Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 11
rufin asiri amma gidan su Haneefa ai masu kud'i ne Wannan kuwa ba wata tsiya sai rab'e-rab'e, shi yasa data shigo gidan da bata tab'a zaton zata samu hutu irin gidan su Haneefa ba shi yasa take so ta kanenaye komai harso take ta aje iri a cikin gidan.
Shirin biki suke ba kama hannun yaro tunda suka sauka Haneefa bata k'ara ganin Narnah ba illa sai wata y'ar uwar Zuby dake zaune a gidan mai suna Hauwa itace ma suke d'an magana kamar yauma shiri suke zasu wajan party dan kuwa gobe ne d'aurin auran Haneefa dake zaune ko tashi bata da niyyar yi yasa Hauwa tace "haba dai Haneefa naga fa baki shirya ba mi kike nufi ne baki zuwa tunda kuka zo jiya fa baki fita ba" Haneefa kuwa cike da y'ar sakin fuska tace "a'a wallahi kawai dai dan kinyi magana amma tunda muka zo banga ita Aunty Narnah ba fa" ta ida maganar tana tab'e baki da sauri Hauwa tace "wai wannan ai kinyi k'ok'arin biyo ma ai ita haka take itafa burinta inta zo waje saita nuna tafi kowa nan ko ina saita je tana nuna tayi aure gidan hutu hmm kinga na zauna itana baki labarinta ai tukun ma sannu a hankali zaku gane wace ita da yawa gidajan data yi aure irin wannan halin kesa tana fitowa shi yasa kika ga bama magana sosai saboda nidai in naga abu wadda k'arya ne koba dai-dai ba sai nayi magana itada da Aunty Zuby halinsu d'aya shi yasa suka fi shiri" ita kuwa Haneefa data saki baki tana sauraronta ashe haka take ma tafi yadda suke tunani ya ilahi Abba ya d'akko masu jidali a family da sauri tace "amma ita kam bata ji dad'i ba" ta ida maganar cike da jin tsanarta Hauwa tace "ki tashi ki shirya zaku fahimci ta a hankali ai nan keda samun ganinta k'ila sai zuwa gobe ko in zaku koma" tashi Haneefa tayi ta shirya kai tsaye wajan party suka nufa wani saurayin Hauwa yakai su ba laifi wajan ya k'ayatar sai a wajan partyn Haneefa taga Narnah inda Narnar ta kirata Narnah tace "yauwa Haneefa ga wannan" kallon hannuta Haneefa tayi kud'i ne Haneefa ta gyara tsayowarta tace "na miye?" "Kije kiyi lik'i kema ki d'an kankaro mana kima" da sauri Haneefa ke kallonta ah lallai gaskiyar Hauwa tada ce komai tana yine dan neman suna Haneefa a zuci tace kinzo dai-dai wajan sai kuma tace "wallahi Aunty kaina ke ciwo kinga yanzu ma gida zamo koma" zata sake magana Haneefa ta fice ta barta sake da baki Narnah kuwa dake kallon Zuby tace "kinga rashin kunya ko wajan waccan y'ar banzar yarinyar ni zataiwa haka ai kuwa wallahi saina ci ubanta bari muje gidan" da sauri Zuby ta dakatar da ita da cewa "a'a karki ma fara tab'a masu d'iya dan kinsan da wayanta zata iya miki shirrin da zai hanaki zama cikin gidan naso rabo da ita kawai badai munje wajan boka ba kuma yace bai baki ma komai ba kuma zau aiko da tsafinsa kai tsaye " "eh kuma haka ne amma wallahi kinga tunda muka dawo daga wajan bokan nan tunda yayi anfa ni dani gaba na ke zafi" cewar Narnah (Wa'iya zubillahi Allah ka kare mu) Zuby tace "ai na gaya miki shi k'aidarsa kenan nima baki gani ba sai dai na tsaya waje da ace na shiga wannan dajin da kuwa tabbas sai yayi dani nima ba ruwansa da wani rako kayi aikinsa nayi ai" "kedai bari k'awa Allah ya kaimu mu koma gidan".
