥰✍️
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
[9/12, 11:54 AM] ZAHRAH ROYAL STAR 🥰: *🤦‍♀️💔ITA CE K'ADDARATA 🤦‍♀️💔*
*©ZAHRA ROYAL STAR CE*🌟✍️
*ROYAL STAR WRITIN'S ASSOCIATION*
PAGE3️⃣9️⃣➡️4️⃣0️⃣
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI
___________________✍️Sosai nake samun kulawa ta musamman a wajen Gwaggo da Inna gaje izuwa yanzu ciki na yayi girma a kwana a tashi babu wuya a wajan Rabb dan kuwa ciki na yayi girman da zakai mamaki haihuwa ya ko gobe, a wajan su Hjy Sa'adha kuwa neman duniya sunma gidanmu sai dai ta warke amma hankalinta a tashe yake dan kuwa sosai Alhaji Mustapha ke gyaran d'ayan part d'in dan kuwa ina Haihu da kwana arba'in zan tare itafa ganin abun take kamar ba gaske ba kuma Alhaji Mustapha babu abinda ya rageta dashi sosai yake bata kulawa kamar da sai dai tak'i ta kwantar da hankalinta, shigowar Dr Aysha ta zauna kusa da ita yasa ta dawo tunanin Khaleesat d'in da takeyi na cewa yanzu fa na kusa haihu koma na haihu Dr Aysha ta dafata tace "ki rage wannan tunanin fa karya sa miki ciwo kuma Albishirinki mun gano a inda wannan makirar d'iyar take Khaleesat" da sauri Hjy Sa'adha tace "da gaske" tana tashi tsaye "kware kuwa yanzu na tabbata in mukaje muka bige mata wunin ko k'afarta bazata tako a cikin gidan nan ba" cewar Dr Aysha da sauri su Maryam dake zaune suka had'a baki wajan cewa "please atafi damu" wani kallon tayi masu yasa suka ja bakin sukayi shuru Hjy Sa'adha tace "ina ku ina wani zuwa wajanta ku bari sai tayi kuskuran shigowa cikin gidan nan nanne ku kuma zan baku Okay d'in kuce ubanta la'ada waje" ta idasa maganar tana huce na b'acin rai sosai sukai murnar abinda tace masu ba b'ata lokaci domin zuwa garin Kankia.
Ni kuwa a dai-dai wannan lokacin muna zaune tsakar gida mu duka Sakina na d'an matsamin k'afa, yatsine baki nake domin kuwa tun jiya nake jin ciwon ciki kad'an kad'an yanzu kuwa da aka tsunkule ni bansan sadda na saki salati ba da sauri har suna rige-rigen cewa "yaya dai Khaleesat ko dai haihuwa ce ga Malam baya kusa" da sauri Gwaggo tace Inna gaje ta sanyo hijabinta mu nufi asibitin dake garin domin kuwa kusa muke da asibitin da sauri suka d'auke ni sai asibiti basu kira Malam ba har muka isa izuwa yanzu sosai nake jin jiki dan kuwa salati kawai nake bansan inda kaina yake ba koda isarmu danda nan aka amshe mu d'akin haihu aka sani su Gwaggo hankali a tashe dasu Haneefa Sakina tace "gaskiya ya kamata a sanar da Abba Mama" da sauri Gwaggo tace "kirasa dan kuwa ta jima gaskiya ko anada muk'atar nemansa a asibitin in hakan ta taso" kiransa akayi bugu d'aya Malam ya d'auka Sakina kemai bayanin komai suna asibiti sosai yayi fad'an mi yasa tun tuni basu sanar dashi ba kashe wayar yayi da tashin hankali ya iso asibitin a rud'e sai zamga masifa yake danmi basu kirasa su sanar dashi ba su dai basu tankai mai ba dan kuwa suma hankalinsu na waje na ace har yanzu shuru,
Ni kuwa sosai nake shan wahala har suma nayi sosai nake tuna Ummah na a dai-dai wannan lokacin ganin cewa yarinya nashan wahala yasa wani likita cewa ayimin aiki fita yayi ya nufo wajan su Abba da sauri har suna had'a baki wajan cewa "likita ta haihu ne" likitan ya amsa da cewa "bata haihu ba gaskiya ayiki muke shirin yi mata kasa hannu a nan dan tana shan wuya wallahi" sosai suka shiga tashin hankali ba d'an kad'an ba hannun Abba har kyarma yake wajan sa hannu likita na shiga d'akin haihuwar dai-dai lokacin ni kuma haihuwar ta taho gadan-gadan cikin ikon Allah da