A wajan bokan da sukaje kuwa yayi yayi ya aika asirinsa daya aikasa sai dawo dan kuwa Malam dai-dai wannan lokacin ma carbi yake ja sunan Allah ne a bakinsa.
KANO
Tunda safe na tashi na shirya Asabe sai jana take cewa zatayi kewata nima dai tafiyar a file ne nake nuna zumu d'i na amma a zuciyata kwata-kwata ta kasa samun sukuni Hjy Sa'adha ce katse min tunani da cewa "Khaleesat ki fito zamu wuce" haka nan dana ji muryarta gaba na ya d'an fad'i tashi nayi jiki ba k'arfi da d'an akwati na muka fito dai-dai wajan parking motaci na gidan saiga Babahr (Alhaji Mustapha kenan) ya dawo daga motsa jiki daga wani b'angare na gidan sanye hake da k'ananun kaya sunyi mai wani mahaukacin kyau da sauri Hjy Sa'adha taje wajan sa tana basa kiss a kumatu ni kuwa dake tsaye wani iri naji haka nan bansan dalili naji ina jin haushin Hjy Sa'adha d'in dan miye zata rink'a yin irin wannan a gaba na a zuci kuwa cewa nake saima fa ta ganni take yi mai irin wannan wani tsaki naji duk abinda nake Babahr na kallo na shifa yarinyar mamaki take bashi kamar wata Aljana kullum k'ara kyau take shifa wani iri yake ji a zuciyarsa game da tafiyar nan ni kuwa k'asa nayi da kaina ganin irin kallon da yake min gaida sa nayi harna fidda ran amsawa naji muryarsa mai taushi ya amsa mai tafiya da hankali ko nima Allah ya gani yana sani cikin wani yanayi gani nake kamar ma da gayya yake shiga mota nayi ina murgud'a mai baki duk yana kallona murmushi ne ya sub'oce mai Allah ya gani yarinyar na birgesa saboda bata da tsoro ko kad'an bayan ya gana da matarsa ta shiga muka fara tafiya dai-dai gilas d'in mota ina hangensa inda yake hana min murmushin nan nasa bansan sadda na sakar mai nawa shi kuwa dake tsaye wani irin abu ne ya dakar mai zuciya dan kuwa wannan murmushi dana yi ashe ya gani ba k'ara min tafiya dashi yayi ba.
Bamu wani dad'e ba muka isa filin jirgi muna zuwa muka tadda Dr Aysha gaisawa mukai dan na tab'a ganinta a gidan muna zaune suna tattaunawa da Hjy Sa'adha aka fara kiran sunayan fasunjoji tashi mukai muka matsa ni kuwa sai yanzu ne hantar ciki ke kad'awa dan kuwa tsoron tashin jirgin na fara ji haka har aka zo kanmu tare muka zauna waje d'aya da Dr Aysha sai Hjy Sa'adha kuma daga bayanmu Dr Aysha ce ta tamin komai daya kamata da yake sanarwa a jirgin zai tashi nanfa ne na runtse idanuwana ciki na na wata irin masifaffiyar juyawa sai da ya gama dai-daita sana na bud'e ido na ina sauke ajiyar zuciya wai yau nice a jirgi Dr Aysha kuwa sai dariya take min tace "kinga nima kwanan nan na saba da tashin jirgi da saukar sa kema haka zaki saba" ni kuwa ji nake anya zan iya sabawa kuwa dan ba k'ara min tsoro naji ba kai inba ikon Allah ba waya isa ya iya tada jirgi harya tsaya a sararin samaniya wani irin tsoron Allah ne ya k'ara shiga ta................✍️
*Niko Zahra nace Allah sarki Khaleesat ga marassa tsoron Allah nan tare dake dan kuwa wannan yafiyar itace mafarin k'addarar to komi zai faru*🤔
*FATEEMAH RABI'U (ZAHRA ROYAL STAR CE)*🥰✍️
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
[9/9, 10:53 AM] ZAHRAH ROYAL STAR 🥰: *🤦‍♀️💔ITA CE K'ADDARATA 🤦‍♀️💔*

*©ZAHRA ROYAL STAR CE🌟✍️*
*ROYAL STAR WRITIN'S ASSOCIATION*
PAGE3️⃣3️⃣➡️3️⃣4️⃣
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI
Koda suka tashi daka wajan partyn suka koma gida basu tadda su Haneefa ba Narnah taitai fad'a tana cewa Zuby "kinga yariyar ni zata rainawa hankali ko kinga fa ba gida suka taho ba" ta ida maganar rai a b'ace Zuby dake Shirin magana sai gasu da kaya nik'i nik'i da sauri Zuby tace "wai Hauwa daga ina kuke ne?" "wallahi mun d'an je wani waje ne nida saurayi na ya d'an mana sayayya" cewar Hauwa ita kuwa Narnah harara Haneefa tayi wadda tayi kamar bata ganta ba tace "yanzu Haneefa keda kika ce gida zaki baki lafiya shine zaku kwashi k'afa ku fice daga wajan ko magana babu" ta ida maganar tana kallon Haneefa dake latsa wayarta ajewa tayi tace "to Aunty Hauwa ce tace dan Allah na rakata ki tabbaye ta kiji da gida zan wuce ai" ta ida maganar tana kallon Hauwa gyara zama Hauwa tayi tace "eh nina ce ta raka ni bansan tafiya da saurayi ni kad'ai a mota gudun matsala" nan dai Narnah badan ta yarda ba suka watsar da maganar.
Washe kuwa tunda k'arfe d'aya dai-dai aka d'aura auran inda gida ya cika da mutane Narnah sai wani iyayi take inda Haneefa taji dangi sai fad'a akewa Nanar cewa tunda tazo bata je ta gaida y'an gidan su ba bare taje wajan uwarta ita dai Haneefa a zuci tace komi za'a je a gano gidan naso inba tsiya ba taya za'ai ace kana gudun gidanku Hauwa ce ta katse mata tunani tace "kinji ko yanzu abunda yasa bata so taje gidan nasu dan karki ga wane irin gida ta taso hakan ba dai-dai bane wallahi" tab'e baki Haneefa tayi tace "yoni Allah na tuba ina ruwana ma da irin gidan data taso to" "kema kya fad'a" cewar Hauwa, tashi sukai suna sa ankon da Hauwa ce ta bada aka d'inka ma Haneefa dan kuwa Narnah ba abinda ta bata game da abinda ya shafi bikin shi yasa sun shik'u da Hauwa har number juna suka amsa washe garin ranar suka shirya domin komawa Kankia inda Narnah cike da farin ciki take zata koma domin cika burinta.
Ai ko zuwansu gida asiri gaskiyar mai shi dan kuwa Malam sake yayi da addu'a ana hidimar wani d'an d'an abokinsa komi a hannunsa yake to da way wannan damar boka yayi anfa ni ya turo anjani yasa masa kasala daya fara azzakar d'in sai bacci mai nauyi ya kwashe shi tunda asirin ya kamasa yake anbaton sunan Narnah su Gwaggo kuwa suna ganin abu Gwaggo ta kira Laure hankali a tashe bayan su Haneefa sun dawo wani sabon abu da Narhnar ta tsuro dashi shine hana sa kwana a d'akin ko wacce mace sai ita tabi ta nainaye komai sai abinda tace Inna gaje kuwa tasha kuka cikim d'aki sai dai Gwaggo da yake itama y'ar duniya ce sai bata nuna komai ba.