buwayarsa na haihu da kaina na haifi d'iya mace ina Haihu wani irin bacci ya kwashe ni mai cike da gajiya sosai likita ya k'ara fitowa da murmushi yake masu Albishir d'in cewa na haihu sosai Malam harda y'an hawayen farin ciki so Haneefa kuwa harda su tsalle bayan an gyara ni suka shigo d'akin da aka kwantar dani inata bacci ga jaririya nan itama sai bacci take sosai yarinyar take kama da ubanta kyakkyawar gaske gata fara sol Gwaggo tace "Allah sarki dole kiyi bacci Khaleesat kinsha wahala yo akwai ma wadda ya isa baraki da d'iyar nan ji irin wahalar data sha ace wai kuma aba wata a matsayin jaririnta wannan ai rashin imani ne ma" shi kuwa Malam fita yayi yana son kiran mijin nawa kana kan danna number d'insa ne shi kuma ya kira sosai Malam yayi murmushi yana cewa "d'an halak" d'aukar wayar yayi yana mai Albishir d'in haihuwa ta sosai yayi farin ciki yana zaune a Office d'insa dake garin Abuja dan kuwa baya Kano cike da tsanin murna yace "Abba toya ita Khaleesat d'in" da y'ar kunya ya ida maganar dama haka nan yau ya tashi da son jin yaya nake Malam yace "tana nan lafiya lau take kilama a sallame mu yau" da sauri Alhaji Mustapha yace "a'a Abba kyau ace a bata duk wata kulawar data dace kamin a sallame mu nima insha Allah yau-yau d'in nan zan taho" cike da ganin kimar sa Abba yace "karka damu lafiya take fa kayi zaman ka ka gama abinda ya kaika a tsanake dan kuwa suna cikin koshin lpy" shi dai Alhaji Mustapha amsa mai yayi da to amma baya jin zai iya kaiwa wani lokacin baije ya ganni ba shi bata yarinyar yake ba ma dan kuwa tunda ya fara gani na a duniya Allah ya samai k'aunata ba y'ar kad'an ba tabbas yasan wannan k'aunar daga Allah ce.
Bayan sun gama wayar Abba ya komo d'akin a yanzu ina zaune sai kallon jaririyar nake sosai nake jin k'aunar ta a raina sosai nake jin jikina yanzu normal shima Abba ganina a zaune yasa shi k'arin wani farin cikin su Haneefa sun tasa yarinyar gaba sai kallo suke cike da sonta a ransu ba'a wani b'ata lokaci ba akai mana duk abinda ya dace aka sallame mu muka nufi gida,
Abunda ya bamu mamaki shine isuwar mu gida muka tadda wata arniyar mota ta paka k'ofar gidan namu cike da d'an mamaki muke kallon motar su Hjy Sa'adha dake kallon ganin cewa kamar na haihu yasata fitowa ba shiri cike da tashin hankali ganin sune yasa na k'ara rik'e yarinyar dake hannu na dan kuwa Gwaggo ce tace a bani taji d'umin jikina kamin su isa gida ganin su Haneefar sai zumud'in d'auka suke da rashin sani su Gwaggo ke kallonsu ganin yadda nayi yasa Gwaggo gane ko su waye dan kuwa Gwaggo tasan takan duniya bamu taho da Malam ba dan kuwa yaje amsu mana wasu magunguna ne Dr Aysha ma fitowa tayi kai tsaye waje na suka taho da sauri Gwaggo ta shiga tsakiya tana cewa "kai ku kuma daga ina haka?" ta idasa maganar tana masu kallon uku saura Dr Aysha tace "ke Malama ke kuma a suwa har zaki tare mana gaba ba amsar yarinya muka zo ba da sannu dai zamu amshe ta zuwa mukai domin mata gargad'i cewa inta sake ta tako k'afarta cikin gidan Alhaji Mustapha wai a matsayin mata to kuwa kamar tazo cikin kabari ne" ta idasa maganar tana kallon fusk'okinmu ganin ba wani tsoro ko d'ar yasa tasha jini jikinta ni kuwa nakai makura zanyi magana Gwaggo ta d'aga min hannu tace "barni dasu Khaleesat kece marar kunyar kenan dan nasan ba ke bace Sa'adar ba kuma amsar d'iyama hakan ma bai taso ba dan kuwa uban kuturu yayi kad'an bare na makaho dan kuwa mai amsarta saiya shirya" ta idasa maganar tana kallon su ido