Zaune suke da Laure da Gwaggo cike da tashin hankali Gwaggo tace "Laure akwai fa matsala gaskiya kinga kud'in nan da aka turo min na aikin Khaleesat ki amsa kije wajan Malam yayi mana saukar al'k'urani ya bamu taimako dan wallahi ni bazan koma shirka ba barni dai da wani abun amma kam banda bin boka yanzu dan wannan matar bata da imani" Laure kuwa tace "ai wadda na amso miki fa bai k'are ba ki cigaba da anfani dashi muga ni" itama ta ida maganar cike da damuwar aminiyar tata da sauri Gwaggo tace "haba Laure abun nan fa yi ake ba wani ci gaba ni wallahi na gaji" "haba k'awa kinsan fa komi d'an ahankali ne shifa aikin Allah bada gaggawa yake yinsa ba gaggawa ai sai bokayan sune zasu yima aiki sha yanzu magani yanzu shi yasa mutanan da basuda hakuri suke fad'a halaka ai" cewar Laure Gwaggo kuwa cike da sanyin jiki tace "hakane kuma amma waccar matar lallai sai naci uwarta wallahi in...... Tunkan ta idasa taji ihun Haneefa da suke waje ai da sauri jar tana bangaje Laure tayi waje Laure na binta sakin baki tayi tana kallon Narnah dake huce ta gama marin Haneefa ga Malam dake tsaye ya kasa komai da sauri ta matsa kusa tace "ke Haneefa miya faru ne?" Kuka Haneefa take ta kasa magana sai Sakina nace dake wankin Narnah da sauri takai dubanta wani irin ashar ta danna tana cewa "kan uban can wanki tasa ku ku kuma da yake shashashu ne sai ku zauna ta saku aiki" Malam ya katseta a tsawace yace "ni ne nan nasa suyi inba hakaba inci ubansu a gidan nan miye aikin su to in basuyi bata ba" Gwaggo data saki baki da hanci data kallon Malam ah lallai bokan Narnah ya iya aiki da sauri Gwaggo tace "maza maza ku tashi daga wankin nan ku wuce d'aki naga ubanda ya isa tsayar daku koke kika haifar min yaran ne" tana doban Narnah dake wani yatsine baki d'aga hannu zatai ta k'ara marin Haneefa dake tashi tana hararr ta da sauri Gwaggo ta rik'e hannu tana d'auke ta da nata Marin "kai kai ni kika mara" cewar Narnah Malam daya d'aga hannu zai kaiwa Gwaggo mari da sauri ta rik'e hannu tana cewa "an mari ki d'in kiyi duk abinda zakiyi kin manta ni ne wallahi bana barin bashi ki kiyaye ni wallahi" juyowar tayi wajan Malam dake huce an marar mai mata tace "kai kuma wallahi ka bani kunya ka zama mijinta ce " Narnah kuwa kukan munafirci tasa da sauri Malam duk ya rud'e sai aikin lallashi yake, wani irin takai cine ya ciyo Gwaggo da sauri tasa yaran gaba da Laure dake kallon ikon rabbe koda suka koma d'akin Gwaggo kawai saita zauna a k'asa tana dafe kai da take jin kamar zai rabe gida biyu tace "to Laure kinfa gani irin halin da muke ciki taya za'ai hankali na kwanta ne nan gaba fa indan bamuyi da gaske bafa akwai matsala burin Matar nan fa tasa ya saki kowa ya zauna da ita" ta ida maganar idonta ya kad'a yayi ja da sauri Laure tace "inshallahu ba abinda zai faru zanje kuma a sauke al'k'uranin yanzu dana fita" Sakina kuwa damuwar ta d'aya yanzu tana kiran wayar Khaleesat a kashe hankalinta yak'i kwanciya .
A wajan Inna gaje kuwa duk taji mike faruwa zama ta gyara a d'akinta dan kuwa koda ta fita itama zai iya dawowa kanta tunani take yanzu ne ya kamata ta kira wani Kawonta dan kuwa Malami ne sosai data kyale abun amma taga abun yayi yawa da sauri tad'au wayarta tana danna kiran Kawon nata bayan sun gaisa sai kuma ta d'anyi shuru daga cikin wayar Kawon nata yace "yaya dai Gaje ina fatan dai kuna lafiya a nan?" Sauke ajiyar zuciya tayi mai nauyi tace "wallahi Kawo ina cikin Matsala nida uwar gida na kasan Malam ya k'aro aure to matar tasa hatsabibiya ce" nan ta koro mai jawabin komai cike da mamaki Kawon yace "amma duk tsawon wannan abun baki kira kin gaya ba ai irin wannan ba'a wasa dashi kuma da alama kuna wasa da addu'a Insha Allah zanyi iya bakin yina wajan taya ku addu'a zan baki wata addu'a zan rubutu miki ta waya in turo tunda kinga munyi nisa ki rink'a ba Malam a abinci ko ruwa kina addu'ar kina tofawa kiyi na kwana bakwai insha Allah za'a samu waraka da yardar Mai sama" cike da farin ciki Inna gaje tace "insha Allah Kawo zanyi yadda kace kuma zamu dage da addu'a Insha Allah" sallama sukai ba'a wani dad'e ba ya turo mata addu'ar tama san addu'ar sake ne kawai datayi amma Qur'ani ai waraka ne ga komai.
Tunda ga wannan rana da kyar Inna gaje ke samun damar ba Malam addu'ar dan kuwa Narnah na manne dashi kullum sai in ta fita yawonta wadda yanzu take ba neman izinin mai gida tunda sai abinda tace shi kansa Malam can k'asan zuciyasa yana jin abunda yake fa ba dai-dai bane amma data bashi umarni jikinsa har kyarma yake wajanyi mata har ciki tace tana shi kuma na k'raya ne tana cin kud'in Malam d'in Inna gaje da Gwaggo kuwa basu fasa addu'ar su ba kullum.
ABUJA
A wajan mu kuwa nidai tunda muka sauka Abuja inata kalle-kalle yadda Abujar ta birge ni dan kuwa Abuja tayi min kyau kamar wata k'asar waje taya za'ai shugaban ninmu suna zama a irin wannan waje harsu tuna da wani talaka ina Abuja batada wani banbanci da wata k'asar wajan kalle-kalle nake kamar ba'a Najeria nake ba sai dai mi tunda muka shiga mota na shak'i wani abu ban k'ara sanin inda kaina yake ba, su Hjy Sa'adha da Dr Aysha tace "yaya dai Dr fatan tayi baccin?" Cewar Hjy Sa'adha Dr Aysha tace "tayi mana ai bata gama nina shik'a mata maganin ba tana can kalle-kalle na k'auyanci" dariya suka saki isarsu asibitin ba'a b'ata wani lokaci ba dama mu ake jira aka shiga aikin dani da bansan inda kaina yake ba hawa uku sukai sana likitocin suka fito suna sharce zufa da sauri yace ko biyo Office koda suka shiga zama sukai Hjy Sa'adha na cewa "Dr fatan dai anyi nasara?" Dr dake murmushi yace "kware kuwa anyi nasara yanzu ma zaku iya tafiya da ita gida domin karta tashi ta ganta a hospital karta zargi wani abu sana saifa kun ciko kud'i domin abokan aiki na" cike da murna Dr Aysha da Hjy Sa'adha har suna had'a baki wajan cewa "baka da matsala da kud'in ka muke tafe" aje mai mak'udan kud'ad'e sukai sana suka fita daga Office d'in kai tsaye d'akin da aka kwantar dani suka nufa Dr Aysha ce ta d'auke ni sai cikin mota kai tsaye gidan Hjy Sa'adha dake garin Abuja suka nufa dan kuwa Alhaji Mustapha yana da gida a Abuja saboda yawan zuwa da yakeyi ya dad'e yasa shi sayan gida kawai.