cikin ido ta k'ara cewa "to iya abunda zaku fad'a kenan? gidan Alhaji Mustapha kuwa ai kamar ma ta shigo ne da yardar Ubangiji dan Allah abinda nake so naku shine inkun cika y'an halak karku barta da rai a ranar data shiga gidan kunji ku har wasu mararsa kunya ne baccin rashin ta ido...... Kamin ta idasa maganar Hjy Sa'adha ta tako har inda take ta tsaya kanta k'erere tace "dakata Malama baki kai na tsaya ina cecekuce dake ba ke kuma" tana kallon na ta k'ara cewa "Allah ya baki ikon shigowa gidana badai had'a kishi dani ba hmm" da sauri Inna gaje tace "ke kuwa baiwar Allah miye a cikin kishiya ai abokiyar zama ce" da sauri takai duban ta ga Inna gaje ta wani yatsine baki tace "a wajanku ko gidadawa in...... Kamin takai maganar su Haneefa sunzo kanta domin mata bugun tsiya da sauri Gwaggo ta tsayar dasu tace "barsu tukun badai rashin kunya ba ke yanzu bamu haifeki ba har ki tsay kina gaya mana magana kuma gidanki Khaleesat wallahi kamar ta had'a miji dake ne kiyi duk abinda zakiyi" da sauri taja Khaleesat tace ku shige gida da sauri Khaleesat ta shiga gida domin kuwa ta gaji ganin cewa kamar gidan suke nufin shiga yasa Gwaggo dakata wa dan kuwa har mutane sun fara taruwa Hjy Sa'adha ta d'aga murya yadda zan jiyo tace "wallahi Khaleesat gargad'i ne inkinji ma kanki kika taimaka in..... Kamin ta idasa maganar Gwaggo tace "ke dalla can dakata nace ank'i a amsa gargad'in naki nace ank'i amsar kiyi duk abinda zaki harsai kinzo kina wani gargad'i ashe baki yadda da kanki ba aikin banza kawai kanki aka fara kishiya ne" bud'e baki zatai domin zagin Gwaggo da sauri Gwaggo tace "wallahi na rantse da wadda raina ke hannunsa kika zage ni kamin kibar garin nan k'ila sai kin fita da fashashshan baki kuma tunkan nasa ayi muku wulak'anci cikin garin nan kuzo ku kama gabanku" ta ida maganar tana nuna masu hanya ganin cewa fa da gaske take yasa kwafa sukai suna jinjina kai suka shiga mota suka bar wajan su Sakina dake huce na b'acin rai Haneefa tace "haba Mama ai dakin kyale mu dasu wallahi" Gwaggo tace "ku bakuda hankali hakan ma nasan sun shak'a yau k'ila sai ta kasa bacci" su duka shiga sukai cikin gida sadda zasu shigo har Inna gaje tayi min wanka da ruwan zafi sosai dan ita gida ta shigo taga wa'innan matan bafa kunya ne dasu ba koda Abba ya dawo bamu sanar dashi komai ba.
A wajan su Hjy Sa'adha kuwa kuka take tace "haba Dr Aysha yanzu Alhaji bai jawo min raini ba kamar ni ya rasa wazai auro sai waccan barzar yariyar kuma wallahi d'iyar data haifa harna ji ina sonta tunda jinina ce" da sauri Dr Aysha tace "kindai ji biya ce kima cireta a ranki dan kuwa yace indai kikai gigin amsar yarinyar to kuwa a bakin auranki kinga yanzu wani shirin zamuyi sai ta shigo tukun ki daina kuka haba kina bada mata wallahi" Suna cikin maganar wayar Hjy Sa'adha tayi k'ara da sauri tace "kingani shi ke kira bari naji mi zaice Kuma" d'auka tayi ya sanar da ita cewa "gashi a hanya taji haihuwar Khaleesat kuwa" tsaki taja tace "to sai mi inta haihu kaike rawar k'afa kanta wallahi Alhaji kaji tsoron Allah ina ruwana da haihuwarta" katseta yayi da cewa "ke ko keda ruwa ko kin manta abinda kikai ne" katse kiran tayi tana tsaki tana cewa "harni zakace da wani ruwana wallahi na tsani yarinyar nan nayi dana sanin saninta a rayuwa" da sauri Dr Aysha tace "haba Hjy Sa'adha ki daina sa abin a ranki duka nawa take wai Khaleesat d'in" nan taita kwantar ma da k'awar tata hankali inda tayi mata Albishir d'in shirin da zasuyi nan gaba.