Koda muka isa gidan har yanzu ban cikin hayyacina sai wajan dare na farka da wata irin yinwa koda na tashi gani nayi sai wani murmushi suke min da lallab'a ni ni kaina abun yaban mamaki jin wani iri a jiki na sosai nake jin sauyi a cikin jikina koda aka kawo abinci ci nake ba k'ak'k'autawa ni kaina nayi mamakin yawan abincin da nake ci kwananmu biyu a Abuja muka d'au hanyar dawowa amma wannan karan a mota muka d'au hanya a wannan kwana kin wani irin ci nake saina ci abincin mutum uku ko biyu ni kaina abun tsoro ya fara ban sai kace wacce aka sawa macijin ciki ga wata irin y'ar kiba dana fara wani irin haske nayi mai kyan gaske ni kaina nasan na canza.
Sun tattauna da Hjy Sa'adha da Dr cewa gara mu hau mota saboda ni mai ciki kar wani abu ya samu cikin sana in watan haihuwata ya kama zasu tahu dani abujar ita kuma tasan yadda zatayi tacewa Alhaji Mustapha tana ciki sun tsara komai nida bansan mike faruwa ba harkata kawai nake koda muka isa mun tadda y'an rainin wayon nawa basu nan sun fita sai Alhaji Mustapha daya tafi wajan aiki can wajan yamma suka dawo Hjy Sa'adha tana d'aki ina zaune ni kad'ai a parlo suka shigo wani uban birki suka ja gani na a saman kujera yoni nasan ma nahau kan kujerar kallon wani abu da yake a tv shiya d'auke min hankali har yasa na zauna a kujerar nidai da bansan da shigowar su ba kawai ji nayi an cikomo wuyan rigata an d'auke ni da mari ba kowa bace sai Ummeeta Maryam har wani cewa take "kinyi dai-dai ke har kin isa kin rik'a kin kai zama a kujera ko?" Tunkan ta ida magana Hjy Sa'adha dake sakkowa hankali a tashe ta fara zazzaga maso masifa dan mi zasu mare ni ni kuwa dake kallonta bazata iya rama min ba ko lallai ma wani mahaukacin bacin rai ne yazo min dama tunda muka dawo haka nan sai rink'a jin haushin kowa abinda ban sani ba shine wannan cikin da aka samin shi yasa ni nake jin duk wani abunda ban saba jiba wadda bansan da zamansa ba Babahr dake shigowa duk yaji mike faruwa shigowa yayi da b'acin rai zasu tafi kenan sukaji muryarsa yace "ku dawo Nan" wani irin kuka cikin su ya bada cike da tsoro suka dawo inda yake d'aya bayan d'aya saida ya wanka masu mari mai zafin dayasa su sakin kuka Hjy Sa'adha kuwa wani irin runtse idanuwanta tayi tana jin zafin marin daya yi masu zatai magana ya dakatar da ita yace "mi zaki ce magana zakiyi akan mi yasa na mare su ko? Ita Khaleesat d'in ba mutum bace kodan bata da kowa ne iyee" yayi maganar a tsawace cike da b'acin rai itama tace "amma baka ga nayi masu fad'a ba ne wai mi kake nufi ne da Khaleesat d'in?" Da mamaki yake kallonta yace "haka zaki ce kenan shikenan ai daya ke su y'ay'an gata ne dole kiyi magana akan an tab'a miki su" sai kuma yakai dubansa gare su yana nuna su da yasa yace "ku kuma wallahi wallahi na k'ara jin kun shiga koda harkar tane ko magana na rantse duk sai nad'au mataki a kanku dalla can ku tashi ku b'ace min a nan" ya idasa maganar a tsawace da sauri har suna rige-rigen wucewa,
Ni kuwa wani irin kimarsa da darajar sa nake ji wuce nayi kawai shi kuwa bina yayi da wani irin kallo wadda shi kad'ai yasan ma'anar sa Hjy Sa'adha kuwa da wata irin tsanata lokaci guda tayi sama domin kiran Dr Aysha...............✍️