A wajan Alhaji Mustapha kuwa juye yake cike da rashin son magana dafe yake da kanshi kwata-kwata baya son hayaniya bud'e idanuwansa yayi masu matuk'ar haske yana taune bak'in sa mai d'auke da jan leb'e lallai saifa ya tashi tsaye akan Hjy Sa'adha inba haka ba akwai matsala ga d'an banzan kishin tsiya sufa mata indai akan kishiya ne babu abinda basu aikata ba sai sunzo sunyi abun suyi nadamar da bata sa anfani tunani yake sosai wadda isarsa Kano kenan kawai saya cema drivern su wuce Kankia dan inya ce zai sauka gida yanzu k'arin wani b'acin rai ne zai tadda.
Ni kuwa sosai aka shirya ni dan ya gayama Abba cewa gashi tafe ya kusa isowa nidai bazance wai ina son Alhaji Mustapha ba bazan kuma bazan iya zama dashi ba yanzu ne ma nake jin zan iya bugawa da Hjy Sa'adha indai akan yarinyata ne ina cikin tunani Sakina ta shigo tace "Khaleesat yafa iso yana parlon Abba ke yake jira ba dad'ewa zaiyi ba" gaba na ne ya hanye ya fad'i har saida na dafe k'irjina da sauri Sakina ta zauna kusa dani tace "ki kwantar da hankalinki ki fuskanci mijinki dan Allah karki nuna cewa baki ra'ayinsa domin kuwa zaki k'aryar mai da zuciyane yaji cewa shi kad'ai yake kid'in sa yake rawar sa ki nuna mai cewa kema fa kina sonsa dan Allah kinga kina da kishiya in kika tsaya jan aji to tabbas ta nan kishiyarki zata amshe mijin kina ji kina gani" da sauri na kalle Sakina yadda take sako zance kamar wata tsohowa ai indai sunyo gado daga wani halin Gwaggo dole su iya zaro zance tashi nayi jikina a sanyaye nace "Insha Allah Sakina zanyi yadda kikace" tashi mukai mu duka muka fito d'akin Inna gaje mukaje tana goye da yarinyar muna shiga tace "da yanzu nake shirin kai miki ita dan Alhajin yazo kuma kinga jikar tawa bata da rigima" amsarta nayi kawai Inna gaje ta k'ara cewa "ni Sakina fatan da muka fito kun kaimai abinci nan da lemo?" Da sauri Sakina tace "muna gaisawa dashi aka kaimai" ashe har sun gaisa dashi ma ni kad'ai yake jira cikin zuciyata nake magana.
Har k'ofar d'aki Sakina ta rakani sana ta juya kamar ince tazo mu tafi tare haka naji Abba kuwa da tun d'azo ya fice domin bamu waje shiga d'akin nayi da sallama muryarsa mai matuk'ar sanyi da taushi ce tamin amsa kuwwa a kunne numshe ido nayi jin wani masifaffan kamshi dake tashi a d'akin wadda yake fitowa daga jikinsa sanye yake da shadda ruwan k'asa ba k'aramin kyau tayi mai ba gani nayi ya k'ara min wani masifar kyau da kwarjini kallo na yake shima da idanuwansa masu matuk'ar kaifi ganin irin kallon da yake min yasa jikina fara y'ar rawa zama nayi a k'asa domin kuwa indai ban zauna ba to tabbas zan iya fad'uwa mudun idanuwan nan nasa na kaina bakina da yayi nauyi da kyar na iya bud'e sa ina gaida shi da sauri ya matso kusa dani yana mik'a hannu in basa yarinyar cike da wata irin masifaffiyar bugawar zuciya kusancin da muka samu dan kuwa muna iya jin numfashin juna da sauri na mik'a mai yarinyar wajan amsarta hannunmu ya goge na juna wani iri mukaji a jikinmu mu duka dayasa da sauri na janye hannun nawa murmushi yayi ganin yadda kwata-kwata nak'i sakewa dashi matsoni ya k'arayi da sauri na d'aga kaina ina kallon kyakkyawar fuskar sa da sauri kuma nayi k'asa da kaina dan bazan iya kallon cikin idon nan nasa ba banyi aune ba naji ya kaimin kiss a goshina yana cewa "Allah yayi miki albarka" samun kaina nayi da amsawa a cikin zuciyata ga wani irin yanayi da nake ji kusancin mu dashi wani abu nake ji tundaga tafin

Chapter 8 of 11