*Wai mike shirin faruwa ne masoya na nima dai ina buk'atar sani, yanzu fa za'a shiga chakwakiya mai zafi mi yake shirin faruwa ne da Hjy Sa'adha🤔 kai kai akwai k'urafa*
*FATEEMAH RABI'U (ZAHRA ROYAL STAR CE)*🥰✍️
Comment and share Fisabilillahi🥰🙏
[9/10, 11:48 AM] ZAHRAH ROYAL STAR 🥰: *🤦‍♀️💔ITA CE K'ADDARATA 🤦‍♀️💔*
*©ZAHRA ROYAL STAR CE🌟✍️*
*ROYAL STAR WRITIN'S ASSOCIATION*
PAGE3️⃣5️⃣➡️3️⃣6️⃣
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI
Fitowa sukai da Nahrnah da Malam sai wani murmushi suke dai-dai sunzo wajan su Inna gaje dake tsakar gida taja Malam suka tsaya Gwaggo kuwa kallon ikon Allah take jira take taji yau kuma da wanne wulak'ancin tazo kamin ta ida tunanin ta taji Nahrnah na cewa "yau Malam maza basu kud'in cefane suyi abincin kamin in dawo inna dawo na raba in..... Kamin ta ida maganar Gwaggo ta tashi a zabure tana cewa "ai wallahi uban kuturu yayi kad'an bare na makahu ke har kin isa ranar girkin kice wai bazaki girka ba sai dai ayi miki to wallahi naga ubanda zai miki girkin Ahh gsky asirin naki harya kai haka to kisani ai bamu duka kika asirance ba shine kadai kika shanye in kin manta in tuna miki" ta ida maganar tana kallon Nahrnah dake kallonta da mamaki Malam ne ya katse masu hanzari da cewa "to baga su Haneefa nan ba su fito suyi gir..... Kamin ya ida Gwaggo ta katse shi da cewa "dakata Malam y'ay'ana ba bayinta bane koko ita ta haifar min sune? dan haka wallahi kama ja mata kunne ta fita harkar yarana ta kiyaye ni ni ba sa'ar yinta bace" tana gama maganar taja yaranta sai d'aki Inna gaje ma tashi tayi tana nufar d'akin dan yaune take so taba Malam ruwan maganin na k'arshe tana gaf da shigewa taji Nahrnah na cewa "kagani ko dear sai da nace ka sawwak'e masu kawai su duka amma da yake kai wani irin namiji ne kagara yi" tsaki taja tana wucewa d'akin ta dan kuwa tayi tayi Malam d'in ya sake su amma cikin ikon Allah zaibi ko wanne umarnin ta amma banda wannan zai bita kenan Inna gaje ta fito da ruwan maganin mai sanyin gaske tace "yauwa Malam ga ruwa kasha samun kansa yayi da amsa kawai yana sha kallonsa Inna gaje keyi cike da tausayin mijin nasu ace wata mata can ta maida masu miji kamar sulub'iyo yana gama sha ya nufi d'akin Nahrnar dan kuwa ji yake in baije ya lallashe taba akwai matsala Inna gaje kuwa murmushi ta saki tace Insha Allah yaune Malam zai dawo dai-dai tsayawa tayi tana tunani ta kasa matsawa a inda take.
Shi kuwa Malam yazo shiga d'akin Nahrnar yaji kansa ya sara kamar an dauke wani abu mai nauyi kallon inda yake yayi miya kawosa d'akin Nahrna to katse tunani yayi jin Nahrnah tana waya da Zuby tana cewa "Zuby akwai matsala fa dan kuwa ina nan tafe Malam asirin nan ya fara sanyi haba har yau ina mai magana yana min gaddama in...... Kamin ta ida maganar taji fad'uwar mutum rigijif a k'ofar d'akin ta Malam ne ya fad'i jin abubuwan ta tayi mai kamar shi ga wani irin jiri da yake ji baiyi aune ba ya fad'i a sume cike da tashin hankali

Chapter 6 of 11